Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   49 / 66

144K to 147K   out of 196.1K words

ta ce "Wallahi
babu inda zaka sai ka sakeni ba zan ƙara zaman aure da kai ba kona kwana ɗaya....



*Kada ku manta sunan Littafin IDAN BA KE masu cewa labari ya ƙare kawai ja nake
you're guys are mistaken.. ni ma ɗin ai na fi na gama ko? Sbd na samu peace of mind
na samu cikakken hutu kafin Allah ya a haɗamu a wani bayan Ramadan. Burina kuna
karatun da idanun basira, kuna hango daidai da kuskuren dake cikinsa ba wai kawai
nishaɗi ba ya haka ne zan fahimci nawa kuskuren..... Mata masu ɗaukan shawarar ko
wanne mutane a kiyaye wata shawarar mugunta ce, kuma ba don Allah ake baka ita ba,
sadaukarwa ga masu ƙaramin tunani irin na Halisa.
[1/21, 9:28 PM] Abk: https://vm.tiktok.com/ZMYeKp4XV/
Follow my account comment, like, share❤️
🫶🏼💋

Yaa Sheikh ya riƙe kan shi daga rungumar da tayi masa, ya rufe idanu yana sauke
numfashi a hankali, ji ya yi komai na shi ya sauka daga kan setting, duk yadda
gangar jikinsa da zuciyar dake ɗauke da sabon son matar malam a kullum sukai kewar
Jikinta, muryar, rigimarta haka ya kame kan shi ba tare da nuna cewa da gaske ya
azabtu da rashinta kusa da shi, ya shirya nuna mata ita ɗin kawai ya ke so, ba wani
abu data mallaka daga baya ba, zai tabbatar sai ta neme shi da kanta.
"Ba zan zauna da kai ba, bana son ka Yaa Sheikh tun da bani ka ke so ba, ba farin
cikina ka ke so ba, gangar jikina ka ke muradi"
Har lokacin tana riƙe da shi tana kuka kamar ranta zai fita, abu biyu ke mata zafi
da ƙona a zuciyarta, yadda ya amince da batun auren Zahrah wanda ko a mafarki bata
yarda cewa zai iya ƙara wani auren ba, balle ta yi tunanin zai auri wata aba wai
Zahrah? Raguwar maza da raguwar mariƙin daya riƙe Yaa Sheikh ɗin Matsayin ɗan cikin
shi, shi ne yanzu ya amince ya amshi raguwar mahaifin shi.
Ya ware idanunsa akanta cikin rashin son magana mai tsayi ya ce.
"Sake ni Matar Malam!"
Tayi saurin sakin shi domin tama manta ta riƙe shin. Ta ce "Ai dan ban sani ba,
kasan ba zan taɓa riƙe jikin ka ba"
Ya jinjina mata kai kawai tare da juyawa a zuciyar shi ya ce "Matar da duk ita ta
lalata dani, da ban ɗanɗani zaƙin ba ina zan damu, ina ganin shaiɗan cin mace ni
Aliyu"
"Don Allah ka sake ni, zuciyata bugawa zatai muddin naci gaba da sanya ka cikin
idanuna matsayin mijin dake aurena, kaje can ka auri raguwar uban riƙon ka"
A wannan karan ya kasa shanye maganganun Halisa, yadda take fidda zance kamar wacce
aka zaunar tare da yi mata huɗuba. Ya juya bakiɗaya zuwa inda take fuskar shi tayi
jajir alamar wannan shi ne karan farko da ranshi ya ɓaci da maganganunta, tai tsaye
zuciyarta na bugawa tare da harbawa ganin yadda ya yo kanta babu wasa akan fuskar
shi, sai tsoro ya kamata.
