Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   21 / 21

60K to 61.8K   out of 61.8K words

Aunt Ramlah take ta fara tayata aikin datake ita Heedayah breakfast ta haɗa
musu itakuma Aunt Ramlah tana harhaɗa kayan dambun da zatayi da zoɓo da zatayi mata so take ta
kammala da wuri dayake da wuri ma Uncle Muhammad ɗin ya fita yau saboda wasu kayansu da suka
ƙaraso a ranar ko breakfast ma bai tsaya yiba ya fita.

Tare sukayi dambun da Heedayah mai rai da lafiya dayaji kayan lambu dan ma dai ta fahimci Hajiyan ba
komai take so ba ta haɗa mata haɗaɗɗen zoɓo mai daɗi tasa mata komai a wani basket madaidaici aka
rufe da wani farin ƙyalle suka gyara kitchen ɗin dan Aunt Ramlah ko ƴar aiki batada ita duk da Uncle
Muhammad yaso a samo mata tace a'a bataso har wani gagarumin aiki ne a gidan da sai an nemo wata
mai aiki? kuma shi aikin datake ai shine rabauta da samun ladan auren dan haka ita bata buƙatar ƴar aiki
ALLAH ya hore mata lafiya ta cigaba da ɗawainiya da hidimar gidanta.

Wanka Heedayah ta shiga bayan sun kammala komai, bayan ta fito ta shafa cream ɗin da suke using
dashi sama sama tayi kwalliyar ta kamar yadda ta saba kullum powder, lipstick sai kwalli datake zizarawa
a fararen idanunta. Doguwar riga ta ɗauko ta atamfa sau ɗaya ma suka taɓa sakata itada Zainab Uncle
Muhammad ya kawo musu ita tare, coffee color ce atamfar da ratsin baƙi da milk daga sama ta kamata
sosai ta fito da halittar ƙirjinta sosai daga ƙugun ta kuma zuwa ƙasa ta buɗe sosai tayi mata matuƙar
kyau ta maƙala ƙaramar barima a kunnenta ta ɗaura baƙin agogon fata ɗaurin ture kaga tsiya tayi na
malaha medium size ɗin gyale coffee tayi rolling dashi ta rataya baƙar jaka ta zura plat shoes black ta
fesa turare. Masha ALLAH kalmar dana ambata kenan lokacin data gama shiryawa tayi kyau sosai Uncle
Muhammad yana ƙoƙari sosai a kansu kuma baya nuna bambanci tsakanin ta da ƙanwarsa a matsayin su
na ƴan University da suke shiga cikin jama'a yana ƙoƙarin yaga sun shiga mutane tsaf tsaf haka ne ma
Aunt Ramlah tana yawan siya musu kayan makeup a matsayin su na ƴan mata dan ma dai ita kwalliyar
bata dameta ba wannan sai Zainab ita ce ƴar kwalliya.

Fita tayi bata samu Aunt Ramlah a falo ba dan haka ta wuce bedroom ɗinta itama a bakin mirror ta
sameta tana shafa mai tayi wani wankan murmushi tayi tace

"Masha ALLAH kinga yadda kikayi kyau kuwa autar Umma".

"Kai Aunt ina wani kyau anan? nida ba kwalliya nake ba?".

"Kwalliya ai ba ita ce kyau ba Heedayah ke kyan a jikinki yake ALLAH yasa a dace a dawo mana da
suruki". Ta ƙarasa maganar tana dariya gami da rufe robar man data gama shafawa kan mirror ɗin, baki
Heedayah ta tura tace

"A'a nikam Aunt Ramlah ni gaskiya karatu zanyi yanzu na fasa auren".

"Lallai kiyi ta kanki yarinya Baba bazai zuba miki ido kiyi wannan dogon karatun ba bakiga ni iya
secondary ma akayi min aure ba kema sa'a kika ci kawai ALLAH dai ya zaɓa mafi alkhairi". Bata amsa ba
sai cewa datayi

"Zan tafi Aunt".

1k Aunt Ramlah ta ciro a purse ɗinta ta miƙa mata ta karɓa ta fita tana yi mata sallama Nusrah dake kan
bed itada Nu'aym yana mata wasa sai ɗaɗɗaga mata hannu take tanaso ta ɗauke ta kissing ɗin
kumatunta kawai tayi ta fita tana dariya Aunt Ramlah na bada saƙon gaisuwa wajen Hajiya, kitchen ta
shiga ta ɗauki kwandon ta fita taja ƙofar falon.

Tana fita titi tasamu napep ta shiga zuwa unguwar su Hajiya.

