Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   13 / 21

36K to 39K   out of 61.8K words

tace

"Kawai fa gani nayi farinka yayi yawa mu a hausa idan akaga irin fararen nan basuda k'wari sai ace musu
nunar rana amma wllhy ba zagi bane".

Idanunshi ya d'an waro ya taso daga kan kujerar yana fad'in

"Sa'anki ne ni? ko abokin wasanki ne ni d'in, nine mara k'wari ko?". ya ida maganar yana nuna k'irjinshi
da d'an yatsanshi.

"Nidai kayi hak'uri please ka maidani gida Auntyna tana ta kira tun d'azu taji shiru ban komaba". Kai
kawai yake kad'awa ya tada motar kuma bawai dan maganar datayi masa ba kawai idan ya cigaba da
zama anan zaiyi missing sallah ne da saiya tsaya ta nuna masa inane bashida k'warin a jikinshi shi zata
rainawa hankali?.

Tafiyar kurame ce akayi ko tari ba wanda ya k'ara yi bayan sun tafi kowa da irin tunanin dayake a
ranshi, gaba d'aya shi tunanin Habeeb ya tafi kan ya akayi suna matsayin twins amma d'aya a gidan
marayu meyasa hakan? lallai akwai wani b'oyayyen sirri ma'ana ita wannan dayake gani a wajen Hajiya
itace take tare da iyayensu? duk yadda akayi ita ta gidan marayun ta b'ata ne tun tana yarinya, dole zaiyi
bincike akai amma kafin nan saiya zauna da Hajiya yaji tarihin wannan d'in saboda yasan ta ina zai fara
binciken nashi. Haka ya dinga sak'a da warwara har lokacin da suka iso gidan Aunt Ramlah ta hanyar
kwatance da Heedayah take masa, yana yin parking Heedayah tasa hannu da sauri da nufin ta bud'e
k'ofar motar taji ta a rufe gam runtse ido tayi cikeda takaicin abinda guy d'in nan yake mata ta fuskanci
mugun d'an tijara ne amma yanzu ita take nema dole ta kwantar da kai dan haka ta kalleshi a marairaice
kafin ma tayi magana yasan abinda zata fad'a shima kuma sauri yake dan haka yayi unlocked tanajin
alamun an bud'e tayi saurin bud'ewa ta fice ko godiya bata tsaya yimasa ba.

Nagode nunar rana". tace tana d'an d'aga murya yadda zaijita tana fad'a ta shige gidan da sauri tana
dariya, baisan ya akayi ba ya tsinci kanshi da sakin wani munafukin murmushi yana cije baki wato
yarinyar nan ta maidashi wani abokin wasanta ko? ALLAH ya k'ara had'ashi da ita zatayi masa bayani ne
dalla dalla wata k'aramar k'wafa ya saki yana jijjiga kanshi yabar unguwar da gudu.

Tana shiga ta samu Aunt Ramlah dasu Nu'aym a falo suna kallo ita Zainab taje gida sai gobe zata dawo,
sallamar datayi Aunt Ramlah ta amsa tana binta da kallo tasamu kujera ta zauna tana mata sannu da
gida Aunt Ramlah ta amsa tana fad'in

"Ke kuwa ina kika tsaya haka har magreebah kuma kinsan nida Abban Nu'aym bamuson kuna kaiwa
dare a waje".

Shiru ta d'anyi kafin ta lalubo abinda zatace

"Aunt Ramlah kinsan Hajiya fa akwai labari ita ta tsareni da hira". Harara Aunt Ramlah ta jefa mata tace

"Kar kiyiwa Hajiya k'arya ai munyi waya da ita tun wuri tace ta had'aki da jikanta zai kawoki gida". jin
aikin gama ya riga ya gama ma baki ta tab'e tace

"Wllhy Aunt Ramlah wani jikanta ne irin arrogant man d'in nan bashida dad'in sha'ani saidaya fara
biyawa dani wani gida ya shiga ya dad'e yabarni cikin mota sannan ya fito muka taho". Kai kawai Aunt
Ramlah ta kad'a tana fad'in

"To ai saiki tashi ki shiga ciki kiyi sallah". tashin tayi ta d'auki jakarta ta wuce bedroom d'insu.



