Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 21

3K to 6K   out of 61.8K words

mace hankalin Ibraheem ya tashi sosai ga waya da Afeefah ke masa akai akai tana k'ara
jaddada masa irin son datake masa taji shiru kuma har yanzu bawani labari dan ALLAH karya gujeta ya
taimaka yadawo gareta, hakan ba k'aramin k'ara d'aga hankalin Ibraheem yayi ba ya cigaba da bin
Malam Ahmad da magiya da rok'on ya k'yaleshi har mutanen da Malam Ahmad d'in yake ganin
mutuncinsu duk ya had'ashi dasu amma fur Malam Ahmad yak'i amincewa k'arshe dai da Ibraheem yaga
haka saiya yanke shawarar tafiya batare da yardar mahaifin nashi ba dan haka ya tattara duk wasu
muhimman abubuwan shi na harkar kasuwancin dayake yayi hayar wasu mutane daga nan suka tafi
Dubai nema masa auren Afeefah.

Ba b'ata lokaci kuwa akayi komai aka gama yayi k'ok'arin yin duk wasu al'adunsu wanda saida jarinshi
ya girgiza saboda yadda tsarin neman auren nasu yake akwai kashe kud'i amma dayake SO ya rufe masa
ido yasa duk baiji k'yashin yin komaiba kuma ko d'ar baiyiba wajen yinsu saboda ALLAH yayi masa lud'ufi
cikin sana'ar shi arzik'inshi kuma a lokacin yafara hab'aka sosai kuma a yadda yakejin zuciyarshi koda
bashida komai ma zaisan duk hanyar dazai bi yasamu abinda zai mallaki Afeefah dashi.

Daga can kuma gida Nigeria Malam Ahmad da sauran ahalin gidan suna cikin damuwa da rashin jin
dad'in abinda Ibraheem yayi Yaya Sulaiman da Yaya Adam sunso binshi Malam Ahmad ya hanasu yace su
k'yaleshi kawai a yanzu koda sunje bazai sauraresu ba saboda giyar soyayya na d'ibanshi kuma bazai
yimasa baki ba koya furta wata magana marar dad'i a kanshi ba.



Maryam Ibraheem Aleeyu💝




*EL--HABEEB*💥



©️Oum Hanan.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)



No 3.



Yasani komai daren dad'ewa zai nemesu dan haka kullum cikin kwantarwa da mahaifiyarsu hankali yake
saboda yadda ta d'aga hankalinta sosai gani take tamkar shikenan fa d'anta ya tafi kenan bazai k'ara
waiwayar gida ba daga k'arshe tasawa zuciyarta dangana ta cigaba da binshi da addu'ar ALLAH ya kare
mata shi a ko ina yake a matsayinsu na iyaye wanda ko yaya suka furta kalma mara dad'i a kanshi saita
bishi ta nakasta rayuwar shi bai kamata suyiwa yaronsu mugun baki ba ya k'ara lalacewa.



Sosai akasha shagalin bikin Ibraheem Ahmad Gashua da Afeefah Habeeb Al-Hussain naira tayi kuka
kasancewar harkar ta masu arzik'i ce dan shima mahaifin Afeefah mai kud'i ne sosai.

Bayan kwanakin da aka d'iba ana shan shagalin biki amarya ta tare a gidanta na wani abokin
kasuwancin shi balarabe daya bashi aro kafin ya mallaki nashi plat house ne wanda aka b'ata lokaci
wajen tsarashi kuma ya tsarun an k'ayatashi sosai. Nan fa aka shiga cin amarci kowa yana k'ok'arin
farantawa d'an uwanshi rai da nuna irin tsantsar soyayyar da sukewa junansu Afeefah na shan kulawa da
tarairaya tsabarsu a wajen Ibraheem duk abinda yasan zai faranta mata shiyake yi haka itama a nata
b'angaren.

