Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 66

18K to 21K   out of 196.1K words

ɗinsa ta nufa tun daga nesa ƙirar arar Sheikh Muhammad didat ta ratsa
cikin kunnuwanta da Mmkin fal fuskar Mother ganin ƙofar shiga parlournsa a buɗe.
Ƙamshin air-cod ya ratsa cikin hancinta. Tana shiga idanunta ya sauka akan Umar-
khan dake zaune gabansa ɗauke da system yana duba wani abu, ganin Mother ya sa
Umar-khan saurin miƙewa tsaye ya ce "Sannu da zuwa Mother" "Yawwa Umar-khan ina
Aliyun?" Hanyar da zata sadaka da bedroom ɗin Sheikh ya kalla yana faɗin "a Parlour
na samesa lokacin da nazo, ina fara yi masa magana akan wannan case ɗin ya tashi ya
shige bedroom har yanzu bai fito ba" jinjina kai tayi ta nufi bedroom ɗin, babu
abin da bedroom ɗin yake sai ƙamshin turarensa ROJA wanda ya a jima da kama ɗakin
duk da cewa bai fiye rayuwa a cikin gidan iyayen nasa ba, yafi rayuwa a Madina idan
yana ƙasa Nigeria kuma yafi rayuwa a gidan Hakimi. ba kowa nan ma a bedroom ɗin sai
tsarin ɗakin da Mother tabi da kallo wanda a kullum yake Sauya mata, komai na ɗakin
fari ne tas, ɓangaren clothes, shoes, perfumes. Komai daban yake. Juyawa tayi zuwa
parlourn tana faɗin "Umar-khan Aliyu baya nan fa? Ko dai ya tafi gidan Hakimi?"
Umar-khan yai shiru ya ce "Bashi da ikon fita, kamar kullum ƴan jaridu na waje ta
ko'ina maybe yana Library ɗinsa" sai a lokacin ta tuna da Library tana zuwa ciki ta
samesa zaune akan wata ƙyakkyawar kujera wacce take juya kanta da kanta ya rufe
idanunsa, sumar kansa ta ɗan bayyana sbd yanayin naɗin rawanin nasa wanda ya yi da
farin hirami. Hannunsa harɗe a ƙirji. Zama tayi kujerar dake kusa dashi tana kama
hannunsa ta ce "Abbana Babana" ajjiyar zuciya Sheikh Aliyu Haydar ya sauke sbd jin
sunan da Mother's ta kirasa da shi amma ya kasa buɗe idanunshi domin baya son ta
fahimci halin da idanunsa ke ciki wanda sune kaɗai suke fallasa raunin zuciyarsa.
"Buɗe idanunka mu yi magana Babana, ba zan taɓa bari kayi gidan yari ba, zan
tabbatar da kai a matsayin mai gsky ba zaka wulaƙanta ba" nan ma shiru ya yi mata
bai ce komai ba kamar yadda ta tsammata. Hawayen da take maƙalewa ne ya kwance mata
wanda ya zuba a tafin hannun Sheikh. Da sauri ya ƙankame hannunsu dake riƙe da nata
yana buɗe idanunsa a hankali wanda suka sauya daka rinewar da sukai. Fararen idanun
nasa ya ɗora akanta ganin hawaye a Fuskarta ya ƙara sashi cikin damuwa amma sam
hakan bai bayyana a garesa ba. "Kayi magana Babana rashin maganarka shike sawa a
dinga tunanin baka da gasky, zuciyata ba zata jure ganinka haka ba" Kallonta yake
har lokacin bai ce komai ba. Ganin bashi da niyyar magana yasa Mother fashewa da
kuka sosai tana miƙe tsaye da sauri ya riƙe hannunta gam! Yana miƙewa tsaye
jallabiya ce jikinsa mai kyau da tsada ga laushi da tsantsi. Kai ya fara Girgiza
mata yana matse hannunta sosai babu abin da Sheikh yake ƙauna sama da mahaifiyarsa
sai Father daga su Hakimi sune duniyarsa. Hannunsa mother ta riƙe ta ce "Try to
