Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 66

102K to 105K   out of 196.1K words

zame fuskarsa zuwa bayanta ya shiga
goga mata hanci ya ce.
"Wace Dada?"
Ta kalle shi da sauri tana juyawa bakiɗaya suka fuskanci juna ta ce.
"Babata ce, ita ta haife ni kuma ta haifi Shatu da Hamma Yabi" ya jinjina kai ya ce
"Allah ya jiƙan shi" ta ce.
"Kasan shi ne?" Ya tura baki ɗaya fuskarsa ƙirjinta yana sauke numfashi a hankali
ya shiga unhooking na bra ɗin jikinta yana gamawa ya yi cilli da ita ta ƙanƙame shi
ya sauka numfashi tare da jan duvet ya rufe su bakiɗaya. "Please Abba kada ka ƙara
baffi" ya shafa kanta yana kwantar da ita saman jikinsa ya ce..
"Barci za mu yi, ba zan ba" ta jinjina masa kai.
Sai wajan sallar Asr Yaa Sheikh ya farka yana rungome abu ya ji pillow ashe ta
gudu. Ya girgiza kai kawai, yana shigewa bathroom.
Ƙamshin turaren Roja ya cika platforn wanda ya tabbatar musu da Yaa Sheikh ɗin ya
fito, cikin rashin fahimta yake bin su Mai martaba da kallo ganinsu shirye ga
Halisa dake jikin Ummul tana ta kuka kamar ranta zai fita,
Sai torelly bag ɗin da kayan ta ke ciki.
Ya gyara zaman jallabiyar jikinsa Mai martaba ya ce
"Aliyu daman kai nake jira, jirgi yana ta jirana kuma ban son ta shinka, sbd
muhimmancin barcin naka" yana ɓalle diamond rolex ɗin shi ya ce. "Fatan dai
lafiya?"
Ya tambaya idanunsa akan Halisa.
Mai martaba ya ce "Al'ƙawarin Abbanka Hakimi zan cika na tafiya da ita" nan fa ɗaya
Yaa Sheikh ya yi ta kallon Mai martaba ya ce.
"Zamu zo tare ko?"
"Na riga nai al'ƙawari bana jin zan saɓa, dole naje da ita, kai ma sauƙi ne gare
ka?" Yaa Sheikh ya kalli Ummul ta jinjina masa kai.
Ko ba a faɗa ba a wannan karan Yaa Sheikh ya shiga damuwa ya yi gaba yana cewa.
"Allah ya ki ya ye" ko Halisar bai kalli inda take ba, gani yake kawai tana sane
data amince zata bisu, yafi jin zafinta fiye da Mai martaba ɗin..
Ummul ta dinga rarrashin Halisa ta ce tare zasu tafi itama za taga gidansu.
Aka bar gida daga Umar-khan sai Yaa Sheikh da ya tafi masallaci. Tun safe daya kira
number Zahrah ya ji a kashe bai sake nema ba. Jirginsu Mai martaba ya ɗaga da El-
bashir, Ummul sai Halisa wacce gabaɗaya zuciyarta na Saudiyya gangar jikinta kawai
ke cikin jirgin.
Har suka isa airport ɗin dake nan garin Kano Halisa bata bar kuka ba, Mai martaba
ya shiga motar Abba Hakimi daya zo ɗaukar shi.
Ummul da Halisa na baya El-bashir na driving motar wanda ya karɓa a airport ɗin.
Sun yi nisa ya ɗauke hanya ya shiga nausawa cikin daji sosai Ummul da Halisa dai da
idanu suke binsa tunda basu san hanya ba, ya yi parking gaban wani gida fuska ba
walwala ya ce "Ke fito" tsoro ya kama Halisa ta ce "Naje ina? Ai ba gidan mother
bane nan" Ummul dai na zaune tana murmushi ba tare da ta ce komai ba. Ya saka hannu
ya fisgo Halisa da ƙarfin gaske ta fasa ihu.
