Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 21

9K to 12K   out of 61.8K words

da amanarshi.
Yauma weekend Aunt Ramlah da yaranta dasu Heedayah suka shirya tsaf dan zuwa gaida Hajiya Inna
mahaifiyar Alhaji Sulaiman dama kuma Aunt Ramlahn tana zuwa jefi jefi wajen iyalan Alhaji Sulaiman
d'in dakuma wajen Hajiya kuma tasu tazo d'aya da Hajiyan.

Saida Aunt Ramlah lafiyayyen dambun tsaki dayaji gyad'a da zogale sanin yadda Hajiyan ke matuk'ar
sonshi ga kuma had'add'en zob'o dayaji kayan had'i wanda shima tasan mutumin Hajiyan ne suka tafi
mata dashi.

Uncle Muhammad d'in ne ya kaisu da kanshi ya saukesu ya wuce, b'angaren Alhaji Sulaiman d'in suka
fara shiga aka gaggaisa suka d'an tab'a hira da uwargidan shi Hajiya Rahma sannan suka nufi b'angaren
Hajiya wanda yake duk a cikin gidan.

Sosai Hajiya tayi murna da ganinsu ta shiga yimusu sannu da zuwa kamar zata goyasu saboda yadda
take musu dan taji dad'in zuwansu sosai dama Aunt Ramlah ta saba dan duk lokacin datazo irin tarbar
datake mata kenan akwaita da karrama bak'o.

Zama sukayi aka shiga gaggaisawa sannan Aunt Ramlah ta bata abinda tazo mata dashi, aikuwa tasha
addu'a daga nan suka shiga hira cikin hirar ne Hajiya Inna ke tambayar Aunt Ramlah ina tasamu
kyakkyawar yarinya haka dayake tasan Zainab sun tab'a zuwa sau d'aya da Aunt Ramlah.

Murmushi Aunt Ramlah tayi tace

"K'anwata ce Hajiya".

"ALLAH sarki takawo miki ziyara kenan?". cewar Hajiya.

"Wallahi Hajiya saurayin ta dazata aura ne ALLAH yayi masa rasuwa sakamakon accident dayayi ana
saura sati d'aya biki ta shiga halin damuwa kullum cikin koke koke to shine zuwan nan danayi na k'arshe
muka taho tare to gashi ma har Abban Nusrah ya samar musu makaranta sun fara zuwa itada Zainab".

Kai Hajiya ta shiga girgizawa cikeda tausayawa tace

"ALLAH sarki, ALLAH yaji k'anshi yayi masa rahma itakuma yabata wani mafi alkhairi".

Da "Ameen" Aunt Ramlah da Zainab suka amsa yayin da idanun Heedayah suka cika da k'wallah saboda
wani abu dataji ya taso mata game da mutuwar Kabeer, a hankali tasa gefen mayafinta ta goge batare
da kowa ya lura ba sai Hajiya data ganta tausayinta ya k'ara kamata lallai dagani ba k'aramin so takewa
wannan saurayin nata ba lokaci d'aya taji yarinyar ta shiga ranta sosai.

"Malam Muhammad da k'ok'ari an bar muku ne gaba d'aya har dasata a makaranta?". Hajiya ta fad'a
cikin dariya.

Dariya sukayi gaba d'ayansu, cikin dariya Aunt Ramlah tace

"Hajiya ai tunda tafara karatu dole abar mana ita gaba d'aya Hajiya".
"A'ah kunso yin dai k'wace kawai". cewar Hajiya tana dariya, nan suka cigaba da hirarsu dayake Hajiya
akwai raha haka tayi ta sasu dariya. Sunci sunsha daga abinciccikan da aka aiko musu daga part d'in
Alhaji Sulaiman dayake itama Hajiyar daga can ake kawo mata dambun da Aunt Ramlah takai mata shi
taci abinta batabi takan fried rice d'in da akayi ba, gashi komai ta wawuro ta mik'o musu irin abunsu na
tsaffi gaskiya Hajiya akwai mutunci abinda Heedayah ta dinga fad'a kenan a cikin ranta.