Yana zuwa ya yi mata rumfa zata ja baya ya saka hannu ya damƙo ƙugunta tare da
jawota ya mannata da na shi ƙugun, ta lumshe ido tana fidda numfashi, sbd wani abu
daya shiga yi mata yawo mai kama da feelings. Ta nemi ƙwace kanta domin iya turaren
rojan daya kama cika ɗakin kaɗai ya isa ya sauya mata lissafi balle kuma yanzu da
ƙugunsu dake manne, kwantaccen gemun shi mai laushi kwance a wuyanta yana shafa
mata, yanayinta ya sauya ta kasa motsi a hankali cikin nutsuwa yana mai ƙara
fahimtar yanayin nata saɓanin ita da bata ga sauyi ko guda tattare da shi ba,
Ya goga mata tsinin hancinsa a fatar wuyanta yana nai fesa mata zazzafan numfashi
mai ɗauke ƙamshin mouth mint chocolate freshener, ta buɗe ido da ƙyar wanda suka
jirkita ta sanya cikin nasa idon kamar yadda yake kallonta. Ya zura hannunsa ta
ƙasan ƴar rigar barcin dake cikinta, ya ɗora tafin hannun a saman cikinta ta wajan
mara, a hankali yaja ido tare da rufewa numfashinsa ya ɗauke na wani lokaci sbd
ɗumin cikinta daya ratsa hannunsa, wata Soyayyar uba da ɗan shi ta bijirowa Yaa
Sheikh, ƙaunar abin da ke cikin Halisa ya mamaye dukkan ƙofofin dake zuciyar shi,
ɗiya maca ce? Ɗa namiji ne bai sani ba, amma son ko wanne jikinsa ya kama Yaa
Sheikh, tare da son uwar Unborn ɗin na shi.
Nan da nan Halisa ta birkice ta nemi nutsuwarta ta rasa, bakin neman sakin ya yi
shiru ji take tamkar ya jata ya rungome, a zame jikinsa ka ɗan tare da zamewa ya
tsuguna akan qwiwoyin shi nutse cikin wani mataccen yanayi duk da yana riƙe kan shi
ya ɗora bakinsa a mararta tare da sumbata, wajan zame bakinsa ya sakar mata wani
kyakkyawan kisses wanda ya sanya tai saurin kama sumar kan shi, ya dinga addu'a
yana tofawa a cikin kafin ya miƙe tsaye, yana miƙewa tayo jikinsa zata rungome ya
ja baya yana faɗin "Ki ke cewa me?" Ya faɗa a gajiye yana jan gemunsa, Baƙin ciki
da takaicin ya cika ta ya kunna ta da ashana tare da sanya fetur ciki, amma ya
barta ita ɗaya tana ƙona kanta.
Zafi biyu! Ya ƙaro da ƙyar take buɗe ido ta ce
"Nace bana son ka Aliyu!"
"Aliyu?" Ya maimaita a zuciyar shi. Is that true ƴar fillon shi ke kiran shi da
sunan da ko Abba Hakimi baya faɗa sbd girmama ilimin Ubangiji? Amma ƴar cikin shi
ta faɗa gatsal! Hankali kwance. Ta ƙara cewa
"Kaje ka auri karuwar uban riƙon naka, ka ɗora daga inda ya tsaya"
Da ace Yaa Sheikh na cikin tsarin maza masu dokan matayensu, da babu shakka sai ya
lakaɗawa Halisa mugun doka wanda zai dawo da ita daga haukan daya sameta, ya juya
yana sauke numfashi har zuciyar shi ta samu nutsuwa daga zafin da tayi dalilin
ambaton sunan Allah.
Murya can ƙasa irin ta marasa lafiya ɗin nan ya ce "Zan baki, ki tuna mini zuwa
safiya" yai shiru ya nisa ya ce.
"Ba Zahrah ba, ko mother idan na yi niyya zan aura, tunda ban sha nononta ba, idan
ina son mace da zuciya ɗaya to ko wacce ta shahara a karuwanci zan iya aura, da
zarar ta tuba ni kuma zan Jahadi, Ina son Zahrah da gaske"
Yana faɗin haka ya juya zuwa wajan freezer ya ɗauki Apple da gorar ruwa mai sanyin
gaske ya koma bedroom ɗin da yake ciki.
