Author : Oum Hanan Category : African Stories & Novels
juna shikenan kuma tasan tayi rashin da har
abada bazata maye gurbinshi ba a yanzu gidan daga ita sai Nihlah.
Kamar yadda addini ya tanadar idan mutum ya mutu za'a raba gadonshi haka akayi Abbu ma anyi rabon
gadonshi an fitarwa da mahaifiyarshi nata kason sannan y'an uwanshi saikuma iyalanshi hak'ik'a Abbu ya
tara dukiya mai tarin yawa ga kadarori inda kowanne saidaya samu kaso mai tsoka cikin abinda aka bashi
cikin abinda aka bawa Habeeb da k'annenshi harda babban kamfanin Abbun wanda yafi kowanne
kamfani ne dayake had'a cinikayya tsakanin k'asashe gefe d'aya kuma akwai masarrafar k'arfe duk a cikin
kamfanin dad'in dad'awa kuma k'aton gidan da suke ciki wanda Abbun ya gina a unguwar Nassarawa
G.R.A shima mallakinsu ne sun samu tarin alkhairi dayawa wanda wannan duk baya gaban Habeeb.
Dole ya ajiye aikinshi yadawo Nigeria dan cigaba da kula da wannan kamfanin da sauran abubuwan da
aka bar musu, sosai wancan kamfanin na Dubai yaji ba dad'i sunyi bak'in cikin rabuwa dashi dan fara
aikinshi a kamfanin ba k'aramin alkhairi yajawo musu ba da k'ara yin suna kullum cikin kawo sabbin
dabaru yake ta kwanyar da ALLAH ya bashi ta yadda kamfanin zai k'ara hab'aka kuma suna ganin cigaba
sosai hakan yasa lokacin dazai bar aiki masu kamfanin suka yimasa gagarumar kyauta ta kud'i tsabarsu
farko ma cewa yayi bayaso bazai karb'a ba saida suka takura masa shima daya tashi ba duka ya amsa ba
ya ciri wani abu ya maida musu sauran dan a ganinshi kud'in sunyi yawa.
Bayan dawowar shi yasa aka k'ara gyara kamfanin ya fito ana zamani sosai aka k'ara samun gogaggun
ma'aikata aka zuba yafara aiki, Mujaheed shiya d'auka a matsayin P.A d'inshi wato personal assistant
manager Mujaheed d'an k'anwar Abbu ne wadda take binshi a haihuwa Hajiya Aisha kuma dama a
kamfanin yake aiki yasan takan aikin sosai, bama shi kad'ai ba akwai y'an familyn Gashua dayawa dasuke
aiki anan.
Ummi taso ta koma k'asarsu Hajiya Inna ta rok'i alfarmar ta zauna dasu saboda matuk'a take k'aunar
Ummin har cikin ranta tanajin dad'in zama da ita k'warai da gaske, tsananin girma da mutuncin Hajiya
Inna da Ummi ke gani yasa ta amince bazata iya yimata musu ba saitaga kamar ko dan babu ran d'anta
ne amma tabbas taso tafiya tunda bataga zaman dazatayi a nan d'in ba.
Alhaji Sulaiman Gashua shima yadawo kusa da gidan Abbu anan ya tamfatsa gida suka dawo shida
iyalanshi da Hajiya Inna dama tana gidanshi.
Har a yau bakin Habeeb bai daidaice da hausa ba magana d'aya zaiyi zaka fahimci ba zallar bahaushe
bane a hakan ma Auwal Mahmood Azare wanda sukayi karatu tare shiya taka muhimmiyar rawa wajen
koya masa hausa tunda dangin ubanshi hausawa ne so dole watarana zai zauna a cikinsu kamar yasan
hakan zata faru kuwa saigashi yadawo cikin nasu dayake yanada brain saiyake d'auke komai duk da
yadda hausar take masa wahala amma yana k'ok'arin yinta sosai saidai maganar tashi ce abin dariya idan
yanayi shiyasa sau tari suke fad'a da MJ idan yaji yana magana da hausa yayi ta masa dariya shikuma ya
hau yaita masa masifa. Ita kanta Ummin har yanzu fama take itama tana magana zaka ganota Nihlah
kam dama y'ar garin hausawa ce da hausa ta taso a bakinta dan ma dai tun tana k'arama Ummi tana
yawan yimata larabci hakan yasa ta tashi da wasu abubuwan sosai kuma tanajin duk abinda aka fad'a
mayarwar ne wani lokacin yake gagararta.
M&S💝
*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO
SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA
MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI
TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI
HAR GUDA BAKWAI.
