Author : Hadiza D Auta Category : Romance
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: *DINGISHIN KWADO 3*
*BY*
*SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*
*Barar addu'arku*
*A irin wannan ranar ta 09/09/2000 Allah ya karbi rayuwar mahaifiyata*.
*Ina barar addu'arku da ku taya ni yi mata addu'o'in smaun rahamar Allah*.
*Saboda haka na saki page din a maimakon 10 ha wata da na ambata a farko*.
*Allah ya jiƙanki Mamah yasa aljannar firdaus makoma da dukkan musulmai gabad'aya*.
Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba.
Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k'addara.
Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad'a bai san abin mayarwa ba.
Duk yadda sakin nan ya yi mata wata irin mahangurba sai da ta yi jarumtar had'iyewa a gabansa.
Da murmushi ta dinga fad'in "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Ubangiji na gode da abin da ka yi mini, na gode da abin da kake yi mini. Na kuma gode da abin da zaka yi mini a gaba".
Ta kalle shi sai ta ga tamkar nadama ce ta shige shi ta farat d'aya.
Gabad'aya jikinsa ya sake ya yi tub'us.
Yayin da ita ta kasa fahimtar komai.
Ya koma ya kwanta. Tsawon lokaci tana zaune tana sauraran yadda yake barcinsa sannu a hankali ba tare da tunanin komai ba.
Ganin ta kasa barci bar biyun dare ya sanya ta yi alwallah ta fara nafila. A cikin sujjuda take kuka tana yiwa ya'yanta addu'ar Allah ya tsare mata su ya kuma k'addara musu kyakkwar rayuwa cikin imani da lafiya.
Tana zaune har asuba ba abin da take yi irin tufka da warwara. Ina zata je ne?
Sai yanzu ta fahimci girman k'alubalen da yake gabanta.
Ta dinga kuka tana yiwa iyayenta da Yaya Sulaiman addu'a.
Sai da aka fara k'iran assalatu ya farka.
Ya shiga bayi ya d'oro alwallah. Shi ma nafilar ya yi.
Sai da ya idar ya ce "Bilkisu ina ba ki shawara ki janye kalaman da kika jefe ni da su, sannan ina ba ki umarnin ki ba ni hakuri don bana son na barki ki tafi kina garari tunda dai nasan ba ki da inda za ki je".
Bak'in ciki har mak'oshinta ta ji tamkar ta danna masa ashariyoyi kala kala tsabar bak'incikin da ya taso mata.
Amma ta yi kamar ba da ita yake ba domin tana bude baki la shakka zaginsa zata yi wanda hakan kuma ba d'ab'iar mace kamila mai ilimi ba ne.
Dan haka ta yi masa bakam.
Har aka fara kiraye kirayen sallar asuba bata tanka masa ba.
Ya tafi masallaci yana fad'in "Ki yi shawara da zuciyarki kafin na dawo.
Ta bi shi da kallon mamaki wataƙila bai fahimci girman tozarcin da ya yi mata. Bai fahimci cewar da ya yi wai bata da inda zata je ma cin zarafinta ya yi ba. Ya manta da kalaman da ya yi wajen sakinta.
*Ki je dan iyayenki masu son zuciya na sake ki saki biyu"*
Zuciyarta ta buga da k'arfin gaske. Ta ke ce da kuka a bayyane domin k'arshen kaskanci da cin mutunci Sahal ya yi mata. Bayan haka bai ishe shi ba shine yanzu ya zo yana sake cin mutuncinta. Wato ga ni yake yi gidansa ne kad'ai mafakarta? Ashe shiyasa yake tuka mata tuwon wulakanci kala kala tana ta yin hak'uri da kawar da kai tare da yi masa uzziri kan uzziri. Ashe shi duk kallon bata da yadda zata yi, bata da gata yake yi mata?
Ta girgiza kai tana fad'in "Ko duk zuri'armu sun k'are ba zan sake zama k'arkashin ikon ka ba. Ko da hakan na nufin na dinga kwana a titi ne.
