Author : Oum Hanan Category : African Stories & Novels
ganin kamar ba daidai bane abinda shirin yin amma a halin yanzu dai bashida wata
dabara data wuce yayi hakan idan ma mutum d'aya ce zai sani koma dai meye zai sani.
Da wannan shawarar ya kwanta bayan addu'oen dayayi har barci yayi galabar d'auke shi.
Wata sabuwa.
Kamar yadda ta saba zuwa masa cikin barcinshi yau d'inma tazo bayan barci ya d'auke shi kuma a yau
yayi nasarar ganin fuskar ta, duk da a cikin barci ne ya ganta amma yayi matuk'ar razana fuskar daya gani
ta matuk'ar girgizashi dan ba wata bace illa wannan yarinyar fuskarta yagani muraran tana jifanshi da
wani irin shu'umin murmushi wani kallo take masa wanda ya kasa fassara shi. Wata irin zabura yayi ya
tashi zaune yana ambatar sunan ubangiji yana sauke wani irin numfarfashi tamkar wanda yake filin tsere
yayin da zuciyarshi take wani irin zillo tamkar zata fito waje tsabar yadda take bugawa sai gumi ne yake
tsattsafo masa ta ko ina.
Zaune yayi a tsakiyar gadon ya kasa koda motsa d'an yatsanshi ne, dama wannan yarinyar ce datayi
shekaru tana azabtar dashi cikin barcinshi ta hanashi sukuni da jin dad'in barci kamar yadda kowa yake ji.
Idanunshi ya rufe yana k'ara hasko fuskar tata wani haushin ta yakeji, lips d'inshi ya cije tamkar zai
hudashi ya sauka daga kan gadon ya shiga zagaye bedroom d'in
Tofah!!! wata sabuwa inji y'an caca shin a cikin su ukun wacece yake mafarki da ita tsahon wannan
lokaci? Heedayah? Seeyamah ce? kokuma waccan wadda har yanzu ba aji sunanta ba??? gareku
reader's.
Bai ankara ba yaji har har anfara kiran sallahr asubah lallai ba k'aramin lokaci yaja cikin duniyar tunani
ba gashi har an kira assalatu, bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya d'aura alwalah ya fito ya zura
jallabiyyah ya fita masallaci. Bayan dawowar shi ya kwanta saboda idanunshi da suke masa zafi saboda
rashin barci gashi duk sunyi ja sun d'add'aga, bai dad'e da kwanciya ba kuwa wani irin barci mara dad'i
ya kwashe shi shi kad'ai yasan yadda yakeji a cikin zuciyarshi.
Washegari da wani zazzafan zazzab'i ya tashi ga wani masifaffen ciwon kai daya addabeshi duk yadda
yaso ya tashi yayi shirin office kasawa yayi dan haka ya cigaba da kwanciya cikin tattausan blanket d'in
daya lullub'a a ciki sam kuma baiyi hausar kiran Ummi ya fad'a mata ba.
Ganin shiru shiru bai shigo gidan kamar yadda ya saba ba yasa Ummi taji hankalinta yak'i kwanciya
tasan indai lafiya to yanzu ya shirya ya fito har sun gaisa ya tafi office, tasan halin babanta sarai yanzu
haka wani abun ne ya d'auki waya ya kirata shine abin ya gagara ya gwammace yayi ta kwanciya a d'aki
batasan wani irin hali gareshi haka ba zurfin cikinshi yayi yawa.
Wasu y'an mintunan ta k'ara ko zai shigo amma shiru dan haka ta tashi da kanta ta fita zuwa side d'in
nashi dan Neehlah tana school bare ta aikata ta gano mata shi.
Tayi sa'a tana tura k'ofar falon ta bud'e dan lokacin daya dawo sallahr asubah baisa key ba turata kawai
yayi, shiru falon sai k'arar air conditioner dake ta aiki da k'amshin shi na musamman da gaba d'aya side
d'in nashi yake d'auka.
