Author : Oum Hanan Category : African Stories & Novels
wajen Ummi tazo ko kuwa dai wajenta tazo? to amma itafa ba
shiri suke ba hasalima magana ta fatar baki bata taɓa haɗasu ba saboda Jawaheer muguwar ƴar rainin
wayo ce sam basa shiri....."ƙaraso mana". Ummi ta katse mata tunanin datake, kusa da Ummi ta ƙarasa
ta zauna har lokacin bata daina tunanin abinda ya kawo Jawaheer gidansu ba.
"Ummi Aunt Mashhoodah tace tana gaisheki".
"Ina amsawa ya kika barosu da yaran?".
"Lafiya ƙalau wllhy, Noor mafa harda kukanta wai saita biyoni kuma matsalar akwai school gobe amma
tace weekend driver zai kawota ta kwana biyu".
"ALLAH ya kaimu, bakiga baƙuwa bane Neehlah?". cewar Ummi tana kallon Seeyamah data sadda kanta
ƙasa tana wasa da yatsun hannunta murmushi ɗauke a fuskarta.
"Na ganta Ummi a ina kika samota?". A taƙaice Ummi ta bawa Neehlah labarin abinda ya faru duk da dai
bata faɗa mata cewa Habeeb ne yasa aka kama ta ba, sosai Neehlah tayi mamaki jin ba wadda take zato
bace wata ce daban jin tayi shiru yasa Ummi tace
"Ya kikayi shiru ne?".
Sai data ƙara kallon Seeyamah sosai taga dai basuda bambanci da Jawaheer sannan tace
"Ummi abin ne akwai ban mamaki a school ɗinmu fa akwai wata irinsu ɗaya da wannan wllhy ba abinda
ya rabasu komai fa Ummi I'm confused wllhy".
"Ikon ALLAH dama haka lamarin ubangiji yake ai wasu ma ba ƴan gari ɗaya bane sai kiga kamannin su
yazo ɗaya". Kai kawai Neehlah take gyaɗawa tana ƙara karantar yanayin Seeyamahn wadda har yanzu
batayi magana ba.
"Ga ƴar uwa nan nakawo miki yadda kike da damar yin komai a cikin gidan nan itama tana da wannan
damar kar in sake inji wani abu ya ɓullo daga wajenki yanzu amana take a wajen mu".
"Insha ALLAH Ummi". Neehlah ta faɗa tana tashi ta koma kusa da Seeyamah ta zauna tana murmushi.
"Kema Seeyamah ga Neehlah nan kamar yadda na faɗa miki itace ƙarama duk abinda tayi miki ba daidai
ba ki sameni ki faɗa min ALLAH ya haɗa kanku yayi muku albarka".
Da Amin suka amsa gaba ɗayansu Neehlah ta miƙawa Seeyamah hannu suka gaisa kowacce da
murmushi saman fuskarta jin an fara kiran sallah yasa Ummi ta miƙe tsaye tana faɗin
"Oya aje ayi sallah tayi amfani da wannan bedroom ɗin na kusa da naki kaya ma tafara using naki tunda
naga kusan size ɗinku ɗaya kafin ayi mata siyayyar nata". sosai Neehlah ta shagwaɓe fuska kamar zatayi
kuka tace
"Haba Ummi inama laifin kice muyi using bedroom ɗaya dama fa ya min girma". murmushi Ummi tayi
tace
"Ba matsala ta zauna a naki bedroom ɗin shikenan?". cikeda murna Neehlah ta rungume Seeyamah
tana dariyar farin ciki harga ALLAH dama zaman gidan nan yana mugun ci mata tuwo a ƙwarya tana shan
zaman kaɗaici ba laifi gidan kawu Sulaiman ne dama gurin zuwanta kuma shi ƴaƴan shi duk maza ne
matan basuda yawa kuma duk sunyi aure tun ma acan Yoben shiyasa har bataso weekend yayi gara idan
da school ɗin tana ɗebe mata kewa.
