Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 21

21K to 24K   out of 61.8K words

ciki ya
d'aura Rolex watch black a tsintsiyar hannunshi sai red p.cap daya zaro inda suke tule a ma'ajiyarsu duk
da bawai ya cika mu'amala da ita bane yakan dad'e kafin ya sata (Ba irin d'an gidan Mom sayyeed da
Aunt jamila ba Abdallah Madugu wadda ta zame masa kamar ibadah 😅).

Gaban makeken mirror d'inshi ya k'arasa wanda ke cikeda uban turaruka masu tsada da asalin kyau,
body spray ya fara shafawa sannan yabi jikinshi da kalolin turaruka kusan kala uku masu mugun k'amshi
da kama jiki uwa uba kuma sanya nutsuwa da kwanciyar hankali ga duk wanda ya shak'a. Bak'in glass ya
d'auka saidai bai sashi a idonshi ba ya mak'alashi a gaban rigar ya fice bayan ya kwashi wayoyinshi.

Kai tsaye side d'in su Ummi ya nufa dan gaisheta yana k'ofar shiga falon kira ya shigo d'aya daga cikin
wayoyin nashi, duba mai kiran yayi yaga Mujaheed ne picking yayi yakai kunnenshi cikin amon muryar
shi mai dad'in saurara yayi sallama Mujaheed ya amsa yana fad'in

"Mazajeee ya jikin naka?".

Baiyi magana ba sai daya k'arasa shiga cikin falon ya tsaya gaban makekiyar TVn dake lik'e jikin bango
yace

"Alhmdulillah".

"Masha ALLAH, ALLAH ya k'ara sauk'i zaka shigo kamfani ne yau?".

"Insha ALLAH, but zanyi wani uzuri kafin in k'araso".

"Okay no prob, saika shigo d'in". Mujaheed yace tare da hang up d'in kiran.

Yana sauke wayar daga kunnenshi Ummi ta shigo falon da sallama taci gayunta cikin bak'ar doguwar
riga k'irar Dubai abayah wadda gaba d'aya gaban rigar akayi mata kwalliya da k'ananun stones masu
mugun k'yalli hakan yasa suke ta faman walwali suna d'aukar ido ta yane kanta da gyalen rigar wanda ya
k'ara fito mata da asalinta na cikakkiyar balarabiya, k'amshi kawai take zubawa mai dad'i tayi kyau abinta
idan ka ganta bazakace tana da cikakken saurayi kamar Habeeb ba.

Kan kujera ta zauna tana murmushi, ya k'arasa inda take ya tsuguna har k'asa yana gaisheta cikin yaren
larabci, cikin sakin fuska ta amsa tana tambayar shi jikinshi ya amsa mata da yaji sauk'i, daga nan dinning
area suka nufa sukayi breakfast duk da dai Habeeb sama sama yayi nashi dan hankalin nashi kuma ya
koma kan yarinyar gidan marayu wadda baisan sunanta ba, ganin Ummi ne ma yasa har ya tsaya yin
break d'in yasan idan yace baya ci fad'a ne zai sha shi kuma ta ritsashi dole saiyaci d'in shiyasa yaci
kad'an ya tashi duk da haka saida Ummi tayi masa k'orafin baici dayawa ba sumbata kawai ya sakar mata
a kumatun ta ya fice yana fad'in yayi latti ne.
Da kallo ta bishi harya fice daga falon yana k'ok'arin toshe idanunshi da black shade d'in dake mak'ale a
gaban rigar shi, girgiza kai kawai tayi tana murmushi kullum da uzurin dazai kawo mata idan yaga tana
k'ok'arin tilasta masa yaci abinci dayawa daga yace yana sauri saiyace zai gana dawasu bak'i a ranar ko
yace akwai important issues da zaije ya gabatar sai yasan yadda dai ya zille mata ya fita ta rasa irinshi cin
abincin ma kamar yana masa wahala ne.