Kai tsaye bedroom d'in ta nufa ta tura k'ofar ta shiga, tun daga k'udundunewar dataga yayi tasan ba
lafiya ba ga kuma A.C daya k'ureta gaba d'aya bedroom d'in ya d'auki wani uban sanyi mai ratsa jiki,
saidata kashe air conditioner d'in sannan ta nufi gadon ta tsaya tareda d'an janye blanket d'in fuskarshi
ta bayyana yayi saurin bud'e idanunshi ya zubasu kan Ummi dake tsaye wadda saida gabanta ya fad'i
saboda ganin yadda idanunshi suka canza launi gaba d'aya gashi sun kumbura, cikin harshen larabci take
tambayar shi me yake faruwa?. mayar mata da amsa yayi da yaren datayi masa magana ya fad'a mata
abinda yake damunshi d'an k'aramin tsaki taja tace
"Abbuna kanada matsala wllhy yanzu saboda ALLAH kana cikin irin wannan halin amma ka gaza kirana a
waya ka sanar dani? yanzu akan lafiyar taka ma sai kayiwa mutane zurfin cikin?.
"I'm sorry Ummi". yace cikin rawar murya mai data shagwab'a, kai kawai ta d'an girgiza ta samu gefen
gadon ta zauna ta fara laluben number a wayarta Dr Huzaifah shine asalin family doctor d'insu dayake
dubasu tun bayan dawowar su Nigeria tun ma da ran Abbu, shi ta kira ta sanar dashi Abbanta ba lafiya
yayi hanzarin zuwa ya dubashi ya amsa mata da gashi nan zuwa yanzu.
Tashi Ummi tayi ta fita bayan ta k'ara ja masa blanket d'in har kanshi, tea ta had'o masa mai kauri
wanda yaji had'e had'e irin nasu na Arab bata had'o masa da wani abun ba dan tasan kota had'o dashi
ba ci zaiyi ba tea d'inma tasan sai tayi fama dashi haka yake kamar k'aramin yaro idan bashida lafiya.
Aikuwa kamar yadda Ummin ta ayyana da k'yar yasha ruwan shayin bayan dogon faman datasha dashi
duk ya wani shasshake mata duk abinda yake kuma duk abin nan dayake tunanin nan yana manne da
zuciyarshi so yake kawai ya tashi yasan abinyi (Gashua jarabar duniya bakada lafiyan ma 🙄).
Kusan a tare Dr Huzaifah da Mujaheed sukazo gidan dan Dr Huzaifah yana shigowa ko rufe gate d'in
maigadi baiyiba motar Mujaheed ta kunno kai, anan farfajiyar gidan suka had'u suka gaisa sannan suka
nufi side d'in Habeeb wanda ke cikin compound d'in.
Baki suka had'a wajen yin sallama Ummi ta amsa musu suka shiga suka gaisa da Ummi Mujaheed yace
"Ashe Gashua ba lafiya Ummi?".
"Wllhy Mujaheed, zazzab'i ne da ciwon kai suke damunshi".
"Ayya ALLAH ya k'ara afwah, ai tunda naje company naga ban ganshi ba nace to ba lafiya dan indai
lafiya lafiya wannan Mr business d'in baya makara nayi trying number shi kuma switch off shine nazo
ingani saikuma na had'u da Dr shima yazo".
Y'ar dariya kawai Ummi tayi jin sunan da Mujaheed ya kira Habeeb dashi wai Mr business, tashi tayi
tace
"Bari inje Mujaheed tunda gaka ka kula dashi please Dr ayi masa duk abinda ya dace".
"Insha ALLAH". Mujaheed da Dr Huzaifah suka had'a baki wajen fad'a, ta fita taja k'ofar.
Tashi yayi zaune yana cije baki saboda kanshi dake masa wani mugun ciwo da k'yar yake bud'e ido,
Mujaheed ne yasa masa pillow a bayanshi ya jingina.
