Author : Nimcyluv sarauta Category : African Stories & Novels
ba" Mother gaba ɗaya haushin duk wasu jami'an
tsaron take ji hakan yasa cikin sauri ta juya zuwa inda Abba Hakimi da Sheikh suke
tsaye, idan ka gansu zaka ɗauka da gaske Hakimi shi ne ya haifi Sheikh sbd tsananin
haibar dake maƙale a jikin ko wanne kusan duk halin Hakimi Sheikh ya kwashe shi
tas.
Kallonsu ta yi cike da son ko wanne wanda ke rinjayar zuciyarta ta ce "Thank you
Abba Hakimi" murmushi kawai ya yi bai ce mata komai ba, tana ƙoƙarin sake magana ya
yi saurin barin wajan zuwa cikin motar da Umar-khan ya buɗe masa baya.
Tsaye Sheikh yana bin mahaifiyar tasa da kallo ganin tai shiru ya waro mata manyan
Idanun shi yana son cewa wani abu amma ya ja bakinsa ya yi shiru a hankali ta ce
"zaka bini ko Abban naka za kabi?" Bakinsa ya motsa yana rufe idanu tare da fara
buga ƙafa yana riƙe jikinsa da kyau cikin In-ina ya ce "Zazzzza... zan zan zanje
gida wajan fa... fa.. father ina soooo son ganinsa"
haushi ne ya kama Mother ganin duk abin da ake Sheikh yana maƙale da son
mahaifinsa. "Father baya gari, kaje wajan Hakimi ka huta da kyau gobe sai kazo mu
tattauna, ina tunanin za a haƙura da zuwa Madina haka" girgiza mata kai ya yi bai
ce komai ba ya juya ganin har lokacin Abba Hakimi na zaune bayan motar, yanzu zuwa
shima ya shiga baya Ishaq-hakim ya jasu. daga nan Bar Zainab gidanta ta shige hakan
yasa Umar-khan ɗaukan Mother a ɗaya daga cikin motocin Sheikh suka nufi gida, Saif-
Wazir kuma ya tsaya domin magana da ƴan jarida.
Suna tafe a hanya Sheikh na yiwa Abba Hakimi hira cikin nutsuwa duk da In-ina yake
amma Hakimi na fahimtar komai da Sheikh ke faɗa, a duk maganganun Sheikh ba za kaji
kalmar MACE ta fito daga bakinsa ba, balle har ya ware wata musamman yana magana a
ganta, Murmushi kawai Hakimi yake Ubangiji ne shaidar son da ya kewa Sheikh a jinin
jikinsa yake.
A haka suka ƙarasa haɗaɗɗan gidan Abba Hakimi dake Dawaki roud, gida ne irin na
sarauta mai kyan tsari da fasali ko'ina ma'aikata ne , motar na tsayawa Sheikh ya
fito ƙwayar idanunsa na nuna gajiyar da yake ciki.
Bai tsaya jiran Abba ba, kai tsaye ya nufi part ɗinsa wanda yake cikin gidan Abba
Hakimin wanka ya yi da ruwa mai zafi yana gamawa ya fito ɗaure da babban towel
idanunshi na janye wa barci na cin ƙarfinsa ya ɗauki wani tsadaddan lotion, Shea
body butter ya shiga shafawa saman fatarsa a kasalance, Engage Cologne Spray ya
fesa a fatarsa sbd ɗauke zafin da ya keji yana gamawa ya miƙe zuwa clothes ɗinsa ya
ɗauki wani trousers mara nauyi ya saka ko riga bai saka ba, ya cilla mint bakinsa
ya kwanta saman bed yana lulluɓe jikinsa da bargo, ganin rana ce ya sa ya kunna A.c
tare da rufe idanunshi cike da fatan barci ya ɗauke shi.
