DINGISHIN KWADO 3 COMPLETE BY D Auta.txt

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   27 / 50

78K to 81K   out of 149K words

tambaye ta dalili, bayan dalilin a bayyane yake tunda ta baro Sulaiman junior ai kinsan ba lafiya."
Momi kuwa ta hau kai ta zauna ta dinga yi mata fadan ta rage ƙulafuncinsa. "Me zai same shi? Yaro yana ta harkokinsa amma ke kin takure zuciyarki haba me za'a yi ne da rashin kawaicinki akan yaron nan."
Kan dole ta yi shiru aka tafi a haka.
Amma gabad'aya nutsuwar zuciya ta yi mata tutsu. Yaya Farouk kadai yasan damuwarta duk da shima a rikicen yake.
Washegari tun safe Abida ta tafi masallaci bata koma ba sai yamma bata ga wanda ta je nema ba.
Haka ta daure don gobe ne zasu je asibiti.
Washegari sai dare suka je asibitin. Aka fara yiwa Baba gwaje gwaje da na'urori daban daban. Har asuba suna asibitin. Wajen takwas suka koma hotel dinsu akan da daddare zasu koma asibitin sannan dukkan sakamakon gwajin sun bayyana. Abida da Baba suna zaune gaban likita yayin da Momi da Yaya Farouk suke waje suna dakonsu.
Komai na baba na tafiya daidai Sai dai dole zai dauwama yana shan maganin hawan jini. Sai kuma idonsa d'aya da dole sai an masa aiki an cire hakiyar da take son mamaye idon . Dan haka likitan ya ce su je b'angaren ido su ga likita sannan a basu ranar da za'a yi aikin.
Likitan ya yaba da hazak'ar Abida har yana mata tayin zai bata takarda ta cike zasu debi likitoci mata a bangaren gynecologist. Don sosai ya gane hazik'ar likita ce.
Ta yi godiya tare da gabatar da uzzirin k'asarta Nigeria na bukatar irinta.
A hanyarsu ta komawa gida suna cikin mota momi ta ce "Ni kam ba dan za'a ce gizo idona ya yi mini ba da na ce tabbas na ga Sulaiman."
Abida ta yi fit ta ce "A ina kika gan shi?"
Momi ta bata amsa da fad'in a asibitin amma shi bai ganni ba, don nima bayansa na ga ni yana sanye da rigar likitoci yana tafiya da sauri gilmawarsa na ga ni, da farko kamar yayanku(Asad). Kunsan tafiyarsu iri d'aya ce, sai kuma na ga gefen fuskarsa kafin na ankara ya b'ace mini, lokacin Farouk ya je siyo magani ke kuma kin koma ofishin likita d'auko gilashinki".
Baba ya ce "Sulaiman nawa kike magana?"
Momi ta ce "Shi fa Alhaji!
Ya ce "Ai kuwa idan har shine k'afata k'afarsa da shi zamu koma gida."
Abida tana son ta ce suma sun gan shi amma tunda bata ji Yaya Farouk ya ce ya gan shi ba, ta daure ta yi shiru.
Hankalinta ya tashi ainun domin a yanzu take dandana azabar soyayya da alamu shi kuma ya shafe ta tunda ya ganta amma ya arce saboda baya ko son ganinta.
"Farouku ka k'ira yayanku ya tuntubi abokin nasa da yake aiki a asibitin nan a bincika mana idan Sulaiman Isa Funtua a asibitin yake aiki yasan yadda zai yi ya kawo mini shi gabana".
Baba Babba ya fadi hakan cikin sigar umarni.

*Mai fitarwa kudin mutum daya ta ba ni, don haka iya kanta ta siyawa Duk wacce ta karanta ba tare da ts biya hakkkn wahalar rubutu ba, to Ina binta ba Shi, Mai tsoron Allah kad'ai ke jin tsoron hakkkn wani a kansa*
*Dingishin KWAD'O*

