Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   52 / 66

153K to 156K   out of 196.1K words

9:00 PM] Abk: *_Sorry for disappointed.. wallahi ban san ydda zan faɗa ba,
nayi busy aiki ya yi yawa am trying my best naga na sauke hakƙi amma i couldn't.
Kuyi haƙuri bear with me, har gobe har bini IDAN BA KE na kuɗi ne, masu yi mini
magana na turo musu daga page kaza zuwa kaza ku saurara, idan buƙata kike ki siya
Ubangiji bai hanaki 500 ba.. 08119237616_*


Ya riƙeta sosai tare da hanata damar yin wani cikakken surutu. Halisa ta tsorata
sosai amma Jikinta ya saki ta lafe jikinsa tana sauke numfashi a hankali, Yaa
Sheikh ya jata zuwa bakin bed ya zauna tare da zaunar da ita saman cinyarsa a
hankali ya riƙe ƙugunta, ya goga mata tattausan gemunsa mai laushi da santsi.
"Waye kai"
Ta furta tsoran na barinta ba tare da sanin waye ba, amma haka nan taji ta daina
tsorata musamman da taji ƙamshin Abbanta a tattare da mutumin. Duk yadda taso
mutumin daya riƙeta ya rungome ya yi magana ƙiyayi, ta luff jikinsa tana sauke
numfashi cikin nutsuwa Yaa Sheikh ya zame hijabin Jikinta tare da yin cilli da shi,
babu wasu cikakkun kaya a Jikinta duguwar riga ce iya qwiwa, kyawawan cinyoyinta a
waje suna ta glowing wanda cikin Jikinta ya ƙara musu gaske. Tsit tayi ta shiga
sauke numfashi abin da ke damunta ya shiga tasowa Idanunta ta rufe tana rirriƙe
hannunsu dake shafata dasu.
"Zaka cutar dani, ka... Ka bari" ta faɗa a rarrafe cikin rawar murya.
Bai amsata ba, sai ɓalle bottles ɗin gaban rigar da ya yi, bai tsaya zarewa ba
cikin wani irin sabon yanayin daya tsinci kan shi, ya fisge ya cillar.
A taushashe cikin harɗewar harshe da ɗaukewar numfashi
Cikin rashin ya ce.
"Yaa Allah! Wayasubuhanallah, Allahu Akbar" a fili kuma ya ja numfashi tare da
sauke shi a wuyanta yana manna mata sajan shi wanda ke ƙara sanyata cikin wani irin
yanayi, wanda a ko wanne lokaci zata iya sakar masa kuka idan har bai bata abinda
gangar jikinta ke buƙata ba, tuni ta sakar masa ragamar komai.
In a romantic style ya zame rigar tare da janta ƙasa shoulders ɗinta suka bayyana,
da sauri ta faɗa saman ƙirjinsa ta riƙe ƙugunsa sosai, sbd babu bra a Jikinta haka
nan ta samu kanta da jin kunyar wanda ke tare da ita, kuma taji a Jikinta wajan ya
zubawa idanu, duk inda yaso kallah gani yake ba ruwansa baya yiwa idanuna shamaki.
Ya faɗaɗa fuskarsa da murmushi tare holding nata back fuskarsa a wuyanta yana zuba
mata wasu hot kisses wanda ta kasa riƙe kanta ta saki wani sangartaccen kuka ta ce
"Waye ne kai? zan faɗawa Abbana tunda mugunta kake mini"
Ya fahimci muguntar da take, ya ɗora hannunsa a cikinta wanda ya fara kumbura sukai
baya ta faɗa ƙasa, shi kuma ya yi mata rumfa hannunsa dake mararta ya shiga murzawa
har ya zame rigar, ta rufe idanu Jikinta ya ɗauki rawa tunaninta wani abu zai mata
sai taji saukar softness lips ɗinsa a cikinta ya sumbata, ya ƙara sumbata murya can
ƙasa ba tare data san magana ya yi ba ya ce.