Yana barin wajan Halisa ta zube ta dinga kuka kamar ranta zai fita, ashe da gaske
son Zahrah yake? Yanzu duk daɗin da Yaa Sheikh ke jiyar da ita Zahrah ce zata samu,
su kwana tare?gado ɗaya wata kilama a manne a jikin Abban nata? Ta dinga kokawa da
numfashinta tana riƙe ƙirjinta, ita kawai jin abin take kamar mafarki, amma hakan
bai dameta ba, indai zai saketa taje ta gana da ƴan uwanta domin tayi al'ƙawarin
idan har igiyar auren shi na kanta to babu inda zata, sai manne cinyoyi take kamar
wacce hauka ya kama wani mugun son kasance da ɗa namiji ya shige ta ido rufe ta
saki kuka ta ce
"Mugu" Yaa Sheikh ya ɗaga gorar ruwan duk sanyinsa haka ya zubawa cikinsa bai iya
shan Apple ɗin ba ya ajjiye gefe guda, kusan abu ɗaya ke damunsu ya shiga sakarwa
kansa shower mai sanyi daga ƙarshe ya fara lafilfilo yana kaiwa Ubangiji kukan shi
akan ya sausauta zafin zuciyar Matar Malam ɗin.
Ummul ta buɗe ƙofar bedroom ɗin ta shigo bakinta ɗauke da sallama tsaye ta kanshi,
yana gyara zaman diamond rolex watch, tai tsaye tana kallon kyakkyawan dattijo ko
magidanci da Allah ya bata matsayin ɗa ɗaya tilo, babban mutum masanin addinin
Musulunci tsantsa babban likita wanda ya san aikin shi, bai haƙuri da riƙo da
ƙaddara a duk sanda ta zo masa, mai tausayi da imani da jinƙan na ƙasa da shi.
"Arɗona" ya juya ya kalleta ya nisa ya ce
"Sabahul khair Ummul"
Ta ce "Yawwa, wani abu ya haɗaka da Daughter?" Kasancewar baya ƙarya kai tsaye ya
ce "Rikici ne, akan sakin ne" ta numfasa cike da tausayin Yaa Sheikh ta ce "Anya ba
zakai mata abin da take so ba?" Ya dubeta a raunace ya ce
"Ummul na saki Zawja?"
Ta ce "Na san zafin da zuciyarka ke ciki, Halisa yarinya ce amma ina mmki taurin
kai da zafin zuciyarta,bana son na fara jin zafinta wata macan sai an mata sakin
take shiga hankalinta, idan sakin ne mafita ya kamata kayi ko ɗaya ne"
Ya taka har zuwa wajan Ummul ya riƙe hannunta a taushashe ya ce
"Kiyi addu'a, komai zai daidai" "To Allah ya kawo sauƙi cikin lamarin ya kuma
daidaita tsakaninku" ya jinjina kai ta ce "Tafiyar ce? Kaje wajan Abba Hakimin?" Ya
ce "Zuwa 11:30 zamu ta shi, yanzu zani" ya faɗa yana jin cewa zai kewar ganin koda
masifar da take masa, amma ko zai sha wahala itama dole ta sha domin ya fahimci
fitinar da cikin Jikinta ya sata.
