Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 66

81K to 84K   out of 196.1K words

da Asr. Zai shiga aljanna" Ya
sauke numfashi ganin ta natsu ya ƙara da cewa.
"Muslim ya rawaito hadisi Acikin Sahihinsa. Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su
tabbata a gare shi) yace:
‫ فإنه من يطلبه من‬،‫ فال يطلبنكم الله من ذمته بشيء‬،‫من صلى صالة الصبح فهو في ذمة الله‬
‫ ثم يكبه في‬،‫ذمته بشيء يدركه‬
‫"نار جهنم‬
Ta rausayar da kai gefe guda ta ce "Shi kuma me hadisin yake cewa Malam?" Ya
tattare sumar kanta tare da ɗaukan hiraminsa ya saka mata bayan ya gama ba tare
daya kalleta ba ya ce.
"Abinda Hadisin yake bayani a Jumlace shine: Duk wanda yayi sallan Asubahi. Ana
nufin yayi ta a lokacin ta, kuma acikin Jam’i in ya zamto yana daga cikin wa’inda
Jam’i ta hau kansu kuma bashi da wani uzuri. Toh yana ƙarƙashin kulawar Allah da
Amincin sa. Kada ku yadda ku cutar dashi har Allah ya kamaku da laifin kun cutar da
wanda ke ƙarƙashin Amincinsa da Kulawarsa. Domin duk wanda yayi haka Allah zai
kamashi kuma ya kifar dashi a wuta" zata taɓa gemun shi ya yi saurin riƙe hannunta
ta ce.
"Malam ya zan samun ladan tunda ba zan sallah ba?" Ya ɗan yi shiru cikin kyakkyawan
lafazi ya ce.
"Azkar, ki rabaci lokacin da Azkar duk wani alkairi da arziƙi da kuma rabauta da
Ubangiji ke bayarwa yana kyautar sune lokacin asuba, kiyi wanka ki ɗaura" ya saka
hannunsa a ƙugunta tare da ɗaga sama ya dire.
Wani ƙaramin littafin azkar ya bata.
Bakinsa ɗauke da tasbihi ganin lokaci ya shige a haka ya nufi Masjid Abu-Abdulla.
"Allah ya tsare mini kai Malam" ta faɗa a sanyaye sai kuma ta sauke ajjiyar zuciya
ta ce.
"Gaskiya Abbana bai da kunya, ashe haka darasin auren yake" murmushi ta saki ta
nufi bathroom ɗin "Modibbo ɗan gayo" komai na toilet ɗin fari ne tas, daga kan
towel, zuwa showel na goge kai, bathrobe, brush, jakuzzie, labulaye komai da komai
fari ne.
Kasancewar ta gama sanin kan abun yasa ta kunna wajan warm water tai wanka sosai ta
gasa jikinta. Ga mmkinta sai taga pads da pats gefe guda ta dinga tunanin ita Malam
ya samesu a haka ta shirya kanta cikin rashin sabo domin gabaɗaya a takure take jin
kanta.
Wasu ƙananun jallabiyu ta gani masu hula ta ɗauki dark brown ta saka tare da
shimfiɗa prayer mat ta zauna. Azkar ɗin safiya ta fara dake duk ya karanta mata
hakan yasa duk ta iya.
Lokaci zuwa lokaci sai ta ɗaga hannu sama ta ce.
"Allah ka bawa Dadata haƙurin rashina kusa da ita, Allah ka dawo mini da naggen
Baffana, Allah ka bawa Abbana lafiya ka bashi kuɗi masu yawa da amfani, Allah kasa
maƙiyansa su mutu, Allah kasa kasa Abbana ya mutu ya barni" a haka har gari ya yi
haske ta dinga gyangyaɗi.
6:30 ya buɗe ƙofa ya shigo bakinsa ɗauke da sallama cikin kamilalliyyar muryarsa.
Ita ya fara gani zaune barcin ya fara cinta shiyasa bata ji shigowar shi ba, ya
sunkuya zai karɓi azkar tayi saurin buɗe ido tana cewa.
"Allah ka bawa Abbana yara da yawa ya Allah" ya karɓe azkar ɗin ya ce.