"Thank you Ummi". tace tana miƙewa tsaye tareda kama hannun Seeyamah suka nufi upstairs inda
bedroom ɗin Neehlahn yake Ummi ta bisu da kallo tanajin farin ciki mara misaltuwa yana ratsata haƙiƙa
taimakon maraya ba ƙaramin lada gareshi ba aiki ne mai kyau ƙwarai da gaske, itama upstairs ɗin ta hau
ta nufi nata bedroom ɗin dan bada farali.
Babban bedroom ne sosai wanda har Seeyamah ta dinga mamakin ace na Neehlah ne kawai ita kaɗai
lallai masu kuɗi sunajin daɗinsu, tamkar ɗakin wata matar auren bed, wardrobe, mirror da sauran
abubuwan ƙawata ɗaki na masu kuɗi sai ƙamshi yake na turaren wuta.
"Bismillah ga bathroom shiga ki fara yin alwalah". Neehlah ta faɗa tana nunawa Seeyamah wata ƙofa
dake cikin bedroom ɗin, inda ƙofar take ta nufa da niyyar shiga Neehlah ta biyota da sauri tana faɗin
"Oh my God! Seeyamah ki cire babban hijabin nan mana please bakyajin ya dameki ne?". Bata saurari
abinda Seeyamahn zata faɗi ba ta fara ƙoƙarin cire mata shi da kanta bata hanata ba ta tayata cirewa.
"Yauwa koke fa Sisi". Neehlah tace tana jefa hijabin kan bed, itadai murmushi kawai tayi ta shige toilet
ɗin.
Ta daɗe tana ƙarewa bathroom ɗin kallo saboda yadda aka ƙawata shi kamar ba toilet ba (dan ma
bakiga na oga ɗan kidnapping ba 😂).
Alwalah ta ɗaura ta fito ta tarar har Neehlah ta shimfiɗa mata pray mat murmushi kawai suka sakarwa
junansu ba tareda wani yayi magana ba Neehlah ta ɗauko hijabin ta miƙa mata sannan itama ta shiga
toilet ɗin Seeyamah ta bita da kallo familyn sun burgeta sunada kirki da sanin darajar ɗan adam amma
shi wancan meyasa duk bashida su ko kaɗan bashida mutunci da tausayi bai biyo halin mahaifiyarsa ba
gaskiya ganin dai tunanin bazai yimata ba tasa hijab ɗin ta kabbara sallah, itama Neehlah bata daɗe ba
ta fito wata dardumar ta shimfiɗa kusa da Seeyamah ta ɗauko hijab a wardrobe ta tada tata sallahr.
Bayan sun idar ma hira suka cigaba dayi duk da dai duk rabin hirar Neehlah ce Seeyamah bata cika
magana ba sai murmushi kawai datake tana jin ƙaunar ahalin har a jinin jikinta.
Suna nan zaune sukaji an kira sallahr Esha'e dan haka suka tashi suka gabatar da tasu suka ƙara zaman
wata hirar, system ɗinta Neehlah ta jawo tana faɗin
"Bari kiga sister na dana dawo daga gidanta yanzu da kuma Big Bro ɗinmu gaba ɗaya". kafin ma
Seeyamah tayi magana Neehlah ta buɗe system ɗin tasa password ta shiga ɓangaren hotuna inda pic
ɗinta ne kawai dana Ummi da Aunt Mashhoodah sai mai gayya mai aiki Habeeb.
"Masha ALLAH Aunt Mashhoodah tafiki kyau gaskiya". Seeyamah tace tana ƴar dariyar tsokana, tuni
Neehlah ta haɗe fuska tana jefawa Seeyamah hararar wasa kamar zatayi kuka tace
"Dama ta ina zaki haɗamu? su fa acan Dubai aka haifesu itada Yah Habeeb nikam 9ja bansan meyasa
aka haifeni anan ba". dariya sosai Seeyamah tayi tace
"Dama mutum yana zaɓar inda za'a haifeshi ne?".