"Allah ya tsare ya kare, ya ƙara maka haƙuri haka lamarin aure yake wani daɗi wani
sai an wahala, wanda aka wahala ɗin sai kaga yafi Kwari da inganci" Shi dai
kallonta yake harta gama ya juya ya nufi waje sai da ya yi nisa ta ce
"Na manta tun safe Maimoon da Daughter suka shige" nan ma ya jinjina mata kai, ya
nufi part ɗin Dattijo da Hajia suka gaisa, Alkyabbar jikinsa na ɗaukan idanu yana
basa ƙamshi mai daɗin shaƙa yana mai gyara zaman hiraminsa ya ƙarasa harabar gidan
ya samu Umar-khan dake tsaye yana jiran shi yana zuwa ya buɗe masa ƙofa yana faɗin
"Barka da safiya Yaa Lee" ya rufe idanu ya buɗe alamar ya amsa domin maganar wahala
take masa, kai tsaye gidan Abba suka nufa, babu wanda ya yi magana har suka ƙarasa
Ishaq-Hakim ya buɗewa Yaa Sheikh Umar-khan ya fito suka nufi ciki A parlour suka
samu mother ta saka Halisa a gaba ta inda ta shiga bata nan take fita ba, gabaɗaya
haushin Halisa ya kamata bata san haka take da taurin kai ba sai yanzu. Dr A'isha
ta ce
"Barrister ni banga abin faɗa ba, ba a ga abin da yake mata ba sai ita za a ga
laifinta, kuma ita ce mace ita zata zauna da shi tunda bata so ba sai a rabu da
ita ta fito da wanda take so ta aura"
Mother ta ce "Kenan ke ce ki ke mata huɗuba?" Tai saurin cewa "A'a,nikam ina ruwana
meye nawa miji kowa da nashi, bayan itama da wayonta tunda har ciki ne a Jikinta ai
ta shige ai mata huɗuba"
Daga bakin ƙofa aka ce
"A'isha ta shi kibar gidan nan" ta ɗago da sauri suka haɗa idanu da Yaa Sheikh,
hantar cikinta ta kaɗa ta tsare shi da kallo kwarjinin shi da cikar kamalar shi da
haiba suka cika mata idanu ta ce "Me ka ce?"
Ya shigo ciki har inda take zaune da hannu ya nuna mata ƙofa ya ce
"Ki bar gurin nan tun kafin na nuna ɗaya ɓangarena, babu ke ba matata" ta ce
"Yaa Sheikh ni ka ke cewa haka kamar wata sa'arka? Ni ka ke rabawa da matarka?"
Abba Hakimi ya ce "Ta shi ki ke, tunda Yaa Sheikh ya yi magana akwai abin da ki ke"
tai ƙwafa tana ficewa daga parlourn.
Yaa Sheikh ya nemi waje ya zauna fuska ɗaure idanunsa a ƙasa ba tare daya ƙara
kallon kowa ba
"Ya akai Aliyu?" Sai a lokacin ya sauka numfashi ya ce "Tafiya zan yi" Abba Hakimi
ya ce "Tafiya da gaggawa haka? Har tsayin yaushe?" Ya miƙe yana cewa "kawai sai
Allah ya dawo dani, bari na je kada na rasa jirgi" Mother ta ce "Allah ya tsare ya
ki ya ye angon Zahrah, muna nan mun fara shirye-shirye yanzu Ummul take sanar mini
ai yanzu zakai aure, daman wata rabuwar alheri ce ka samu kyakkyawar mata" Umma
A'isha tai murmushi tasan da biyu! Wai anjefi uwar miji da rani, an jefi tsuntsu
biyu da dutse ɗaya. Yaa Sheikh ya juya yana cewa "Wajanta zan fara zuwa" Ya fice
abin sha da sauri Halisa ta miƙe Mother na kiranta tai banza da ita, tana zuwa ta
tsaya Idanunta kaca-kaca da hawaye ta ce "Ka ce na tuna maka, ka sake ni, ko sati
ba zan ƙara ba zan samu mijin aure dalilin cikin nan kawai zan jira na haihu" Yaa
Sheikh bai damu da Umar-khan da Ishaq-Hakim dake tsaye ba ya riƙo hannunta tare da
dawo da ita gaba.
