Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   63 / 66

186K to 189K   out of 196.1K words

mari cikin faɗa ta ce "How dare you ahh? Wacce irin banza dabba ce ke kina
tafiya kai a sama kamar tinkiya mai yasa talakawa suke haka ne mtwss" wani zafin
zuciya ya tasowa Zahrah ta ɗaga hannu zata daki budurwar Ummul ta riƙe hannun tana
murmushi
"Ummul mahaifiyata da mara fa?"
Ummul ta ware idanu ta ce "Oh da gaske? Har kin manta?" Ummul ta ƙara murmushi ta
ce
"Idan maye ya manta uwar ɗa ba zata mance ba, faɗin Ubangiji ne da kansa, wanda ya
zagi uwar wani haka za a zagi tasa, kin mareni kin zageni ba akan idanun ɗana ba,
yau gashi an mari mahaifiyarki akan idanunki an kuma ci mutuncin ta, shi ya sa a
kullum kake iya bakin ka naso ɗaukan mataki sai na share domin iya son ɗana da
Ubangiji ya gwada miki shi kaɗai ya isa ya zame miki ishara, sai dai ba zaki taɓa
zama inuwa ɗaya da Aliyu ba, kamar yadda ki ke mafarki nasan ya kasa faɗa miki ko?"
A gigice Zahrah ta ce
"Don Allah Ummul kiyi haƙuri ki rufa mini asiri kada ki ɗauki fansar abinda nayi
miki ta hanyar rabani da Yaa Sheikh ki tausaya mini shi ne kaɗai inuwar da nake jin
gina naji daɗi" ta saki kuka sosai.
"Babu ruwana Fatimerh, banyi lalacewar da zan raba aure ba, zanan ƙaddarar damu
kanmu bamu san da shi ba, shi ne Ubangiji ya yi ikonsa akan haka zai kuma rabaki da
Yaa Sheikh cikin ruwan sanyi" Halisa da Umma A'isha da suka fito domin tafiya gida
an bata sallama suka tsaya suna kallon ikon Allah.
Kowa ya kasa magana,
Abin mamakin dake faruwa bai shige dukkan wanda yazo hucewa sai ya juya ya kalli
Halisa wasu suna nunata da hannu suna cewa ita ce
Ƙarar jiniya suka ji ko ta ina Mother ta ce
"Wai meke faruwa ne?" Halisa ta marairaice fuska ta ce "Mother me ya sa ake kallona
ne?"
Aka buɗe motocin kai tsaye wani ya nufi wajan Halisa Ummul tayi saurin shan gabansa
ta ce
"What's going on?"
Ya fito daga Card ya ce
"Ɗan sanda daga hukumar C.I.D Criminal Investigation Division" Ummul ta ce "Ok
then, mene ya kawo ku?" Da hannu ya nuna mata Halisa ya ce "To Arrest that young
lady behind you......

08119237616
Paid book
₦500
Complete ₦1000

*_After 3yrs🫣....._*
[2/18, 11:39 AM] Abk: _*Sarautar marubuta 80*_
"Arrest?" Suka haɗa baki wajan faɗa Halisa ta gigice ta riƙe Ummul domin ita take
gani kamar mijinta Yaa Sheikh cikin rawar murya ta ce
"Wallahi banyi komai ba, me nayi su waye ku?"
"Hakan ya ƙara saka mini shakku akan ki"Ya faɗa yana ƙara jinjina kai ba tare da
tsoro ko fargaba ba. Ummul ta ce
"Excuse me Officer, kasan matar wace da za kayi arresting nata?
Akan wanne dalili, me tayi" Ya duba lokaci ya ce
"Sorry Madam, kina wasting time ɗina, idan muka ke office ɗinmu zaki ji komai
wajan tuhumar mata laifin daya sanya mukai arresting nata" Halisa ta fashe da
matsanancin kuka
"Ummul, Abba, Mother I don't wanna go to prison"
Gabaɗaya ta gigice ta saka kuka, ga jikinta babu ƙwari abinka da ɗanyan jiki irin
na masu jego. Mother ta bawa Umma A'isha Hala ita kuma ta riƙe Halisa dake neman
fita hayyacinta daman ita bata iya firgita ba yanzu zata zauce.