"Idan matar malam ta amince" tayi saurin buɗe ido ta ce.
"Modibbo ka dawo?" Ya ɗaga mata kai tayi saurin sumbatar kumatunsa duka biyun a
hankali ta sumbaci lips ɗin sa.
"Sabahul khair Yaa Sheikh ‫"صباح الخير‬
Yana ɗaukanta tare da nufar bed da ita, ya kwantar da ita yana yi mata light kisses
na barka da asuba ya ce.
"Ana bikhayr walhamd lilah" yana juya ta diro daga bed ɗin ta ce.
"Abba kana shan tea da sassafe zan haɗa maka" Har ransa yaji nutsuwa ta saukar masa
ganin duk ta gama haddace wani abu nasa ya ɗauke ya ce.
"Inni sa'im"
"Kuma kai mini kiss Abba?" Ya na tafiya gaban wardrobe kamar ba zai magana ba sai
ya ce "Banji komai ba" tai murmushi kawai ta ce "Amma yau Laraba, kuma Alhamis da
Litinin kake?" Ya yi mata banza duk da yasan abune mai wahala tambayar ta tsaya iya
nan bai gama tunani ba ta ce.
"Daman ana azumi Laraba ne Abba?" Ya ɗaga mata kai yana sauke numfashi ya ce.
"Na ƙarin lafiya" ya sauya kayan jikinsa yana zama kan kujera hannunsa riƙe da wani
littafi da yake nazarinsa yana ganin lokacin data kwanta jikinsa bai ce mata komai
ba, tun tana masa surutu tana cewa "Abbana gasky kana da kyau" ko kuma ta ce "Ina
son ka Modibbo" a haka har barci ya ɗauketa.
Kwantar da ita ya yi saman gado ya shirya cikin kyakkyawar tufa. A gidan ya barta
bayan ya kulle ko'ina da kansa ya ƙara driving zuwa gida.
Kamar haɗin bakin Zahrah ta fara shigowa cikin gidan kafin shi. Ganinsu tsaye a
main parlour ya dubi Ummul kana ya dubi Zahrah alamar meke faruwa?.
Ummul ta ɗan saki numfashi ta ce.
"Halisa ce ba a gani ba" ya harɗe hannunsa yana kallon Ummul ƙasa-ƙasa da idanu ta
gane abin da yake cewa.
Ta ce "Har asuba na duba tana bedroom ɗinta, kawai yanzu na tashi nace ta shirya
makaranta na nemeta na rasa, Allah yasa ba mutunanta sukai wani wajan da ita ba"
"Wallahi da sun kyauta mini, bata da wani amfani" cewar Zahrah cikin suɓutar baki.
Ummul ta ce "Haba Zahrah keda ƴar uwarki? Kamata ya yi ki fimu shiga damuwa" Zahrah
ta ce "Nasha faɗa mata tana addu'a bata ji" Duk wannan ba shi ne ya damu Yaa Sheikh
yatsun daya gani kwance a fuskarta shi ne damuwar shi.
"Barka da safiya Ummul, wani abu ya faru dake ne?" Ummul ta shafa fuskarta gaban
Zahrah ya faɗi. "Kada ka damu, kaje ka huta munyi magana da Umar-khan In shaa Allah
lafiya take" badan ya yarda ba sai dan shi ba ma'abocin jayayya bane. Har ya shige
ta ce.
"Bari a kawo maka shayi" ya girgiza kai tare da cewa "Ina azumi" Ummul ta saki baki
tunda take bata taɓa ganin Yaa Sheikh ya yi azumi ranar Laraba, amma dole akwai
wani abu.
Zahrah ta shige part ɗinta cike da farin cikin rashin Halisa. Yaa Sheikh na shiga
part ɗinsa ya zame Alkyabbar jikinsa tare da nufar bathroom ya saukarwa kansa ruwa
mai sanyin gaske ya saka hannu ya hargitsa sumar kansa mai launi biyu. Idanunsa
gabaɗaya ya rikiɗe.
A hankali ya kifa kansa a jikin Sink yana sauke numfashi ya ɗauki azumin amma bai
tsira daga abin da yake ji ba, wani irin al'amari ne da zai bijiro masa rana tsaka.
