Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 21

42K to 45K   out of 61.8K words

baka mamaki Aleeyu very stupid".
Dole tasa Aleeyu yaja bakinshi ya tsuke ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana jiran jin abinda zai biyo baya
yasan dai ya riga ya rasa aikinsa duk da dai baisan laifin dayayi ba tunda har lokacin baisan cewa
Mujaheed yazo gidan ba kawai dai yayi tsammanin gano shi ɗin da akayi ya ɗauke yarinyar ne ya ɓata
masa rai haka.

Tana zaune daga ƙasan gadon kan rug ɗin dake shimfiɗe a ƙasa ta cusa kanta tsakanin gwiwoyinta duk
da dai ba kuka take ba, jin an buɗe ƙofa an shigo yasa ta ɗago kanta da sauri ta kalli bakin ƙofar tayi arba
da Mujaheed da kuma wata mata wadda kallo ɗaya tayi mata taga tsantsar kamannin su da wanda ya
ƙwamuso ta, tsaye ta miƙe da sauri tana cigaba da kallonsu har suka ƙaraso inda take hannuwanta Ummi
ta riƙo suka tsirawa juna ido kafin Ummi ta janyota jikinta ta rungume ta tsam a jikinta tamkar ta santa,
wani irin kuka Seeyamah ta saki wanda tun farkon zuwanta gidan rabon datayi irin shi. Patting ɗin
bayanta Ummi ta shiga yi cikin tsananin tausayinta lokaci ɗaya wata soyayyar yarinyar da ƙaunarta na
ratsata, Mujaheed yana gefe sai kallonsu yake yana murmushi cikin farin ciki.

Ɗago ta Ummi tayi tasa hannu tana share mata hawaye da faɗin

"I'm sorry daga yau kukan ki ya ƙare yarinya kisa a ranki kin samu UWA nikuma daga yau na samu ƳA
insha ALLAH muna tare har abada". Wani kukan ne ya ƙara tahowa Seeyamah ta ƙara faɗawa jikin Ummi
tana kukan, murmushi Ummi tayi ta kalli Mujaheed tace

"Mujaheed mu tafi kasan orphanage house ɗin ko?".

"Eh Ummi na sani". Mujaheed ya bata amsa

"Okay let's go". tace tana maida Seeyamah gefenta na dama ta rungume ta Mujaheed yayi gaba sukabi
bayansa Seeyamah na maƙale jikin Ummi kamar wani zai rabasu.

Har lokacin Habeeb da Aleeyu na tsaye cikin falon su Ummi suka fito, sosai gaban Seeyamah ya faɗi
lokacin data ga Habeeb dan batayi tsammanin tare suke ba a tsorace ta ƙara shigewa jikin Ummi shi
kuma ya bita da wani mugun kallo wanda yasa ta ƙara tsorata tayi hanzarin sadda kanta ƙasa, har sukaje
bakin ƙofar fita daga falon Habeeb bai biyosu ba kuma bashida niyyar biyo ɗin jira yake su Ummi su fita
ya yiwa Aleeyu rashin mutunci juyowa Ummi tayi ta kalleshi sai data harareshi kafin cikin faɗa tace

"Tsayuwar me kake a nan?".

Baice komai ba ya nufi ƙofa, kallon Aleeyu tayi wanda tun ɗazu ya kasa ɗagowa ya haɗa ido da kowa
Ummi tace

"Kaima mai tayashi ɗin ba tsayawa zakayi ba tahowa zakayi mu tafi tare muji dalilin dayasa kuka
aikatawa baiwar ALLAH wannan abin kai da maigidan naka". Bata saurari cewar shi ba ta fice Aleeyu yabi
bayanta jikinsa duk a sanyaye.

