Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 21

27K to 30K   out of 61.8K words

ya
d'auki remote d'in TV da tun d'azu takeyi a tashar larabawa ana labarai channels ya shiga canzawa yana
fad'in

"Mudai ba larabcin nan mukeji ba bari mukai inda mukafi wayo".
Habeeb da bayan gama tattaunawar tasu ya d'auki waya ya cigaba da danne danne ya d'ago ya kalli
Mujaheed yana b'ata rai yace

"Wai meyake damunka ne MJ akan me zaka canzamin channels?".

"To kallon kake? tunda na shigo d'akin nan banga ka d'aga kai ka kalli TVn nan ba".

"Dole saina kalla zanji abinda ake fad'a? ba kunne ne yake jiba". Habeeb ya fad'a yana antayawa
Mujaheed harara. Baki kawai Mujaheed ya tab'e ya cigaba da neman channels d'in dayake so kan N.T.A.
ya tsaya daidai lokacin da zasu fara news ya ajiye remote d'in yana fad'in

"Yawwa bari muga abinda duniyar ke ciki". tsaki kawai Habeeb yayi ya maida kanshi kan wayar dake
hannunshi shikuma Mujaheed kacokam ya maida hankalinshi kan TVn, bayan mai gabatarwa ya gabatar
da kanshi da kuma kanun labaran sannan aka tsunduma cikin gundarin labaran.

Labari na farko da mai labaran ya fara karantowa shine na b'atan Seeyamah bayan wasu y'an
maganganu dayayi hoton Seeyamah ya mamaye fuskar talabijin d'in a matsayinta na wadda ake nema,
tana sanye da k'aton hijabi kamar yadda ya saba mai hannu light blue fuskarta d'auke da k'ayataccen
murmushi wanda har beauty point d'inta saida suka lotsa wanda take dashi a gefen kumatun ta na dama

"Innalillahi". Mujaheed ya fad'a cikin razana yana zaro ido ganin yarinyar nan ta gidan marayun da suka
tab'a zuwa da Gashua wadda har yace saita bar gidan garkuwa akayi da ita kenan?.

"Gashua kaga wani abin mamaki". Mujaheed yace cikin fad'uwar gaba yana dafa kafad'ar Habeeb
wanda gaba d'aya hankalinshi yake kan wayarshi da alamu wani abu mai muhimmanci yake yi a ciki. A
hankali ya d'ago kai idanunshi suka fad'a kan Seeyamah da har zuwa lokacin ba'a d'auke hotonta daga
TVn ba, ba zaice gabanshi bai fad'i ba amma dayake namijin duniya ne saiya maze ya shanye fad'uwar
gaban nashi ya kalli Mujaheed yana neman k'arin bayani daga wajenshi.

"Wlhy wai b'ata tayi ba'a ganta ba har gidan marayun aka shiga aka d'auketa nasan ka ganeta ko? kai
jama'a duniya ina zaki damu ne? marainiyar ALLAH bata jiba bata ganiba anje anyi garkuwa da ita Yaa
ALLAH". ya k'arasa maganar cikin tsananin jimami yana dafe goshinshi sosai labarin b'atan Seeyamahn ya
dakeshi saiya tuno lokacin daya tambayeta sunanta ta fad'a masa da irin murna da farin cikin daya hanga
daga cikin idanunta lokacin dayace ta tashi ya maida ita gidan marayun yau gashi anje har cikin gidan
inda take tunanin nan ne garkuwar ta bango abin jinginar ta an saceta.

Sam Habeeb kasa d'auke idanunshi yayi daga kan allon talabijin d'in idanunshi k'ur akan Seeyamah duk
yadda yaso janye idanunshi ya kasa har zuwa lokacin da aka d'auke hoton mai gabatarwar ya cigaba da
labaran shi, a hankali yayi k'asa da kanshi ya cigaba da danne dannen dayake a zahiri wanda a bad'ini
kawai shige shige yake a cikin wayar batare dayasan ina yake shiga yake fita ba tunanin kacokam ya tafi
can wani waje daban.