Ya rasa yadda zai da yaransa duk da ya yi nisa da ƴar fillonsa ya taho gida a zaton
shi kusancin da suke samu ne. Al'amarin yaso fin ƙarfinsa, ya kwanta yana rufe
jikinsa sai kiran sunan Allah yake.
Umar-khan ya yi wa waya akan yaje can ya ɗakko Halisa, kuma zai ɗakko Mai martaba
daga airport.
Misalin 6:00 na yamma Zahrah na zaune a Main parlour watching TV taji saukar muryar
mai sanyi a kunnanta. Da sauri ta ɗaga kai sukai idanu biyu da Mai martaba Ahmad
Sarki. Sam bata lura da El-bashir dake bayan mahaifinsa ba. Sarki sarki ne amma duk
yadda Sarki Ahmad ya yi mata kwarjini bai kai kwarjinin da Yaa Sheikh yake bata ba.
Ba yabo ba fallasa ta ce.
"Baƙi mukai ne?" Umar-khan ya ce "Wannan ba baƙi bane" ta watsa masa harara ta ce
"Wanda baka sani ba ai baƙi...," Sauran maganar ta haɗiye lokacin da tayi arba da
El-bashir. Shi kam ko inda take bai kalla ba. Suka nemi waje suka zauna, Zahrah ta
shiga ruɗu idan ta kalli Halisa sai ta kalli El-bashir.
Daga El-bashir har Sarki Ahmad da Umar-khan sun gane abin da yasa Zahrah take haka.
Halisa ta kalli Umar-khan ta ce.
"Umar-khan ina Abbana?" Tunanin Zahrah ya tsaya tana son taji waye Abban nata?
"Jeki duba yana cikin part ɗinsa" ta nufi ɓangaren cikin nutsuwar data fara samunta
El-bashir da Sarki Ahmad suka bita da idanu.
Ummul ta kawo musu kayan motsa baki dangin Inibi da Apple.
Itama Ummul tai mmkin ganin El-bashir sai ta share.
Halisa ta samu ƙofar a rufe kamar yasan zata shigo. Jiki a sanyaye ta koma
ɓangarenta, Zahrah ma gabaɗaya tunaninta ya tsaya. Sarki Ahmad da El-bashir tare da
Umar-khan na tsaye sun yi alwalar sallar magriba, ba jimawa ƙamshin Roja ya cika
parlourn a hankali ya fito cikin farar jallabiya da hirami fuskarsa ɗauke da tarin
nutsuwa cak ya tsaya jin an rungomesa ta baya ya rufe ido. "Nayi kewarka Abba, shi
ne ka gudu kabarni?" Ya ɗan share yana kame fuska Sarki Ahmad ya ɗauke kai ta dawo
gabansa tana riƙesa ya riƙe kafaɗarta tare da matsar da ita gefe bai ce komai ba.
Ya shige zuwa waje ya yi nisa ta ɗaga murya ta ƙarfi ta ce "Ina son ka Modibbona"
murmushi Umar-khan ya yi. El-bashir ya yi mmkin yadda tai tamkar bata san shi ba.
Bayan sun dawo sallah har Yaa Sheikh a zauna saman dining Room Ummul ta haɗa masa
kayan buɗe baki. "Aliyu baka da lafiya ne?" Kafin Yaa Sheikh ya yi mata Halisa ta
ce "Eh mana ɗan tsuhu, amma Abba ya ce nice nan maganin kuma munyi darasin aure..."
Ummul ta rufe bakinsa Halisa, kamar gilmawar walƙiya haka Yaa Sheikh ya ɓace daga
kan dinning tare cup ɗin hannunsa.
Ummul surutun Halisa ya fara bata tsoro anya ita ke wannan duk shirman? Ace komai a
fallasa yake a wajanta.
Cikin dare Yaa Sheikh na barci yaji an shige jikinsa yasan ita ce dan haka ya ƙara
bata damar raɓar shi ko zaiji sassauci. Washegari da kansa ya kaita makaranta.