"Me nayi maka? daman nasan kai babu Allah cikin ranka tunda ka nemi kashe Abbana"
El-bashir ya ce "Abban naki macuci, Azzalumi, ma yaudari wanda kassara rayuwata, ya
lalata mini farin cikina, ya mayar dani abin tausayi cikin ƴan uwana har shi ki ke
jin tausayi?" Cikin kuka ta ce "Ƙarya ka ke, Modibbo ba mugu bane, kai ne Azzalumi
wanda ka nemi kashe shi" El-bashir ya zaro bindiga ya ce "Yanzu kuma ke zan kashe
tunda ke ce rayuwar shi, ba zai iya rayuwa babu ke ba, idan na kashe ki nasan zai
mutu ya yinda ya kasa jure rashin ki" Halisa ta kalli Ummul wacce take tsaye jikin
mota ko a jikinsa sai waya ma da take dannawa tana ɗan waƙarta. "Ummul kina jin me
yake cewa zai kashe ni akan idanunki?" El-bashir ya saki dariya ya ce "Wai wannan
ki ke tunanin zata kuɓutar dake? Waye ya bada shawarar a bawa Yaa Sheikh poison?
Waye ya shaida mini ke ce raunin Yaa Sheikh? Waye ke mini aiki gidan Yaa Sheikh?
You have no idea about it, ki yi numfashi na ƙarshe" El-bashir na shirin sakarwa
Halisa bindiga ya ji an ɗora masa bindiga akan shi. Ya juya da sauri ya yi idanu
biyu da Ummul dake tsaye hannunta riƙe da bindiga ta zare a bayar jikinta kayan ƴan
sanda ya bayyana a jikinta. Ya kalleta ya ce.
"ASP Ummul-khairy ni uban gidanki ki ke ɗagawa bindiga.....
[1/4, 7:47 PM] Abk: "Mamakin yadda na ɗora maka bindiga aka, ka ke yi ko IGP?"
El-bashir ya kasa magana sai kallon ASP Ummul-khairy yake mamakin yadda ta juya
reshe zuwa mujiya yake.
"Me hakan yake nufi Asp? Ni shugabanki ki ke sakawa bindiga akai? For what reason?"
El-bashir ya faɗa yana gyara tsaiwar shi. Ummul ta ce. "Oh! You're so fool El-
bashir Ahmad Nuran Sarki, You lost completely lost" El-bashir ya ja numfashi
fargaba da mamaki sauyawar al'amarin lokaci guda,
Ya shige shi.
"Ba haka mukai dake ba, kinje gidan Yaa Sheikh domin kawo mini information na abin
da yake faruwa a can"
Ya girgiza kai launinsa na sauyawa ya ce.
"Why Asp Ummul-khairy? Ke na faɗawa Abin da Yaa Sheikh ya aikata mini, na yarda
dake ka amince maki don me za kici amanata?
akan me zaki hana ni kashe Halisa bayan dake muka haɗa plan ɗin zan kasheta?"
Ummul ta ƙara gyara tsaiwa still tana riƙe da bindiga ta ce.
"You're right El-bashir Ahmad Nuran Sarki, kayi kuskuren saurin yarda dani, without
knowing me, kana tunanin zan zuba idanu ka kassara ni ka kassara zuciyata?"
"Mene haɗin kashe Halisa da zuciyarki?"
Cewar El-bashir.
Ummul ta kalli Halisa ta ce. "Enter into the car"
Jikin Halisa na rawa ta buɗe ƙofa ta shiga hawaye kawai take zubarwa,
Ga rashin sallama da ba suyi ba da Abbanta, ga firgicin bindigar da El-bashir ya
nuna mata,
Uwa uba sabon al'amarin daya kunnu kai,
Ganin Ummul cikin police uniform ta ƙara tayar da hankalin Halisa.
Ummul ta ɗauke shirun da cewa.
"Dan me na shiga aikin ƴan sanda baka sani ba, kuma ni na nemeka da aiki ba kai ba
kai ka nemeni da aiki ba, El-bashir kayi kuskure daka hari Asp Ummul-khairy ta san
sirrinka ta kuma san manufarka, kana tunani zan zuba maka idanu ka kashe mini
sirika? Ko kana tunanin zan saka maka idanu ka kassara zuciyar wanda ta cika da son
ka?
