Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 21

24K to 27K   out of 61.8K words

wa
sauran kamfanunuwan da suke yin harkar.

Har wayar ta katse baiyi picking ba wani kiran ya k'ara shigowa, k'aramin tsaki yaja dan duk hankalinshi
ya tafi ga gine ginen yanaso ya tantance wanda zaifi k'ayatarwa idan aka gina, hannu yakai ya d'auko
wayar dake ajiye bisa table d'in kusa da tashi system d'in ya duba mai kiran yaga Aleeyu ne, picked up
yayi yayi yakai kunnenshi batare dayace komi ba jin an d'aga yasa Aleeyu yace

"Yallab'ai yarinyar nan fa batada lafiya nazo na sameta kwance tana ta rawar d'ari da alamu tana jin jiki
gaskiya".

Haka nan yaji gabanshi ya d'an fad'i ya dake tareda fad'in

"Tun yaushe?".

"Yanzu dai dana dawo kawo mata kayan dakace a siyo mata na sameta a haka". Aleeyu ya amsa masa.
So yake ya cewa Aleeyun ya samu Dr ya dubata ayi mata duk abinda ya dace amma saiyaji ya kasa
fad'ar hakan yaji yanaso ya ganta yaga halin datake ciki dan haka ya tsinci kanshi da fad'in

"Okay I'm coming".

Yana sauke wayar daga kunnenshi yaga Mujaheed ya k'ura masa ido yana kallonshi, yasha mur sosai
yana bankawa Mujaheed d'in harara yace

"Kallon na meye?".

Tsaki Mujaheed yaja yace

"Uban me zan kalla a jikinka kai ba mace ba?".

Gira ya d'age yace

"Shiyasa ai naga ka tsura min ido saikace wani maye".

"Mayu dai ba maye ba". Mujaheed yace yana hararar shi, bai k'ara magana ba sai mik'ewa tsaye dayayi
ya d'auki wayoyinshi yasa d'aya a aljihun wandonshi d'ayar kuma ya rike a hannunshi yana k'ok'arin ture
kujerar dayake kai baya.

"Ban gane bafa wai ina zakaje ne haka?".

"Inda ake zuwa". amsar daya bashi kenan yana k'arasawa wajen shelf dan ajiye wasu files daya d'auka
kan table d'in.

"Kutt amma ka rainamin hankali ma wallahi ina zaman zamana a office ina aikina ka tasoni kace lallai
lallai inzo in nuna maka tsarin gine ginen zaka zab'a shine kuma zaka tashi lokaci d'aya kace fita zakayi
bak'in halin kama baisa kayi budurwa ba bare inyi tunanin itace tayi maka wannan kiran urgently haka".

Tsaki kawai Habeeb yayi, Mujaheed yace

"To yanzu maganar da muke fa?".

"Please MJ ka k'yaleni haka mana banason hayaniya by 8pm ka sameni a gida mu k'arasa okay?".

"Ai ba bawa ka aje ba da zan bika har gida". cewar Mujaheed yana rufe system d'in gabanshi, k'ofar fita
Habeeb ya nufa yana fad'in

"Ok check your account shi zaiyi maka bayani".

Da sauri Mujaheed ya mik'e yana fad'in

"Ah haba Dude kar muyi haka dakai mana ka rik'emin salary ai akwai matsala mugu duk wani salon
mugunta ka sanshi, wai gidan uwar wa zakaje ne?".

Bai tanka masa ba ya fice yana cewa idan ya gama tsayuwar ya rufo masa office d'in.
"Mtwss ALLAH ya shirya ka mutum saikace aljani". yayi maganar yana d'aukar system d'in ya fita ya rufe
office d'in lokacin har Habeeb ya shiga lifter, shikuma ta elevator yabi zuwa 2nd floor inda nashi office
d'in yake.



Wani Dr'n daban yasamu ba Dr Huzaifah ba tunda shi na gida ne bayaso kuma kowa yasani har zuwa
lokacin dazai sallame ta.

