Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   47 / 66

138K to 141K   out of 196.1K words

‫َأ‬ ‫َأ‬ ‫َأ‬
‫ الّلُهَّم ِإْن ُكْنَت َتْعَلُم َّن َهَذا ْال ْمَر‬،‫ َو ْنَت َعّالُم الُغيوِب‬،‫ َوَتْعَلُم َوال ْعَلم‬،‫ْقِدر‬
Idan zama da Halisa matsayin matata shi ne alheri
‫َو ْن ُكْنَت َتْعَل‬ ‫َأ‬ ‫َأ‬
‫ ِإ‬- ،‫ َعاِجِلِه َو ِجِلِه َفاْقُدْرُه ِلي َوَيِّسْرُه ِلي ُثَّم َباِرْك ِلي ِفيِه‬،‫َخْيٌر ِلي ِفي ِديِني َوَمَعاِشي َوَعاِقَبِة ْمِري‬
‫َح ْي ُث َكا َن ُث َّم َأ ْر ِض ِني ِب ِه‬ ‫ِل‬
‫ َفا ْص ِر ْف ُه َوا ْص ِر ْف ِني َع ْن ُه َوا ْق ُد ْر ي ا ْل َخ ْي َر‬،‫ َأ ْم ِري‬."
Bayan ya kammala Sallar Istihara ɗin ya jingina da jikin gado idanunsa rufe, barci
ya ƙaura cewa Idanunsa tare da yi masa hijira, ƙaramar yarinya na son Jan shi a
ƙasa ya zama kamar bita zai-zai, bai taɓa mafarkin zata ƙaurace masa har haka
ba,bai ɗauka bayan shi zata damu da ganin wasu nata ba, ya ɗauka iya shi ɗaya ya
ishe ta a rayuwa. Ya ɗauka ba zata nemi soyayya mai zafi daga gare shi ba, sai
gashi tunaninsa ya saɓa zaton shi. Har aka kira Assalatu yana zaune, rabon shi da
cin kyakkyawan abinci har ya manya. Ya miƙe yana ɗaukan casbawa tare da yin waje. A
harabar gidan yaci karo da Abba Hakimi da kuma Umar-khan da Ishaq-Hakim sun fito
zasu nufi Masjid. Suka jera ba tare da kowa ya yi magana ba,cikin takun shi mai
kama dana wahainiya, nutsuwa,kamala, kwarjini da tarin Ilhama dake kwance saman
fuskar YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU ya shiga wajan liman tare data kabbarar
harama, karatu ya fara a sanyaye cikin rashin sautin murya saɓanin da, gabaɗaya
suka rasa meke damun shi yana yi yana rafkanwa, bayan ya sallame ya yi sujjada
bayan sallama. (Sujjadar ba'adi). Wa'azi ya fara akan gudun duniya da duk wani
kayan kyale-kyale dake cikinta.
Misalin 10 na safe Abba Hakimi da Mother da kuma Umma A'isha na zaune saman kujera
Halisa fito sanye da ƙaton hijabi har ƙasa, ta durƙosa har ƙasa ta gaishe su.
"Matar ya ya akai ne?"
Ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Jon wuro makaranta nake son na koma Please" ya
daɗe yana kallonta yana jajanta lamarin kafin ya ce. "An shige ki da yawa, wanne
mataki ki ke kafin ku dawo?" Ta ce "Jss2 zan shiga" ya ce "Tab, yanzu Kinyi girma
sai dai a biya ki zana weac da neco, bana jin kuma zaki iya karatun University"
Da sauri ta ce "Zan iya Jon wuro, Allah ina da ƙoƙari ko karatun Alkur'anin da ka
ke mini haddace shi nake, gashi yanzu ina izu talatin da biyar" ya ce.
