Author : Oum Hanan Category : African Stories & Novels
*EL--HABEEB*💥
©️Oum Hanan
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Da sunan ALLAH mai rahma mai jin k'ai tsira da amincin ALLAH su k'ara tabbata ga shugaban mu ANNABI
MUHAMMAD sallallahu alaihi wa alihi wasallam.
Yadda nafara wannan book din lafiya ALLAH ya bani ikon gamawa lafiya.
Duk wanda yaci karo da wani gyara ko kuskure a cikin book din nan ya nemeni ta wannan number
09139964697 k'ofa a bud'e take nagode.
Writer of
*DANA SANI*
*SURAYYAH*
*NIDA YAH SAYYADINMU*
*HAD'IN ALLAH*
*D'AN BASAJA*
*KAUTHAR*
*DR SAIF*
*KALLON KITSE*
*WATA SOYAYYAH*
No 1.
Shimfid'a.
Kwanciyar shi ya k'ara gyarawa a faffad'an gadon nashi wanda yaji tausasan shimfid'u na alfarma a
karo na ba adadi yana k'ara k'ank'ame pillown dake rungume a k'irjinshi cikeda shauk'in samun nasarar
dayayi a yau d'in nan zata bud'e masa fuskarta yagani, har wani tsuma yake yana sakin lallausar
murmushi akan kyakkyawar fuskarshi tareda k'ara ware manyan manyan idanunshi dan yaji dad'in ganin
fuskar tata saidai kash kafin takai ga bud'ewar kamar wanda aka mintsina yayi saurin tashi daga
nannauyan barcin dayake zumbur ya tashi zaune yana wuwwurga idanunshi gefe da gefenshi dako ina
na d'akin tamkar wanda yake neman wani abu. Kanshi ya dafe da duka hannaye biyun cikeda b'acin rai
tareda rufe idanunshi gam yana sauke numfashi wannan masifa dame tai kama? ace sama da shekara
biyar yana wannan mafarkin daya rasa ta inama zai fassara shi kullum ta ALLAH saidai idan bai kwanta ya
rufe Ido da sunan yin barci ba ya zamar masa kamar k'aidah ne idan baiyiba bayajin dad'i abin ya zamar
masa bala'i ya rasa ta inda zai b'ullowa al'amarin shin wannan yarinyar dake zuwa masa wacece ita?
meye alak'arta dashi datake addabar rayuwarshi haka? a ina take? a ina zai ganta? matacciya ce ko
rayyaya? meyasa take zuwa masa cikin barcinshi ta hanashi sukuni? tarin tambayoyin da har yagaji
dayiwa kanshi su batare da har yanzu yasamu amsarsu ba to waye ma zai amsa masa su? bayan ba
wanda yasan yanayin mafarkin, sosai yake k'ara hango kyawawan idanun yarinyar wanda su kadaine
suka bayyana a fuskarta sai tudun dogon hancinta da shima ya kasa b'oyuwa ta cikin bak'in mayafin data
rufe fuskar tata dashi. Wasu irin idanuwa ne farare k'al masu mugun kyau da shek'i ga wani k'yalli da
cikin k'wayar idanun nata keyi kamar wadda hawaye suka fara tarar mata a ido, dad'in dad'awa kuma
yanayin shape d'in idanun nata da bai tab'a ganin makamantan su ba saboda yadda ubangiji ya tsara
mata su.
A hankali ya bud'e idanunshi da launinsu ya d'an fara canzawa kad'an cikeda damuwa ya sauka daga
kan gadon ya nufi wata k'ofa wadda nake kyautata zaton bathroom ne dama boxer ne kawai a jikinshi
hakan yasa kai tsaye ya wuce ciki da alamu wanka zaiyi.