Mujaheed ne mai driving ɗin Habeeb na gefenshi sai cika yake yana batsewa fuskar nan tamkar an aiko
masa da saƙon mutuwa ba alamun rahma sam, Mujaheed yana so yayi dariya yana tsoro dan yasan wllhy
a yadda yake ɗin nan tsaf zai iya kai masa duka shi yadda ya haɗe ran nema ya bashi dariya.
Ummi, Seeyamah da Aleeyu sune zaune a back seat Seeyamah ta kwantar da kanta kan kafaɗar Ummi
jefi jefi tana sakin ajiyar zuciya motar shiru ko tari ba wanda yayi a ciki kowa da saƙe saƙen dayake a
ransa da haka har suka ƙarasa orphanage house ɗin su Seeyamah, kallo ɗaya zaka yiwa Seeyamah ka
hango zallar farin ciki da murnar datake ciki wanda har ya bayyana kan kyakkyawar fuskarta sai
murmushi take saki ba tareda ita kanta tasan tanayi ɗin ba.

Tunda mutanen gidan suka ƙyalla ido sukaga Seeyamah gidan ya ruɗe ya kacame da murna da ƙyar
suka yakice wani daga cikin ƴan gidan marayun yayi musu iso zuwa babban office ɗin gidan, gaba
ɗayansu suka shiga nan da nan aka sanar da dawowar Seeyamah sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci office ɗin
ya cika da mutane maza da mata kowa cikeda farin ciki da murnar ganin Seeyamah ta dawo cikin ƙoshin
lafiya ba abinda ya sameta.

Bayan ƴan gaishe gaishe da akayi da Ummi da sauran mutanen ɗakin sannan Ummi ta fara rattabo
musu yadda al'amarin ya kasance tayi da hausa ta haɗa da turanci saboda yanayin hausar tata.

Tashi tayi ta nufi inda Habeeb yake tsaye tun shigowar su yaƙi zama ma gaba ɗaya sai faman muzurai
yake daga tsaye saikace soja, hannunsa ta kamo ta kaishi har gaban shugaban gidan marayun Alhaji
Abubakar Imam ta damƙa hannun Habeeb ɗin a na Alhaji Abubakar Imam ɗin tace

"Wannan ɗana ne dana haifa da cikina kuma a yanzu zan damƙa muku shi a hannunku kuna da damar
da zaku kai ƙarar shi gaba abi muku haƙƙin ku a kanshi nidai na fita duk hukuncin da kuka yanke daidai
ne". Kowa baki ya buɗe cikin ofishin cikeda mamakin karamci da dattaku irin na matar nan lallai su
Ummi basuda yawa a zamanin nan, Habeeb kam wani ƙululun abune ya tokare masa ƙirjinsa ganin
abinda Ummi take masa tamkar bata sonsa huci kawai yake fitarwa yana ɗan lumshe ido tsabar yadda
ranshi ya ɓaci.

Murmushi Alhaji Abubakar yayi yace

"Naji daɗi sosai Hajiya kuma samun irinku a wannan zamanin da gaskiya tayi ƙaranci sai an tona madalla
da samun uwa kamar ki wannan abu da kikayi yasa naji na yafewa yaronki tunda alhmdulillah Seeyamah
ta dawo hannunmu cikin ƙoshin lafiya ba abinda ya sameta babban burin mu kenan kulawa da amanar
da ALLAH ya bamu mun gode sosai ALLAH ya saka da alkhairi".

Kai Ummi ta kaɗa tana murmushi tace

"Jazakallah khair nagode sosai nima sai abu na gaba inaso insa hannu zan ɗauki Seeyamah daga gidan
nan daga yau nayi alƙawarin bazata ƙara kukan rashin mahaifa ba insha ALLAH kun yarda zaku bani?".

Kabbara ƴan ɗakin suka ɗauka cikeda farin ciki.

"Masha ALLAH masha ALLAH, ubangiji ya faranta miki kamar yadda kika faranta mana mun gode sosai
ALLAH ya ƙara girma da sutura yayiwa zuri'ar ki albarka". maganganun da suka dinga tashi kenan cikin
office ɗin kowa yana yiwa Ummi addu'ar gamawa lafiya.
"Zo nan ƴata". Ummi tace fuskarta ɗauke da mayalwacin murmushi tareda miƙawa Seeyamah hannu,
cikin sassarfa Seeyamah ta taho ta faɗa jikin Ummin tana sakin wani kuka mai taɓa zuciyar mai sauraro
cikin shashsheƙar kuka Seeyamah tace

"Nagode Hajiya".