1- *KAUNA CE*
NA UMM ASGHAR
2- *RUKUQI*
NA FEEDHOM
3- *WANI SO*
NA ZEE YABOUR
4- *SO DA ALAKA*
NA UMMI AISHA
5- *MUGUN GANI*
NA SADIYA NASIR DAN
6- *ABDUL_HAMEED*
NA NANA DISO
7- *MUKULLIN ZUCIYA*
NA MAMAN KHADY
Daya 200
biyu 400,
guda uku 500
Guda hudu 700
Guda biyar 750
Shida 800 bakwai 1000 da programs
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL
KAI KA KAI....!
TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-
SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA
AGAREKU MASOYAN MU...
1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍
*DAGA CHEF RAHMA NA LELE*
2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA
YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA
*DAGA AYUSHER MUH'D*
3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN
AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI
*DAGA HAJJA CE 👈*
MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN
_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN
ACCOUNT👇🏼_
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS
*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*
+447894142004
IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*
07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki
_GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO
ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_
+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.
MUN GODE.
*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*
_Wannan garabasar tamai rabo ce😍
sa kud'i kad'an ki debi hani'an😂_
*EL--HABEEB* 💥
©️Oum Hanan.
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
No 5.
Haka zatayi ta bak'in rai musamman idan taga Aunt Mashhoodah tazo sun zauna da Ummi sunata hira
tunda ita bawai komai ne take jiba.
Back to story.
KATSINA.
K'ofar K'aura.
Madaidaicin d'aki ne wanda aka lailayeshi da siminti sai ledar tsakar d'aki da aka malaleshi da ita sai
k'aramin fridge da y'ar k'aramar TV ta jikin bango kallo d'aya dai zaka yiwa gidan ka gano na masu rufin
asiri ne da wadatar zuci.
Yarinya ce y'ar kimanin shekara sha bakwai zaune cikin d'akin a kan tabarma sai faman kuka take
tamkar ranta zai fita sai wata dattijuwa zaune a gefenta d'aya gefen kuma wata matashiya ce wadda
bazata wuce haihuwa d'aya zuwa biyu ba sun sata a tsakiyarsu kukanta take bilhaqqi da gaskiya duk da
irin rarrashin da suke mata kuwa amma sai k'arawa kukanta volume take kamar wadda ake yankar
naman jikinta.
Wannan matashiyar ce ta dafa kafad'arta a karo na ba adadi tun zamansu a wajen cikin sanyin murya
da son yin rarrashi tace
"Haba *HEEDAYAH* dan ALLAH kiyi shiru haka kar kiyi ciwon kai, tun d'azu fa kike kukan nan ki
sassautawa ranki haka mana addu'arki Kabeer yake da buk'ata a halin yanzu ba kukanki ba Kabeer ya
mutu kuma muna masa kyakkyawan zaton samun rahmar ubangiji kiyi hak'uri dan ALLAH".
Cikin shasshek'ar kuka tace
"Aunt Ramlah shikenan fa nida Yah Kabeer mun rabu har abada bazan k'ara ganinshi ba taya zansamu
kamar Yah Kabeer Aunt Ramlah? mutumin da tun ina y'ar tatsitsiyata yake dako da d'awainiya da sona
yake wahalta min duk d'an abinda ya samu a kaina yake k'arewa koyaushe farin cikina shine nashi taya
ba zanyi kuka ba". Ta k'are maganar tareda fad'awa jikin dattijuwar dake gefenta tana cigaba da kukanta
itakuma ta shiga jijjigata tana shafa bayanta alamun rarrashi, lallai dole Heedayah tayi kukan rashin
Kabeer ya sota ya nuna mata k'auna duk da irin tarin k'alubalen daya dinga fuskanta daga wajen
danginshi da mahaifiyarshi akanta saboda wani dalili wanda basa son had'a auratayya tsakanin d'ansu da
ita wanda ita kanta yarinyar bata san dashiba kuma batasan akanme suke nuna mata k'iyayyar ba, saura
kwana bakwai bikinsu ALLAH yayi masa rasuwa sakamakon accident din daya samu akan hanyarshi ta
zuwa Kaduna inda yake sana'ar shi ko shurawa baiyiba ubangiji ya d'auki abinshi yau kusan sati biyu
kenan da rasuwar tashi amma har yanzu Heedayah bata bar yin kukan rashin shiba sosai rasuwar tashi ta
bugeta kullum cikin kuka da sambatu duk da rubutun dangana da Malam ke amso mata wajen malamin
da suke d'aukar karatu bayan sallahr magreebah abin harya fara bawa Umma tsoro, cikeda tausayawa
Aunt Ramlah tace
"Nikam Umma wata shawara mana mezai hana mutafi da Heedayah can Kano ta d'anyi nisa da garin
nan ko yayane maybe ta d'an samu salama ta daina yawan tunanin shi amma sai abinda kukace Umma".