Shekarar su d'aya da aure ALLAH ya bata ciki kuma har lokacin bai tab'a tunanin waiwayar gida ba
kuma ko sau d'aya bai tab'a gwada koda kiran waya ba kawai matarshi yasa a gaba musamman data
samu cikin nan sai kulawar ta ninka ta baya fiye da tsammanin mai karatu har zuwa lokacin da ALLAH ya
sauketa lafiya ya azurtasu da samun k'aruwar d'a namiji wanda gaba d'aya zubinshi da kamannin shi na
asalin jinin larabawan ne babu ta inda ya d'auko mahaifinshi komai na mahaifiyarshi ne. Fad'ar irin farin
ciki da murnar da wannan ahali sukayi ma b'ata baki ne amma tabbas sunyi matuk'ar farin cikin zuwan
jaririn duniya musamman Alhaji Ibraheem Gashua daya d'auki son duniya ya aza kan jaririn nan da ranar
suna ta zagayo yaro yaci sunan mahaifin Afeefah wato *HABEEB* ba k'aramin dad'i Afeefah taji ba a
lokacin saboda karar dayayi mata yasawa first born son d'insu sunan babanta ta rungume shi tana fad'a
masa wasu kalmomi masu tsada na soyayya da nuna jin dad'i da godiya duk da larabci take maganar
wanda yakejin yaren sosai a yanzu saboda zama da Afeefah, rungumeta ya k'ara yi sosai a jikinshi yana
murmushi na jin dad'in ya faranta mata.

Ta b'angaren Habeeb Al-Hussain ma wanda suke kira da Abi yaji dad'i k'warai da gaske na samun
takwara dayayi tuni yaji yaron ya k'ara kwanta masa cikin ranshi tuni ya shiga yimasa kyaututtuka na
alfarma abinka ga wad'anda sukaci suka tada kai da naira. Ba k'aramar dukiya aka salwantar ba wajen
sunan yaron ga kyaututtuka dayake ta faman sha tako ina daga b'angaren kakannin shi na wajen uwa
kowa son yaron yake da nuna masa k'auna.



Afeefah ta cigaba da rainon yaronta cikin tsananin kulawa da taka tsantsan kan duk abinda zai cutar
dashi ya taso cikin gata kowa ji dashi yake. Yarone daya taso da mugun k'ok'ari fikrah, zalak'a, da tarin
baiwa suka fito k'uru k'uru tun yana k'ananun shekarunshi abu d'aya zaka fad'a masa ya d'aukeshi a
kanshi koda da wasa ka fad'a kuwa musamman dayake samun k'warin gwiwa daga mahaifanshi dasu
Abi.

Saida Habeeb ya shekara biyar sannan Afeefah wadda yake kira da Ummi ta k'ara wata haihuwar
wannan karon mace tasamu wadda suka rad'a mata suna Mashhoodah, sai a lokacin Ummi ta fara
tuntub'ar Ibraheem Gashua wanda Habeeb ke kiranshi da Abbu a yanzu batun zuwa gida da nuna masa
lallai ya kamata ace ya waiwayi gida haka yaje yaga halin da suke ciki ya kuma gabatar dasu a matsayinsu
na iyalinshi tunda ga zuri'a sun fara tarawa, mirsisi Abbu yayi yace sam ba yanzu zai komaba idan ya
tashi tafiya ma saidai kawai yace ta shirya su tafi amma dai ba yanzu ba ya fad'i hakan ne saboda tsoron
komawa dayake baisan da irin kalamin dazai tunkari iyayen nashi ba idan ya koma yasani shi babban mai
laifi ne a wajensu ya bijire musu yayi fatali da maganar da suka gindaya masa saboda soyayyar Afeefah
data rufe masa ido yana tsoron komawa saboda baisan yadda zasu karb'eshi ba amma hak'ik'a cikin
shekara d'aya data wuce zuwa yanzu yana yawan tunanin gida yakan yi mafarkinsu sosai tabbas yana
son komawa k'asar sa ta haihuwa. Wannan abinda ya fad'a d'in shine harya haifar musu y'ar hatsaniya
tsakanin shi da Ummi wanda wannan shine karo na farko a rayuwar aurensu dasuka samu matsala dan
sosai yake biye mata sai abinda takeso akeyi a ganinta lokaci yayi daya dace ace taga mahaifarshi,
iyayenshi y'an uwanshi dama tushenshi gaba d'aya.