"Na gamsu, duk da ina mamakin kaifin tunaninki da basirar da Ubangiji ya baki
Halisa" Mother tai murmushi ta ce "Duk wanda ya zauna da YAA SHEIKH ai ba zai taɓa
zama daƙiƙi ba,balle kuma wanda ya rena" walwalar fuskar Halisa ta ɗauke ta ce "Ai
da ƙoƙarina Dada ta haifeni"
Mother ta ce "Haka fa" ita dai tai shiru
Abba Hakimi ya ce "Tambayi mijinki, shi ne zai baki iznin idan ya amince zan bawa
Umar-khan ya yi komai"
Tamkar zatai kuka ta ce
"Ni bani da wani miji, ka dai na haɗani da kowa don Allah Jon wuro" daga bakin ƙofa
aka ce.
"Anƙi ɗin, bayan duniya ta gama shaidawa Gadanga shi ne mijinki kuma shi ne
gatanki"
Jadda ta ƙarasa faɗa tana shigowa ciki, Maimoon ta biyo bayanta. Daga tsaye Jadda
ta ce "Halisa ki ke meye ne? Ke kam ba a nonon Khadijah ki sha wannan mugun halin
ba, uwarki ba haka take ba, ta san halarci ta san kuma wanda ya yi mata, tun wuri
ina baki shawara ki bi mijinki dau da ƙafa, kafin wata can tayi ciki tashi, ni
Alkur'an da zai aure mata uku ma da ya kyauta mini, ai lafinki ne da ki ka sake
masa jiki yana lugudan da ya yi niyya da shi, har ya banka miki ciki, waya faɗa
miki ana yi wa namiji haka? Ai basu da kunya ta wannan ɓangaren kuma tunda kuka
fara dole ku ƙare tare, balle namiji kamar Malam wanda ya karanta yaji komai a
Muslunci"
Wani takaici ya kama Halisa ta ce.
"To ya yi auren mana, ni daman ai bana son shi" Jadda ta dungure mata kai ta ce
"Laa! Ji tsinanniyar ƙarya, mai ƙarya a ƙona shi a wuta yasin, gashi nan kin cika
kin yi fam! Alamar kin son buƙatar mijinki mayya kema ɗin fitinanniyya ki yi ta
lalata ɗan jama'a yanzu ki guje shi" ta juya kan Abba Hakimi ta ce "Can fa naci
karo da shi, wallahi sai dana zubar masa da ƙwalla, ni na ɗauka ma da wani ɗan
ganyen nai karo kai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, wai Malam ne soyayya ta
rugurguza shi haka, huhuhu! Ke kam ba zaki taɓa gamawa da duniya salamun ƙaulin ma
idan har baki rungomi mijinki da hannu bibbiyu ba, idan ba yara ki ke so kina samun
cikinsu akan titi ba" ba wanda ya kulata can ta nisa ta ce.
"A to meye ma ruwana, wannan rayuwar kowa yaji da abin da yake gaban shi, Allah ya
sa ba wata tsiyar na ce ba, amma dai ƴar mutan Rome kinci amanar malam" Umma A'isha
ta ce "Amana kam ta ci" Jadda ta muskuta ta ce
"To Ubangiji ya san yadda zai da lamarin, ko kuma kawai ya saki ƴar banza mai zubin
zabiya, ni da ƴata ce da tuni na haɗa mutin a gaban kowa zai ɗaga mata nono" ta
jinjina kai ta ce "Allah ya san yadda zai da lamarin" Halisa ta haɗe fuska sosai ta
ce
"Idan auren a hannunki yake yanzu ki sake mini shi, ko ki je ki sanya ya sake ni ki
ga idan zan mutu masifaffiyar mata kawai" Jadda tai mitsi mitsi da idanu ta ce
"Kiga masifa akan Mai rawani Wlh shi ne azababbe, meye nawa da zan raba haɗin
Allah?" Mother ta shiga cikin zan can ta ce.
