Author : Hadiza D Auta Category : Romance
kai mata".
"Ta kyauta, to sai anjima"
Daga haka ta mikawa Abida wayarta.
Ta gyara ta kwanta. Abida ta mike ta ce "bari na je asibiti sai dare Zan dawo in sha Allah."
Ta dauki jakarta ta fice.
"A dawo lafiya". Asad ya amsa mata babu wani karsashi don sosia ya ji wani iri da ya ji Bilki na magana da yaranta amma shi tunda ta zo asibitin nan bata taɓa bude baki don ta amsa masa ko da sannun da yake yi mata ba. Kuma ta ga ya shigo amma ta bude baki ta ce ta amsa gaisuwar tsohon mijinta.
Sai da Abida ta fita sannan ya zauna a kujerar gaban gadon. Ya ja kujerar daf da ita, ya zauna ya kama hannunta na dama ya rik'e Yana dannawa a hankali. Murya ba amo ya ce "Sannu Maigado" Bata amsa ba, ya sake maimatawa a karo na biyu, maimakon ta amsa da baki sai ta daga masa hannu tabbacin ta ji ta amsa. Takaici ya mak'ure shi tunda ya fahimci tafi tsananta rashin yin magana a kansa.
Ya numfasa ya ce "Na so mun tafi London kin haihu a can. Momi kuma ta ce 'ba zai yiwu ki yi tafiya a yanzu ba'.
"Ba zan iya ba, kuma bana son tafiyar ma".
Ta fad'a a hankali.
Daga haka bata sake magana ba, Duk yadda yake ta yin maganganu na rarrashi da kwantar da zuciya.
K'arshe ma sai ya ga barci ya yi awon gaba da ita.
Ya tsura mata ido abubuwa masu yawa na taso masa a kanta.
Ya fahimci gabad'aya ta hak'ura da shine.
Damuwa ta yi masa ya yawa. Ya rasa inda zai tsoma ransa.
Suna cikinn haka k'iran Yaya Hamida ya faɗo wayarta.
Ta dauka suka gaisa ta yi mata sannu, daga suka yi sallama tunda tasan bata iya doguwar magana.
Mintina biyu a tsakani k'iran Ansari ya shigo, Shima ta amsa, bata ajiye wayar ba na Saddiqa ya shigo, haka ma na Anisa.
Oga Asad yana zaune yana jinsu kowa jikinta yake tambaya tare da fad'a mata ta yi hak'uri ta cire damuwa bawa ba ya wuce k'addararsa.
Ya yi shiru yana nazarin wato Hamida ce Duk ta fad'a musu yau ta samu Bilki shine duk suka k'irata d'aya bayan d'aya amma su basa k'iran kowa a cikinsu hatta Baba kuwa in aka cire Saddiqa da Ansari da su din ma sai an d'auki lokaci mai yawa.
Auren da yake kan Hamida kad'ai ne ya shatawa Oga Asad layin cin mutuncinta amma tabbas ya washeta tamkar yadda ta washe shi. Bata da mutunci ko kad'an. Tunda ya auri Bilkisu ya ga bata zo ba, har yau kuma bata tako ta zo gidansa ba, ya tabbatar da gaske take gaba da shi. Rashin zuwa yi mass ta'aziyar Rukayya bata bige shi ba kamar rashin zuwanta aurensu. Anan ya tabbatar hatta ubansu ma bata ganin kimarsa ko kad'an tunda gidan da yake nr ba zata zo. Shiyasa bai cika zafafawa akan kiyayyar da suka girka masa ba haka siddan, tunda wan ubansu ma bai tsira ba.
Ya kuma yi ammanar ita ta cusa wa k'annenta k'insa don ya yi imani da Allah ita ta zuga Bilki ta so fasa aurensa bisa hujjar baya son uwarsu bai zo musu ta'aziyar rasuwarta ba9baya son yayansu Sulaiman.
A yanzu ba zai ce musu komai ba amma idan Sulaiman din ya bayyana ya ci ubansa a gabansu sa yi a hankali da shi.
