Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   48 / 66

141K to 144K   out of 196.1K words

ta shiga bata ruwan, Maimoon na murza hannunta
zuwa tafin ƙafarta.
Duguwar ajjiyar zuciya ta ja a wahale idanunta na buɗewa da ƙyar, wani irin zafi da
raɗaɗi take ji a ƙasan zuciyarta wani abu na yi mata yawo.
"Sannu Daughter, ƙwarewa ki kai hala?" Maganar Ummul ta ƙara dawo da ita daidai, ta
ɗauka it was a dream ganin Alhaji Farouk zaune ya sa ta runtse idanunta muryarta na
rawa ta ce. "Zuciyata zafi take Ummul gida zani" ta faɗi hakan ta biyu, tunaninta
ko Yaa Sheikh zai tashi hankalinsa har yazo gareta ta sauke masa masifar dake
damunta, sai taga ko inda yake bata kallo balle yasan meke damunta, hakan ya ƙara
tunzurta wani baƙin ciki ya ƙara ninkuwa sosai fiye da sosai ta fashe da kukan
sanin abin da yake damunta. "Mene na kukan kuma?" Ta shagwaɓe fuska tare da basarwa
ta ce "Ummul kai na ke ciwo sosai, na ji ba zan iya cin wainar ba"
Ummul tai murmushi kawai ita ma ta nuna kamar ba komai ɗin ta ce
"Daughter baki dai na kukan ciwo ba, jeki kwanta to" ta kasa cewa komai sai naɗe
ƙafa da tayi kawai Ummul ta koma ta zauna, Maimoon kuka ta ɗauke wainar ta fara ci.
"Alhaji Farouk ban fahimci zan can ka ba?"
Ya numfasa ya ce
"Ina nufin ki yarjewa Yaa Sheikh ya auri ƴata Zahrah a karo na farko, ciwon zuciya
ne ya kamata,kuma tana matakin ƙarshe don Allah kada soyayyar ɗanki tayi silar
mutuwar tilon ƴata da nake da ita a duniya"
A wannan karan Halisa zama tayi kamar zararriyya duk sukai banza da ita, idan ta
kalli Yaa Sheikh sai taga idanunsa rufe, tana ɗauke idanu yake buɗe na shi ya
kafeta da jirkitattun idanunsa masu ɗauke da wutar sonta kamar rai da Ajali.
Ummul ta ce "Da zan yi taking revenge akan Zahrah da tuni nayi, kawai bata gabana
bata kai na tsaya ɗaukan hukunci kan ta ba, nasha ganin cases kala-kala, bayan
kasancewa police ina aiki da hukumar NASA tare da CVI, ina son ka ɗauki wannan
matsayin ƙaddara, wanda kuma ance cikar imanin mutum shi ne yarda da ƙaddara, idan
ni zan saka Arɗo ya auri Zahrah to har abada ba zan sahale masa ba, domin babu
kyautatuwar hakan, dubi abin da ya faru tsakaninta da wanda ya raini Aliyu, amma
idan har shi Aliyu ya amince zai aureta to gaka ga shi nan, ba zan hana shi aure
ba, domin Ubangiji ya umarci maza da auren mace sama da ɗaya har zuwa huɗu, idan
kuma ba zai iya adalci ba, ya auri ɗaya domin ita ce mafi a'ala a gare shi"
Umar-khan da Maimoon hadda ita Halisa suka kalli Yaa Sheikh suna jiran jin abin da
zai ce
Alhaji Farouk ya ce
"Ka taimaki addinin Musulunci, ka auri Zahrah ka ɗauka jahadi kayi,ina iya yin
komai domin ganin ka amince" ya shiga ƙoƙarin durƙosawa gaban Yaa Sheikh, Yaa
Sheikh ya yi saurin kama hannayen Alhaji Farouk ya ce.