Aleeyu na zaune kan sofa Habeeb da Dr Ameer suka shiga bedroom d'in, har lokacin tana kwance a
k'asan saidai ta daina rawar sanyin da alamu tasamu barci ne.

Bai zauna a bedroom d'in ba saiya koma falo ya zauna bayan ya k'ara jaddadawa Dr Ameer ya tabbatar
yayi mata duk abinda ya dace.

Yana nan zaune a falon yana aikin danne danne a waya Aleeyu ya fito daga bedroom d'in bai d'aga kai
ya kalleshi ba ya cigaba da abinda yake, gefenshi Aleeyu ya tsaya ya d'an rissina yace

"Yallab'ai sai kazo fa daga kusa tun d'azu Dr yakeso yayi mata allura tak'i yarda shine yace a kirawo ka".

Bai tankawa Aleeyun ba haka kuma bai daina latsa wayar ba ganin haka Aleeyu yakoma bedroom d'in
yasan bazaiyi maganar ba.

Sai bayan shud'ewar wasu y'an mintuna sannan ya tashi ya nufi bedroom d'in bayan ya k'ara tamke
fuskarshi yadda bazata kawo masa wargi ba.

Sab'anin da datake kwance a k'asa yanzu akan gado ya hangeta a zaune hawaye kawai ke ziraro mata ta
mak'ure waje d'aya jikinta sai rawa yake.

"Yawwa Mr Habeeb gara da kazo ai tun fitarka nake fama da ita wallahi taki yarda ayi mata injection".
Dr Ameer ya fad'a bayan shigar Habeeb d'akin.

Tana ganinshi ta k'ara matsawa can jikin fuskar gadon tana k'ara curewa waje d'aya haka ma rawar da
jikinta yake ta k'aru saboda ganin shi datayi.

A hankali cikin takunshi na k'asaita da zallar mazantaka ya nufi wajen gadon ya had'e gabas da yamma
tamkar baisan wani abu dariya ba ya nutsar da idanunshi cikin nata wanda hakan ya k'ara mata mutuwar
jiki.

"An gaya miki wasa mukazo yine anan? allura kawai kinzo kina b'atawa mutane lokaci gyara ayi miki ko
in b'ata miki rai yanzun nan".

Duk da tsoron shi datake bala'in ji hakan bai hanata fara yimasa magiya ba da fad'in ita batason allura a
k'yaleta kawai dan ALLAH".

Idanunshi ya d'an lumshe kad'an yana cije baki ya nemi gefen gadon ya zauna ya kalli Dr Ameer yace
"Yi aikin ka".

"Dan ALLAH balarabe kayi hak'uri". tayi maganar cikin kuka tana kallon Habeeb daya d'ora d'aya kan
d'aya yana girgizasu, da sauri Aleeyu ya juyar da kanshi yana matse dariyar data taho masa jin sunan da
Seeyamah ta kira Boss dashi, shima Dr Ameer d'in sai daya d'an dara kafin ya matsa daf da Seeyamahn
ya rank'wafa yana fad'in ta janye hijabin ta nad'e hannun rigar ta.

"Dan ALLAH kayi masa magana balarabe kar yayi min allura banaso wllhy". ta k'ara fad'a cikin wani
kukan, a fusace ya juya ya kalleta yace

"I will slap u idan kika k'ara kirana da wani balarabe". yayi maganar yana maka mata harara kafin kuma
ya juyo gaba d'ayanshi ya fuskance ta ya cigaba da fad'in

"Ta bud'e ayi mata ko ranta ya b'aci yanzun".

Haka nan dole ta yaye hijab d'in ta shiga tattare dogon hannun doguwar rigar dake jikinta gashi ya kafa
mata ido ba yadda za'ayi tayi masa musu tana ji tana kallo Dr Ameer yayi mata allurar, y'ar siririyar k'ara
tasaki bayan shigar allurar jikinta kafin ta fashe da wani kukan tareda saka kanta tsakiyar gwiwar ta.