"Wai bakaji abinda nace bane Gashua ka maida kanka ka cigaba da abinda kake?". Mujaheed ya fad'a
cikin jin haushi yana kallon Habeeb.
"Me kakeso ince MJ? ko zuwa zanyi in nemota da kaina?".

"Bakaji na fad'i haka ba amma dai at least ko addu'a ce kayi ta ALLAH ya bayyana ta tunda ba'a san a
wani irin hannu take ba anya kanada imani kuwa Gashua?".

Wani banzan kallo Habeeb ya jefi Mujaheed dashi kafin yace

"Ina nake dashi? ai imani sai sheikh Mujaheed". yayi maganar cikeda gatse.

"Ai naga alama kam inba hakaba ai duk wani musulmi mai imani idan yagani zai tausaya har ma yabita
da addu'a".

Tsaki kawai Habeeb yaja ya zame ya kwanta yana cigaba da duba wayarshi.

"ALLAH ya shiryeka ya canza maka halinka". Mujaheed ya fad'a shima yana d'auko wayar shi wadda ya
ajiye kan center table tun bayan shigowarshi falon, ko kallonshi Habeeb baiyiba bare ya tanka masa.

Yanar gizo Mujaheed ya shiga nan ya fara cin karo da hoton Seeyamah a Facebook da labarin b'atan ta,
kai kawai ya girgiza cikeda tausayin yarinyar ko a wani irin hali take ciki yanzu? ALLAHU A'ALAM, ALLAH
dai ya tona asirin wad'anda suka d'auketa.

"ALLAH ya bayyanaki cikin k'oshin lafiya Seeyamah". Ya fad'a a fili cikin alhini, baki Habeeb ya tab'e cikin
ranshi yana mamakin irin yadda yaga Mujaheed ya nuna zallar damuwarshi kan b'atan yarinyar da sai
yanzu ma yake jin sunanta.

D'aya wayar tashi wadda ke ajiye gefenshi ta fara bada sautin kid'a mai dad'i, kamar bazai d'auka ba
saikuma yakai hannu ya d'auka ya duba mai kiran yaga Aleeyu ne batare da shayin komai ba yayi picking
ya kara a kunnenshi cikin muryar nan tashi mai cikeda amo da sautin mai dad'in saurara yace

"Ya akayi?". Sam bai saurari gaisuwar da Aleeyun keyi masa ba, daga b'angaren Aleeyu yace

"Yallab'ai yarinyar nan fa tak'i cin abinci na kad'a na raya amma tak'i kulani kuma dole sai taci abincin
sannan tasha maganin ko d'azu da rana ma kad'an ta yafita tace ta k'oshi sai aikin kuka datakeyi tun
d'azu".

K'aramar ajiyar zuciya Habeeb ya saki yana d'an dafe goshinshi da sakin numfashi kamar bazaice komai
ba saikuma yace

"Bata wayar".

Aleeyu dake tsaye akan Seeyamah datake ta kuka tun d'azu ya mik'awa wayar yana fad'in

"Zakuyi magana da yallab'ai".

Gaba d'aya jikinta rawa ya d'auka saboda tsoro ita sam batayi tunanin kiranshi zaiyi ba sai dataji yafara
magana dashi wllhy mugun tsoron mutumin nan take ji, hannu na rawa ta karb'i wayar takai kunnenta
saidai ta kasa magana sai shasshek'ar kuka datake k'asa k'asa wanda yasa Habeeb lumshe idanunshi ya
k'ara gyara kwanciyar shi kafin cikin cinkushasshiyar murya ya k'ara had'e rai sosai kamar yana gabanta
yace

"Ke! kin raina mutane ko?".

Girgiza kai kawai tayi kamar yana kallonta tana share hawayen idanunta da d'aya hannun, Aleeyu dai
yana tsaye yana kallonta.

"Ki kama abinci kici kafin ranki ya b'aci duk ranar da kika bari ya k'ara min complain akan rashin cin
abincinki sai ranki ya b'aci banason gardama ki kiyaye".

