Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 21

30K to 33K   out of 61.8K words

Afwan idan nasamu dama gobe zakuga update idan akaji shiru kuma sai zuwa jibi insha ALLAH idan
muna da rai da lafiya, ku cigaba da bina wasan yanzu aka fara 🤸🤸karku manta da comments and share.



Masu buk'atar a tallata musu hajarsu zasu iya nemana ta wannan number

09139964697.



Jummah Kareem 💝



Maryam Ibraheem

Mrs Salees Mu'az 💝



Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk
wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun
mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda
kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm
yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga
glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn
new soap dinne,😯
😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya
maida kudi gida

You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:3k

maiso yy mgn

08062991549

07046881166

07067210195

Call 08062991549



Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai 11k



Munaturawa Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free



Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).



No 20.



Aunt Ramlah tana komawa bedroom d'inta ta iske tarin miss call na jama'a y'an uwa da k'awayenta
wad'anda suka san Heedayah ciki har dana Hajiya Inna tana cikin dubawa wani kiran Hajiyan ya k'ara
shigowa, ta d'aga kiran tana kaiwa kunnenta a rud'e Hajiya ke tambayar ta ina Heedayah idan ta fahimta
dai itama Hajiyan taga abinda ya faru a labarai kai wannan abu da mugun d'aure kai yake.

"Hajiya yanzu suka tashi daga falo suka koma bedroom itada Zainab".

Ajiyar zuciya Hajiya Inna ta saki kafin tace

"Alhmdulillah! sai yanzu hankalina ya kwanta wllhy tun d'azu ina cikin alhini da tarin mamaki naga an
haska wata yarinya a talabijin wai an saceta basuda maraba da Heedayah komai iri d'aya shine na kiraki
inji kan labarin".

Zama Aunt Ramlah ta gyara tasan dai ko giyar wake tasha bata isa ta bayyana sirrin dayayi shekara da
shekaru a rufe ba ta ina zata fara fad'in Heedayahn 'YAR TSUNTUWA ce? sirrin da iyayenta ma basu
tonashi ba wace ita da zata bankad'a shi? murmush ta d'anyi tace

"Wllhy muma mun gani Hajiya munyi mamaki sosai amma Heedayah lafiyar ta k'alau yanzu suka gama
karatu a falo suka tashi".

"Ikon ALLAH, to masha ALLAH ubangiji ya k'ara kiyayewa itakuma waccan ALLAH ya bayyana ta cikin
k'oshin lafiya".

"Amin Amin". Aunt Ramlah ta amsa mata, har sukayi sallama Hajiya bata daina jinjina maganar ba ita
kanta Aunt Ramlahn har lokacin mamaki bai gama sakinta ba, suna gama waya da Hajiya kiran Maman
Ilham wannan k'awar tata wadda ta tab'a aiken Heedayah da Zainab gurinta wadda anan suka had'u da
Habeeb ta kirata, itama d'in dai tambayar ta Heedayah tayi amsar dai data bawa Hajiya itama ita ta bata
itama tana ta mamaki.

A wannan dare Alhaji Mansur Jik'amshi, Hajiya Saudah da Aunt Ramlah sun sha amsa wayoyin jama'a
da dama kowa da irin tambayar dayake rattabo musu har wani lokacin ma su rasa amsar bayarwa.

Jawaheer kam cikin kwanciyar hankali tasha barcinta sam ta manta ma da wata maganar Fauziyyah
datayi mata a ganinta idan banda k'arya taya za'a ce anga wata da basuda bambanci da ita ko twins ai
kafin kaga masu kama d'aya aikine saidai kowa da kamarshi sai ita za'a wani ce anga irinta shirme kenan.

Ta b'angaren Heedayah ma duk juyin da zatayi cikin barcinta sai fuskar data gani d'azu a TV ta fad'o
mata sam batayi wani cikakken barci ba sai wajen asubah shima kuma baiyi wani nisa ba aka kira sallah
dolenta ta tashi barci cikeda idanunta sukayi alwalah sukayi sallah kuma ba damar komawa tunda su
suke aikin gidan gaba d'aya kafin su tafi school musamman yau da suke da lecture by 7@m.

A gurguje sukayi breakfast sannan suka tafi da Uncle Muhammad zai saukesu a school d'in dayake yau
ya fito da wuri da alama akwai inda zaije.