Halisa aka haɗu da ƙawarta Abir ta ƙara ɗora ta akan hanya. Ƙarfe 2:32 motar shi
tai parking yana baya Umar-khan ne driver, headmaster ya fito da sauri jikinsa na
rawa ya ce "Yaa Sheikh ya akai ne?" Yaa Sheikh ya kalli Headmaster kana ya kalli
Umar-khan, Umar-khan ya ce "An tashi daga karatu zamu tafi da ita ne" da mmki
Headmaster ya ce "Yanzu motarka ta fita fa? Wacce Halisar bayan wacce kazo ka tafi
da ita?...

Paid book
500
08119237616
[1/3, 4:48 PM] Abk: "Ga Yaa Lee muna tare da shi, yaushe yazo ya ɗauki Halisa?"
Headmaster ya goge zufar dake bin fuskarsa al'amarin ya fara bashi tsoro ya ce.
"Wallahi ina faɗa maka, yanzu ka shigo ka tafi da ita, har kana ce mini ya karatun
nata, kuma sai ka dawo kace tana ina?" Yaa Sheikh ya yi shiru.
"Wani irin murɗaɗɗen abune, ba dai Yaa Sheikh yazo ba, sai dai wani kai kuma baka
duba ba" "Ta ya ya za kai mini musu? bayan muna da cct.v Camera yanzu sai na duba
maka"
Umar-khan ya ce "Muje, amma da sake" Yaa Sheikh ya ɗaga kansa sama a hankali cikin
sauyawar murya ya ce.
"Na fahimta,muje" Umar-khan zai magana Yaa Sheikh ya ɗaga masa hannu alamar ya yi
shiru. Tunda suka ɗauki hanya Yaa Sheikh ya kasa samu damar yin cikakken tunani.
"Waye?" Ya furta a zuciyarsa ya ɗauka tuntuni ya magance wannan matsalar ashe ya
kashe maciji bai sare kansa bane. Yanzu kuma ya yi girman da idan ya ce zai raba
shi da ita babbar matsala ce. Duk da bashi da cikakken hujja akan abin da
ƙwaƙwalwarsa take faɗa,amma zuciyarsa na son gaskata hakan.
Har suka iso gida Yaa Sheikh bai san sun ƙarasu ba. Sai da Umar-khan ya ce.
"Lafiya kake dai?" Ya kame fuska tare da saukowa sai da ya yi nisa ya tsaya ya ce.
"Ka nemi abin faɗa"
Umar-khan ya ce "Kada ka damu da hakan" bai bari ya shiga ta asalin ƙofar gidan ba,
ya ratsa da bayan gidan ya shiga sashinsa.
Umar-khan na shiga ya samu El-bashir da Mai martaba Ahmad Sarki zaune suna hira
sama-sama Ummul ta cika musu gabansu da kayan cima kala-kala.
"Ina Aliyun fa?" Umar-khan ya zauna cikin matartabawa ya ce "Yana ɓangaren shi,baya
jin daɗi" Ummul ta ajjiye plate na hannuna ta ce.
"Halisa fa?" Ya ce "Tana makaranta" Ta kallesa alamar bata fahimta ba ya ce.
"Tana ɗaya daga cikin yaran da aka zama masu ƙwazo, wanda za ai quiz dasu, an riƙe
ta zuwa kwana biyu dan bata huro" Ummul ta ce "Something fishy" maganar ta tsaya
iya ranta, ta san babu hujjar da zata sanya Yaa Sheikh yabar Halisa a wani wajan
har tsayin kwana biyu, dole akwai abin da yake ba daidai ba. Ko yini ya yi bai ji
motsinta ba, ba zai tambayi ina take ba, amma daya fito Main parlour tasan neman
lafiyarta yake son ji, da rashin jin motsinta.
Tai murmushi kawai ta ce. "Ah ba shakka, Allah ya bada sa a" Umar-khan ya ce "Amin"
"Umar-khan ya batun Companyn Sarrafa shinkafa na Aliyu?" Umar ya ɗan kalli El-
bashir da yake danna waya hannunsa riƙe da Apple yana sha ya ce "Allah ya taimaki
Mai martaba, komai lafiya yake cikin yarda da amincin Ubangiji" Mai martaba ya
sauke numfashi yana jinjina kai kafin ya ce.