speak Sheikh ban damu ba nasan zan fahimce ka, zamu Court bani da wani proof da zan
kareka, mene gasky?" Riƙe hannun Mother Sheikh ya yi tare da fara buga ƙafa yana
ƙoƙarin buɗe bakinsa. Ganin haka yasa Mother taimaka masa wajan riƙe hannunsa tana
faɗin "Ahha say something, speak Babana, say it" hannunta duk biyun ya kama ya riƙe
yana runtse idanunsa sai buga ƙafa yake tuni hawaye ya fara cika idanunsa. "Yee...
Ƙaƙƙƙaaa... M...mmm" kai ta ɗaga masa tana shafa kansa a fisge bayan ya buga
ƙafarsa da ƙasa yana saka hannun Mother a bakinsa ya ce "Babbbban akaita ba, bbbb
ba zan taɓa yin yin yin haka ba mother" yana faɗin hakan yana ƙara saka hannun
Mother a bakinsa duk ya jiƙa mata hannu da yawunsa mai ƙamshi a ƙoƙarinsa na ganin
ya yi magana daidai waya baiwa ta Sheikh idan koyarwa zai yana samu maganarsa ta
fita yake fara karatu cikin sauri baya tsayawa sai ya gama yana gamawa baya ƙara
cewa komai yake fita daga hall. Wani irin rauni ya kama zuciyar Mother tausayi da
ƙaunar Sheikh ya ƙara wanzuwa a zuciyarta wacce irin larura ce haka wacce bata
barin har babban mutum? Zare hannunta ya yi domin har ransa bai san lokacin daya
saka hannunta a baki ba a hankali ya juya zai bar wajan da sauri mother tana goge
hawaye ta ce "Aliyu" cak ya tsaya tana ƙoƙarin magana Umar-khan ya shigo wajan da
sauri gaba ɗaya suka bisa da kallo Umar-khan ya ce "Sheikh na shirya mota a ƙofar
baya, yanzu zamu bar gidan nan jami'ai na hanyar zuwa nan zasu kamaka" ko motsawa
Sheikh bai ba shi dai ya san ba zai taɓa hana abin da Ubangiji ya tsara afkuwa ba.
"Jeka Aliyu ka bisu su fitar dakai Sheikh" Mother ta faɗa tana jan hannunsu ganin
haka yasa ya bita har zuwa bakin wata sabuwar mota shiga ya yi. Drivern yaja, Umar-
khan shima ya shiga mota, Saif-Wazir ya shiga wata motar. Motar ƙarshe kuma Ishaq-
hakim ya shiga kai tsaye suka nufi wata hanya ta daban. Sbd gujewa haɗuwa da
jami'an da kuma ƴan jaridu, kasancewar duk sunyi connecting wayoyinsu dana juna
yasa Umar-khan gyara bluetooth na kunansa ya ce "Saif-Wazir" Saif ya amsa da "Ina
kan layi" haka Ishaq-hakim da kuma Drivern Sheikh. Cikin jin daɗi Umar-khan ya ce
"Saif-Wazir idan mun isa Shatalelen gidan gwamna kabi hanyar Amado bello way" Saif-
Wazir ya ce "Noted bro" Umar-khan ya ce "Ishaq-hakim kabi hanyar Asibitin nasarawa,
Drivern Sheikh Kabi hanyar ƙofar nasarawa,ni kuma zanbi hanyar kasuwar tarauni,
gaba ɗaya hanyoyin zasu haɗamu a titin Dawaki roud zamu sauka gidan Hakimi.." haka
duk suka amince suna zuwa Shatalelen gidan gwamna ko wacce mota ta ɗauki hanyarta
suka ɗauke tunanin jami'an tsaron daka hanyar da zasu bi, Sheikh na bayan mota ya
zubawa ikon Allah idanu a haka suka ƙarasa Dawaki roud motocin suka haɗu waje guda
kai tsaye suka ƙarasa gidan Hakimi. Sheikh na fito da ƙafarsa waje aka riƙe hannuna
tare da saka masa sarƙa kamar daga sama yaji ance "You are under arrest.....