Itama saitayi fushin bata k'ara tayar masa da maganar zuwa 9ja ba shima bai k'ara yimata maganar ba
ta zubawa dai sarautar ALLAH ido taga iya gudun ruwanshi.



10yrs After.

Habeeb yanada shekaru goma a duniya yayin da Mashhoodah take da biyar ALLAH ya d'auki ran Abi
sakamakon ciwon ciki daya turnuk'e shi lokaci d'aya rai yayi halinshi mutuwar data jijjiga familyn su da
sauran abokan arzik'i musamman ma iyalinshi da sukafi kowa jinta su Ummi sunyi kuka kamar ba gobe
mutuwar uba wani babban gib'i ne a rayuwar mutum wanda duk wani gata da za'ayiwa mutum shi
bazaikai wanda mahaifi zaiyiwa d'anshi ba daga k'arshe dai suka bishi da addu'ar samun rahmar ubangiji
da dacewa.

ALLAH kaji k'anmu badan halinmu ba kayi mana rahma badan aikinmu ba dan alfarma da martabar
sayyadil wujuud (S.W.A.)👏🙏



★...★...★

Tun bayan rasuwar Abi Abbu yafara ganin y'an canje canje a rayuwar shi especially ta b'angaren
kasuwancin shi yaja baya sosai tamkar Abi ne ya tafi da rabin arzik'in nashi ga ciwon hawan jini daya
kamu dashi saboda yadda ya saka tunanin gida da iyayenshi a cikin ranshi ga wasu mafarkai dayake
game da Malam Ahmad wanda ya kasa gane kansu hakan ya k'ara haddasawa jikin nashi rikicewa sosai
k'warai da gaske yakeda buk'atar yasa ahalinshi a idonshi, a lokacin Ummi ta k'ara bijiro masa da
maganar zuwa 9ja duk da alk'awarin data d'auka a baya cewar bazata k'ara yimasa maganar zuwa
Nigeria ba amma yanayin yadda taga mijin nata tasan damuwarshi dai bata wuce ta gida. Sam bai mata
musu ba a lokacin dan haka suka shirya sukaje suka samu mahaifiyar Ummi da maganar a lokacin
shekara d'aya kenan da rasuwar Abi, sunyi zaton zasusha fama da ita amma ga mamakin su kai tsaye
saita amince dama tuni taga dacewar hakan.

Nan da nan suka fara shirin tafiya Nigeria Abbu farin cikinshi ya kasa b'oyuwa ta gefe d'aya kuma cike
yake da tararrabin irin amsar da zasuyi masa.

Cikin y'an kwanaki ya kammala musu duk wasu shirye shiryen tafiya suka d'aga zuwa 9ja k'asarshi ta
haihuwa bayan sama da shekaru goma daya d'auka baya nan.

Abinda ya tarar ne a ranar da suka iso yayi matuk'ar girgizashi wato labarin rasuwar Malam Ahmad
daya samu shekara d'aya data wuce lokaci d'aya kenan data Abi yayi kuka tamkar ranshi zaibar jikinshi,
dana sani da d'imbin nadama suka shigeshi ALLAH bai k'addara saduwarsu ba bare harya nemi gafararshi
hak'ik'a rasuwar mahaifin nashi ta dakeshi ya zube gaban Hajiya Inna yana kuka da neman yafiyarta
tsakanin d'a da uwa sai ALLAH saitaji duk wani fushi datake dashi na tsahon shekarun ta nemesu ta rasa
ta rungume d'anta wani irin dad'i na ratsa zuciyarta, hakama sauran y'an uwan nashi da duk sukazo
gidan suka rungume shi cikin farin cikin dawowarshi gida, anan Hajiyan ke sanar dashi ai kafin rasuwar
mahaifin nasu yace ya yafe masa duniya da lahira wannan kalma ba k'aramin dad'i tayiwa Abbu ba dama
damuwarshi d'aya mahaifinshi daya tafi da tabon b'acin ranshi.