A hakan dai ake tafiya ta fara samun sauk'i sosia amma fa babu magana. Baba da Momi da Yaya Faruku kawia take bude baki ta gaishar, suma daga gaisuwar bata sake ce musu uffan sai ido. Su duk suka damu yayin da Abida ta fahimci ba matsalar da sauki tunda tana gaida wadanda ta san ya kamata ta gaishe da su. Oga Asad ne kawai bata gaisarwa, sai kuwa su members. A ranta ta ce yanzu zaka gane Bilki ta fini daru da gaske, ni hayaniya na fita sannan kalata a bayyane take. Amma irinsu Bilki kafin a gane azaabr da suke ganawa mutum ai sai ya kusa shekawa lahira.
Tana kallon yadda idan ya zo yake bare baren yiwa Bilkin magana tare da rarrashi da tambayar me take so ita kuma tana yin biris tamkar wacce ta hadu da lalurar rashin ji. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:11]
Har zuciyarta take dan jin babu dad'i na yadda take yi masa, amma ta yi maza ta cire abin a ranta tana fad'in kun fi kusa, matsalata kad'ai ta ishe ni.
Amma ita da kanta Abida mamakin zaman Farha a wajen Momi take yi. Tunda Bilki ta koma ta ga Farha da Alti na gidan ta tambayi momi akan yaushe zasu tafi ne, gara Farha ta tafi tunda makarantarsu d'aya da Noor. Kuma makarantar tafi kusa da gidan Bilkin. Haka kawai ta fad'aomi ta balbale ta da fad'a ina ruwanta da maganar Farha. Bilki take rikewa ita kafin ta haihu. Ta daina tisa ta a gaba tana yi mata tambayar da ba huruminta ba ne. Guiwa a sake ta bar d'akin Momi tana ayyana tunda zamanta ya yi nisa dole a gundura da ita. Abu kad'an zata yi momi ta yi ta mata sababi. Yanzu Hatta junior idan yana wasan tsaleltsalle momi zata hau fadan ya fitine su, baba baya son hayaniya amma ta bar d'anta ya cika musu gida da k'iriniya. Har ta kai ta kawo matuk'ar suna gida rufe su take yi a d'aki shi da ita tana ayyana Sulaiman ne ya janyo mata ta zama mujiya a gidansu. Ita mamaki take yi wai kuwa ba a canja zuciyar iyayenta a kanta ba?
A yadda take ganin take take momi ba dan kullum tana fita asibiti ba, da sallamar y'an aikinta zata yi. Tunda indai tana gidan bata saka y'an aiki hidima kowacce irice. Komai Abida zo ki yi kaza, Abida je ki wanke mini band'aki, Abida zo ki yi mana girki ni da Babanku. Abida na fi son ki wnake mini kayana da kanki. Abubuwan dai tamkar da gayya, ta tabbatar momi ta gaji da ganinta a gidanta. Bata da wanda take iya faɗawa laifin momi sai Yaya Salaha da take Ibadan a yanzu. Itama hak'uri take bata tare da fad'a mata ta bita a hankali komai zai wuce.
Tun yammaci Bilki ke ta fama da ciwon cikin da ta tabbatar yau kam haihuwa za'a yi ta da ikon Allah.
Da yake tare da Abida zasu kwana sai bata faɗawa kowa ba. Sai dai wajen asuba ciwo ya tsananta hankalin Abida ya tashi ta fara tunanin ta amince a yi amince a yi mata c.s.
Ta shige cikin likitoci asibitin aka fara shirin yi mata aiki. Ana idar da sallar asuba ta kira baba ta fad'a masa halin da suke ciki. Tana kashewa ta k'ira oga Asad ya sanar masa.
A kidime ya ce "Sai da na ce zan tafi London da ita aka ki".
A sanyaye ta ce "Just pray Daddy in sha Allah aikin will be successful."
Daga haka ta katse wayar a dalilin yadda haihuwar ta taso gadan gadan. Nan da nan suka kewaye ta.