08119237616.
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*

10....
Kasa magana Mother tayi sai Ishaq-hakim da tabi da kallo tana son gasgata abin da
yake faɗa. "Ta ya ya Sheikh zai amsa laifi fyaɗe? Laifin da duk duniya ta san ba
zai iya aikatawa ba?" Ta faɗa a fili tana sakin wani raunataccen kuka mai tsayawa a
zuciya ba zata iya kallon Sheikh cikin sarƙa a ɗaure ba, kamar wani ɗan fashi ko
Kidnapper. Umar-khan ne ya kama Mother wacce take ƙoƙarin zubewa a wajan sbd kukan
da take idanunsu ya yi jajur ya ce "Ki daina kuka Mother, wata kila Sheikh ya amsa
laifin ne sbd rashin mafita, mu duka abin ya zo mana cikin wani sabon yanayi wanda
bamu taɓa riskar kanmu ciki ba, Ubangiji ka ɗai ya san gaskiya kuma shi muke roƙa
ya fidda Sheikh Aliyu daga cikin wannan jarrabawar" gaba ɗaya zuciyar Mother ta
karaya tunaninta ya tsaya cak duk inda take neman wata hujja ta kare ɗan nata babu.
Da hannu bibbiyu ta riƙe Umar-khan ta ce "Kai ne kake tare da Babana Umar-khan, ka
taimaka mini nasan kasan Aliyu ba zai iya aikata hakan ba, yana tsare imaninsa yana
amsar rayuwa a duk yadda ta zo masa" Umar-khan ya mayar da hawayen dake cika
idanunsa kafin ya zaunar da Mother ya ce "Be patient Mother, muyi addu'a kawai amma
da ace zan iya bada shaida, da iya abin da zan faɗa ya isa ya wanke Sheikh daga
cikin zargi"

"That's enough, this is not a place to make noise" Wani daga cikin jami'an tsaron
ya faɗa yana daka musu tsawa.
Sai a lokacin Abba Hakimi ya yi ajjiyar zuciya domin shi ma Al'amarin ya girgiza
shi fiye da tunanin kowa, zuciyarsa shi zafi take masa sosai. A nutse ya juya ya
kalli Ishaq-hakim ya ce "Ka mayar da Barrister Maryam gida yanzu, ka ce ina buƙatar
ganin Aliyu immediately" da girmamawa Ishaq-hakim ya amsawa mahaifin nasa,
idanunshi akan Mother yana jiran ta miƙe.
Cikin kuka ta kalli Abba Hakimi ta ce "Ina son nayi magana da Aliyu Please Hakimi"
Kafin Abba Hakimi ya bata amsa wani daga cikin Jami'an tsaron ya ce.
"No way Madam" tana share hawaye ta ce "Don girman ka bani 2 minutes nayi magana da
ɗa na, ina son tambayarsa, tare da kwantar da hankalin shi" cutting nata out ya yi
da faɗin. "Isn't necessary Maaah..." A ƙagauce Abba Hakimi ya ce "take her out
Ishaq-hakim" Mother na kuka sosai tana kiran sunan Sheikh Aliyu aka fitar da ita
waje, Aliyu shi ne rauninta ka kaf cikin yaranta tafi ƙaunarsa duk abin da Mother
ta mallaka daga cikin dukiyar iyayenta Aliyu ta bawa, She owned all her property
for him, Lands, houses, companies, all signed in the name of Aliyu's property.
Su Mother na fita Abba Hakimi ya kalli jami'an tsaron cikin murya mai taushi ya ce
"Kun samu hujja mai ƙarfi da kuka kama mini ɗa na?" Ɗaya ya sunkuyar da kai cikin
girmamawa ya ce "Har yanzu bamu da hujja, amma a duk bin ciken da mukai Sheikh ƙara
shiga ciki yake, yaƙi buɗe baki ya yi magana, gwamnatin Madina da universityn ƙasar
sun matsa akan kwana biyu suka bayar idan ƙasa Nigeria bata ɗauki mataki ba, zasu
ɗauka da kansu domin su irin wannan cases ɗin kai tsaye suke bincike kuma hukuncin
kisa ne" runtse idanu Abba Hakimi hukuncin kisan ya daki zuciyarsa ainun. Umar-khan
da bakinsa ke rawa tun ɗazo sbd masifa ya ce "Ita kanta gwamnatin Madinan idan bata
da hujja dole ta haƙura, ina masu kawo ƙarar? Daga ina wannan zan can ya fito? Ina
ƴan matan da akaiwa fyaɗen suke?"
"Stop raising your voice, we are working on our system, nan ba Court bace" Umar-
khan zai sake magana Abba Hakimi ya yi gyara murya kafin ya ce "Ka bari abu komai a
nutse, shi ya sa na mai da Barrister Maryam gida" Saif-Wazir dai na tsaye duk
yadda suka so a basu Sheikh su yi magana hanawa akai. Kuma a gobe za a kaisa court
domin fara gabatar da Shari'a tun da case ɗin ya zo da hargitsi. Haka suka komai
gida zuciyoyin kowa babu daɗi.
Sheikh na zaune daga shi sai single da wani farin trousers mai laushi tunda yake a
duniya babu wanda ya taɓa ganin tsari da zubin halittarsa sai yanzu, an tuzarta shi
tuzarcim daya har zuƙa kuturwar zuciyarsa, shi kaɗai sai tsuma yake shi da ko sauro
baya so baya ƙaunar yaga baiwar halittar da tsaraicin jikinsa, yana tsarkake
jikinsa domin sirrinsa ne, amma yau da wanda ya dace da wanda bai dace ko wanne tom
and jerry gani yake abin ya yi masa zafi ainun. Dalilin daya sanya ya amsa laifin
kenan ba tare daya shirya hakan ba.

