Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 66

15K to 18K   out of 196.1K words

Sheikh ya
ɗago kansa tare da sauke ganinsa akan Abban nasa Hakimi, raunin idanun Sheikh ya
bayyana sakamakon zuwan Hakimi wanda shi kaɗai ya fahimci hakan, shi kansa ya kasa
yiwa Sheikh ɗin gwaggwaran kallo, idan akwai abin da Hakimi ya keso a rayuwa bai
shige Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ba, son da yake masa ko ƴar ƴan cininsa su Ishaq-
hakim ba ya yi wa soyayya ce ta musamman tun Sheikh na zanin goyo.

Zame ido Abba hikima ya yi daga kan Sheikh yana mayar wa kan jami'an tsaron da suke
jiran suji mai zai ce, domin su basu da wani laifi akan aikinsu suke komai, ko da
basu aikata hakan ba, gwamnatin ƙasar Madina zata ɗauki mataki, matakin da zaiwa
kowa ciwo da zafi a zuciya. "Zaku iya tafiya da shi" Abba Hakimi ya furta a nutse
yana shafa sumar Sheikh tare da ɗaukan hiraminsa ya fara naɗa masa sabon rawani. Da
sauri Ishaq-hakim ya ce "Abba ta ya ya zaka bari a tafi da Yaa Lee? Kai ne wanda
nake tunanin zaka dakar dasu daha tafiya da shi?" Murmushi mai laushi Abba Hakimi
ya yi yana ɓoye damuwar ransa kafin ya ce "Mulki daban, hukuma daban Ishaq-hakim a
barsu suyi aikinsu muma muyi namu" Umar-khan juyawa ya yi tare da shiga mota ya
kifa kansa jikin Kujera ba zai iya zuba idanu a gabansa a tafi da Sheikh ba. Saif-
Wazir idanunsa ya yi jajur gaba ɗaya yanayin baya yi masa daɗi. "Aliyuna" Abba
Hakimi ya kira sunan a taushashe yana kallon Abban nasa, cikin kulawa ya ce "Kayi
haƙuri, ƙarya fure take bata ƴaƴa, lashakka gaskiya zatai halinta ka ɗauka kai ni
kana daga cikin bayin da Ubangiji zai gwada imaninsu" ƙanƙame hannun Abba Hakimi
Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya yi, hakan ya tabbatar wa da Abba Hakimi Sheikh ya
amince da zan can nasa. Sakin hannunsa ya yi gaba ɗaya jikin jami'an tsaron ya yi
sanyi bisa dole suka saka Sheikh cikin mota tare da tafiya da shi.

