Author : Nimcyluv sarauta Category : African Stories & Novels
da Halisa da Maimoon. Mother ta ce ba zai taje
rakiya ba.
Kai tsaye gidan Abba Hakimi suka nufa. Yaa Sheikh ne kawai ya shiga sbd babu
lokaci, ya shige jikin Abba Hakimi yana sauke numfashi, rauninsa ya bayyana
kasancewar yana jikin Abban nasa, a karo na farko ya riƙe Abban da kyau murya bata
fita ya ce.
"Ba zan iya ba Abba" Abba Hakimi bai fahimta dan haka ya ce "Kai mutum ne mai
tsoran Allah da gudun hakƙin wani, balle matarka kada ka damu, ita Halisa ƴar riƙo
ce shekara nayi zan amshi abata" ya zare jikinsa yana sauke numfashi tare da yin
sallama.
Daga nan suka ɗauki Umar-khan kai tsaye suka shige Airport inda jirgi ke jira.
Tunda daga jirgin hankalinta ya tashi amma bata nuna ba, ta riƙe hannunta da kyau,
Umar-khan na gaba sai Zahrah Halisa na biye da ita a haka suka shiga cikin jirgin,
suna shiga Halisa ta riƙe kanta sbd tsoro, Umar-khan ya kalli Zahrah ya ce "Wajenku
na cikin vip" Zahrah ta kalle shi ta ce "Yana ciki ne?" Umar na zama a mazauninsa
ya ce "Gaskiya ban sani ba, ku shiga ku gani" ba tare da Zahrah ta ce komai ba ta
nufi vip ɗin, jin takun tafiya a bayanta yasa ta tsaya tare da kallon Halisa ta ce
"Ke kuma lafiya kike boye ni? Na manta ba a saba ba, Umar nuna mata wajan zama"bai
ɗago kai ba ya ce "Wajan zamanku ɗaya ne ai duk vip" Zahrah ta riƙe ƙugu ta ce "kan
uba, tayaya haka ya kasance kana nufin tare zan zauna da ita ga mijina kuma?" Sai a
lokacin ya ɗaga kansa tare da kallonta ya ce "To ai suna ɗaya kuka amsa, matsayi
ɗaya"
"Kamar yaya suna ɗaya? Umar ya kamata kasan me zaka ce dani, ka gane" ya haɗe
hannaye waje guda ya ce.
"A'a ranki ya daɗe, mai da wuƙar mijin naki shi ne ya bada umarnin haka" ta haɗiye
yawun takaici tare da shigewa vip, daman ita Halisa ta jima da shigewa, dan haka
Zahrah na shiga ta samu Halisa zaune ta sunkuyar da kanta ƙasa, wajan ya haɗu sosai
akwai duguwar kujera wacce Halisa take zaune akai, sai kujera mai guda biyu,
tunanin Zahrah ya bata mai guda biyun ita ce wacce zasu zauna ita da Yaa Sheikh, ta
nemi waje ta zauna idanunta akan Halisa ta ce.
"Ina mijina?" Tai shiru taƙi cewa komai. "Ba magana nake miki ba, na lura kin fara
ganin wajan barcina?" Ta ɗago lulu eye's ɗinta wanda suke sheƙi kamar an tara musu
ruwa sbd yadda hawaye ya kwanta cikinsu. A tsiwa ta ce.
"Ina mijina?" Zahrah ta zare ido tare sakin baki da jin abin da Halisa ta ce. Ƴar
fillo tai murmushi kawai tare da girgiza kai ta ce "nifa kamar haka naji kince Anti
shi ne nake ƙara tambaya, to a haka naga wajan kam" Zahrah ta ɗaga hannu zata ɗauke
Halisa da mari suka ji gyaran murya.