Kallonta kawai yake shi gaba d'aya ma he's totally speechless ganin yadda take wannan uban kukan
daga yin allura (d'an rainin wayo shima fa tsoron allurar yake nasan kun tuna lokacin da akayi masa tashi
allurar 🤣 kula ne kawai basuyi ba amma lokacin da Dr Ameer ya tsira mata sai daya runtse idonshi gam
yanajin tamkar shi aka tsirawa Lol).

Drugs Dr Ameer ya rubuta mata ya mik'awa Habeeb paper, daga nan yayi musu sallama bayan Habeeb
yayi masa sallama mai kyau danshi kanshi baisan nawa ya damk'o ya bashi ba aikuwa ya fita yana ta
faman washe baki da fad'in gobe da safe zai dawo za'a k'ara yimata wata allurar hakan dataji yasa ta
k'ara sautin kukan ta, a rayuwar ta ta tsani allura tablet ko guda nawa ne zata iya sha amma allura kam
basa shiri, bazata manta ba duk lokacin da batada lafiya indai za'a yimata allura tofa ranar kowa sai yaji
kanta dan sai an taru kanta.

Paper ya mik'awa Aleeyu dawasu kud'i daya k'ara d'aukowa, karb'a Aleeyu yayi sannan yayi hanyar fita
bedroom d'in duk da baiyi magana ba yasan abinda yake nufi ( jigila ta sameka Aleeyu 🤧).

Shiru d'akin ya k'ara d'auka sai sautin kukan Seeyamah dake tashi kad'an kad'an wanda yafara sawa
Habeeb ciwon kai, k'aramin tsaki yaja a karo kusan na hud'u kenan kafin cikin dakakkiyar murya yace

"Shut up ur mouth".

Da k'yar ta had'iye kukanta cikin ranta tana k'ara jin tsanar mutumin duk inda azzalumi yake to wannan
bawan ALLAHn yakai ya daketa kuma ya hanata kuka ALLAH ba azzalumin bayinsa bane saiyayi mata
sakayya akan wannan zaluncin da akayi mata batasan hawa ba batasan sauka ba batasan laifin datayi ba
amma ya rabota da y'an uwanta ya kawota wani waje daban bazata gaji dakai kukanta wajen sarki
ALLAH ba.
Daga k'arshe ma tashi yayi ya fita daga bedroom d'in, nan kan kujera ya zube yana jiran dawowar
Aleeyu ya dafe kanshi da hannayenshi duka biyun.



Sai bayan sallah idan Allah ya nuna mana da rai da lafiya hop za'aci nama a hankali 😅.



Mrs Salees Mu'az 💝




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.



HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)



Alhmdulillah! I'm back ina yiwa kowa fatan alkhairi tareda fatan anyi sallah lafiya ubangiji ya amshi
ibadunmu Amin. I'm so sorry na rashin update babban uzuri ne ya rik'eni zamu cigaba da yardar ALLAH
sai a dinga hak'uri da yanayin yadda posting zai dinga zuwa harkar mai iyali sai a hankali, duk lokacin dai
dana samu time zanyi bakin k'ok'arina wajen yin typing.

Nagode! 1luv my dearest fans jazakumullahu khair.💝



No 17.



Yana nan zaune yana faman tufka da warwara a cikin zuciyarshi har zuwa lokacin da Aleeyu ya dawo
gidan hannunshi rik'e da wata leda mai tambarin sunan wani pharmacy wanda ledar kawai zaka kalla ya
tabbatar maka da babban pharmacy ne.

"Sir ga drugs d'in an siyo". yaji maganar Aleeyu cikin kanshi wanda ya katse masa tunanin dayake sai
sak'e sak'e yake cikin ranshi tausayin yarinyar yanaso ya rinjayesa saidai bazai bari tafaru bazata bar
gidan nan ba har saita fad'a masa alak'arshi da ita data sawa rayuwar shi ido kuma take zuwa masa cikin
barcinshi.

