Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

El Habeeb Complete Hausa Novel by Oum Hanan

Author :  Oum Hanan Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 21

39K to 42K   out of 61.8K words

waje, tsaki kawai yake ja yana duba agogon hannunshi saboda sauri yake
yakoma gida yanada uzurin da zaiyi, kamar ance ya waiga gefenshi ya hango Aleeyu shima zaune a cikin
mota yana jira a bada hannu, shifa dama ya dad'e baiga Aleeyun ba to yayi zaton ko har dashi ya kora ne
abinda ya k'ara bashi mamaki bai wuce ganin yadda Habeeb yake yawan yin waya da Aleeyu ba dama
gashi yana zargin Habeeb d'in akan Seeyamah hakan yasa lokacin da aka bada hannu yabi bayan Aleeyu.

Tiryan tiryan ya dinga bin Aleeyu batare daya bari yagane shi yake bi ba har lokacin da suka isa unguwar
ta lamid'o crescent Aleeyu ya shiga cikin unguwar shikuma Mujaheed anan bakin titi yayi parking ya fito
ya dinga takawa a k'afa yana bin Aleeyu bayan ya toshe idanunshi da bak'in glass ga face mask dayasa,
binshi yake yana mamakin unguwar da sukazo d'in sun tab'a zuwa da Habeeb ya nuna masa wani plat
house daya siya kuma idan bai manta ba nan unguwar ne.

Aleeyu bai dad'e yana tafiya ba yayi parking a k'ofar wani gida, ido Mujaheed ya zaro ganin k'ofar gidan
dayayi parking d'in nan ai shine gidan da Gashua ya kawoshi d'in hakan na nufin......bai k'arasa tunanin
shiba yaga Aleeyu ya fito daga cikin motar da sauri yasamu wani d'an lungu ya lab'e ya lek'o da kanshi
yana kallon Aleeyu ya bud'e gidan ya shiga da wata leda mai d'auke da tambarin sunan wani gidan abinci
a hannunshi, mamaki, tsoro, al'ajabi gamida d'imbin tararrabin abinda zaije ya tarar ne a cikin gidan
suka sandarar dashi a tsaye a wajen kardai abinda ya dad'e yana zargi tun bayan sanarwar b'atan
Seeyamah daya gani ya tabbata idan kuwa hakane me yake damun Gashua? ta ina ya kamata ya shiga
gidan addu'a yake a cikin ranshi ALLAH yasa Aleeyun ya fito ko zai samu hanyar shiga yaga meye a ciki.

Addu'ar shi taci kuwa dan Aleeyu bai dad'e da shiga gidan ba sai gashi ya k'ara fitowa da sauri ya k'ara
lab'ewa har Aleeyun yazo ya k'ara wucewa a mota yabar layin.

Cikin hanzari Mujaheed ya fito daga d'an lungun dayake ya nufi gidan, cikin sa'a kuma yana tura k'ofar
gate d'in yaji ta bud'e abin mamaki, shiga yayi ya maida k'ofar ya rufe yana k'arewa gidan kallo. A hankali
ya shiga takawa zuwa k'ofar babban falo na gidan itama dai yana murd'a handle d'in yaji ta a bud'e shiga
yayi ya rufe yana bin ko ina na falon da kallo an k'awata ko ina yaji royal chair shi a lokacin da Habeeb
d'in ma ya kawoshi ba asa komai a cikin gidan ba.

Dube dube ya shiga yi ko zaiga wani abin amma ba komai hakan yasa ya maida akalar binciken nashi
kan d'akunan barcin gidan na b'angaren dama nan ma duk inda ya bud'e ba abinda yake gani a ciki,
d'ayan b'arin yakoma ya bud'e bedroom na farko yaga ba komai gaba yayi yasa hannu ya bud'e na biyun
idanunshi suka d'auko masa hoton Seeyamah tana zaune akan gado ta tsurawa waje d'aya ido da alamu
ta fad'a cikin zuzzurfan tunani, kamar ko yaushe babban hijabine a jikinta ta rufe ko ina na jikinta hatta
k'afafunta ba'a ganinsu fuskar tace kawai ta bayyana.

Wani mugun bugawa k'irjinshi yayi zuciyarshi tamkar zatayi tsalle ta fito tsabar tsorata da yayi da
abinda idanunshi suka gani har wani jiri jiri ne yaji yana neman kada shi.....




Masu buk'atar a tallata musu hajarsu zasu iya nemana ta wannan number

09139964697.