Mintuna k'alilan ya fito daga bathroom d'in ya d'aure k'ugunshi da babban towel sai k'arami dake
saman kanshi wanda yake goge sumar kanshi zuwa fuskarshi da cikin kunnuwan shi, wajen k'aton mirror
dake cikin bedroom d'in ya nufa wanda yake shak'e taf da manya manyan turaruka masu masifar
k'amshi da mayuka masu matuk'ar tsada sama sama ya shafa lotion ya taje lallausar sumar kanshi da
zagayayyen gemunshi ya shafa musu mai sannan ya nufi wata k'atuwar clothed ta jikin bango wadda ta
kusan mamaye duka bangon ya bud'e kayane gasu nan iya ganin mutum shaddoji ne voil, yadika, suits da
sauran k'ananun kaya na kamfanunuwa kala kala da sukayi fice a duniya, jeans ya d'auko dark blue da
riga body hook mara nauyi light blue ya shirya cikinsu sosai kayan sukayi mugun amsarshi wajen takalma
yaje wanda suma gasu nan lodi lodi tamkar shagon siyar dasu farin boot ya d'auka ya zauna gefen
tamfatsetsen gadon ya saka yaje wajen ajiyar agoguna ya d'auki wani bak'i k'irar kamfanin Gucci ya
d'aura, wajen mirror yakoma ya feshe jikinshi da sanyayan turaruka masu matuk'ar k'amshi da sanyaya
zuciya daga nan ya fice daga bedroom d'in bayan ya d'auki wayoyinshi.
Kai tsaye cikin gidan ya nufa dan yasan Ummi nacan na jiranshi musamman yau daya d'anyi late ba
kamar lokacin daya saba shiga gidan ba da safe.
Da sallama ya shiga makeken falon wanda yaji kayan k'awa masu tsada tako ina sai k'yalli da walwali
yake ga k'amshin turarukan wuta had'i da air freshener spray da aka k'ara dashi. Cikakkiyar dattijuwa
mai cikar kamala na hango kan d'aya daga cikin kujerun falon tasha adonta cikin wani dakakken lace blue
black da torch d'in pink na fulawoyi wuyanta da kunnenta zuwa hannayenta sunsha gwala gwalai sai
faman walwali suke, kallo d'aya zakayi mata kaga tsantsar kamannin su da wannan saurayin daya shigo
babu ta inda ya barota daga zaunen datake zaka iya ganin tsayin datake dashi kamar yadda shima yake
dogo sosai har d'an rank'wafawa yayi daga sama.
Tun shigowarshi falon fuskar matar ta washe da fara'a shima dolenshi ya d'an saki fuskar sakamakon da
datake a d'inke ya had'e gabas da yamma, wajenta ya k'arasa ya tsuguna har k'asa yafara gaisheta cikin
sakin fuska ta amsa masa tana shafa kanshi sai yaji duk tarin damuwar dayake ciki game da irin mafarkan
dayake ta fara raguwa a hankali yace
"Ummi zan fita ayi mana addu'a".
"Breakfast d'in fa?". tace tana kallonshi tana k'ara nazarin yaron nata kamar yanada damuwa.
Fuska kawai ya d'an yatsina yana girgiza kai yace
"Banajin zan iya cin komai yanzu Ummi kawai zan fita zansamu abinda zanci acan".
Sosai ta b'ata rai tace
"Ban yardaba sam, halinka ne ban saniba? kokuwa yau ka fara fad'ar haka kuma har kaje ka dawo baka
sawa cikinka komai ba? meyasa kake son yin wasa da cikinka ne mai babban suna?". Shagwab'e mata
fuska yayi yana shirin yin magana ta dakatar dashi ta tashi tsaye tareda rik'o hannunshi batare datayi
magana ba ta bayan kujerar datake sukabi suka nufi dinning area shidai yana biye da ita har suka k'arasa
k'aton dinning table d'in daya gaji da had'uwa wanda aka cikashi da warmer's kala kala masu muguwar
tsada da plates da cups duk masu kyau da sauran kayayyakin da ake ajiyewa a dinning d'aya daga cikin
kujerun dinning d'in taja masa ya zauna da kanta tayi saving d'inshi ta tura masa plate d'in gabanshi da
mug da aka had'a tea mai kauri wanda yaji kayan k'amshi da na'a na'a da sauran had'in da larabawa
sukeyiwa shayi sai tashin k'amshi yake, fuska ya shasshake yana kallon Ummi ganin babu alamun wasa
saman fuskarta sam yasa baima fara yin magana ba ya maida kallonshi kan abinda ke gabanshi dan dole
zaici abincin nan jin cikinshi yake duk a wani cunkushe ba dad'i bai sha'awar sa masa komai sosai
mafarkin nan yafara tsaya masa cikin ranshi yarasa kuma ta yadda zai b'ullowa al'amarin gashi bayaso
kowa yasani. Kujera Ummi taja itama ta zauna kusa dashi tana fad'in
"Saikace wani k'aramin yaro kullum sai anyi fama dakai wajen cin abinci kafi kowa sanin yadda kake
matuk'ar shan wahala idan ulcer d'inka ta tashi amma bazaka dinga kiyayewa ba".