Bayan komai ya natsa ne ya gabatar musu da Ummi da yaransu biyu da ALLAH ya basu hannu bibbiyu
suka amshesu basu nuna musu wani abu ba Hajiya ta rungume y'an jikokinta tanajin dad'i sudai kallonsu
kawai suke cikin rarraba idon ganin wasu bak'in fuska da basu sansu ba gasu kuma bak'ake ba yadda
suka saba ganin farar fata ba.

Da k'yar aka gaggaisa da Ummi saboda ba hausa danma Abbu yakan yimata jefi jefi hakan yasa tasan
wasu y'an abubuwan kamar gaisuwa da sauran maganganu marasa tsayi.

Goggo Fatu d'aya daga cikin k'annen shi mata guda hud'u ita kad'ai ce Ummi ta kula tun zuwansu tana
binta da wani irin kallo na tsana dan a ganinta Ummin itace silar dayasa d'an uwansu yabarsu na tsahon
shekaru batare daya k'ara waiwayar suba dan haka taji da Ummin da yaranta duk ta tsanesu bata
k'aunar su.

Sauran kuwa ba ruwansu sun sakarwa Ummi fuska sosai Hajiya ma ta jata a jikinta sosai hakan ba
k'aramin dad'i yayiwa Abbu ba nan da nan yaji duk wasu sauran y'an ciwace ciwace sun tafi dama
tunanin gida ne da kuma zullumin yadda dangin nashi zasu amshe shi alhmdulillah kuma dayake masu
ilmi ne da kuma aiki dashi yasa basu nuna masa komaiba sun d'auki hakan a matsayin k'addarar shi.

Bayan sun huta na y'an kwanaki suka shiga yawon zaga dangi na kusa dana nesa yana gabatar musu da
iyalinshi kuma ko ina sukaje ana nunawa Ummi da y'ay'anta soyayya tuni itama taji dangin mijin nata sun
shiga ranta dan sunsan abinda suke k'warai da gaske ga karamchi da girmama d'an adam.



Gaba d'aya sai kasuwancin Abbu ya sake dawo dashi Nigeria dan bayan dawowar tashi arzik'in nashi
saiya k'ara hab'aka da d'aukaka.

Alhaji Sulaiman Gashua babban yayansu shiya bashi k'aton gida mai kyau yace yafara zama da iyalinshi
anan kafin ya gina nashi yadda zaiyi nashin a nutse daga nan suka cigaba da zama anan tare dasu ya
cigaba da ginin daya fara anan kusa da gidan Alhaji Adam Gashua.

Ummi batada matsalar komai sai Goggo Fatu data takura mata itada yaranta har gida take zuwa taci
mata mutunci duk da bawai sanin ma metake fad'a tayi ba amma dai tasan zagine da cin mutunci, bata
tab'a bari Abbu yasani ba tunda dama bata zuwa sai lokacin da baya nan ta rasa abinda ta tsare mata
hantara da zagi kuwa ba wanda bata yiwa Habeeb da Mashhoodah abin baya yiwa Ummi dad'i amma
batada yadda zatayi.
Makaranta mai tsada aka nemarwa su Habeeb suka cigaba da karatun su, har yanzu dai Habeeb yana
nan da wannan brain d'in tashi da d'auke abu tafar d'aya.



Mrs Salees Mu'az 💝




*EL--HABEEB 💥*



©️Oum Hanan.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)



No 4.



Hakan yasa yana shiga school d'in sunanshi yayi fice daga malaman har d'aliban sonshi suke musamman
dayake kyakkyawa balarabe wasu ma kawai kyawun nashi sukeso dan haka kowa ya shiga neman yadda
zai k'ulla alak'a da Habeeb.