Cike da nutsuwa Yaya Farouk ya ce "To Baba".
Yayin da d'adi ya kama Abida ta samu nutsuwa sosai don a yanzu bata da matsala a duniya irin ta Sulaiman. Bata taɓa hararo zai iya tsallakewa ya barta shekaru uku babu waiwaiye ba.
Ya bace bat don kusan kullum sai ta duba dukkan handles d'insa na media amma ba alamun yana amfani da su. Dama kuma shi bai damu da su ba. Twitter yake yi to account d'insa da ta sani ta tura sak'o ya kai sau hamsin amma babu reply ko d'aya.
Da yamma suka tafi asibitin za'a yi masa wata allura a idon sannan bayan awa uku sai a shiga da shi tiyata.
Abida da Farouk sun je sun biya kud'i. Yayin da Baba da Momi suke d'akin da aka kwantar da shi. Suna tafe suna hira Yaya Farouk ya ce "Ta je bari ya siyowa Baba laban a store din waje tunda idan anyi aikin ba zai ci abincin da za'a tauna ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:56]
Kamar ta bishi sai kuma ta fasa ta ce "Sai ka dawo, idan ka ga gashasshen kifi zan ci".
Ya ce "Anya kinsan yawanci sai dare suka fi hada hada, amma zan duba miki, idan ban samu ba sai na siyo miki da daddare."
Ta ce "Na gode ".
Tana shan kwana ta shiga wani korido kawai suka yi kicibus. Had'uwa ta gaba da gaba idanuwansa suka fad'a cikin nata. Ya maze ya dauke kai, ya yi wura Save Restricted Content Bot, [Oct 13, 2025 at 11:58]
wura ya rasa yadda zai yi.
Ai kafin ta ankara ya juya da mugun sauri ya yi waje ba tare da ta ankara ba..

*Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke da kyau da nagartar.*
*Gunis hijab ado cikin wayewar addini da rayuwa*
*08163761797*
*Surayya Gwaram*
*Wannan littafin na kudine*
*Pay 1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*.
08032773332.
*Don samun damar karantawa cikin aminci a telegram*.


*Teemah data service mtn monthly*
*1gb @550*
*2gb @950*
*3gb @1450*
*5gb @1700*
*Dm 08112392177*
*Call 8037026306 Fatima Musa Ibrahim opay*

*For your beautiful kids wears:tees,shorts,trousers,dresses,kids towels, perfumes,body mist contact 08067239846*

A guje ta bi shi tana ayyana yau duk bala'insa ba zata ba'ri ya sake tserewa ba.
Ganin da gaske yake ya sanya ta k'ara gudun da take yi, ta isa gare shi, bata jira komai ba ta sanya dukkan hannuwanta tare da tattaro dukkan k'arfinta ta cakume shi. Ya yi iya k'ok'arinsa ya fizge amma ya kasa don idan ya ce zai fincike ta k'arfi to sai dai ya wancakalar da ita, bai san kuma a yadda zata fadi ba.
Dan haka ya dinga kokarin banbare hannunwanta a jikinsa tun ba'a ankara da su an baibayesu ba. Ya kuma tabbatar kyamarorin asibitin suna ɗaukarsu.
Da k'yar ya bude baki murya ba amo ya ce ",Wanne irin wulakanci kika shiryo mini haka? Akan me za ki karya mini darajata akan titi, me na yi miki, wace ce ke?"
Mamakinsa ya shak'e Abida. Ta kasa ce masa komai amma ta k'udire ba zata bari ya tafi ba har sai Baba Babba ya gan shi.