"I'm sorry Ummi zanci fa". yayi maganar yana b'ata rai kamar mai shirin sakin kuka shifa hidimarshi ma
tafi k'arfin shi dan haka yake ganin tsayawa ma cin abincin kamar b'ata lokaci ne shiyasa saiya kusan yini
da yunwa a cikinshi sai coffee da ako yaushe yake d'irkawa cikinshi.
Kan dole yafara tura abincin ganin yadda Ummi ta kasa ta tsare ba alamar ma zata bar wajen bare yayi
sharp sharp ya tashi, bai wani ci dayawa ba ya ture mug da plate d'in daga gabanshi ya yagi tissue ya
mik'e tsaye yana goge bakinshi da hannu d'aya d'ayan kuma yana k'ok'arin d'aukar wayoyinshi dake zube
kan table d'in.
"Oyaa koma ka zauna". cewar Ummi tana kallonshi.
Sosai ya marairaice mata ya wani langab'e kai yace
"Please Umminah I'm full wllhy ALLAH bansan ina zansa sauran ba kinji". ya k'are maganar yana d'an
tura baki gaba.
Kamar zatayi magana kuma saita fasa ta girgiza kai kawai tare da fad'in
"To ai shikenan ALLAH ya kiyaye yabada sa'a". Murmushi yayi kad'an wanda ba lallai ma mutum ya
fahimci murmushin yayi ba saboda yadda suka tsaya iya labb'anshi kawai cikeda jin dad'in addu'ar yace
"Amin Amin Ummi thank you so much". ya k'arasa maganar yana sakar mata kiss a gefen kuncinta ya
nufi k'ofar fita daga falon da kallo ta bishi har ya fice daga falon cikin zuciyarta tana k'ara bin yaron nata
da kyawawan addu'oe.
Tun fitowarshi harabar gidan bodyguard d'inshi suka fara d'iban gaisuwa hannu kawai ya d'aga musu ya
shige dank'areriyar motarshi wadda dama already an riga an bud'e masa tun kafin ya k'araso.
D'aya daga cikin motocin ne tafara fita bayan an bud'e k'aton gate d'in gidan sai wadda yake ciki ta take
mata baya saikuma wata guda d'aya data biyo bayan wadda yake ciki suka shilla kan titin unguwar
wanda yake kamar an shareshi saboda rashin mutane da motoci. Shi kad'aine a bayan motar ya lafe a
bayan sit d'in idanunshi a lumshe ya lula can duniyar tunani kan irin mafarkin dayake tunani yake ya
fad'awa Ummi ko Mujaheed babban amininshi kokuwa dai yayi shiru da bakinshi abin yana matuk'ar
cimasa tuwo a k'warya yanaso ya samu mafita to ta ina mafitar zatazo masa ma? bai saniba yana rok'on
ALLAH dai ya yaye masa dukkan wani duhu daya baibayeshi.
*H. I .A GASHUA ENTERPRISES LIMITED* Sunan dana gani kenan manne daga gaban companyn bayan
shigarsu wanda yadda aka rubuta sunan ma kad'ai abin kallo ne da yadda aka tsarashi.