Gaba ɗaya suka ɗaga kai a tare daga Uwar gidan har amarya Zahrah, basu yake kallo
ba wayarsa yake sakawa a airplane mode. Yaa Sheikh ya riƙe ya saba akan duguwar
kujera yake zama, sbd yana ɗan samun hutu yayi barci kafin ya isa inda zashi, kai
tsaye ba tare daya lura da Halisa ba ya nufi duguwar kujera tare da zama dab da
ita. Numfashin Halisa ya kusa ɗaukewa sbd wani mugun shaƙar ƙamshin Roja da tayi,
gashi Yaa Sheikh ya zama ƙato babba sosai har kafaɗar shi na rufe kanta.
A karo na farko zuciyar Zahrah ta shiga bugawa gabanta ya faɗi,ta juya ta kalli
Halisa wacce ta kafe Yaa Sheikh da idanu, a hankali kuma ta kalli Yaa Sheikh wanda
ya nuna kamar bai san da mutane a wajan ba. Ta kasa magana ta rasa a wanne ma'auni
zata saka haka, anya bata hau tsaunin da zai kaita zuwa ga hallaka ba?. A zahiri
Yaa Sheikh ya mance ya taho da matayen nasa har biyu, da uwar mata da kuma ƴar
rainon shi. A hankali aka fara sanarwar a ɗaura blet, Zahrah ta ɗaura Halisa kuma
ta rasa me ake cewa sbd cikin harshen turanci ake maganar, sai faɗa computer take
tana ƙara sanarwa.
A nutse ya ware rawani kansa domin duk a zaton shi, shi kaɗai ne a cikin vip ɗin,
kyakkyawar sumar shi ta bayyana abin mamaki ilahirin sumar kan shi daga gaba jajir
take tamkar wanda ya fara furfura, daga baya kuma baƙaƙirin tai luff har wuyan shi.
Ya sauke hannunsa akan Alkyabbar jikinsa ya ɗan buɗe gaban kaɗan sbd nauyi da tayi
masa, yana kammalawa yaja blet, daidai lokacin aka fara sanarwar a shirya jirgi zai
tashi, Halisa ta razana ta ƙanƙame jikinta, kanta ya shiga juyawa sai tayi nan luu
tayi nan luu, lokacin da jirgi ya ɗaga zuwa sama Yaa Sheikh ya lumshe idanunsa ba
zato ba tsammani yaji an fasa wata gigitacciyar ƙara kafin ya buɗe idanu ta faɗo
kan cinyarsa babu numfashi....
Paid
It's 500
08119237616
[1/3, 4:48 PM] Abk: Da fararen idanunsa masu tsari yake bin ta da idanu da mamaki,
ganin da gaske bata mutsi tsoran da ya yi mata yawa ya sanya numfashinta ya ɗauke,
hannunsa basu taushi ya sanya akan fuskarta kamar mai jin tsoran gently ya shiga
bubbuga kumatunta amma ko motsi ba tayi ba, ya ɓata fuska ganin tun ba a je ko'ina
ba, yarinyar zata fara bashi wahala.
Yatsun hannunta biyu ya kama yaja da ƙarfi yana buga tsakiyar kanta ajjiyar zuciya
ta sauke da ƙarfi tana jan numfashi, sai kuma ta fashe da kuka tana riƙe wanda taji
kusa da ita sosai cikin fillatanci take faɗin.
"Don Allah ku sakko dani ƙasa zan mutu wayyo Dada wajanki zan dawo" saukar
numfashin da yaji yana sauka a fuskarta da ƙamshin da ba zata manta da shi ba ya
sanya ta buɗe idanunta wanda ta rufe su saboda tsoro, wanda ta gani take jikinsa ya
bata mamaki numfashinta ya kusan ɗaukewa, sbd yadda ya yi mata kwarjini a idanu ga
Alkyabbar jikinsa duk ta rufe mata jiki, a jikinsa yaji shi take kallo bai kalleta
ba, ya sanya hannu tare da riƙo kafaɗunta da kyau yana zaunar da ita akan kujerar
sosai.