Kamar bazai d'ago ba dan yafi mintuna biyar bai d'ago kai ya kalli Aleeyun ba wanda yake tsaye yana
jiran umarnin ogan nashi, tsaye ya mik'e key d'in motarshi kawai ya karb'a ya wuce yana fad'in

"Kaje ka bata tasha".

"Ok Sir". Aleeyu yace yana nufar hanyar bedroom d'in.

"Ka tabbatar taci abinci before tasha maganin". Habeeb ya fad'a yana ficewa daga falon yaja k'ofar.

Shi yaso ya shiga yabata maganin da kanshi amma saiyaji ya kasa bashida wannan k'warin gwiwar haka
nan kukanta ke masa ciwo cikin ranshi kuma yasan tana can tana aikin yinshi dan haka kawai ya zab'i fita
daga gidan gaba d'aya.

Ba k'aramin fama Aleeyu yasha da Seeyamah ba kafin yasamu taci abincin tasha maganin dan saidaya
ciro wayarshi yace zai kira Habeeb dama yace idan tayi masa gardama ya kirashi sai sannan ta d'an
tsakuri abincin tana kuka tasha maganin takoma ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya irin wadda tasha kuka
ta k'oshi yaushe zata yarda ya kira mata wannan mutumin bala'in tsoron shi takeji tun daga lokacin
dayasa aka d'auko ta ta cireshi daga cikin jerin masu tausayi da imani.

Shima Aleeyun ajiyar zuciyan yasaki tareda girgiza kai sannan ya fita daga bedroom d'in yaja k'ofar.



★________________★

Y'an sanda sun fara bincike kan b'atan yarinyar da gidan marayu suka kai musu report amma har
lokacin basu samu abinda sukeso ba saidai sun tsananta bincike da fatan samun nasara.

Wani daga cikin shugabannin gidan marayun ne ya kawo shawarar ya kamata sukai cigiya kafafen
sadarwa ko ALLAH zaisa a dace, hakan kuwa akayi sunkai gidajen radio da talabijin nan ma suka bada
hotonta a gidajen talabijin d'in da suka kai cigiyar.



Duk yadda Mujaheed ya dinga tambayar Habeeb ina yaje ya fita cikin gaggawa haka yak'i kulashi
k'arshe ma zagi ya auna masa yace ya k'yaleshi kar ya dameshi Mujaheed yayi k'wafa ya fita ya rufo
k'ofar da k'arfi shima yana zaginshi da kallo kawai ya bishi tsaki yaja yayi baya yayi relaxing sosai kan
kujerar idanunshi a lumshe yana jujjuyawa.

Gaba d'aya yinin ranar bai hasala wani abin kirki ba duk da yadda yaso yayi aikin kuwa, kasa hak'uri
yayi saidaya kira Aleeyu yaji ya jikin nata ya tabbatar masa da taji sauk'i yanzu ma ya shiga ya dubata sai
a lokacin hankalin shi ya d'an kwanta yasamu nutsuwa.
Haka yinin ranar yazo ya wuce bazaice ga wani muhimmin aiki d'aya dayayi a office ba a ranar, da wuri
ma yabar kamfanin yatafi gida batare daya nemi Mujaheed ba duk dayaso su k'ark'are aikin dasuka fara
d'azu saboda yanaso yayi magana da wad'anda yabawa kwangilar aikin ginin kamfanin da za'a fara dole
zai nemi Mujaheed d'in ko zuwa dare ne su k'arasa.

Yaso biyawa ta lamid'o crescent yaga halin da yarinyar take ciki saikuma ya fasa kai tsaye ya wuce gida.



★★★________★★★

Bayan magreebah.