"Inafa amma nidai banso ba wllhy a rasa inda za'a haifi mutum sai Nigeria". ta ƙarasa maganar tana
wani taɓe baki, dariya Seeyamah tayi tana cigaba da duba hotunan tana murmushi tana yin next
idanunta suka faɗa kan pic ɗinshi yana tsaye kusa da wani ƙaton tamfatsetsen building daya gaji da
haɗuwa sanye yake cikin Italian suit dark blue sai shirt ɗin ciki data kasance white color hannayenshi
duka suna sanye cikin aljihun wandonshi ya toshe idanunsa da black shade tamkar wanda baisan ma za'a
ɗauki pic ɗin ba dan hankalin shi gaba ɗaya baya kan mai ɗaukar hoton can wani gurin yake kallo daban,
daga yadda tsarin wajen yake da irin mutanen dake wajen zai tabbatar maka da ba'a 9ja aka ɗauki hoton
ba yayi matuƙar yin kyau duk da fuskarshi ba'a sake take ba haka yanayin tsayuwar tasa ma ta bada citta,
haka nan Seeyamah ta tsinci kanta da faɗuwar gaba mai tsanani ido ta ɗan lumshe tayi saurin buɗewa
saboda Neehlah dake wajen ita sam Neehlahn ma bata lura da yanayin da Seeyamahn ta shiga ba a
lokacin ta fara faɗin
"Big B kenan miskili kafi mahaukaci ban haushi kin ganshi nan shine babban yayanmu". Kai kawai
Seeyamah ta kaɗa batace komai ba ta cigaba da dubawa duk pics ɗinshi ne kala kala a mabanbantan
gurare mafi yawa ma duk ba'a Nigeria aka ɗauka ba gaba ɗaya ba wanda aka ɗauka yana dariya
kowanne fuska a tamke kuma hakan baya hana yayi kyau baifi guda biyu tagani ba wanda ya ɗanyi
murmushi, tana shirin tambayar Neehlah shikam baya dariya ne taji muryar Neehlahn tana faɗin
"Haka fa yake baya dariya shi murmushi ma saita kama yake yinshi kullum ta ALLAH fuska a tamke yana
baƙin rai kuma yafiso yadda yake kowa ma ya zauna a haka ko dariya fa akayi a gabanshi saiya kori
mutum na rasa irin halinsa Mr ɗacin rai kenan". ta ida maganar tana dariya, itama Seeyamah ƴar dariyar
tayi a ranta take faɗin
Lallai na tabbatar kuwa ko ita ɗin nan da bata daɗe da sanin shi ba bata taɓa ganin dariyar shi ba ya iya
dai mugunta yasan ta kanta.
"Kinsan ai kowa da yanayin yadda ALLAH yake halittar sa wasu masu fara'a da sakin fuska wasu kuma
akasin haka".
Baki Neehlah ta taɓe tace
"Nashi fa daban ne Sisi ALLAH Yah Habeeb da wuya kiga haƙorin shi a waje kullum a cunkushe kamar
wanda baijin daɗin rayuwa ni wllhy ma na matsu yayi aure yabar min gidan in wataya abina". Seeyamah
zatayi magana kenan aka buɗe ƙofa Ummi ta shigo tana murmushi tace
"Oh Neehlah kina nan kin tsareta da surutun nan naki ko? a fito maza ayi dinner". haɗa baki sukayi
wajen amsa mata ta juya ta fita Neehlah ta rufe system ɗin ta tashi tsaye Seeyamah ma ta miƙe suka fita
duk jinta take wani iri daban kamar ba ita ba ba haka ta saba da rayuwar ta ba yau ɗaya ALLAH ya canza
mata.
Dinning area suka nufa inda Ummi take zaune, Neehlah tajawa Seeyamah kujera ta zauna sannan ya
fara serving ɗinsu.
"Ummi banga Yah Habeeb ba?". Neehlah tace bayan tagama zubawa kowa ta zauna
"Ƙyaleshi kawai yau baiyi niyyar yin dinner ba". tana faɗa taja plate ɗin gabanta ta fara cin abincin
Neehlah ma bata ƙara magana ba kowa ya maida hankali kan abincin dayake ci.