Yana daga inda yake ya ranƙwafa sosai tare da miƙa hannu zuwa inda blet ɗin take,
kwantaccen sajansa ya shafi fuskarta ta sauke numfashi mai zafi wanda ya sanya Yaa
Sheikh daka tawa da kama blet ya jima kafin ya zaro blet ɗin da sauri ya maƙala
mata, yana ƙoƙarin janye jikinsa ta ɗora hannunta a tsakiyar tafin hannun shi..
"Uhmmm" ya ce a ransa yana ɗaga idanunsa zuwa gareta ya kalli cikin idanunta ba
tare da ya ce komai ba, Halisa ta sake damƙe hannunsa da kyau cikin rawar murya ta
ce. "Usako miyetti masin" idanu kawai ya lumshe mata tare da matsawa waje guda.
A fusace Zahrah ta kunce blet ɗin jikinta tare da tashi tayi kan Halisa tana kumfar
baki ta ce.
"Ke dan uwarki mijina sa'anki ne da har zaki faɗa kansa da ƙazamin jikinki? Shegiya
mara ƴan ci" Halisa ta kalli Zahrah ta ce "To Anti godiya nayi masa fa, kuma dana
faɗa ƙasa naji ciwi ba ƙwara na faɗa kan shi ba, kuma ai ban masa nauyi ba ko kaji
ciwo?" Ta faɗa tana juyawa tare da kallon Yaa Sheikh, shi gaba ɗaya hankalinsa baya
kansu hannunsa riƙe da darija yana dubawa, tuni ya mayar da hiramin kansa baya
buƙatar kowa yaga wani sashe na jikinsa.
"Kauuu!!" Zahrah ta ɗauke Halisa da mari tare da nuna ta hannu ta ce "zanci uwar
data haifi babarki" ƙarfi da girman zagin yasa Yaa Sheikh kallon Zahrah a zuciyarsa
yana Istigifari bai ɗauka wani zai iya zagin ba, ba a taɓa zagi a gaban shi ba,
hakan ya zama abu sabo a gare shi. Bai ce komai ya ɗauke kai tare daci gaba da duba
jaridar hannunsa, zafin marin yasa Halisa fashewa da kuka sosai tana kifa kanta a
cinyarta, kuka take sosai wanda rabin kukan baƙin cikin zagin da Zahrah tayi mata
ne. Yaa Sheikh kukan yake ji har tsakiyar kansa jin kukan na neman tarwatsa masa
kai yasa ya miƙe tsaye tare da buɗe wata ƙofa ya shiga.
Zahrah ta kasa haɗiye mamakin yadda Yaa Sheikh ya nuna kulawa ga Halisa, haushin
abin da ya yi yasa ta huce akan Halisa ɗin.
Sun yi nisa da tafiya sosai wata maid ta shigo cikin wajan tana tambayar Zahrah me
za a kawo musu, Zahrah ta karɓi abin hannun matar ta duba, kana ta zaɓi abin da
take so. "Nace ko zaki iya sauyawa wannan yarinyar waje?"Flight attendant ta ce.
"Her name please?" Zahrah ta ɗan kwaɓe fuska ta ce "Something Halisa.." ta ɗan
danna wani abu a jikinta tare da yin magana bayan ta gama ta ce. "I think ita ce
Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu right Maah?" Zahrah ta ce "No, bana tunanin ita ce
her name is Halisa Danejo Rome" Flight attendant ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce
"Sorry Maah babu da wani suna a jerin wanda za su yi tafiya yau, Halisa Sheikh
Aliyu haydar Aliyu shi ne" A fili Zahrah ta ce "Kan uba" sai yanzu ta tuna sunan
Yaa Sheikh kenan, da sunansa akai mata visa kenan?.
"Oh maybe she's the one, zaki iya sauya mata wajan zama?" Matar ta ce "Yes Maa,
daman yanzu na duba ta samu sauyin wajan zama tuni" Zahrah tai murmushin jin daɗi
matar ta kalli Halisa wacce ko inda suke bata kalla ba sai Ajjiyar zuciya take
saukewa.