"Babu inda zata ba tare da faɗin dalilin arresting nata ba" Mutumin ya kalleta ya
ce.
"Ki saurara da maganganunki, ko mutuwa tayi sai mun tafi da gawarta" a ruɗe Mother
ta ce "What! Are you at of your sense?"
Mothers na gama magana Ummul ta fito da card ɗinta wanda take shirin kai wa.
Ta nuna mishi ta ce
"I am police officer, nasan kana da matsayi mai girma ba rukuninmu ɗaya ba, amma
zan baka mmkin ƙarfin ikon daga sama" "And am ready to be her lawyer" cewar Mother!
Cikin tsawa ya ce "Arrest her!"
Ya faɗa a tsawa ce cikin zafin rai. hankalin Familyn ya ta shi, Ummul taja gefe
tana waya mai matuƙar muhimmanci yadda take wayar zaka san ranta zai ya ɓaci.
Mother ta riƙe Halisa, Dada daman kasa cewa komai tayi taja gefe Idanunta cike da
hawaye.
Cikin sauri Zahrah ta shiga tsakani ta ce
"Arrest me first before her, ko tausayi baka da shi mace ta haihu a sallamata yanzu
shi ne kake tunanin tafiya da ita Oh My Goodness"
"Officer" "Yes Sir!" Wani ya faɗa yana ƙamewa ya miƙa masa hannu ya bashi wayar
gallery ya shiga ya fito da photo tare da juya screen ɗin wayar ya nunawa Zahrah ya
ce "Yanzu sai ki fahimta" Zahrah ta zare idanu tare da dafe ƙirji cikin sauri ta
matsa daga kusa da Halisa tana amsar wayar tare da duba photon da kyau.
*Halisa* ce tsaye hannunta riƙe da wuƙa ta cakawa wani mutum. Daga nan ya nuna mata
vedion cc.t.v camera.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Halisa wa kika kashe" a ruɗe Dada ta ce
"Kisa?" Halisa wacce numfashinta ya fara gardama ta riƙe Mother da ƙarfi tana
girgiza kai idanunta na rufewa sosai cikin kaɗuwa da fitar hayyaci ta ce
"Ban kashe kowa, wallahi bani bace banyi kisa ba na shiga uku Ku kira mini Abbana
shi yasan ba zan kashe kowa ba"
"You're lie. Liar"
Zahrah Said tana sakin kuka ta kasa yarda Halisa zata iya kisan kai, amma photon ya
nunata komai da komai.
Dada ta amshi wayar cikin tsananin tashin hankali tayi baya tana salati ya akai
Halisa tayi kisa? Ya akai ta shiga cikin har ta kashe rai mene alaƙarta da wanda ta
kashe. Jikinsu ya yi sanyi suka kasa magana banda Ummul dake can tana waya. Ya
watsa hannu baya ya ce
"So allow me to arrest her" Halisa ta riƙe Mother tana girgiza amma Mother ta kasa
komai, ta koma kan Umma ta ce "Wallahi ƙarya suke bani bace ban kashe kowa ba kada
su rabani da ƴata kada su rabani da mijina"
Wani murmushi Officer ɗin ya yi ya ce.
"So that's true daman ance kina da ɗaure gindi a duk wani iskanci da kike, yanzu
zamu ga wanda ya tsaya miki zamu kawo ƙarshen barikin ki ƴar ta'adda kawai" Ya miƙa
hannu tare da kama nata zai sanya mata handcuff ya ji an fisge hannunsa tare da
murɗe shi baya, ya bada sauti. Ya saki ƙara "How dare you torch my sister's body,
wanne ɗan iska ne kai waye ya baka damar kama matar *Yaa Sheikh, Ƴar sakin
Sokoto* ?"