Bare kuma Ubangiji ya riga ya rufa mini asiri.
Kuka ta ke sosai wanda ba na zafin sakin ba ne , kuka take yi na yadda gidansu na Funtua ya zama kongo. Da ace Baba Babba na cikin gidan da ko bangarensu zata je ta bude ta zauna har zuwa ta samu nutsuwa.
Amma a yanzu fa?
Maiduguri zata tafi gidan Ansari ta zauna a hannun yarinyar matarsa ko kuwa Kano zata tafi gidan Yaya Hamida?
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Gidan Yaya Hamida ai ba dolenta ba ne tunda itama a k'arkashin wani take.
"Ina zan tafi ni Bilki?"
Ta fad'a cikin rawar murya irin ta kuka.
Ta yi shiru tana tunani. Gidanta ne ya fado mata. Tana da gidaje a Katsina. Bata son ta zauna a gidanta da suka zauna domin ya yi mata girma a matsayinta na marar aure. Sannan zata so ace ba ita kad'ai zata zauna ba. Take ta tuno da d'aya gidanta mai hawa biyu wanda akwai y'an haya a k'asa, saman ne babu kowa watanni uku da suka shud'e aka yiwa wanda yake ciki sauyin wajen aiki zuwa jihar Jigawa. Shine iyalinsa basu tashi ba sai sati biyu da suka shud'e. Wanccan satin ta je ta ga gidan ta saka a gyara a yi sabon fenti don idan za'a sake karɓa a bata kudi da daraja.
Take ta lalubo lambar wanda yake kula da gidajen. Ya dauka yana fad'in "Hajiya da fatan dai lafiya?"
Murya ba amo ta ce "Zan tambaye ka ne an kammala aikin gidan nan kuwa?".
Da girmamawa ya ce "An kammala fenti Hajiya sink din kicin ne ba'a saka ba amma na siyo sabo yanzu haka ma yana gidan."
Ta ce "To ka yi kokari a saka zuwa goman safiyar sannan a share a wanke gidan kafin zuwa azahar din yau. "
"To za'a yi hakan Hajiya da ikon Allah. "
"
Ta ajiye wayar tana jin saukin tashin hankalin da take ciki. Gidan a unguwa mai kyau yake babu hayaninya awon gwamnatine. Matsalar d'aya ce ba ruwan famfo sai dai da rijiya a harabar gidan. Zata samu almajirin da zai dinga d'ebo mata kullum.
Zata tafi da Alti da Alawiyya. Duk da auren Alawiyya wata d'aya ya rage . Nan da sati biyu ma zata tafi garinsu.
Kawai matsalar da tafi damunta makomar Amrah da Faruk ne. Ya ya zusu yi idan suka tashi Babu ita, babu Farha babu Alti ba Alawiyya?"
Ta kifa kanta a akan gado tana gunshekin kukan tausayin ya'yanta.
Bata jin zata fasa barin gidan Sahal. Amma tausayin ya'yanta yana matuk'ar tayar mata da hankali.
A haka ya dawo ya tarar da ita.
Ya zauna a gefen gadon. Ya ce "Ki daina kuka Bilkisu. Ni kaina haka nake jin jikina babu k'wari. Amma maganganunki sun mini ciwo sun tayar mini da hankali. Ki janyesu, ki yi tuba shike nan sai na mayar da ke ki cigaba da zama a d'akinki.".
Ta zuba masa ido hawaye yana ambaliya. Ta ce "A a Sahal ai zama a tsakaninmu ya riga ya k'are, tunda na fahimci baka sona, baka bukatata nake ta faɗawa Allah ya kawo mana mafita a tsakaninmu. Ka san ai ban yi shekarun da zan ce bana buk'atar namiji ba. Kai ka samu mafita, ka samu wata ni ce ban samu ba. Da haka kuma ya faru na yi imanin nima tawa mafitar ce ta zo".