Shiru Umma tayi tana nazarin maganar Ramlah to amma saidai ba lallai bane Malam ya amince ganin
ita kad'ai ce a gabansu shi Mustapha ba'asa lissafi dashi shi namiji ne saisu yini ma basu sashi a idonsu ba
yana can wajen sana'ar shi ta d'inki.
"Umma ya kikayi shiru ko baki amince bane". Aunt Ramlah tace tana marairaice murya.
Zama Umma ta gyara tareda k'ara gyarawa Heedayah dake jikinta kwanciya tace
"To ai ni kad'ai bazan yanke hukunci ba Ramlah, tunda ba yaune tafiyar taki ba kibari zuwa anjima idan
Malam yadawo saiki tambayeshi idan ya amince ai bawani abu bane saiku tafi taren indai hakan zai
samar mata nutsuwa da kwanciyar hankali".
"Insha ALLAHU ma zai yarda Umma ai hakan saiyafi kinga nan fa tana fita ga gida ga gida ko bataso
indai zataga gidansu saiya tuna mata dashi". cewar Aunt Ramlah.
Kai kawai Umma ta jinjina ta maida kallonta kan Heedayah da kanta ke kan cinyarta tace
"Zakibi Auntyn ki gidanta Heedayah?".
"Ni Umma banaso inyi nesa dake idan natafi fa bakowa saike kad'ai shi Yah Mustapha ba ganinshi
akeba". Murmushi Umma tayi tana k'ara jin tausayin yarinyar na shigarta, kanta ta shiga shafawa tana
fad'in
"Ba komai Heedayahta indai kinason zuwa kije kinji ALLAH yayi miki albarka yabaki miji nagari kije
famfo ki wanke fuskarki kizo kici abinci kinga duk yau baki sawa cikinki komai ba". Amsawa Umman tayi
tana k'ara share hawayen idanunta ta tashi ta fita tana gyara d'aurin d'ankwalin ta, duk da kallon tausayi
suka bita harta fice kowanne yana k'iyasta halin dazata samu kanta duk ranar datasan ita d'in
WACECE ?.
Kamar yadda Umma tacewa Aunt Ramlah ta tambayi Malam idan ya yarda hakan akayi kuwa bayan
yadawo sallahr Esha'e yaci abinci ya huta taje ta sameshi da maganar da farko dai k'in amincewa yayi sai
data dinga faman magiya sannan ya amince cikin murna da farin ciki take masa godiya ta d'ora da fad'in
"Kaga Baba tunda ga yadda ta kasance idan mukaje sai a samar mata makaranta ta cigaba kafin ALLAH
ya kawo mata miji tayi aurenta". Kai kawai ya jinjina mata yace
"ALLAH yasa hakan shine mafi alkhairi".
Da ''Ameen" ta amsa sannan ta tashi tabar wajen.
Washegari da daddare Heedayah tana shirya kayanta na tafiya tanayi tana kuka tana k'ara tuna
masoyinta ashe babu rabon suyi aure kullum buri da mafarkinsu su mallaki junansu a matsayin
ma'aurata ashe babu rabon hakan watannin bikinsu ma da akasa yaji yayi masa yawa haka yaje ya tasa
babanshi a gaba yanata masa magiyar dan ALLAH yasamu Malam suyi magana a rage shi wllhy watannin
sunyi masa yawa hakan akayi kuwa shima baban nashi ya biye masa yasamu Malam sukayi magana aka
sauko da bikin har Mustapha yayanta yanata zaginshi a lokacin wai bashida kunya dayake abokinshi ne,
dariya kawai yayi masa a lokacin yana masa gwalo, batasan lokacin data k'ara fashewa dawani irin kuka
ba ragowar kayan ma sai Umma ce ta k'arasa shirya mata su.