"Abbie is here, Ammi is here" ya ƙara yi mata wani kisses ɗin a cibiya yana shafa
cikin ya ce
"Oh God, protect my unborn child"
Ya zame jikinsa tare kallon fuskarta da yake ganinta tarwai a idanunsa ita kuma ta
lumshe idanunta, ya sumbaci goshin da kuncinta daga nan bata sake sanin meke faruwa
ba, sai farkawa tayi taga ƙarfe 5:15 na yamma.
Ta farka a tsorace da ƙyar ta iya addu'ar tashi daga barci, ji tayi duka gabɓanta
ciwo suke, ta saka hijabi tare da kunna hasken bedroom ɗin
ta shiga ƙarewa ɗakin nata kallo babu komai sai ita ɗaya,ta dafe ƙirji ta ce "Ya
Allah meke shirin damuna ne? Me ya sa nake ganin Abbana?" Ta dafe kai tana zama
bakin kujerar.
Mother data buɗe ƙofa ta shigo ta ce "Halisa?" Tai firgigit ta buɗe ido a rarrabe
kamar mara gasky ta ce "na.. na'am"
"Meke damunki, ɗazo na shigo na sameki kina ta barci zuwana na uku kenan, yanzu
kuma ina sallama shiru"
Ta juya ta kalli bedroom ta ce "Mother ba kiji ƙamshin Modibbona ba?" Ta saki baki
ta ce
"Wanne irin ƙamshi ni Maryamu, ƙamshin kuma na Yaa Sheikh bayan kin san baya ƙasar"
Ta saki kukan tsoro, shagwaɓa hadda rigima ta ce "shi na gani, yanzu ya shigo muna
tare har barci ya ɗaukeni"
Mother ta saki tsaki ta ce
"Kin fara samun matsala, ki tashi kiyi wanka da sallah kici abinci, ina son duba
lafiyarki"
Ta goge idanu tare da yin kicin-kicin da rai.
"Meye kika haɗa fuska, ba zaki mini wannan sangarta taki da kukan rashin abinyi ba"
Ta ƙara haɗa fuska ta ce
"Allah ya baki haƙuri, naga dai Abbana Dr ne, kije kawai zai duba ni"
Mother ta ce
"To sannu ƴar Abba ba kiji kunya ba? Bayan kin gama yi masa ɗiban Albarka, baki
duba girman shekarun shi da gemun shi, da ilimin da Allah ya bashi kika watsawa
idanunki toka kika ce bakya son shi ya sake ki?" Ta marairaice fuska tana tura baki
ta ce
"To yanzu na cire tokar shikenan? Nifa ina son Abbana ko ya yi sakinma wallahi ban
sako ba"
Mother ta saki baki gudun kada ta sake magana, Halisa ta sakar mata layi ta ce
"Uhm ki fito ina jira" ta ce "To, amma idan kin san zaki mini wannan allurar
wallahi bana so" ita dai Mother ba ta ce komai ba, sai da taje ƙofa zata fita
Danejo ta ce
"Mother wallahi idan Father yazo ki bisa zama babu miji babbar masifa ce kuma
jarrabawa uhm"
da sauri Mother ta fice daga cikin bedroom ganin tsakani da Allah ita Halisa
shawara take bawa Mother ɗin. Wanka tayi tai sallah tare da yin Istigifari na
makarar da tayi, ta shirya cikin wata light blue ɗin abaya mai stones da flowers
tana da faɗin wuya hakan yasa rigar ya zauna sosai a ƙirjinta wanda ya ƙara cika da
sauyi, babu rama a Jikinta domin kullum ƙara buɗewa take musamman waje biyun nan,
da hips da brest ta fuska ne ta fayau Idanun ya faɗa sai dogwan hancinta kawai.