"Can you follow me please?" Zahrah ta ce "ki mata hausa maybe she understand you"
matar tai murmushi ganin yadda Zahrah take kwaɓe fuska ta ce "But she's your
daughter?" Wata uwar harara Zahrah taiwa matar ta ce "Kinga alamar ina da ƴar ne?"
Ita ma tai murmushi ta ce "Ai babu mmki idan nace miki a tunani zaki haifi yara
biyar ma" Zahrah ta kalli jikinta da kyau ta kasa cewa komai, sbd baƙin cikin
Flight attendant.
"Halisa biyo ni kinji" a sanyaye duk da tsoran jirgin da take tabi bayan matar har
zuwa champer 2 na jirgin. Nan ma dai kujeru biyu ce kawai a wajan ba kowa, ta nemi
waje ta zauna cike da tsoro.
Not too long da zamanta ya shigo tare da zama kan kujera da sauri ta sunkuyar da
kanta domin a tunaninta faɗa zai mata, sai taga mai kulata ba ƙafarsa kawai ya
miƙe. Tana zaune aka turo basket na abinci, zallar fruits ne sai gorar ruwa, aka
ajjiye a gaban Yaa Sheikh ita kuma aka ajjiye mata chips da egg sai haɗin salad da
ruwa. A hankali ya ɗauki orange ya saka bakinsa ya shiga taunawa cikin nutsuwa,
Halisa ta kalle shi bakinta na rawa ta ce.
"Amma wannan abin yabann sha'awa ɗan sammani" ya jita sarai amma yai mata banza sai
da orange ya ɗin ya rage guda uku ya ɗauki guda ɗaya zai ƙara sakawa a bakinsa tayi
saurin riƙe hannun shi, bai zaici haka ba ya kalli hannunta tare da kallon gefen
fuskarta ta langwaɓar da kanta gefe ta ce "Ayya ka sammin bana, ni ma idan kaga
abuna zan maka naga kana ta haka da idanu" yabi idanunta da kallo yadda ta lumshe
su tare da buɗewa tana gwada masa yadda yake, ta kwance na hannunsa tare da kawai
bakinta, ta ɗauka wani daɗi ne a orange ɗin.
Ya sauke numfashi ganin hannunta na neman taɓa dugun gemun shi cikin ƙasa da murya
mai sanyi ya ce. "Ci kani" ta yi saurin saƙona tana komawa wajanta, bai ƙara taɓa
komai ba a kayan sai ruwa daya sha sosai.
Misalin 10 na dare jirginsu ya sauka a Prince Muhammad bin Abdul'aziz International
airport, sai nasarwa ake kowa ya saka blet jirgi zai sauka, ganin bata fahimci me
ake cewa ba ya kalleta da kyau, ya riƙa ya saka blet a jikinsa ba damar cirewa kuma
sun ɗan bada tazara, a hankali jirgi ya fara girgiza yana rawa Halisa ta rikice
daga tai nan sai tayi nan, shuuuuu jirgin ya yo ƙasa tai gaba luuu zata kifa shiru
tayi jin an riƙo kafaɗar ta, ya haɗa da gefen ƙirjinsa tare da riƙeta.
Ƙuri tayi masa da idanu ganin nasa idon a rufe ta kasa motsawa shima kuma bai
saketa ba, tunda har lokacin jirgin bai gama daidaita ba, balle ya samu damar sauka
a titinsa. Ɓangaren Zahrah sosai taji daɗin ganin an ɗauke Halisa yanzu zata samu
damar kasancewa da mijinta hankali kwance, sai dai tun tana jiran dawowar shi amma
shiru gashi bata da ikon tambayar wani, bisa dole tai shiru. Bata tsammaci abin
haka ba, sai ji tayi ana faɗin sun ƙarasu Madina tuni ai. A hankali ta saka blet
tasan dai dole tare zasu tafi gida. Jirgi na yin parking ya saketa da sauri kafin
ta buɗe ido ya fice daga cikin wajan, ta shiga zare idanu yanzu idan guduwa sukai
yaya zatai?. Tana wannan tunanin Umar-khan ya shigo yana murmushi ya ce "Matar
Malam tasu muje" ta miƙe tana kallon Umar-khan ta ce "To kai gida kaje ka dawo ne?"