Ta haifo yaro kukansa ya cika dakin. Aka yi kokarin rabasu. Jikin Abida ya mutu a dalilin yadda ta ga Bilki ta galabaita Anya zata iya sake haihuwar na biyun da kanta? Tunda ita tasan twins zata haifa tuntuni ta fad'a mata, yanzu kuma da take duba file dinta ta ga ni. Itama kuma bata faɗawa kowa ba, zata taya Bilki bawa family suprise.
Haka dai aka yi ta fama da gurmuzu suka sake tayar mata da nakuda. Cikin taimakon Ubangiji na biyun ya iso duniya.
Shima da kukan ya iso tamkar gyare. Sai da suka kwashe mata jini bayan mabiya ta fito sannan aka yi mata dinki dan kuwa ta samu tear sosai.
Tunda Bilki take haihuwa bata taɓa cin ko da kwata din azabar da sha a wannan haihuwar ba. Sai Dai kuma ana gama mata dinkin da aka gyara mata jiki ta sha tea sai ta ji babu wanccan azabar da ta kwana a cikinta.
Ana kammala shirya yaran Abida da rawar jiki ta d'auki guda d'aya ta fita da shi. Kaitsaye Baba ta mikawa da suke zaune a reception tare da Momi da oga Asad da kuma Yaya Faruku.
Ya karbe shi da Bismillahi ya yi masa addu'a ya duba kunnenta ya ga da duhu ya ce "To wannan bamu bane su baba K'arami aka kwaso" .
Asad bai ce komai ba don kuwa ya fahimci duhun fatarsa ya d'ebo. Wani irin tsuma yake yi so yake ya karbi yaron ya gan shi da idanuwansa ashe dai zai samu boy a duniyarsa? Sai dai nauyin idon iyayensa ya saka ya had'iye zakuwarsa.
Baba ya yi mass addu'a Abida tana Shirin cewa zata basu suprise Kawai baba ya ce "Je ki dauko mini d'ayan Abida".
Da mamaki ta ce "Ai d'aya ne Baba! Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:15]
Ya girgiza kai ya ce "Na kai wata a jere kullum sai na yi mafarkin Bilki ta haifi tagwaye. Tun abin bai shiga raina ba har na gamsu tunda tsohonmu tagwaye ne ya biyo. Haka a dangin gyatumarmu sun gaji haihuwar tagwaye."
Abida ta yi murmushi ta ce "A a Baba to Dai dan d'aya ta haifa ".
Ya jijjiga kai ya ce Idan na yi mafarki na rik'e ban manta ba, sannan na sake yin irinsa to Sai na Ga abin nan a zahiri bare wannan na yi jar na kagu na ga yanbiyu cikin ahalinmu".
Ta murmusa ta ce "To menene tukuicin wannan jaridar Baba?"
Daga shi har ita jikinsu ya yi sanyi a dalilin sun tuna da, don da a shekarun baya ne da saniya ko tunkiya zai bata.
Ganin hakan ya sanya ta juya da sauri.
Yayin da oga Asad ya mik'e tsaye ya kasa zama, gabad'aya sai kai komo yake yi, tare da tunanin dama Bilkisu da Babanta har ma da Abida sun sani shine ba wanda ya taba fad'a masa. Ikon Allah yake ta fad'a a fili a k'asan zuciyarsa kuwa hailala yake yi tare da istigifari.
Haka ya hango Abida sabe da sabon jariri lullube cikin shawul irin na d'anuwansa. Tabbas Bilki ta san twins zata haifa tunda ga kaya nan iri daya a jikinsu tabbacin an yi musu shiri. Kai wannan shine mafi girman ba zata da aka yi masa da bai taba jin dad'i irinsa ba.
Baban ta sake mikawa ya ce wanne ne babban kenan?"
Ta nuna wanda ta kawo yanzu. Ya ce "To Abdallah ne ga kuma Abdulrahman".
Abida ta ce "Baba gaskiya ba haka za'a yi ba, ka yi mini alfarma nima na yi iko irin wanda Bilki ta gwada mini akan sunan junior ".
Murmushi na sosai Baba ya yi tare da fad'in "Ho Abida".