"Ishaq-hakim kawo mota, zuwa wajan Aliyu da Barrister Maryam" jinjina kai kawai
Ishaq-hakim ɗin ya yi, tare da buɗewa Abba Hakimi bayan mota ya shiga, Saif-Wazir
da Umar-khan suka bi bayan motar su Sheikh domin suji inda zan can zai tsaya.
Mother na tsaye ta kasa zama sai number ɗaya daga cikin samarin take gwadawa amma
basa ɗagawa, hankalinta ya ƙara tashi fiye da ko yaushe tunanin abin da ya samu
Sheikh ya wanzu a zuciyarta. Upstairs tayi da sauri kai tsaye part ɗin Father ta
nufa yana zaune a ƙawataccen parlournsa mai kyau, hannunsa riƙe da jarida cikin
baƙin ciki yake karanta inda aka saki zan can Sheikh tare da photonsa,gaba
Al'amarin ya wanzu a duniya dama media baki ɗaya. Shigowar mother ya sanya Father
Kallonta yana jiran jin abin da zata faɗa wannan karan. "Barrister Maryam lafiya ki
kai mini tsaye?" Da mmki ta dubesa sosai kafin ta ce "lafiya kake tambaya? Wai me
Aliyu ya yi maka da baka kula da al'amarinsa ne?" Hannu ya ɗaga mata ya ce "Saurara
Barrister Maryam ni na aiki Aliyu ya aikata hakan? ko da izinina ya ke lalata yaran
jama'a yana musu fyaɗe?At Aliyu's age, I will not be surprised at all that he did,
ba a shaidar ɗan yau Maryam da ace yana da mata babu mai zarginsa da aikata haka"
tarin mamaki da ya gama cika Mother ya sanya ta kasa cewa komai sai kallon Father
kawai da take "Aliyu ɗan ka na cikinka kake wa wannan shaidar, shaidar iyaye ita ce
shaidar Allah fa, banda na san kai ne mijina kai ka samar da Aliyu da babu abin da
zai sanya nace ba kai ka haife shi ba, amma kaje lokaci ne zaka fahimta idan baka
son sa muna son shi" kai kawai ya girgiza mata yana faɗin "Zaki iya zuwa ki nemi
Mahaifinsa a waje, tunda kina tantama" kafin Mother tayi magana Fattoumah ta shigo
Parlourn kallon iyayen nata tayi ganin kamar hayaniya suke, fahimtar hakan yasa
Mother yin murmushi ta ce "Mamana ya akai? Ban hanaku zuwa waje ba without
permission zan fara bulala fa" marairaice fuska tayi ta ce "Am sorry mother ina ta
sallama tun ɗazo" kallon yadda Fattoumah ta tsare Father da ido mother tai cikin
sauri ta ce "Ya akai to?" Da sauri ta ce "Abba Hakimi yana Parlour kizo ke da
Father" tana faɗin hakan ta juya da sauri tana jin Father na faɗin "Fatimah..
Zarahh..!!" Amma tai banza da shi, Fattoumah irin yaran nan ne masu riƙo da kuma
kishin iyayensu mata gaba ɗaya taji abin da Father yake faɗa akan Sheikh.

Fita Mother tai tana sakkowa fuskarta ɗauke da fara'a tasan tun da taga Abba Hakimi
to Sheikh yana can gida cikin kwanciyar hankali. A ƙasa ta zauna tana gaida shi ya
amsa a nutse kafin ya yi magana Father ya fito shi ma ya zauna saman Kujera ya ce
"Sannu da hanya Abba Hakimi" kai kawai ya jinjina idanunsa akan Fattoumah yana
faɗin "Matar zo nan mana ke dawa haka?" Turo baki tayi idanunta na sauyawa ta ce
"Mijin me ya sa Father baya son Yaa Lee?" Sa mamaki Hakimi ya kalli Father yana
faɗin "Aliyu ya akai haka? Me ya sa kake barin raya su san abin da ke zuciyarka
ne?" Father ya ce "Abba Hakimi ta ya ya zan ƙi ɗana? Shirman Fatimah ne" da sauri
Fattoumah ta ce "Da gaske nake Mijin,ina jin yana faɗawa mother wai a nemo mahaifin
Yaa Lee kuma ai ba kyau ƙarya" surutun Fattoumah ya jijjiga Mother bata taɓa haifar
yarinyar mai kaifin bakin Fattoumah ba. "shige ki bamu waje Mamana kafin ranki ya
ɓaci laɓe kike mana kenan?" Turo baki Fattoumah tayi tace "Mother kawai ki nemowa
Yaa Lee Abbansa wanda zai so shi tunda father baya son sa" Abba Hakimi da Mother
suka kalli juna da sauri kuma suka janye idanunsu ko wanne tunani fal ransa. Tsawa
Mother ta yiwa Fattoumah ta tafi ɗakinu Maimoon tana sakin kuka ta fara bori a
ƙasan carpet.