"Ƴar sarkin Sokoto? A information ɗin da aka bayar ance yarinyar a gidan karuwai
take da zama" Manyan motoci ne suka shigo cikin asibitin a guje har da ta wasu
polices nada ban.
Yaa Sheikh ya fito da sauri hankali ta she yana sanye da Jallabiya idanunsa ya yi
jajir da alama fitowar ba zata ce wacce ba'a shirya yinta ba. Halisa na ganinsa da
raguwar ƙarfinta ta nufe shi ta faɗa jikinsa kamar yarinya taba rufe kuka.
Ya rungumeta yana bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi.
Yadda jiniyar kan shi tayi zai baka mamaki haka tabbatar yana cikin fushi mai zafi,
zuciyar ƴan maza Aliyu na kusa, babu batun malunta.
"Abba banyi komai ba, kada su tafi dani kada su rabani da kai da Hala ban musu
komai ba"
Ya runtse idanunsa wanda ruwa ya kwanta cikinsu tsabar zuciya takaicin yadda suka
gigita masa mata yafi komai bashi haushi, ya ƙara sanyata jikinsa yana rungumeta da
kyau ya kasa magana sun jima haka kafin ya kama hannunta zuwa dalleliyar motar shi
ya sanyata a baya, zai juya ta riƙe shi ta ce "Habibi kada ka barni nan" ya watsa
jajayen idanunsa akanta ita kanta ta firgita sai taga idanun tamkar bana mutum ba
ya yi wani kala-kala yana sauyawa.
Ya riƙe hannunta alamar
"Relax" yana zame jikinsa tare da juyawa.
Kai tsaye wajan Umma A'isha ya nufa ba tare da ya ce komai ba, ita ma ta miƙa masa
*HALA SHEIKH ALIYU HAYDAR*
Ya amsheta yana jin yadda take wurga ƙafa tare da tsotsar hannu.
Motar ya koma ya sanya mata Hala a cinya ta rungumeta sosai tana ganin kamar wani
zai rabasu idanunta cike da hawaye ta ce
"Modibbo kazo mu gudu Please rabamu za suyi" ya juya mata idanu kai tsaye ta
fahimta shi ne *IDAN BA KE*
El-bashir Ahmad Nuran Sarki ya riƙe wuyan Officer ɗin ya ce
"Akan me zaka yanke hukunci ba bincike" Garbati ya ɗimauce wani ya zo da sauri ya
ce
"Officer munyi kuskure ashe kama ce kawai suke da juna ba ita bace"
Wanda aka kira da Officer kuma shi ne Garbatin cikin In-ina ya ce "Oh! to to ya yi,
kuyi haƙuri kamanni ne ba ita ba ce" Ɗaya daga cikin jami'an da suka shigo tare da
El ya ce
"Babu sunanka cikin list ɗin Officers namu daga ina aka turo ka?"
"Sunan shi Garbati Nuhu, ɗan gidan Mai gadin da aka kai Court" gabaɗaya suka kalli
Garbati kenan yayi haka ne da nufin su sake mishi Uba? Ta hanyar basaja da kayan
ƴan sanda da kuma cin amanar hukuma..
"Fake news ne kenan? What about the vedio mene shirinka?" Yaƙi magana Yaa Sheikh ya
kasa jurewa ya kuma kasa lamunta daya rufe idanunsa yadda Garbati ya damƙi Halisa
yake gani, cikin zafin nama ya ɗauke shi da kyakkyawan maruka. Ya ce.