Ganin yasa d'aya daga cikin security's d'in dake tsaye jikin motar Habeeb ya bud'e masa k'ofar motar,
saidai ganin yayi tsaye yasa ya bishi da kallo da alamu yau zasusha fama dashi ganin black shades d'in
daya manna. Hannu kawai Habeeb ya tara masa batare dayayi magana ba, kallon rashin fahimta yabi
Habeeb dashi da tunanin me zai bashi?.

"Give me my key". yace k'asa k'asa yana d'an hararar shi ganin saida yasa shi magana batare dayayi
niyyar yiba, da sauri ya mik'a masa key d'in.

"Kowa ya tafi bana buk'atar kowa yau". yace yana k'ok'arin bud'e driver seat ya shiga ya tada motar ya
fice daga gidan suka bishi da kallo.

Kai tsaye unguwar lamid'o crescent ya nufa inda gidan yake, unguwar sam ba yawaitar mutane sai
motoci da suke d'an yawan wucewa kasancewar safiya ce kowa na tafiya wajen aiki.

Parking yayi a k'ofar gidan bai shiga da motar ba, ya kira Aleeyu yace ya fad'a masa yana waje, nan da
nan Aleeyu ya fito ya bud'e masa suka shiga ciki tare Aleeyu na mik'a gaisuwar shi da hannu kawai ya
amsa masa ya wuce ciki, suna shiga falon yaja tunga ya tsaya yana kallon Aleeyu da alama so yake ya
tambaye shi wani bedroom d'in take amma ya bud'e baki yayi maganar ne aiki Aleeyu ya saba ganin
haka daga gareshi dad'ewar da sukayi tare yasa ya fara lak'antar shi.

"Left bedroom". Aleeyu yace yana kallon Habeeb, baice komai ba ya wuce ya nufi corridor'n dazai
sadashi da side d'inshi na hagu inda bedroom d'in yake, kafin yabar cikin falon ya tsaya ganin haka
Aleeyu ya k'araso ya tsaya a bayanshi, hannu yasa cikin aljihun jeans d'inshi ya ciro rafar kud'i

y'an five hundred ya cillawa Aleeyu yace

"Kaje kayi breakfast itama ka samo mata abinda zataci". daga haka yayi gaba Aleeyu kuma ya fita daga
falon yaja k'ofar.

Gaba yayi zuwa bedroom d'in, Seeyamah na zaune gefen gado ta k'udundune cikin hijabinta tun bayan
sallahr asubah data idar tana zaune a wajen tasha kuka har ta gode ALLAH, idanunta sunyi matuk'ar yin
ja sun kumbura saboda kuka da rashin barci dan koda wasa barci bai d'auke ta ba tunda taga bathroom a
ciki ta shiga ta d'aura alwalah tazo ta kabbara sallah, kwana tayi tana sallah tana kai kukanta wajen
ubangiji subhanahu wa ta'alah ya fitar da ita daga hannun wannan azzalumin daya d'aukota wanda
batasan laifin datayi masa ba, to wane laifi ma zatayi masa? su daba fita suke ba kullum suna gida, sai a
lokacin nema ta k'ara k'arewa d'akin kallo madaidaicin gado ne royal sai k'aramar drawer saikuma sofa
guda d'aya tak kalar gadon su kad'ai ne a d'akin inka d'auke lallausan carpet d'in da aka malale k'asan
dashi.
Jin alamun takun tafiya zuwa bedroom d'in datake yasa gabanta yayi muguwar fad'uwa ta runtse
idanunta tana kiran sunayen ubangiji tsarkaka saboda batasan da wacce yazo ba yanzun saboda tunda
ya kawota ma magana bata had'asu ba.