"‫ِإ ْن ِخ ْف ُت ْم َأ َّلا ُت ْق ِس ُطو ْا ِفى ٱ ْل َي َٰت َم ٰى‬
‫َأ‬
‫َفَٰوِحَدًة ْو َما َمَلَكْت‬ ‫َعۖ َفِإ ْن ِخْفُتْم َأاَّل َتْعِدُلو َٰو‬
‫ْا‬ ۖ ‫ٰىَٰل َوُر‬
‫َثَٰب‬ ‫َفنِكُحوْا َما َطاَب َلُكم ِّمَن لِّنَسٓاِء َمْثَن‬
‫َٰبَوُث‬ ‫ٱَٰل‬
‫ٱٰىَف‬
‫َأ‬
‫َٰذَٰذِلَك ْدَنٰٓى ٰٓى اَّل َتُعوُلوْا‬ ‫َأ‬ ‫"َأْيَٰم‬
ۚ‫ُنُكْم‬
‫َأۚ َٰم‬
‫ْي‬
Yaa Sheikh ya dubi Alhaji Farouk da kyau ya ce "Dalilin da suke sakawa mutum ya
ƙara aure na da yawa, akwai rashin samun mace ta gari, akwai rashin kwanciyar
hankalin iyali, akwai rashin gamsuwa da iyali, sai ka ƙara aure idan kaga da
cutuwa" ya yi jim kafin ya miƙe tsaye ya ce
"Wani matar shi ke buƙatar hakan, akan sake da damar ta, taji yana iƙirarin IDAN BA
KE amma ai ba ita ɗaya ba ce a duniyar ko? Wani ƙazamar mace ya haɗu da ita, wani
kuma ya bi kyau wajan auren daga baya fahimci kyan yana gushewa ba kuma shi ne
fa'ida ba, shi ya sa Manzon Sallallahu alaihi Wasallama ya ce "Mafi cancantar aure
shi ne, wacce zaku aura dan nagarta,ko nasaba mafi alheri ita ce mai addini, a
wannan gaɓar na amince da auren Zahrah matsayin nagartar da ka ke da ita, ina fatan
zata zama macen rufin asiri"
Maganar ba iya Halisa ba, har Ummul sai ta daka, tasan da biyun yake maganar amma
batun amincewa auren fa? Halisa daɓas! Ta yi Idanunta ƙurr a gefe guda ta ka ɗaita
a zuciyarta tana auna zantukan Yaa Sheikh.
Alhaji Farouk hawayen farin ciki ya sakko masa ya riƙe hannun Yaa Sheikh ya ce "Na
gode, Na gode Allah ya saka da alheri Malam, Allah ya jiƙan magabata" suka jere har
waje, suna fita Yaa Sheikh ya dakata tare da fara yiwa Alhaji Farouk magana mai
muhimmanci, cike da farsaba da lafazi mai daɗi. Halisa ta rarrafa da ƙyar tare da
shigewa wani bedroom tana zuwa tasa key ta murza ta zube a gado tana rusa kukan
rashin makama da abin yi, ta rasa abin da ya sanya take kukan kawai ta ji ba zata
iya bari ya wulakanta ta ba, bayan da auren shi a kanta, inma zai auren ya tabbatar
ya bata divorce paper ɗin ta.
