Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IDAN BA KE Complete Hausa Novel by Nimcyluv Sarauta

Author :  Nimcyluv sarauta Category :  African Stories & Novels

Chapter   55 / 66

162K to 165K   out of 196.1K words

Abba, Zawja rigima"
Kamar tana jinsa ta tura baki tana ƙara shige masa da kyau, hakan ya ƙara rikita
Yaa Sheikh ya kame bakinta ya shiga kissing cikin zafin nawa da kewa, tayi saurin
buɗe ido sbd juyawar da abin cikinta ya yi ya daki mararta nan da nan fitsari ya
taso mata, kallonsa kawai tayi tare da zare Jikinta ta nufi bathroom, tunda ta
shiga bata fito ba har barci ya fara ɗaukan shi.
Da Subhi Zahrah ta farka ta shafa taji babu Yaa Sheikh, ƙirjinta ya harba ta miƙe
da sauri tana tashi taga ya buɗe ƙofa ya shigo jikinsa kayan jiya ne, amma kamar
wanka ya yi gabaɗaya sumar kansa ta kwanta tana zubar da ruwa, bai bari ta kalli
cikin idanunsa ba ya shige bathroom ɗin shi, Alwala ya ɗaura tunda ya riga da ya yi
wankan da bai niyya ba, ya fito ya ganta tsaye bai ce komai ba, ya shirya cikin ash
ɗin Jallabiya mai kyau ya nufi masjid, Zahrah ta koma tare da kwanciya ta ci-gaba
da barci.
Da ƙyar Halisa tayi sallah sbd ciwon da Jikinta yake, da gajiyar da Abbanta ya tara
mata, sai jiya ta ƙara tabbatarwa Yaa Sheikh namiji ne bai nuni tausayi ko ɗaya a
gareta ba, sai daya fanshe gabaɗaya kewar daya ɗauka, duka abinda ya tara a jikinsa
sai daya juye mata shi, da ƙyar ta samu kanta, ta miƙe da ga kan prayer mat ta nufi
kitchen ta kunna gas ta shiga haɗa tea ta yanka albasa da Attahiru, bayan ta
kammala dafa tea ɗin da yaji kayan ƙamshi domin komai an zuba mata a kitchen
musamman kayan ƙamshi, ta soya lafiyayyan ƙwai da yaji albasa. Ta juye tea ɗin a
mug mai ɗan girma ta zuba soyayyan egg ɗin a plate mai faɗi.
Kasancewar ya gaji kuma yunwa yake ji sosai yasa 6 daidai ya dawo gidan, mmki ya
ƙara kama shi ganin Zahrah kwance ya nufeta yana bubbuga pillow ta buɗe ido ta ce
"Sweetheart" a taƙaice ya ce "Kinyi sallah?" Ta ce "What's the time? 10 ya yi" ya
buɗe baki ya ce "10? To tashi ki koma part naki idan yyi kiyi sallah" kafin tayi
magana yaji ƙamshin Matar Malam ya kawo masa ziyara, yana daga tsaye ya juya suka
haɗa idanu sai yaga ta sakar masa murmushi fararan haƙoranta a bayyane, Zahrah dake
kan bed ta kalli Halisa batai tunani zata kula Yaa Sheikh a yanzu ba, Halisa ta
ajjiye tray ɗin hannunta ta zuba ƙamshin turare daga ita sai wata riga ƙarama sai
wando three gaiter cinyoyinta duk a waje ta ɗaure kanta da ribbon, tana zuwa ta
rungome Yaa Sheikh tare da yin tsayin ƙafa shi kuma ya riƙe ƙugunta, ta sumbaci
cheeks ɗinsa both sides, Idanunta cikin nasa ta ɗora bakinta a nasa tayi kissing ta
ce "Sabahul khair ‫"حبيبة قلبي‬
Halisa ta juya ta kalli Zahrah da tayi tsaye ciki da mmkin makircin yarinyar ta ce
"Ke bakisan yau rana ta bace?" Halisa marairaccen fuska ta ce "Sorry Anty Zahrah,
Abbana yunwa yake ji ba zan iya barinsa haka" Ta saka hannu taja gemun Yaa Sheikh
daya kasa cewa komai har lokacin hannunsa yana riƙe da ƙugunta ta ɗan bugi ƙirjinsa
ta ce "Abbana shi ne da muna wanka ɗazo a bathroom na ka gudu ko? Bayan ko rama
cizon da kayi mini a breast ɗina ban yi ba.....[2/1, 10:38 AM] Abk: Gabaɗaya Idanun
Zahrah ya rufe sbd tashin hankali, ta ƙara buɗe idanunta akan Yaa Sheikh da yaƙi
yarda ya kalleta cikin damuwa taja tsaki tare da juyawa tabar ɗakin ko gabanta bata
gani ta riƙe ƙirjinta dake mata zafi. Tana fita daga bedroom ɗin Halisa ta zame
jikinta daga na Yaa Sheikh tana haɗe fuska tare da yin kicin-kicin da ranta kamar
ba ita ta gama kissa da kisisina ba.