Ta cikin mirror Uncle Muhammad yake k'ara k'arewa Heedayah kallo har sai data tsargu, so yake yaga
meye bambancin su da yarinyar jiya amma ya kasa ganowa dole ya maida hankalinshi kan driving d'in
dayake tunda shidai bazai iya fad'ar abu d'aya wanda Heedayah take dashi waccan yarinyar bata dashi
ba, zuwa yanzu ya k'ara tabbatarwa lallai Heedayah twins ne wani abu ya rabasu to meye abinda ya
rabasu d'in? itace tambayar da kowa bai saniba.

Gaba d'aya Heedayah saidata tsargu tayi dana sanin zuwan nata school d'inma saboda yadda ake
faman kallonta tamkar wadda tayi wani abin kunya duk tasan hakan kuma yanada alak'a da abinda kowa
yagani jiya idan baka gani a TV ba zaka gani a waya, farko ma cewa tayi gida zata tafi Zainab ta hanata
kuma ba wanda ya tunkareta yayi mata magana saidai nunata da ake tayi da hannu duk inda suka wuce
ana binta da kallo maza da mata gaba d'aya abin ya isheta tamkar ta tsala ihu duk saita dabarbance
tafiyar ma taso gagararta hannunta Zainab ta kama suka shige Hall d'in da zasu gabatar da lecture su ta
ranar anan d'inma dai bata tsira ba dan wasu ma kasa hak'uri sukayi saida sukayi mata magana ta rasa
amsar da zata basu, harda masu cewa wai yaushe aka ganta? surutai dai iri iri anata maida magana har
zuwa lokacin da Dr Naseer Sufi ya shigo Hall d'in hakan yasa akayi shiru kowa ya nemi wajen zama ya
shiga gabatar da abinda ya kawoshi.

Sai 8:30a@ sannan aka gama, Dr Naseer Sufi yana shirin fita daga Hall d'in class rep d'insu ya d'aga
hannu da fad'in

"Sir". tsayawa yayi ya juyo yana kallon mai maganar, tashi class rep d'in yayi ya isa inda yake k'asa k'asa
ya d'anyi masa magana kafin ya nuno desk d'in da Heedayah take zaune itada Zainab gabanta fad'uwa
kawai yake ta sunkuyar da kanta k'asa amma Dr Naseer Sufi yace ta d'ago kanta dole haka ta d'ago tana
kallonshi, ido ya k'ura mata sosai yana kad'a kai kafin kuma ya fice daga Hall d'in gaba d'aya wasu daga
cikin student's suka rufa masa baya.

Tuni idanunta suka ciko da k'walla ta kalli Zainab tana fad'in

"Na shiga uku Zainab dana sani banzo school d'in nan ba yau kiga fa yadda ake faman nuna ni ana
magana ta ga Dr Sufi ya ganni yanzu ya fita yana girgiza kai me hakan ke nufi?".

"Please calm down mana Heedayah meye abin d'aga hankali a ciki wai? tambaya cefa kawai da amsa
kece wance? a'a bani bace finish kuma mutane ma da suke ta wannan shirmen inace an rubuta sunan
yarinyar da ake nema Seeyamah ce ko Sawwamah na manta duk wannan shegen Nura Ahmad (class rep)
d'inne yaja ai".

Heedayah ta bud'e baki zatayi magana kenan akazo aka kirata wai ana nemanta a office d'in VC, ido ta
zaro tana kallon Zainab, Zainab bata bari tayi magana ba ta tashi ta kama hannunta suka fita daga Hall
d'in.

Sai data rakata har wajen office d'in VC sannan ta tsaya tace ta shiga ita kad'ai.

Da sallama ta shiga office d'in, tunda ta shigo yake kallonta yanaso yaga bambancin su da yarinyar jiya
daya gani a labarai amma shidai baiga wani abu d'aya dazaice ya bambanta su ba. Guri ya nuna mata ta
zauna ta sunkuyar da kanta k'asa cikin fad'uwar gaba, sai daya kalleta sosai kafin yace

"Whats ur name?".
Cikin d'ar-d'ar ta amsa da

"I'm Heedayah Abubakar".

"What's ur address?".

"Rijiyar zaki".

Tambayoyi ya shiga yimata kala kala a tak'aice dai a wannan rana saida Uncle Muhammad yazo school
d'in ya tabbatar musu da ba yarinyar da ake cigiya bace wannan asalinta ma ba y'ar Kano bace daga
Katsina take, dan da farko ma har police sukaso su saka a cikin maganar wai za'a maida ita gidan
marayun da k'yar suka yarda da Uncle Muhammad daya dinga rantsuwa, Heedayah kam har kuka saida
tayi musamman dataji sun sako maganar y'an sanda da kuma cewar za'a maida ita gidan marayu. Tare
ma suka tafi da Uncle Muhammad d'in batare da sun gama lecture d'insu ba duk ta tsorace har abin
yakoma bawa Zainab dariya.