Da iyakacin gaskiyarsa ya ce "Wallahi Bilki ina son ki. Har yanzu bana jin Hawwah irin yadda nake jin ki a zuciyata. Amma ban san meyasa bana jin sha'awar ki ba. Na dade ina zargin ko saka hannune don ina jin sha'awar matayen da ba su kai ki komai na cikar halitta ba. Amma watan jiya da na ji karatun Shaikh Ibrahim Khalil da yake bada tabbacin ana cirewa namiji sha'awar matarsa ko da kuwa yana sonta. Ganin ina cikin wannan matsalar ya saka na dinga nazarin to ai ni da ke bamu yi irin wannan shekarun da zamu kai ga wannan bigiren ba. Bayan haka na gasgata ina da rauni a wannan fagen sabanin ke da kike da k'arfi bukatar al'amarin. Sai na ji tamkar na ba ki dama ki je ki yi aurenki, amma sai na ji gara mutuwa ta riske ni kafin na ga kin zama matar wani. Amma jiya sai da kika yi mini cin mutuncin da ya zame mini dole na sallama ki".
Na goge hawayen na ce "Zaman ne ya k'are."
"Yanzu Bilki ba za ki karbi shawarar da na ba ki, akan ki janye kalaman da kika yab'a mini ba? Ba za ki bi umarnina ki ba ni hakuri ba?"
Ya fad'a a zabure.
Cikin nutsuwa ta ce "Ai duk duniyar nan ba mai sakawa na baka hak'uri Sahal. Don ban yi lalacewar da za'a zagi iyayena yayin da za'a sake ni sannan na bada hakuri ba. "
Ya mike yana fad'in"Girman kai ba na ki bane ina jiye miki ragaita duk kasaitaacciyar mace za'a same ta ne a gidan mijinta ko na iyayenta ko na d'anta ko kuma na y'anuwanta shakikai".
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Bata kula shi ba don bata da abin fad'a kuma.
Ya sake zama ya sassauta ya ce "kin yi nazarin ya ya rayuwar ya'yanki zata zama idan nabu ke a kusa da su?"
Rauni irin na uwa ya shige ta nan da nan, amma ta shanye ta ce "Idan na mutu ya ya zasu yi ne? Kuma a gidan ubansu zan barsu, don ba zai yiyu da gatansu na tafi da su muna ragaita a titi ba. Ni dai da ba ni da gata zan tafi, ko barance na yi".
Ya yi shiru da alamu ya gane magana ta cab'a masa.
Ta numfasa ta ce"Duk irin musgunawar da ka yi mini na yafe maka darajar ya'yanka. Wannan gidan da aka gina shi da dukiyata Allah ne shaidar na bar maka halak malak, na yafe maka. Amma dan Allah ko ban ci arzikin komai ba a gunka ka dubi Allah ka rike y'ay'anka da amana da tausayawa, na barsu a hannun Allah na barsu a hannunka."
Daga haka kuka na sosai ya k'wace mata.
Ya kamu da ciwon tausayinta ainun, a sanyaye ya ce "Bilki ki zauna na mayar da ke".
Ta kuwa yi wata irin zabura ta mik'e tare da fad'in"Wannan kuwa shine gangan Sahal!
" Ina yi maka rantsuwa da Ubangijin al'arshi zama ni da kai ya k'are ila yaumil k'iyama. Ka mayar da ni, na kuma maidu a fuskar shari'a sai dai tunda shari'ar ta ba ni damar idan ina cutuwa na bijire. To ba zan zauna ba. Aure ya haramta a tsakaninmu tunda ka yi gigin mayar da ni dan kuwa a yanzu ba sai anjima ba sai ka sake ni ".
Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi ya ce "Idan ba za ki zauna saboda ni ba, to ki zauna ki reni ya'yanki".
A zafafe ta ce"Ba zan zauna ba. Na barwa Allah amanarsu, na barsu a hannun ubansu. Zan je na nemi wanda zai mini adalci, wanda ba zai ga tsufana ba, ba wanda zai ga son zuciyar iyayena ba, wanda zai kashe mini k'ishin da nake fama da shi tsawon lokaci."