"Sannu Gashua how are u feeling now?". cewar Mujaheed yana zama a bakin gadon.
"Alhmdulillah".
Yace yana lumshe idanunshi.
"ALLAH ya k'ara lafiya". Kai kawai ya gyad'a masa shima Dr Huzaifah yayi masa ya jiki tareda tambayar
shi abinda yake damunshi
"Zazzab'i ne sai kaina yana min ciwo sosai inajin kamar zai fad'o". yayi maganar yana dafe kanshi wanda
yafi takura masa sosai.
"Oh sorry insha ALLAH zaiyi sauk'i fatan ka sawa cikinka wani abu?". Dr Huzaifah ya fad'a yana fito da
kayan aikinshi daga jaka.
Kai kawai ya kad'a masa batare dayayi magana ba.
Sosai Habeeb ya had'e rai yana wani yamutsa fuska ganin Dr Huzaifah yana had'a injection a rayuwar
shi ya tsani allura kuma tun asalinshi haka yake lokacin da yana k'aramin yaro.
Bakin gadon Dr Huzaifah ya k'arasa yana fad'in
"Bismillah Mr. Habeeb Gashua".
"Ka sani fa bana son wannan abin please ka bani magani kawai Dr". yayi maganar yana cin d'aci da
yatsina fuska.
"A'a kar muyi haka dakai mana d'an balarabe nayiwa Ummi alk'awarin zan baka dukkan kulawar data
dace kuma allurar nan itace best solution dan sam zazzab'in ba magani yake jiba".
"Wai Gashua allurar kake wa wannan goce gocen saikace wata mace? haba karka bada maza mana dan
ALLAH".
Duk da yanayin dayake ciki na jin jiki saidaya dallawa Mujaheed harara kafin ya juyo inda Dr Huzaifah
yake tsaye da allura a hannunshi.
"Haka nan dai zaka daure mutumina". cewar Dr yana y'ar dariya dan mutum ne mai wasa da dariya.
Haka nan yana ciccin magani ya shiga nad'e dogon hannun jallabiyyahr dake jikinshi, Mujaheed sai
matse dariyar shi yake yana kallon Habeeb wanda yanayin shi ya nuna kamar wanda zai saki kuka.
Matsawa Dr Huzaifah yayi ya saita inda zaiyi masa allurar a hannunshi, runtse ido yayi gam Dr Huzaifah
ya tsira masa a inda ya dace.
"Ahhhhshh". ya fad'a lokacin da allurar ta shiga jikinshi ya k'ara runtse idonshi yana k'ara damk'e
hannun da akayi masa allurar da d'aya hannun kamar zaiyi kuka.
"Ahhh kajimin wani sabon iskanci Dr allurar kakewa haka Gashua?". Mujaheed yace yana bud'e baki da
sakin dariya.
Dariya Dr Huzaifah yayi yace
"Ai kad'an ka gani Mujaheed indai Habeeb ne da allura last rashin lafiyar dayayi da ulcer shi ta tashi
danayi masa I think har kuka ma saida yayi time d'in".
"Ah haba dan ALLAH". Mujaheed ya fad'a yana zaro ido na shegantaka.
Kai Dr ya jinjina masa yana dariya gami da d'auko drip yana neman inda zai sak'alashi.
Cikin dariya Mujaheed yace
"Kutt amma dai anji kunya wllhy ka bada maza wllhy dan ubanshi saiya fita yayi tayiwa mutane muzurai
a waje yana tsorata yaran jama'a amma allura kad'ai tana girgizashi ALLAH ya kyauta maka to".
Babu wanda ya kula a cikinsu sai zamewa dayayi ya kwanta yana sauke numfashi har lokacin yanayin
fuskarshi bata gama daidaita ba. Drip d'in yasa masa sannan ya rubuta magunguna yaba Mujaheed
takardar yace a siyo su idan drip d'in ya k'are Mujaheed ya cire masa sannan ya k'ara samun abinci yaci,
daga nan yayi musu sallama ya fita Mujaheed yana k'ara yimasa godiya.