Ya ce "Sake ni tun ban miki sanadin da za ki tozarta ba."
Ta d'auke kai ta ce "Ba wani tozarcin da zaka yi da zai fi wanda ka yi mini. Ka tafi ka bar ni da aurenka a kaina shekaru hudu babu waiwaiye, kuma ba wanda yasan inda ka ke, sannan yanzu ka ce zaka tozarta ni, wanne irin tozarcin kuma?"
Ba fargaba ya ce "Jira nake yi na ji kin yi aure na dawo mu sake shiga kotu, kinsan na tsotsi kafiya da rashin mutuncinta".
Ta rikice gabadaya take ta ji ta rasa kuzarinta don har rikon da ta yi masa sai da ya yi sakwasakwa.
Idanuwanta sun ciko da k'wallar nadama ta ce "Na janye kalamaina, ban tab'a jin nadama a dukkan tsayin rayuwarta irin wacce na yi akan kalaman da na jefeka da su ba, ka yi hak'uri. Na yarda ban kyauta ba. Allah ya baka hak'uri!
Ya murmusa ya ce "To sake ni."
Ni fa ba zan sake ba har sai Baba Babba ya gan ka.".
Abida ta fad'a idanuwanta cikin nasa.
Ya zabura ya shammace ta ya fizge ya fara k'ok'arin tafiya wajen adana motoci. Ta kuwa sake kai masa wawura. Takaici ya k'ume shi ya ji tamkar ya gaggaura mata maruka masu zafi ko ta shiga taitayinta amma ba zai iya ba.
Juyin duniya ya b'anb'are hannunwanta tuburan ta k'i ba shi damar hakan tabbacin da gaske take yi sai ya gurfana gaban Baban nasu.
Suna cikin haka securities suka zo wajensu. Suka yi magana da Sulaiman da larabci ita dai ba ta ji me suka ce ba ta ga sun tafi ne kawai.
A hassale ya ce "ba za ki sake ni ba ko?"
Ko uffan ba ta ce masa ba illa iyaka tsananta rikon da ta sake yi.
Ita da kanta mamakin cakuikuiye shin da ta yi take yi, bata gane matsanancin son da take yi masa ba sai a ranar. Don kuwa ji ta yi matuk'ar zai sake kubuce mata bayan ta gan shi gara ta mutu ko ta huta da azabar da ke dandana ta rashinsa.
A haka ta hango ya Farouk ya shigo.
Nan da nan ta bude murya ta ce "Yaya Farouk ga shi na rik'e maka shi".
Da hanzari ya iso kusa da su ya kallesu kowa fuskarsa babu walwala sai suka tuna masa shekarun baya da suke y'ar tsama da junansu.
Ya kaurara harshe ya ce "Sake shi Abida ya za ki cakume shi irin haka?"
Nan da nan Sulaiman ya ce "Ba ta riga ta raina ni ba. Saboda tana da gatan da zata yi komai yadda take so, ba tare da an kwabe ta ba.
Ya fad'a cikin fishi sosai.
Ta sake shi a sanyaye don ta lura fishi mai tsananin gaske ya yi da su.

Deenah cakes and more -Kano
09038055790
IG @Deenah cakes and more
Snacks such as :
Birthday cakes
Cupcakes
Samosa
Springrolls
Meatpie
Frozen snacks
Event snacks
Patronage my daughter.

Yayin da Faruku ya hassala da kalaman Sulaiman.
Amma ya yi jarumtar had'iyewa ya ce masa "Wuce mu je ciki".
Cikin sigar umarni.
Bai musa ba ya yarda suka tafi ba don komai ba sai saboda Yaya Farouk mutum ne da kowa a gidan nasu yake jin kunyar yi masa rashin kunya saboda tsananin kirkinsa da haba haba da yake da su ba tare da tunanin su din k'annensa ba ne.
Tiryan tiryan har d'akin da su baba suke ciki. Kaitsaye gadon da Baba Babba yake zaune Sulaiman din ya nufa ya durkusa tare da fad'in "sannu Baba ya jikin, ya kuma iyali?"
Duk d'akin aka zuba musu ido domin dai Baba Babba bai amsa masa gaisuwar da ya yi masa ba, asalima d'auke kai ya yi tare da juyar da fuskarsa d'aya gefen.
Hankalin Sulaiman ya tashi ya yi k'asa da kansa cikin girmamawa ya ce "Ka yi mini hakuri Baba a gafarce ni dan Allah".
Baba bai ce komai ba, bai kuma juyo ba.
A sanyaye yaya Farouk ya ce "
A yi hakuri Baba.".
Amma ko motsi Baban ya k'i bare ya tanka musu. Karon farko da suka ga an gaishe shi ya tankwabar da gaisuwar a dukkan tsayin rayuwarsu gabad'aya.

Ganin haka ya sanya Momi ta ce "daure Alhaji, sake yin hak'uri."
Hankalin Sulaiman ya yi tashin gauron zabi duk da shima cike yake da gillin ba'a yi masa abin da ya kamata ba, amma ya gamsu ya yi laifin da Baba zai yi masa fishi. Fishinsa a kansa kuwa tamkar fishin mahaifinsa ne don haka zai yi iya k'ok'arinsa don ganin Baban ya huce ya karbi gaisuwarsa har ya saka masa albarka.
Ya mik'a hannunsa ya rik'e hannunsa cikin girmamawa da taushin harshe ya ce "Dan Allah Baba ka yi hak'uri, na yi kuskure ban kyauta ba. Dan Allah a gafarce ni!
Sai lokacin Baban ya juyo da fuskarsa ya d'ora akan ta Sulaiman sai ya ga ya sake girma da kuma alamun yana cikin nutsuwarsa.
Ya ce "Anya kuwa Sulaiman zan hak'ura da abin da ka yi mini? "

Kansa a k'asa ya ce "Da kaina ina k'alubalantar kaina Baba. Amma dai ka daure ka yi hak'uri ka karbi tubana da gaisuwata dan Allah!