"Bakya jine". yayi maganar a fusace cikin d'an d'aga murya jin tayi masa shiru ya tsani yayi magana ayi
biris dashi har saida Mujaheed yabar danna wayar dayake ya kalleshi, cikin dashasshiyar murya ta amsa
masa da

"Toh". Wata tsanar shi na k'ara samun gurbin zama a cikin zuciyarta, k'aramin tsaki yaja ya kashe wayar
batare da sun k'ara yin magana da Aleeyu ba wayar ma gaba d'aya saiya kasheta ya cillata gefenshi yana
d'agowa suka had'a ido da Mujaheed wanda yake binshi da wani irin kallon tuhuma, basarwa yayi ya
d'auke kanshi gefe Mujaheed kasa shiru yayi yace

"Gashua dawa kake waya haka?".

"Zoka matseni sai in fad'a maka munafuki". yace yana masa wani irin kallo mai kama da harara.

"Oh my God! nifa ba fad'a na nema ba tambaya ce kawai nayi, ALLAH Gashua kazama masifaffe nidai
sanin danayiwa wancan Gashuan ba haka yake ba maganar fatar baki ma bata dameshi ba amma lokaci
d'aya ka canza ka zama jarababbe magana kad'an saika hau kan mutum da bala'i why?".

Banza yayi masa bai tanka shiba, baki Mujaheed ya tab'e ya mik'e tsaye yana fad'in

"Naga alamar idan ban bar gidan nan ba duka zaka kai min".

"Ai kasan ga mahaukaci ko?". Habeeb yace yana sakar masa harara gamida cije lips d'inshi, dariya
Mujaheed yayi yana zura system d'inshi a jaka ya rataya yana fad'in

"A'a nidai bance ba Mr Habeeb Gashua good night sai mun had'e gobe". daga haka ya d'auki wayarshi
ya nufi k'ofar fita yana cigaba da dariyar shi wadda ta k'ara k'ular da Habeeb sosai ya bishi da kallon
takaici yanajin tamkar ya shak'oshi yayi ta dukanshi ganin irin dariyar dayake masa ya maidashi wani
shashasha.

Zaune Mujaheed yake a cikin motar shi bayan fitarshi da wace yarinya Gashua yake waya har yake mata
bambamin idan bataci abinci ba sai ranta ya b'aci? wacece ita? meye alak'arshi da ita? bayaso ya
tabbatar da zargin da zuciyarshi take yimasa akan abokin nashi kuma d'an uwanshi amma dole yasa ido,
d'azu kafin yazo office yace yana da uzurin dazaiyi kafin yazo dayazo kuma suna cikin aiki an kirashi a
waya yabar komai dayake ya tafi yanzu kuma an kirashi yana magana kan taci abinci duk da baiji
maganar wanda suke wayar dashi ba ya tabbatar mace ce duk me hakan yake nufi? ya tuno lokacin da
Habeeb d'in yayi ruwa yayi tsaki yace dole sai Seeyamahn tabar gidan marayun datake kodai wani abun
ya shirya bayan faruwar lamarin yasan halin abokinshi sarai da kafiyar tsiya da taurin kai koma dai meye
zaibi ba'asi da diddigi har saiya gano bakin zaren. Motar ya tayar ya fice daga gidan zuciyarshi cikeda
tunanika kala kala.

Habeeb bai samu nutsuwa ba sai daya k'ara kiran Aleeyu ya tambaye shi taci abinci da magungunan
kuwa? Aleeyu ya tabbatar masa da taci kuma tasha maganin ta kwanta.

B'oyayyar ajiyar zuciya ya saki lokaci d'aya yana sauke numfashi tareda yamutsa lallausar sumar kanshi,
kayan kallon ya kashe ya shige bedroom yayi wanka yasa jallabiyyah blue black ya fesa turaruka sannan
ya tada sallah kamar yadda ya saba ko wani dare kafin ya kwanta.