Mother na komawa gida ta samu Fattoumah na zaune ita ɗaya a Parlour da sauri
Fattoumah ta ce "Mother ina Yaa Lee? Ba zai dawo ba?" Murmushi mother ta yi tana
ɓoye damuwar ranta ta ce "Ya dawo mana Manana, yan gidan Abba Hakimi where's your
sisters?" Da hannu ta nuna mata part ɗinsu, Mother ya kama hannunta suka shiga
ciki. Yaran duk suna zaune sanye da hijabi sunyi shiru bayan sunci kuka sun ƙoshi,
cikin faɗa ta ce "Maimoon, Zeefa what's this? Kuna da hankali zaku shigo ɗaki
kuyita kuka kamar anyi mutuwa, Depression kuke son ya kamaku ko mene?" Gaba ɗaya
suka miƙe tsaye jikinsu na rawa za su yi magana ta ɗaga musu hannu ta ce "Ku fita a
nan wajan, maza aje a kunna kallo ayi" fita gaba ɗaya sukai jiki babu ƙwari mother
ta bisu da kallo tausayin su na kamata tasan duk sanadin Aliyu Haydar suka shiga
wannan damuwar. Kuma ita idan har ƴar halak ce ba zata sake zuwa wajan Father ba
akan maganar Sheikh Aliyu ɗin ba.
Tana fitowa daga cikin bedroom ɗin upstairs ta haura zuwa nata bedroom ɗin wayarta
ta ɗauka ta shiga kiran Barrister Zainab akan gobe zasu shiga Court sun daɗe suna
waya kafin ta kira Yaya Halima anan ta kwantar mata da hankali ta ce ita ma ta nan
zuwa dan sunyi nisa ne. Har Mother ta miƙe da sauri kuma ta koma ta zauna domin
gaba ɗaya ta manta da batun Jadda cikin sauri ta danna numberta wayar ta jima tana
ringing kafin a ɗaga a fusace akace "Allah dai yai gutsi gutsi da duk wanda yake
addabata wannan masifar har ina, ba lallai mutum yaga Annabi ba" A hankali Mother
ta ce "Jadda ni ce Maryam" Jadda ta ce "Wata abace Maryam kuma? daga wacce duniya
mena haɗa dake?" Shiru Mother can kuma ta ce "Mahaifiyar Sheikh Aliyu" Jadda ta
zabga salati da duk ƙarfinta ta ce "Yanzu Maryam cewa nayi ban gane ki ba? Masifar
gaisuwa ce bana so, Ina shi Aliyu yana can Madina ɗin ne?" Mother ta ce "Baki san
meke faruwa da shi ba?" Jadda dake kishin giɗe tayi saurin Miƙewa zaune tana faɗin
"Allah ya isa, dake Maryam da shi Aliyu Allah dai ya isa wani abu ne ya samu Sheikh
bani da labari?" Kafin Mother tai mgn father ya ƙwace wayar tare da kashewa baki
ɗaya ya kalli Mother ya ce. "Yanzu Barrister akan wannan maganar zaki haɗani da
Mahaifiyata? Su kike ta tsine mini tunda kin san bakinta ba shi da tsarki wajan
sakin magana da kwasa ta" banza tai masa ba tare da ta ce komai ba, yana ƙoƙarin
sake magana ta miƙe tsaye tana faɗin "Idan ka gama ka ajjiye mini wayata, I have
something to do with my phone" tana faɗa ta shige toilet domin zuciyarta a kusa
dake da shi. da idanu ya bita kana ya ajjiye wayar yana mmkin halin mata a wasu
lokutan.