Da suka gama ma cikin falon suka koma suka zauna suna kallo jefi jefi suna ɗan taɓa hira.
★__★
Matsananciyar yunwa ke rarakar cikinsa dan rabon da wani abu mai nauyi ya shiga cikinsa harya
manta saidai yaita bankawa cikin shi coffee saikuma fruits dayake ma'abocinsu ne, yau kam yaji yana
sha'awar yasawa cikin shi ɗan abu mai nauyi gashi har wajen 9:25pm baiji kiran Ummi na yazo yayi
dinner ba da alamu fa har yanzu Ummi bata sauka ba, shikam yaga ta kanshi wani lokacin idan Ummi
tayi fushi takan daɗe bata sauka ba.
Tashi yayi daga kishingiɗen dayake ya ɗauki wayarshi ya fita daga side ɗinshi ya nufi nasu Ummi, a
hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar falon ya shiga bakinshi ɗauke da sallama duk da dai ba fitar ta akaji ba
motsin da bakinshi yayi ne ya tabbatar musu da yayi sallamar dama Ummi da Neehlah sun saba gani,
sallamar kawai Ummi ta amsa ta kawar da kanta daga kallonshi tun daga haka ya ƙara shan jinin jikinsa
sai ya cigaba da takawa cikin takun nan nashi mai cikeda izza da mazantaka wanda ya zame masa jinin
jikinshi.
Tun shigowar shi Neehlah tayi tsit kamar ruwa ya cinye ta duk wannan surutun datake tai ɗif da ita ta
shiga zare ido, ta ɓangaren Seeyamah ma haka nata harya zarta na Neehlah dan ita banda faɗuwa da
gabanta yake har wani rawa rawa jikinta ya ɗauka yana ƙara kusantowa gabanta na ƙara faɗuwa wani
mugun kwarjini yayi mata sai taji tamkar ya cika falon shi kaɗai ɗinshi, ta ƙasan ido ta ɗan saci kallon shi
kayan shan iska ne a jikinshi marasa nauyi na kamfanin Adidas jan wando da farar riga wadda akayi mata
ado da jan layi layi irin wandon gashi dai kayan bana kwalliya ko gayu bane amma sun bala'in haskashi
dama ba'a maganar ƙamshi dan yana shigowa falon ya ɗume da ƙamshin sa wanda zuwa yanzu ya riga ya
rasa zauna a ƙwaƙwalwar Seeyamah duk inda taji shi saita ganeshi.
Kusa da Ummi ya ƙarasa ya zauna ƙasan ƙafafunta ya buɗe baki da niyyar yin magana kawai yaga Ummi
ta tashi tabar wajen ta nufi upstairs.......
Saura two pages book one ya ƙare karku manta book two isn't free ALLAH ya bada abinda za'ayi
patronizing ɗina 300 only ALLAH ya bada ikon siya Amin.
Nagode
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu'az 💝
*EL HABEEB*💥
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's).
No 29.
Da kallo ya bita lokacin da take hayewa upstairs ɗin zuciyar shi na masa wani irin zafi wai Ummin shi
ce ke masa haka yau? duk akan wannan yarinyar, Neehlah da Seeyamah ma da kallon suka bita
Seeyamah tasan dalilin fushin na Ummi yayin da Neehlah kuma batasan komai akai ba tayi dai mamaki
ƙwarai tunda bata taɓa ganin abu makamancin hakan ya shiga tsakanin Ummi da Yah Habeeb ɗin ba
kullum rarrashi da lallaɓawa ne tsakanin su to yau kuma meye ya faru?