Kishi mai tsananin gaske ya shak'e shi, har kan harshensa yake jin d'aci.
Ya ce "Yanzu so kike na furta miki na ukun a zo a jarrabe mu Bili?"
Ta ce "Ba wata jarabawar da zamu shiga ai an gama, ina binka a hankali ne saboda alfarmar da Ubangiji ya baka a kaina amma Wallahi komai zai iya faruwa a tsakaninmu idan ka kafe!
Ta fad'a cikin tashin hankali da matsanancin fishi.
Ganin zai fita ya sanya ta yi maza ta wuce shi ta rufe k'ofar d'akin. Ta sunkuya ta ja plate din da ta ci tufa a daren jiya. Y'ar karamar wuka ta dauko mai tsini da kaifi ta ce "Ka sake ni ko ka mini sanadin da zan rasa rayuwata gabad'aya don da na zauna da kai gara na kashe kaina na huta da azabar da kake gana mini da raina!
Ganin gabadaya ta rikice kuma iyakacin gaskiyarta yake ga ni har cikin kwayar idanuwanta ya sanya ya ce "Na sake ki Bilki! Allah ya yi miki musayen alheri".
Ya zauna don sai ya ji jiri na katantanwa da shi.
Dukkansu kuka suke yi irin kukan nan mai taɓa zuciya, kukan kaico, kukan da ake jin an tsinci kai ba a yanayin da ake so ba.
Shi ya yi jarumtar ce wa "To ki yi zamanki a nan Bilki. Na amince ba zan zo wajen ki ba, kinsan nasan dokokin Ubangiji ina kokarin kùma kiyaye su."
Ta girgiza kai ta ce daga yau zuwa gobe zan tafi ba zan zauna ba Sahal. Kuma Wallahi har zuciyata na yafe maka duk irin musgunawar da ka yi mini. Duk hakkina da ka danne mini a zamanmu Ubangiji ne shaidar na yafe maka, bana fatan sakayya ta dawo maka ko ta sauka akan Amrah."
Ya ce "Na gode, na gode Allah ya hana ki kuka Bilki. Amma dan Allah zan roke ki arzikin abu d'aya tak. Ki bar Farha a tare da yaran nan, zan rike ta amana."
Ba ja in ja ta ce "Ka roki abin da ba zan iya yi maka ba. Mutuwa kad'ai zata raba ni da ita, ko uwarta da ubanta a yanzu basu isa su ce na basu ita ba. Bare kuma ace na bada ita a inda ba dolenta ba. Na dai yi maka alk'awarin zata dinga zuwa hutu wajen y'anuwanta ba kuma kowanne hutun ba. Duk inda rayuwa zata wulla ni to zata wulla ni ne tare da ita, itace kad'ai abin da na mallaka da ba wanda zai mini iko ko ya yi mini gayya da ita."
Ta fad'a hawayen tausayin ya'yanta na zuba. Don a yanzu sune damuwarta. Yadda zasu shigo su ga babu ita, babu Farha babu su Alti sai su kad'ai yana matuƙar d'aga mata hankali.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ya share hawayen idonsa ya ce "Ki yi hakuri, in sha Allah zan iya k'ok'arina akansu sai dai ai ba kamar suna tare da ke ba.
Ya mike tsaye ya ce "Ni fa ji nake yi idan har na bar ki kika tafi ni kuma na zauna da wata matar a wannan gidan na yi zalunci."
Ta zuba masa ido ta ce "katon zalunci ma kuwa Sahal. Ai ko sakina da ka yi cikin izgilin ba ni da inda zan je ma zalunci ka yi. Shiyasa ni kuma na haramtawa kaina zama da kai. Amma kuma Wallahi tunda aure ya k'are a tsakaninmu har abada, to na yafe maka dukkan kuskuren da ka yi mini har zuciyata in sha Allah ba zaka tashi da haƙƙina ba. Ni kuma Allah ya mini sakayyar alheri albarkacin hakuri da afuwar da na yi maka".