"Za mu yi masa hukunci irin na addinin musulunci, za a kashe shi ta hanyar jifa ya
aikata fyaɗe da auren shi" El wanda zuciyarsa ke kusa ya saka hannu ya naushi
Garbati gani yake kamar ubansa yake doka. Garbati ya galabaita ya ce "Wannan shi ne
karo na biyar da mahaifina yake fyaɗe, kuma a duk wanda ya aikata a matsayin me
gadi ne, da ya yi sai ya gudu imma an kama shi zan saka kayan ƴan sanda na yiwa
iyalan yarinyar kashe di a haka har magana ta mutu, hankalina ya tashi lokacin da
naji ya yi fyaɗe ga zuri'ar babban Malamin nan da ake faɗa Yaa Sheikh Aliyu haydar
Aliyu. Bana da ikon yi musu bara zana, domin ahhali ne babba, mun shirya sakin
labarai a Social media akan cewa Yaa Sheikh bashi da Uba, mu kaga hakan bai ba, sai
muka duba yarinyar da kuka fi ƙauna a cikin ahhalin wato Halisa ita matar Yaa
Sheikh ɗin, mun san idan muka kamata mukai barazanar kisa gareta dole zaku saki
mahaifina, manufar shi ne ana sakin shi zan bar garin da shi"
Suka saki salati, Ummul ta dinga girgiza kai.
Mother ta ce "Sai inda ƙarfinmu ya ƙare akan Ubanka dole ya baƙunci halira" Bala
Tukur ya ce
"Shi kenan?" Garbati ya ce "Eh" "Batun dabar da kake kana fashi tare da kashe
jama'a, ka mance yarinyar daka nuna musu vedionta tare kuke aiki"
Garbati ya Girgiza da lamarin Yaa Sheikh.
Kamar mai gani har hanji, daman yana lura da yadda zubin fuskar shi ke sauyawa
lokaci zuwa lokaci.
"Amma ya naga Halisa a jiki" "kama ce kawai" inji Garbati ya ce "Nima da kamar nayi
amfani, haƙiƙa idan Halisa ta ɓata za'a iya kama Fariderh sbd tsananin kama ban
taɓa yarda ana iya samun masu kama da juna ki babu haɗin jini ba sai yanzu"
Aka tattara su Garbati zuwa Police station. Yaa Sheikh ya juya cikin nutsuwa amma
zuciyarsa zafi take ya buɗe bayan mota ya shiga cikin sauri Umar-khan ya shiga
shima. Ya dubeta ta shiru ta riƙe Hala sai kuka take gently ya saka hannu ya jawota
jikinsa ya riƙeta sosai yana shafa kanta ta sauke ajjiyar zuciya da ƙarfi. For some
minutes ya ɗagota suka haɗa idanu cikin kulawa yana tattara dukkan kulawarsa akan
ta ya ce "Are you Okey?" Ta ce "Abba ban yi komai ba"
Ya jinjina mata kai yana jin abu mai ƙarfi yana fisgar shi akanta.
Ya ce "Nutsu, ba wata sauran damuwa, am here, and I'll always be by your side ok?"
Ta ɗaga masa kai ya rungumeta ta jinsa ya saka hannu a riga yana shafawa tayi
murmushi kawai tasan me yake nufi don haka ta gyara zaman Hala ta shiga feeding
nata, har lokacin yana rungume da ita tana ɗago kai yake zaro mata idanu sai ta
fahimci a yanzu shi ɗin rabi da rabi ne. Wato *MUTUM DA ALJAN*
Sabuwar rigima ta ɓalle domin Umma A'isha cewa tayi gida za a dawo da Halisa shi
kuma ya ce sam ba a isa ba, babu mai tafiyar masa da matan shi aure nawa ne ya mutu
daga tafiya wankan jego. Halisa taso tafiya domin ta fahimci waye Yaa Sheikh tunda
ya sameta ya mayar da ita abinci, ya daina azumi sai na Alhamis da Litinin daya
zame masa jinin jiki...
A wannan lokacin hankalin El-bashir Ahmad Nuran Sarki dana duk wani makusan cin shi
ya tashi, abinda ake ɓoyewa ya fito aka rasa daga gidan wacce jaridan aka samu
labarin fyaɗen Matar El-bashir Ahmad Nuran Sarki wato Fattoumah Aliyu. Zan can kuma
sai fasuwa yake wasu suna haɗa jijita akan daman can hanyar ƴar iska ce, daga kan
Social media, gidan rediyo, gidan t.v
Babu wata hujja data nuna daga wajansu maganar ta fita, da abun ya yi tsamari
maganar abinda Father ya aikata da Zahrah ta fito harda batun Muhammad.