Gari na waye Barrister Zainab ta zo suka fita zuwa State C.i.d ita da Mother abin
mamaki gaba ɗaya ƴan jaridu sun cika gidan Redio, da t.v kowa yana jiran a fito da
Sheikh Aliyu Haydar Aliyu. Cikin nutsuwa Barrister Zainab dake driving ta kalli
mutanan ta ce "Am still wondering ta ya ya zan can nan ya shiga kunnuwan Al'umma"
Murmushin taƙaici kawai Mother ta yi wai duk akan Innocent son ɗinta ake wannan
tururuwar kamar wanda ya kashe mutum?. "Allah ya kyauta, mutane akwai su da son
gulma musamman ƴan jarida wallahi" I.d card ɗinta wanda ke nuna ita cikakkiyar
lawyer ce mai zaman kanta ta nuna kana aka basu damar shiga, tun kafin Barrister
Zainab ta yi parking idanun Mother ya sauka akan Sheikh wanda aka fito dashi cikin
wata ƙatuwar sarƙa tare da wasu manyan ƴan fashi, wani abu ya tsaya mata wanda bata
taɓa jin irinsa ba, ko hawaye ta kasa a wannan lokacin. Da sauri ta fita haka ma
Barrister Zainab ɗin, ana ƙoƙarin saka Sheikh Aliyu cikin mota wata mota ta shigo
da gudu cikin haraba wajan hakan ya sa duk suka daka ta. Wani babban jami'in tsaro
ne tare da Abba Hakimi suka fito daga cikin motar sai wata matashiyar budurwa wacce
Fuskarta ta kumbura sosai sbd kuka. I.G ya kalli jami'an tsaron cikin tsawa ya ce
"Maza a cire sarƙar nan, a bawa Sheikh Aliyu Haydar Aliyu kayansa ya saka, He's
Innocent ya fita daga jikin zargi, Wannan matar ita ce wacce ta shirya komai, she's
the reason behind, She is the one who harmed Aliyu"
Gaba ɗaya kallon budurwar sukai wacce take kuka kamar ranta zai fita. A karo na
farko Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya ɗago idanunshi tare da sauke su akan budurwar
wani irin lallausan murmushi ya sauke wanda ya kusan ɗauke hankali jama'a tare da
basu mamaki, hatta Mother tai mamakin ganin murmushi a fuskar Aliyun. Cikin ƙaramin
lokaci aka sakawa Sheikh wata jallabiya mai kama da Alkyabba tare da wani farin
hirami nan da nan kamalarsa ta fito haibarsa ta cika Idanun kowa. I.G ya bada
umarnin a kama budurwa Sheikh ya yi gyara murya yana tafiya a nutse cike da kamala
tsayawa yai daidai inda budurwar take, for the first time a tsayin rayuwarsa daya
tsaya gaban mace kana ya juya ya kalli I.G sanin cewa ba zai iya taɓa jikin I.G ba
yasa ya kama hannun Abba Hakimi ya riƙe da kyau yana runtse idanunshi, ƙafarsa ya
ɗaga ya buga a ƙasa cikin In-ina ya ce "Aahhhh ahhha abarta, dooo.. do.. domin ba
ba ba....ba a faɗa da Aljani.