Ganin zata juya ya riƙo hannunta yana dawo da ita cikin murya mai sanyi ya ce "Baki
isa ba"
"Kana jin yunwa, kuma aikina ne banda haka babu abinda zan zo nayi" ta faɗa tana
ɗauke fuskarta dake tafin hannunsa, ya zame tare da zama saman kujera idanunsa
lumshe sbd gabaɗaya ta gama kashe masa jiki garin kurar wata daga bedroom ɗin.
Ganin da gaske barin ɗakin za tayi ya sanya Yaa Sheikh haɗe yatsun hannunsa suka
bada sauti fuska kame ya ce
"Don't leave Haliyserh Sheikh Aliyu haydar Aliyu" muryarsa babu wasa cikinta, ya
kuma kame alamun umarni yake bata ba shawara yake nema ba.
Ta dawo tare da zubewa a ƙasa wajan ƙafafuwansa ta saki wani irin raunataccen kuka,
bai ce mata komai ba domin tana buƙatar kukan har zuciyarta tayi sanyi cikin kuka
ta ce
"Modibbo ya kake so nayi? Kasan yadda naji dana zo naga Anty Zahrah kwance a
gadonka, sabon gadon da ko zama banyi akai ba amma har matarka ta kwanta kenan a
jikinka ta kwanta tayi barci"
Ya harɗe hannu a ƙirji tare da buɗe ido yana kallon yadda take rigima da rikici
wanda zallar kishi ne ya haifar da su.
Ta miƙe tsaye, tare da cire rigar Jikinta, ya rage sai bra a Jikinta, tana kuka
sosai ta ƙara cire three gaiter ɗin Jikinta nan ma ya rage daga ita sai white lace
pat.
Tuni idanun Yaa Sheikh ya jirkice ya juye tare da yin ja, wani abu na fisgar shi
bai taɓa ganinta zahiri a cikin haske ba sai yau. Duk inda yaso yake cilla idanunsa
ya kalla a jikin nata, a ransa banda tasbihi da kiran sunan Allah babu abinda yake.
Halisa ta juya ta ƙara juyawa ta ce
"Ka faɗa mini wacce halitta ce a jigina bata cika ba har kaje ka auri raguwar wasu?
Ka faɗa mini dame ta fini har ka aureta ba tare da sani na ba sbd bani da
muhimmanci a wajanka, why Abba why me ya sa kasan zafi da raɗaɗin da nake ji a
raina kasan yadda kishinki ke barazanar ɗauke rayuwata?" Bata duba cikin Jikinta ba
ta durƙoshe a wajanta tana kuka sosai ta ƙara cewa
"Ka mayar dani wajan Ummul ni ba zan zauna dakai ba, ba zan iya sharing mijina da
wata ba" Ya wani irin kyakkyawan murmushi Yaa Sheikh ya yi wanda ya fidda fararan
haƙoransa gently ya miƙe tsaye tare da ƙara sawa inda take ya ce.