A nutse Abba Hakimi ya kalli Mother ya ce "Aliyu yana state c.i.d Barrister Maryam"
a ruɗe Mother ta Kalli Hakimi hankali tashe take faɗin "An kama Babana? Innalillahi
wa'inna ilaihir raji'un wallahi sharri ne ba gaskiya ba, kuma zan tabbata da hakan"
Hakimi ya ce "Samu nutsuwa Barrister Maryam, mu duka ba zamu ja da ikon Allah ba,
kuma da hujjar kare Aliyu, shi ya sa nazo naji ko ya faɗa muku wani abun?" Father
ya yi dariyar baƙin ciki ya ce "Wannan ne zai magana? Ko ya yi bata da wani amfani
me zamu fahimta banda, A...Aaaa...ƙikkkk... Yeee gaba ɗaya Aliyu bashi da amfani a
rayuwarmu, naji baƙin cikin samunsa Matsayin ɗa namiji" wani baƙin ciki ya tukare
zuciyar Mother idanunta na cika da hawaye ta ce "Sai yanzu na fahimta larurar Aliyu
ta sanya kake ƙinsa? Ubangiji ya ɗora masa shi nake roƙa kuma ya ye masa" Abba
Hakimi ya numfasa kalam Father sun bashi mmki a haka ya share ya ce "kayi babban
kuskure Aliyu, kuma Sheikh abin Alfaharin duk wani ɗan Kano dama Najeriya ne,
muhimmancin bai tsaya iya ƙasar shi ba, har ƙasa mai tsarki.. Allah ya kyauta wata
rana zaka gane gaskiya lokacin da za kaji kunya" juyawa kan Mother yai ya ce "Akwai
abin da ya faɗa miki ne, ina son shigar da maganar zuwa court ne" Mother ta ce
"Yana cikin ƙoƙarin fahimtar dani suka taho wajanka ya faɗa mini bashi ya aikata
ba, kuma ni ma na shigar da ƙara ni zan tsaya masa tare da Barrister Zainab" wayar
Mother ce ta fara ringing ganin sunan Umar-khan ya sanya ta ɗauka cikin sauri ta
miƙe tana faɗin "Ohhh ok on our way" kashe wayar tayi idanunta akan Abba Hakimi ta
ce "Umar-khan ya ce muzo yanzu al'amarin ya shige tunani" da sauri ta nufi ɗaki
tare da ɗakko mayafi da key car.
Abba Hakimi da Mother suka nufi state c.i.d hankali a tashe Maimoon da Zeefa da
Fattoumah sai kuka suke a rayuwa suna ƙaunar yayan nasu duk da babu wata jituwa a
tsakaninsu. Ko abinci suka kasa ci sai sallah kawai da suke suna addu'ar Allah ya
kuɓutar da Sheikh ɗin. Hankali kwance Father yake zaune yana waya da babban
amininsa ko da wasa bai masa magana akan matsalar da suke ciki ba, duk da cewa
al'amarin ya gama zaga ko'ina a faɗin Nigeria.
A kiɗime Mother take bin su Saif-Wazir da kallo ganin yadda idanunshi ya yi jajur
alamar kuka suka sha. "Ina Babana ina Aliyu mai ya faru da shi?" Shiru Saif-Wazir
ya yi mata, ta juya kan Umar-khan ta riƙe wuyansa sosai cikin faɗa ta ce "Where's
my son Umar-khan? Ina Aliyuna?" Umar-khan ya yi ƙasa da idanun shi ba tare da ya ce
komai ba. Sakin Umar-khan tayi ta nufi wajan Ishaq-hakim ta ce "Ishaq-hakim faɗa
mini gsky ina Aliyu me akace yana da gsky ko? Ba aikata abin da ake zarginsa ba?"
Hannunsa ya ɗaga tare da nuna mata wani waje da sauri ta juya Idanunta ya sauka
akan Sheikh Aliyu Haydar Aliyu wanda aka cire masa Jallabiyar jikinsa aka ɗauresa
da Sarƙa tun daga wuyansa hannunsa zuwa ƙafarsa farar fatar jikinsa tayi jajir
bakin Ishaq-hakim na rawa ya ce "Mother Sheikh ya amsa laifin da ake zarginsa ya
tabbatar shi ne ya lalata ƴan matan hadda ciki.....