Washegari gari tun da Sheikh ya farka bai koma barci ba, har ya fita sallar Subhi
sai da gari ya yi haske wajan 6:30 ya dawo gida jikinsa duk ciwo yake masa sbd
rashin gym da bai ba, wanka ya ƙara yi ya shirya cikin Scabal wool suit white
colour sai red ɗin necktie. Sai Diamond Rolex daya maƙala a hannunsa, yau a Yaa Lee
ya fito ba a Sheikh ba, domin kusan siffa biyu gare shi, idan zashi bank shigar
suit yake duk abin da ya danganci addini ajjiye shi yake a gefe amma yana zuciyar
shi, idan kuma ya sanya Alkyabba da rawani yana matsayin Sheikh a wannan lokacin ne
ba Yaa Lee ba. Wayarsa ya ɗauka jacket ɗin sa a hannu cikin nutsuwa ya fita zuwa
main parlour.
Ƙamshin ROJA shi ne ya fara kaiwa su Abba Hakimi ziraya yana zaune da jallabiya
gefensa kuma Ishaq-hakim ne da Saif-Wazir shirya zasu shi wajan aiki, sai Momi
A'isha tana zubawa Abba Hakimi Shayi mai zafi. "Mrng Yaa Lee" jinjina kai ya yi
idanunshi akan Abba Hakimi ya furta. "B...bar bar barka da safi fifi fiya".
"Ya ka kwana? da ciwon kan?" Rufe ido ya yi tare da buɗewa alamar "Allahamdulillah"
Momi A'isha ta amsa gaisuwar Sheikh ɗin wacce ya yi mata ita cikin In-ina, tea ta
haɗa masa mai zafi ta zuba 2spoon na honey ta juya kaɗan tare da bashi. Amsa ya yi
a kame yake shan tea ɗin yana sauraran maganar Abba Hakimi da yake ce masa "komawa
Madina ba yanzu ba, kada ya fara tunanin hakan" sanin ba zai iya ja da maganar Abba
Hakimin ba yasa ya miƙe yana ajjiye cup ɗin hannunsa, Ishaq-hakim da Saif-Wazir
suka miƙe tare da bin bayansa, wata farar mota ya shiga mai Sheikh no 5 yana shiga
driver ya ja. Ishaq-hakim da Saif-Wazir kowa ya shiga motarsa suka nufi S.A.H BANK.
tun kafin ya Ƙarasa cikin bank ɗin wanda ya kasance mallakinsa ma'aikatan bakin
Sheikh Aliyu Haydar bank suka shiga mutuwarsu ƙwarai. miƙewa ake ana gaida shi
hannu kawai yake ɗaga musu har ya shige wani baban office. Wunin ranar Sheik cikin
duba files and Ducoments yake.
3:30 yana ƙoƙarin barin Office ɗin saƙon father ya sauka Wayarsa. Da fararen
idanunsa yake bin message ɗin da kallo yana mamakin yanzu kuma kiran gaggawar
mene?. Da wannan tunanin ya shiga mota Driver ya ja suka nufi unguwar su Sheikh.
Tun a harabar gidan ya san akwai matsala domin kai tsaye idanunshi ya sauka akan
motar Abba Hakimi data Yaya Halima sai ta Uncle Haroon.
Ƙamshin turarensa ya bayyana zuwansa, Mother dake zaune saman Kujera yana kaɗa ƙafa
ta kalle shi kafin ta ɗauke kai, Uncle Haroon ma kallon Sheikh ɗin ya yi, a kame ya
ƙarasa kusa da Abba Hakimi ya zauna yana ɗauke idanunshi daga kan jama'ar daya rasa
meeting ɗin me ake.
"Tun da Allah ya kawo shi sai aji ta bakinsa, amma Sheikh ya shige lokacin da za a
yi masa auren dole, a baya ba ai masa ba balle yanzu?" Yaya Halima ta furta cike da
jin haushin father. Shi ma father da zuciyarsa ke kusa ya ce.