β˜…______________β˜…

Kwana Habeeb yayi yana tunanin su Seeyamah da yadda zai b'ullowa lamarin, dan haka yana
tashi da safe bayan yayi wanka ya shirya yaje ya gaida Ummi ya fita ya nufi gidan Kawu Sulaiman inda
ana ne Hajiyan take, sai daya shiga side d'in Kawu Sulaiman d'in suka gaisa dashi da matarshi Hajiya
Rahma sannan ya fito ya shiga sashin Hajiya.

Tana zaune taci wankanta da sabuwar atamfar ta ta kashe d'aurinta irin na tsofaffi sai k'amshin turaren
wuta ne yake tashi a falon, tana ganinshi ta washe baki tana masa sannu da zuwa, waje yasamu ya zauna
yana gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar shi lafiyar su Ummi tareda yimasa tayin abin
karyawa yace yayi breakfast a gida.

"Hajiya nazo ne muyi wata magana dake please". zamanta ta k'ara gyarawa tace

"Toh Habibu ALLAH yasa dai lafiya?".

Jimm ya d'anyi kafin yace

"Hajiya yarinyar nan ta jiya da kika had'ani da ita in kaita gida.....tun kafin ya k'arasa abinda zai fad'a
d'in Hajiya ta wani washe baki tana fad'in
"Alhmdulillah ALLAH nagode maka, ai karka damu Habibu ni d'in nan zan tsaya maka tsayin daka in
shige maka gaba har sainaga tabbatuwar al'amarin nan ALLAH yasa alkhairi masha ALLAH abu yayi kyau
ALLAH yasa ayi damu". Duk saiya rasa gane inda maganganun Hajiyan suka dosa ya wani had'e rai yana
yatsine fuska yace

"Wai me kike nufi ne Hajiya?".

"A'a ban gane me nake nufiba? inace kaga yarinya kanaso kazo kanaso in shiga maganar".

"OMG! tsohuwar nan kinada matsala wllhy ni na miki kama da wanda zai auri k'aramar yarinya kamar
wannan haba ki daina ma wannan zancen please". Tuni Hajiya ta tamke fuska tace

"Heedayahn ce yarinya? ALLAH na tuba idan a kauye ne yanzu ai Heedayah tayi wajen yara uku a'a
jaririya ce k'arewar yarinta". Hajiya ta k'arasa maganar cikin fad'a tana maka masa harara, goshinshi ya
d'an dafe yana murza fatar goshin yace

"Nifa ba hayaniya nazo kimin ba Hajiya wata magana ce very important takawo ni akan yarinyar nan".

"Ina jinka". cewar Hajiya ta wani juyar dakai gefe ita a lallai ba haka taso ba.

"Inaso insan asalin yarinyar nan da abinda ya had'aku har take zuwa wajen ki?".

"Duk wannan bin k'wakk'wafin na meye kuma?". Ido ya lumshe yana d'an taune lips d'inshi cikeda
gajiyawa da maganar dayake tun d'azun yace

"Hajiya dan ALLAH, kaina yafara ciwo saboda maganar danake tun d'azu ki taimaka please ki gayamin".

Baki Hajiya ta tab'e tace

"Yaron kawunka Sulaiman ne mijin yayarta kuma y'an Katsina ne can shi Muhammadun ya aurota".

Kai ya shiga jijjigawa yana fad'in

"Kenan y'ar Katsina ce ita d'in?".

"K'warai kuwa dalilin zuwanta kuwa shine yaron dazata aura ne ya rasu ana saura sati d'aya biki ta shiga
cikin matsanancin hali shiyasa yayar ta taho da ita ko zata samu sauk'in abinda take ji".