Anan sukayi sallahr magreebah sannan Uncle Muhammad yazo, bayan sun gaisa da Hajiya suka tafi
bayan sun shiga sun yiwa Hajiya Rahma sallama tayiwa su Heedayah kyautar kayan makeup su Nusrah
kuma biscuits, chocolate dasu sweet's itama kam akwai mutunci ta fahimci kamar haka familyn suke
gaba d'ayansu.



Tun daga xuwan da sukayi shak'uwa ta shiga tsakanin Hajiya Inna da Heedayah kamar irin sun dad'e
d'in nan tare ko bata jeba tayiwa Aunt Ramlah waya tace ta turo mata Heedayah wani lokacin ma daga
school suke wucewa itada Zainab.



★★★★★★

Ranar asabar da yammaci lik'is bayan sun taso daga islamiyyar da suke zuwa Aunt Ramlah ta aikesu
gidan wata k'awarta zasu karb'o mata sak'o, layi d'aya ne a tsakaninsu ba nisa gidan dan haka a k'afa ma
suka shiga takawa suna hirarsu gashi dama layin irin dogon nan ne kuma sam ba yawaitar mutane a layin
ko ina shiru.

Heedayah atamfa ce a jikinta riga da siket purple color da bak'i sai hijab kalar atamfar iya gwiwarta mai
hannu, itakuma Zainab doguwar rigace pink color tayi rolling da mayafin rigar a hankali suke takawa
kamar masu tausayin k'asar.

Tsadaddun motoci ne guda uku bak'ak'e wuluk suka shigo cikin layin da wani irin matsiyacin gudu
sukayi kan su Heedayah kamar zasu bankesu ga uban horn dasuke ta dannawa kamar zasu tashi
unguwar hakan ya gigita su Heedayah suka rasa inda zasu nufa duk suka diririce ta gefensu sukazo
sukabi a tsiyace kamar zasu tashi sama, wani takaici ne ya kama Heedayah ga gabansu dake ta fad'uwa
daga ita har Zainab d'in batasan lokacin data tsuguna ta rarumi dutse a k'asa ba ta cillawa motocin duk
da irin yadda Zainab take rik'e hannunta dutsen nan bai tsaya ko ina ba sai a bayan motar dake tsakiya
wanda hakan yasa dole mai tuk'a motar ya taka birki ba shiri shima na bayanshi ya tsaya na gaban nasu
ma ganin sun tsattsaya yasa shima ya tsaya.

Banda dukan uku uku ba abinda zuciyar Heedayah da Zainab keyi tamkar tayi tsalle ta fito waje tsabar
tsoro amma saboda k'arfin hali irin na Heedayah haka ta tunkari motocin tun ma kafin taga suwaye zasu
fito daga ciki, tsananin tsoro yasa Zainab takasa ko motsawa bare tayi yunk'urin hanata zuwa sai tai
tsaye tana kallon Heedayah data tunkaresu lokacin duk sun fiffito daga cikin motar kowanne cikin
bak'ak'en suit.
Tun kafin ta k'arasa tafara d'add'aga hannaye tana musu masifa da bala'in makafi ne su dazasu buge
mutane kokuwa dai shaye shaye sukaje sukayi yasa suke gudun rashin hankali da tarbiyya a unguwar
mutane?. gaba d'ayansu sukayo kanta da nufin gyara mata zama musamman Aliyu babban bodyguard
d'in da harya d'aga hannu da nufin kifa mata mari saikuma yaji muryar maigidan nasu wanda shi sai
yanzu ne ya fito daga cikin motar.

"Stopped Aleeyuh". ya fad'a cikin tattausan sound d'inshi kuma cikin wani salon magana mai dad'i, mai
maganar nabi da kallo idanuna suka hangomin Habeeb Gashua wanda yake tsaye jikin motar ya dafa
murfin motar da hannayenshi yana sanye cikin bak'in wando da farar shirt mai dogayen hannu ya matse
wuyanshi da black tie yasha torking da bak'ar belt wanda ya bayyana shafaffen cikinshi dayayi kama da
wanda ba'a sawa komai a cikinshi sumar nan tasha uban gyara sai k'yalli take zubawa hakama sajen
fuskarshi a kwance luf yasha mayuka masu tsada.