Tsaye yayi a bakin k'ofar d'akin ya lumshe ido yana sauke numfashi haka nan ya tsinci kanshi da
fad'uwar gaba wanda ya rasa dalilin hakan, Ido ya bud'e yasa key d'in bedroom d'in wanda Aleeyu ya
bashi yasa ya bud'e ya bud'e k'ofar ya shiga, daga bakin k'ofar ya tsaya yana k'arewa Seeyamah kallo ta
cikin glasses d'inshi wadda take a mugun tsorace kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da hakan daga inda
yake tsaye yana iya hango rawar da jikinta yake ta takure waje d'aya cikin babban hijabinta mai hannu
pink color.

Tsananin tsoro yasa Seeyamah ta kasa d'agowa ta kalli wanda ya shigo d'in tayi nasarar dai shak'o
daddad'an k'amshin jikinshi wanda ya baza ko ina tun shigowarshi gidan.

A hankali ya shiga takawa zuwa wajen wani dogon stool na zama wanda yake kusa da sofa, stool d'in ya
jawo zuwa gabanta ya ajiye bai zauna ba sai daya kai wayoyinshi kan wannan drawer ya ajiye sannan ya
dawo ya zauna, daga zaunen dayake ya cusa duka hannayenshi a aljihun wandonshi yana kallonta da
yadda jikinta ke shaking ta cikin glass d'inshi.

Baice komaiba haka itama bata d'ago kai ta kalleshi ba sai had'add'un takalman shi datake kallo ta
k'asan idanunta da suke zubar da ruwan hawaye.

Sai daya fesar da iskar daya cika bakinshi da ita ya sauke k'aramin numfashi sannan ya rank'wafa daf da
ita ta yadda har yakejin hucin numfashin ta itama take jin nashi wanda ke had'e da wani sihirtaccen
k'amshi so take ta d'ago kai taga waye shi d'in amma ta kasa ganinshi take duk yabi ya cika wajen.

"Look at me". yace cikin wata irin dakakkiyar murya wadda duk da ba da k'arfi yayi maganar ba amma
sai data jita har tsakiyar kanta, bata d'ago ba sai kukanta data cigaba dayi wanda k'asa k'asa ne yanzu
kuma yake k'ok'arin fitowa fili. Lumshe ido yayi yana cije lips ganin tak'i yin abinda yace mata.

"I said look at me". ya fad'a a tsawace wanda hakan yayi matuk'ar razana Seeyamah ta d'ago kanta ba
shiri ta kalleshi hawaye na zarya a kumatun ta, kallonshi kawai take batare data gane ko shi d'in waye ba
saboda glass d'in dake manne a idonshi.

"Kin gane ni?". yace cikin tsananin had'e rai da tsare gida. Kai ta girgiza da sauri alamun a'a, shima kan
ya jijjiga yana d'an taune lips lokaci d'aya yasa hannu ya zare glass d'in idonshi idanunsu suka shiga cikin
na juna wanda hakan ya haddasawa Seeyamah tsananin fad'uwar gaba fiye data d'azu ganin wanda ke
zaune a gabanta hakan yana nufin shine yasa aka kawota nan d'in kenan? why? me tayi masa haka?.

Glass d'in ya mak'ala a gaban rigar shi p.cap d'in kuma ya cire ya jefata kan gado yana fad'in

"Yanzu fa?".

Kai ta kad'a masa alamun eh ta ganeshi. "Good". ya fad'a yana kad'a kanshi.

Shiru yayi kamar bazai k'ara magana ba kafin yace
"Zanyi miki wasu y'an tambayoyi, idan kika fad'amin gaskiya zan k'yaleki insa a maidake inda aka d'auko
ki sab'anin hakan kuma bazai miki dad'i ba zan d'auki babban mataki a kanki wanda bazai miki dad'i ba
kin gane?".

Kai ta d'aga masa tana rufe bakinta da hijabinta.

Sai daya k'ara tamke fuskarshi tamau yaci d'aci sosai sannan ya k'ara sunkuyawa daf da ita yace

"Kinsan waye ni?". A mugun tsorace take hakan yasa batasan lokacin data d'aga masa kai ba alamun ta
sani.