"Bashi da amfani, domin ba zai faɗi abin da kowa ke buƙata ba, na daɗe da sanin
cewa Aliyu shi ne ƙaddarata, shi da yake namiji wanda ya kamata ya tsaya kan
dukiyata amma ya kasa hakan, duk mutanan da suke buƙatar contract daka gareni idan
har suka ji yadda Aliyu ke banzar maganar shi suke contract In-inar Aliyu ta ja
mini asara mai yawan gaske, don haka ni bashi da amfani a gareni" sai a yanzu suka
fahimci rashin jituwar da babu tsakanin father da Aliyu cikin ladabi Abba Hakimi ya
ce "Baka yarda Ubangiji ya ɗorawa Aliyu wannan larurar ba? kenan baka alfahari da
Aliyun matsayin ɗa?" Cikin sauri Father ya ce "Aliyu bai taɓa yi mini rana ba, to
akan me zan yi alfahari da shi? Idan yana so mu shirya dole ya daina wannan In-inar
ko kuma ya yi aure cikin satin nan"
"Aliyu akwai wacce ka ke so ne?" Sai a lokacin Sheikh ya kalli Uncle Haroon yana
runtse idanunshi zufa na yanko masa a ƙoƙarin shi na ganin ya yi magana babu In-ina
amma ina ba zai iya ba ƙaddarar shi ce hakan.
Cikin fitar hayyaci yana rirriƙe jikinsa da kyau tare da buga ƙasa da hannun kujera
ya ce "ba...ba ba bana son son kowa uncle.. ba ba bazan iyyyya zama dadda da mace
ba" shiru duk sukai baƙin ciki ne kuma ya hana mother magana. Father ya ce "Ok good
a Sbd haka ka shirya zama da Zahrah ƴar gidan babban aminina, cikin satin nan za a
yi aurenku kai da Zahran babu fashi" miƙewa Mother ta yi cikin faɗa ta ce "Wallahi
Aliyu kayi kaɗan ka saka Sheik ya auri wannan Yarinyar da ban amince da tarbiyyar
ta ba, me Sheikh zai da ita? Yarinyar da take kusan sa'ar shi kaɗan ne babu ta
girme shi ba? duk shekarun da Aliyu ya yi babu aure sai kuma ya ƙare wajan tsohuwa,
ban amince ba kuma ban yarda ba, ka bawa Aliyu duk wacce kaga dama amma ban da
Zahrah" murmushi father ya yi ya ce "Idan har ni ne uban Aliyu ba wani ba? Ya zama
dole ya auri Zahrah idan kuma bani ne mahaifinsa ba sai ki bashi wacce kikai niyya
Barrister Maryam" hawaye ya cika Idanun Mother ta ce "Oh yanzu kuma sheganta Aliyu
zaka fara bayan zarafinsa da ka ke ci akan larurarsa?" Banza father ya yi mata.
Uncle Haroon ya numfasa ya ce "Engineer Aliyu Wannan bai kamata ba, idan kana so
Aliyu ya yi aure,Let him choose the woman he wants to marry himself, ka sassauta
yanayin da ka keji game da Aliyun" Father ya ce "Abu ɗaya ne zai kawo Shira
tsakanina da Aliyun shi ne auren shi da Zahrah idan bai amince ba yaje na zare
hannuna daga Lamarinsa kuma ya zare sunana a matsayin Uba" Dakawa Father tsawa
Uncle Haroon yai ya ce "Wai Aliyu wanne irin banzar magana ce kake haka? Ni da kai
na zan iya samawa Aliyu matar aure, ka daina ganin kai ne ubansa ni ma uba ne a
wajansa, ga kuma babban Uba hakimi duk mun isa mu tsayawa Aliyu, ka daɗe baka cire
hannunka ba, kuma wallahi ka sake na rabaka da Aliyu ka rabu dashi kenan har abada"
Girgiza kai Abba Hakimi ya yi ya ce "Ba za a yi haka ba Haroon, haƙƙin Aliyu ne
samawa Sheikh matar aure a barshi ya aura masa Zahrah Allah ya sa albarka,kada ka
damu da Sheikh nasan zai amince" miƙewa Sheikh ya yi cikin zafin e da kutuwar
zuciya irin ta kurmaye Aliyu ya fara faɗa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba,