Ta b'angaren Jawaheer ma hakan ce ta kasance a inda take karatu dan dai kawai ita ba mutunci dataga
mutum yana mata kallon k'urilla zata tsaya ta zabga masa rashin mutunci ta k'ara gaba dan haka aka
dinga shakkar kallon nata ma dan ba wanda baisan JAWAHEER MANSOOR JIK'AMSHI ba a school d'in.



★__________★

KATSINA

K'ofar K'aura.

Shagon d'inki ne wanda ke cikeda matasa wasu na kan keke suna d'inki wasu kuma y'an tayin hira ne.

Wani matashin saurayi wanda ke zaune kan kujera da keken d'inki a gabanshi amma ba d'inkin yakeba
wayace a hannunshi yana danne danne.

"Kai! Musty wannan ba k'anwar ka Heedayah bace naga anyi posting a Facebook ana cigiyar ta". ya
k'arasa maganar yana nuno masa wayar hannunshi.

Wanda aka kira da suna Musty ne ya dakata da d'inkin dayake ya mik'a hannu ya karb'i wayar abokin
nashi yana kallon screen d'in, baki ya bud'e tareda zaro ido yana k'ara bin hoton da kallo gabanshi na
fad'uwa lokaci d'aya cikin rawar baki yace

"Itace wllhy, itace Isma'eel innalillahi wa inna ilaihi rajioun". Bai saurari cewar kowa ba ya tashi ya fice
da sauri ba tareda yabawa Isma'eel d'in wayarshi ba duk aka bishi da kallo.

Machine d'inshi roba roba ya hau yabashi wuta kafin ya figeshi da uban gudu yabar k'ofar shagon.

Yakai kai zai shiga soron gidan kenan sukayi kacib'us da Baba shikuma zai fita, ganinshi duk a rud'e yasa
Baba ya shiga tambayar shi lafiya kuwa meya faru?.
"Baba mukoma ciki wani abu Isma'eel ke nunamin yanzu a waya". Baba bai musa ba ya juya suka koma
cikin gidan tare hankalinshi duk a tashe da tunanin abinda ya faru.

Umma tana zaune kan tabarma da wake a tray tana gyarashi suma kan tabarmar suka nemi waje suka
zazzauna.

"Lafiya dai Malam na ganku haka kamar ba cikin nutsuwar ku ba?". Umma ta tambaya ganin yanayin su
kamar akwai wani abu dayake faruwa.

"To nima dai zan fita muka had'u dashi zai shigo, muna jinka Mustapha meye ya d'aga maka hankali
haka?".

Zama Mustapha ya gyara yana fad'in

"Yanzu Isma'eel ya nuna min wani hoto wai ta b'ata ana cigiyar ta a Kano". yayi maganar yana mik'awa
Baba wayar, shi kanshi Baba saidaya zaro ido ganin Heedayah k'uru k'uru wai ta b'ata, kalmar innalillahi
kawai yake ambata cikin tsananin tashin hankali Heedayah ta b'ata amma meyasa Ramlah bata kira ta
sanar dasu halin da ake ciki ba? b'atan d'an mutum sukutum da guda?.

Umma ya mik'awa wayar ta karb'a ta duba hoton dayake ita mace ce akwai raunin zuciya har tafara
hawaye ganin Heedayahnta a matsayin wadda ta b'ata dama rabon ayi hakane yasa tabar gabansu tabi
Ramlah Kano?

Wayar Baba ya karb'a daga hannun Umma data tsurawa hoton Heedayah ido tana hawaye ya mik'awa
Mustapha wayar yana fad'in

"Kiramin y'ar uwarka Ramlatu inji dalilin dayasa ta b'oye mana irin wannan muhimmiyar maganar
saboda shashanci".

Wayarshi ya zaro daga aljihun gaban rigarshi yasa password ta bud'e ya shiga jerin numbers yana
neman number Aunt Ramlah.

Bata dad'e tana fara ringing ba akayi picking sai yasata handsfree ya rik'e ta a hannunshi yana amsa
sallamar Aunt Ramlah.

"Ramlah Baba ne zakuyi magana dashi gashi a kusa dani".