Not Edited
08119237616
🫰🏽kai tsaye ga mai buƙatar littafin.[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*

11.....
Abba Hakima ya kalli Sheikh a nutse yana mai sakin murmushi shi ma, tare da juyawa
ya kalli budurwar wacce taƙi yarda ta kalli inda Sheikh ɗin yake, tun daga sama
zuwa ƙasa Abba Hakimi ya ƙare mata kallo kafin ya ce "A'uzu bi wajhillahil karim,
Wabi kalimaatil lahillati la yujawizuhunna barran wala fajiran, wabi asma'illahil
husna kulliha, ma alimtu minha wa malam a'alam min sharri ma yanzilu minas sama'i,
wa zara'a fil'ardhi, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min fitnatillaili wan
nahari, wa min ɗawariƙil laili wan nahari, illa ɗariƙan yadruƙu bikhairin ya
Rahamanu. Wa min sharri kulli dàabbatin Rabbi akhizun bi nasiyatuha inna Rabbi ala
siraɗin mustaƙim" jikin budurwar ne ya fara rawa sosai, tsoran Abba Hakimi da
Sheikh Aliyu Haydar Aliyu suka cika mata zuciya, bata son su cutar da ita tunda ita
bata zo da nufin hakan ba, kuma daman Ubangiji ya ɗora mata tsoran Sheikh ɗin tun
ba yanzu ba, tana jin girma da nauyinsa tare da shakkar sa kwarjininsa yafi komai
dagula mata lissafi. Idan ka ɗauke Abba Hakimi, No one understands the words of
Sheikh Aliyu.

"No!!!"
Sheikh Aliyu Haydar ya furta a nutse yana riƙe hannun Abba Hakimi wanda bakinsa ya
kasa yin shiru da addu'ar da yake, dalilin hakan yasa budurwar ta nemi birkicewa
wanda kuma daga Abba Hakimi sai Sheikh ɗin ne kawai suke ganin hakan. Shiru ya yi
da addu'ar yana kallonta kafin ya juya ya kalli Sheikh fuskarsa ɗauke da annuri
irin na cikakkun dadtawan nan ya ce. "Yaushe Aliyu ya samu abokai haka bani da
labari" a wannan karan Sheikh bai murmushi ba sai rirriƙe hannun Abba Hakimi da ya
yi yana lumshe idanunsa tare da buɗewa alamar "Bai san yadda akai hakan ya faru ba"
riƙe hannu Sheikh ɗin kai tsaye Abba Hakimi ya yi domin kai tsaye ya fahimci
karatun idanun na Sheikh.
I.G dake tsaye shi da Barrister Maryam yana bata haƙuri ya ce.
"I'm sorry, action was taken without investigation, we were wrong" kasa riƙe kanta
mother ta yi cikin losing control ta ce. "You have defamed Sheikh's name, all those
who respect him have now stopped, Sbd Kuskuren ku my son is innocent na riga dana
faɗa muku, but you refused to understand me" Bar Zainab ta numfasa cikin rashin jin
daɗi ta ce "Everything that has happened has already happened, kawai a kira ƴan
Jaridu a shaida masa Sheikh bashi da laifi, sharri ake masa bai san komai ba a
wanke sunan shi daga ɓacin da ya yi" cikin martabawa da nuna rashin daɗin abin da
duk ya faru I.G ya ce.
"Aikinmu ne hakan, za muyi abin da ya dace muma ba zamu so sunan Sheikh ya lalace
ba yana da girma da daraja a idanun

7 / 66