idanunshi gaba ɗaya ya rufe Innar ta hana ya ji abin da yake faɗa, idan kuma ya
fara faɗa babu wanda ya isa ya tsayar da shi daga faɗan da yake. Saukar wani
zazzafan mari da Sheikh ya ji a saman kamilalliyar fuskarsa ya sanya ya yi saurin
rufe idanunsa Father ya nuna Sheikh ya ce "Ni kake ɗagawa murya Aliyu? Ni sannu
kuturu uban ƴan zuciya daman zuciyar taka nake buƙata auranka da Zahraan kuma babu
fashi" ƙwafa Sheikh ya yi domin baya iya riƙe kansa idan zuciyar ta motsa uban kowa
sai ya san babu lafiya a gidan. Wuyan rigar Father ya riƙe da kyau zufa na mamaye
dukkan goshinsa a wannan karan bai buga ƙafarsa ba amma tamkar zai ɓalla wuyan
rigar haka ya riƙeta da kyau cikin huci da faɗa ya ce "heee na... na na amince amma
ka ka ka tabbatar mutuniyar kirki ce" Father da yaji shaƙar Sheikh ɗin har ransa ya
ce "Idan kuma ba ita bace ba fa Aliyu?" Sheikh ya girgiza kai idanunshi ya yi jajur
ya ce "Haaaaa ɗakkkkkk" yana faɗin haka ya saki Father tare da barin gidan baki
ɗaya...
We're still in free pages🫰🏽 Littafi nan na kuɗi ne, a koda yaushe zan iya datse
free pages. Salo na musamman biya 500 ta Wannan acct ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu
sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616.
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*
*_Nimcyluv sarauta_*
12....
Bayansa suka bi da kallo ganin yadda ya fice a fusace. Father yaja numfashin
wahalar da ƙyar kafin ya ce "Irin wannan ban zan yaron za a bawa mace mai ƙarancin
shekaru? Ai ko Zahrah sai dai ta yi haƙuri da shi" Mother zatai magana Yaya Halima
ta hanata ta hanyar danne hannunta tare da girgiza mata kai. Ganin ba wanda ya sake
cewa father komai ya juya zuwa upstairs. Uncle Haroon ya kalli Abba Hakimi ya ce
"Afuwa ranka ya daɗe kayi haƙuri da halin Engineer Insha Allah komai za yi daidai,
Jadda ba zata barshi ya aikata hakan ba, I'll talk to him" murmushi Abba Hakimi yai
yana faɗin "Me ne na haƙuri Haroon? Sheikh ɗan sa ne ba wanda zai yi jayaya da
hukuncin da uba ya yi akan ɗan sa, idan hakan zai sa shi farin ciki da amincewa da
Sheikh a barshi ya yi" "She's 32 years old Hakimi, tayi wa Sheikh girma ba zata iya
yi masa biyayya ba, babu tarbiyya a wajan yarinyar nan na jima da saninta" Mother
ta faɗa cikin damuwa. Yaya Halima ta ce "Barrister ke uwa ce a kullum, addu'a kawai
za kibi Sheikh da shi, addu'ar ki zatai ta zagaya rayuwarsa sai kiga albarkacin
haka Ubangiji ya daidaita tsakani kuma ya shirya yarinyar, ba a jayaya a cikin
lamarin aure" Uncle Haroon ya ce "Ki bar Barrister ta faɗi abin da yake ranta, idan
akwai wanda yafi sanin halin Sheikh da raninsa to ita ce mai biye mata shi ne
Hakimi, babu kyautatuwar a zuwa Engineer idanu yana abin da ya ga dama, idan baya
ra'ayin Sheikh a rayuwarsa sai muyi yarjejeniya mun ashe sa mu suke sunan shi daga
jikin na Aliyun" miƙewa tsaye Abba Hakimi ya yi yana gyara zaman alkyabbar jikinsa
cike da nutsuwa ya ce. "Wannan shawara ta Haroon ba dani ba, ban taɓa jin inda aka
raba uba da ɗana ba, lokaci ku barshi ya bayyana mana komai" yana faɗin hakan ya yi
waje yana dogara sanda. Uncle Haroon ma ya miƙe tare da yi musu sallama.