Maryam Ibraheem Aleeyu

Mrs Salees Mu'az 💝




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF.
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).



Jama'a bafa paid book bane anata tambaya na har nagaji da amsawa 😒 free book ne.



No 25.



Seeyamah ma hankalinta ta maida kan k'ofar taga wani tsaye yana kallonta ba Aleeyu bane sannan
kuma ba wancan mutumin dayasa aka k'wamuso ta bane tunda shi yafi wannan d'in datake gani tsayi
gashi kuma ya rufe idanunshi, sosai gabanta ya buga tafara tunanin kodai wani ne daban yazo ya cutar
da ita? A hankali ya shiga takawa zuwa cikin bedroom d'in yana k'ara jin mamakin abinda yasa Gashua ya
kawo wannan yarinyar gidan nan.

A tsorace ta shiga ja baya kamar zatayi kuka tana kallon yadda yake k'ara kunsanto ta, yana zuwa bakin
gadon ya tsuguna kan gwiwoyinsa yana cigaba da kallonta wani mugun tausayin ta na k'ara ratsashi.

"Dan ALLAH karka cutar dani bawan ALLAH kayi hak'uri I'm sorry please". ta fad'a cikin rawar murya
tana had'e hannayenta waje d'aya alamun rok'o idanunta duk sun cika da ruwan hawaye, gam ya runtse
idanunshi cikin tsananin tausayin ta, hannu yasa ya zare glass d'in idonshi da face mask d'in fuskarshi ido
ta zaro ganinshi datayi a gidan nan dan bazata tab'a mantawa da fuskar bawan ALLAHn nan ba shine yayi
sanadin komawar ta gidan marayun bayan wannan ogan na Aleeyu ya koreta, duk saitaji wata nutsuwa
na shigarta tana rok'on ALLAH ta sanadiyyar shi ta fita daga cikin wannan prison d'in kana ganin fuskar
shi kasan mutumin kirki ne.

Ganinshi yasa ta saki wani marayan kuka na tausayin kanta da halin datake ciki, da sauri ya tashi ya
zauna bakin gadon kusa da ita cikin taushin murya data had'u data rarrashi yace

"Please Seeyamah stop crying I'm so sorry". ya k'arasa maganar kamar shima zaiyi kukan gamida zaro
wani kyakkyawan k'aramin hanky fari mai adon pink d'in flowers a jiki ya mik'a mata daga aljihunshi ya
mik'a mata sai tashin k'amshi mai dad'i yake, hannu tasa ta karba ta shiga sharewa tana sharewar wasu
na k'ara zubowa.

"Please I'm sorry mana Seeyah, kiyi shiru ya isa haka uhmm? ko kinaso kanki yayi ciwo?". A hankali ta
girgiza masa kai.

"Ko so kike nima inyi kukan?". Nan ma kai ta girgiza masa
"Okay yanzu ki fad'amin waye ya kawoki nan gidan kuma tun yaushe kike anan?". ya ida maganar
tareda zaro wayarshi daga aljihu ya danna recording ya ajiyeta kusa dashi, cikin kuka Seeyamah take
fad'in

"Ba wannan abokin naka bane wanda ya tab'a korata daga gidan marayu yasa aka d'auko ni ya kawoni
nan".

"Why me kikayi masa?". Yace yana k'ok'arin had'iye b'acin ranshi hak'ik'a Habeeb ya bashi mamaki.

"Wallahi ni bansan me nayi masa ba kawai yasa an d'aukoni yacemin wai meyasa nake bibiyar rayuwar
shi kuma dole saina fad'a masa waye shi sannan zai maidani na rantse da ALLAH ban sanshi ba bansan
wani abu game dashi ba ka taimakeni dan ALLAH". tayi maganar tana shirin k'ara sakin wani kukan cikin
sauri yace

"No no Seeyah don't cry please insha ALLAH zaki bar gidan nan kinji?".

Kai ta gyad'a masa tana fad'in

"Ka tafi dani yanzu dan ALLAH".

Kai ya girgiza yace

"Ba yanzu ba Seeyamah ki kwantar da hankalinki kinji kamar kin fita kin gama ne yanzu dai karki fad'awa
kowa zuwana shima Aleeyun dayake tsaronki karki nuna masa nazo zan dawo anjima ko gobe in tafi
dake relax ur self ok?". Sosai ta marairaice fuska tana kallonshi gani take tamkar idan ya riga ya tafi bazai
dawoba jitake tamkar ta rik'eshi saiya tafi da ita.