Duk Wannan maganar da abinda yake faruwa Yaa Sheikh yaja baki ya yi shiru, shirun
na shi na nufin abubuwa da dama. Hankalin Mai martaba Ahmad Nuran Sarki ya tashi
domin ana shirin lalata masa masarauta ne jama'ar garin Sokoto sun fara surutu
akai. Sati na zagayowa aka sha shagalin sunan Halisa Yarinya ta ci sunan *Ummul-
khairy Sheikh Aliyu haydar* ana kiranta da *Hala* bayan sallar zhur aka ɗaura auren
*Umar-khan Abba Hakimi, da Hafsat Sheikh Aliyu Haydar* sai kuma *Prince Khalil
Ahmad Nuran Sarki da Maimunatu Aliyu* Tare dana *Saifuddeen Abba Hakimi* Sosai aka
sha shagali farin ciki wajan angwayen ba a magana, kada ma Khalil Yaji labari he
can't believe wai yau ya auri Maimoon. El burinsa daman a sallami Fattoumah domin
ƙasar zai bari da ita, duk da kwaɗayin Mai martaba na son yin murabus ya dan ƙawa
El kujerar mulkin amma ya rufe idanu yaƙi sam, daga ƙarshe ma ya ce baya so shi
yafi ƙaunar siyasa. Shiru babban makami ne shirun da Yaa Sheikh ya yi da wanda ya
sanya El ya yi ya tayar da hankalin Fulani Atine domin ita ce wacce ta fitar da
bayanan komai zuwa gidan jaridar da ba a son da zaman su ba, suka fara haɗa shi a
twitter ya shiga jerin news ɗin da yake trending. Sai gashi ta fito tana surutai
akan ko basu ga abin bane sun ɗauka wasa ne sai abu ya tabbata ta zare ta zama
zautacciyya ta dinga tunawa kanta asiri abu yaci tura Mai martaba ya ce a dangana
da ita zuwa gidan mahaukata.
_*After 3 week's*_
Saukar su kenan daga airport Ummul da kanta ta zo ɗaukan su ta amshi Hala ta ce
"Ma sha Allah, takwara tafi iyayenta kyau"
Halisa ta ce "Kai Ummul kada dai ki ce yanzu ita kike so" Ummul tayi murmushi ta ce
"Babu laifi idan nayi haka, a daina kwasar mata sanyi fa kusan weather ya sauya,
ayi sanyi ai zafi daga haka damuna zata sauka"
Yaa Sheikh yana tsaye a tsayin satin ukun zaka ɗauka shekara ɗaya ne, domin fatar
shi ya sauya ya ƙara haske saje da gemu sun ƙara ƙawata fuskar ya daina aikin komai
sai na wa'azi wanda ake sakawa a gidan redio da t.v yanzu, yana ji da gidan
maruyansa. Ta dube shi ta ce "Me kuke ci a Sokoto ne?"
"Laa ai satinmu ɗaya a can muka shige Makkah" Ummul ta riƙe baki ta ce "Ikon Allah
ba gaya dangi" Suka shiga mota ita take jansu da kanta Halisa na baya shi kuma yana
gaba rungome da Hala wacce Ubangiji ya sanya masa ƙaunarta yana jinya tana ta
tsotsar hannun shi alamar nono take buƙata. "Idan zaka zauna da Zahrah to ba kayi
mata adalci ba, naga tausayi na neman ya sanya ka shiga hakƙinta" Halisa tayi shiru
domin a zaman da sukai ta fahimci haƙurin Zahrah daman wani lokacin akwai huɗubar
ƙawaye. "Ummul..."