Har akayi parking a cikin harabar k'aton companyn wanda yayi mugun had'uwa yaji glasses tako ina ko
cikinshi ba'a gani bai bud'e ido ba saida aka bud'e k'ofar motar sannan ya bud'e idonshi da suka d'anyi ja
k'afafunshi yafara zurowa kafin gangar jikinshi ta biyo baya saida ya daidaita tsayuwarshi sannan ya
shiga takawa cikin sauri da kazar kazar irin na mai wadatacciyar lafiya da ubangiji ya hore masa ita
sauran suka rufa masa baya.
Tunda ya shiga cikin companyn ma'aikata keta faman mik'o gaisuwa da hannu kawai yake amsawa
batare dayace komi ba wanda sun riga da sun saba da yanayin amsa gaisuwar tashi dan haka ba wanda
ya damu suka cigaba da ayyukan gabansu.
Maryam Ibraheem Aleeyu
(Ummee)
Mrs Salees Mu'az 💝
*EL--HABEEB*💥
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
©️Oum Hanan.
No 2.
Daga inda zai hau lifter ta kaishi 2nd floor inda office d'inshi yake suka rabu dasu bayan sun bashi
briefcase d'inshi.
K'aton office ne mai girman gaske wanda aka k'awatashi da duk wasu nau'ikan kayan k'awa da akeyin
ado dasu a office k'amshi kawai yake zubawa da k'yalli tako ina saboda gyaran dayasha, wani d'an
k'aramin katako ne wanda shima akayi masa wani irin fenti mai kyau aka k'awatashi da tambarin
sunanshi ajiki wato
*HABEEB IBRAHEEM AHMAD GASHUA* daga k'asan sunan nashi aka rubuta matsayin shi a kamfanin
wato _GENERAL MANAGER_.
Had'add'iyar office chair d'inshi wadda take har yanzu a ledarta kamar yaune aka ajiyeta ya nufa ya
zauna bayan yayi bismillah wanda ya zame masa k'aidah kullum sai yayi kafin ya zauna k'asa ya d'anyi da
kanshi ya dafe goshinshi da hannu d'aya d'ayan kuma ya shiga d'an bubbuga table d'in da pen d'in daya
d'auka bayan zamanshi kujerar ta shiga jujjuyawa dashi tarin ayyuka ne a gabanshi saboda shirye shiryen
bud'e wani sabon company da babban kamfanin nasu zaiyi na sarrafa fata shiyasa a y'an kwanakin
bashida tsugun koyaushe yana busy hakan nema ya k'ara rage masa tunanin yarinyar shi ta mafarki sai
yau kuma da abin yadawo sabo fil.
Knocking akayi daga bakin k'ofar
"Yes coming". yace a hankali tamkar mai ciwon baki cikin daddad'an sound d'inshi da ubangiji ya azurta
shi da ita batare daya bud'e idonshi ba koya daina jujjuyawa kan kujerar ba, wani kyakkyawan saurayi ne
dogo ya matse cikin suit light blue da tarin files files a hannunshi ya shiga office d'in
"Mazajeeeee". wannan saurayin ya fad'a yana zube tulin file's d'in bisa table tareda jan kujera ya zauna
fuskarshi d'auke da fara'a, cak ya tsaya da juyawar dayake yaja siririn tsaki tareda bud'e idanunshi ya
sakarwa wannan saurayin harara a hankali kamar mai tsoron yin magana yace
"Matsalata dakai kenan hauka MJ ya zaka shigomin office ba sallama saikace ba musulmi ba".