Bayan ni abu biyu Yaa Sheikh yake so kuma yake ƙauna, da kai da kuma Halisa Danejo
Rome, bani da lokacin yi maka bayani amma ka sani na shige tunaninka, ko da nace ka
bawa Halisa poison tazo da shi sbd nasan har abada Halisa ba zata bawa Yaa Sheikh
poison ba, ban faɗa mata komai akan haka ba, amma aljanun dake kanta tun yarinyarta
ko nace tun tana ciki ba zasu bari Yaa Sheikh ya sha poison ba,
Next target naka shi ne zuba hudar iblis cikin kayan Companyn Sarrafa shinkafa na
Yaa Sheikh,
Ka saurara ka tsaya da wasan iya nan, Aliyu ba sakarai bane baka san waye shi ba,
zakai ladama mai ciwo ta har abada idan kasan abin da ya akai ta"
Ta sauke bindigar tana mayar da ita gefen wandonta, ta ɗauki abaya ta riƙe ta ce.
"Ka sakani abin da ban niyya ba Mubasshir, i don't know how to explain idan mai
surutun nan ta tambaya, ka jamu zuwa gidansu Yaa Sheikh kada kai tunanin yin komai
domin ina da record naka"
Ta buɗe mota ta shiga Halisa na ganinta tayi saurin saka kuka ta ce.
"Meke faruwa ne Ummul,me ya sa zai kashe ni? Naji bana son shi" Ummul ta riƙe ta.
Tana faɗin "Ba komai Daughter nutsu"
"Ummul Abbana" Ummul ta riƙeta da kyau ganin gabaɗaya duk ta tsorata ta ce.
"Arɗona, ko Modibbonki jirkin shi na hanya, bari muje kuyi waya ko"
"Ummul bana son wannan mugu ne, azzalumi ne tsoro ya kamani ki kai mu gida da kai
ki" Ummul ta girgiza kai kawai.
"Ban san area naku ba, shi ne da kan shi zai kaimu" Ta jinjina kai tana yin shiru.
Ummul tai murmushi tana danna wata number a wayarta.
El-bashir sai hargitsa sumar kan shi yake,
Ta shammace shi, bai zaton haka ba, yana ta shuka a idon makwarwa,
Ya ɗauka da gaske ya samu amintacciyar investigator ashe ita aiki take da shi,
Tsakanin shi da ita wake farautar wani ne?.
No Answer!
Shi ne kawai, ya rasa yarda zai yana ji yana gani ba zai bari Ummul ta tuna masa
asiri acikin jama'a da Idanun Mai martaba ba,
Kuma ba zai taɓa barin Yaa Sheikh ba, dole ne ya yi masa rauni a zuciya kamar yadda
shi ma ya yi masa. Rai ɓace ya buɗe gaban motar ya shiga tare da yi mata key.
Babu wanda ya sake magana har sukai nisa lokacin tuni barci ya ɗauke Halisa jikin
Ummul, suna zuwa wani waje Ummul ta ce.
"Drop me here"
Ya yi kamar bai ji ba ta sake cewa "Ka sauke ni a nan" ya yi parking gefen titi
Ummul ta zare Halisa a hankali tare da kwantar da ita. Ta fita tana daidaita kanta
ta ce.
"A gaida jama'ar gidan, kada ka manta I Asp Ummul-khairy Abdullahi Abdul-majeed"
Ya figi motar da ƙarfi tare da yin gaba, murmushi kawai Ummul tayi tana kiran
number ana ɗagawa ta ce.
"Na iso"
Tana nan tsaye wata haɗaɗɗiyar mota ta tsaya a gabanta ta buɗe ta shiga motar ta
harba kan titi. Abba Hakimi ne tsaye yana duba agogo kafin ya juya ya kalli Mai
martaba ya ce.