_*IDAN BA KE...* labari ne da kuka daɗe ba kuci karo da irinsa ba, ƙaddarar labarin
akan soyayya ne mai tsayawa a zuciya da saka shauƙi a zuƙatan masu karatu.....
Tsammaci abin da baka tsammani salo na musamman🫣💋 08119237616._
[1/3, 4:48 PM] Abk: *🌈 IDAN BA KE 🌈*

_*Zaku samu cikakken labarin a Arewabooks, kuyi searching sunan littafin ko
username Arewabooks@Nimcyluv*_

8....
Ihu da kururuwa Prince ya din ga yi, sbd tsananin azabar da Abba ya ganawa masa.
Cikin wata kakkausar murya wacce take nuna cewa ko a cikin Aljanu shi ɗin nada
banne, kuma taƙadiri ne. "Akan aurena dake kan Halisa banƙi na kashe kowa na illata
shi ba, daga ci hadda kai Abba, ba ruwana da kasancewar ka mahaifina, kada ka
rabani da Danejona zakai babban kuskure zanyi ɓarna a duniya" Bakin Abba na fitar
da hayaƙi kamar zai kunna wuta a ciki ya ɗaga hannunsa sama gaba ɗaya ya naɗe
Prince cikin wata sarƙa da yana bakinsa ɗauke da addu'ar neman samun nasara akan
Prince ɗin.
Duk ihun da yake bai hana Abba ya sarƙafesa cikin yanar ba idanunshi ya yi wata
kala. Cikin ɗaga murya mai amo! Ya ce "Na raba aurenka da Halisa, babu kai ba ita,
kuma a yanzu zan cire cikin dake jikinta mara imani mai muguwar zuciya" yana faɗin
haka ya yi girgiza tare da ɓatar da Prince ɗin baki ɗaya daga wajan. A hankali Abba
wanda Asalin sunansa ya kasance MURWAS ya sauke numfashi, tare da juyawa ya kalli
Halisa dake kwance a ƙasa tana barci, juyawa ya sakeyi ya kalli Safwan dake kwance
shi ma. Cikin nutsuwa wacce ba zata addabi dabbobin dajin ba ya yi Girgiza tare da
rikiɗewa ya koma suffar mutane sak. Hannuna ya ya ɗauki Halisa Dajeno Rome da sauri
ya nufi cikin Rugar Rome zuciyarsa fal farin ciki ganin yau ya raba ɗansa Bilal da
Bil-adam.
Babu kowa cikin rugar kamar an share hakan yasa ya fara bin bukkokin Rugar da kallo
kamar daga sama Hamma Yabi ya fito daga cikin ruga zufa na yanko masa hannunsa riƙe
da ƙwarya maganin gaba ɗaya tunaninsa ya yafi wani wajan bai lura da mutumin dake
tsaye yana binsa da kallo ba. "Jamɓanduna" Abba ya faɗa yana kallon Hamma Yabi dake
ƙoƙarin yin gaba, tsayawa ya yi yana duba mutumin da ya ce masa Ina kwana, cike da
mamaki ya ce "Jamni tawon" ma'ana lafiya. Abba ya jinjina kai ba tare da ya ce
komai ba, jikin Hamma Yabi na rawa ya amshi Danejo daga hannun Abba kafin ya ce
"Ikon Allah, ina kasa meta? Tsayin mako guda ta ɓace mana ba ita ba labarinta, shai
Allahamdulillah" Murmushi mai sanyi Abba ya yi cikin nutsuwa ya ce "Ayyah ni ma
yanzu ina iyu a cikin ruwan na ganta kwance gefen ruwan" cikin nuna jin daɗi da
manta halin da Dada ke ciki wanda duk rashin Danejo ya haifar da haka ya ce
"Shannu, wallahi shannunka kaji" kai kawai Abba ya ɗaga yana ƙarewa yanayin rugar
kallo kafin ya juya bayan sun yi Sallama da Hamma Yabi yabar wajan. Yana fita ya
ɓace a wajan baki ɗaya.