"Rabo da Jadda kin ji daughter, gidan Aliyu ne ba zaki koma ba" Ta kalli Abba
Hakimi ta ce
"Jon wuro makarantar?" Ya numfasa ya ce "A'a, ba ruwana jeki nemi izini wajan
mijinki,kafin ya ce baƙin ciki nake masa"
Ta miƙe zuciyarta babu daɗi bata son duk abin da zai sanya ta shiga sabgar shi.
Bayan tafiyarta Jadda ta ce
"Maryam haƙuri nazo baki, ki daina gani na kamar tsohuwar banza nasan me nake,
Yaran da Ubangiji ya azurtaku dasu zaki duba, kada rayuwar su ta ƙare a haka"
Mother ta ce.
"Ayya Jadda kin yi mini adalci kuma ki fahimci ni, wallahi a yanzu bana son
Engineer ko kaɗan, zaman court kawai nake jira ya sawwaƙe mini kuma ya bani
ƴaƴana..." Mother ta dinga faɗa ta inda ta shiga bata nan take fita ba. Jadda ta
fashe da kuka ta ce.
"Azaba, daga nemen taimako sai zagi Maryam?" Dr A'isha data shigo yanzu ta ce.
"Babu batun zagi, Gasky ce kawai ya bata raguwar sakin ya je ya yi rayuwa da sauran
karuwai" Mother ta kalli Dr A'isha haka kurum kalmar ƙarshe ta ɓata marai har taji
zafin Dr A'isha ɗin. "Ya je ya yi rayuwar da sauran karuwai" hausawa sun yi gaskiya
da suka ce ba a shiga tsakanin miji da mata, duk lalacewar mijinki dole a kira shi
da uban ƴaƴanka, bare kuma _first love_
Jiki a sanyaye Jadda ta fito daga gidan, Engineer dake cikin mota gaban shi ya faɗi
ganin yadda mahaifiyar ta shi ta fito, gabaɗaya Ƴan-uwan shi suƙi saka baki cikin
matsalar.
Dr A'isha ta miƙe ganin Mother bata tanka ta ba, ta nufi bedroom ɗin Halisa ta
shiga bata kyakkyawan darasi akan ƊA-NAMIJI ta ɗora ta akan tubalin da zata ka Yaa
Sheikh hankali kwance duk ta nunawa Dr A'isha ita bata ra'ayin Yaa Sheikh yanzu,
karatu kawai take so. Ta rantse da abin da zai kasheta ba zata koma gidan shi ba,
balle auren shi.
Dr A'isha ta bata sabuwar waya mai kyau tare da sim, ta buɗe mata komai WhatsApp,
Arewabooks, wattpad. Ta nuna mata yadda ake karatun littafin duk ta iya Hausa harda
ɗan turanci. Kana ta sakata cikin wani shahararren group na MU MA MATA NE.
Ta ƙara yi mata gargaɗin kada ta kuskura ta ƙara barin Yaa Sheikh ya taɓa koda
hannunta ne.
Kiran Ummul a waya ya sanya Yaa Sheikh shiryawa cikin wata dakakkiyar shadda mai
kyau da ɗaukan idanu, fara tas ya ɗora hirami idanunsa maƙale cikin sirirn farin
Glasses photochronic and faɗawar da kwayar idanunsa tayi. Kasancewar ranar juma'a
ne ya ɗora Alkyabba mara nauyi, ya fito a babban malami mai ɗaukan ƙaddara a ko
wanne lokaci da yarda da ita, ba zai iya driving ba haka ya sa Umar-khan ya yi
driving nasa zuwa grandparents house ɗin shi. Ya fito a nutse bakinsa ɗauke da
zikirin ranar juma'a ya ɗaga idanunsa ganin garin a lullume alamar hadari ne a
ƙasa, ya ɗauke yana shigewa ciki.
Wacce ya gani zaune a parlourn ya bashi mamaki ainun, yaushe ta zo? da izinin wa ta
fito? Ƙarar shi ta kawo wajan Ummul ɗin shi ko ya ya?