Nan Mujaheed ya cigaba da zama da Habeeb duk dama dai barci ne ya d'auke Habeeb d'in Ummi ma ta
k'ara shigowa ganin jikin nashi ta sameshi yana barci, fita tayi tana yiwa Mujaheed sannu.
*EL--HABEEB*💥
©️Oum Hanan.
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
No 13.
Har drip d'in da Dr yasawa Habeeb ya k'are Mujaheed ya cire masa bai sani ba yanata barci, sharp sharp
ya fita yaje wani babban pharmacy ya siyo magungunan yadawo yasamu har lokacin bai farka ba. Sai
abincin daya gani da lemuka da alamu Ummi ce ta kawosu.
Sai daf da Azhar sannan Habeeb ya tashi ba laifi ya d'an ji dama dama sosai a jikinshi zazzab'in kuma
tuni ya sauka sai ciwon kan da har lokacin bai gama sakinshi ba.
"Gashua ya jikin naka?". Mujaheed ya fad'a yana kallonshi bayan tashin shi
"Alhmdulillah". yace yana k'ok'arin mik'ewa tsaye ya nufi hanyar bathroom dan yin wanka Mujaheed
ya bishi da kallo kafin ya maida kanshi kan wayar da dama ita yake dannawa, ya d'an d'auki lokaci kafin
ya fito sanye da bathrobe black color da k'aramin towel a kanshi yana goge sumar shi kai tsaye clothes
d'inshi ya nufa ya bud'e wani side wanda kayan shan iska ne kawai na zaman gida ya d'auko wasu riga da
wando red color da adon fari a jiki ya koma toilet d'in ya shirya ya fito, gaban mirror ya tsaya ya taje
sumar kanshi ya shafa mata mai ya fesa turaruka sannan ya shimfid'a pray mat ya tada sallah.
Yana zaune akan dardumar bayan ya idar da sallahr Mujaheed ya kalleshi yace
"Ni zan wuce Gashua, accountant yafara kirana kasan munada lissafi dashi yau d'in nan amma tunda ga
yadda ta kasance sai mu d'aga lissafin".
Kai ya girgiza cikin sanyin murya irin ta marar lafiya yace
"No, zaku iya yi ba dole sai ina wajen ba tunda gaka hakan ma yayi".
"Okay bari inje ga abinci nan ga kuma drugs d'in nan kan bedside ALLAH ya k'ara afwah". Bai jira
amsawar Habeeb ba ya fice dan yasan mawuyacin abune ya amsa d'in.
Kallon inda kayan abincin suke yayi an shiryasu cikin babban tray yunwa yakeji sosai kuma bayajin zai
iya ci bai sha'awar komi a yanzun ga bakinshi dayake masa wani iri ba dad'i, lumshe ido yayi yana k'ara
tuna abinda ke faruwa dashi cikin y'an kwanakin nan kamar wanda akeso a haukata koma dai meye yazo
k'arshe insha ALLAH dan zai d'auki matakin dayake ganin yafi masa, saita fad'a masa dalilin dayasa take
masa wannan iskancin na canje canjen yanayi datake.
Tashi yayi ya fita falon shi ya shiga k'aton kitchen d'in dake cikin falon wanda yaji uban kayayyakin
electric, black coffee ya had'a ya koma kan kujera ya zauna ya shiga sha da zafinshi kamar yadda ya saba,
sam bai bi takan magungunan da Mujaheed yace ya siyo ba bare yayi tunanin shan su.
★
9:45pm.
K'aramar farfajiya ce wadda aka k'awata ta furanni masu k'amshi sai rumfa irin ta bunu d'in nan teburi
ne guda d'aya kacal sai kujeru guda hud'u da sukayi masa k'awanya an wadata ko ina da hasken fitilu
masu kyau da d'aukar hankali wannan duk a cikin sashen Habeeb yake nan yake d'an zama jefi jefi yana
shan iska duk da bawai zaman gidan ya cika yiba kafin ya zauna d'in ma aiki ne.