Wayarta ta ɗauka ta shiga kiran Dr A'isha tana ɗauka ta fashe da kuka ta ce "Na
shiga uku Adda A'isha zuciyata zata buga" Dr A'isha ta ce
"Kin san bugawar zuciya kowa? Meke faruwa ma tukun?" Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce
"Abbana aure zai yi, kuma Zahrah zai aura" Dr A'isha ta rusa wata ashar ta ce
"Kut wannan zance ne, This is something that will never happen, ƴar iskar yarinyar
zai haɗa muku shimfiɗa, da ita?" Kukan Halisa ya ƙaro sosai fiye da kima ta ce
"Allah ni ya bani takardar sakina na ji bana son zama da shi ɗin" Dr A'isha ta ce
"Oh no dear, ba haka za ai ba, dole shi zai nemeki da kansa, kada ki taɓa yarda da
cewa kin masa laifi kuma ki basa haƙuri, har abada shi zai na baki haƙuri ke macace
ke ce wacace ki ke da abin bashi, ina ƙara jan kunnenki kada ki kuskura ki bashi
damar da zai riƙe koda hannunki ne, ki jan shi a ƙasa ya zo har inda ki ke"
Halisa ta yi sak a lokacin tana jin kamar ba daidai bane wannan zan can na Dr
A'isha ta ce "Abbana zan ja a ƙasa? Babbane fa kuma Malami" Dr A'isha ta ja tsaki
ta ce
"Mtwss ji shirme ko? Shi namiji ba ruwan shi, duk girman shi, duk maluntar shi akan
wannan abin dake wajan mace sai ya zama yaro ƙarami saboda da maita, da zarar abin
da suke kwaɗayi ya tsofa sai su fara tunanin hanyar da zasu bi su ƙara aure domin
ya yin ta gida ya kau, kuma ai laifin na shi ki nuna da gaske bakya ra'ayin shi
takardar saki kawai ki ke ya baki"
Nan da nan Dr A'isha ta ƙarasa kurɓata raguwar tunanin ƙaramar kwakwalwar Halisa a
sanyaye ta ce "Thank you, I'll try my best ganin nai haka" sukai Sallama daga nan
Halisa ta kunna network ta shiga WhatsApp kai tsaye grp ɗin MU MA MATA NE ta shiga
bayan ta yi sallama ta ce "Don Allah ƴan uwana mata ga muhawara" kasancewar yamma
ce ya sa duk manyan matan suna online suka shiga faɗin.
"Muna ji"
Ta ce "Kana da miji, yana son ka, so irin na mutuwa, sai saɓani ya haɗaku akan ba
zaka je kaga dangin mahaifinka ba, bayan tun da aka haifeka baka taɓa ganinsu ba,
kuma su ne farin cikin ka, har ya furta cewa idan har ta je to ya yanke auren dake
tsakaninsu, ita kuma bata je amma ta dage sai ya saketa, ya bata haƙuri amma taƙi
gashi yanzu aure yake shirin ƙarawa, shi ɗin mabuƙaci bashi da haƙuri akan abin da
ya ke, don Allah idan ke ce ya zaki?"
Da wata number mai username ɗin: Akeela Mrs Akeem. Aka ce _Shir me kawai_
Wata babbar mace harta shige Maganar sai ta dawo ta fara typing ta ce
"Kai tsaye zan iya cewa mahaukaciya ce, kuma In sha Allah sai ya ƙara aure,mata
wani lokacin basu da tunani" Akeela ta tura emoji na dry tare da yin reply akan
maganar Sarah ta ce
Akeela😂 Sarah Mrs Abeedeen Abdul-jabbar Abas wannan ba yi ba ne gasky, idan kuma
matsalar ta Halisa ce fa?" Sarah bata bada amsa ba, sai wata mai suna Julde ce ta
ce
Julde: Ta yi kuskure gasky, ni ma haka na tafka wannan kuskuren har mijina Abu-
maleek ya fara masturbation, shi namiji ba a hukunta shi da Wannan akwai hanyoyi na
hukunta miji banda wannan, ni ma dai zan so ya ƙara auren ƴar banza taci malafar
gidansu"
Sarah: ta ce "Bari kawai Julde, ita Halisa ai ba zata aikata haka ba, mijinta ba
shi ne babban malamin nan ba?"
Da sauri Halisa ta fara typing ta ce.
"Laa Wallahi ba ni ba ce, kawai a wani grp na gani shi ne na yi sharing da ku"
maganar tai girma aka fara tafka muhawara mai zafi wasu su tsinewa Halisa ba tare
da sun sani ba, wasu kuma su goya mata baya akan ƴan uwa su ne komai, miji zai iya
barinka banda ƴan uwa. Jiki ba ƙwari tai Offline tana sakin wani sabon kukan a haka
har barci ya ɗauke ta.
Bayan sallar magriba Yaa Sheikh na zaune a wani haɗaɗɗan parlourn gidansu Ummul da
ƙyar ya iya shanye kunun gyaɗar da tayi masa, he lost his appetite.