Baba ya nisa ya ce " Zan karbi gaisuwarka ne kad'ai idan ka yarda ka zo mun tafi gida, don sai mun je gida zan fad'a maka sharadina akanka idan ka amince da sharadina to sannan zan hak'ura na kuma huce. Idan ba haka ba kuwa to lah shakka ba zan karbi gaisuwarka ba, bare na huce da kai, kuma yanzu na gane kai ne Dr Isa din da zai yi mini aikin ido to kuwa ba zan amince a mini aikin ba gabad'aya ".
Nan da nan Sulaiman ya ce "Zamu tafi tare Baba. Zan nemi izinin tafiya da hukumar asibitin, idan da rabon zan dawo na cigaba da aikin da su sai na dawo, idan kuma iya adadin da k'addara ta rubuta zan yi aikin da su shike nan sai na yi zamana a asibitin k'asata."
Dad'i ya kama Baba Babba ya ce"Madallah da Sulaiman ya bayan rabuwa?"
Kunya ta kama shi ya yi k'asa da kansa ya kasa amsawa.
Daga haka ya juya ya gaida momi daga durk'ushen da yake. Ta amsa da sakakkiyar fuska tare da tambayarsa aikinsa.
Bai tashi ba sai da ya gaida Yaya Farouk duk da shi Farouk din hannu ya ba shi tare da mik'ar da shi yana fad'in Dr Sule sai kuma Dr Abida ta yi mana ram da kai!
Gabadaya d'akin aka hau dariya ban da Sulaiman da ya maze. Ita kuwa Abidan murmusawa ta yi wanda tun daga k'asar zuciyarta yake kutsowa.
Dadai lokacin nurse din da zata yiwa Baba allura ta iso d'akin. Ta yi aikinta ta fice.
K'arfe goma na dare aka shiga da Baba dakin tiyata k'arkashin jagorancin d'ansa Dr Sulaiman Isa Funtua!
An yi aiki cikin nasara kwana d'aya ya sallame su.
Sulaiman da kansa ya kai su masaukinsu tare da bawa Baba tabbacin zai sayi ticket din da zai bisu Nigeria in sha Allah.
Baba dai duk hidimar da Sulaiman yake yi masa kallonsa kawai yake yi don kuwa da ace yana cikin shekarun k'arfinsa, kuma ba Abida ce matarsa ba da zane Sulaiman zai yi tabbas.
Washegari momi da Abida suka fara shiga kasuwa yiwa yara tsaraba.
Tun ranar da aka ga Sulaiman Baba ya gargade Slsu gabad'aya akan kada a sake a bayyana an gan shi, a bari sai Allah yasa sun isa lafiya kowa ya gan shi.
Duk zumudin Abida akan ta sanarwa Bilki wuridin kiranyensu ya ci haka ta had'iye ta kama bakinta bata fad'a mata ba.
A hanya Momi ta kalle ta ta ce "Abida ban ga kina gaida Sulaiman ba, ba sai na fad'a miki komai akan halayyarsa ba. Ki bi shi a hankali ki ajiye girman kanki ki lallaba ku sasanta ki koma dakinki tunda dai bai sake ki ba. Kin ga dai yadda ya jingine ki tsawon shekaru babu waiwaiye, idan kuma kin ki jin shawarata ki tabbatar kwabarki ce zata sake cabewa. Ya bar ki da k'aramin cikin da wataƙila ma bai san da shi ba. Ga yaro nan yana gudu har yana gwalantun surutu. Duk sababinki Sulaiman ya dame ki ya shanye kin sani sarai, dan haka ki kwantar da kai har Allah yasa ki koma dakinki".
"To momi shine fa baya ko kallon inda nake, sau biyu ina gaishe shi yana yin kamar bai ji ba tsabar dan sababi ne, shiyasa na daina, ni dai ki taimake ni, ki fad'awa Baba a cikin sharadin da zai gindaya masa har da ya dauki iyalinsa ya zauna da su lafiya".
Dariya momi ta yi ta ce "Sannu Abidan Baba! Amma ai kinsan ba zai yi hakan ba. Da dai ace ba ke ce iyalin nasa ba zai yi hakan. Yanzu ke za ki gyara laifinki, tunda ke ce a k'asansa."
Abida ta ce "Ni Wallahi Momi wulak'ancisa ne bana so. "
Da sauri momi ta ce "Ai tunda ya fara sonki ya daina yi miki, sannan kin sani da kuka yi auren ai rarrashin zuciyarki yake yi. Daga baya kuma ke kika bijire akan ba za ki zauna da shi ba, akan laifin da ba shi ya yi mana ba. Ni dai na fad'a miki gaskiya ki yi maza ki gyara tazarar da kuka haifar a tsakaninku. Don kuwa ke kanki kin san na gaji da ganinki a gidana".
101