"Yauwa dama Mustapha dama ina niyyar kiransu, jin haka yasa gabansu ya k'ara fad'uwa, cikin b'acin
rai Baba ya fara magana da fad'in

"Haba Ramlatu, ya ina ganinki kamar mai wayo ashe ba haka bane inbanda sakarci taya zaki b'oye mana
irin wannan maganar?.
MG'S SKINCARE



In kid'a ya chanza rawarma semutaru asauyata,

Wani Kaya se amalende

Haka Wani Hadi na musamman se MG'S,



Ina ma'abota amfanida kayan MG'S SKINCARE?



To bana fa tafi bara munqarawa kayanmu inganci muncire muntsefe munkawo maku qayatattun kayan
gyaranjiki da Baki taba amfanida irinshiba a wannan qarnin,



Wani irin salo na gishirin kyan daukar magana zakiyi duk kikayi amfanida hadinmu b cika bakiba,ko yayan
Hutu basa nuna maki tsadar fataba,duk a 11k fa kachal👌🏻



Beauty kit:11k

Student package:7k

Soap:3k

Bridal kit 18k



Kicire kokonto ki warwaro Lalita kidebi Kaya n kerewa SAA



Chat:08062991549 or 07046881166 or 07067210195

Call:08064532391



Available in Kano and Kaduna
We also have beautiful yet luxury and unique frames for your apartments chat or call 07046881166



Serious buyers only please,



Inamasu bukukuwa😍

Kugarzaya @inteesar cakes nd more kuyi order small chops domin bakinku irinsu

Cupcake,fishroll,samosa,spring rolls dama duk kayan kwalam da makulashe kunemata 07067210195

Cika alkawari shine takenmu🤝

Thank you




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).



D'imbin godiya ga masu bibiyar littafin nan nagani kuma na yaba sak'onnin ku na riskata ako yaushe
thank you very much ALLAH yabar k'auna alkhairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke sakallahu
khayran.💖



No 21.



Gaba d'aya sai Aunt Ramlah ta kasa gane inda maganganun Baba suka dosa musamman dataji yana
k'ara fad'in
"Duk duniya su ya kamata ace ta fara sanarwa wannan labarin ta inda yake shiga bata nan yake fita ba
itama Umma tasa baki sukayi tayi, sosai hankalin Aunt Ramlah ya tashi dataji Umma na kuka take
maganar cikin sanyin murya tace

"Baba, Umma har yanzu fa ban gane akan abinda kuke magana ba wllhy dan ALLAH ku sanar dani laifin
danayi".

"Haba Ramlatu ace Heedayah ta b'ata har kwanaki biyu amma baki sanar damu ba? yarinyar nan fa
amana ce a wajenmu idan baki fad'a mana ba wa zaki fad'awa? saifa yanzu da Mustapha yagano hotonta
a wayar Isma'ila abokinshi ana cigiyar ta sannan yazo hankali tashe yake nuna mana".

Aunt Ramlah batasan lokacin datayi murmushi ba idan ta fahimta daidai suma sunga yarinyar nan irin
Heedayah suke zaton Heedayahn su ce. Dariya ta d'anyi wadda tasa mamaki ya k'ara kamasu kafin wani
yayi magana tace

"Ku kwantar da hankalinku Baba wannan yarinyar ba Heedayah bace yarinyar ku lafiyar ta k'alau muma
munga hoton yarinyar haka mukasha mamaki wlhi yanzu ma Abban Nu'aym ya dawo da ita daga
makaranta suma shugabannin makarantar sunyi zaton itace da k'yar dai suka yadda shine duk ta tsorata
ta kasa zaman school d'in ta biyoshi suka dawo gida".

"Hukmullah la ajab". Haka kawai Baba ya fad'a yana faman jijjiga kai, Umma da Mustapha ma sakato
sukayi suna saurarar Ramlah cikeda d'imbin al'ajabin abinda take fad'a, yayin da Umma kuma ta d'auki
tunanin ta cak ta maidashi wani waje daban tana ayyana abubuwa da dama a k'asan ranta.

Y'ar dariya Aunt Ramlah ta k'ara yi tace

"Baba bari ku tabbatar ma da abinda nake fad'a bari in kirawo ta ku gaisa". murya tasa ta kira sunan
Heedayah da k'arfi wadda suke kitchen itada Zainab suna shirin d'ora abincin rana, Heedayah ta amsa
tareda ajiye albasar datake yankawa ta wanke hannunta a sink ta fito daga kitchen d'in zuwa falon inda
Aunt Ramlah ke zaune kan kujera, wayar ta mik'a mata tana fad'in

"Su Baba ne zaku gaisa dasu". karb'a tayi cikin murna tana murmushi takai kunnenta tayi sallama tana
gaishe da Baban ya amsa cikin jin dad'i haka ma Umma wadda tuni tabar kukan datake farin ciki ya maye
gurbinsa, har da Yah Mustapha saida suka gaisa yayin da Baba ya tubure shi lallai saidai Heedayah ta
dawo Katsina shi ya tsorata da wannan al'amari da k'yar Aunt Ramlah ta shawo kanshi ya hak'ura ko dan
saboda karatun data fara, haka dai ya hak'ura bada son ranshi ba sai dan irin magiyar da Ramlahn ta
dinga zabga masa.