Ɗagota Ummi tayi ta girgiza mata kai tana murmushi tace

"Daga yau da sunan uwa zaki kirani sunan da kowane ɗa yake kiran mahaifiyarsa dashi ki kirani da
Ummi kamar yadda yarana na cikina suke kirana dashi".

"Nagode UMMI". Seeyamah tace cikin wani kukan tana ƙara faɗawa jikin Ummi ta matseta tsam itama
tana goge ƙwallar data taho mata, duk ɗakin saiya rikice kowa ka gani fuskar shi ɗauke da murmushi na
jin daɗi.

Ogah Habeeb kam yana tsaye ba wanda ya ƙara bi ta kanshi, shikenan yanzu yarinyar nan ta koma
gidansu da zama? wani irin kallo zata dinga yimasa kenan? shidai angama dashi kawai....



Manage please👏🏻




Maryam Ibraheem Aleeyu

Mrs Salees Mu'az 💝




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).
No 27.



Wata takarda aka bawa Ummi tayi signing bayan sun ƙara tattaunawa tsakanin Ummi da Alhaji
Abubakar Imam daga nan aka rakosu har bakin motar su sukayi musu sallama, suna ta ƙara jaddada
godiyarsu ga Ummi, rungume juna Seeyamah da aminanta Fadeelah da Khairat sukayi suna kukan
rabuwa sosai suke jin rabuwar da zasuyi tana taɓa zuciyar su tun suna yara suke tare a yadda suka samu
labari ma kusan rana ɗaya aka kawo su gidan sunyi matuƙar shaƙuwa tare suke yin komai ba abinda yake
rabasu gashi yau rana ɗaya za'a rabasu, Ummi ce ta ƙarasa wajen cikin tausaya wa take rarrashin su da
faɗin sunada damar zuwa a duk lokacin da suka so ganinta suje gidan ƙofar ta a buɗe take, da rarrashi
dai da ban baki tasamu sukayi shiru.

Duk abin nan da ake Habeeb yana kallon su ta cikin glass ɗin motar dan tun fitowar su ya shige mota ba
tareda daya kula kowa ba, ta ciki yake kallon kowa ɗaiɗai yana ayyana abubuwa da dama a cikin ranshi.
Idanu ya lumshe yana sakin tsaki lokacin dayaga Ummi tana rarrashin su Seeyamah har yanzu abinda ya
faru bai daina ɗaure masa kai ba daki daki yake tuno komai daga lokacin dayasa aka ɗauke yarinyar da
zaman datayi a gidan shi ƙarƙashin kulawar Aleeyu zuwa yanzu da komai ya bayyana har gashi Ummi ta
ɗauki nauyin kulawa da ita a yanzu, numfashi ya sauke mai nauyi yana ƙara jan wani tsakin ganin har
lokacin ba wanda yazo ya shiga motar da niyyar tafiya ya rasa me suke tattaunawa tun ɗazu haka, da
zaman ya ishe shi saiya zaro wayarshi daga aljihu ya shiga latse latse.

Sai zuwa can sannan su Ummi suka shigo motar bai kula kowa ba kamar yadda ba wanda ya kulashi, sai
bayan sun hau kan titi ne ya kula akwai wata ƙaramar mota dake bin bayansu ko tantama bayayi daga
gidan marayun ne aka biyo bayan su dan aga mazaunin Seeyamahn a yanzu, ƙarfi da yaji dai Ummi ta
ƙara musu yawan ƴan gidan.

Suna yin parking ya fice daga motar ya nufi side ɗinshi Mujaheed yaso yabi bayan shi yayi masa magana
Ummi ta dakatar dashi.

Har cikin gidan Ummi tayi musu jagora suka shiga daga nan suka ɗan ƙara tattaunawa tareda ƙara
damƙa amanar Seeyamah a hannun Ummi ta ƙara jaddada musu ta karɓa da hannu bibbiyu saidai fatan
ALLAH ya tayata ruƙo. Daga nan sukayi mata sallama har cikin compound ɗin inda motar su take Ummi
ta rakosu har suka tada motar suka fita daga gidan su Ummi na tsaye itada Mujaheed da Seeyamah da
itama tayi musu rakiya.