A yau dai a daidai kuma wannan lokacin yana zaune a ciki yana jiran zuwan Aleeyu wanda sukayi waya
dashi yana son ganinshi. K'arar ringtone d'in wayarshi ne yasa ya bud'e idanunshi da suke rufe, hannu
yakai ya d'auko wayar dake ajiye bisa table d'in yayi picking yakai kunnenshi sam banji abinda yace ba
saboda yadda yayi maganar tashi murya a shak'e kamar mai ciwon mak'ogwaro.
Shud'ewar wasu y'an mintunan da basu wuce biyu zuwa uku ba Aleeyu ya shigo cikin farfajiyar ya
k'araso inda Habeeb yake, sallama yayi ya shiga ciki.
"Yallab'ai barka da hutawa". yace yana d'an rissinawa alamun girmamawa, sallamar kawai ya amsa yayi
masa nuni da d'aya daga cikin kujerun wajen cikin mak'alalliyar murya yace
"Sit".
Kujera Aleeyu yaja ya zauna ya sunkuyar da kai yana jiran yaji abinda maigidan nasu zai fad'a, Habeeb
bai k'ara magana ba yayi shiru tareda rufe idanunshi sai faman girgiza k'afa yake, shidai Aleeyu yana
zaune yana jiran Habeeb ya gama shan k'amshin nashi yaji kiran dayake masa, muryar Habeeb yaji yace
"Ina tunanin zaka gane yarinyar nan da muka gani a orphanage house wadda nace sai tabar gidan?".
"Yes sir, zan ganeta".
Baki Habeeb ya d'an cije lokaci d'aya yana lumshe ido sannan ya bud'esu akan Aleeyu dayake jiran k'arin
bayani.
"Inaso ka sace min ita". yayi maganar yana k'ara had'e rai sosai, a razane Aleeyu ya zaro ido yana kallon
Habeeb wanda hankalinshi kwance baza kace ma shi yayi magana makamanciyar wannan ba (jama'a
kowa yayi ta kanshi Habeeb Gashua ya zama d'an kidnappers 🙆🏃🏃).
Wani mugun kallo Habeeb ya jefawa Aleeyu hakan yasa ya danne tsoratar dayayi ya shiga shafa kai da
fad'in
"Sorry sir".
K'aramin tsaki Habeeb yaja yace
"Idan ka d'auko ta ka kaita can k'aramin gidana na lamid'o crescent ka tabbatar babu abinda ya sameta
ko kwarsane (k'warzane) kunsan mutumin no hausa 😅) banaso ya sameta do you hearing me?". ya
k'arasa maganar yana d'an kama gefen kunnenshi tareda yiwa Aleeyu kallon gargad'i, Kai kawai Aleeyu
yake gyad'awa da tunanin yaushe maigidan nasu ya koma haka? kidnapped fa kenan duk da baisan
dalilin shi na b'oye yarinyar ba, maganar Habeeb ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi
"Zaka iya tafiya, kar kowa yasan da wannan maganar bare har yasan ka d'auko wata yarinya yin hakan
zai iya ja maka matsala understand?".
"Yes sir, yaushe za'ayi hakan kenan?". cewar Aleeyu.
"A yau da daren nan". yace kai tsaye yana mik'ewa tsaye tareda zura hannu a aljihun wandonshi ya
zaro wani key ya mik'awa Aleeyu, rissinawa yayi ya karb'a key d'in duk da yadda gabanshi yake ta
fad'uwa saboda irin aikin da yallab'ai yasa shi.
"Good luck". Habeeb yace murya a dashe tareda fita daga cikin rumfar Aleeyu ya take masa baya.
"Ka kula". Habeeb ya k'ara fad'a lokacin da Aleeyu yake k'ok'arin fita daga side d'in nashi.
"Insha ALLAH". Aleeyu ya amsa masa.