"Thank you Hajiya". yace yana mik'ewa tsaye, da kallo ta bishi tana fad'in

"Wai duk wad'annan tarin tambayoyin na menene saikace wani d'an jarida".

Hannayenshi duka ya zube cikin aljihun wandonshi ya saki wani miskilin murmushi yace

"Bazaki gane bane Hajiya, nina wuce ayi mana addu'a". daga haka yasa kai ya fice daga falon yabar
Hajiya tana rakashi da kallon mamaki.
Kamar ance ya waiwaya bayanshi bayan fitowarshi gidan Hajiya ya hangi wata matashiyar budurwa
kamar Heedayah wadda a yanzu yakejin sunanta a bakin Hajiya zata shiga gidan Alhaji Saminu wani
mak'ocin su Kawu Sulaiman ne kuma abokinshi gidaje uku ne ya raba tsakanin su da gidan Kawu
Sulaiman d'in, da sauri ya juya da sassarfa ya nufi gidan saidai kafin ya k'arasa harta shige gidan.

"Oh my God!". Yace yana kai hannu kanshi yana yamutsa sumar kanshi gaba d'aya ya kasa barin k'ofar
gidan ya shiga sintiri a k'ofar gidan kamar d'an doka sai faman kai da kawowa yake daga k'arshe daya gaji
da zaryar saiya jingina jikin wata mota daya gani a k'ofar gidan yayi crossing legs d'inshi hannayenshi
duka biyun ya cusasu cikin aljihun jeans d'in dayake jikinshi, idanunshi k'urr akan k'ofar gidan yana jiran
fitowarta.

Jawaheer tazo aiken Mummyn tane Hajiya Saudah wadda matar Alhaji Saminun Hajiya Kareemah
k'awar tace sosai a yadda Mummyn take bata labari tare sukayi school tun zamanin y'anmatancin su, to
yau d'in ma wani sak'o tazo kawowa Hajiya Kareemahn.

Wayace kare a kunnenta ta fito daga gidan tana amsawa, tsaye tayi daga inda take tana k'are masa
kallo idan bata manta ba shine gayen nan daya tab'a tareta a ShopRite har yana mata wasu maganganu
data kasa fahimtarsu a lokacin to meya kawoshi nan unguwar? koma d'an gidan ne bata saniba? koma
dai waye shi ba damuwar ta bace.

"I will call you back". abinda ta fad'a kenan ta kashe wayar ta nufo inda yake tsaye dan d'aukar motar ta
fuskar nan tata a d'inke.

Ido cikin ido suke kallon juna kowa fuska a tamke kamar wad'anda aka aikowa sak'on mutuwa, shigar
jikinta yake bi da kallo yana k'ara had'e rai jeans ne pencil dark blue da farar riga body hook data
matseta sai kimono ash color data d'ora akai da wani siririn ash gyale datayi rolling dashi, k'afarta sanye
cikin hill shoes black color mai igiya da wata black hand bag dake mak'ale a hannunta, wato yarinyar nan
RUWA BIYU ce yau tasa kayan arzik'i gobe tasa na tsiya ko jiya ma hijabi ne ai a jikinta lokacin daya
d'auketa a motarshi amma dubi irin shigar datayi yau sosai ranshi ya b'aci yau saiya titsiyeta ta fad'a
masa uban dayasa take wannan d'abiar dama ga haushin nunar rana data k'ara cemasa jiya bayan ya
sauketa.....



Afwan a k'ara hak'uri dani yanayin yadda page d'in yake zuwa ba yawa sosai harkar mai iyali sai hak'uri
naji mutane dayawa na complain page d'in yana kad'an I'm so sorryπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ».

Sai masu bina PC suna cewa in basu book din nan daga farko dan ALLAH suyi hak'uri su dinga tambaya a
group abin zaimin yawa ga typing ga turawa daga farko kuma anfara nisa mutum ba d'aya ba ba biyu ba
dayawa duk da nasan k'auna ce ta kawo hakan amma dai ayi hak'uri a dinga tambaya cikin grup.