Dad'i ya ratsa ta don kuwa rabin da ta ga wnanan murmushin na gaskiya a tsakaninta da shi tun komai bai taɓarbare musu ba.
Ya yiwa wanda ta kawo addu'a ya duba kunnensa shima ya ce "A a wannan ma baya bangarenmu duk kune Abida. "
Ta ce gara da ya biyo mu ai Baba, don kun fimu yawa."
Daga haka aka bawa Momi ta gansu sannan aka mikawa Yaya Faruku.
Abida ta ce "ABBA duba ka ga wadannan layinmu ne ba naku ba."
Ya karɓa da Bismillahi tare da kurawa yaron ido yana mamakin fuskar oga Asad akan ta yaron. Haka da ya duba d'ayan ma sai ya ga dukkansu kama suke da junansu irin sosia din nan, tamkar babansu ya yi kakinsu.
Ya yi musu addu'a. Ya kalli Abida ya ce "Wanne sunan za ki saka musu rigimatu?"
Ta ce "Sunan Baba Babba da Baba K'arami zasu amsa.
Dukkansu har baba da Momi na wanda ya tanka tabbacin sun aminta da ra'ayinta.
Faruk da kansa ya kaiwa Momi yaran. Ita kuma ta rik'e Su a jikinta.
Baban Bilkisu tamkar ya je ya karbe su ya gansu Amma ya daure ya cije ya yi jarumtar kawar da kai. Amma k'asan ransa ba k'aramin takura ya yi ba.
Har aka dawo da Bilki ainihin d'akin da take kwance suna asibitin Basu tafi ba. Gabad'aya suka dunguma zuwa d'akin don yi mata sannu.
Tana zaune ta shirya tsaf tamkar ba itace ta tsallake siradi ba
Sannu suke ta yi mata, tana amsawa a hankali.
Abida ta ce "Yanzu me yake yi mini ciwo?"
A hankali ta ce "Ciki amma ba sosai" .
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Dan Allah ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Sanyi flusher kuwa best seller ne*
*Just DM for your order @08033773332*.
"Sannu zai daina tunda an yi miki allura. Yanzu bari Ki ci abinci ki sha magani sai ki kwanta ki huta".
Abida ta fadi hakan da kulawa.
Momi ta mik'a mata yaranta cikin tufafi iri d'aya farare kal.
Ta noke ta k'i karɓa ta ce "A a zan gansu ne momi".
Asad ya ji wani iri Ashe da gayya Shi ta ki ba shi yaran. Momi zata sake da kowa amma ban da shi har yanzu bata ware da Shi ba. Zata yi hira da Faruku tamkar ta goya shi amma shi indai ta ja doguwar magana a tsakaninsu laifi ya yi. To nan kam ta dinga yi masa fad'a tare da yi masa jirwayen Faruku ne dattijo mai halin manya. Kai Hausawa da kuttu suke Wallahi. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:18]
Idan ka zo a dan fari a shekarun baya kana cikin talajaurar duniya. Daidai da sunanka uwarka mahaifiya ya haramta ta fad'a kaitsaye. Har ya yi aure wannan yaron take ce masa. Sai da y'ay'ansa suka fara girma ne ta koma cewa yayanku. Amma da kunnensa bai taba jin ta ce Asad ba, kai ko Abubakar ma bata fad'a.
A ransa ya fara jin takaicin zamowarsa dan fari dama Faruku ne babba ba shi ba.
Ya numfasa tare da auna banbancin iyayen da na yanzu. Y'ay'an yanzu don sun zo a farko iyaye mata basa yin alkunya a gaban kowa suke nan da nan da su ko da kuwa a gaban iyayensu ne ba ruwansu.
Muryar Abida ta katse masa tunaninsa da ta ce "Ya kamata su sha nono, dazu basu sha sosia ba."
Ta kalli inda Asad yake zaune a takure ta san kuma ganinsu Baba ya hana shi sukuni. Ta karbi yaran a hankali tare da fad'in "Bari Dady ya Gansu momy ".
Cikin nutsuwa ta bashi Su sannan ta ce "Ga Baban Abida da Baban Munira nan Allah ya raya su."