Kwance yake akan doguwar kujera dake falon nashi yana sanye da farin wando 3quater mai aljihuna
gaba da bayan wandon sai k'aramar riga ta shan iska ash color, wani sassayan k'amshi ne yake tashi tako
ina a jikinshi da kuma falon wanda aka k'ure A.C hakan yasa falon ya d'auki uban sanyi kamar k'ank'ara
kuma ba abinda ya dameshi ga kayan jikinshi bawasu na kirki ba. tamfatsetsiyar wayarshi ce a hannunshi
yana latse latse ya hard'e k'afafunshi daga kwancen dayake, number Mujaheed ya lalubo ya danna masa
kira jinsa shiru har yanzu baizo ba saidai yana kira akace masa line busy alamun waya yake tsaki yayi ya
kashe ya k'ara dialing still dai akace masa akan waya yake wani tsakin ya k'ara ja ya yanke kiran yana
tunanin ko da uban wa yake waya? Saida aka d'an d'ebi wasu y'an mintuna sannan ya k'ara trying
number cikin sa'a ta shiga bata dad'e tana ringing ba Mujaheed yayi picking bakinshi d'auke da sallama
ko amsa sallamar baiyiba yace

"Da uwar wa kake waya ne wai tun d'azu?".

"Ah ban ganeba an fad'a maka kowa ma irinka ne idan akaji kana waya kan business ne bawata y'ar
soyayya da nishad'in nan irin na zamani da y'an mata".

"Mtwss! An fad'a maka kowa ma bashida aikin yi irinka? dallah malam kazo ina jiranka karka b'atamin
lokaci". Bai jira abinda Mujaheed yake fad'a ba yayi hang up yana fad'in

"Useless man kawai wazai b'ata lokacin shi wajen yin wata soyayya salon yara su rainaka ai shi ko
soyayyar zaiyi bazaiyi da k'aramar yarinya ba sai wadda ta amsa sunanta na mace ta mallaki hankalin
kanta I thought ma sa'ar shi koma wadda ta girmeshi zai aura hankalinshi kwance amma auren k'aramar
yarinya ba abinda yake janyowa illah raini da zubar da girma shikuma duk abinda zai zubar masa da
girmanshi baya shiri dashi.

Bayan sun gama waya da Mujaheed ya kira Aleeyu ya k'ara jin lafiyar Seeyamah, saidaya k'ara jan
kunnenshi kan ya k'ara kula da ita sosai kuma kar yayi saken dazata gudu sannan ya kashe wayar yana
tuna kukanta na d'azu da yadda take kiranshi da balarabe sai yanzu abin ya bashi dariya amma dayake
ba gwanin yinta bane murmushin gefen baki kawai ya saki yana cije lips d'inshi na k'asa.

Bayan wani d'an lokaci Mujaheed ya iso gidan wajen Ummi ya fara shiga dan su gaisa, suna zaune a
k'ayataccen falon nasu wanda ke tashin k'amshin turarukan wuta na asalin larabawa suna kallon tashar
Aljazeerah Ummi da Neehlah, yana shiga idanunshi suka sauka kan Neehlah datake zaune kan kujerar
dake facing d'in k'ofar falon suka had'a ido dashi wani k'ayataccen murmushi suka sakarwa junansu ya
matuk'ar yimata kyau cikin bak'in wandon jeans da farar riga long sleeve da bak'in agogon fata dake
d'aure a tsintsiyar hannunshi, kamar yadda shima tayi masa kyau ainun cikin shigarta material ne bak'i
da adon golden na fulawoyi a jikinshi riga da siket kasancewar ta fara yasa yayi bala'in haskata ido ya
kashe mata tayi saurin sadda kanta k'asa tana murmushi gamida addu'ar ALLAH yasa Ummi bata ganshi
ba Mujaheed bashi data ido wlhy, Kai tsaye wajen Ummi ya nufa ya zauna k'asan k'afafunta yana
gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar shi mutanen gida ya amsa mata da

"Lafiyar su k'alau sunce a gaisheta". ya ida maganar yana satar kallon Neehlah wadda itama daidai
lokacin ta d'ago kanta ya kasheta da wani irin kallo dayasa duk ta daburce cikin y'ar rawar murya wadda
ta had'u da siririyar muryar ta tace

"Yah Mujaheed ina yini".