Bayan tafiyar su Yaya Halima ta kalli Mother ta ce "Barrister ki nutsu kada kiyi
jayaya da hukuncin da uban yaron nan ya zartar ni ina ji ajikina akwai wani abu
ɓoyayye a ƙasan auren mu amince da hakan" ƙwafa kawai Mother ta yi tana girgiza
ƙafa kafin ta kalli Yaya Halima ta ce "Kin san Allah Yaya ko zan amince da auren
nan sai dai Sheikh ya auri mata biyu?" Yaya Halima ta waro idanu sosai ta jima tana
kallon Mother kafin ta numfasa ta ce "Tab, mata ɗaya ya zata ƙare wajan Sheikh bare
mata biyu? Ai Wallahi mantawa zai yi da zamansu a gidan"
"Ai ko zai yi shekara ɗaya bai kalli ko wacce ba, Wallahi sai dai ya auri mata
biyu" Yaya Halima ta ce "Naji zaɓin Uba, wace kuma zaɓin uwa?" "Bani da zaɓi amma
duk wacce Allah ya nufa data kwanta mini ko ƴar gidan wace zan saka Hakimi ya ɗaura
musu aure"
girgiza kai kawai Yaya Halima tai tana faɗin "Wata drama ɗin abin dry a gidan
Engineer da Barrister a bani abinci naci ni dai" Mother ta miƙe tana kiran sunan
Maimoon. Fitowa tayi daga part ɗinsu jikinta sanye da duguwar riga ta rusuna ta ce
"Ina yini Mama?" Yaya Halima ta ce "Lafiya lou Maimoon ya karatu? Kwana biyu Mother
ta hanaki zuwa ko?" Maimoon ta juya ta kalli Mother wacce ta ɗauke kai tamkar bata
jin abin da suke cewa ta ce "A'a Mama, karatu ne ya yi zafi amma muna exam zan zo"
"To Allah ya taimaka, a kawo mini abinci" murmushi Maimoon tayi ta nufi kitchen.
Yaya Halima ta kalli Mother tana mamakin zafin zuciyar ƙanwar ta ta. Arabian Mandi
rice wacce ta sha kayan haɗi sai ƙamshi take Maimoon ya zubu a plate tare da haɗin
salad da ya sha bama da egg with some of vegetables. "Ki sakko muci abinci Maryam"
Mother ta ɗauke tana faɗin "Anya? ci kawai Yaya bana jin zan iya ci" murmushi kawai
Yaya Halima tai tana faɗin "Allah ya kyauta komai ya yi zafi maganinsa Allah"
Yana tsaye gaban madubi banda huci babu abin da yake maganganun father nayi masa
amsa kuuwa a kunnuwansa "Bashi da amfani, bai taɓa yi mini rana ba, ya yi mini
asarar contract ɗina" hannu ɗaya ya sanya ya dafe kansa dake masa ciwo sosai, ɗaya
hannun kuma ya rufe kunnansa a zatonsa hakan zai taimaka wajan rage tuna maganar
mahaifin nasa. Ɗago jajayen idanunsa ya yi ya tsurawa kansa ido ta cikin madubin. A
wannan karan dole ya nunawa father shi ma namiji ne yana shiru ne sbd bai damu da
duniya da abin da ke cikinta ba. Juyawa ya yi zuwa Library ɗinsa dake gidan Hakimi.