Sam Ummi bata lura da Aleeyu dake cikin compound ɗin ba sai lokacin da suke shirin komawa cikin
gidan, yana tsaye kusa da wata fulawa kanshi a sunkuye tunanin shi ɗaya haɗuwa da Habeeb shikenan
yasan ƙarshen aikinsa yazo gashi da shine yake taimakawa iyayenshi da ƴan uwansa saboda shi kansa ya
sani Habeeb yana masa biya mai kyau kuɗin dayake bashi yafi na aikinsa Habeeb mai yawan alkhairi ne
hakan yasa yake jin daɗin aiki dashi kuma yake samun abinda zai taimakawa iyayenshi a wadace, yayi
karatu sosai inda har yayi degree ɗinshi na
"Mujaheed kira min yaron can". Ummi tace tana kallon Mujaheed, amsawa yayi sannan ya nufi inda
Aleeyu yake tsaye har ya ƙarasa bai sani ba sai daya dafa kafaɗarshi sannan ya zabura ya kalli wanda ya
taɓa shi ɗin yaga Mujaheed ne tsaye duk sai yaji kunya ta kamashi dukansu kunyar su yake ji a halin
yanzu.

"Barka dai yallaɓai". yayi maganar a rarrabe yana ƙara yin ƙasa da kanshi.

"Barka dai, muje Ummi tana son ganinka". Mujaheed yace yana yin gaba ba tare daya tsaya jin amsar
shiba, shikenan ta faru ta ƙare Aleeyu ya ayyana cikin ranshi yana bin bayan Mujaheed.

Rissinawa yayi yana gaida Ummi bayan ƙarasawar su amsawa Ummi tayi ba yabo ba fallasa tana ƙare
masa kallo a girme ma zai girmewa Habeeb amma saboda yanada kuɗi ya zama shine babban sai abinda
yace masa yake aiwatarwa, sai data gyara tsayuwar ta sannan tace

"Yanzu yaro abinda kayi ka aikata daidai kenan? meyasa ka biyewa sakarcin Abbuna kuka aikata
wannan mummunan aikin? a shekarun ka kaine ya kamata ace ka saitashi a hanya idan kaga yana shirin
yin ba daidai ba

'Kutt bala'i Gashuan ne zai yarda Aleeyu ya shiga sha'anin shi har yayi masa gyara? ai koni sai nayi da
gaske sai anci uban juna kafin a daidaita dama ni kaɗai ne nake ɗan iyawa dashi'. Mujaheed ne yayi
maganar cikin zuciyarshi yana kaɗa kai wani murmushi na suɓuce masa kan fuskarsa cigaba Ummi tayi
da faɗin

"Kun taɓa tunanin halin da kuka jefata itada ƴan uwanta wani irin tashin hankali suka shiga kun taɓa
tunanin wannan? kai kawai Aleeyu yake jijjigawa yana ƙara yin dana sani kan abinda ya aikata.

"Ayi haƙuri Hajiya nayi nasan nayi ba daidai ba ayi min afwah insha ALLAH hakan bazata ƙara faruwa
ba". Wani nannauyan numfashi Ummi ta sauke kafin tace

"Shikenan ya wuce ALLAH ya yafe mana gaba ɗaya a kiyaye dan ALLAH a dinga kuma auna abu a
mizanin hankali kafin a aiwatar dashi".

"Insha ALLAH Hajiya nagode sosai ALLAH ya saka da alkhairi ya ƙara girma".

Duk da Ameen suka amsa Ummi tace

"Bayan wannan aikin da kake a ƙarƙashin Abbuna akwai wani aiki daban dakake yine?". Kai Aleeyu ya
girgiza yace

"Bana yin komai Hajiya kasancewar ogah mai yawan alkhairi ne koyaushe cikin miƙawa yake hakan yasa
banyi yunƙurin neman wani aikin ba tunda abinda yake biyana dashi yana isata harkokin rayuwarta".