"Lafiya k'alau k'anwata ya kike?". Yace yana murmushi bayan ya d'ago kai yana kallonta.

"Alhmdulillah". Kawai tace ta tashi tabar falon kafin Ummi ta ramfo su duk da hankalin Ummin ma dai
yana kan TV, da idanunshi ya rakata da kallo har ta shige ya daina ganinta ajiyar zuciya ya saki ya mik'e
tsaye yayiwa Ummi sallama ya fita.

Yana dosa kai falon Habeeb wani uban sanyi yayi masa maraba sallama yayi ya shiga har lokacin
Habeeb na kwance saidai sab'anin d'azu da wayace a hannunshi yanzu wata y'ar madaidaiciyar laptop ce
apple daya d'orata kan cinyarshi yana sarrafa ta, ciki ciki ya amsa sallamar Mujaheed batare daya juyo ya
kalleshi ba.

Jakar hannunshi ya ajiye wadda shima system d'inshi take ciki ya d'auki remote control na air
conditioner d'in ya rageta sosai ya daidaita sanyin yadda baiyi yawa ba kuma baiyi kad'an ba, sai a
lokacin Habeeb ya juyo ya kalleshi cikin had'e rai yace

"Malam meye haka wai?".

"Kamar ya?". Mujaheed yace yana zama kujerar dake fuskantar wadda Habeeb d'in yake kwance, zaune
ya tashi yana b'ata rai yace

"Ya daga zuwanka zaka canzamin tsarin yadda nakeson d'akina ya kasance".

"Kowa ma mahaukaci ne irinka? in banda hauka taya zaka dinga bankawa kanka sanyi haka ko tsoron
pneumonia bakayi saboda tsabar bakada hankali wautar d'an fari na d'awainiya dakai".

Wata uwar harara Habeeb ya jefawa Mujaheed yace

"Banason iskanci, d'akinka ko nawa, inada right d'in inyi duk abinda nakeso a ciki ba matsalarka bace".

Baki Mujaheed ya tab'e yana d'age kafad'a yace
"To kabari inbar d'akin idan ma cikin k'ank'ara zaka shiga Gashua k'arewar sanyi kanada damar yin haka
amma yanzu kam saidai kayi hak'uri".

Kai Habeeb ya kad'a yana sakin k'wafa ya daidaita zaman system d'in ya cigaba da dannawa batare
daya k'ara kallon sashen da Mujaheed yake ba.

"Naga alamun baka lallab'a lafiyar ka ko?". yaji Mujaheed ya k'ara fad'a, banza yayi masa bai tanka
shiba, baki Mujaheed ya k'ara tab'ewa ya janyo jakar dayazo da ita ya ciro tashi system d'in ya tashi ya
koma kusa da Habeeb d'in ya zauna ya d'auke system d'in dake kan cinyar Habeeb ya d'orata kan wani
center table na glass daga gefenshi ya juyo yana fad'in

"Malam ka maida hankalinka kan aikin daya kawoni inyi in tafi tsabar jaraba irin taka daren ma bazaka
hak'ura ba kana min bak'in cikin huawar da zanyi kayi hak'urin goben shine bazaka iyaba". Habeeb
yanajin Mujaheed yanata faman mita k'ala baice masa ba idan ya biye ta Mujaheed sai sun zama kamar
zararru shiyasa wani lokacin yake masa banza yayi yagama.

Dolenshi ya maida hankalinshi kan abinda zasuyi d'in tunda shiya matsawa Mujaheed d'in saiyazo gaba
d'ayansu suka maida hankali Mujaheed ya cigaba da nuna masa tataccen speech kawai ke tashi a wajen
har zuwa lokacin da suka kammala suka tsaida mgn.




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)



No 18.



Rufe system d'in Mujaheed yayi bayan sun kammala ya ajiyeta kusa data Habeeb, zamanshi ya gyara

9 / 21