"Oh shiiit wllhy na sha'afa ne". Mujaheed yace yana d'an dukan goshinshi, idanunshi ya k'ara mayarwa
ya rufe batare dayace komi ba murmushi MJ yayi yana kama kunnuwanshi da duka hannayenshi yace
"Afwan abokina kaina bisa wuya salamu alaikum". zamanshi ya gyara yana amsa sallamar ya mik'awa
MJ hannu kamar yadda shima ya mik'o masa alamun suyi musabaha, takardun MJ ya janyo gabanshi da
nufin fara yimasa bayani saiyaga yayi relaxing kan kujerar ya d'aga kanshi sama yana kallon roofing office
d'in wanda ya wadatu da fitilu masu kyau da tsari, ido kawai MJ ya k'ura masa yana nazarinshi alamu sun
nuna abokin nashi kuma d'an uwanshi yana cikin damuwa zamanshi ya k'ara gyarawa yace
"Hey Mr Gashua what's wrong with u? uhmm akwai matsala ne?".
"Nothing". Habeeb Gashua yabashi amsa a yadda yake batare daya d'ago kaiba, kai MJ ya girgiza yana
fad'in
"No is possible kanada damuwa Gashua fad'amin menene?".
"Nace babu komai MJ please ka k'yaleni haka mana". Wani d'an murmushi MJ yayi alamun bai yarda
da maganar daya fad'a ba yace
"Nikuma nace akwai wani abu ba yau nafara ganinka ba Gashua na sanka farin sani duk da dai dama
kullum cikin k'unci da takurawa kanka kake amma tarayyarmu dakai da dad'ewar da mukayi da juna yasa
a hakan nake iya gane farin cikinka da akasin hakan please tell me what's problem.......A fusace Habeeb
ya d'ago kanshi har yana d'an dukan table d'in gabanshi yace
"Nace maka ba komai ba komai har sau nawa kakeso in maimaita maka ne kurma ne kai ko makaho?
zaka dameni ko maye ne kai ban saniba?". Dariya ma yaba MJ ya d'an dara tare da fad'in
"Maye ne mana amma ban fara cin mutane ba wai kodai duk rashin mace a kusa dakai ne yake kawo
hakan?".
Harara ya dalla masa yaja wani dogon tsaki ya janyo takardun da MJ yazo dasu yana fad'in
"Mahaukaci kawai". Dariya MJ ya k'yalk'yale da ita hakan ya k'ara fusata Habeeb a hasale yace
"Zaka tsaya kayi min bayanin abinda ya kawoka kokuma dariyar zaka tsaya yi?". Gimtse dariyar yayi ya
tattara nutsuwarshi suka shiga yin abinda ya baroshi daga nashi office d'in. Sun d'an d'auki lokaci a tare
sannan MJ ya tashi ya tattara takardun zai koma dasu office d'inshi tsayawa yayi ya kalli Habeeb zai k'ara
yimasa wani iya shegen yaga yaci serious ya tamke fuskar nan tam yaci d'aci tamkar wanda bai tab'a yin
dariya ba murmushi kawai MJ yayi ya fice daga office d'in batare dayace komi ba kuma bawai dan
murtukewar da Habeeb d'in yayi ba sai dan tarin ayyukan dake a gabanshi wanda yakeso ya kammala a
yau idan ya tsaya kuma zai b'ata lokacin shi anan.
Numfashi ya sauke tareda lumshe ido bayan fitar MJ yanajin tamkar ya kirashi ya fad'a masa
damuwarshi ko zaiji sanyi a zuciyarshi idan ya fitar da abinda ke cikin ranshi bayaso lamarin nan ya shafi
aikinshi gashi kuma abin ya fara worsted dannewar dayake yi ada tana neman gagara a yanzu.
Tsayin mintuna kusan ashirin ya d'auka a haka daga bisani ya tashi ya nufi inda coffee machine yake ya
zuba a mug yadawo tsakiyar office d'in inda aka k'awatashi da leather chair milk color kalar fentin office
d'in da glass table a tsakiyarsu, bisa 2sitter ya zube ya shiga shan coffee'n duk kuwa da irin zafin dayake
dashi haka ya dinga sha yana lumshe ido.
A tak'aice dai a wannan yinin ranar ba wani abin kirki daya tsinana a office d'in har lokacin tashi yayi ya
tafi gida.
Flashback.
GASHUA'S FAMILY.