Zamansu cikin hausawa yasa suka fara jin hausa sosai saidai abinda ba'a rasaba. Haka zamansu ya
cigaba da tafiya har Abbu ya kammala ginin daya fara suka koma ciki babban gida ne mai kyau da tsari da
aka tsarashi sosai. Tun daga kan Mashhoodah Ummi bata k'ara haihuwa ba saida aka d'ebi kusan wasu
shekaru biyar d'in sannan ubangiji ya nufeta da k'ara samun wani cikin sunji dad'i kuma sun yiwa ALLAH
godiya daya k'addara musu samun wata haihuwar ta cigaba da rainon cikinta har zuwa lokacin data
haihu ta k'ara samun wata y'a macen taci sunan Hajiya wato Karimatu sai suke mata alkunya da Nihlah,
Ummi tana yawan zuwa Dubai akai akai dan kaiwa mahaifiyarta ziyara da k'aninta Muhseen.



Bayan wasu shekaru.

Habeeb ya kammala karatunshi na secondary school ya fito kuma da kyakkyawan sakamako wanda
Abbu yaji dad'i sosai harya bashi zab'in irin k'asar dayake so ya cigaba da karatunshi kai tsaye yace Dubai
yakeso yaje dariya kawai Abbu da Ummi sukayi a lokacin dan sunsan dalilin dayasa ya zab'i Dubai d'in bai
wuce shak'uwar dake tsakaninshi da Maman Ummi ba ko ziyara zasu kai musu yafi kowa murna. Tashin
farko da Abbu ya k'ara tambayar shi me yakeso ya karanta a can d'in bai wani dogon tunani ba yace irin
na Abbun wato business shiyake ra'ayi, jinjina kai kawai Abbu ya dinga yi yanajin dad'i anan suka bishi da
addu'ar samun nasara da sa'a shida Ummi, k'arin jin dad'in nasu ma yaron nasu basai ya zauna a Hall ba
tunda ga gidansu Ummi shikam gida yaje ai karatun.

Tun daga lokacin Abbu ya shiga yiwa Habeeb shirye shiryen tafiya Dubai shiri yake masa sosai har
lokacin tafiyar shi yayi ya d'aga zuwa k'asar Dubai cikeda jin k'warin gwiwar yin abinda ya kaishi k'asar.

Fatan nasara HABEEB GASHUA.



Gidansu Ummi nan ya sauka daga nan yake zuwa school d'in har lokacin bashida yawan magana miskili
ne sosai badai ka ganshi yana hira yana raha da mutane ba saidai ya keb'e kanshi kullum cikin karatu
yake d'alibai dayawa a makarantar sunyi zaton kurma ne gashi ba wanda yake kulawa yafi gane yayi
zamanshi shi kad'ai wani d'an Nigeria ne da suka shiga makarantar kusan lokaci d'aya Auwal Mahmood
Azare shiya dinga shige masa yanason suyi abota da Habeeb d'in farko sam baya kulashi saidai yazo ya
zauna a inda yake ya k'araci surutunshi amma uffan Habeeb bazaice masa saidai yagaji ya tashi sai daga
bayane sannan ya fara d'an kulashi shima bawani sosai ba baya baya.

Ya cigaba da karatunshi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa su Abbu na yawan kawo masa ziyara shima
kuma idan suka samu hutu yana zuwa ganin gida.



A gurguje.

Bayan wasu shekaru Habeeb ya kammala karatunshi cikeda tarin nasarori wanda hatta makarantar
saidata bashi lambar yabo ta jinjina masa kuma. Akwai babban kamfani a k'asar wanda suke kasuwanci
da k'asashe daban daban su suka rok'i alfarmar ya zauna yayi aiki dasu tun a lokacin kai tsaye baice musu
zaiyi ba bai kuma bazaiyi ba yace dai zaiyi shawara da iyayenshi duk abinda suka zartar shi zaiyi.

Bayan dawowar shi yasamu Abbu ya sanar dashi abinda kamfanin sukace Abbu yaso Habeeb ya zauna
yayi aiki a nashi kamfanunuwan ya taimaka masa amma abin alfaharinshi ne ace yaronshi yana aiki a
wancan kamfanin na Dubai dan ya sanshi babban kamfani ne sosai kuma a hakan ma su suka nemi
dayayi aiki dasu gaskiya yaron nashi mai sa'a ne dan haka kawai ya umarci Habeeb d'in ya koma yayi aiki
dasu d'in ALLAH ya taimaka.