Rufe side d'in nashi yayi ya koma ciki, wanka yayi ya d'aura alwalah cikin nutsuwa yayi raka'ah biyu yayi
addu'oen shi sannan ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya barci. Abin mamaki kuma sam
a wannan daren baiyi mafarkin yarinyar ba kamar yadda ya saba abin ya d'aure masa kai da tunanin me
hakan kuma ke nufi???.
°•°•°•°•°•°
A wannan daren Aleeyu yayi nasarar k'wamuso Seeyamah yarinyar gidan marayu bayan ya k'ulle mata
baki ta yadda koda tayi ihu ma babu wanda zaiji ALLAH ya bashi sa'a kuma sam bai samu matsala ba har
ya fice da ita ya sata a mota yabar wajen da mugun gudu.
Tun a daren ya kira Habeeb ya sanar dashi aiki ya kammala, yaji dad'i sosai ya k'ara jaddada masa ya
kula da ita zuwa da safe zai shigo unguwar daga nan sukayi sallama.
Plat house ne gidan da Aleeyu yakai Seeyamah had'add'e ne sosai yaji kayan k'awa tako ina masu kyau
da tsada, kuka sosai Seeyamah take na fitar hankali tareda yiwa Aleeyu magiyar ya taimake ta maida ita
inda ya d'aukota karya cutar da ita, baiyi magana ba bare ya tanka mata yasa ta cikin wani bedroom ya
rufo ya koma falo ya zauna yanajin duk ba dad'i ga tausayin yarinyar daya cika masa rai bai san dalilin
d'auko yarinyar ba wato bai hak'ura kenan dama, jiyake tamkar ya d'auketa ya maida ita inda ya
d'aukota lokacin da shasshek'ar kukanta ke ratsowa cikin falon dayake.
A takure take a k'asan royal bed d'in dake d'akin ta matse kanta cikin gwiwoyinta tana kuka mai cin rai
waye wannan mutumin daya d'aukota? meye had'inshi da ita? wane laifi tayi masa? tambayoyin datake
ta maimaita su cikin zuciyarta ta kasa samun amsar su, kasancewar ya rufe fuskar shi da face mask
shiyasa batasan waye ba kuma koda ta ganshi d'in ba lallai ta ganeshi ba tunda ranar da sukaje gidan
marayun bata ganshi ba koma dai waye tana addu'ar ALLAH ubangiji ya kub'utar da ita daga sharrin shi.
Afwan da kad'an, na shiga busy ne wayar ma sai in yini ban d'auke ta ba hidima tayi yawa 🙏.
Mrs Salees Mu'az 💝
*EL--HABEEB* 💥
©️Oum Hanan.
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
No 14.
Gajiya Aleeyu yayi da zaman ya zame ya kwanta kan leather chair d'in dake falon yana lumshe idanunshi,
so yake yayi barci amma kukan Seeyamah ya hanashi badan karya rasa aikinshi ba daya d'auki yarinyar
nan ya maida ita gidan marayun daya d'auko ta, shi dai ba zaice yallab'ai yayi kidnapping d'in nan saboda
kud'i ba to dan me yayi kenan? shine amsar da har yanzu ya kasa samu kuma bashida wanda zai
tambaya tunda daga shi sai yallab'ai suka san abinda yake faruwa ba'a kuma buk'atar wani ya shigo ciki.
Da wad'annan tunane tunanen barci yayi nasarar sace shi cikin rashin jin dad'i.
Hankali kwance Habeeb yasha barcinshi, koda ya dawo daga masjeed ma sallahr asubah wani barcin
ya k'ara komawa sai k'arfe tara da y'an mintuna sannan ya tashi, bathroom ya shiga yayi wanka, cikin
k'ananun kaya ya shirya k'irar kamfanin D&G black trouser jeans da red shirt mai gajerun hannuwa
wanda hakan ya bawa cikakkun fararen damatsen shi damar fitowa, bak'in takalmi yasa k'afa