Ido ya lumshe yana sauke numfashi haɗi da cije baki saboda yadda ranshi ya ɓaci a hankali ya buɗe
idanunsa da suka ɗan fara canza launi ya saukesu kansu Seeyamah wani ɓacin ran ne ya ƙara ziyartar sa
ganin duk a kanta ne Ummi tayi masa haka gashi kuma ta kunyata shi a gabansu wani mugun kallo daya
antaya musu yasa ba shiri Neehlah ta kama hannun Seeyamah suma suka nufi upstairs ɗin jiki na rawa
duk da ita Seeyamahn batama ga irin kallon da yake musu ba, da kallo ya bisu har suka ƙarasa hayewa
tsaki yaja da ƙarfi ya tashi a fusace ya fita daga falon. Da sauri yake tafiya zuwa part ɗinshi yana shiga ya
maida ƙofar da ƙarfi ya rufe ta bada wani sautin ƙara bammm, kan kujera ya zube tareda dafe goshinshi
haɗi da lumshe idanunshi yana jin duk ba daɗi basu saba irin haka da Umminshi ba Ummi bata fushi
dashi saboda yana ƙoƙarin ganin ya kiyaye ɓacin ranta duk abinda yasan zai ɓata mata bayayi baya
ƙaunar fushinta ko kaɗan.
A hankali ya buɗe ido yana furzar da zazzafar iska daga bakinshi ya zama dole yaje yabawa Ummi haƙuri
yanzu bazai iya haƙurin zuwa safiya bama, cikin hanzari ya miƙe tsaye ya ƙara ficewa daga falon ya ƙara
nufar part ɗinsu Ummi, falon ba kowa kamar yadda ya fita ya barshi yana shiga kai tsaye ya nufi upstairs
zuwa bedroom ɗin Ummi. A bakin ƙofar ya tsaya yayi knocking daga ciki Ummi ta amsa cewar a shigo
handle ɗin ƙofar ya kama ya buɗe ya shiga tareda sallama tana zaune kan sofa da wani littafi a hannunta
na addu'oe tana dubawa gabanta kawai ya zube ya dafa gwiwoyinta da duka hannayenshi cikin
marairaicewa ya fara mata magana cikin harshen larabci yana haɗawa da turanci banza tayi masa kamar
bata ganshi ba hakan yasa ya ƙara marairaice murya kamar zaiyi kuka.
Littafin hannunta ta ajiye ta ƙura masa ido duk saiya bata tausayi basu saba irin wannan a tsakaninsu ba
ita kanta tasan yaron nata yana matuƙar gudun ɓacin ranta.
"Zauna sosai muyi magana". tace har lokacin bata saki fuskarta ba, zamewa yayi yai zaman dirshan a
gabanta tareda kamo hannayenta ya riƙe su gam cikin nashi hannun yana kallon ta, dariya yabata sosai
ganin yadda yayi ɗin kamar irin ƙananan yaran nan duk yabi ya wani shasshake mata gimtse dariyar ta
tayi ta ƙara haɗe fuska dan a yau take so taji dalilin shi na ɓoye Seeyamah baiwar ALLAH yarinyar data
taso gidan marayu bataji ba bata ganiba.
"Bakason ɓacin raina ko?". da sauri ya gyaɗa mata kai
"Kanaso kuma in sauka daga fushin danake dakai?". Nan ma kai ya jijjiga mata alamun tabbatarwa, kai
ta jinjina itama tana gyara zamanta tare da faɗin
"Dalilin ka na ɓoye Seeyamah nakeso inji yanzun nan". ido ya ɗan zaro dan baiyi zaton abinda zata faɗa
kenan ba.
"Ummi please abar maganar nan k....."Shut up". Ummi ta katse shi cikin tsawa, shiru yayi ya sunkuyar
da kanshi ƙasa cikin faɗa Ummi tace
"Tashi kabani waje tunda banida matsayin da zaka faɗa min".
"I'm sorry Ummi please zan faɗa miki".
"Ina jinka". cewar Ummi tana kallonshi.