B'oyayyar ajiyar zuciya Heedayah tasaki wanda babu wanda yaji, gaskiya ALLAH ne ya taimaketa da
wannan gabjejen k'aton baikai hannu jikinta ba data kad'e har ganyenta dama kuma duk abinda take
k'arfin hali ne kawai amma inbanda bugu ba abinda take, kallonta ta maida kanshi ido ta zaro cikin
fad'uwar gaba tana kallon tsabar kyau da tsari wanda ubangiji yayi masa.

'Ashe balarabe ne ma ogan nasu' ta fad'a cikin ranta, Kai tsaye ta tunkari inda yake tsaye har yanzun
idanunshi akan Heedayah dake nufoshi, da masifarta ta k'arasa tana fad'in

"Ashe dama ba d'an k'asar nan bane kazo kake mana abinda kaga dama a garinmu? to ka maida
hankalinka wllhy inba hakaba watarana sai an d'aureka.



Maryam Ibraheem Aleeyu

M&S💝




*EL-- HABEEB*💥



©️Oum Hanan.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's)
No 7.



Shiru kawai Habeeb yayi ya tsurawa d'an k'aramin bakinta wanda keta masifa ido dan maganganun
nata ma dayawa ba ganesu yake ba sai faman juya baki take tana fad'a.

Hannu Aleeyu ya k'ara d'agawa da niyyar maketa jin yadda take ta fad'awa Boss d'insu maganganu
Habeeb ya k'ara dakatar dashi a tsawace.

"Nunar rana kawai". Abinda ta fad'a kenan daga k'arshe bayan ta juya masa idanu ta juya tayi tafiyarta
kallo kawai ya bita dashi harta koma wajen Zainab dake tsaye a k'ame tana kallon ikon ALLAH da tsabar
k'ok'ari irin na Heedayah.

"Dan ALLAH yallab'ai ka barni inje in casa maka yarinyar can mara kunya yarinya k'arama sai fitsara da
rashin kunya".

Kai kawai Habeeb ya girgizawa Aleeyu tare dayi musu alama ta cikin idanunshi subar wajen, nan da nan
kuwa kowa ya shige mota shima ya koma ciki Mubarak direban dake jansu ya shiga ya tada motar duk
suka bar wajen.

Lafewa ya k'ara yi a back seat d'in kamar yadda yake ada ya lumshe idanunshi yana k'ara hango d'an
k'aramin bakin yarinyar data gama musu rashin kunya yanzu kalmar nunar rana d'in data fad'a na masa
yawo a brain d'inshi anya ba zaginshi tayi ba kuwa? lallai saiya nemi ma'anar kalmar nunar rana idan ya
kasance zagine to kuwa zaisa a nemo masa ita duk cikin fad'in Kano ya koya mata darasi.

"Innalillahi, Heedayah? dama haka kike ban saniba?". Zainab ta fad'a cikin zaro ido lokacin da Heedayah
ta k'arasa wajenta.

Ajiyar zuciya Heedayah ta saki tareda dafe k'irjinta tace

"Wayyo ALLAH nah ashe ni d'in dai jaruma ce ban saniba sai yau".

"Jarumar gaske kuwa ni ina zan iya irin wannan abinda kikayi".

"Ke nimafa k'arfin hali ne kawai wlhy amma bakiji yadda k'irjina ke lugude ba".

"Duk da hakan ma dai kinyi k'ok'ari na sara miki, ke daganin irin motocin nan ai kinsan ba k'aramin
mutum bane a ciki".