Mrs Salees Mu'az 💝




*EL--HABEEB*💥



©️Oum Hanan.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)



No 15.



Da mamaki sosai shimfid'e a fuskarshi yake kallonta, koda yake ba abin mamaki bane dan tace ta
sanshi dan da ace bata sanshi ba bazata dinga bibiyar sa duk inda yaje ba da batayi masa wasa da hankali
ba.

Seeyamah kam sai bayan data gyad'a masa kai sannan ta gano irin katob'arar datayi na cewa ta sanshi
harga ALLAH tsabar kwarjini da cikar haibar shi ne da yadda yayi mugun cika mata ido dad'in dad'awa
kuma da bala'in tsoron shi daya mamayeta lokaci d'aya shine ya haddasa mata hakan gashi ta janyowa
kanta.

Shiru d'akin ya d'auka sai sautin kukan Seeyamah dake fita k'asa k'asa cikin fad'uwar gaba.

Knocking door akayi, da k'yar Habeeb ya bud'e baki yace
"Yes coming".

Bud'e k'ofar akayi Aleeyu ya shiga hannunshi rik'e da wata leda mai tambarin wani restaurant sai daya
rissina sannan ya mik'a masa ledar had'i da car key d'in hannunshi, key d'in kawai ya d'auka yayi masa
alamu da ido ya ajiye ledar a k'asa, ajiyewar yayi kamar yadda ya umarce shi sannan ya fice tareda jan
k'ofar. Har yanzu bai daina mamakin abinda yasa Boss d'in nasu ya d'auko yarinyar ba especially data
kasance marainiya idan ba'a tausaya mata ba ai ba'a cutar da ita ba.

"Who I'm?".

Taji sautin muryar shi a dake wanda yasa hantar cikinta kad'awa, shiru batayi magana ba to kota bud'e
baki batasan me zatace masa ba. bata sanshi ba, bata tab'a ganin ko mai kama dashi ba, abu d'aya tasani
a kanshi yana yawan taimakawa gidan marayun su koda yaushe akance musu akwai wani bawan ALLAH
dayake taimaka musu bayan haka batasan komai a kanshi ba.

Iskar daya cika bakinshi da ita ya fesar ranshi yana k'ara b'aci da rainin hankalin da yarinyar take masa
bayaso ya fito mata a asalin Habeeb Gashua d'inshi shiyasa yake d'an bida ita a hankali kafin ya fito mata
a true color d'inshi. (Ka d'auki abin da zafi Habeeb 🙄).

"Who I'm?". yace yana lumshe ido da alamun b'acin rai cikin muryar tashi wanda yasa tsinkewar
gabanta ya k'ara tsananta.

"I said waye ni?". ya fad'a cikin wata hargitsattsiyar murya wadda saida d'akin ya amsa tareda tashi a
fusace yayi ball da stoll d'in dayake zaune, a razane tayi baya tana k'arawa kukanta volume lokaci d'aya
tana rufe bakinta da hijabinta jikinta sai rawa yake tamkar mai jin sanyi.

Hannu yakai kan sumarshi ya shiga yamutsa ta idanunshi a lumshe ya rik'e k'ugunshi da hannu d'aya
yana sauke numfashi.

Takowa yayi har gabanta yaja trouser d'inshi sama sannan ya tsuguna daf da ita har numfashin su na
had'uwa waje d'aya.

"I'm asking u". yace cikin cool voice kamar bashi ya gama hayagaga ba yanzu idanunshi a kanta. Yawun
tsoro ta had'iya kafin cikin kuka da rarraba maganar tace

"Bal.....ba.......balarabe ne kai, ALLAH shi kad'ai nasani a kanka sai taimakon da kake yiwa gidan
marayun mu".