Dada na kwance bakinta na fitar da wani ruwa kamar dafara Shatu na gefe tana kuka
tamkar ranta zai fita. A cikin wannan halin Hamma Yabi ya shigo cikin bukkar
hannunsa ɗauke da Danejo wacce har yanzu take bacci. Jikin Shatu na rawa ta miƙe
fuskarta cike da hawayen halin da mahaifiyarsu ke ciki, amma hakan bai hana
Fuskarta baiyyanar da farin cikin da zuciyarta ke ciki ba na ganin Yayarta Danejo.
Bakinta na rawa ta ce "Hamma ina ka samu Danejo, da gaske ita ce yanzu Dada zata
tashi naji daɗi sosai" bai ce komai ba ya kwantar da Danejo gefen Dada idanunsa
akanta ya ce "Maza kawo mini ruwa" Shatu ta miƙe da sauri tare da nufar tulo ta
tsiyayi ruwan mai ɗan sanyi, tana bashi ya shiga shafawa Danejo yana kiran sunanta.
A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana buɗe ido a nutse. "Danejo"... "Halisa" Shatu
da Hamma suka kira sunanta lokaci guda,a sanyaye cikin sanyin jikinta kamar kullum
ta shiga binsu da idanu. "Kin farka?" Kalmar Hamma ta sanya ta lumshe idanunta kana
ta buɗe a hankali tana sake binsa da kallo kafin ta yunƙura zuwa zaune "Naga kuna
ta kallona kamar za a cini ɗaya?" Murmushi Hamma ya yi ya ce "Munji daɗin ganinki
Danejo, mako guda kenan mun rasaki kin ɓace daga idanunmu" da Mmki take kallonsa
ɓata? Mako guda? Taje ina? Ita gani tayi kamar barci take mai ɗauke da mafarkai
kala-kala. Shiru tayi tana ƙara sauke numfashi tare da fara tunanin maganar Hamma
Yabi. "Hankalinmu ya tashi, Kullum Dada cikin kiran sunanki take, gashi yanzu ko
buɗe ido ba tayi jikinta ya tashi ina tsoro kada mu rasa Dada kamar yadda muka rasa
Baffa" ambaton sunan Dada ya saka Danejo saurin juyawa zuwa gefenta manyan idanunta
ta buɗe "Dadata" ta furta a ruɗe ganin yadda Dada ta ƙanƙame jiki, idanunta na
kafewa kamar mai shirin mutuwa cikin muryar kuka ta ce "Na lalashe ni Danejo Dadata
kada ki barni kada ki mutu do Allah,Kada kibi Baffana" sai girgizata take amma ina
Dada ko motsi ba tayi.
Da sauri Hamma ya fita zuwa bakin hanya tare da samu abin hawa yana zuwa suka ɗauki
Dada a mota zuwa asibiti, asibitin babu jama'a sosai. Dr Hamza na zaune a Office
gabansa cike da kuɗi ya kalli Dr Iliya ya ce "Kawo maganin nan ya yi mana rawa
sosai, na ƙara tura saƙo zuwa ɓangaren lafiya akan magungunan da suka bayar ya
ƙare, sbd cututtukan da suke damun jama'ar rugar, ina saka ran cikin satin nan za a
kawo maganin" Dr Iliya ya numfasa yana jinjina kai kafin ya ce "That's good. Amma
da gaske maganin ya ƙare ne?".. "No ba wani ƙare wa da ya yi, har yanzu ban bawa ko
mutum ɗaya ba" cikin fahimta Dr Iliya ya kalli Dr Hamza yana faɗin "huh! za a kawo
maganin sauro kyauta ma a raba, sbd yawaitar Maleriya"