Bashida yadda zaiyi UWA tafi ƙarfin wasa dole ya sanar da ita abinda bata saniba, daki daki a tsanake
ya shiga bata labari tun farkon haɗuwarsu da Heedayah akan layi da haɗuwa da yayi da Jawaheer again
kuma yaga Seeyamah a gidan marayu da irin zargin da yayi na itace take sauya kamanni take bibiyarshi
duk inda yaje hakan yasa ya ɗauke ta da nufin saita faɗa masa inda ta sanshi da dalilin dayasa take binshi
sannan zai saketa har zuwa lokacin da Mujaheed yabi diddigin inda take yazo ya faɗa mata.
Sosai Ummi ta nutsu tana jin wannan labarin mai cikeda al'ajabi idan ta fahimta yaran su uku ne kenan
kuma duk kamar su ɗaya kuma kowacce da inda take tsai tayi da ranta tana auna kan labarin lallai ko
waye dole ya rikice ko ita kanta abin ya matuƙar ɗaure mata kai da shiga ruɗani.
Nannauyan numfashi ta sauke kafin tace
"A ina ita yarinyar daka gani a gidan Hajiyan take?". A taƙaice yabata labarin Heedayah kamar yadda
Hajiya ta sanar dashi yaje kuma yaga har gidan ranar da Hajiya tasa ya maida ita gida.
Kai kawai Ummi take jinjinawa cikin zuciyarta tana ayyana wasu abubuwa masu tarin yawa idan har
hasashen ta zai zama gaskiya to yaran nan ƴan uku ne maybe wani abun ya tarwatsa su kuma ba wadda
tasan da zaman ɗaya a cikinsu danƙari akwai cakwakiya cikin al'amarin nan warware shi sai ALLAH.
"Ita waccan yarinyar da kake gani a shopping mall ɗin kasan inane gidansu?".
"No Ummi har yanzu bansan inane gidansu ba shine nakeso inyi bincike dan gano gaskiyar al'amarin".
Kai Ummi ta jinjina tana faɗin
"Hakan yayi tun farko ma da abinda kayi kenan ka tsaya shirme da sakarci tabbas lamarin yana buƙatar
bincike kuma na baka goyon baya hundred percent dan ta hakane za'a gano iyayen su na asali jikina
yana bani duk inda yaran nan suka fito daga babban ahali suke sanin abinda ya tarwatsa su kuma sai
ALLAH zanfi kowa farin ciki idan aka gano real parents ɗinsu ALLAH ya bada sa'a".
Cikin farin ciki yake kallon Ummin yana ƙara jin wani ƙwarin gwiwa na shigarshi ada bai bawa abin
muhimmanci ba kamar yadda yake jinshi yanzu cikin ranshi saboda mahaifiyarsa data shigo cikin
lamarin.
"Thank you so much Ummi". yace murmushi na suɓucewa kan fuskarsa, itama murmushin ta saki tana
faɗin
"Karka damu nidai fatana karka shiga cikin lokacin aikinka abi komai a sannu har zuwa lokacin da ALLAH
zai bayyana mana abinda ke ɓoye kar ayi gaggawa idan kana buƙatar wata shawara ka sameni".
"Insha ALLAH Ummi thank you very much".
Kanshi kawai ta shafa tana murmushi shikuma yayi kissing hannunta.
"Good night Ummi". ya faɗa yana miƙewa tsaye da niyyar barin bedroom ɗin Ummi ta dakatar dashi da
faɗin
"Ya kamata gobe idan ALLAH ya kaimu kuje da Seeyamah a samar mata kayan sawa". tuni yanayin
fuskarsa ya canza ya wani haɗe rai yace
"Ummi driver fa?".
"Ɗazu yake sanar dani anyi masa waya daga ƙauyensu mahaifiyarsa ba lafiya zaije ganota". Ummi ta
amsa masa tana tsareshi da ido, shiru kawai yayi yana murza fatar goshinsa daya tattareta shine ma zai
kaita siyan kayan sai kace wani ɗan aikinta?
"Bakaji abinda nace bane wai Abbuna?". Ummi ta katse masa tunanin dayake, sai daya zura hannu ɗaya
a aljihu ɗayan kuma ya shiga shafa sumar kanshi