"Stand up" tayi shiru tana shassheƙar kuka, ya saka hannu ya ɗagota tsaye yana
janta zuwa bakin gadon shi ya zauna, tare da zaunar da ita saman cinyarsa ta saka
hannu zata ɗauki riga ta saka ya kame hannunsa bakinsa a kunnanta ya ce.
"Kinyi kaɗan" ta ƙara ɓata fuska ta ce "Ka sakeni, ai baka marmarin jikina kana da
wanda ya fishi, bani rigata" shi dai bai ce komai ba ya rungumeta ta baya yana
shafa cikinta ta ce
"Abba me ya sa" a taushashe ya ce "Ƙaddara Zawja, ban son rigima" ta juya ta kalle
shi ta ce "Au rigima? Wannan abin ka ɗauka matsayin rigima Yaa Sheikh?" Ya dubi
cikin idanunta ya numfasa ya ce "Ko wanne bawa yana da zanan ƙaddarar shi a bangon
littafin shi wanda aka bashi na tsayin rayuwa...," Ya yi jim yana ɗora kanta a
ƙirjinsa ya riƙe hannuwanta ya ce
"Yarda da ƙaddara shi ne cikar imani, kinsan zan aureki?" Ta girgiza masa kai ta ce
"Amma ina ganinka ai, a barci na" Ya yi murmushi mai kyau ya ce "To auren Zahrah a
farko ƙaddara ce, haka yanzu ma, Ubangiji ya umarci mu da auren mata sama da ɗaya
idan muna da hali da iko, ya ce idan ba zamuyi adalci ba mu auri ɗaya ita ce mafita
a garemu, ki duba suratul Nisâ'i 3 ayat zuwa 4 Hafizata"
Ta ce "Meyasa ka ɓoye mini? Meyasa kuma ka gudu ka barni? Meyasa kace ka divorce
paper nawa through bashi bane?" Ganin yana ta kallonta ya kasa cewa komai ta ce "I
understand,amma kasan ina sonka ko Yaa Sheikh?" Nan ma ya yi mata shiru, bisa dole
tayi shiru tasan idan ya yi haka akwai dalili, inma yanayin da yake ji yafi
ƙarfinsa,ko kuma abinda yake zuciyarsa yake son faɗa amma ya yi masa nauyi a
harshe.
Kamar daga sama taji ya ce "Ki bari na gwada miki banbanci a aikace, kin kurar mini
mata kinzo kina rikici sunan Breakfast aka kawo, Ya Allah ka dubi bawanka Aliyu" ta
tura baki gaba ta ce "to ina ruwana da matarka tazo ta zauna mana, ba wani kurarta
da nayi gulma ce kawai"
Ya haɗe fuska cikin nutsuwa da kulawa ya ce
"Zawja ki tayani yin adalci, yanzu ku biyu ne kowa ni yake buƙata kina da
muhimmanci a gareni ki yarda ƙaddara ce auren Zahrah, kin san idan kina haka
tsakani da Allah ni zaki jefa a wuta ya zaki dinga tsirara kina ƙulla mini sharri"
Ta kalle shi ganin da gaske kuma bai taɓa magana mai tsayin haka ba ta ce "Tom
Malam"
Yai mata shiru ta ce
"Tea ɗin fa?" Ya miƙa mata hannu ta ɗauki cup ta tsiyaya masa ta saka 2spoon na
honey kana ta bashi. Cikin nutsuwa yake sha har lokacin tana zaune akan ƙafafuwansa
ta ce "Malam ina da tambaya" ya jinjina mata kai ta ce "Wannan zumar meye
amfaninta?"
Da idanu ya kalleta bai mata amsa ba, ta saka hannu ta fara cin soyayyan egg ɗin,
harta manta da batun Zahrah domin ta samu Soyayyar mijinta, abu ɗaya ne ba zata iya
jure ganinsu waje guda ba, ta ciro wani zata kai bakin ya kama hannun tare da
turawa bakinsa yana ɗan yatsuna fuska, daga cin abinci Yaa Sheikh ya fara juye mata
duk da yana iya ƙoƙarin shi wajan ganin bai shiga hakƙin Zahrah ba amma sai ya yi
da gaske.