Nagode.
Maryam Ibraheem Aleeyu

Mrs Salees Mu'az πŸ’




*EL HABEEB*πŸ’₯



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*πŸ’‘

(Home of expert & perfect writer's).



Special thanks for

Ameenah Abubakar, Husnah Abdullahi, Mum Elham, Haneefah S.G, Maryam kabuga, Aseeyah Buhari,
Mrs Kabeer, Miss Ayshaa, Rabi'atu Musa, Maman sadeeq, Mum Farouq, Oum Anwaar. jazakumullah
khair all nagode sosai da yadda kuke nunawa book din nan k'auna fatan alkhairi πŸ’–.




No 24.



Cikeda b'acin rai yake kallonta harta k'araso inda yake tsaye ko motsi baiyi ba bare ya matsa daga
jikin motar duk da alamu sun nuna masa motar tace tunda gashi tazo inda yake.

"Excuse me". Ta fad'a cikin had'e rai bayan k'arasawar ta tana wani kad'a car key d'in dake hannunta,
sam bai nuna ma yasan abinda ta fad'a d'in ba sai kallon takaici dayake binta dashi yanajin tamkar ya
daddalla mata mari hakan yasa ta k'ara k'uluwa ganin irin kallon rainin dayake mata.

"Wai Malam baka jine? bakaji abinda nake fad'a ba? ko kurma ne ban saniba?". Ta jero masa
tambayoyin a lokaci d'aya tana wani yatsina fuska, sai a lokacin ya d'ago daga jikin motar yayi mata tsaye
a gabanta ido cikin ido suke kallon juna kafin cikin b'acin rai ya fara fad'in
"Meyasa ke bakida kamun kai ne? yau kiyi shigar arzik'i gobe kiyi ta tsiya why? kina tallan jikinki a waje
saboda bakida hankali meyake damunki ne?". Ya k'arasa maganar yana wani zare mata ido, cikeda
d'imbin mamaki take kallonshi da tunanin anya mutumin nan kanshi d'aya kuwa? to inba hakaba ina
ruwanshi da ita dazai tsareta yana mata wasu maganganu marasa kai taga alamun saita kafta masa
rashin mutunci sannan zai shafa mata lafiya dan haka cikin masifa tace

"Kai dallah malam bansan hauka, ya zakazo ka tareni kana min wani soki burutsu a ina ka sanni? meye
had'ina dakai?". Ta ida maganar tareda jan wani dogon tsaki wanda Habeeb ya jishi har tsakiyar kanshi
tsabar yadda ranshi ya b'aci baisan ya akayi ba sai gani yayi ya canza musu position d'in tsayuwar tasu ita
ta koma jikin motar shikuma yana tsaye a gabanta ya matseta da k'irjinshi sai huci yake idanunshi sun
fara canza kala, cikeda bala'i yake fad'in

"Waye mahaukaci? nace wa kike kira da mahaukaci?". Ya k'arasa maganar cikin tsawa, batare da shayin
komai ba ta kalli cikin idanunshi cikin tsiwa da rashin kunya tace

"An fad'a maka haka, me zakayi? ko akwai matakin da zaka d'auka ne? inba hauka ba ni ban sanka ba
kazo kaita min wasu shirmen maganganu wllhy idan bakayi was......Wata wawar damk'a yayiwa bakinta
wanda yasa dolenta tayi shiru ba shiri ta saki wata siririyar k'ara amma tsabar taurin kai bata daina
antaya masa uwar harara ba tamkar idanunta zasu fad'o k'asa duk kuwa da irin zafin dake ratsa ta, sai
daya cije baki kafin ya had'e leb'enta na sama dana k'asa ya murje da dukkan k'arfinshi ta k'ara sakin
wata k'arar kuka take so tayi saboda azaba amma bazata iya kuka a gabanshi ba ai kamar ta kasa ne yaga
lagonta dan haka ta shanye kukanta ta cigaba da watsa masa harara, so take ta tureshi saboda yadda
kusan nasu tayi yawa gaba d'aya yayi mata rumfa ya babbake ko ina bata ganin komai sai shi d'in, a
fusace yace