Juyar da kai yayi yana lumshe ido gamida cije lips d'inshi, amma yarinyar nan ta mugun raina masa
hankali duk wannan tada jijiyar wuyan dayake saboda yanaso yaji actually abinda yasa take canza
kamanni take kuma binshi duk inda tasan zaije shine zata bud'e baki tace wai balarabe ne?.

Juyowa yayi yana jan tsaki yace

"Hakan yana nufin zaki cigaba da zama a nan gidan kenan har zuwa lokacin da zaki gaji ki bayyana min
gaskiya understand?".
"Dan ALLAH kayi hak'uri ka maidani inda ka d'aukoni wllhy bansan komai a kanka ba daya wuce
wannan please help me".

Idanunta ya k'urawa nashi hazal eyes d'in yanason gano gaskiyar abinda ta fad'a, itama kallon nashi take
da idanunta da sukayi jawur saboda kukan datasha ko iya wannan hawayen data zubar sai ALLAH yayi
mata sakayya akansu.

Kai kawai ya girgiza yana datse bakinshi kamar zaice wani abu saikuma ya fasa ya janyo ledar da Aleeyu
ya kawo ya bud'e ya tura mata gabanta.

"Eat". ya furta hakan kamar mai ciwon baki, kai ta girgiza masa wasu hawayen na gangarowa kumatun
ta, fuskar sa ya k'ara tamkewa sosai yace

"Bana gane body language open ur mouth".

Cikin rawar murya tace

"I'm full".

Wani mugun kallo ya watsa mata hakan yasa ba shiri ta janyo ledar gabanta ta bud'e takeaway d'in dake
sama sakwara ce da miyar ganye da akayi mixing da egusi taji naman rago sai k'amshin spices take.
Yadda ya tasata a gaba ne yasa ta fara ci a hankali, kallon yadda take gutsurar sakwarar yake tamkar
jariri za'a bawa saboda k'ank'antar ta, bai daiyi magana ba ya tashi tsaye ya isa inda ya ajiye wayoyinshi
ya d'auki d'aya ya fara danne danne a ciki.

Kad'an ta yayyafita ta ture gefe, tana shirin tashi taje ta wanke hannunta yadawo wajen saita fasa
tashin tayi k'asa da kanta cikin fad'uwar gaba, hannu yasa ya d'auke takeaway d'in da sakwarar ke ciki
yana kallon yadda ta fiffincine ta ya d'auko d'ayan dake k'asa ya bud'e ya tura mata gabanta, abinda ke
ciki tabi da kallo potatoes with eggs sai miyar hanta a gefe. So take tayi masa musu amma ta kasa
saboda yadda yabi ya tamke fuskar ba alamun rahma samanta dole tasa hannu ta fara ci duk da kawai
dai turawa take batare da tanajin dad'in shiba sam bakinta ba wani d'and'ano, shima d'in kamar wancan
kad'an taci ta tureshi cikin ranta tana addu'ar ALLAH yasa kar yace saita k'ara ci saikuma aka ci sa'a bai
tanka ba, toilet taje ta wanke hannunta a sink ta fito bata sameshi a d'akin ba harya fice, gefen gado ta
samu ta zauna ta matse jikinta cikin hijabinta wani kukan nason k'wace mata.

Tare da Aleeyu suka tafi kamfanin bayan ya tabbatar an kulle ko ina ta yadda ba zata samu hanyar fita
ba.



★________________★

A safiyar ranar orphanage house suka wayi gari da tashin hankalin b'atan Seeyamah lungu da sak'o
na gidan ba inda ba'a duba ba, ba ita ba alamunta ba k'aramin tashin hankali jama'ar gidan suka shiga
ba, manya da yara musamman k'awayenta da suka shak'u sosai Ikram da Aminah sai kuka suke sauran
na kwantar musu da hankali duk da suma d'in dai hankalin nasu a tashe yake. Abin ya mugun d'aure
musu kai, ganin suna k'ara b'ata lokaci yasa mutum biyu suka wakilci sauran sukaje suka kai report police
station da hoton ta, anan D.P.O d'in ya tabbatar musu da insha ALLAH zasuyi iya bakin k'ok'arinsu wajen
ganin sun nemota.