Ta miƙe tare da ɗaukan kayan rigarta cikin sauri tabar bedroom ɗin tana masa gwalo
ya bita da gajiyayyun Idanunsa. Ya jima a wajan kafin ya miƙe ya wanke bakinsa tas
ya nufi bed ɗin shi ya kwanta yana lumshe idanunsa, kwana biyu yana stressed kansa
da yawa jiya kuma da zai huta ya ƙarar da Lokacin shi wajan yin ibada da raya sunna
ta Manzon Allah. Zahrah tana shiga ɗakinta ta shiga safa da marwa kanta ya ɗaure ta
kira number Surry tana ɗagawa ta ce "Surry kina ina?" Ta ce "Gidan surukanki mana"
ta ce "Ina son ganinki yanzu pls" Surry ta ce "Rite away Maa" hanging up na kirar
sukai, bata tashi a wajan ba sai wajan 9 sbd ciwon da kanta yake mata sosai, tayi
wanka tare da Alwala sai a lokacin tayi sallar Subhi kana ta shirya cikin fitted
gown na atamfa Holand blue and white tayi mata kyau, duk abinda take bata jin daɗin
ranta, gudun kada zuciyarta ya buga da abin da bata shirya gani ba ta nemi waje ta
zauna tana chat a wayarta. 12:45 daidai ya shiga sakkowa daga upstairs ɗin sanye da
Ash ɗin shadda shampoo sai ɗaukan idanu take ya ɗora hula jaddara hannunsa a baya
nutsuwarsa ta bayyana shekarunsa a fili ya dinga bin main parlour ɗin da kallo jin
shiru ba motsin kowa sai ƙamshin dake fitowa ba tare da yasan daga ina bane.
Fita ya yi zuwa Masjid ɗin dake unguwar a lokacin kuma wata black ɗin mota ta shigo
gidan, bai bi takan motar ba ya shige abinsa, Dr A'isha da Surry suka dinga kallon
Yaa Sheikh har sai da Surry ta ce "Wannan kallon fa Dr" Dr A'isha ta ce "Na rasa
wanne kyau Yaa Lee ke da shi, Ummul nada kyau haka grandparents nasa, but shi ɗin
kamar ruwa biyu ne" Surry ta ce
"Kin san Fulani nada kyau amma ko? Kuma ita kanta Ummul banji asali bahaushiya ce,
ni nutsuwa da kwarjinin shi ke hanani nutsuwa idan yana waje" Dr A'isha ta rufe
idanu tana sauke nauyin ta ce "let's go in"
Fitowa suka yi tare da shiga ciki, gabaɗaya suka zauna a main parlour Surry ta
ɗauki wayarta ta shiga kiran number Zahrah tana ɗagawa ta ce "Ina parlour" ta
ajjiye wayar tana bin parlourn da kallo ko'ina birgeta yake, an narka dukiya wacce
baki ba zai taɓa iya faɗa ba.