Ta fito Main parlour tana rolling vail ɗin abayar hannunta riƙe da waya. Ba kowa a
parlourn kai tsaye ta shige kitchen ta samu salad da tumatir da albasa ta haɗe waje
guda fal cikin plate, ta zuba white oil da yaji kaɗan ta saka maggi, ta haɗa da
lemon tsami yawonta har tsiyaya yake sbd wani irin kwaɗayi daya taso mata, daman ta
jima ba taci komai ba, sai abincin da Ummul ta bata. Ta fito da kwaɗon salad ɗin da
lemon citta data haɗa ta daka ice ya yi wani irin sanyi na shige misali. Zama tayi
saman kujera ba tare data lura da wanda ke zaune ba, hannu baka hannu ƙwarya ta
dinga cin salad ɗin, fisgewa taji anyi kamar tai hauka ta ce
"Wane mai son ɗaukan zunubin ne" ta faɗa tana miƙewa Idanunta ya sauka akan Khalil
Ahmad Sarki ta saki murmushi tana tsalle tare da rungome shi ta ce
"Oyoyo my prince my hamma" ya watsa mata harara ya ce "Princess wannan yajin is not
good for your health" ta marairaice ta ce
"Please Hamma ka bani wallahi ji nake kamar zan amai idan banci ba" Umma A'isha ta
ce
"Kada ka damu babu abin da zai mata" ya watsa hannu ya ce "daman dai fushin Yaa Lee
nake jiye mana" Halisa bata sake cewa komai ba sai cin salad take, tana gamawa ta
ɗauki ruwa mai sanyi tasha. "El-bashir karɓo mini ruwan nan" El-bashir dake zaune
kusa da Halisa bata sani ba,ya ware idanu ya ce "ki barta mana" cikin tsawa ta ce
"Mubasshir ka kawo mini nace ko?"
Halisa na tsaka da shan ruwan sanyin wanda take jin daɗin shi taji an ƙwace ta juya
da sauri suka haɗa idanu da El-bashir cikin masifa ta ce "Waye kai? Meye haɗinka
dani da zakai mini shisshigi cikin lamarina?" El ya kasa ce mata komai sai Dada ce
ta ce "Ni zakiwa rashin kunya ba El-bashir ba, kuma ba a taɓa sauya tuwo suna"
Halisa ta miƙe duk da taji daɗin ganin mahaifiyarta amma hakan bai hana ɓacin ranta
bayyana ba ta ce "Ba zan taɓa son shi tunda baya ƙaunar Abbana ya nemi kashe shi"
tana magana faɗin hakan tai bedroom idanunta cike da ƙwalla. Dada ta miƙe zata bita
El-bashir ya ce "Please Mom u hve to understand her feelings komai tayi daidai ne,
ni ne mai laifi nima kuma bisa kuskure amma dani da ita ba a san wanda yafi son Yaa
Lee ba"
Dada ta ce "Duk wannan bai zama dalilin da zata wulaƙantaka kuma ta tsaneka ba"
Khalil ya ce
"Be patient Mom, I'll talk to her tana da zafi da riƙe abu ne" ya lallaɓa Dada ta
zauna shi kuma ya nufi wajan Halisa..
Washegari Halisa ta shirya ta nufi makarantar Ibadur-rahman.
Zahrah na zaune gefen gado Dr yana ƙara dubata domin yau za a sallameta daga
asibiti ya ce "Allahamdulillah jiki da sauƙi, kici gaba da shan magani" tai
murmushi ta ce "Thank you Dr, da baka taimaka mini ba, ba zan taɓa samun farin ciki
da auren Yaa Sheikh ba, naji daɗi yadda plan ɗinmu na ciwon Cancer ya tafi daidai
babu matsala" Dr ya ce
"Imagine da gaske ace kina da Cancer" ta ce "Please daina faɗa ban shirya tafiya
lahira na bar Yaa Sheikh ba, burina naga ranar aurenmu amma sai nan da wata uku ai
thank God an kawo kuɗi dai" Dr ya jinjina kai ya ce
"Congratulations, yanzu kin daina sharholiyya kenan?" Ta ce "Har abada babu ni ba
ita, daman can tsautsayi ne balle yanzu dana fahimci Yaa Sheikh tsanar da ya yiwa
kalmar Zina, sai naji na tsaneta nima, ina son shi kamar zan mutu ina buƙatar
soyayyar shi da kulawar shi, wannan dalilin yasa nace ka faɗa masa ina da ciwon
Cancer it was all my plans" Surry dake bakin ƙofa riƙe da Muhammad ta dafe ƙirji a
ranta ta ce
"That's means she's lying to him? ba wani ciwon Cancer" tai murmushi tana girmama
ƙarfin son zuciyar Zahrah. ta juya ba tare data shiga ba, Dr ya sallami Zahrah suka
koma gida ta fara shirye-shiryen biki a karo na biyu duk safiyar Allah sai ta kira
Yaa Sheikh wani lokaci ya ɗaga wani lokaci ya share, tun tana dannewa harta fara yi
masa complain shi kuma ya ɗan fara sassauta yanayin sbd condition ɗin da take ciki.
