Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 21

54K to 57K   out of 61.8K words

bayan isar shi ƙofar gidan ne ya tuna cewar bama lallai idan yasamu Muhammad ɗin a gida ba.

"Yaa salaam". ya faɗa ƙasa ƙasa yana dafe goshinshi tareda hura iskar bakinsa yana ƙara kallon gidan ta
cikin motarshi so yake ya samu Muhammad ɗin su fara maganar duk da baisan yadda zai ɗauki maganar
ba, fita yayi daga motar yana ƙarewa unguwar kallo kafin ya fara takawa cikin takun nutsuwa ya isa bakin
gate ɗin gidan ya ƙwanƙwasa ba daɗewa maigadi ya buɗe ƙofar ya leƙo dan ganin mai bugawa, gaisawa
sukayi kafin maigadin ya tambaye shi lafiya wa yake nema? tambayar shi yayi ko maigidan yana nan?.

"Kai maigadin ya gyaɗa yace

"Kaci sa'a bai daɗe da dawowa gidan ba wa za'a ce yana magana?".

Wa zaice masa ne? ya tambayi kanshi yana shafa sumar lallausar sumar kanshi.

"Kace masa daga gidan Alhaji Sulaiman ne".
"Toh bari a sanar dashi". maigadin ya faɗa tareda juyawa ya rufe ƙofar.

Mintuna kaɗan ya ƙara buɗe ƙofar yace

"An sanar dashi zuwanka yace a faɗa maka yana fitowa".

"Thank you so much". yace a hankali tareda kai hannu aljihun shi na baya ya ciro kuɗi ba tare daya
ƙidaya su ba ya miƙawa maigadin, hannu na rawa ya durƙusa har ƙasa ya karɓa ya shiga zabga godiya bai
bi takan shi ba ko ya tsaya saurarar godiyar dayake masa ba ya juya ya koma wajen motarshi ya jingina a
jiki ya harɗe hannayenshi kan ƙirjinshi ya zubawa gidan idanu.

Uncle Muhammad yana fitowa yayi ido biyu dashi ido ya ɗan zaro yana mamakin abinda ya kawo shi
yau Mr. Habeeb Ibraheem Ahmad Gashua C.E.O a H.I.A GASHUA ENTERPRISES ne a gidansa? kuma yake
nemansa? da sauri ya ƙarasa fuskarshi ɗauke da murmushi cikin girmamawa Uncle Muhammad ya miƙa
masa hannu sukayi musabaha ALLAH ALLAH Uncle Muhammad yake yaji abinda ya kawo Mr. Gashua
gurinsa sai faman saƙawa da kwancewa yake a cikin ranshi.

"Nasan kayi mamakin abinda ya kawoni wajenka ko?". Habeeb yace yana gyara tsayuwar shi, ƴar dariya
Uncle Muhammad yayi yace

"Ƙwarai kuwa yallaɓai ALLAH yasa dai ba wani laifin mukayi ba?".

Kai kawai Habeeb ya girgiza masa alamun a'a, shiru Uncle Muhammad yayi yana jiran Habeeb yayi
magana, sai daya ɗan jima kafin yace

"Magana ce akan ƙanwar matarka wadda take zaune a gidanka".

"Heedayah?". Uncle Muhammad yace cikin sigar tambaya.

"Yes". Gashua yace yana jijjiga kai dan gaba ɗaya yama manta sunan nata.

"ALLAH yasa lafiya yallaɓai". cewar Uncle Muhammad.

"Magana ce nakeso muyi dakai ta sirri a kanta wata magana bata taɓa haɗaku da ita ba game da
yarinyar?".

"Kamar tame fa yallaɓai?".

Duk saiya rasa abinda zaice masa shifa bai saba irin wannan ba to me zaice masa ne ma? ya tambayi
kanshi yana murza fatar goshinsa da hannu ɗaya ɗayan kuma ya sokeshi cikin aljihu.

"Yallaɓai ina saurarar ka". Uncle Muhammad ya faɗa cikin girmamawa.

Numfashi ya ɗan sauke kafin yace

"Kwanaki bakaga wata yarinya da ake sanarwar ɓatan ta ba a gidajen talabijin da kafofin yaɗa labarai?".

"Ƙwarai kuwa mun gani". Uncle Muhammad yabashi amsa
"Kaga kamar su ɗaya da yarinyar gidanka ko?".



Maryam Ibraheem

Mrs Salees Mu'az 💝




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).



No 33.



"Kaga irinsu ɗaya da yarinyar gidanka ko?".

"Gaskiya ne muma munyi mamaki sosai lokacin da muka gani".

"Bakayi zargin wani abu ba lokacin daka gani?". ( Su Gashua yau an zama ɗan jarida ba jin kai wajen yin
magana ).

Cikeda rashin fahimta Uncle Muhammad yake kallonshi ƙasan ranshi yana tunanin ina ruwan Mr.
Habeeb ɗin da har yakeson jin ƙwaƙƙwafi.

"Eh to banyi zargin komai ba gaskiya tunda inada tabbacin Heedayah ƙanwar Ramlah ce".

"Ita ta tabbatar maka da hakan?". Gashua ya ƙara jefa masa wata tambayar, zuwa lokacin dai Uncle
Muhammad ya fara gajiya da waɗannan tambayoyin na Mr. Habeeb mutum saikace wanda yayi karatun
jarida? shikam gaskiya duk dayake ganin mutunci da ƙima na Habeeb ɗin bazai iya fallasa wannan sirrin
ba idan yayi haka kamar yaci amana ne dan haka kawai saiya jijjiga masa kai alamun tabbatarwa.
Shiru Habeeb yayi yana tunani kafin can wata dabara ta faɗo masa yace

"Please ko zan iya ganin ita Heedayahn?".

Kawai dan babu yadda zaiyi ne ya ɗaga masa kai saboda wani irin kwarjini dayayi masa cikin idanunshi
wanda ubangiji ya halicce shi dashi.

"Bismillah muje daga ciki". Uncle Muhammad ya faɗa yana nuna masa hanya, har ciki yayi masa jagora
ya kaishi wani ƙaramin sitroom a cikin compound ɗin da alamu na saukar baƙi ne.

"Bismillah ka zauna bari ayi mata magana". cewar Uncle Muhammad yana juyawa yabar wajen, bai
zauna ɗin ba saiya shiga ƙarewa ɗakin kallo kujeru ne masu kyau ba laifi sai carpet a tsakiyar kujerun da
ƙaramin center table a kai bayan haka ba komai a cikin ɗakin.

A bedroom yasamu Aunt Ramlah tana haɗa kayan wankinta da za'a haɗa a kaiwa mai wankewa sai
Nusrah dake kwance kan gado tana barci Nu'aym dama baya gidan sunje weekend shida Zainab gidansu
Muhammad ɗin dama yanzu can take yin weekend ɗinta. A taƙaice Uncle Muhammad yayiwa Aunt
Ramlah bayanin komai ya faɗa mata kuma ta tura Heedayahn sitroom ɗin baƙi a zuwan takai masa ruwa
da lemo kawai, ita kanta Aunt Ramlahn tayi mamaki ta fara tunanin dalilin dayasa yakeso ya tono
*RUFAFFEN SIRRI* wanda ya daɗe a rufe mutumin ma da takejin labarinshi wajen Hajiya mugun miskili
ne baya shiga harkar kowa kuma Heedayah ma ta bata labarinshi ance fa ko dariya bayayi to meya
sakoshi cikin lamarin?.

Taso tayiwa Uncle Muhammad ɗin musu tsoronta ɗaya kar yaje ya faɗawa Heedayah wata maganar har
wani zargi ya ɗarsu cikin zuciyarta abu yazo ya caɓe ba laifin wanda za'a gani sai nata musamman su
Baba waɗanda koda wasa basa ƙaunar a nunawa Heedayah wani abu ko kaɗan ne wanda zaisa tayi
tunanin wani abun a cikin zuciyar ta, dan dole ta nufi bedroom ɗin su Heedayahn dan cika umarnin
mijinta.

A gaban mirror tasamu Heedayah tana shafa lotion fitowar ta wanka kenan bayan ta zura doguwar riga
milk color.

"Yauwa Heedayah Abban Nu'aym ne yayi baƙo zaki kai masa ɗan abin taɓawa yana sitroom". Aunt
Ramlah ta faɗa bayan shigar ta bedroom ɗin.

"Tom bari inzo". ta amsawa Aunt Ramlahn tana ajiye powder hannunta data gama shafawa.

"Okay kiyi sauri". Aunt Ramlah tace tana juyawa tabar bedroom ɗin, lipglosses ta shafa ya ɗauki
shinning sai kwalli datasa ta taje girarta ta kwantar da ita dama a ƙa'idar ta sam bata jagira saboda
ALLAH ya hore mata tarin gashin gira a ganinta ɓata lokaci ne ta tsaya ƙarawa da wani abu.

Turare ta shafa sannan tayi rolling da mayafin rigar ta zura plat shoes fari ta fito zuwa falon kitchen ta
wuce tasamu Aunt Ramlah ta haɗa komai a tray ruwa lemo da snacks karɓa tayi ta fito ta fita daga falon
Aunt Ramlah ta sauke numfashi tana bin bayanta da kallo.
Cikin siririyar muryar ta tayi sallama wadda ta haddasawa Gashua faɗuwar gaba da baisan dalilin taba
ya ɗan runtse ido yana cije lips ɗinshi na ƙasa, kasancewar ya bata baya yasa sam bataga ko waye ba kan
center table ɗin ta ajiye tray ɗin ta buɗe ruwan ta fara zubawa a glass cup lokaci ɗaya tana gaisheshi jin
ba'a amsa ba yasa ta ɗago kai taga wane isasshen ne wannan? tayi sallama bai amsa ba kamar wani arne
yanzu kuma ta gaisheshi a matsayin shi na wanda yake gaba da ita still dai bai amsa ba to me yake
taƙama dashi ne? ta tsani dizgi a rayuwar ta. Ido ta ɗan zaro ganin wanda ke hakimce akan kujerar ya
ɗora ɗaya kan ɗaya yana faman basarwa, dama shine baƙon Uncle Muhammad ɗin? to ya akayi suka san
juna? kin manta Uncle Muhammad ɗin yaron Alhaji Sulaiman ne wanda yake kawu a wajen nunar ranar?
wata zuciyar ta faɗa mata haka, sosai gabanta ya faɗi ALLAH ALLAH take ta gama zuba ruwan ta fece dan
alamun wannan mutumin ba mutunci zaiyi ba.

"Nagode nunar rana". kalmar data faɗa masa ranar daya dawo da ita gida ta faɗo mata a rai da alamu
kuma bayason sunan, tsaye taga ya miƙe cikin salon tafiyar shi na gayu da ƙasaita ya nufi bakin ƙofar
falon ya tsaya yayi bake bake hannayenshi duka ya sokesu cikin aljihun wandonshi yana binta da wani
munafukin kallo wanda ba kowa ne zai fahimci kallon nata yake ba.

Tuni glass cup ɗin datake zuba ruwan ya kusa cika amma dayake hankalinta sam ba'a wajen yake ba sai
dataji ruwa yafara taɓa hannunta data dafa center table ɗin alamun ya cika harya fara zubewa sannan ta
ankara, da sauri ta ajiye robar ruwan ta miƙe tsaye da alamu fa guy ɗin nan ɗan neman fitina ne ji yadda
yazo ya wani tare mata ƙofar fita ƙundunbala tayi kawai ta nufo bakin ƙofar kanta a ƙasa tana wasa da
yatsun hannunta.

"Excuse me". tace bayan ƙarasowar ta wajen har lokacin bata ɗago kai ta kalleshi ba, ido ya ɗan rufe ya
buɗe yana tuno lokacin da Jawaheer itama ta faɗa masa hakan lokacin daya tsaya jikin motar ta muryar
tasu ma kanta iri ɗaya ce bambancin su kawai waccan cikin ɓacin rai da hayaniya ta faɗa wannan kuma
kamar irin wadda tayi laifi aka ritsata ɗin nan.

Maimakon ya matsa ɗin saima ya ƙara gyara tsayuwar shi ya kankane ko ina yana mata kallon ƙasan ido
har lokacin bai cire hannayenshi daga aljihunshi ba.

"Ple....a..sse". tayi maganar a rarrabe cikin yanayin shagwaɓa wanda har saida ya ɗan lumshe idanunshi
yayi saurin buɗesu a kanta yana ƙara matsawa kusa da ita tayi saurin ja baya ya ƙara binta ta ƙara yin
baya taci karo da kujera wadda dolenta tasa ta tsaya ta ɗago kai tayi ƙwal-ƙwal da ido tana kallonshi
hannunta akan gefen mayafinta tana wasa dashi ƙirjinta sai bugawa yake kamar wadda tayi tseren gudu
gashi kusancin nasu yayi yawa duk yabi ya cikata da sassanyan mayen ƙamshin shi mai matuƙar daɗi da
sanya nutsuwa hannu ɗaya ya zaro yakai kanshi yana shafa sumar shi yace

"Ke Heedayah kike ko Hadiye wuce ki koma ciki ki zauna inason magana dake". ya ƙarasa maganar yana
ɗage mata girarshi guda ɗaya.

Baki ta tura cikin jin haushi tace

"Wace magana ce? ni koma meye ka faɗamin a haka amma fa bayan ka matsa baya". ta ƙarasa maganar
cikin ƙunƙuni tana ƙara kumburo baki, bakin nata dama yake ta kallo tun ɗazu yadda take juyashi tana
magana yanata faman ƙyalli bai taɓa tunanin akwai wani abu dazai ɗauki hankalin shi a jikin ƴa mace ba
sai gashi yau ya shagalta da kallon bakin yarinya yana jin wani irin yanayi a jikinshi daya kasa fassara shi.

"Kinsan me zanyi idan baki koma kin zauna ba?". ya tambaye ta yana ƙureta da ido, kai ta girgiza kamar
zata sakar masa kuka fatanta da burinta a lokacin ya kauce ya bata waje saboda yadda ya matseta kamar
wanda zai shige jikinta.

"Rungumar ki zanyi". yace kanshi tsaye murya ba alamun wasa yana wani karkace kai.

Kutt lallai dama Man ɗin nan ɗan duniya ne bata saniba? itafa koda wasa akace zai saki irin wannan
maganar haka bazata yarda ba, da gaske dama maza basuda kunya duk shiru shirun su kuwa dama kuma
ance irin masu simi simi ɗin nan kamar munafukai sunfi sanin takan tsiyar. duk cikin ranta take ayyana
waɗannan maganganun bayan ta ƙwalalo ido tareda hangame baki tana kallonshi.

"Yes kina mamaki ne? karki ƙara gigin bani umarni ba'a bawa Habeeb umarni saidai shi ya bayar sa'anki
ne ni? ko wasa nake dake?

Saikace wata ƴar aikinka. ta faɗa cikin zuciyar ta tana ƙara turo baki, kai ya kaɗa yana cije baki kafin
yace

"Zan gyarawa bakin nan zama yanzu idan baki daina turoshi ba ki ƙara gwadawa kuma ki gani". ya
ƙarasa maganar yana zagaye ta ya koma cikin falon ya zauna yayi crossing legs ɗinshi yana wani
girgizasu, da harara tabi bayanshi ji take tamkar ta shaƙoshi ya cika rainin hankali wllhy nunar rana
kawai.

"In taso kiga tsayina ne?". ta tsinkayi muryar shi na faɗa, da sauri ta nufi inda yake ƙasan rug ɗin ɗakin
ta nema ta zauna ta sadda kanta ƙasa tana jiran taji maganar dayace zasuyi.

Shiru yayi kamar bazai ƙara magana ba harta fara gajiya da zaman ranta fa ya fara ɓaci ALLAH zata masa
rashin kunya ta gudu tunda taga alamun shi bashida mutunci.

"Daga wane gari kikazo nan?". ya jefa mata tambayar, da mamaki ta ɗago tana kallonshi da tunanin
tambayar rainin hankalin dayayi mata, taso tayi banza dashi amma kaifin idanunshi daya kafeta dasu
yasa batasan lokacin data furta

"Katsina".

"Me kikazo yi nan ɗin?".

"Karatu".

Kai ya jinjina kafin yace

"Ya kuke da matar Muhammad?".

"Yaya ta ce".
"Uwa ɗaya uba ɗaya?". Kai kawai ta gyaɗa masa tanajin tamkar ta fasa ihu wai me yake damun mutumin
nan yau? aikin jarida ya koma ne? kokuwa dai bai cikin hayyacinshi inba haka ba meye haɗin shi da ita da
zaizo yana mata wasu tambayoyin yaya uwarka ta haifeka.

"Ƴan gidan ku basu taɓa nuna miki wata alama ba?".

"Alama tame fa?". ta maida masa da amsa.

"Baku taɓa zama kunyi wata magana da babanki ko mamanki kan abinda ya shafeki ba?".

"Ni bamu taɓa ba". tace tana harararshi ta ƙasan ido haushi duk ya isheta, ƙasa ya ɗan yi da kanshi yana
murza fatar goshinshi wanda hakan ya zama kamar wata al'adarshi ne yana yawan yin hakan a lokuta da
dama, kai ta ɗago ta dinga zabga masa harara harda murguɗa baki tana ganin zai ɗago kai tayi hanzarin
maida nata kan ƙasa tareda miƙewa tsaye zata bar ɗakin dan bazata cigaba da zama yana mata
waɗannan tambayoyin na rainin hankali ba.

"Sit down ban gama dake ba". ya faɗa cikin haɗe rai yana mata wani irin kallo...



Mrs Salees Mu'az 💝




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)



No 34.

Second to the last page.
Bata koma ta zauna ɗin ba kamar yadda ya umarce ta ɗin tayi tsaye tana tura baki da gunguni wanda
baisan abinda take faɗa ba.

"I said sit down". yace cikin ɗan ɗaga murya yana buɗe mata ido dan yaga alamun yarinyar magana
ɗaya batayi mata.

"Ni wllhy bazan zauna ba kawai sai kaita min wasu tambayoyi da ban gane kansu ba". tayi maganar
kamar zatayi kuka tana harararshi ta ƙasan ido, kai kawai yake jinjinawa yana kallonta itakam taƙi yarda
ma sam ta kalleshi.

"ALLAH idan kika bari na tashi zanyi miki abinda bakiyi zato ba so kwanciyar hankalin ki koma ki zauna
mu karasa maganar da muke batare da wani yaji kanmu ba kar kiga a cikin gidan ku kike wannan bashi
zai hana in hukuntaki ba".

Kamar zata saki kuka ta koma ta zauna bakin nan kamar zai taɓo Gashua dake zaune tsabar yadda ta
turoshi gaba yau dai tana ganin ikon ALLAH azo har inda take a nuna mata fin ƙarfi da iko ALLAH
mutumin nan ba ƙaramin ɗan rainin hankali bane gaban kujerar ya matso sosai yace

"Kina kallon TV?". Haushi yasa tace a'a

"Why?". ya ƙara jefo mata wata tambayar

"Ra'ayi na ne hakan". ta faɗi hakan cikeda rashin kunya, tsaye ya miƙe yana kaɗa kai ya nufo inda take
zaune duk da gabanta ya faɗi amma bata nuna alamun haka ba harya ƙaraso gabanta yana zuwa ya ɗora
ƙafa ɗaya kusa da ita ya ranƙwafa kanta murya ba alamun wasa yace

"Zaki faɗa min gaskiya kokuwa saina baki mamaki yanzun nan?".

"Nifa gaskiya na faɗa maka". tace kamar zatayi kuka harga ALLAH ta fara gajiya da halin mutumin nan.

"Wai ina wasa dake ne? bazaki faɗa min gaskiya ba". Ganin yadda ya ƙarasa maganar cikin tsawa yasa
ta ɗan tsorata ta ɗaga masa kai.

"Good! kinga yarinyar da aka haska wadda ta ɓata ake nemanta?". Nan ma kai ta gyaɗa masa hakan
yasa yace

"Kamar ku ɗaya ba abinda ya bambanta ku me hakan ke nufi?".

"Nima ban saniba". ta bashi amsa kai tsaye.

"Kin santa ne?".

"A'a ni ban taɓa ganinta bama". Kai kawai yake kaɗawa yana cije lips kafin ya tashi daga ranƙwafar
dayayi a kanta ya zura hannayenshi duka cikin aljihun wandonshi ya fara zazzagayawa cikin falon ta bishi
da harara kamar idanunta zasu faɗo tsabar haushin shi datake ji, ba tare daya juyo ya kalleta ba yace
"Zaki iya tafiya amma kina iya gani nadawo koda yaushe idan buƙatar hakan ta taso". Dama kamar jira
take jinta take tamkar akan ƙaya, saurin miƙewa tayi ta nufi ƙofar fita har lokacin bai juyo ya kalleta ba,
sai data tabbatar data fita sannan ta tsaya daga bakin ƙofar tace

"Karka sake ka dawo gidan nan wllhy inba haka ba saina baka mamaki kaima kamar yadda kace zaka
bani Mr. Nunar rana". tana faɗa tabar wajen da hanzari tana ƴar dariya tasan dai tagama kunna shi
tunda ta faɗa masa wannan sunan yo inba nunar ranar ba me za'a kirashi? ragowar shawara kawai.

Lips ɗinshi ya cije tamkar zai hudashi ya runtse ido yana tunanin wane irin raini ne yakeso ya shiga
tsakaninsu da yarinyar ne? yaushe ma sukayi zaman da har zata rainashi haka? lallai ya kamata ya goge
rainin dake tsakaninsu tun kafin ya ƙara yawa ta wace hanya kenan zaiyi hakan? ƙwafa ya saki ya fito
batare di takan abinda ta ajiye masa ba tun ɗazu ya fice daga gidan, motarshi ya shiga ya figeta da wani
irin mugun speed ya fice daga layin sam bai iya bin mota a hankali ba a duk lokacin dayake driving.

A falo ta samu Aunt Ramlah, zama tayi kusa da ita tana jan tsaki duk yagama ɓata mata rai wannan
gayen.

"Lafiyar ki kuwa Heedayah meya faru kike tsaki?". Aunt Ramlah ta tambaye ta.

"Nida wannan jikan Hajiyan mana ɗan rainin wayo yazo sai wasu tambayoyi yake min marasa kai ko ina
ruwanshi dani".

"Wane irin tambayoyi yayi miki?".

"Nifa Aunt Ramlah sam ban gane ma inda ya dosa ba yana ta wani tambayata wai ya muke dake daga
ina nazo me nazo yi nan bla bla bla bla ya isheni da surutu". dariya Aunt Ramlah tayi cikin zuciyar ta tana
ayyana anya kuwa wannan mutumin baisan wani abu akan rayuwar su Heedayah ba kuwa? zuzzurfan
tunani ta shiga wanda batasan lokacin ma da Heedayah ta tashi tabar wajen ba.

Kai tsaye gidan Hajiya yayi parking bai ƙarasa nasu gidan ba.

Tana zaune Larai mai aikinta tana shafa mata man zafi a ƙafafunta waɗanda suka ɗan matsa mata cikin
ƴan kwanakin nan ya shiga cikin falon da sababbiyar sallamar shi daya saba a ciki, waje ya nema ya zauna
Larai na masa sannu da zuwa kai kawai ya ɗaga mata ta rufe kwalbar man zafin dama tagama shafawa ta
tashi tabar wajen.

Kallon Hajiya yayi yana gaisheta ta amsa tana tambayar shi lafiyar su Ummi a taƙaice

19 / 21