Bilki bata ce komai ba, jikinta ya gama bata matuk'ar ya tabbata maza ta haifa to kuwa Sunan da zasu amsa kenan. Amma a yadda Abida ta ce Babanta da na Munira ta fahimci so take ta gane itace ta zaba musu suna. Don a da da suke yara idan ta so bakanta mata sai ta ce "Baba Babba babanta ne Baba k'arami kuma na Yaya Munira ne ita yar rik'o ce daga danginsu baba shiyasa take kama da shi". A lokacin Bilki ba wayo sai ta yi ta kuka. Baba K'arami kuma ya gasgata batun Abida na cewar rik'o aka kawo ta gidan.
Bilki ta girgiza kai tare da murmushi kadan Abida ta yi tsiyataku mata kala kala.
K'asan zuciyarta kuma zargi take yi itama iko ta nuna mata kamar yadda itama ta nuna mata akan junior.
Zata yi magana Kawai hankalinta ya kai Kan talabijin din da take makale a jikin bango inda tashar T.V.C News ta rubuta breaking news. Hankalin Bilki ya raja'a ta mayar da hankalinta kan talabijin din. Tabbas ba gizo idonta yake yi ba. Sunan dai shine babu kuskure. Ta kalli y'an d'akin duk hankalinsu ba ya kai, mussaman oga Asad da yake rungume da yara yana ta faman kallonsu. A ranta ta ce "Ya tisa yara a gaba da kallo a gabansu Momi.
Bakinta ya yi nauyi ta kasa fad'in komai kawai ta fara nuni da hannunta izuwa talabijin din.
Hankalinsu ya kai kan fuskar talabijin din don ganin abin da take yi musu nuni.
Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 10:49]
*Surayya Dee*
*08032773332*.
*Wannan littafin na kudine*
*Ga mai son biyan hak'kin wahalata 1k ne*
*2384876855*
*Zenith Bank*
*Surayya Ibrahim*
*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*
*Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.*
*07036662633*
*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*
Asad Musa Funtua as A.I.G of the Federation.
Haka aka dinga jero sunayen wadanda suka zama A.I.G. din. Baba Baban sai hamdala take yi yayain da momi take addu'ar fatan alheri, da fatan Allah ya yi riko da hannayensa. Faruku kuwa yana bude baki ya ce "In sha Allah dukkanmu nan sai mun ga ka zama I.G gabad'aya."
Oga Asad kuwa Alhamdulillahi yake ta fadi a zuciyarsa da kan harshensa. Yau ranar ta mussaman ce a kundin tarihinsa.
Twins da k'arin girma duk kuma sun zo masa a bazata k'warai da gaske. Blessings bi da bi.
Farinciki da zumudinsa basa boyuwa, kowa ya gane ya jarrabu akan yayan nan tamkar yanzu aka fara yi masa haihuwar. Bilkisu ta sake gasgata shi mai son ya'ya ne matuƙa don idan ya zo har ya tafi suna jikinsa yana yi yana duba su. Paediatric daban daban ya sanya suka duba yaran aka tabbatar masa lafiyayyayu ne. Amma duk da hakan idan ya dauke su sai ya dudduba jikinsu tare da bude idanuwansu don ya sake tabbatar basu da shawara(joindince).
Kwanaki biyar ta k'ara suka sallame ta tunda jininta ya daidaita sannan yara lafiyarsu k'alau.
Tana isa gidan ta tarar da ko ina stickers mai d'auke da welcome to the world twins. Ga balloons. Ko ina haske ke tashi wal wal a duka kusurwaowin gidan cikin da waje. Sosia abin ya k'ayarta da Bilki.
Tana hawa samanta kuma ta ga falonta tsadaddun stickers mai dauke da welcome to Home Mahmah. Idonta ya cika da k'walla don sai take ganin Amrah, Faruk da Farha ne kad'ai zasu yi mata irin haka. Ga shi kuma nabu su a tare da ita. Zuciyarta ta harba lallai Bilkisu ce zata yi hakan don kuwa Amal da Noor ba su kawo k'arfin yin haka ba.
Ta juya ta ga Bilkisu