A hankali yake tafiya kan shi a ƙasa yana gyara zaman alkyabbar jikinsa fitowar shi
kenan daga zaman tattaunawar da sukai akan aikin hajjin da za a fara nan da kwana
goma. A yau ɗin kuma yake son barin Madina zuwa Makka, amma yana da muhimman wajan
da yake son ya ziyarta ya kaiwa Allah kukan shi, ya kuma karkato da hankalin Saif-
wazir zuwa gida. Daga nan masallacin juma'a ya nufa yaja jam'i kana ya yo gida.
Umar-khan dake zaune ya ce
"Ka samu kira, da saƙwanni" ya jinjina kai idanunsa rufe a taushashe cikin gajiyawa
ya ce "Kayi magana ko?"
Umar-khan ya ce
"Abubuwa da yawa sun ƙare a kamfanin sarrafa shinkafa, munyi magana da Manager
Khalil dole za a tura wani Chaina"
Yaa Sheikh ya yi shiru ya
ware idanu ya ce
"El-bashir" Umar-khan ya ce "I don't have his number" da ido kawai Yaa Sheikh ya
kalli Umar-khan ya ce, da sauri cikin ladabi ya miƙa masa wayar a hankali kamar
mara lafiya ya zuba number El-bashir a wayar ya danna kira tare da saka handsfree.
Lokacin El-bashir yana tare da Abba Hakimi da Dada tare da sauran family wayarsa ta
fara kaɗa Algaita, ganin sunan da bai taɓa tunani ba da sauri ya ɗauka yana faɗin.
"Assalamu alaika"
Yadda ya amsa wayar with so much respect yasa sukai tunani Mai martaba ne. Yaa
Sheikh ya amsa kafin ya ce
"You're alone?" El ya ce
"Many people" lokacin Halisa ta shigo hannunta riƙe da Alkur'ani fuskarta rufe da
liƙab El-bashir ya ce "Include your wife" Halisa kamar wacce ta fahimta tayi saurin
ƙwace wayar Jikinta na rawa ta kara a kunnenta ta ce "Abbana" Ya runtse idanunsa
zuciyarsa tai kyakkyawan bugawa gabaɗaya Jikinta ya ɗauki sautin muryarta wacce ya
yi kewa da jinta , ya rungume hannayensa a ƙirji, ganin haka ya sanya Umar-khan
miƙewa tare da fita yasan yanzu ba lallai ayi maganar kamfanin ba. Yadda taji anyi
shiru ta ƙara tabbatarwa Abbanta ne akan layi ta zame wayar daga kunnenta ta ɗora a
bakinta ta sakar matsa kiss ta ƙara sakar masa wani kiss ɗin
"Muu'ah... Muu'ah" Abba Hakimi ya yi ƙasa da kai, Dada ta miƙe tabar wajan, mother
ta saki baki da hanci Umma A'isha dake kakace tayi murmushi kawai, Khalil Ahmad
Nuran Sarki ya kalli Halisa yana yabawa rashin ta indonta.