Fuska Heedayah ta yatsina tace

"Balarabe ne mafa a ciki nasan duk b'ab'atun dana dingayi ma ba jina yake ba shiyasa ma ya hana
bodyguard d'in ya dakeni saboda bayaji nasan da bahaushe ne saiyasa an tumurmusa ni a wajen can,
gani nayi kawai yazo k'asar mu kuma garinmu zai raina mana hankali shiyasa nayi musu haka".
"Nifa tsoro nakeji kar yaje yayi mana wani abun kinsan masu kud'in nan maybe shirun dayayi na d'aukar
mataki ne". cewar Zainab da har yanzu take a tsorace. Hannunta Heedayah taja tana fad'in

"Dallah zomu tafi bai isa yayi mana abinda ALLAH baiyi mana ba". daga nan suka cigaba da tafiyarsu
suna hira sai bayan magreebah suka koma gida dan saida sukayi sallah ma a gidan Aunt Rumaisa k'awar
Aunt Ramlahn ta tsaresu tace sai sunyi sallah sunci abinci sannan zasu tafi.



Nunar rana shine kalmar data dinga yiwa Habeeb Gashua yawo a kanshi (Kunji dorawa kai fa reader's
🤣). Shi duk zatonshi wani salon zagine da hausawa suke amfani dashi wajen zagin mutum, dan haka a
washegarin ranar bayan sunyi wani taro da ma'aikatan kamfanin a babban d'akin taro na kamfanin
bayan antashi ya rage daga shi sai Mujaheed a d'akin, ganin yanata kallonshi yasa Mujaheed yace

"Wai kai lafiya kuwa ko kama nake maka da baby dream d'inka ne kake ta kallona haka?". Tsarabar
harara yasamu daga wajen Habeeb kafin yace

"Tambaya zanyi maka".

Saidaya d'auki ruwan faro dake gabanshi yasha sannan yace

"Ina jinka meyake faruwa?".

Saidaya cije baki yana wani girgiza k'afa sannan yace

"What the meaning of nunan rana?". yayi maganar yana tsare Mujaheed da fararen idanuwanshi.

"Nunar rana?". Mujaheed ya maimaita yana yiwa Habeeb kallon mamaki.

"Yeah". Habeeb ya amsa masa yana k'ara gyara zaman tie d'inshi.

"Kai Gashua ka cika shirme wllhy d'an fari sak idan kayi wani abun meye na wani son jin ma'anar kalmar
nan".

"Malam zaka fad'amin ne kokuwa".

"Eh to ya danganta dai shi nunar rana misali kamar yana nufin......shiru yayi yana sosa kai kafin yaja tsaki
yace

"Kaji ma'anar ta kwanta min ne gata a raina amma dai kabari zan....."Shut up ur mouth, d'an iska dama
duk k'aryar kai bahaushe ne kake mana k'aramin kalma ya gagareka".

"Kai banason iskanci fa, cewa nayi ta kwantamin bawai ban saniba gaba d'aya zakamin iskanci".

"Damuwarka ce". cewar Habeeb yana hararar shi.

"To wai me zakayi da itane?". Bai tanka masa ba ya tashi ya tattara takardun dake gabanshi ya diresu a
gaban Mujaheed yayi gaba abinshi yana kallon agogon fata dake d'aure a tsintsiyar hannunshi mai
cikeda kwantacciyar gargasa bak'a sid'ik, ganin haka yasa shima Mujaheed din ya mik'e ya d'ebi takardun
yaji bayanshi.




★★★____★★★____★★★

"Amshi wannan idan kun tashi lecture ki biya ki kaiwa Hajiya". Aunt Ramlah tace tana mik'awa
Heedayah wani abu da batasan ko meye ba acikin leda dan duk anyi wrapping d'insu amma dai tasan
bazai wuce nakiya da alkakin datayi ba shine za'a kaiwa Hajiyan, hannu biyu tasa ta karb'a tace

"Toh insha ALLAH". daga nan sukayiwa Aunt Ramlah sallama suka tafi itada Zainab.

Wajen 3pm suka fito daga lecture, sai lokacin ne take ji ashe itama Zainab wai gida zata wuce saboda ta
kwana biyu bata jeba sam bataji dad'i ba taso ace tare suka tafi haka sukayi sallama kowacce ta tari
tricycle ta fad'i unguwar da za'a kaita.