Ya tsareta da narkakkun idanunsa ta ɗauke kai a hankali ya jawota jikinsa tare da
shigar da ita cikin Alkyabbar shi zata ƙwace ya riƙeta da kyau! Ya ce
"Bake na rungome ba, jina na, ƙwan dana zuba miki har ki ka ɗauka da shi zan
sallama" ta ɗago zata kalle shi gemun shi yaƙi bata damar haka ta ce "Ɗana dai,
daga yau ka daina tunanin kai ne uban shi" shi dry ma ta bashi ya shafa cikinta ya
ce "Shi ya sa naga ke ki kai cikin, nutsu muyi magana" tai banza ko wanne second
guda sai zuciyarta ta buga na fargabar da gaske wai wajan Zahrah za shi? Ya ce
"Haliyserh da gaske baki so na?" Ta ce "Wallahi bana son ka, na tsaneka, ka rabu
dani" ya jinjina kai ya ce "Zan miki abin da ki ke so, zan kuma tafi tafiyar da
zaki mamaki wacce ba lallai na dawo da rai ba, ki faɗawa abin da zaki haifa ba
Mahaifinsa yaƙi babarsa ba, ita mahaifiyar ita taƙi uban, wannan zai zama rungoma
ta ƙarshe, ki jiƙa jikin ki, ki sha Haliyserh Ahmad Nuran Sarki, zan je nai sabuwar
rayuwa da Zahrah ina fatan alheri" ya jim yana ɗan matseta a ƙirjin shi kafin ya
sumbaci goshinta yana zareta daga jikinsa, ya zaro farar Envelope daga jikinsa ya
damƙa mata ya ce "Your Divorce paper" yana bata ya shiga mota Umar-khan yaja motar
da gudu zuwa airport...

Tsammaci abin da baka tsammani, aiki da hankali yafi aiki da kwakwalwa😊
[1/22, 12:22 PM] Abk: https://www.instagram.com/p/CnqD-7co24F/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

Follow my I.G Account😍
Comment tag your fam and friends share the link🔥💪🏾
Much love

Ta dinga juya Envelope ɗin a hannunta Idanunta akan gate tana kallon yadda motar
Yaa Sheikh ke ficewa, ji tayi kamar yana tafiya da zuciyarta da ruhinta Jikinta ya
yi sanyi wani abu mai kama da faɗuwar gaba ya risketa. Ita ce ta ɓukaci sakin amma
sai taji wani baƙin ciki na sakin, kamar yadda ki wacce ƴar mace taje jin baƙin
ciki idan an saketa, shikenan ta zama bazawara Yaa Sheikh zai je ya yi rayuwa da
Zahrah "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Na shiga uku, wayyo Allah"
Ta faɗa tana dafe kanta tare da yin baya zata faɗi Mother tayi saurin tare ta ta ce
"Ke lafiyarki ɗaya ki ke shirin suma?"
Halisa ta riƙe Mother ta ce "Wallahi ya sake ni, ya sakeni na shiga uku" ta fasa
wani ihu tana riƙe Mother. Ita kanta Mother sai da ƙirjinta ya buga tsoro ya
kamata,
Wanne irin hukunci Yaa Sheikh ya yankewa zuƙatansu? Ta tabbata ya haƙura da Halisa
kenan? Ta ce
"Saki kuma? innalillahi....," Tama ƙarasa faɗar abin da tayi niyya ganin Halisa
kamar zata data iska sbd yadda yake kuka, ya sanya ta jata zuwa cikin parlourn Abba
Hakimi yana shirin barin wajan sai ya tsaya ya ce "Lafiya dai?"
"Ina fa lafiya, abin da take hauka neman ta samu" Abba Hakimi yai shiru yana
nazarin maganar. "Kamarya Maryam?" Mother ta nuna mata Envelope ta ce "He divorced
her, Now she is a widow"
"Lallai ran Malam ya ɓaci, tunda har ya iya rubuta saki, banso haka ta kasance ba
da yabi komai a hankali"
Abba Hakimi ya koma ya zauna ya ce "Muga"
Mother ta miƙa masa Envelope ɗin, ya amsa yana gama warewa ya ci karo da rubutu
kamar haka.