Yai dare ya ce "Hhhhhh ai kam na koma Nigeria na dawo" tabi bayansa da sauri ta ce
"Kasan me" ya ce "sai kin faɗa" ta lumshe idanun ta buɗe ta ce "A ciki da abin ya
tashi sama kawai na faɗa kan Malam na ɗauka zai dukeni kamar yadda anti da dake ni,
sai naga kawai ya lumshe idanu ni kam nace masa na gode"
"Uhm" kawai Umar-khan ya ce domin bashi data cewa a wanann batun, suna fitowa
Zahrah na fitowa suka kalli juna da Halisa kowa ya ɗauke kai. Bayan sun sauka daga
jirgin Zahrah ta kalli motar dake gabansu ta ce "Ina My Excellency?" Ya ce "Yana da
meeting ne, sai zuwa 12 zai dawo" Zahrah ta ce "meeting da wannan daren?" Umar-khan
ya ce "Manyan mutane daman sai dare suke meeting, muje kada mu ɓata lokaci" Zahrah
ta shiga bayan mota Halisa ba haka, Umar-khan na gaba shi da driver.
Wata haɗaɗɗiyar area suka nufa gaba ɗaya mazauna wajan larabawa ne, gidan dake kusa
da na Yaa Sheikh sune hausawa, faɗar kyau da tsarin gidan Yaa Sheikh ɓata baki ne,
flat gida na zamani, motoci birjik a harabar gidan ga tarin flowers da ɓangaren
swimming pool, ga
Wajan tsuntsayen shi kusan duk rubutun gidan da rabci ne, yana da ɓangare na
Musamman da yake bawa manyan mutane darasi.
Zahrah ta dubi haɗaɗɗan parlourn mai ɗauke da wasu ƙawatattun kujeru, sai ƙamshi
yake, ga wasu fitito masu kyau iya haɗuwa ya haɗu. Umar-khan ya kammala shigo da
kayansu ya ce. "Ɓangare uku ne a gidan, wancan ɓangaren Yaa Sheikh na tsakiyar
kenan, na gefen dama babu na kowa na hango ma babu kowa, ya ce ki zaɓi wanda kike
so, ɗayar ki bawa mai aikin naki" Zahrah ta kalli part ɗin hannun hango taga bayan
na Yaa Sheikh yafi kyau dan haka ta ce "Na ɗauki na ɓangaren hango ka shigo mini da
kayana ciki" tana faɗin haka ya miƙa mata key ɗin ɓangaren ta amsa hana shigewa
ciki. Ya kalli Halisa ya ce.
"Daman girman kine shiga ɓangaren damar" murmushi kawai tayi, Umar-khan ya riga
yasan da ɓangaren Yaa Sheikh da wanda Halisa zata zauna a manne suke, domin akwai
ƙofa kai tsaye daga ɗakin Yaa Sheikh wacce zata kawo shi ɓangaren Halisa ɗin. Ya ja
mata kayan zuwa jiki, ya yi mata bayanin komai da kitchen da banɗaki komai dai,
kana ya nuna mata yadda ake amfani da kayan kallon ɓangaren ta.. "Sai da safe Matar
Malam" ta jinjina masa kai. Zahrah ma ya kai mata kayan kana ya nufi nasa gidan.