"To daga yau zaka bar aiki a ƙarƙashin shi.....ido Aleeyu ya runtse cikin faɗuwar gaba dama yasan sai
anyi haka

"Meye matakin karatun ka?". yaji Ummi ta tambaye shi, idanunsa ya buɗe yace
"Nayi har degree biyu duk akan business na nemi aiki ban samuba hakan yasa lokacin dana samu
labarin mai kamfanin H.I.A GASHUA yana neman ma'aikata wanda zasu zama bodyguard ɗinshi nazo
kuma cikin sa'a nasamu aikin".

Kai Ummi ta jinjina tace

"Shikenan zamuyi magana da Alhaji Sulaiman kawun yaran nan ya saka cikin harkar kasuwancin amma
yanzu dai kaje gida ka ƙyale Abbuna".

Sosai Aleeyu ya shiga zuba godiya a wajen Ummi dayi mata addu'a, har suka suka bar wajen itada
Seeyamah, Mujaheed ya dafa kafaɗarshi yana faɗin

"Ya isa haka Malam Aleeyu yanzu dai muje kabawa Boss ɗin naka haƙuri yau an haɗa masa zafi
dayawa".

"Anya yallaɓai zan iya tunkarar ogah a yanzu kuwa?". cewar Aleeyu.

"Ba damuwa muje gara ayita a ƙare ai yadda kasan kuturu haka yake wajen zuciya shegen". Dariya ce ta
kufcewa Aleeyu shima Mujaheed ɗin dariyar yayi yana nufar part ɗin Habeeb Aleeyu ya mara masa baya.

Kamar koyaushe falon banda sanyi ba abinda yake fitarwa ya ƙure A.C sai bankawa kanshi sanyi yake,
can suka hangoshi kan kujera ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya sai girgizasu yake sarai yaji an shigo ɗin amma
yaƙi ɗagowa yaga waye duk da dai yasan bazai wuce Mujaheed ba.

Ƙarasawa inda yake sukayi Mujaheed ya zauna kusa dashi Aleeyu kuma gefe yasamu ya zauna kan
tattausan carpet ɗin dake malale a wajen.

"Ranka ya daɗe ga Aleeyu nan na kawo zai baka haƙuri bisa sakaci dayayi na amanar daka damƙa masa
har Mujaheed yayi nasarar shiga gidan yaga abinda ake ɓoyewa a ciki". Mujaheed yayi maganar yana
ƙunshe dariyar dake cinsa.

"I'm so sorry Boss banyi hakan dan na ɓata maka ba forgive me dan ALLAH". Aleeyu yace yana haɗe
hannayen shi guri ɗaya alamun roƙo.

"Get out from my room". yace yana wani lumshe ido na ɓacin rai.

"Dan ALLAH ka......."I said get out". Habeeb ya katse Aleeyu cikin tsawa wanda dole tasa Aleeyun yaja
bakinshi ya tsuke.

"Kaga Aleeyu tashi kaje abinka rabu dashi ni banga ma laifin dakayi ba da har kake ta wani binshi kana
bashi haƙuri ya daɗe bai haƙuran ba dan ubanshi tashi kaje". tashi Aleeyu yayi ya fita daga falon bayan
ya yiwa Mujaheed sallama yana ta mamakin yadda Mujaheed ɗin yake zagin Habeeb ɗin kai tsaye batare
da wani shayin komai ba.