Tun asalin ahalin masu arzik'i ne wanda suka gaje shi tun iyaye da kakanni tun lokacin ma arzik'in na
noma da kiwo ne da sauran nau'ikan abubuwa da mutanen da suka dogara dashi ta hanyar cin abincinsu.
Malam Ahmad da inna Karime sune iyayen Ibraheem wanda shiya kasance d'a na uku a gurin iyayenshi
akwai maza biyu kafin shi Sulaiman da Adam saikuma mata hud'u dake binshi dukansu dai su bakwai
ALLAH ya azurta Malam Ahmad dasu sun tsaya tsayin daka wajen ganin sun basu cikakkiyar kulawa
tarbiyya ilmin addini dana zamani sannan mazan duk wanda ya taso zai nuna masa kasuwanci dan haka
suka taso masu neman na kansu ga kuma ilmin suna kan nema. Adam da Sulaiman tare sukayi aure
lokaci d'aya dan dama tsiransu a haihuwa bawani mai yawa bane, Ibraheem kuwa saidaya dad'e sosai
baiyi aure ba yanata bawa biro da takarda hakk'insu da neman kud'i har Malam Ahmad ya gaji dasa
masa ido ya magantu ganin bashida alamar yi ko maganar ma bayayi dama kuma shi kad'ai ya rage a
gidan sauran k'annen nashi mata duk sunyi aure, wata tafiya da zaiyi Dubai kan harkokin kasuwancin
Malam Ahmad yace yana dawowa koya nemi yarinyar dazai aura kokuma shi ya nema masa cikin dangi
da abokan arzik'i yace to insha ALLAH yana dawowa zai duba matar aure ashe matar auren ce ke kiranshi
acan Dubai d'in dan yana zuwa kwananshi biyu ya had'u da wata yarinya balarabiya mai suna AFEEFAH
mazauna k'asar Dubai d'in ALLAH ya d'ora masa masifar sonta lokaci d'aya yasha matuk'ar wahala kafin
ma yasamu ganinta dan irin gidan nan ne masu mugun tsaro wancan ganin nata ma dayayi har yaji yana
sonta sa'a yaci da kuma ubangiji daya rubuta itace matarshi kuma uwar y'ay'anshi.
Gani d'aya tayi masa itama taji ya kwanta mata sosai cikin ranta duk ya fiye mata samarin larabawan
nan dake kai mata hari kasancewar ta kyakkyawar gaske dama ance SO GAMON JINI.
Ta guri d'aya suka samu mishkila a soyayyar tasu wato iyayen Afeefah musamman mahaifinta Habeeb
Al-Hussain a ganinsu idan suka bari ya aureta zai tafi da ita k'asarshi ya rabasu da ita gashi dama yara
biyu kawai ALLAH ya basu daga ita sai k'aninta Muhseen.
Da k'yar da k'yar aka samu suka amince ya aureta amma sun kafa mashi sharad'in saidai yadawo Dubai
d'in da zama gaba d'aya dan bazasu iya nisa da yarinyar su ba kai tsaye ya amince batare da wani dogon
tunani ba saboda soyayya data rufe masa ido a lokacin burinshi kawai yaga ya mallaketa a matsayin
matarshi, ALLAH ALLAH ya dinga yi ya kammala abinda ya kaishi yabaro k'asar yaje yasamu iyayenshi da
maganar yana kammalawa kuwa ko kwana d'aya bai k'ara yi a k'asar ba ya dira 9ja cikeda zumud'in
zaijewa da iyayenshi labari mai dad'i na samun matar aure.
Bayan dawowar shi ya sanar dasu abinda ke tafe dashi yasamu matar aure balarabiya, Malam Ahmad
bai wani ja da tsayi ba ya amince tareda sawa lamarin albarka amma koda yaji maganar Ibraheem ta
k'arshe ta saidai yakoma can da zama gaba d'aya anan fa Malam Ahmad ya tubure yace sam bazai
yiwuba bai amince ba idan har zai aureta to kuwa saidai su dawo Nigeria su zauna anan bawata k'asa da
zaibi wata y'a