★______★

A daidai wannan lokacin da aka haska hoton Seeyamah a NTA ana cigiyar ta, Heedayah da Zainab ma
suna zaune a falo da yaran Aunt Ramlah kasancewar suna duba books d'insu na school ne yasa basu
maida hankali wajen canza tasha ba dan indai suna zaune a falon basuda tashar kallo sai Arewa 24 ko
MBC Bollywood, Zainab ce ta fara ganin hoton Seeyamah daya mamaye fuskar talabijin d'in a mazaunin
wadda ake cigiyar ta ta b'ata kwanaki biyu da suka wuce. A matuk'ar razane ta zaro ido tana k'ara bin
fuskar Seeyamah da ido kafin ta girgiza kafad'ar Heedayah wadda kanta ke sunkuye tayi nisa cikin duba
littafin hannunta, d'agowa tayi ta kalli Zainab tace

"Menene wai?". Hannu Zainab tasa ta nuna mata TV tabi hannun Zainab d'in da kallo, Ido ta k'walalo
kamar zasu fad'o k'asa tsabar yadda ta fito dasu.




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).
Jama'a kuyiwa Habeeb uzuri baku tunanin ta sanadiyyar d'auke Seeyamah dayayi komai zai bayyana?
duk inda na lek'a anata yadawa Habeeb Gashua magana 😅 easy guys mubi komai a sannu har zuwa
lokacin da zamu gano bakin zaren, Gashua a cigaba da kidmashin Mom sayyeed da Aunt jamila na
bayanka 😝😂.

Godiya mai tarin yawa a gareku reader's alkhairin ALLAH yakai muku a duk inda kuke jazakumullah
khair 💗💗💗.



No 19.



Batasan lokacin data saki littafin hannunta ba cikeda tsantsar mamaki da al'ajabi basuda bambanci a
komai na halitta hatta dimple d'in da Seeyamah take dashi itama Heedayahn tana dashi a fuskarta
wannan lamari akwai d'aure kai da rikitarwa ta sani cewa akwai mutane dayawa masu kama da junansu
ako ina amma wannan dai kamar tasu ta b'aci ta yadda idan d'aya ya b'ata za'a iya kama d'ayan ace
shine he's totally confused ta rikice da ganin wannan baiwar ALLAH da ake haskawa.

"Aunt Ramlah fito kiga wani abin mamaki please kafin a d'auke". Zainab ta k'walawa Aunt Ramlah dake
kitchen tana had'awa Abban Nu'aym fruit salad zata kai masa bedroom d'inshi saboda bayacin abu mai
nauyi da dare, fitowa tayi tana mitar me zata nuna mata take k'wala mata wannan uban kiran ko knife
d'in hannunta bata samu ajiyewa ba.

"Aunt Ramlah kalli TV kigani dan ALLAH wata kamar Heedayah wai ta b'ata ana cigiyar ta". Zainab tace
tana nunawa Aunt Ramlahn plasma d'in dake manne a jikin bango, itama d'in dai idon ta zaro na mamaki
har wuk'ar hannunta na shirin fad'uwa wannan abu da ban al'ajabi yake.

"ALLAH buwayi gagara misali, kuga fa wani ikon ALLAH wllhy badan ina ganin Heedayah tsaye a gabana
ba da ba abinda zai hana ince itace wannan ALLAH mai hikmah". Aunt Ramlah tayi maganar tana rik'e
bakinta.

"Wllhy ko nima Aunt tunda basuda maraba da Heedayahn kiga fa Aunt har wannan dimple d'in iri
d'aya". cewar Zainab tana kai hannu kumatun Heedayah inda nata dimple d'in yake, kallon Heedayah
Aunt Ramlah tayi tace

"Heedayah ya kikayi shiru bakice komaiba?".

Wani nannauyan numfashi Heedayah ta sauke tace

"To ai nikam narasa tacewa Aunt Ramlah ki dubafa babu wani bambanci da za'a iya gane tsakanina da
ita komai iri d'aya".