Baki Mujaheed ya buɗe zaiyi magana a fusace Habeeb yace
"Ka sake kai min magana ubanka zanci wllhy ɗan iska mara mutunci". ya ƙarasa maganar yana komawa
bayan kujerar yayi relaxing yana cigaba da kaɗa ƙafa sai huci yake yana cije baki, baki Mujaheed ya
hangame yana kallonshi kafin yayi murmushi yace

"Duk naji na kuma gode da zagin da kayi min amma ka sani Gashua banyi hakan dan in ɓata maka ba
nayi hakane dan in ceto ka daga halakar dakake shirin faɗawa a ciki I'm sorry to say kai......."Dan zaka
faɗawa Ummi? meyasa ka sakota cikin maganar? meyasa bazaka sameni muyi magana dakai ba kasa
mahaifiyata tana fushi dani why Mujaheed?". duk sai Mujaheed ɗin yaji jikinsa yayi sanyi amma har a
lokacin baiji wai abinda yayi ba daidai bane yanzu ba gashi ta sanadin hakan ba Ummi ɗauki yarinyar,
murmushi ya ɗan saki kafin yace

"Gashua bakada fahimtar da zamu zauna muyi magana dakai ta fahimta a tsakanina dakai kai ɗin wani
irin mutum ne mai wuyar sha'ani wanda ake rasa gane hagunshi da damanshi dole tasa na samu Ummi
da maganar saboda kai ɗin ba zaka fahimce ni ba....."Kazo ka sameni dan muyi magana kaga naƙi
fahimtar ka? maganar banza kawai kake". ya katse Mujaheed a fusace, dariya Mujaheed yayi yace

"Haba ɗan balarabe yau nafara saninka? kokuma yau nafara zama dakai? Ummi ce kawai zance zata fini
sanin halayyar ka saboda ita takawo ka duniyar close the chapter now tambaya ɗaya gareni yanzu
meyasa ka ɗauke Seeyamah wane laifi tayi maka? a ina ma ka santa da har tayi maka laifin da zaka yanke
mata irin wannan hukuncin? Please answer me".

Wani banzan kallo Habeeb ya jefa masa yace

"Zaka iya shaƙeni sai in faɗa maka mara mutunci". sosai Mujaheed ya ƙyalƙyale da dariya yace

"Kaji ba in ance maka bauɗaɗɗen mutum kace ba haka ba any way nidai nayi abinda ya dace kar ALLAH
yasa ka faɗa min abinda ya haɗaku muna zaune a shararren waje zamuji koma menene I'm sorry fa da
marukan da Ummi ta daddalla maka ta sanadina ga fuskar nan har yanzu bata washe ba wllhy ta ƙara ja
sos.....hannu Habeeb ya dunƙule yana miƙewa tsaye da niyyar kaiwa Mujaheed dukan da saiya kusa
sumar dashi ganin haka yasa Mujaheed ɗin yayi hanzarin tashi yabar falon da gudu yana dariya.

Tsaye Habeeb yayi yabi bayan Mujaheed ɗin da kallo, Mujaheed yana masa abinda yaga dama ba
wanda yake faɗa masa magana son ranshi irin Mujaheed saikuma Muhseen daya biyo bayanshi.

Juyawa yayi ya shiga bedroom ɗinshi ya cire kayan jikinsa ya shiga bathroom, yana tsaye saitin shower
ruwa na tsiyaya a jikinshi ya zama dole yazo yafara bincike kan yaran nan dayake tunanin su ɗin triplets
ne....



Afwan da kaɗan👏🏻.



Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu'az 💝



*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).



No 28.



Duk abinda ake sam Neehlah batada masaniya kwananta biyu bata gidan tana gidan Aunt Mashhoodah
data damu Ummi da waya tana roƙon ta Neehlah taje ta mata ko kwana biyu ne sai a yau ne ranar da
Seeyamah tadawo gidan itama daf da magreebah driver'n Aunt Mashhoodahn yadawo da ita, lokacin
Ummi da Seeyamah na zaune a falo Ummi na ɗan bata tarihinsu a taƙaice tareda nuna mata ta saki
jikinta duk abinda takeso tayi magana.

"Oyoyo Umminah nadawo". muryar Neehlah ta karaɗe falon tun kafin shigowar ta, murmushi kawai
Ummi tayi tareda girgiza kai itama Seeyamahn murmushin tayi tasamu labarin ta yanzun nan a wajen
Ummi, tsaye tayi tana bin Seeyamah da kallo bayan ta shigo falon tana tunanin abinda ya kawo
Jawaheer Mansoor Jiƙamshi gidansu to

15 / 21