Hajiya murna kamar me saboda zuwan Heedayah itadai ALLAH ya had'a jininta dana yarinyar, bayan
sun gaisa ta bata sak'on Aunt Ramlah godiya ta shiga yi kamar ta ari baki k'warai take jin dad'in yadda
yarinyar take kula da ita, tashi Hajiya tayi ta fita da nufin tasa akawo mata abinci.

Tana zaune bayan fitar Hajiya taga kamar gilmawar mutum da fararen kaya wajen ta kalla kafin ta k'ara
juyar da kanta inda yake ada saikuma ta k'walalo ido ta k'ara waigawa dan ganin abinda tagani d'in da
gaske ne kokuwa, sanye yake cikin farar jallabiyyah fara tas kuma sabuwa dal sai irin hular nan tashi ka
fiya naci wadda ya d'ora sai hirami daya d'ora a kafad'arshi kalar fari da pink, mug ne a hannunshi ya fito
daga k'ofar kitchen yafara taka steps d'in dazai sadashi da cikin falon cikin wani irin taku na mazantaka
yana juya spoon a cikin mug d'in dake ta fidda turirin zafi.

Habeeb Gashua ne wanda idanun Heedayah suka hasko mata shi tuni yawun bakinta yafara k'afewa
wani irin bugu da kai kawo zuciyarta keyi tamkar zata fito saboda tsabar tsoro shikenan itakam tata ta
k'are dama ashe jiya da aljani tayi fad'a bata saniba dama saida Zainab ta fad'a tace maybe shirun dayayi
mata na d'aukar mataki ne gashi kuwa ta tabbata ya biyota har inda take zai cutar da ita, tuni jikinta ya
d'auki rawa sosai tafara fad'in innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir raheem da duk
wata addu'a data sani ta neman tsari daga shaid'anun aljanu wani irin fitsari na son kufce mata wanda
yazo mata a lokacin.

Tun fitowarshi daga kitchen d'in ya ganta kuma kallo d'aya yayi mata ya ganeta itace yarinyar datayi
masa rashin kunya jiya, amma duk ba wannan ba abinda ya kawota gidan yakeson sani metazo yi wajen
Hajiya? sam bai nuna yaga wata halitta a falon ba ya k'araso ya zauna a 1sitter yayi crossing legs d'inshi
kanshi a k'asa yana cigaba da jujjuya tea d'inshi. Rawa bakinta yafara tana nunashi da hannu kafin ta
k'walla wata uwar k'ara wadda ta ratsa dodon kunnenshi ya runtse ido gam saboda yadda k'arar ta
shigar masa k'wak'walwar kanshi amma duk da haka bai d'ago ya kalleta ba so yake su tafi a matsayin shi
aljanin ne kamar yadda yaga tayi zato haka nan ya tashi da sonyin irin shigar har dayazo Hajiya na
tsokanarshi wai yatuna k'asar su kenan.

Da sauri Hajiya Inna ta shigo kamar zata kifa dan sauri tana fad'in

''Lafiya kuwa Heedayah meya sameki?".

Cikin rawar baki da murya take nunashi da fad'in

"Hajiya gamo nayi wllhy, aljani ne ya biyoni nan dan ALLAH kibashi hak'uri bazan k'ara yiwa wasu rashin
kunya ba kinji Hajiya dan ALLAH kibashi hak'uri ya tafi na tuba wllhy". Inda take nunawa Hajiyan tabi da
kallo taga Habeeb tamkar baisan me akeyi ba, d'an murmushi Hajiya tayi itama dason yin tsokana tace

"To aini banga komaiba Heedayah". Sosai Heedayah ta k'ara tsurewa tace

"Hajiya gashi nan fa yana sha miki tea dan ALLAH Hajiya ki rok'eshi yayi hak'uri karya cutar dani".

Kafin Hajiya tayi magana sai gani tayi, tayi luuu tana shirin fad'owa daga kan kujerar ido Hajiya ta zaro
ta nufi wajen da sauri saidai kafin ta k'arasa Habeeb Gashua ya rigata wanda hakan yabani mamaki sosai
tunda kanshi a k'asa yake bare har yaga fad'uwar da zatayi shi kanshi yayi mamakin hakan, tallafota yayi
ta fad'a hannayenshi gaba d'aya jikinta ya saki alamun suma tayi lallai yarinyar nan ba k'aramar
matsoraciya bace wato tsiwar ce kawai da fitsara.