"Na samu Information ɗin hakan, amma idan an kawo gidan sauron, asibitin nan za a
Ajjiye mu zamu raba, so za a bawa Kowa akan 1500 each one" waro ido waje Dr Iliya
ya yi kafin ya ce "baka ganin zamu iya samun matsala, tunda kyauta gwamnati ta
bayar?" Ɗaga hannu Dr Hamza ya yi yana dakatar da Dr Iliya da faɗin "Hakan shi ne
ribarmu, ba za mu yi musu bauta ba kamar wasu bayi, they have to pay"
Kafin Iliya ya yi magana Hamma Yabi ya faɗo office ɗin da sauri cikin tsawa Dr
Hamza ya ce "Malam ya haka zaka faɗo kamar wani mahaukaci? Me ya sa duk fulanin nan
baku da ilimin zaman rayuwa ne, baku san yadda ake mu'amala ba?" Hamma baya gane
zancan nasu ya ce "Don Allah ka taimaki Dadarmu, kada ta mutu cikin wannan halin
ita kaɗai ta rage mana, sau wajan goma ina zuwa" "Idan munje kanta lafiya zamu bata
kenan? Ko zamu hanata mutuwa? Zan maka last warning Kada na sake ganin ƙafarka
cikin asibitin nan, na faɗa maka bamu da maganin ko ɗaya me kake so nayi maka? Haba
kuna yi mana adalci mu likitoci sai an bimu a hankali mai ya sa zan zuciyarku ya yi
yawa ne?" kasa magana Hamma yai sbd Hawayen daya cika masa idanu me ya sa su Fulani
ake musu kallon mahaukata wanda basu san me suke ba? Akwai wani bambanci a jikinsu
wanda ya bambanta su da sauran jama'a ne? Juyawa ya yi yana zuriyarsa babu daɗi.
Danejo na ganinsa ta ce "Hamma ya naga ka daɗe, numfashi Dadata zai gudu ka
taimaka, ina masu bada lafiya ɗin?" A hankali ya kama hannunta ya riƙe yana shafa
kanta dake ɗauke da suma mai kyau can ƙasa ya ce "Muje gida, ba zamu ƙara zuwa
asibitin nan ba, Allah ya a bamu Kuɗi mu kaita asibitin burni" shiru kawai tayi
tana kallonsa tare da son fahimtar abin da yake nufi a haka suka koma gida jiki
babu daɗi, kwana sukai ba su yi bacci ba, Shatu kawai ta runsta sbd ƙarancin
shekarunta. A daren Danejo ta sanyawa ranta zata sai da nono iya iyawarta ta tara
kuɗi masu yawa akai Dada asibiti. Hakan yasa ta tashi da asuba ta tatsi kindirmo a
ƙwayar gari na fara haske ta nufi cikin burni wajan Abti America.

Mother ce ke sakkowa daga upstairs kunnanta maƙale da waya idanunta sanye cikin
farin glasses ta fito a Barrister Maryam ɗinta sak. A hankali ta ce "Na riga nayi
reporting case ɗin, idan ba a samu good evedance ba akan wanda suka kawo ƙarar
Aliyuna, kai tsaye zan maka ko wacce ƴar banza a court dama kawai nake jira" daga
cikin wayar aka ja numfashi tace "Barrister Maryam kasa aje court,idan akaje to kin
bawa duniya damar zata fahimci halin da ake ciki,abi komai a sannu" ɓayayyiyar
ajjiyar zuciya Mother ta sauke idanunta na sauka akan Zeefa da Fattoumah "Ok za mu
yi magana bari naje wajansa Allah ya sa ya yi magana, al'amarin Sheikh na bani
tsoro yana bani mamaki" ƙara tattaunawa sukai kafin sukai sallama. "sannu da
sakkowa mother" idanunta akan Plasma ɗin da suke kallo ta ce "Fattoumah sau nawa
zan ce bana son kuna kallon zee world ne? Ashe ban isa daku ba ko?" A sanyaye
Fattoumah ta ce "We're sorry Mother ba zamu sake ba" zama tayi ta ce "Change the
channel immediately Mamana" Sauya channel Fattoumah ta yi zuwa Aljazeera tana faɗin
"Ok Mother" kallonsu ta yi sosai ta ce "Where's Maimoon and Auta?" Zeefa ta bata
amsa da "She's inside the kitchen, Auta barci take" Mother ta ce "Bana son barcin
yamma taso mini ita" tana faɗin ta miƙe tare da nufar kitchen daga bakin ƙofa ta
tsaya tana kallon Maimoon dake haɗa coffee ta ce "Ina Lunch ɗin Sheikh?"... "Gashi
a tray mother bari na kai masa" tsareta tayi da idanu ta ce "Bani nan" tray ɗin
lunch ta bawa Mother tana ci-gaba da aikin gabanta.
Haɗaɗɗan part

6 / 66