"Bakinki yasan irin kalmar da zaki dinga fad'a a kaina Habeeb ya wuce da saninki very stupid". Hannu
tasa da k'arfi ta fincike hannunshi ta yarfar dashi gefe tace

"Dalla Malam sakeni, idan ka saba iskanci da y'an mata to Jawaheer tafi k'arfinka wllhy aikin banza
kawai".

Sunan dayaji ta fad'a ne yasa mamaki ya kamashi idan bai manta ba Heedayah yaji Hajiya ta ambata
amma ita kuma wannan yaji ta ambaci wani sunan daban mai hakan yake nufi? bai ankara ba yaji ta
tureshi saboda yadda ya shiga rud'ani, tsugunawa tayi ta d'auki kayan hannunta da suka watse lokacin
daya fincikota.

Yana gani ta bud'e motar ta shiga mamaki yasa ya kasa hasala komai bare yayi yunk'urin binta.

"ALLAH ya isa mugu azzalumi". tace tana lek'o da kanta ta window'n motar kafin ta bata wuta tabar
layin da gudu, tsaye yayi kawai ya kama k'ugunshi da duka hannayenshi yabi motar da kallo har zuwa
lokacin da motar ta b'acewa ganinshi.

"Yaa Ilahee". Ya ambaci hakan yana dafe goshinshi gami da runtse idanunshi gam g kanshi ke wani irin
sarawa yana jujjuyawa wai kodai aljanu ne keson bud'e masa ido ne? Seeyamah, Heedayah again kuma
wata Jawaheer daban? hakan na nufin triplets ne kenan? kokuma dai Heedayahn ce Jawaheer? gaba
d'aya k'wanyar kanshi ta d'auki zafi ya rasa wane tunanin ma zaiyi.

Kamar wanda aka mintsina ya zabura da sauri ya nufi gida, kai tsaye side d'inshi ya nufa yana shiga ya
wuce kitchen ya d'auko swan water medium size bottle ya fito tsakiyar falon ya tsaya ya b'alle murfin
robar ya kafa kai ya shiga kwankwad'ar ruwan duk da irin sanyin dayake dashi kuwa sai daya shanye shi
tas sannan yayi jifa da robar ya rik'e k'ugunshi da hannu d'aya d'ayan kuma ya shiga yamutsa lallausar
sumar shi mak'wallaton shi sai kai da kawo yake yana sauke numfashi idanunshi a rufe sam yayi ragon
azanci daya bita yaga itakuma inane gidansu shifa yanzu yafara zargin maybe yaran nan aljanu ne suke
masa yawo da hankali Seeyamah gidan marayu, Heedayah Katsina ance gidan yayarta take da zama and
now Jawaheer itama anan Kano kai wannan lamari akwa mugun d'aure kai amma insha ALLAH zaibi
komai step by step domin gano gaskiyar lamari, tabbas akwai wani b'oyayyen sirri inba hakaba ace yara
har uku a matsayin su na triplets amma kowa da inda yake rayuwa?

Wani dogon numfashi yaja ya zube bisa kujera idanunshi a rufe yayi relaxing sosai yana cije lips.

Kusan mintuna biyar yana zaune a haka ko cikakken motsi bayayi har lokacin bai bud'e idanunshi ba sai
sak'a da warwara yake kan ta inda ya kamata ya fara da lamarin.

Bud'e k'ofar da akayi aka shigo ita tasa ya bud'e idanunshi a hankali ya kalli wanda ya shigo d'in
cikakken saurayi ne kamar shi wanda zasuyi kusan sa'anni dashi shima dogo ne saidai shi yanada y'ar
k'iba kad'an very handsome guy ne bashi da hasken fata sosai amma kallo d'aya zakayi masa kasan hutu
yasamu gurin zama a jikinshi duba da yadda fatar jikinshi take wani shek'i da d'aukar ido.