_“Ta ya ya ki ke tunanin ni Malam Aliyu Haydar Aliyu zan iya sakin matata Princess
Halisa Ahmad Nuran Sarki? How can i spend my time ba tare da ƴar fillona ba? Taya
zan jure ganin rigmar da take mini tana wa wani? Zan ci gaba da rainon ƴata,
matata, gimbiyar masarautar Sokoto, Yaci gaba da son Matar Malam na tsayin rayuwa
zuwa mutuwa, na barki zuwa lokacin da zaki nemeni da kan ki, ki ɗauka aurar Zahrah
mu duka ƙaddararmu ne kece sanadi kuma, One thing shi ne IDAN BA KE ba Yaa Sheikh
na ki, Abbanki, Modibbonki na yarje kiyi makaranta ki je garinku idan hakan zai
faranta ranki.. Fatan alheri”_
Abba Hakimi ya yi murmushi a ɓoye bayan ya kammala karatun, zuciyar Mother cike da
zullumi ta ce "Saki nawa ya yi mata Abba?"
"Sakin tsayin rayuwa!"
Cewar Abba Hakimi.
Ya bawa Mother takardar ta fara karantawa, ta jinjina kai tana sakin ajjiyar
zuciya. Umma A'isha ta karanta itama, Dr A'isha data shigo yanzu ta miƙa hannu zata
amsa Abba Hakimi ya ce "Aishatul-humaira bani nan" Umma A'isha ta miƙa masa.
"Abba mu gani,naga duk kun duba ko?"
"Eh, amma ba dole kowa ya gani ba" tai shiru ba don ranta ya so ba.
Halisa ta kalli Abba Hakimi ta ce "Da gaske Abbana ya sakeni Jon wuro?" Ta faɗa da
ƙyar.
"Na ɗauka haka ki ke so?" Ta ɗaga masa kai zuciyarta na zafi da soya.
Ya ce "To meye na damuwar?" Ta fashe da kuka mai cin rai sai da tayi mai Isarta
babu wanda ya tankata ta ce
"Kuma sai ta sakeni da ciki, daman da gaske baya so na? Zai je ya auri karuwa"
mother tai murmushi a ɓoye
kafin ta ce "me zai sa ya zauna inda aka tsane shi? gashi can wata zata mutu akan
son shi, aini naji daɗin haka kina haihuwa sai ki fito da miji musha biki" ta ƙara
fashewa da kuka tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗinta ta faɗa gado ta mance da cikin
Jikinta birgima kawai take akan bed ɗin tana ihu tana tsinewa Zahrah albarka.
daga ƙarshe ta fara cilli da komai na bedroom ɗin ta rasa wa zata faɗawa damuwarta
waye zai bata shawara mai kyau, Dr A'isha ce mai sonta kawai, kuma ya rabata da ita
ta zauna tana ta kuka.
Ƙarar wayarta ya tsayar da ita daga kukan da take ganin sunan Dada ya sanya taji
zuciyarta ta karaya ta ɗaga wayar murya a dashe ta ce
"Hello!" Dada ta ce
"Kin kyauta Danejo, Allah ya yi miki Albarka, ko da wasa naga ƙafarki gidan sarauta
sai ranki ya ɓaci, idan har sbd haka ki ka aikata abin da ki kai"
Cikin kuka ta ce
"Hande en boni na lalashe me na yi kuma?"
Dada ta ce "Ba ke ba, hatta ni Besty nada iko dani balle ƴar dana haifa, ke ko
nauyin furfurar shi ba kiji ba? Shekarunsa? Darajar ilimin addinin shi,ki zubawa
idanunki toka sbd baki data ido ki ce wai ya sake ki? Kin san hukuncin macan dake
neman saki wajan mijinta? Kin san azaba da tanadin da Allah ya yi musu? Wallahi ba
ruwana wannan ba tarbiyyar dana baki ba, akwai wacce ke son lalata mini ke, ko kuma
wata ɗabi'a ki ka sauya wacce ban sani ba, ki tuba ki bi

49 / 66