Washegari wajen k'arfe sha biyu na rana direban Aunt Ramlah yazo d'aukarta, tunda Heedayah taga
dai gadan gadan tafiyar za'ayi har ansaka kayansu a mota tafara kuka ta rirrik'e Umma kamar wadda
akace idan tatafi bazata k'ara dawowa ba da k'yar Aunt Ramlah ta jata suka fita ko sallama basuyi da
Umman ba, bare da suka fito ta kalli gidan su Kabeer saita k'ara fashewa dawani kukan kawai tana tuno
irin rayuwar da sukayi dashi mai dad'i shikenan yanzu mai rabawa ta raba saita k'ara tuno yadda idan
yazo ganin gida duk ranar dazai koma Kaduna wajen kasuwancin shi haka zatasa masa kukan shagwab'a
ita bataso yatafi ya barta haka zai lalace wajen rarrashin ta har sai yaga yasata dariya sannan zai iya
tafiya yabar wajen ko wane irin sauri yake kuwa, yau gashi yayi doguwar tafiyar da har abada bazai k'ara
dawowa ba bare tace zasu had'u watarana.
A hanya ma saida Aunt Ramlah tayi ta faman rarrashi sannan tasamu tayi shiru daga baya ma barcine
ya d'auketa a jikin Aunt Ramlah.
★★★
Habeeb ne da Mujaheed zaune a kyakkyawar harabar gidansu Habeeb d'in kusa dawasu shuke shuke
masu ban sha'awa da k'ayatarwa kan wasu kujeru na gini sai table da aka had'a shima da abinda akayi
kujerun, soft drink's ne kala kala akai da fruits a yayyanke a plate plate anyi wrapping d'insu da leda.
Habeeb sanye yake cikin riga mai gajeren hannu da wando red color marasa nauyi na kamfanin Adidas
wanda sukayi matuk'ar haskashi kasancewar shi fari, Mujaheed kuma manyan kaya ne a jikinshi riga da
wando na maroon shadda, kowanne kanshi a sunkuye yake da waya a hannunshi hakan yasa babu mai
magana a cikinsu kowa hankalinshi nakan waya can kuma Mujaheed yaga Habeeb ya daina kallon wayar
ya k'urawa wata k'aramar bishiya ido kamar wanda yake son lissafa ganyen jikinta kallonshi yake tayi
amma sam baisan yanayi ba da alamu yayi nisa cikin duniyar tunani.
"Gashua". Mujaheed ya ambaci sunanshi cikeda mamakin meye damuwarshi haka?
a hankali ya maida kallonshi kan Mujaheed daya kira sunanshi.
"Are u okay?" Mujaheed ya tambaya.
Saidaya sauke wani nannauyan numfashi sannan yace
"Yes I'm fine". yace yana zame tattausan slippers d'in k'afarshi ya mik'eta kan table d'in ya maida kanshi
kan wayar.
"Banga alamun hakan ba Gashua, yaushe kafara b'oyemin damuwarka? kanaso mufara y'ar haka ne a
tsakaninmu ko? kokuma baka yarda dani bane kai kanka kasani bana b'oye maka komai daya shafeni duk
wani sirrina na fili dana b'oye kasani Gashua dan me kai kake k'ok'arin b'oyemin bayan kuma nasan
akwai wani abu".
Ido Habeeb ya lumshe yakai hannu yana yamutsa lallausar sumar kanshi kafin ya bud'e ido ya kalli
Mujaheed dake kallonshi cikin sanyin murya yace
"MJ, na dad'e a cikin wannan halin tun abin baya damuna yanzu yanaso yayi tasiri a kaina, shiru ya
d'anyi kafin ya cigaba da fad'in
"Mafarki nake MJ".
"Mafarki kuma? kamar yaya Gashua?". Mujaheed yace cikin mamaki yana kallon Habeeb dake shafa
sajen fuskarshi.
"Mafarkin mace". yabashi amsa kai tsaye batare da tunanin Mujaheed zai fassara maganar ba, cikin
matse dariya Mujaheed yace
"Kuna wani abune a cikin mafarkin?".
Kallon zanci ubanka Habeeb ya jefa masa yace
"Kullum tana zuwa min ne fuskarta a rufe da mayafi saitazo zata bud'e sai in farka narasa yadda zanyi
I'm confused MJ". ya k'arasa maganar yana d'an girgiza kai da cije lips d'inshi na k'asa.
"Tun yaushe kenan?". cewar Mujaheed.
"Five years". Habeeb ya bashi amsa. Ido Mujaheed ya zaro yace
"Five years fa kace Gashua? hod'ijam inji fulani gaskiya ya kamata ka tashi tsaye da addu'a indai hakane
koma wacece ita ALLAH ya bayyana mana ita tafito fili mu ganta ra'ayul aini bata dinga zuwa cikin
mafarki tana susuta mana Boss d'inmu ba koya kace mutumin?". Banza yayi masa bai kulashi ba
Mujaheed yace
"Kokuma wajen masu fassarar mafarki zamuje a fassara mana abinda mafarkin yake nufi?".