Sun jima suna hira har saida credit d'in ciki ya k'are wayar ta katse sannan suka hak'ura, a tare su Baba
suka sauke ajiyar zuciya sai yanzu hankalinsu ya kwanta tashi Mustapha yayi ya d'auki wayarshi data
Isma'eel daya taho da ita ya k'ara yimusu sallama ya fita.

Baba ya juya ya kalli inda Umma take yaga itama kallon nashi take kowa da abinda yake tunani a ranshi,
numfashi ya sauke yace
"Anya Sa'adatu babu wani b'oyayyen abu a cikin wannan al'amarin? abin nan fa akwai d'aure kai da
tsantsar mamaki".

"Wallahi Malam abinda yake raina kenan tun lokacin danaji ba Heedayah bace yarinyar nan anya ba
y'an biyu bane ba kuwa? dan wannan ba za'ace iya kamanni kawai suke da Heedayah ba dan wllhy idan
an kwana dubu ana ce min ba Heedayah bace bazan yardaba kaga abu saikace almara". Umma ta k'arasa
maganar tana rik'e hab'arta tana k'ara jinjina girman al'amarin. Shima Baba kai ya shiga jinjinawa
hundred percent ya yarda da maganar Umma datace ko y'an biyu ne ba shakka wannan babban al'amari
ne dayake buk'atar bincike sosai idan ya kasance hakan ne kuwa zaifi kowa farin ciki zai sada Heedayah
da asalin iyayenta duk da yasan ba k'aramin rud'ani da tashin hankali Heedayah zata shiga ba lamarin zai
girgizata, Baba sun dad'e suna k'ara tisa maganar da Umma kafin shima ya tashi yayi mata sallama ya fita
dama ya fitan wani abin ne ya dawo dashi.



Matuk'a Aleeyu yake kula da Seeyamah zuwa yanzu harta fara sabawa da zaman kad'aitakar da
wannan azzalumin ya gadar mata, wani har hira suke zama suyi da Aleeyu. Habeeb kuwa tun ranar
dayaje batada lafiya har akayi mata allura bai k'ara zuwa ba ako yaushe dai yana kiran Aleeyu yaji lafiyar
ta, sau d'aya ya tab'a cewa Aleeyun ya bata suyi magana shima ba wata maganar arzik'i bace cewa yayi
idan ta shirya barin gidan ta fad'awa Aleeyu shikuma zaizo ta fad'a masa waye shi da dalilin dayasa take
masa BASAJA bai saurari cewarta bama ya datse kiran tasha kuka a ranar har saida kanta yayi ciwo
Aleeyu yana rarrashinta bama ta kulashi ba ta cigaba da kukanta zuciyarta na mata zafi.

Ta b'angaren Mujaheed kuwa sosai yasa ido akan duk wani takun abokin nashi batare dashi Habeeb
d'in yasani ba, yayi busy sosai cikin kwanakin dan anfara ginin d'aya kamfanin na sark'ok'i da fidda design
d'insu hakan yasa sam baya samun lokacin kanshi ma.

Police suna iya bakin k'ok'arinsu matsalar da har yanzu wad'anda sukayi garkuwar da ita basu kira waya
anji daga garesu ba bare aji kud'in da zasu yanka wanda za'a fanshe ta har abi diddiginsu abin dai sai
addu'ar ALLAH ya bayyana ta kawai.



★★__________★★.

K'arar spoon kawai ke tashi a dinning area d'in Ummi da Neehlah su kad'ai ne masu cin abincin
Habeeb kam wayace a hannunshi yana ta faman danne danne kanshi a k'asa ga abincin a gabanshi
amma kota kanshi baibi ba hakan yasa da Ummi ta gaji tace

"Ajiye wayar nan ka kama abinci kaci". d'agowa yayi ya kalli Ummin ya d'an b'ata fuska da fad'in

"I'm full fa Ummi tea ma kawai is okay".

Had'e rai Ummi tayi tace
"Ban yardaba Abbuna meyasa kake son yin

11 / 21