"Ikon ALLAHn kenan ai Heedayah mai yin yadda yaso kuma a lokacin dayaso ku cigaba da karatun ku
nima bari inje in k'arasa aikina". Aunt Ramlah tace tana komawa kitchen d'in can k'asan ranta kuma tana
hasaso abubuwa da dama, sukuma nan suka zauna suna k'ara maida maganar hat yanzu basu bar
mamaki ba.

Bayan Aunt Ramlah ta gama had'a fruit salad d'in ta zubashi a wani madaidaicin bowl mai kyau ta d'ora
kan tray da spoon ta nufi bedroom d'in maigidan nata har lokacin da tunanin datake a ranta.

A zaune ta sameshi kan sofa sanye da jallabiyyah ruwan k'asa shima kuma news d'in yake kallo, bakinta
d'auke da sallama ta shiga ya d'ago kai yana amsa mata wajen shi ta k'arasa ta janyo wani k'aramin stool
ta d'ora bowl d'in akai ta zauna kusa dashi daga gefen gado tana fad'in

"Abban Nu'aym kaima labaran kake gani kenan kaga wani abin mamaki da aka hasko yanzu?".

Kai ya gyad'a yace

"Bakiga yanayi na ba, gaba d'aya mamaki yagama kasheni ALLAH mai yadda yaso yarinya saikace
Heedayah".

"Wllhy kuwa Abban Nu'aym abin akwai d'aure kai a ciki zuwa yanzu nafara tunanin anya Heedayah ba
twins bane ba kuwa?".

"Tabbas kuwa nima nayi wannan tunanin gaskiya ALLAH ne ya barwa kansa sani amma kar wannan
yasa kuyi wata magana har tasan halin da ake ciki ki k'yaleta kawai".

"Insha ALLAH! na sake ma nayi mata magana makamanciyar wannan ai na shiga uku wajen Umma da
Baba daidai da rana d'aya basa son abinda zai tada maganar nan har Heedayah ta fahimci wani abu".

Kai kawai Muhammad yake gyad'awa yana k'ara ganin girma da k'imar surukan nashi ko shi badan wani
irin sirri da ubangiji ke kimsawa tsakanin miji da mata ba da har Ramlahn ta fad'a masa da bazai tab'a
sanin Heedayah ba k'anwar Ramlahn bace da suka fito ciki da itaba tsabar yadda basa bambanta su da
y'ay'an da suka haifa saima fifitata da sukeyi akan yaran nasu da suka haifa da cikinsu, bowl d'in ta
d'auka ta mik'a masa ya fara shan fruit salad d'in.



★★★_______★★★

A ranar kuma a daidai wannan lokacin bayan kammala labaran da aka gabatar na hangi wasu miji da
mata daka gansu zakaga jikinsu a sanyaye yake har lokacin mamaki da d'imbin al'ajabin abinda suka gani
yanzu bai sakesu ba wanda hakan ya nuna har akan fuskokin su.

Mutumin wanda ak'alla yabawa shekaru hamsin baya ya kalli matar tashi wadda a k'iyasin shekarun ta
zasuyi arba'in da biyar.

Wani nannauyan numfashi ya sauke kafin yace

"Lallai Hajiya inaji a jikina wani babban al'amari yana doso mu wanda bamu san ko meye ba".
"Cikin raunin murya tace

"Ni kaina Alhaji inaji a jikina kamar wani abu daya shafi JAWAHEER zai bayyana yanzu dan ALLAH wazai
dubi yarinyar da akayi cigiyar ta yanzu yace ba Jawaheer d'inmu bace ba alamu sun nuna ita d'in twins ce
irin identical d'in nan inaji a jikina wannan yarinyar da aka haska jinin Jawaheer ce ina tsoron ranar da
zamu rabu da Jawaheer Alhaji". ta k'arasa maganar tana sakin kuka wanda ya dad'e yana cinta tana
matuk'ar son Jawaheer kamar ranta kamar yadda shima maigidan nata yake mutuwar k'aunarta, hannu
yasa ya rungumota ta gefenshi cikin taushin murya da rarrashi yace