"No, kamar dai yadda ka fad'a d'in zan cigaba da addu'ar amma idona idon yarinyar nan saina
hukuntata dan ba k'aramin wuya take bani ba". yace yana cije lips d'inshi gamida shafa kwantaccen
sajenshi.
Dariya sosai Mujaheed ya fashe da ita yace
"How? kaida har yanzu bakaga face d'inta ba ta yaya zaka iya ganeta a fili? kaidai kawai kayi addu'a
Gashua kar a kauce hanya ta mafarkin".
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu'az 💝
*EL--HABEEB*💥
©️Oum Hanan.
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
_Ina mik'a sak'on ta'aziyya ta ga Ummi Aysha dama k'ungiyar mu ta HASKE na rashin mahaifiya datayi
ALLAH ubangiji yaji kanta yayi mata rahma yasa aljannace makoma yabawa iyalanta hak'urin rashi ya
kyautata namu k'arshen yaji kan dukkan musulmai baki d'aya_.
No 6.
A fusace Habeeb ya d'ago ya kalleshi jin yadda yake tamasa fatan kusantar yarinyar duk da a cikin
mafarkin ne, cikin harshen shi na hausa da har yau bai gama daidaita ba yafara masa masifa dan duk
miskilancin shi idan aka tab'oshi haka yake zagewa yayita bala'i kamar bashine maganar ma take masa
wahala ba.
Tsaki Mujaheed yayi yana dafe goshinshi yace
"Ka taimakeni ka daina min masifa da hausa Gashua, ka dinga yimin da turanci yadda zan dinga ganewa
amma ni wllhy wannan rub'abb'iyar hausar taka bawani fahimtar ta nakeba kuma kace lallai lallai sai
kayi". Sosai Habeeb ya k'ara shak'a tsaki yaja ya mik'e ya zura slippers d'inshi ya d'auki wayarshi yabar
wajen Mujaheed ya bishi yana masa dariya da kiran sunanshi amma ko juyowa baiyiba bare ya kulashi ya
shige part d'inshi dake cikin harabar gidan wanda shima zaman kanshi yake dan kamar wani k'aramin
gidan ne saboda girman shi.
Kano.
Rijiyar zaki.
A y'an kwanakin da Heedayah tayi a gidan Aunt Ramlah tafara jin dad'in zaman gidan k'warai
kuma damuwarta tafara raguwa ta rage tunanin Kabeer ba kamar lokacin datake Katsina ba musamman
daya kasance akwai k'anwar mijin Aunt Ramlah d'in a gidan Zainab wadda suke kusan sa'anni da ita
saidai Zainab d'in zata d'an girme mata bayan tagama secondary school ya d'aukota tadawo gidanshi da
zama da nufin sama mata gurbin karatu a jami'a wanda bayan zuwan Heedayah shi mijin Aunt Ramlahn
Uncle Muhammad ya yanke shawarar samar musu tare Aunt Ramlah tayi ta godiya.
Cikin d'an zaman da sukayi suka saba sosai da Zainab ita kanta Zainab d'in sai yanzu zaman gidan yake
mata dad'i sab'anin da daga ita sai yaran Aunt Ramlah Nusrah babbar school take tafiya tahfeez tun safe
sai yamma sai d'ayar dataci sunan mamansu suke kiranta da Hajiya itakam batafi shekara d'aya bama
goyonta ake shiyasa gidan duk yake mata ba dad'i yanzu kam da Heedayah tazo tasamu abokiyar hira.
Ba'a d'auki dogon lokaci ba Uncle Muhammad ya samarwa Heedayah da Zainab gurbin karatu a YUSUF
MAITAMA SULE UNIVERSITY kusa dasu, sunyi murna sosai suka sameshi sukayi masa godiya.
Nan da nan suka fara zuwa d'aukar lecture, Heedayah ta k'ara kyau farinta ya k'ara fitowa sosai Uncle
Muhammad yayi musu sabbin d'inkuna da dogayen riguna saboda shiga school ba abinda zata cewa
bawan ALLAHn nan saidai ALLAH ya saka masa da alkhairi yasa yagama da duniya lafiya yanada matuk'ar
kirki da sanin ya kamata aikuwa ya k'ara fito dasu sosai suke d'aukar wanka idan zasu tafi kuma bana
rashin hankali ba dan yawanci ma sunfi using da hijabs irin na yayin nan da akeyi kuma ba ruwansu da
shiga shirgin kowa kawai abinda ya kaisu sukeyi.
Uncle Muhammad d'aya daga cikin yaran Alhaji Sulaiman Gashua ne a kasuwa kuma yana jidashi da
mutunta shi saboda rik'on gaskiya