Ya yi sallama bashi da tabbacin da amsa, amma yana da yaƙinin zata amsa ɗin, kafin
ya zauna Ummul ta fito hannunta riƙe da plate na wainar fulawa da lemon kankana,
suka haɗa idanu ta ce.
"Sai yanzu?" Ya zauna gefenta yana jinjina kai ta ce "Daughter ga wainar nan, ɗan
malalen kuma ba a ƙare ba" Halisa ta yi murmushi ta ce "Thank you Ummul ɗina"
Maimoon ta ce "Zan ci ni ma" Halisa ta shagwaɓe fuska idanunta cike da ware tana
buga ƙafa ta ce.
"Ummul kin ganta ko?" Ummul ta ce "Maimoon bar mata, taci tai ƙiba" Yaa Sheikh ya
tabbatar gangar jikinsa ce kawai ke tare da shi, amma gabaɗaya tunaninsa,
zuciyarsa, ruhinsa yana gare ta, bai taɓa ganin yadda aka so uwa kuma aka tsani ɗan
ta ba.
Ummul ta juya kan Yaa Sheikh ta ce.
"Ina son ka bawa Daughter dama ta koma makaranta" kafin Yaa Sheikh ya yi magana
Alhaji Farouk ya faɗo cikin parlourn...
[1/20, 7:09 AM] Abk: Alhaji Farouk bai gama sanin Ummul ba, amma nutsuwarsu da ta
zo ɗaya da Yaa Sheikh ya sa kai tsaye ya gano ta, ya yinda da ita Ummul ɗin ganin
farko ta wayi fuskar shi sbd kamar da suke da Zahrah, ba tare da nuna wata damuwa
ba kasancewar ta wayayyiya ta ɗauke kai daga duban shi.
Yadda ya faɗo musu parlour without everyone's permission ba sallama ba komai shi ya
ɗan sosa mata ranta.
Halisa ma ɗauke idanu tayi haka kawai ta ji zuciyarta na buga Jikinta ya mance
murus.
Yaa Sheikh bai kalli Alhaji Farouk ba, bai kuma yi mmkin zuwan na shi ba, a irin
gane-ganen shi ya gano kusan dalilin zuwan Alhaji Farouk ɗin.
Alhaji Farouk ya zube saman carpet bakin shi na rawa ya ce.
"Am sorry na shigo without permission, ayi mini afuwa" Ummul ta ce
"Ba damuwa,idan har lafiya?" Ya girgiza kai ya ce "wallahi ba lafiya ba Hajiya
Ummul-khairy, ina cikin tashin hankali, damuwar da kuɗin da nake da shi bai isa ya
siye ta ba, ko ya biya mini ita ba" Ummul tai jim
Kafin ta ɗauke numfashi idanunta can akan plasma ta ce
"To! Ubangijin al'arshi ya yi mana magani" Alhaji Farouk ya kasa cewa komai, sbd
wani irin nauyi da Ummul ta yi masa a cikin idanunsa, wani kwarjininta na musamman
ya mamaye shi har ya gaza cewa komai, gabaɗaya kalaman shi suka ɗauke tare da yin
hijira daga cikin bakinsa.
Ummul ta fuskance shi tana girgiza ƙafa ta ce
"Alhaji Farouk ko? Ya akai ne ka same mu cikin uzuri mu ma"
Ya goge zufar data yanko masa, Ummul ta kalli Umar-khan daya shigo ta ce "Umar-khan
ƙaro mana A.cn nan ko?" Ya ce "To! Ummul!"