Mubasshir El-bashir Ahmad Nuran Sarki ya kalli kyakkyawan ƙanwar ta shi mai
tsananin kama da shi, komai nasu iri ɗaya ne so da ƙaunar Princess Halisa Ahmad
Nuran Sarki kuma Halisa Danejo Rome uwa uba Matar Malam Halisa Yaa Sheikh Aliyu
haydar Aliyu ya wanzu a zuciyarsa. Ta buga tsalle tama mance da cikin Jikinta tana
sakin dariya hawaye na zubu mata ta fasa ƙara da ihu wanda ya karaɗe parlourn
bakiɗaya ta ce
"I love You Abbana, I miss you Modibbona, ina sonka Yaa Sheikh ina sonka ina sonka
zan cinyeka da soyayya Mijina mai gemu" tuni Khalil ya ɗora Camerar iphone ɗinsa
akanta. Yaa Sheikh ya nutse cikin lallausan kujerar da yake yanayin da yake ciki ba
zai barshi yayi magana ba, bai sai adadin ke yake ji akan wawta da ƙuruciyar ƴar
fillo ba. Ƙit ya kashe wayar yana fesar da numfashi ya faɗaɗa fuskarsa daga kamewa
yana jan gemunsa ya ce.
"Bbyn Abba, Matar Malam" wayarsa tai haske ya duba.
"Check Your WhatsApp"
Number Khalil da ita aka turo saƙon.
Akwai Wi-Fi gidan yana shiga vedio ya shigo, milk ɗin hijabi idanunsa ya gane masa,
ya yi downloading vedion da sauri ya miƙe idanunsa akan Halisa dake tsalle na
muryar jin muryarsa ya katse ya kira number Mother tana ɗauka, a karo na farko
cikin zafin murya harshensa na riƙewa ya fara faɗa da masifa ta inda ya shiga bata
nan yake fita ba, don me za'a barta tana tsalle bayan ansan ba ita ɗaya bace if
something happens to her fa? Yana gama faɗan ya kashe wayar ba tare daya bar Mother
tayi magana ba. Ta riƙe haɓa ta ce
"Yau zafin zuciyar Aliyu Gadanga ya motsa masifa kenan" jikin Halisa ya yi sanyin
ganin yadda Yaa Sheikh ya yi mata banza ko dai da gaske bashi bane kamar Yadda El-
bashir ya faɗa?...
*_3 month later_*
Gabaɗaya harabar filin da ake saukar Alkur'anin da bikin hafizan mahaddata a cike
yake da manyan baƙi, iyayen yara da ɗaliban saukar. Kimanin ɗalibai 100 ne cif sai
hafizai guda 35 sanye suke da fararan hijabi tas sun san rufe fuska da liƙab,
hannunsu sanye da safa haka ƙafarsu, wanda sukai saukar kuma milk ɗin hijabi ne a
jininsu, makarantar matan aure ce amma ba'a taɓa sauka wacce takai wannan ba acikin
shekarar. Ɗaya bayan ɗaya aka dinga kiran sunan hafizan suna karatu daga ƙarshe aka
ce "Halisa Sheikh Aliyu haydar Aliyu" a sanyaye ta miƙe tana ƙara buɗe hijabinta
sbd cikinta daya fara tasawa na kimanin wata huɗu zuwa biyar. Yau ta ƙara
tabbatarwa Abbanta Yaa Sheikh ya gujeta rana mafi muhimmanci da zai tayata murna
amma babu shi a wajan ko wacce mace mijinta na tare da ita, amma banda ita. Tayi
ƙasa da murya tana sauke numfashi a hankali cikin sautin murya mai amo! Wanda duk
wanda yasan yadda Yaa Sheikh yake ƙira'ar Alkur'ani yaji karatun Halisa zai san
cewa rainon shi ce, cikin fidda tajweed da makarijin huruf ta fara karatun cikin
suratul Nisâ'i. Wajan ya yi shiru aka shiga tasa Camera a kanta duk da ba a ganin
fuskarta wani irin karatu take mai cike da nutsuwa. A hankali ya juya fararen
idanunsa akanta yana mai yabawa da karatun nata farin cikin da yake ciki ya ninka
nata, shi ne maƙo na musamman da sarkin Kano amma har ya bata Alkur'ani da
certificate da allo bata san shi ne ba, tana gama karatun ta saki kuka wanda an
ɗauka na farin ciki ne, ita kuma zallar damuwa ke damunta na rashin ganin nata
gwanin ko ta ce tsohon mijinta. Aka dinga basu kyaututtuka anan aka Shaida akwai
muhawarar Alkur'ani ta ƙasa da ƙasa wacce hadda sunan makarantar a wacce za a fara
karawa ta cikin gidan kafin a samu gwarzuwar da zata tsallake matakin ƙarshe.