"Ina son Mota guda da za a rabawa jama'a na kyautar Ramadan, waye manager na
Companyn?" Kan Umar a ƙasa sbd nuna girmamawa ya ce
"Yarima Khalil Ahmad Sarki shi ne Manager na Companyn Sarrafa shinkafa na Yaa
Sheikh" El-bashir ya ɗago kai da sauri jin abin da Umar ya ce, wato Yaa Sheikh ba
ƙaramin kai wayo bane, kamar yana da sanin cewa za a iya yi masa sharri cikin kayan
da yake kawowa, shi ne ya saka Khalil matsayin Manager ya san cewa El-bashir ba zai
taɓa cutar da Khalil ba, dukkan abin da ya faru za a alaƙanta shi da Khalil tunda
da saka hannunsa komai ke tafiya.
"Ikon Allah, bani da labari zanwa Khalil ɗin magana" Mai martaba ya miƙe tsaye
domin ziraya yake son ya fara kaiwa tun kafin watan Ramadan ɗin ya fara, zuciyarsa
har yanzu ta kasa yarda da ƙaddarar data faɗa masa gani yake kamar akwai wani abu
dake shirin faruwa. El-bashir ya miƙe tsaye tare da bin bayan mahaifinsa har zuwa
harabar gidan Yaa Sheikh suka shiga mota.
Yaa Sheikh ne zaune gaban Alƙibila hannunsa riƙe da ƙaton Alkur'ani gaba ɗaya ya
rufe fuskarsa karatu yake cikin suratul Yaásin, ɗakin baki ɗaya yai duhu sai zoben
dake hannunsa ne kawai yake bada haske mai kyau.
Ya yi nisa sosai cikin karatun yaji ɗakin ya fara girgiza wata ƙaramar ƙara ta fara
cika ko'ina na ɗakin. Cikin murya mara daɗin saurare aka shiga faɗin.
"Laifinka ne, laifinka ne, laifinka ne" Yaa Sheikh ya saurara da karatun da yake
tare da sauke numfashi ajajjere kwana biyu abu na neman fin ƙarfinsa, Shikenan ba
dama ya karanta suratul Yaásin sai su bayyana kamar dai ya kirasu, sun nace sai sun
zauna tare dashi amma me yasa yanzu suke neman takura masa duk da sharuɗan daya
kafa musu?. Ya buɗe fuskarsa yana ƙara gyara zaman shi ba tare daya saurari abin da
suke cewa ba.
Abin da ke magana ya bayyana a suffar wata baƙar mage mai manyan idanu. Can nesa da
Yaa Sheikh taja ta tsaya ta ce.
"Ba zai taɓa rabuwa da matarka ba, indai baka mayar da ita cikakkiyar mace ba, ka
halakta auren dake tsakaninku, kasancewar ku tare da kuma mai da ita babbar mace
kamar ko wacce matar aure shi ne zai kawo ƙarshen shi, a ranar da kuka zama
ma'aurata a ranar komai nasa ya ƙare" Yaa Sheikh ya miƙe tsaye yana son barin
ɗakin don yasa abin da ya daɗe bai tasar masa ba yana gab da tashi, kafin ya fita
magen tai tsalle ta hau saman wuyan shi bakinta na wani irin hayaƙi ta ce.
"A shirye yake, a shirye yake, a shirye yake, kawo yanzu muma bamu san inda ya
kaita ba" a fusace kamar wanda ya samu juyewar tunani haka Yaa Sheikh ya damƙi
magen bakinsa ɗauke da addu'a ya bugata da jikin bango, a tare suka saki ihu ita da
Yaa Sheikh sai dai nasa ihun yana da banbanci da nata, shi mai ɗauke da kiran sunan
Ubangiji ne, ita kuma ji tayi kamar Yaa Sheikh ya zuba mata dalma a jiki.
Cikin gilmawar haske a cikin duhu haka magen ta ɓace ɓat, Yaa Sheikh kuma ya sulale
a tsakiyar carpet ɗin bedroom ɗinsa, tare da ɗaukan hiraminsa ya naɗa wani rawani
mai masifar kyau a kansa, a nutse ya harɗe ƙafafuwansa kamar wanda yake tsakiyar
fada zaune akan karagar mulki. Ilahirin fuskarsa zufa ce take yankowa kansa a ƙasa
ya ɗora hannunsa saman cinyoyinsa.