Bayan ya d'an huta ya k'ara shiryawa yayi sallama da iyaye da abokan arzik'i ya k'ara komawa Dubai da
shirin yin aiki.

Sunji dad'in komawarshi sosai suka bashi gida da had'add'iyar mota mai tsada ya amshi motar dai
gidan kam yace yanada inda zai zauna ga k'aton office d'inshi dayaji kayan alfarma bashi dai da matsalar
komai alhmdulillah nan da nan ya k'ara fasowa gari tuni y'anmatan larabawa suka fara kai masa hari
saidai ko a kwalar rigarshi ba abinda yasha masa kai ko kallo basu isheshi ba hakan yasa wasu dayawa
suke ganinshi mai bala'in girman kai da fariya wanda kuma a zahiri ba haka bane kawai dai shi haka
ubangiji ya halicceshi sam bai cika son shiga cikin jama'a ba yafiso ya dinga kad'aicewa shi kad'ai gashi
bayason surutu ko hayaniya.

Su Ummi sunso zuwa bayan yafara aikin kasancewar sun d'an kwana biyu basuje ba saikuma taji bikin
k'aninta Muhseen da za'ayi ya kusa dan haka suka hak'ura sai lokacin da za'ayi bikin sannan sukaje
wannan karon harda Hajiya Inna aka tafi suka sha bikin Muhseen da amaryar shi Abeedah, daga nan
suka wuce sukayi umrah sannan suka dawo Nigeria.



Bayan dawowar su da y'an watanni ne akayi bikin Mashhoodah inda tasamu mijin cikin y'an uwa dan
babban d'an Alhaji Adam ne Musaddeeq wanda tun dawowar su k'asar bayan tafara girma yaji yarinyar
ta shiga ranshi sosai baidai bayyana bane sai data kai munzalin fara saurarar samari sannan ya fito ya
shiga cikin jerin y'an takara kuma ALLAH yayi shine mijin nata akasha biki iyaye da y'an uwa kowa na
murnar wani zumunchin da aka k'ara had'awa. Goggo Fatuu taso wargatsa al'amarin amma ALLAH bai
bata iko ba gashi dangi kowa yayi mata caa hakan yasa tayi shiru ta daina sukar lamarin.



"Baifi shekara d'aya da fara aikin ba ALLAH ya yiwa Abbu rasuwa, mutuwar data tab'a mutane da dama
kasancewar shi mutumin kirki ga taimakon al'ummar musulmi marasa k'arfi duk inda gidan marayu suke
yakan sa a nemosu dan ya taimaka musu, katsam sai waya Habeeb yaji wai Abbunshi ya rasu zuciyarshi
ta girgiza k'warai da gaske da wannan labarin daya samu saiya dinga tuno irin wayoyin dasuke dashi a
kwanakin kullum magana d'ayace dai ya dinga taimakon na k'asa dashi ya taimaki marayu dan su d'in
masu rauni ne suna buk'atar masu kulawa dasu zuciyarshi ta k'ek'ashe ko d'igon hawaye babu sai kukan
zuci dayake wanda yafi na fili dan a ganinshi shi akayiwa rasuwar saboda shi yayi rashin mahaifi mai
sonshi da k'aunarshi, har a lokacin Goggo Fatu ta samu abinyi ganin a gabanshi aka fitar da gawar Abbu
amma ba d'igon hawaye a idanunshi wai dama zubin marasa imani da tausayi gareshi amma mahaifinka
ya mutu ka gaza yin kuka kamar yin kukan shi zai dawo da mutum babu wanda yabi ta kanta a lokacin
kowa na cikin alhinin mutuwa.



Bayan rasuwar Abbu da d'an wani lokaci Habeeb ya koma bakin aikinshi cikeda kewar Abbunshi
shikenan sun zama marayu a yanzu, gaba d'aya sai Ummi tazama abar tausayi a lokacin takan tuna irin
zaman da sukayi dashi cikin kwanciyar hankali da mutunta

2 / 21