Shigar k'ananun kaya ne a jikinshi blue black d'in jeans ne da lemon green d'in riga mai gajerun
hannuwa wanda hakan yaba cikakkun damatsen shi bayyana sai P.cap blue black daya d'ora a kanshi,
tunda ya shigo falon shima k'amshin turarenshi ya cika ko ina ya had'e dana Habeeb wanda ke zaune har
lokacin yana binshi da kallo ko motsi baiyi ba, duk da cewa yayi farin cikin ganinshi kuwa.

Cikeda fara'a da murna ya k'arasa kujerar da Habeeb yake ya zauna kusa dashi.

"Matsalata dakai kenan wulak'anci d'an balarabe duk lokacin da muka d'auka bamu had'u ba amma ji
irin tarbar daka yimin saboda bakada mutunci". Ya fad'a yana dukan kafad'ar Habeeb d'in da tashi
kafad'ar, harara ya watsa masa kafin ya tashi zaune sosai yace

"Zaka iya komawa inda ka fito indai saina tashi nayi hauka nayi ihu saboda ganinka saikace wani
ubana".

"Halin dai yana nan yadda nasani a baya". MUHSEEN yace yana d'an tab'e baki da jijjiga kai, cikin yaren
larabci Habeeb ya bashi amsa.

"A'a fa karka zageni Malam muma fa munajin larabcin nan ma ismuka, aina tazhab....... kafin ya k'arasa
Habeeb yasa dariya (Yaudai naga dariyar Gashua πŸ˜‚).
"D'an iskan abokina". ya fad'a cikin dariyar tareda kamoshi ya rungume, shima Muhseen d'in dariyar
yake suka rungume juna cikin farin ciki.

Muhseen d'an gidan abokin Abbu ne Alhaji Usman Shareef sun had'u ne ta harkar kasuwancin su ALLAH
ya had'a jininsu, bayan kammala karatunshi dayayi lokacin daya dawo 9ja suka had'u ta silar iyayen nasu
daga nan suka k'ulla abokantaka duk da Habeeb d'in ma bai bawa zumunchin nasu wani muhimmanci ba
amma shikam Muhseen ya d'aukakeshi sosai kuma yana hak'urin zama dashi har a yanzu Alhaji Usman
d'in bai yada suba jefi jefi yana zuwa suna gaisawa da Ummi dasu Hajiya da Kawu Sulaiman, shima dai
irin Mujaheed ne bakin abin magana basa gani su k'yale dayake ta dalilin Habeeb d'in shima Mujaheed
d'in sun saba dashi. shikuma engineering ya karanta yana aiki a wani babban kamfani na software a
Abuja amma dayake iyayenshi y'an Kano ne yasa yake yawan zuwa sosai yanzu ma dalilin dad'ewar shi
baizo ba sunje wani course ne a Italy na watanni kan abinda ya shafi aikinsu na engineer.

Anan kuma hira ta b'arke tsakaninsu duk da dai duk rabinta ma Muhseen d'inne ke yinta, sun dad'e
anan sannan suka tashi Habeeb yayi masa jagora zuwa part d'in Ummi dan ya gaisheta, itama tayi murna
da ganinshi bayan sun gaisa suka fito compound d'in gidan sukayi sallama Muhseen ya shiga motarshi ya
tafi shima Habeeb part d'inshi ya koma dan d'auko key d'in motarshi ya tafi office dama wancan banzan
sai kiranshi yake a waya, duk abinnan da ake tunanin triplets na nan daram mak'ale a ranshi da tunanin
samun mafita.



Yammacin ranar.

Danger ce ta tsaida motoci, cikin wad'anda aka tsayar d'in harda Mujaheed wanda bayan tashin shi
daga wajen aiki ya biya ta wani

13 / 21