Bazamu tab'a rabuwa da y'armu ba Saudah bana fatan in riski ranar saidai a matsayin mu na iyayena
kuma masu k'aunar ta dole abin farin cikine a garemu ace ta had'u da asalin iyayenta na gaskiya karki
damu kanki muna tare da Jawaheer har k'arshen rayuwar mu insha ALLAH". Ya k'arasa maganar yana
goge mata hawayen idanunta yana cigaba da fad'a mata tausasan kalamai na kwantar da hankali ta lafe
sosai a jikinshi tana tuno abubuwan da suka faru shekaru sha takwas da suka wuce a lokacin da suka
tsinci jaririyar sabuwar haihuwa.

Nan gaba zamuji su waye wad'annan bayin ALLAHn Alhaji Mansur Jik'amshi da Hajiya Saudah.



Had'add'en bedroom ne mai d'auke da madaidaicin gado da k'atuwar wardrobe sai tamfatsetsen
mirror wanda aka cika samanshi taf da kayan makeup da turaruka,gaba d'aya kayan d'akin kalar light
blue ne da white har curtains da sauran abubuwa da ake k'awata d'aki dasu, an kashe fitilun d'akin sai
bedside lamp dake kunne wadda ta bada kalar dark blue.

Kyakkyawar matashiyar budurwa na hanga kwance akan gadon dayasha tattausan bedsheet tayi shirin
barci cikin riga da wando masu kauri kalar peach mai haske ta rufe k'afafunta zuwa kan cikinta da
blanket mai laushi ba komai a kanta hakan ya bani damar ganin k'ananun kalbar dake kanta wadda ta
sauka har kan kafad'unta, rik'e take da had'add'iyar wayarta tana ta faman danne danne tana dariya da
alamu tana matuk'ar jin dad'in yanayin datake ciki chatting take da k'awayenta na school cikin nishad'i
kiran Fauziyyah ne ya shigo wayar tata a lokacin k'awar tace sosai tare suke school, picking tayi takai
kunnenta tareda fad'in

"Hello Babe ya daren?".

"Banza kina ina muna nan yanzu muka gama ganin abin mamaki a NTA news kinsan Yah Abdul da shegen
son labarai TVn d'akin shi kuma tasamu matsala shine fa yazo falo ya kunna a TVn falo".

"Wani abun kuka gani a news d'in?". cewar Jawaheer tana k'ara jan blanket d'in sama.

"Hmm bari kawai bestie wallahi wata aka hasko ana cigiya kinsan ALLAH badan d'azun nan muka rabu
dake ba dasai ince kece kika to dan dai ita wannan ance kwana biyu da b'atan nata kamar kefa Jawa
wllhy ina rantse miki bakuda maraba da ita su kansu y'an gidanmu sunyi mamaki wai anya bake bace
kuwa nace musu bake bace gaki a online ma lokacin muna magana".
Baki Jawaheer ta d'an tab'e cikin yatsina tace

"ALLAH ya bayyana ta amma nasan kawai shegen kwakwazo ne irin naki amma ya za'ayi ace komai
namu iri d'aya haba saikace a film ke nifa irina ni kad'ai ce a duniya".

"Ba zaki gane bane k'awata amma ke kanki da kin gani saikin razana wllhy nidai ban tab'a ganin abin
mamaki irin wannan ba amma ba'a mamaki da ikon ALLAH".

K'aramin tsaki Jawaheer taja tace

"Naji to go and sleep Hajiyata barci nakeji". bata jira cewar Fauziyyah ba ta katse kiran ta santa da
nanata magana yanzu idan ta barta zancen dazata isheta dashi kenan shiyasa tayi maganinta duk da har
yanzu bata gama yadda da maganar Fauziyyah ba kawai dai taga wadda suke yanayi da ita shine zata
dameta da maganar komai nasu iri d'aya ta yaya hakan zata kasance???.



10 / 21