Taro ya tashi Halisa taci kuka ta ƙoshi Mai martaba ya dinga alfahari da Princess
haka Dada, Ummul ta rungome Halisa jin hadda zazzaɓi a Jikinta,cikin kuka ta ce
"Ummul baya so na da gaske, na shiga uku Ummul zuciyata" Ummul ta ce "kada ki damu
kanki, akwai gajiya da zazzaɓi tare da ke" kafin Halisa tayi magana suka ji ance
"Assalamu alaikum" ƙamshin turaren Roja ya ƙara bayyana mai sallamar Halisa ta juya
da sauri tana cire liƙab ɗin fuskarta sukai idanu huɗu da Yaa Sheikh dake tsaye
cikin wata dakakkiyar shadda fara tas ya ɗora Alkyabba mai tsananin kyau da tsada
ya fito a Yaa Sheikh ɗin shi. Hawayen fuskarta ya ƙasa tsayawa,Ummul tai murmushi a
hankali ya shiga takawa har zuwa inda take tsaye ta haɗe fuska kamar ba ita ke
kukan rigima ba, yana zuwa ta juya zata gudu ya saka tattausan hannunsa ya kama
nata tare da dawowa da ita baya, a hankali cikin wani kyakkyawan yanayin ya juyawa
su Ummul baya yana mai shigar da Halisa cikin Alkyabbar shi ya zagaye ƙugunta da
hannunsa duk biyun suka manne da juna, ya ranƙwafa daidai wuyanta ya sumbaci
kuncinta da bakinsa mai tsafta tare da hura mata iska a kunne cikin raɗa ya ce.
"Congratulations Hafizata.... Ruhin Aliyu" ya faɗa yana lashe gefen kunnenta...
[1/28, 11:21 AM] Abk: Halisa ta ɓata fuska tare da yin kicin-kicin da ranta, Yaa
Sheikh ganin idanun jama'a baya kansu ya saka tattausan hannunsa tare da tallafo
fuskarta ya ɗora fuskarsa saman nata idanunsa na yawo a fuskarta yana son ta sanya
nata idanun cikin nasa, ko ya fahimci rigimar ta yanzu ta mece? Duk da yasan ya yi
laifi mai yawa har bai san ta ina zai fara ba?.
Yadda gangar Jikinta tayi kewar shi haka zuciyarta, ta kasa jurewa yanayin musamman
ƙamshin turaren dake sauya mata yanayin da take ciki.
Ta ɗago Idanunta a hankali ta zuba cikin nasa gently ya lumshe nasa gajiyayyun
idanun yana jin abu na fisgar shi kamar ya jawota ya rungume na tsayin lokaci
Ganin nata ya fara kassara masa jiki da son sauya masa yanayin da yake ciki
Ya rufe ido ya buɗe a hankali ya zameta daga jikinsa ba tare da ya ce komai ba ya
juya daidai lokacin Umar-khan ya yi parking da mota, kai tsaye ya shiga suka bar
wajan da sauri.
Tabi motar da kallo tana jin kamar ya tafi da zuciyarta ne, tsoro ya kamata ta
shiga addu'ar Allah ya sanya ba tafiya ya sake yi ba a karo na biyu?. "Hankali ya
kwanta?" Cewar Mother dake tsaye cikin wata atamfa ta ɗora mayafi akai murmushi
Halisa tayi ta ce
"Ni daman a kwance yake" Mother ta riƙe baƙi ta ce "Ba shakka, to zan sanar masa
kada ya dawo" tayi saurin ɓata

52 / 66