"Kace El-bashir ya ɗakko su?" Mai martaba ya ɗaga kai with so much respect ya ce
"Shi ne, i wonder why ya jima haka"
"To Allah ya kawo su lafiya, amma sun jima ga mutuniyar sai a hankali"
Mai martaba ya ce "Allah dai ya sa ba rigima take ba" Abba Hakimi ya yi murmushin
manya ya ce.
"Idan tayi ba laifi, amma nasan Aliyu ba zai taɓa biyo sahunta ba, tunda dole mukai
masa na tafiya da ita"
Mai martaba ya ce "Anya? Ka shirya rabasu kenan?" Kafin Abba Hakimi ya yi magana
motar El-bashir ta shigo da gudu ashe ya jima yana horn kafin gatekeeper ya buɗe
masa gate ɗin gidan.
Gabaɗaya suka bi motar da kallo El-bashir ya fito ganin babu wanda ya a fito yasa
Abba Hakimi kallon El-bashir ya ce.
"Mubasshir ina sauran, Halisa da baƙuwar da aka ce?" Yana shiga cikin gidan ya ce.
"Tana mota, ɗayar kuma ta sauka" ya ƙare maganar yana shigewa cikin gidan. Kafin
Abba Hakimi ya ce komai Mother ta fito fuskarta ɗauke da farin ciki ta nufi motar,
ganin Halisa kwance na barci ta ce.
"Ikon Allah!"
Ta buɗe motar a hankali ta shiga bubbuga kumatunta ta ce.
"Daughter, Daughter"
Halisa ta buɗe idanu da sauri ta miƙe zaune tana faɗin "Ummul" Mother tai murmushi
ta ce..
"Da alamar Ummul na neman ƙwace mini ɗiya, zan so naga Ummul ɗin nan" da idanu
kawai Halisa ke bin Mother kafin ta juya cikin motar ta ce "tare muke da ita fa,
shi ne ta barni ba Abba ba ita?" Mother ta ce.
"Oh! Ita ce? El-bashir ya ce ta sauka a hanya ai muje ciki daughter"
Gabaɗaya suka nufi cikin gidan Mother sai jan Halisa take jiki ganin yadda ta sauya
bakiɗaya ta ƙara kyau haske ƙiba, skin ɗinta sai glowing take. Umma A'isha ta saki
murmushi ta ce.
"Maraba da baƙin Saudiyya, barka lale" ganin yadda suke ta nan nan da ita yasa
Halisa sakin jikinta ta ce.
"Ina yini Umma?" Umma A'isha ta ce "Lafiya lou Halisa ya Abban naki?" Tai murmushi
kawai tana kallon Mother, Mother ta ce "Kije kiyi wanka akwai kaya dana ɗakko miki,
ki shirya kizo kici abinci ko?" A sanyaye ta ce.
"To Mother" ta shiga bedroom ɗin da aka nuna mata, tana shiga ta fara kallon ɗakin
komai tsaf ya haɗu sosai.
Ta lumshe fararen idanunta hawaye ya shiga sakko mata babu wanda take son sakawa a
cikin idanunta kamar Yaa Sheikh, ta lura da zafinta a cikin idanunsa ko kallonta
bai ba lokacin da zasu bar ƙasar Saudiyya. wanka tayi ta shirya cikin simple ɗin
Abaya baby peach ta zauna jikinta sosai ta ƙara haska fatar ta, ta shimfiɗa ladduma
tai sallar magriba wacce aka kira yanzu..
Bayan ta idar tai shiru a hankali kuma ta sauke numfashi tana riƙe jikinta moment
ɗinsu da Abbanta Yaa Sheikh take tunawa komai nasa nada banne, salon shi da yadda
yake gabatar da komai. "Kayi haƙuri ka yafe mini Abba"
"Me ki kace?" Cewar Mother tana shigowa cikin bedroom ɗin. Tai murmushi kawai ba
tare da ta ce komai ba, Mother ta nemi waje ta zauna tana lura da sabuwar nutsuwar
Halisa ta yaba da ƙoƙarin Yaa Sheikh wajan bata tarbiyya da karatu mai kyau ya riƙe
amanar da aka bashi da hannu biyu, duk ƙoƙarin Mother na hango wani abu tattare da
Halisa bata fahimta ba, ta sauke numfashi ta ce. "Ya Abban naki? Baya miki komai
dai? Ba wani daya faru?" Kamar ba zatai magana ba sai ta ce. "Lafiya lou Mother,
Ina Maimoon?" Da ace Ummul da Yaa Sheikh na wajan mamakin shirun baki Halisa sai
ya kashe su. "Masha Allah, Allah ya yi miki Albarka muje ko?" Mother ta miƙe itama
ta miƙe tare da bin bayanta. Akan dining room suka samu, Abba Hakimi, Umma A'isha,
Mai martaba, Ishaq-Hakim. Mother taja kujera Halisa ba taja idanunta akan Abba
Hakimi dake vedio call ta zame a hankali ƙirjinta na ɗagawa.