Misalin 1:30 motar Yaa Sheikh tai parking driver ya buɗe masa ƙofa, a hankali ya
fito ya ɗan tsaya yana duba ko wanne ɓangare yana yin addu'a sbd ya saba, ganin
hadari a garin kuma yasa duk ya rufe Windows na gidan. Ya nufi ɓangaren shi, wanka
ya yi ya ɗora jallabiya mai kyau a jikinsa, black tea yake son sha amma bai san
yarda zai ba, gashi kuma yasa a sallami masu aikin shi. Haka dole ya zame
jallabiyar ya saka kayan barci yana buƙatar hutawa sosai, sbd ya samu peace of mind
kwana biyu yana stressed kansa da yawa. Kiran sallar farko a kunan Yaa Sheikh da
Halisa domin zamanta wajan mother ta saba da tashin asuba, a hankali ya nufi
bathroom tare da sakarwa kansa ruwa mai zafi kana ya yi alwala tare da yin brush,
cikin zafin nama ya shirya cikin kyakkyawar shigar shi wacce ya saba, farar
jallabiya ya ɗora hirami a kan shi, bakinsa ɗauke da aswaƙ ya nufi Masjid Malik
wanda shi ke gabatar da jam'i a can, bayan idar da Sallah ya yi karatu wa jama'a
kamar yadda ya saba.
7:00 ya shigo gidan da mmki yake jin parlour ƙamshi mai daɗi, yana ƙoƙarin shigewa
part ɗin shi ta ce "Jamɓanduna?" Jin fillatanci yasa ya fahimci ba Zahrah bace
amanar shi ce kuma ƴar riƙonsa, ya juya tare da kallon ta, tana cikin wata duguwar
riga mai kyau plush pink sai baby hijab a kanta, kai ya ɗauke ta ce.
"Anti Zahrah ba ta shi ba, ni tun ɗazo na tashi ina ta kallo" shi dai bai ce komai
ba ya shige part ɗinsa tabi bayan shi da kallo kafin ta juya zuwa kollon girke-
girken da ta keyi.
Yana shiga part ɗin sa ya zauna saman kujera, tare da kiran number Umar-khan babu
jimawa ya ɗauka a nutse ya ce "Ka yi komai, kada ya shige kwana biyu a nemi gurbin
karatun" yana faɗin hakan ya kashe wayar, tare da kiran wata number mgn ɗaya ya yi
ya kashe..
Halisa na zaune taji telephone line na ƙara ta miƙe sauri daman Umar-khan ya faɗa
mata yadda ake amfani da ita, tana ɗagawa taji ance "Mrng maaa, the breakfast is
ready Yaa Sheikh na jira" Halisa ta ce "Kika ce me?" Ta ce "Abincin Yaa Sheikh ya
kammala kina magana da ɓangaren kitchen, yanzu maid zata kawo" Halisa ta taɓe baki
tare da komawa ta zauna, babu jimawa wata mata mai fararen kaya ta shigo ɗauke da
tray da butar shayi ta ce "Mrng Maa ga shi Yaa Sheikh na jira"
Halisa ta amsa tana miƙewa tsaye Zahrah ta fito cikin kayan barci da alama ko
sallar ba tai ba, ta kalli matar ta ce "lafiya?" Tai mata bayani ta ya mutsa fuska
ta ce "Ok daman ita ce mai aiki bata ta kai, ki sama mini breakfast mai kyau yanzu"
matar ta juya Halisa ta riƙe tray Zahrah ta ce "Sai ki fara aikin ki tun yanzu,
kije ki kai masa breakfast ɗin ki dawo ki shirya mini kayana a wardrobe" Halisa ba
ta ce komai ta juyawa zuwa inda taga Yaa Sheikh ya nufa, bakinta ɗauke da sallama
bata sani ba ko ya amsa ko bai amsa ba, yana zaune kan kujera ta ƙarasu har inda
yake ta tsuguna ta ce "Ga shi wai" ya gyara zama yana tsiyaya tea ɗin tare da
kaiwa bakinsa. "To kai iya wannan kake sha ne? Ko nayi maka abinci?" Da idanu
kawai yake bin gefen fuskarta da kallo ta gyara zama ta ce "Mother ta ce kai mijina
ne" ya ware idanu da sauri yana binta da idanu, ta buɗe baki zata sake magana caraf
ya saka hannu tare da kame