Ya rasa me zai ce mata amma har cikin zuciyarsa yasan bai taɓa cin karo da mutum a duniya mai karamci da hakurin Bilki ba. Ya yi asara ba kad'an ba. Sai dai ya yi murna da ya bata dama don ta nemi farincikinta a gaba don idan ba haka ba, hak'kinta kad'ai ya ishe shi zunubin da zai hana shi kwanciya cikin salama.
Ya tausasa harshe ya ce "Allah ya yi miki alheri da kansa Bilina na gode Allah ya had'amu da alheri ya shirya mana zuri'armu da ya bamu".
A hankali ta ce "Ameen.
Daga haka ta tashi ta bude masa kofar ya fice a rikice.
Sai da ya yara suka tafi makaranta ta k'ira Alti d'aki ta fad'a mata halin da take ciki. Suka yi kukansu suka more don Altin ma da take bata hak'uri a yau kukan ta taya Bilki sosai.
Da k'yar suka hak'ura.
Alti da Alawiyya suka fara had'a mata kayan sawarta. Kafin Yara du dawo sun gama had'a wadanda zasu iya.
Sai da daddare ta zauna da ya'yanta cikin hikima ta fad'a musu gobe ko jibi zata koma gidanta amma su zasu zauna a gidansu ne.
Amrah ta ce "Mamah kun rabu ne?"
Ba boye boye ta ce "Aurenmu ne ya k'are amma tunda muna da ku ai bamu rabu ba".
Hawaye ya k'wacewa yarinyar. Yayin da Farha da Farouk suka yi tsamo tsamo.
Ta yi jarumtar rarrashin Amrah da fad'in kina babba kina kuka su kuma su yi ya ya ke nan?"
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Da k'yar ta shawo kanta ta nutsu ta yi shiru. Ta dinga yi musu nasiha.
Farouk ya ce "Yanzu mu kad'ai zamu zauna a nan side din Mamah?"
A tausashe ta ce "A a tare da Dady sannan Antin ma zata dawo nan din".
Ya yi shiru amma ba haka ya so ba. Can ya ce "Amma ki fad'awa Dady kada ta ce zata dinga takura mana. Sannan Mahma if possible ki bar mana Alti".
Bilki ta shanye tausayinsu ta ce "Ku zauna lafiya da Antinku, kada ku yi mata rashin kunya.
Duk abin da ta ce ku yi, to ku yi mussaman ke Amrah."
Amrah da take kuka sosai ta kasa magana.
Farouk ne ya ce "Mahma to ki bar mana Alti please ".
Sai lokacin Amra ta ce "Maimakon ka bata hak'uri ta zauna da mu sai ka ce ta bar mana Alti?"
Kaitsaye ya ce "Ba zan bata hak'uri ba. Kullum fa sai na ga ta yi kuka duk yadda bata son mu gane.
Kullum Dady ne ya kai anty school da duk inda zata je a mota. Amma when last ya dauki Mamah a motarsa ko kuma mu?Kina ganin Dady yana siyo abu a leda ya kawo side din nan? Amma kullum sai na ga ya kaiwa ta sama abu a leda. Kawai Mahma ki je inda ba za ki dinga kuka ba." Ni fa tuni na gaji kawai dan ba ni da kudin da zan siya mata gida ne. Duk ranar da na je Abuja zan faɗawa uncle Farouku senior ya siya mata gidan tunda uncle Sulaiman ba dawowa zai yi ba"
Wannan karon Bilki ta kasa jarumta danne kukanta. Ta fashe da kuka ainun yayin da Amra da Farha suke kukan suma amma da yake namiji tun yana k'arami zuciyarsu mai taurice Farouk bai yi kuka ba. Amma idanuwansa sun yi tsilli tsilli tabbacin yana cikin damuwa sosai.
Gabaɗayansu har Alti sai da kukan ya k'wace musu don kuwa duk abin da ya fad'a gaskiya ne. Sannan basu yi zaton Faruk yana ankare da