"Sun iso lafiya, saura kai ko?" Cewar Abba Hakimi yana riƙe wayar shi da kyau, ta
cikin wayar suka ji an yi ajjiyar zuciya ba tare da ya ce komai ba.
"Matar ga Abbanki ku gaisa ya miki ya hanya?" Ya juya mata screen ɗin wayar.
Idanunta ya sauka cikin na Yaa Sheikh wanda ya kafeta da idanu shima fuska babu
alamun rahama, sosai yake jin zafinta a ran shi don me zata bi Mai martaba? Akan me
da wanne dalili kuma?
Bakinta na rawa sosai ta ce "Ab... Abbana" ɗib! Ya kashe wayar haske ya mamaye
gurbin kamilalliyyar fuskar Yaa Sheikh dake maƙale jikin screen ɗin wayar.
Hawaye ya sakko mata sosai ta kasa furta komai. Ganin abin da ya faru gaban su Abba
Hakimi ya ƙara tabbatar musu babu Soyayyar Halisa ko kaɗan cikin zuciyar Yaa
Sheikh.
Ya ɗauka zai biyo bayansu a gobe amma amsar daya bawa Abba Hakimi ta bashi mamaki
sosai. Da ƙyar taci abincin zuciyarta babu daɗi ta miƙe tana musu sai da safe.
Har akai sallar Issha Halisa bata fito ba, Mother tayi duk yadda zatai ta bugi
cikin Halisa amma bata samu abin da take son ji ba.
Mother tai mata sai da safe kafin ta fita zuwa nata bedroom ɗin.
Abba Hakimi ya kalli Mai martaba ya ce "Anya ba aljanna ce ta auri Aliyu ba?" Cike
da tarin girmansa shekarun Abba Hakimi Mai martaba ya ce "Meka gani? Don me ya sa
ka ce haka?"
"Na lura da gaske Aliyu babu jimmilar aure a tattare da shi, ina jin tsoro idan
lafiya yake baka lura bai damu da tahowa da Halisa da akai ba?" Murmushi kawai Mai
martaba ya yi, domin abubuwan da Idanun shi suka gane masa a gidan Aliyu yana da
yawan gaske. "A bashi lokaci mana?" Abba Hakimi ya ce "Nayi masa al'ƙawarin zan yi
masa abin da yake so, idan har ya riƙe deal ɗin mu, na fahimci Aliyu ya san girma
da darajar riƙe al'ƙawari, ya yi amfani da yarjejeniyar da mukai, bana son raba
auren Aliyu da yarinyar nan, na rasa mafita"
Mai martaba ya ce "A karo na biyu a kiran Aliyu akan idanun kowa a maimaita
tambayar da akai masa akan Halisa, idan ya furta abin da ya ce abaya, sai muyi masa
abin da yake so, idan kuma ya ce yana son ta sai ka hukunta shi" Abba Hakimi ya ce
"Bana jin zai furta kalmar so akan wata ƴar mace, tunda ya yi rashin abin da yake
so a baya" suka miƙe ganin dare ya yi Mai martaba ya ce "Mu barwa Allah komai,
everything will be fine" Abba Hakimi ya ce "Inn shaa Allah"
Halisa barci ya ƙaura cewa idanunta juyi kawai take akan gado, idan ta tuna tabar
Abbanta da kishiyarta Zahrah a ƙasa ɗaya sai ƙirjinta ya yi mata nauyi zuciyarta
tai zafi da ƙyar take jan numfashi, barci ɓarawo shi ne ya ɗauketa.