Da rana ma waya Habeeb yayiwa Aleeyu yace yayi launch yakai mata, nan da nan kuwa ya cika umarnin
shi yayi takeaway na fried rice with chicken da lemon aya ya had'a da fresh milk ya nufi gidan.



Tun daga falo yake jin shasshek'ar kukanta, wani tausayin ta ya k'ara kamashi wato har yanzu bata
daina kukan ba.

Key yasa ya bud'e bedroom d'in ya shiga bakinshi d'auke da sallama, kan darduma ya sameta ta d'aga
hannayenta sama tana kuka gamida rok'on ALLAH ya fitar da ita daga wannan wajen.

Lumshe ido yayi cikeda tausayin yarinyar ya k'arasa ya ajiye ledar a kusa da ita, kallonshi tayi cikin kuka
tace

"Bawan ALLAH kaji tsoron ALLAH ka maidani inda ka d'aukoni ka duba maraicina da tashin hankalin da
zakusa bayin ALLAHn da basuji ba basu ganiba ka taimakeni ka fitar dani daga nan wllhy bansan akan me
oganku yake tuhuma ta ba help me please".

Sosai jikin Aleeyu yayi sanyi wata zuciyar na fad'a masa ya fitar da ita kawai yayin da wata zuciyar take
masa kashedi da jan kunne na rasa aikinshi da zaiyi wanda da shine yake taimakawa iyayenshi da basuda
k'arfi.

"I'm so sorry". abinda yace kenan ya juya ya fita dan idan ya tsaya zuciyarshi zata iya karyewa ya aikata
abinda bai shirya yinshi ba.

Wani kukan ta k'ara fashewa dashi bayan fitarshi, kanta sai wani irin sarawa yake saboda kuka bata ko
dubi inda ya ajiye ledar ba saboda ba damuwar ta bace tasan abinci ne dai kuma ba iya cinshi zatayi ba.

Kafin kace me zazzafan zazzab'i ya rufeta ruf batayi yunk'urin hawa gadon ba nan saman pray mat d'in
ta kwanta ta k'udundune cikin hijabinta tana rawar sanyi.



Afwan da kad'an 👏.



Mrs Salees Mu'az 💝




*EL HABEEB*💥
©️Oum Hanan.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)



No 16.



Aleeyu yana kan hanyar shi ta komawa kiran Habeeb ya shigo wayar shi bayan yayi picking yace masa
yasamu boutique ya siya mata kayan sawa. Aiki ja wato har kayan sawa ma za'a siya mata kenan ba
ranar sakinta? Aleeyu ya fad'a cikin ranshi yana yin reverse yakoma baya inda ya d'an gota wani babban
boutique clothing store yayi parking ya shiga ya fara jidar mata kaya duk dogayen riguna ne ya d'ibar
mata da skirt and blouse wad'anda basa matse jiki yaje ya biya kud'in ya shiga mota ya k'ara komawa
baya inda gidan yake dan kai mata kayan (Aiki ya sameka Aleeyu Lol).

Sosai hankalin Aleeyu ya tashi lokacin daya isa yaga halin da Seeyamah take ciki, har lokacin tana
kwance akan dardumar tana rawar sanyi bata ma san da shigarshi d'akin ba, ba shiri ya ciro wayarshi a
aljihu yayi dialing number Habeeb.

Lokacin suna zaune a office d'inshi shida Mujaheed yana gwada masa tsarin wasu gine gine na
companies a cikin labtop d'inshi yana zab'ar irin design d'in dayake so kasancewar suna shirin fara gina
wani company daya shafi necklace, earrings, bangles and rings kuma zasu dinga fitar da design

8 / 21