****
102
A sanyaye ta ce "To." A zuciyarta kuwa itama ta gajin kawai bata son dan tijarar ya gane ne, bare ya sake samun kuzarin cin kasuwa akanta yadda ya so".
Don gabad'aya tunanin ta inda zata bullo masa take yi.
Ta tabbatar ba k'aramin artabu zasu yi ba, mussaman da ya ce ya yi jirwayen an zuba mata ido tana yin yadda ta ga dama babu mai kwabarta.
Murmushi ya k'wace mata a dalilin ta tuna fad'ansu na k'uruciya a duk sadda aka tare shi idan ya yi nufin kai mata duka sai ya tunzura ya ce 'Ana bata lasisin ta cigaba da raina shi, a yiwa Allah a taimake shi a bar shi ya yi mata dukan da ko mai irin sunansa ta ga ni sai ta shiga taitayinta. Ana marawa Abida baya ta cigaba da yin isgili yadda take so".
Ta tuna mafi yawa baba Karami yake hana shi dukanta. Ya kan ce masa "Sulaiman ai ba'a kanta zaka gwada kwanjinka ba, daure ka daina kula ta ai kanwarka ce. Ni dai zan so na ga k'arshen wannan fadan naku da baya k'arewa. Ba dama ku zauna a inuwa d'aya.
Shiyasa da ya ji suna soyayya har sun amince a yi musu aure ya dinga jinjina k'arfin k'addara dan dai shi ba mai barkwanci bane irin baba Babba ba. Amma tabbas ya yi mamaki, ya yi murna ya dinga ce wa 'Sulaiman ashe da na sani na bari ka yi mata dukan da zaka targad'a ta da shikenan sai ka zama mijin gurguwa.'
Gabadaya wata irin nutsuwa da walwala ne ya dabaibaye zuciyar Abida.
Ta dinga jin wata irin soyayyar Sulaiman na sake bin dukkan ilahirin jikinta. Amma a yadda ya karbe ta ta tabbatar ba k'aramin gumurzu zasu yi ba kafin su daidaita. A zuciyarta ta kud'ire duk inda k'arfin zuciyarta ya buya sai ta lalubo shi, duk yadda ta matsu ya bayyana, duk yadda take jin soyayyarsa ba zata bari ta bayyana masa muraran ba tunda shima k'wallon kansa ne, to ba zata bari ya jata a k'asa don tana son ya zauna da ita ba. Barinta da ya yi tsawon shekaru hud'u ya isa hukuncin zaginsa da ta yi ba zata bari ya sake wani hukunci mai yawa ba.

**
Abuja

Oga Asad da Bilki dai zama ya yi tsami kowa harkarsa yake yi a tsakaninsu. Abinci ma sai ya dawo yake saka Angela sabuwar chep din gidan ta yi masa abin da yake son ci. Hakan ba karamin sake tunzurata ya yi ba.
Yana gama uzzirinsa kuwa zai saka Bilkisu ta karbo masa twins ya dinga fama da su har sai dare ya fara nisa sannan zai mayarwa Alti su.
Ya tattara ya fita a harkarta.
Sai dai daga shi har ita kowa ya shiga damuwa. Bilki ta fara gasgata lallai ta fara sonsa. Fishin da ya dauka ya dameta ainun.
Ranar alhamis tura ta kai masa bango. Har sha d'ayan safiya yana gida

27 / 50