Zuwan Ummul huɗu sashin Yaa Sheikh tana samunsa a rufe, yanzu ma tana tsaye a zuwa
na biyar tana mmkin abin da ya hana Yaa Sheikh fitowa tasan kuma azumi yake tunda
yau Alhamis ne. Ta duba lokaci taga lokacin sallar Asr ta kusa kuma shi ne zai ja
jam'i ta shiga bubbuga ƙofar amma taƙi buɗewa.
Cike da damuwa ta juyawa daidai lokacin kuma Mai martaba Ahmad Sarki da Umar-khan
suka shigo Parlour ganin yanayin Ummul yasa Umar-khan cewa.
"Yaa Lee?" Da sauri ya ƙarasa wajan ƙofar yana tambayar Ummul "Lafiya mene ya samu
Yaa Lee?" Ta girgiza kai ta ce "Kawo yanzu ban sani ba, amma nasan dole akwai abin
da ke faruwa aciki" Umar-khan ya ciro key ɗin sashin na Yaa Sheikh jikinsa na rawa
ya fara buɗewa, ƙofar na buɗewa Ummul ta ce.
"Tsaya a nan Umar, ganinka zai sanya yaƙi kulamu" Ya tsaya yana addu'ar Allah yasa
lafiya.
A hankali Ummul ta shiga baya parlour kai tsaye ta nufi cikin bedroom ɗinsa
idanunta ya sauka akan shi zaune tsakiyar parlour, hakan kaɗai ya isa ya zama hujja
da zai sanya Ummul tasan yau fa ba iya Yaa Sheikh bane, hadda sarakunan da suke
bibiyar rayuwar shi.
"Aliyu, Aliyu!"
Ta faɗa tana bubbuga kafaɗar shi, bai kalleta ba bai kuma motsa ba a fili ta ce.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Wanne abu ne haka Aliyu kake gani a rayuwarka
daga wannan sai wannan" ta saki kuka tana juyawa. Mai martaba bai ce mata komai ba
yabi gefenta ya shige bedroom ɗin Yaa Sheikh.
A rikice Umar ya ce "Ummul lafiya? Me ya samu Aliyun naki?" Ummul hawayenta yaƙi
tsayawa cikin shassheƙar kuka ta ce.
"Umar-khan na gaji, wallahi na gaji ina tunanin lokaci ya yi da kowa zai san abin
da ke faruwa, ba zan jure ganin halin da Aliyu ke shiga ba, kasan cewa wani lokacin
ki barci bama yi idan hakan ta faru? Mene yasa duk ƙarfin ilimi da sanin da
ubangiji ya bawa Aliyu Aljanu ke bibiyar shi ne?" Umar-khan ya goge zufa ya ce.
"Kiyi addu'a Ummul, ita yake buƙata daga gareki kada ki zubar da hawaye azabace a
gare shi, kowa da zanan ƙaddarar shi, Yaa Sheikh kalar tasa kenan, mu gode Allah da
iya abin yake tsayawa, kuma da yawan malamai zai wahala ki same su, su kaɗai"
Ta goge idanunta ta ce.
"Shikenan, amma Umar ka faɗa mini gaskiyar abin da yake faruwa, ruwa baya tsami
banza" ya kalli ko'ina kafin ya ce.
"Munje makarantar su matar malam ance wani mai kama da Yaa Sheikh ya zo ya tafi da
ita, na ƙaryata Headmaster ɗin ya ce muje ya nuna mini CCTV camera amma Yaa Sheikh
ya ce a'a ya fahimci komai, Halisa missing" murmushi kawai Ummul tayi ta ce
"Na sani daman, ba haka kurum bane wallahi duk ranar da Aliyu ya rasa Halisa a
rayuwar shi ka tabbatar za a ɗauki gawar shi ne" baki buɗe Umar-khan ya ce.
"But baya son ta ai, zuwa yanzu na fahimci da gaske Yaa Sheikh baya son Halisa"
Ummul ba tai magana ba ta

28 / 66
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted