Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   20 / 21

57K to 60K   out of 61.8K words

ya amsa mata da
lafiyar su ƙalau yaja bakinshi yayi shiru.

"Yadai maigidan daga ina haka?". cewar Hajiya tana kallonshi murmushi ɗauke a fuskarta, rai ya ƙara
haɗewa sosai yace

"Ƙarar yarinyar nan na kawo miki Hajiya kija mata dogon gargaɗi a kaina dan ni ba sa'anta bane".

"Tooo wace yarinya ce haka?". Hajiya ta tambaya cikin mamaki.

"Wannan yarinyar mai zuwa wajenki I mean Heedayah ne ko menene?".
"A'a ikon ALLAH, a ina kuka haɗu da Heedayahn ne kuma me tayi maka?".

"Ayi mata warning dai Hajiya dan zan iya karya yarinya ba damuwa ta bace".

"Eh lallai ba shakka tunda ga ubanta ai dole ka karya ta yau naji neman masifa da bala'i saika faɗa min
abinda tayi maka da har kake maganar zaka karyata".

Baice komai ba ya tashi ya fice yabar Hajiya tana ta faman mita kamar zata biyoshi.

Ya shiga mota kenan kafin ya tayar da ita wayarshi ta fara ringing yana dubawa yaga Auwal Azare ne
mai kiran, picking yayi ya kara wayar a kunnenshi kafin yayi magana Auwal yace

"Mr. Gashua how far?".

"Alhmdulillah ya kaje gida?". ya mayar masa da amsa.

"Masha ALLAH ina maganar mu ta kwana ne Gashua please kayi wani abu mana".

Sam yama manta da Auwal ɗin yace yana son Neehlah dan haka cikin rashin fahimta yace

"Wace magana kenan?".

"Habaaa mana mutumina maganar ƙanwarmu mana kasan jiya fa ko cikakken barci banyi ba saboda ita
dana rufe idona sai in ganta". ya ƙarasa maganar da iya gaskiyar shi yana sauke numfashi daga ji
maganar daga cikin zuciyar shi take fita, takaici ya hana Habeeb cewa komai sai tsaki kawai dayaja jin
yayi shiru yasa Auwal marairaice murya yana faɗin

"Please say something mana Mr Gashua zaka bani ƙanwar ka da gaske na faɗa dayawa batare da sanina
ba".

Wayar kawai Habeeb ya kashe bayan yaja tsaki a fili yace

"Shege babban banza Neehlah har takai macen da zaiyi irin wannan ruɗewar akanta? wani kiran Auwal
ɗin ne ya ƙara shigowa a fusace ya ɗaga kiran yana faɗin

"Idan ban zageka ba kace ba sunana Habeeb ba wai mayen inane kai Auwal? akan ƙaramar yarinya kake
wannan shirmen dan ubanka ka dawwama baka barci indai a kanta ne karka ƙara sani cikin wannan
maganar banza mara aikin yi".

"Ɗan iska dama ai nasan halin rashin mutuncin ka bazaka goyamin baya ba to ni sai inda ƙarfina ya ƙare
a kanta".

Murmushi yayi yana taɓe baki yace

"Goodluck Dr Auwal Azire". yana shirin kashe wayar yaji Auwal ɗin yana faɗin

"Sanin danayi maka da Gashua ko magana bata dameka ba amma yanzu ka zaƙe da yawa ka koyi rashin
mutunci da faɗa what wrong with you Dude?".
"Ni kaina bansan yaushe na koma haka ba amma nafi tunanin mutane ne suka canzani". bai jira Auwal
yayi magana ba ya kashe wayar yayi switch off ɗinta ma gaba ɗaya dan yasan mawuyacin abune bai ƙara
kira ba shi mamaki ma abin yake bashi yadda Auwal ɗin yabi ya ruɗe akan Neehlah shifa soyayyar ma
duka gani yake ɓata lokaci ne bare harya ruɗe haka akan mace.

Motar ya tayar ya nufi gidansu.



A ranar da dare bayan yagama da duk wasu abubuwa daya saba gabatarwa kafin ya kwanta kamar yin
wanka gabatar da sallah raka'a biyu da addu'oe shan coffee brush da sauran ƴan abubuwan daya saba yi
kafin ya kwanta, yau ɗin ma bayan duk hakan ta kasance ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya
barci, ya rufe ido bayan gama karanto addu'ar saurin buɗewa yayi saboda gano Heedayah dayayi kuma
ba abinda yake gani irin bakinta lokacin datake faɗa masa nunar rana, tsaki yaja ya buɗe idanunshi ya
ƙara juyawa ɗaya gefen tareda ƙara rufe ido still dai ƙaramin bakin nata ya ƙara gani wanda yasha
lipstick yaketa shining yayin datake ta juyashi tana magana.

"Yaa Ilahee". yace ƙasa ƙasa yana dafe goshinshi gaba ɗaya haushin kanshi ya kamashi me yake
damunshi haka ne? ALLAH idan ya kama yarinyar nan sai taji ba daɗi baisan ma wane kalar hukunci zaiyi
mata ba kawai dan tsabar mugunta tazo zata hanashi barci hakan na nufin duk mafarkin dayake a can
baya ita ce kenan?.

Ƙananun tsaki ya dinga ja yana juye juye da cije lips da ƙyar yasamu barci ya kwashe shi a wannan rana
batare daya daina ganin Heedayahn cikin idanunshi ba.



★★★________★★★

Washegari bayan ya taso daga office kai tsaye inda ake ginin ɗaya kamfanin nasu ya wuce yaga yadda
ginin yake tafiya yayi nisa ma sosai abinka da akwai kuɗi zubasu kawai ake.

Daga nan babban shagon da Muhammad yake mallakin Alhaji Sulaiman ya nufa, sosai yaran shagon
suka dinga girmama shi sai miƙa gaisuwa suke saboda sun san ko waye sun san kuma kusancin dayake
dashi da mai wajen, hannu kawai ya ɗaga musu duk yawansu ya nemi da ayi masa iso wajen manager.

Bayan gaisawa da sukayi Habeeb ya nemi Muhammad daya bashi address ɗin gidan matar shi a Katsina
zaije yayi wani bincike a can ya tattauna kuma da iyayen matar tashi, Uncle Muhammad yaso musa
masa amma tsabar yadda ya cika masa ido da kwarjinin dayayi masa a idanunshi yasa take ya rattaba
masa kwatancen gidan shima zuwa yanzu ya fara tunanin anya bata hanyar Mr Habeeb Gashua ɗin za'a
gano asalin iyayen su Heedayah ba? wannan ai abin farin ciki ne a gurin Heedayahn dasu kansu su Baban
dan haka baiji ko ɗar ba yana sa ran insha ALLAH ta sanadin Habeeb ɗin a gano real parents ɗinsu
Heedayahn.
"Thank you so much". Abinda yace kenan ya tashi yabar office ɗin Uncle Muhammad ya bishi da kallo
shifa har yanzu tunani yake meyasa Mr Habeeb ɗin yasa kanshi cikin wannan lamarin?.



Safiyar talata.

Bayan yayi shirin fita office ya shiga gaida Ummi kuma yayi breakfast kamar yadda ya saba, bayan yayi
breakfast ɗin yana shirin fita Ummi tace ya tafi da Neehlah ya sauketa a school kasancewar har zuwa
yanzu driver'n nasu bai dawoba Monday ma saboda batada lecture ne shiyasa bataje ba, ficewa yayi
yana faɗin ta fito yana jiranta kar ta ɓata masa lokaci.

Dama tunda Neehlah taji Ummi tace shine zai yi drooping ɗinta ta shirya da wuri gudun samun matsala
dan Yah Habeeb ba uzuri zaiyi mata ba....



Maryam Ibraheem Aleeyu

Mrs Salees Mu'az 💝

09139964697




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).



No 35.

Last page.
Neehlah na shiga motar ya figeta da uban gudu kamar yadda ya saba dama already maigadi ya riga ya
buɗe masa gate, ko tari Neehlah batayi ba tunda suka tafi ba abinda ke tashi cikin motar sai sautin
karatun Alqur'ani mai girma dake tashi kaɗan kaɗan cikin ƙira'ar Khusary wadda yake biyo farkon suratul
Ma'idah.

A bakin gate ɗin makarantar su Neehlah SKY LINE UNIVERSITY dake cikin birnin Kano yayi parking bai
shiga ciki ba. A ɗan tsorace Neehlah ta ɗan saci kallon shi alamun neman ƙarin bayani.

"Get out". yace ba tare daya juyo ya kalleta ba, kamar zatayi kuka tace

"Yah Hab......"I said get out from my car". ya katse ta cikin ɗaga murya ba shiri ta buɗe murfin motar ta
fita yayi reverse ya cilla motar kan titi yabar wajen tana tsaye tana kallonshi yau kuma haka ALLAH yayi
da ita ji yadda ya watsar da ita anan kamar kayan wanki ta saba kullum driver ya kaita har cikin
makarantar ya sauketa cikin girmamawa da mutunta wa ita wllhy ma matar dazai aura take tausayawa
ta shiga uku gaskiya ba fata dai take mata ba koma wacece shi iya masa sai ALLAHn daya halicce shi ina
rayuwa zata yiwu a haka?

Baki ta taɓe ta nufi gate ɗin tana gyara side bag ɗinta ta shiga cikin school ɗin.

Tun daga wajen ajiye motoci na cikin kamfanin ake ta faman miƙa masa gaisuwa kamar yadda ya saba
ɗaga musu hannu yauma hakan yayi ya shige cikin kamfanin cikin zafin nama da wadatacciyar lafiya da
ubangiji ya hore masa yana shiga kowa ya nutsu waɗanda suke tsaye suka zazzauna kowa ya maida
hankali kan aikin dayake, kalaman barka da zuwa ne kawai ke tashi lokacin daya shiga sun riga sun saba
da yanayin amsa gaisuwar tashi dan haka ba wanda ya damu kowa ya cigaba da aikin gabansa.

Lifter ya hau zuwa 1st floor inda office ɗinshi yake ya buɗe ya shiga, a gyare tsaf ko ina ƙal-ƙal tamkar
ba'a amfani dashi sai tashin ƙamshi mai daɗi yake, brief case ɗin ya ajiye kan babban table ɗin dake
office ɗin sannan ya zauna kan kujerar yana zama yayi baya ya kwantar da kanshi kan kujerar yana sauke
numfashi lokaci ɗaya yana rufe idanunshi tareda jujjuyawa kan kujerar.

Buɗe ƙofar da akayi baisa ya buɗe idanunshi ba dan yasan ko waye mutum ɗaya ne yake da damar yin
hakan a duk faɗin kamfanin wato Mujaheed.

Motsin da bakinshi yayi ne kawai ya tabbatarwa da Mujaheed ya amsa amsa sallamar dayayi idan da
sabo ya saba shikam wane hali ne na Gashua bai sani ba?.

"Welcome Mr. Habeeb Gashua". Mujaheed ya faɗa yana zama kan ɗaya daga cikin kujeru biyun dake
kallon wadda Gashuan yake zaune tare da zube wasu tarin pepper's akan table ɗin, ɗagowa yayi yana
buɗe idanunshi ya kalli Mujaheed kamar bazai yi magana ba saikuma yace

"Mr. Mujaheed Yusuf meya hanaka shigowa Company jiya?". cikin tsare gida yayi maganar yana janyo
computer ya buɗe ya fara danne danne a ciki.

"I'm sick". Mujaheed ya bashi amsa.
"Why did you call me?". yace har lokacin bai daina latse latse a laptop ɗin ba, shegen wato yau dai ƴan
rashin mutuncin ne a kanshi Mujaheed ya ayyana hakan cikin ranshi kafin yace

"Wai Gashua me yake dam......."Look MJ I'm still your Boss karka kawomin maganar banza mana". Yace
a zafafe yana kauda laptop ɗin gabanshi gefe.

"Toooh yau kuma da haka kazo? dan ubanka nabi Boss ɗin da gudu ba wando kai meyasa bakada uzuri
ne a rayuwar ka Gashua? ni dalla malam kayi min signing a takardun nan in tafi inada aikin yi a gabana".
ya ƙarasa maganar yana harararshi, shima hararar ya jefa masa kafin ya janyo takardun yayi sign,
Mujaheed ya miƙe ya ɗauke su ya fita yana maganganu wanda bayajin abinda yake faɗa amma ya
tabbatar iskanci yake masa ƙwafa yayi a fili yace

"Ubanka zanci very soon wllhy". System ɗin ya janyo ya cigaba da aikinsa a ciki.



Neehlah ba ƙaramin ruɗu da tarin al'ajabi ta shiga ba lokacin da Jawaheer Mansoor Jiƙamshi ta shigo
cikin school ɗin exactly ba abinda ya rabasu a komai da Seeyamah har yanayin maganar su kuwa
bambancin kawai ita Seeyamah cikin sanyin murya take maganar ta wanda hakan ya kasance kamar
halittar ta ne hakan, saɓanin Jawaheer dake magana gatsal gatsal ba alamun rissinawa anya babu wata
alaƙa kuwa tsakanin Seeyamah da Jawaheer ɗin? tunanin data dinga yi kenan har zuwa lokacin da suka
shiga lecture.



Da wuri yabar office ranar, yana kan hanya ma Ummi tayi masa waya yaje ya ɗauko Neehlah daga
school ƙiri ƙiri dai Ummi ta maidashi driver'n ƙarfi da yaji dole ya canza akalar tafiyar tashi zuwa school
ɗin su Neehlahn.

Tunda ya shiga cikin school ɗin idanun ɗalibai da yawa suka dawo kan motarshi ana jiran aga wanda zai
fito daga wannan zuƙeƙiyar motar saidai ko buɗewa ba'a da alamun yi, Neehlah da sai yanzu ta hango
motar tayi saurin yin sallama da ƙawarta Haneefah Isma'eel ta nufo wajen motar.

Waya yake lokacin data shiga motar cikin sautin muryar shi mai cike da amo mai haɗe da sanyi cikin
tataccen speech yake maganar cikeda ƙwarewa, kamar ance ya kalli gefenshi ya hangeta tana shirin
shiga motar ta da niyyar barin school ɗin ido ya ɗan zaro yana ƙare mata kallo da tunanin dama a school
ɗin su Neehlah take? magana ake tayi masa daga can ɓangaren wanda suke wayar amma sam bayajin
abinda yake faɗa ganin har ta shiga ta tayar da motar tana shirin barin wajen yasa cikin sauri yace

"I will call you back Mr Williams". Daga haka ya kashe wayar zai cillata front seat yaga Neehlah a zaune
sam ya manta ma da ita a motar tsaki yaja yace

"Get out kisamu abin hawa ya maidaki gida yanzu". Yace yana karkacewa ya zaro kuɗi a aljihunshi na
gefe 5k ya wurga mata.
"Get up". Yace cikin tsawa yana zare mata ido ganin tana shirin yin magana kar ta ƙara ɓata masa
lokaci, kamar zatayi kuka ta buɗe murfin motar ta fita ya juya kan motar lokacin Jawaheer ta fita daga
gate ɗin makarantar ya rufa mata baya ba tare data lura ma wani yana bin bayanta ba.

Tsaye Neehlah tayi ta bishi da kallo harya fita daga cikin makarantar cikin tsananin jin haushi da takaici
kamar ta ƙwala ihu wllhy abinda mutumin nan yake sam baya kyautawa tun farko ma daya sani haka
yace ta tafi basai ta shiga ba ya fito da ita yau dai tana ganin rayuwa, kafaɗar ta da aka dafa daga
bayanta yasa ta juya dan ganin ko waye taga ƙawarta Haneefah ce take tambayar ta lafiya harta shiga
motar ta fito?

"Hmm kedai rabani da halin mutumin can haka fa ɗazu nace miki bakin gate ya zubeni ya ƙara gaba
abinsa yanzu kuma yace wai ina fito in nemi abin hawa ALLAH kamar Ummi taji ta gama ne". ta ƙarasa
maganar cikin tura baki kamar zata saki kuka.

Ƴar dariya Haneefah tayi tace

"Ai kedai ki bari kawai Bestie sam irinsu basuda daɗin sha'ani nima muna nan da wani yayanmu Yah
Khaleel wllhy shima haka yake da abin haushi haka muke fama amma dai gaskiya bai kai wannan Yah
Habeeb ɗin naki ba".

"ALLAH shirye su to". Neehlah tace tana taɓe baki, daidai lokacin Haneefah ta hango motar gidansu
anzo ɗaukar ta hannun Neehlah ta kamo tana faɗin

"Yauwa ga Isah nan ma yazo ɗauka na kizo muje kawai sai muyi drooping ɗinki zuwa gida".

"Kai Bestie ba za'ayi haka ba ba hanyar mu ɗaya bafa kije kawai zan fita in samu drop ɗin napep".

"No please kizo kawai meye abin wahala a ciki". kafin tasamu zarafin magana Haneefah taja hannunta
zuwa gurin motarsu ta sanar da direban zasu fara ajiye ƙawarta a gida kafin su wuce cikin girmamawa ya
amsa ya buɗe musu suka shiga ya tada motar suka bar harabar makarantar.

Tiryan tiryan yake bin bayan Jawaheer har zuwa unguwar su saidaya tabbatar yaga gidan data shiga da
motar ta sannan yayi reverse ya koma da niyyar zai ƙara dawowa ya ɗora da binciken shi.

Tsoro ya hana Neehlah faɗawa Ummi yadda akayi yau da Yah Habeeb da zai kaita da lokacin dayaje
ɗaukota kamar yadda da ta ƙudurta tana dawowa zata faɗa mata tasan dai idan Ummi tayi masa
maganar kanta abin zai koma haka nan tana zamanta lafiya bazata jawowa kanta ba dan haka taja
bakinta ta tsuke sai Seeyamah kawai data faɗawa ita Seeyamahn ma sai abin ya batada dariya ta hau yin
abarta aikuwa Neehlah ta shaƙa kamar zata fashe ta haɗe rai da ƙyar Seeyamah ta shawo kanta ta
haƙura daga nan kuma ta shiga bata labarin Jawaheer wadda suke tsananin kama da ita wadda a farkon
ganinta ma tayi zaton Jawaheer ɗin ce sam Seeyamah bata ɗauka wai kamannin da Neehlahn take faɗa
tanayi da waccan ba wata kama ce ta azo a gani ba bare har tayi wani tunani cikin ranta.



★★_____________★★
Kwana biyu Hajiya sam bataji ɗuriyar Heedayah ba dan tun zuwan datayi tasa Habibu ya maida ita
bata ƙara dawowa ba batasan wane irin shaƙuwa da soyayya ke tsakanin ta da yarinyar ba tana jinta a
ranta sosai dan haka ta fara jajen ta wayar Aunt Ramlah ta kira bayan gaishe gaishe da tambayar iyali
Hajiya tace

"Wai nikam ina ƴar gidana Heedayah ne kwana biyu tayi min yaji lafiya kuwa?". ƴar dariya Aunt Ramlah
tayi tace

"Lahh ba komai fa Hajiya kinsan mutuniyar taki ƴar kaga dama ce kuma ko jiya saida mukayi maganar ki
da ita".

"Toh ya kamata dai tazo a gaisa".

"Insha ALLAH Hajiya gobe ko zuwa jibi zatazo".

"To ALLAH ya nuna mana da rai da lafiya".

"Ameen Hajiya ko ayi mata mutumin naki ta taho miki dashi?". Aunt Ramlah ta faɗa tana dariya cikeda
jin daɗi Hajiya tace

"Kaji ƴar albarka ALLAH ya saka miki da alkhairi yayi miki albarka ya raya miki zuri'a". Da Ameen Aunt
Ramlah ta amsa cikin jin daɗi ta ɗora da faɗin

"Kai Hajiya baki raina abin godiya ai bawani abu bane".

"Kulawa ai yabawa nagode sosai a gaida maigidan".

"Zaiji insha ALLAH". Daga haka suka yanke kiran, bayan dawowar Heedayah daga school Aunt Ramlah
take yimata maganar wayar da sukayi da Hajiya tana bikon ta taga kwana biyu bata leƙa ta ba, zama
Heedayah tayi tana tura baki da faɗin

"Nifa Aunt Ramlah yanzu banson zuwa gidan Hajiyan nan wllhy".

"Saboda me?". Aunt Ramlah ta tambaya cikin mamaki, cikin tura baki tace

"Wannan jikan nata mana ɗan takurar da matsawa mutane shi indai aka haɗu dashi ba za'a rabu lafiya
ba gashi kamar aljani saidai kawai ki ganshi tsulum ya shigo gidan".

"To aini kuwa har nayiwa Hajiya alƙawarin zakije gobe ko jibi".

"Haba Aunt Ramlah ni gaskiya ba inda zanje". tace kamar zatayi kuka, haɗe rai Aunt Ramlah tayi tace

"Aikuwa baki isa ba inama laifin mai nemanka inajin ko jikokin ta bata nema yadda take nemanki sai
kuma hakan ya zama laifi? shi wanda kike maganar shi ai bashi ya haɗamu ba kuma bazai zama
sanadiyyar rabamu ba Hajiya mutum ce tasan ƙima da mutuncin ɗan adam duk da irin ɗaukaka da tarin
dukiyar da ALLAH ya azurta su da ita bata jin kanta ita wata ce dan haka ki shirya kije ɗin kamar yadda ta
nema".
"To Aunt Ramlah kibari idan Zainab tadawo sai muje tare kokuma ranar Monday idan muka haɗu a
school saimu wuce can ɗin ( Dayake Zainab ɗin yanzu duk Friday take wucewa gidansu idan an tashi
daga makaranta Heedayah ce kaɗai take dawowa can take weekend ranar Monday sai tazo makaranta
daga nan sai su dawo da Heedayahn tare). Kai Aunt Ramlah ta girgiza tace

"A'a bazan saɓa alƙawari ba gaskiya goben kawai ki shirya kije".

"ALLAH ya kaimu". Ta faɗa ba dan ranta yaso ba sai dan batason musu da Aunt Ramlahn.

"Yauwa ko ke fa autar Umma goben idan ALLAH ya kaimu zanyi mata dambun tsaki zaki wuce mata
dashi".

"Ba matsala ALLAH ya nuna mana".

"Ameen". cewar Aunt Ramlah tana maida kanta kan shirin da ake haskawa a TV.

Data shiga bedroom ma ita kaɗai ta dinga maganganu wllhy koda sun haɗu idan yayi mata ba ƙyaleshi
zatayi ba saidai ya kasheta duk da bata fatan ma su haɗun dashi taga alamun shi ba'a yi masa alkunya.

Washegari asabar da wuri ta tashi ta hau gyaran gidan tayiwa Nu'aym da Nusrah wanka ta shiryasu
dama indai weekend ne ita take yi musu wanka da safe.

Kitchen ta shiga inda

20 / 21