A karo na farko da Ummul ta ce "Yaa Sheikh wannan kasa dace, auren Zahrah?" Ya
kalleta idanunsa na rufewa ya rame sosai ya ce "Ya zan Ummul?ke ma kin goya mata
baya" Ummul ta ce
"Ba baya na goya mata ba, kai na haifa ba ita ba, babu yadda za ai na tilasta
Halisa ta dawo wajanka za taga kamar don kai na haifa ba ita ba, zan ƙara faɗa maka
kayi kuskure daka hana ta tafiya da kuma furucin da kayi shi ne ta riƙe a ranta har
haka" ta jina kai yana son amsar laifin shi ko ta halin ƙaƙa kafin a raunace ya ce
"Ban hanata da wani dalili ba Ummul, ina son na zama ni ne silar zuwanta gare su,
na kasa jure yadda ake mini hawan ƙawara, ita ɗin ƴar gata ce, tana da Abba, Dada,
grandparents ɗinta they are still alive, tana da yaya uwa ɗaya uba ɗaya, she have a
siblings kamar su Khalil Maimoon, ni fa? Ke ɗaya nake da ita, Zawja kawai nake gani
a idanuna bayanke.." Ummul tai ƙasa da kanta she was trying to hide her tears
Sarai ya fahimci me take don haka ya miƙe tsaye zai fita tayi saurin miƙewa ta riƙe
hannunshi ta ce "Idan auren Zahrah kana ji shi ne mafita, kuma shi ne tubalin da
zai dawo maka da wacce zuciyarka ta buɗe ido a sonta kayi haka, bana son ka auri
sbd ba zaka iya adalci ba, kuma kafi kowa sanin hukuncin hakan, ni ɗin dana rage
maka na ɗauki nauyin Uwa, Uba, ƴan uwa a gare ka Aliyu, ka lalace sbd mace ka fita
hayyacinka bana son ganinka haka, kada ka sake naji labarin ka ɗauki azumi gobe"
ganin Ummul na shirin kukan da gaske muryarta na rawa sosai ya shige Jikinta ya
rungometa ya ce "Ba zan ba Ummul, amma sai na fi azabtuwa idan har ban azumi ba" ta
rungume shi tana shafa kan shi ta ce "Akwai Allah Arɗo, lokaci ya yi da zaka koma
Rugar Bello ka amshi kujerar mahaifinka ka gana da ƴan uwanka na can" ya jinjina
mata kai ya ce.
"Ina shirye-shiryen tafiya aikin hajji, zan fara zuwa Yola ta can sai na shi ge,
bana son a sanar da Zawja zan yi tafiya ko barta karatu ne na sahale mata tayi zan
yi haji daga gare ta" Ummul ta sake shi ta ce "Haji kuma?" Ya lumshe idanunsa ya ce
"Koyarwar Annabi ne, lokacin da matansa suka ɓata masa rai sai ya tattara kayan shi
yabar gidan tsayin kwana 40 zuwa arba'in da wani abu"
A nan bedroom ɗin Ummul ya kwanta bayan yaje wajan dattijo kan shi a cinyarta tana
shafawa tun yana magana a hankali har barci ya ɗauke shi. Ta ƙora masa idanu babu
abin da ya bari na mahaifin shi,komai ya ɗauke haƙuri da sanyin hali, da kuma
kafiya a soyayya
ta ajjiye kan shi saman pillow kana ta fita, cikin dare kamar haɗin baki wajan
ƙarfe 3 suka buɗe ƙofa dake duk gidan Ummul ɗin suka kwana ba tare da sanin junansu
ba, karon dasu ka yi ya sa Yaa Sheikh ya ɗan ja baya ita kuma ta yi baya zata faɗi
sbd tsoro ya saka hannu ya riƙeta tare da dawo da ita dab da shi, suka kalli juna
ya zame zai bar wajan tayi saurin shan gabansa kamar yanzu ne komai ke faru ko
sunan Zahrah bata ƙaunar a ambata ta ce "Kabani takarda ta" ya harɗe hannu a ƙirji
sosai yana ƙare mata kallo bai ce komai ba, bai kuma raɓi inda take ba ta fashe da
kukan rainin hankalin shi gabaɗaya tayi kan shi tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da
zagaye hannayenta a ƙugun shi ta fasa wani irin ihu tana ƙanƙame shi

48 / 66