Cikin dare ta juya sbd ƙamshin Roja daya cika mata hanci ya hanata sukuni, cikin
magagin barci ta juya sai taji ta a jikin abu mai laushi, slowly slowly ta shiga
buɗe idanun sosai cikin rashin sa a idanunta ya sauka akan kwantaccen sumar ƙirjin
mutum, wanda bata da maraba da sumar namiji...
[1/4, 7:47 PM] Abk: Domin ƙara tabbatar da abin da zuciyarta ke faɗa mata ya sanya
ta ɗaga hannu tare da shafa kamilalliyyar fuskar shi,
Hannunta ya sauka a kwantaccen gemun shi mai laushi.
Tsoro ya ƙara kama Halisa tayi saurin tashi zata miƙe ya riƙe ta sosai numfashinsa
na sauka a hankali yanayin fitar numfashin kaɗai zai tabbatar bashi da lafiya,
A ruɗe ta kira sunan shi cikin sanyin murya ta ce
"Abba" ya yi shiru yana sauke numfashi mai zafi
Ganin bai amsa ba kuma bai da niyya ta amsawa ya sanya ta miƙa hannu,
Zata kunna socket ɗin dake gefen gadon.
A hankali cikin murya mara hayaniya ya ce
"Ban son haske"
"To Abba" was yadda ya yi mata magana.
Sukai shiru na wani lokaci ta ce "Yaushe kazo? Ina ne Ummul taje?" Sai a lokacin ya
yunƙura daga kwancan da yake har time ɗin yana riƙe da ita, ya gyara mata zama bisa
tattausan cinyar shi.
ya fesar da numfashi cikin wani irin sabon yanayi na kasala ya manna gemunsa a
wuyanta.
Ta sauke numfashi tana riƙe kafaɗar shi. "Nazo ne ki nemi yafiyata" tayi saurin
cewa "Yafiya kuma?" Ya jinjina mata kai har lokacin fuskarsa ɗaure take.
"Kina cikin fushin Allah, dana Manzon shi haɗi da Mala'iku"Halisa ta zare idanu
domin ita bata san babban laifin data aikata
Har haka ba, wanda yaja mata fushin Ubangiji.
"Me nayi Abba, taya zan jure fushinka bare na Ubangiji?" Ya sauke numfashi a
hankali ya zura hannunsa ta ƙasan rigarta ya cusa fuskarsa tsakanin wuyanta yana
shaƙar wani sahihin ƙamshin,
Wanda yake sanya shi ya yi over acting ba tare da ya yi niyya ba, a nutse ya buɗe
baki tare da manna softness lips ɗin shi ya lashi wuyanta,
Tayi saurin zabura sbd tsigar jikinta data tashi haɗi da zubewa, a karo na biyu ta
ƙara riƙe shi muryarta na rawa ta ce.
"Wayyo Abba"
Ta faɗi hakanne sbd wani sumbata da ya yiwa fatar wuyanta tare da ɗan cizawa, a
hankali yake bin gabaɗaya wuyanta da hot kisses masu zafin gaske da tsayawa a rai,
Ita kanta tayi kewa to ya rayuwarsu zata kasance idan sukai nisa na wani lokaci?
ganin yadda Yaa Sheikh yake komai a gaggauce yasa ta san yau ba sauƙi.
Bai kuma nemi hanyar bi ta sauƙi ba, jikinsa ya ɗauki zafin zazzaɓin masassara dake
damun shi. Ya zame fuska tare da komawa jikin frame ɗin bed ɗin ya jingina yana
sauke numfashi.
"Laifin me na yi Yaa Sheikh? Mena aikata wanda Ubangiji ke fushi dani?" Da ƙyar ya
ware idanunsa ya watsa a kanta yana son gasgata cewa da gaske bata son laifinta ba?
Ko faɗa kawai take.
"Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce,

35 / 66