Zama ya yi saman kujera cikin sauri ya duba dukkan mayan kadarorinsa kama daga kan
filaye, gidaje, ɓangaren Library na karatun addinin dana kimiyya ya buɗe, S.A.H
bank duk yana fahimtar dukiyar tasa har ya kasa shi kansa bai yi tunanin abin da ya
mallaka ya kai girman hakan ba, a haka kuma bai haɗa dana wajan Mother ba wanda
suke mallakinsa. Tunani ya fara tunda yana da bank a kano me zai hana ya buɗe S.A.H
BANK a sauran jahohin da suke Nigeria? Da kuma kamfanin sarrafa shinkafa ƴar hausa
mai kyau wacce za taiwa talakawa sauƙin siya kan fara shi mai sauƙi?. Da wannan
tunanin ya yi na'am da zuciyarsa cikin nutsuwa ya fita daga Library ɗin ya koma
haɗaɗɗan bedroom ɗin nasa, kai tsaye toilet ya shige tare da sakarwa kansa shower
yana sauke numfashi a hankali ya fara sauka daga dokin zuciyar yama mance da batun
aure baki ɗaya. Domin daman shi bai dame shi ba indai macace da kanta zata gudu ta
ce bata son shi domin ba zata samu abin da take buƙata ba daga gare shi. Fitowa ya
yi yana ƙamshin shower gel Shea body butter ya shafa jikinsa ko body spray bai
fesa ba ya cilla mint bakinsa tare da kwanciya saman bed ya rufe idanunsa.
Umar-khan ne ya shigo cikin parlourn Abba Hakimi bakinsa ɗauke da sallama. A
hankali Abba Hakimi ya ajjiye azkar ɗin hannunsa wanda yake na yamma tare da duban
Umar-khan cikin kamala da kamewa ya ce.
"Umar-khan yaya dai?" Shafa kai ya yi yana tare da faɗin. "Abba Hakimi daman Mother
ta ce ko Sheikh yana nan? Gaba ɗaya baya can gida" murmushi mai laushi Abba Hakimi
yai yana zame idanunsa daga kan Umar-khan ɗin "Aliyu ai ba yaro bane?" Abba Hakimi
ya faɗa a gajarce Umar-khan ya miƙe ba tare daya samu cikakkiyar amsa daga bakin
Abban Sheikh ɗin ba ya ce "Ni ma zan je gida, sai da safe Abba Hakimi" yana buɗe
azkar ɗin ya numfasa kaɗan cikin sakin fuska ya ce "A gaida Abdulrashid"
"Zaiji sosai"
Umar-khan ya amsa wa Abba Hakimi yana barin gidan baki ɗaya tare da tunanin inda
Sheikh ɗin ya yi domin yana tsoro idan zuciyar ta motsa kowa sai yaji babu daɗi.
Momi A'isha ce ta shigo ɗauke da tray ɗin abinci zama tayi bayan ta ajjiye ta ce
"Ina ta mamakin abin da ya sanya mahaifin Sheikh ke aikata haka kamar wani mara
ilimi, kuma ya dace ace ka saka baki ko auren ya keso Sheikh ya yi sai ka zaɓa masa
ƴar mutunci, kaga hankalin Barrister bai kwanta da zaɓin Engineer ba" gaba ɗaya
Abba Hakimi ya tattara nutsuwarsa kafin ya ce "Ku dai mata yawanci tunaninku ɗaya,
bani da ikon ture umarnin uwa ga ɗan shi,kada ki manta ni uban rana ne kuma mariƙi,
I don't have the courage to deny the Engineer what he wants"
"Gaskiya dai, ni ina tunanin ko sbd Sheikh bashi da lafiyar yin magana cikin jama'a
ya sanya Engineer ke yi masa haka? Kuma yana ganin He is the only male among his
children, shi ne ya kamata ya tsaya kan harkokinsa na yau da gobe ya ɗauki buri ya
saka akan Sheikh ɗin?" Abba Hakimi ya amshi fruits ɗin data gama yanka masa kafin
ya kalleta da kyau ya ce
"Baki ke aiki ko ƙwaƙwalwa? Babu wani