Alhaji Farouk ya rusuna sosai tare da yin zaman ƴan bori ya ce
"Taimako nake nema Hajiya Ummul, ki dobi girman Allah dana Manzon shi, kada ki dubi
girman laifin da Zahrah ta wanzo tana aikatawa a gareki, wallahi ke kaɗai ce
matakin da zanbi wajan ceto ran ƴata dake gadon asibiti, cikin halin rayuwa ko
mutuwa...,"
Ummul ta tari numfashin shi da cewa
"Kamar Alhaji Farouk ya yi makkowa, Ubangiji ke da rayuwa shi ke da mutuwa, kuskure
ne haɗa wannan da wani bawa" ya jinjina kai ya ce
"Haka ne, na ji na ƙara samun ƙarfin gwiwar faɗa miki komai, na fahimci ba iya
ɗanki ke da ilimin addini da sanin Allah da yarda da ƙaddara ba, hadda ke kan ki"
Yaa Sheikh gabaɗaya a takure ya ke jinsa, duk kalma ɗaya da ake faɗa har tsakiyar
kan shi yake jinta, shi ya sa ya yi baya a hankali tare da yin lamo jikin kujera
yana riƙe hannun Ummul.
Alhaji Farouk ya ɗora da faɗin "Nasan idan na faɗi abin da yake rai ka, za kuga
kamar na zama mara kunya, na sani duk wani uba dole zai so abin da yarinyar shi ke
so, irin son nan na mutuwa wanda zai iya kaita lahira, ki kwatanta hakan matsayin
ke ce mahaifiyar Zahrah, zaki iya zuba idanu ta mutu akan soyayyar wani babban
Malami, masanin addini, a faɗin nahiyar nan tamu ta wajanta baki ɗaya, malamin da
yake da nagarta wanda ake sauraran tafsirin shi fiye dana sauran Malaman da muke da
su, malamin daya mallaki bankununi adadin wajan biyar, reshen, Kano, Kaduna, Abuja,
Katsina da sauran su, wanda ya mallaki kamfanin sarrafa shinkafa domin ra gewa
talakawa farashin yadda suke siye wajan wasu, malami na farko da aka samu ya buɗe
gidan marayu yake ciyar da su, da kuɗin shi, yake basu karatu, malamin daya raya
makarantun tsangayoyi zuwa na zamani, ina nufin YAA SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU" Cak
Halisa ta ajjiye wainar data ɗakko da zummar kaiwa bakinta, daman tunda aka kawo
bata ci ba, tana ƙoƙarin ci Alhaji Farouk ya shigo.
Bayanan shi suka sanya ta kasa ci sai yanzu da take shirin ci ta ji abin da ya nemi
tarwatsa mata zuciya da sanya ƙaramar kwakwalwarta cikin halin troma, wani irin
masifaffan kishi ya ta so mata, ƙirjinta ya yi mata nauyi, numfashinta ya tsaya cak
wanda ya sanya ta shiga kokawar dawo da shi amma abin ya gagara idanunta ya shiga
rufewa kamar mai shirin suma, hawaye na fitowa daga cikin idanunta da sukai jajir.
A firgice Maimoon data ankara ta ce "Anti Halisa me ne ya sameki, lafiya
innalillahi Ummul Yaa Sheikh Anti Halisa suma take wallahi"
Yaa Sheikh ya buɗe gajiyayyun Idanunsa wanda kwana biyu barci ya ƙaura ce daga
cikinsu, yana yunƙurin ta shi Ummul ta girgiza masa kai tare da yi masa nuni daya
koma ya zauna
Ya bi umarnin ta, ya zauna yana mai riƙe kan shi, a zuciyar shi tsoro da fargabar
abin da ya jefa Zawjan shi cikin wannan yanayin yake, yanzu ƙwayar idanunsa suka
hangota lafiya lou yanzu kuma ta rikice kamar wacce ke farfaɗiyya ko wacce Aljanu
suka bugar.
Ummul ta tallafo Halisa Jikinta tare da amsar ruwa mai sanyi daga wajan Maimoon ta
shiga shafa mata a fuska, a hankali

47 / 66