"Aliyu" Yadda ta kiran sunan zaka san babu sauƙi a sanyaye yana shafa kan Hala da
yake cike da suma ya ce "Kiyi haƙuri"
Gani ya yi ta ɗauki hanyar gidansa mai makon na grandparents nasa, suna shiga suka
samu Jadda riƙe da Apple tana ci ga jakar kayanta a gefe, Zahrah wacce ta rame
sosai sbd tsananin buƙatar namiji ta miƙe ta ce "Wlcm Sweetheart" tayi ƙasa da kai
ganin Ummul Jadda ta ce.
"Daɗi miji, kin bi miji kullum cikin dare ya danneki kamar ayu babu mmki yanzu ya
ƙara ɗirka miki wani cikin....

08119237616
Paid book aji tsoran Allah an ga mana magana ina sane fa! Kawai duk abinda kafi
ƙarfin shi babu batun tsayawa ɓata baki akai
[2/20, 7:46 AM] Abk: *Da wasu suka biya da wanda suke karantawa Free 🤣 aje
arewabooks ayi following acct ɗina, har girma ake taɓa Allah wadai da masu fitar da
book ba haka da masu karantawa matsayin free, to ina naga lokacin surutun hakan ma🤣
typing da ƙyar sbd busy, ku shiga link ɗin kai tsaye👇🏾ku danna following*
https://www.arewabooks.com/notifications

"To ai gwara nayi cikin dana zauna zaman gulma" Jadda tayi mitsi mitsi da idanu ta
ce "Azaba, daga maganar alheri sai gasa magana to ai babu laifi don kin samu ciki
da ki zauna hoto kamar wannan fa?" Ta nuna Zahrah kafin ta girgiza kai cikin
takaici ta ce
"Ga waccar ƴan banzar mai mugun hali ita fa ta dinga zuƙa matarka can watannin baya
akan ta tsaneka" Halisa ta nemi waje ta zauna, Yaa Sheikh ya haura upstairs cikin
nutsuwa tun a hanya ya fara zame Alkyabbar jikinsa sbd tsananin gajiya kuma tayi
masa nauyi a jiki.
Zahrah ta bishi da kallo tana son shi a ko wacce daƙiƙa yana ƙaruwa a zuciyarta,
balle yanzu daya ƙara sauya ya riƙe kan shi haibarsa kullum ƙara bayyana ga cikar
kamala. Jadda ta gyara zama tana ƙara saka Apple bakinta ta ce "Ina baku labari
babu kalar wulaƙanci da tijarar da Likitan nan A'isha take kowa bata yiwa mijinta
ba, wai baya haihuwa dake shi sauna ne ya tsaya yana biyewa Iskancin mace banda
abinsa ba sai kawai ya saki ƴar kazan uba ta kama gabanta ba, mata nawa ne a duniya
ba suyi aure ba suke jiran mazan shiru"
Zahrah ko a jikinta, Ummul kuma tana riƙe da Hala wacce ta farka tana wurga hannu
da ƙafa. Halisa ta mayar da hankalinta akan zancan Jadda amma zaka ɗauka maganar
bai dameta ba, sbd yadda ta mayar da hankalinta zuwa ga plasma. Jadda ta girgiza
kai irin zance na cinta ɗin nan.
Ta ce "tijara kala-kala tayi ina baku labari, ashe burinta ta kashe auren, ta auri
mijinku malam kinji rashin amana shi yasa amana tayi ƙaranci duk yadda Matar Malam
ta yarda da ita amma zata aure mata miji, haka ta dinga zugaki dake kema rainon
fulani ce kika biye mata, Allah dai ya yi mijinta ba zai wulaƙanta ba, kuma babu
rabon ku zama ku uku ashe ita ce bata haihuwa, yanzu dai tana can ta fita hayyacina
mijin kuma kamar maye yana nan riƙe da ita kamar takalmi a hammata"
Cikin alhini ta ƙara girgiza kai ta ce
"To ni dai bance komai ba, yanzu ma ba wani abu nace ba, amma dai ta kusa cin
amana"
Babu wanda ya kulata, Halisa kishi ya motsa Idanunta ya ya yi jajir domin gani take
har yanzu Dr A'isha tana bibiyar Yaa Sheikh shi kuma ya san

63 / 66