Ƙarfe ɗaya da kusan rabi ta shiga gidan side ɗin Alhaji Sulaiman ta fara shiga suka gaisa bata iya zuwa
bata shiga sun gaisa da Hajiya Rahma ba saboda mutuncin ta itafa tana tunanin gadon mutunci familyn
sukayi nunar rana ne kawai bashida mutunci (Ba ruwan Mero ). 😃

Da sallama ta shiga falon Hajiya na zaune tasha kwalliyar ta cikin haɗaɗɗiyar atamfa da gani mai tsada
ce taci ɗaurinta Irin na tsaffi sai ƙamshin turaren wuta falon yake wa'azi take kalla a Sunnah TV daga
bakin Shiek Abdallah Usman Gadon ƙaya, murna sosai ta bayyana kan fuskar Hajiya tana amsa sallamar
lokacin da Heedayah ta shiga ita har mamaki abin ya bata lallai ba ƙaramin so ƴar tsohuwar take mata
ba, kusa da ita ta zauna bayan ta ajiye basket ɗin cikin dariya Hajiya tace

"Ah lallai Ramlatu ta cika alƙawari ai da baki zoba da kaina zanzo har gidan nayi biko".

"Haba dai Hajiya". Tace tana murmushi tareda saukowa har ƙasa tana gaisheta ta amsa cikin sakin fuska
da jin daɗi tana tambayar Aunt Ramlah da yara ta amsa mata da lafiya itama tace a gaisheta daga nan ta
gabatar mata da saƙon Aunt Ramlah irin farin cikin da Hajiya ta nuna tamkar ranar aka fara kawo mata
taji daɗi sosai ta shiga godiya tanasa mata albarka tace ta kai mata kitchen ai yau abincin ranar ta kenan
da dare ma shi zataci abinta Heedayah na dariya ta ɗauki kwandon ta nufi kitchen ta ajiye ta dawo suka
cigaba da hirarsu da Hajiya.

"Nikam Hajiya ba kunun gyaɗa ne a gidan nan yau Aunt Ramlah na tsamiya tace a dama nikuma kinsan
na gyaɗa ne mutumina". Heedayah ta faɗa tana kallon Hajiya.

"Kin taki sa'a kuwa yau shi Larai ta dama mana yana nan a kitchen da zafinshi kije ki zubo".

"Yauwa Hajiya bari inje in zuba". ta faɗa tana miƙewa tsaye ta nufi kitchen ɗin, itama Hajiya ganin
lokacin sallahr zuhr yayi ta tashi ta wuce bedroom ɗinta dan gabatar da farali.

Hajiya na shiga bedroom ɗin shikuma ya shigo falon, sanye yake cikin ƙananan kaya dark ash ɗin trouser
da red color ɗin riga mai dogayen hannuwa ya matse ƙugunshi da baƙar belt ta kamfanin D&G ƙafarshi
sanye cikin baƙin takalmi cover writs watch ɗin shi ma baƙi ne na fata sumar kan nan tasha gyara sai
ƙyalli take zubawa, tunda ya falon ƙamshin jikinshi ya doke wanda falon yake yi ada nashi ya mamaye ko
ina zama yayi ya ɗauki waya ya fara latse latse. Jin alamun motsi a kitchen yayi tunanin Hajiyan ce a ciki
dan haka ya tashi kanshi tsaye ya nufi hanyar kitchen ɗin yana ƙoƙarin cusa wayarshi cikin aljihu, ta kawo
kai kenan zata fito da madaidaicin mug da spoon a ciki wanda ta haɗa kunun gyaɗar a ciki dayasha
madara a daidai lokacin shikuma ya kawo kai zai shiga kitchen ɗin sukayi wani mugun karo saboda ba
wanda ya kula da tahowar ɗan uwansa goshinta ya bugi ƙirjinshi mug ɗin hannunta yayi kamar zai faɗi
hakan yaba damar abinda ke cikin shi yayi uban fallatsi sai a jikin rigar Gashua da nata gaban rigar, a
gigice ta zaro ido tana ja baya ganin wanda ke gabanta yana bin rigar jikinshi da kallo data gama ɓaci
cikin ƙyanƙyami da ɓacin rai mara misali ɗagowa yayi dan ganin wace shashashar yarinya ce wannan
idanunshi ya sauka cikin na Heedayah datayi tsamo tsamo jikinta na ɗan ɓari har lokacin bata gama
dawowa daidai ba dan ba ƙaramin tsorata tayi ba musamman ganin wanda sukayi gwaren dashi, wani
mugun kallo mai haɗe da harara ya jefa mata kafin ya nufi inda take tsaye baya ta shiga ja tana girgiza
masa kai kamar zatayi kuka shikuma ya cigaba da binta fuskar nan ba alamun rahma sam a samanta tana
ja baya yana ƙara kusanto ta har lokacin data kai jikin luckers ɗin kitchen ɗin ta yadda ba damar ta ɗara
nan da can dole tayi surrender ta tsaya tana dafe baki sai zazzare idanuwa take irin na marasa gaskiya da
alamu tsautsayi ne dama ya kawota gidan nan.