Babu jimawa ta fito tana rangaji ganin Dr A'isha kuma yasa tayi turus sai kuma ta
zauna tana faɗin "Wlcm" Surry ta ce "Sannu Amaryar Yaa Sheikh, na ɗauka yau ai ba
zamu samu ganinki ba sbd soyayya"
Zahrah ta ce "Uhm wacce soyayya nayi kwanan baƙin ciki" Surry ta ce "Subuhanallah,
bar faɗa" ta ce "Bari kawai, can you imagine a gabana yarinyar nan ke rungome Yaa
Sheikh tana faɗin wai ya cije ta ji nayi zuciyata ta buga ƙirjina ya fara zafi"
Surry ta dinga dry tana riƙe ciki ta ce "What funny, bar raina Allura, ƙarfe ce
wallahi"
Kafin suyi magana Halisa ta fito hannunta riƙe da waya, ta kallesu sau ɗaya ta
marairaice fuska ta ce "Habibi ƙalbi sai kace baƙi akai shiyasa ka tafi lambu,
bari nazo musha lambun soyayya" ta cire wayar ta ɗora a baki tare da manna kiss ta
ce
"Mu'ah Uban ƴaƴana ga ƴar rainonka nan, ƴar filloka kuma matarka nan zuwa" ta kashe
wayar shi dai Yaa Sheikh jinta kawai yake ya kasa fahimtar maganganun nata. Halisa
tayi murnar ta ce "Ashe baƙi mukai har haka?" Surry ta ce "Uwar gida ykk?" Ta ce
"Ni lafiya nake sai dai Antyna Zahrah kin san ita ce amarya ita ce on duty maybe
tasha jiki, kin san Mijina or Surry ba rago bane ya san ta kan soyayya" Zahrah tayi
murmushi ta ce "haka ne ƙanwata domin na tabbatar da ƙwarewar shi a jiya" Halisa ta
miƙe tsaye tana gyara zaman duguwar rigar Jikinta ta buba farin lace lace da White
ɗin flowers, rigar ta zauna mata sosai ga ƴar ƙaramar necklace ɗin wuyanta tayi
kyau sosai ta ce "Point of correction Anty a gidan Yaa Sheikh dai nice babba kin
san uwar gida, ki faɗa mishi ya mance gajeren wandon shi akan bed ɗin jiya bari
naje" tana faɗin hakan tayi gaba Surry ta ce "Wannan yarinya zata iya kashe aure ji
magana kamar ana karanta mata?" Zahrah ta ce
"Idan kissa ce aini babarta ce a wajan, mu zuba mu gani" Halisa na fitowa wata
haɗaɗɗiyar farar mota na shigowa sai ɗaukan idanu take, motar na shigowa wasu
motoci guda biyu suka shigo ya zamana baƙin motocin huɗu ne a gidan harda tasu
Surry.
Halisa ta ƙarasa inda Yaa Sheikh tana murmushi ta ce "Yallaɓai" ya dubeta tare da
murmushi wani mutum ya fito daga motar ya ce "The car key" ya amsa tare da jinjina
kai alamar godiya, El-bashir da ya yi driving su Dada ya ce.
"Abba sabuwar mota kayi ko ni ka siyawa? Wannan motar latest car ce bata jima da
zuwa ba" Yaa Sheikh ya shafa gemunsa a taushashe cikin yanayi na riƙe kansa ya ce
"Prince guda a siya masa mota?" El ya ce "Please mana Abba wlh nayi broke" Ya juya
ya kalli Halisa da take da kallon motar ya kama hannunta tare da damƙa mata key ɗin
daidai kunnenta ba tare dasu Dada da mother sun ji ba ya ce "For you Wife, Hadda
Alkur'ani gift" Maimoon dake laɓe ta buga tsalle ta ce "Yaa Lee Anty Halisa ka
siyawa mota" Ya jinjina kai Maimoon ta buga tsalle ta ce "Wow it's expensive"
hawaye ya cika idanun Halisa ta kasa cewa komai, ta kalli motar ta kalli Abbanta ta
kalli su Mother, Maimoon tai cikin gida tana kwallawa Dr A'isha kira da Zahrah akan
su fito Yaa Sheikh ya siyawa Halisa mota, Halisa ta fashe da kuka ta faɗa jikinsa
tana cewa "Thank you Habibi ƙalbi... Thank..." Ta kasa maganar sai kuka, Mother ta
ce "Allah ya sa albarka" Dada murmushi kawai tayi tare da yin cikin gidan, El kuma
kamar ya zauce sbd haɗuwar motar sai taɓawa yake, ganin ba kowa wajan yasa Yaa
Sheikh yayi holding nata back tare da kissing hannunta ya damƙi hannunta ya ɗora
daidai ƙirjinsa dake harbawa wajan saitin zuciyar shi a hankali ya yi mata raɗa ya
ce "Na baki wannan" ya nuna zuciya ya ce "Virgin gift to my lovely wife, i have
never thank you before, Jazakallah-bil khair I will never forget that day, ranar da
ki kai mayar da tuzurun Ummul rangaɗeɗan ango.....