Hajiya na k'arasowa ya sakar mata ita ya juya ya fice batare daya k'ara bi takan shayin ba.

A rud'e Hajiya ta janyo wani ragowar ruwa a cikin glass cups dake kan center table ta shafa mata a
fuskarta, ajiyar zuciya takawo ta zabura daga jikin Hajiya tana kallon inda Habeeb yake zaune saidai
wayam babu shi ba alamarshi, kuka tasa tana fad'in

"Shikenan Hajiya na shiga uku harya b'ace ban bashi hak'uri ba".

Hajiya da batasan kan labarin ba tace

"Wai wanene meya had'aku dashi ne?".

A tsorace tabawa Hajiya labarin abinda ya had'asu kwana biyu da suka wuce, dariya Hajiya tayi tace

"To kinga wannan saiya zamar miki darasi Heedayah ba kowane mutum zaka gani a hanya ba kaci masa
mutunci wasu ba mutane bane suke shigowa cikin mutane su saje dasu kuma ko ina ana samun irin haka
abu kad'an zakiyi kuma suzo su cutar da rayuwar ki dan haka ki dinga kiyayewa kinji, wannan da kika
gani jikana ne nina haifi babanshi amma ALLAH yayi masa rasuwa mahaifiyarshi ce balarabiya shiyasa
kika ganshi haka baiyi kama damu ba saiya d'aukota".

Ajiyar zuciya Heedayah ta sauke tana dafe k'irjinta sai a lokacin taji sanyi cikin ranta wllhy duk zatonta
aljanin ne da gaske musamman da Hajiya tace bataga kowa ba amma duk da hakan da a tsorace take
dan gani take tamkar zai dawo yaci k'aniyarta a wajen dan da ganinshi da k'yar idan zaiyi mutunci wllhy
amma fa she's very very handsome guy dole ma yayi kyau ai tunda Arab ne.
A zatonku Heedayah ce Habeeb Gashua yake mafarki?




*EL--HABEEB* 💥



©️Oum Hanan.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION* 💡

(Home of expert & perfect writer's)



No 8.



Da k'yar Hajiya tasamu Heedayah ta d'an tsakuri abinci dan har lokacin bata koma normal ba gani take
tamkar zai dawo ne bini bini ta kalli k'ofar shigowa falon. Tana gama cin abincin tayi shirin tafiya duk da
yadda Hajiyan taso ta k'ara zama tace a'a tafiya zatayi akwai abinda zatayi a gidan idan takoma.

Tana fita ta shiga waige waige a k'ofar gidan ko zataga irin motocin data ganshi ranar dasuka had'u
amma ba komai da sauri tabar unguwar,sai yanzu ne abinda tayi d'azu yakeson bata dariya tafiso idan
taje gida su dara tareda Zainab.

Lokacin data koma gidan Zainab d'in ma bata dawoba sai bayan data d'an jima da komawa sannan ta
koma, aikuwa tana ganinta tajata d'akinsu ta hau bata labarin abinda ya faru a gidan Hajiya, sosai Zainab
tahau dariya harda rik'e ciki jin wai har suma saida Heedayahn tayi cikin dariyar take fad'in

"ALLAH ya k'ara, maganinki kenan ai to shi Man d'in meyace?".

Baki Heedayah ta tab'e tace

"Ko k'ala baice ba nifa nafi zaton ma ko kurma ne dan baiyi kama da masu maganar ba".

"Toh kodai shine zai maye gurbin marigayi Kabeer?". Zainab ta fad'a tana kashe mata ido, wani kallo
Heedayah tayi mata tace

"Ai mai maye gurbin Yah Kabeer saiya shirya wllhy shikam banga wani alamun jarumta a gurinshi ba sai
tsayi daya ajiye kamar daren sallah".
Dariya Zainab tayi tace

"Jarumta ai ba'a k'irar jiki

4 / 21