Daf da ita ya tsaya kamar zai haɗe jikinshi da nata ya tara mata hannu yana kallon mug ɗin hannunta
alamun ta bashi, cikin rawar hannu ta miƙa masa ya karɓa ya ajiye shi can gefe ya juyo yana ƙara
matsawa jikinta ba abinda take gani sai shi yama ɗora hannayen shi duka biyun kan luckers ɗin gefe da
gefenta yayi mata rumfa yayi kane kane tako ina bata da hanyar guduwa bare tayi tunanin zillewa ta
gudu fatan ta da roƙon ta a lokacin ALLAH ya jefo da Hajiya kitchen ɗin ta ceceta dan da gaske kallon
mara imani take wa mutumin......



Alhmdulillah Masha ALLAH.

A nan nakawo ƙarshen littafi na ɗaya ina roƙon ALLAH ya yafe min kuskuren danayi a cikinsa.
_*Shin su waye iyayen waɗannan triplets ɗin ne?*_

*_Meye silar rabuwar su da iyayensu?_*

*_Meye zai biyo baya bayan gano asalin nasu?_*

_*Shin ta wace hanya ake gano real parents ɗinsu? Habeeb Gashua ne yake yin nasarar hakan ko kuwa
dai ta wata hanya ce daban ake ganowar?*_

_*A cikin triplets ɗin nan wace take nasarar ƙwamushe zuciyar Mr. HABEEB IBRAHEEM AHMAD
GASHUA?*_

_*Shin cika bakin ma dayake na bazaiyi soyayya da masu ƙananan shekaru ba hakan zai yi tasiri a kansa?
*_

*_Wace babbar gudunmawa Ummi ke bayarwa a haɗuwar su Seeyamah da danginsu?_*

*_A cikinsu wacece take folawa GASHUA taji duk duniya bata gwani sai shi?_*

_*Duk waɗannan tarin tambayoyi dama wasu da kuke hasasowa duk amsoshin su suna cikin EL
HABEEB 💥 Book two*_



*A yayin tafiya taci karo da wata mahaukaciya wadda ta bigeta da mota wadda dalilin haka ta dawo da
ita gidanta da zama dan nema mata magani, makarin asirin da akayi mata yana jikin yaran wadda da
zarar sun haɗa ido zata samu lafiya shin wacece wannan mahaukaciyar? waye kuma ya tsinceta? an
samu nasarar kallon juna cikin gaggawa ta yadda asirin zaibar jikin matar ko kuwa saida aka ɗauki wani
lokaci? Amsa tana cikin littafin EL HABEEB 💥 Book two*

Karku bari a baku labari tafiyar ta musamman ce takun na daban ne salon mai ƙayatarwa ne ta yadda ba
zakuyi dana sani ba💃💃💃.



_Na fara samun complain sosai daga reader's masu yawa saboda jin yadda nace bazan fara sakin book
two ba saina kammala typing ɗinshi sun matsu suji yadda labarin zai kai ƙarshe, so maganar gaskiya
banason ƙorafi kuma banaso in karɓi haƙƙin mutane inzo ina musu delaying wajen yin posting ba ba daɗi
tafiyar da rayuwar mu ba'a hannun mu yake ba uzururruka suna iya faɗowa mutum ako wane lokaci
batare daya shirya hakan ba shi yasa tun farko na yanke shawarar yin hakan idan na kammala sai in
sanar da account ɗin da za'a turo kuɗin ta yadda za'a dinga samun update kullum kamar hakan zaifi
amma inaso inji ra'ayoyin ku akan hakan duk da dai da wuya in sauka daga kan nawa🫣🤪 ku kanku sai
kunfi jin daɗin hakan ba maganar sai nayi typing zan turo saidai inyi editing kawai in sambaɗo muku
kunsan idan book ya ɗauko hanya ba'a son jira amma dai duk shawarar dana yanke zan sanar daku
ALLAH ya iya mana yasa mudace dan arziƙin Annabi 👏👏👏._
*Masu son a tallata musu hajar su ta yadda zasu samu nasarar samun customer cikin sauƙi zasu iya
tuntuɓar wannan number* 09139964697.



Akwai paid book ɗina guda biyu

_KALLON KITSE_

_WATA SOYAYYA_

Da sauran daɗaɗan littattafan mu na ƙungiyar HASKE WRITER'S ASSOCIATION 💡 waɗanda suka riga suka
kammala kaɗan ne daga ciki ba'a ƙarasa ba cikin sauƙi da rahusa kuyi magana ta wannan number dake
sama kunsan dai haziƙan marubutan da aka tara a cikin ta ba zakuyi dana sanin zuba kuɗi ku ba😍.



*EL HABEEB 💥🔥🔥🔥 Book two for paid 300 only ALLAH ya bada ikon siya da amfanuwa da darasin dake
ciki*.



Maryam Ibraheem Aleeyu

Mrs Salees Mu'az 💝

(Ummee).

09139964697.

21 / 21