[2/2, 8:26 PM] Abk: Ta ɓoye fuskarta sbd kunya while hawaye da kuka na sake cin
ƙarfinta, Ita kam a yanzu mene ya rage mata banda cikawa da imani da rabuwa da
iyaye lafiya, duk wata Soyayyar miji ta samu. Ya saka hannu ya ɗago kanta data ɓoye
a ƙirjin shi ya tsareta da fararen idanunsa masu sauya mata tunani cikin ƙasa da
murya ya ce.
"Ƴar fillo? Meye?"
Ta sunkuyar da kanta ƙasa idan tace a yanzu bata jin nauyin Yaa Sheikh tayi ƙarya
sbd kullum cikar zati da haibarsa ƙaruwa take ga wata tarin kamala da Ilhama na
cikakken nutsatssen mutum mai tarin ilimin Addini.
Muryarta na rawa ta ce
"Thank you Abba, Allah ya saka da alheri ya ƙara arziƙi da wadata, ya baka halak a
kullum ya rabaka da haramun cikin dukiyarka, Allah ya bamu zuri'a mai albarka masu
kulawa damu kamar yadda ka kula da rayuwata"
Tunda ta fara magana ya harɗe hannu a ƙirji ya zuba mata idanu, har ranshi yaji
daɗin addu'arta ya kuma ya bawa tunaninta, wanda a zamanin yanzu ba ko wacce mace
take tsayawa ta yiwa mijinta addu'a kamar haka ba, wasu babu haka ma a lissafin
tunaninsu. Ya lumshe idanunsa yana shaƙar iskar dake tashi a wajan take tahowa da
ƙamshin Jikinta, rufe idon ya bata damar ƙare masa kallo sosai, sai yanzu ta ƙara
gasgatawa Yaa Sheikh ya fita kyau nesa ba kusa ba, shi ɗin cikakken Bafullatani ne,
sbd gabaɗaya dangin mahaifinsa Fulanin Yola ne na Usuli kuma Makiyaya, Fari tas
farin da kai tsaye ya shige na Fulani yafi kama dana _Half-caste_ ƙwayar idanunsa
ba nrml ɓaka bace ba kuma za a ce mata Brown ba, ko ace Blue kamar ta turawa,
sauyin ƙwayar idanunsa ya sanya kallon shi ya zama wani irin wanda yafi kama da
romantic, He has a round face, da saje wanda ya kewaye and a long beard irin gemun
nan mai tsayi na Manyan malamai, labɓansa jajir suke sbd yawan taune su da yake da
kuma tea ɗin da yake sha ko liquid abu, hancinsa siriri kuma dugo, sumar kansa
yalwataciyyace kamar wacce ya sanya mata dayin sbd rabuwa da tayi kala biyu daga
tsakiya zuwa goshinsa tai baƙi sosai sai ƙyalli take, daga tsakiya zuwa wuya kuma
tayi jaa yawancin jikinsa gargasa ce, ga ƙirjinsa mai faɗi kamar yana ɗaga ƙarfe
kullum yana da tsayi sosai but his ears are big suna da faɗi. Ya saka hannu ya
zungureta tayi saurin ɗauke kai tana sauke numfashi ya ce.
"Kin wani tisani a gaba"
Ta kwaɓe fuska ta ce "to me zan yi bayan ka cika zuciyata da farin ciki"
Sai kuma ta ƙara sakin kuka hadda na shagwaɓa da zarar zai kalli Idanunta sai ta
ɗauke kai ya kamota gabaɗaya tunda har lokacin El yana can yana duba motar Halisa,
ya bata side hug tare da ɗora hannunsa a kafaɗarta ya ce
"Dodo na zama?" Ta girgiza kai ta ce "Wallahi Abba haka kurum kunyarka nake ji" ya
saka hannu ya dungure mata kai yana girgiza kansa a taushashe ya ce
"Allahumma yaá hadiki Zawja" tayi dariya shi kuma ya ɗaga kiran Abba Hakimi tare
da nufar mota ya juya ya ganta

55 / 66