Murmushi ya d'an saki yace

"I'm promise to u insha ALLAH karki damu". ya k'arasa maganar yana mik'ewa tsaye ya maida wayarshi
cikin aljihu ya juya zai tafi.

"Dan ALLAH karka k'i dawowa ka taimakeni". Mujaheed ya tsinkayi muryar Seeyamah na fad'a cikin
rauni.

Wani irin tausayin tane ya k'ara shigarshi ya runtse ido tsigar jikinshi na tashi a hankali ya juyo ya kalleta
tareda sakar mata wani murmushin yak'e cikin k'asa k'asa da murya yace

"I'll promise insha ALLAH". daga nan bai saurari abinda zatace ba ya fice da sauri zuciyarshi na bugawa.
Yana fita Seeyamah ta k'ara sakin wani kukan ta cusa kanta tsakanin gwiwarta tana rizgar kukanta gani
take tamkar shikenan Mujaheed ya tafi bazai dawoba.

Ya dad'e sosai zaune a cikin motarshi ya kwantar da kanshi kan seat d'in motar idanunshi a rufe har
lokacin bai gama dawowa daga rud'ani da d'imbin mamakin abinda yasa Gashua ya gark'ame Seeyamah
ba me yake nema a duniyar nan? meye ubangiji baiyi masa ba da har zaiyi garkuwa da yarinya, yarinyar
ma ta gidan marayu wadda idan ba'a tausaya mata ba ai ba'a cutar da ita ba, tsaki yaja a karo na ba
adadi yana tunanin ta ina zai fara yanzu? bazai tab'a bari Gashua yayi abinda ranshi yakeso ba saiya gane
kuskuren shi anya ba police kawai zaije yayi k'arar Gashua ba? da sauri ya girgiza kai a fili ya furta

"No impossible, to kodai Habeeb zai samu da maganar nan ma kai ya girgiza yasan Gashua farin sani
kamar yunwar cikinshi yanzu yana iya yayi masa maganar ya nuna sam baisan ma wani abu makamancin
wannan ba ko ya nuna yayi d'in ya d'auki matakin da duk yake ganin zai d'auka dan haka ma bazai
yimasa maganar ba Ummi kawai ya kamata ya samu ba wani zancen ya rufa masa asiri yayi ba daidai ba
yanaso kuma har cikin ranshi yaji ba daidai d'in yayi ba a nuna masa kuskuren shi, sosai ya aminta da
shawarar da zuciyarshi ta bashi hundred percent dan haka cikin hanzari ya tada motar kai tsaye ya nufi
gidansu Habeeb wajen Ummi.



★_____________★

Shiru falon ya d'auka bakajin komai sai k'arar air conditioner dake d'akin bayan Ummi ta gama
saurarar abinda Mujaheed yaje mata dashi ya kuma kunna mata recording d'in dayayi da abinda
Seeyamah take fad'a, ba k'aramin rud'ani da tashin hankali Ummi ta shiga ba a lokacin ta shiga b'acin rai
fiye da tunanin mai karatu abin ya tab'ata fiye da tsammani d'anta na cikinta wanda ta haifa shine yayi
kidnapping me yake nema a rayuwar nan? wane mataki ne bai taka ba a rayuwar shi? jikinta har rawa
yake ta d'auki wayarta ta lalubo number Habeeb d'in ta danna masa kira sai sauke numfashi take sama
sama fuskarta tayi jawur saboda b'acin rai, Mujaheed kanshi saiyaji dama baizo mata da maganar ba
amma kuma hakan shine daidai bai kamata ya rufe maganar ba bawai dan bayason Habeeb d'in ba
kokuma yanaso ranshi ya b'aci bane hasalima yana matuk'ar gudun b'acin ran Habeeb kuma har a
yanzun yanaji baiyi wani abu wanda ba daidai ba.

Habeeb na d'aga kiran Ummi tace yazo tana nemanshi duk inda yake kuma duk abinda yake ya bari
yazo, sam bata saurari tambayar dayake mata ba na lafiya kuwa meyake faruwa ta kashe wayarta ta
ajiyeta gefe sai gaman girgiza k'afa take tana huci.

Nan suka cigaba da zama ita da Mujaheed ba wanda ya k'ara yin wata magana, ko cikakkun mintuna
goma ba'a rufa ba Habeeb ya shigo cikin falon kamar ko yaushe sallama a ciki ciki, Mujaheed nema
kawai ya amsa sallamar Ummi kam wani irin mugun kallo tabi Habeeb dashi wanda take yasha jinin
jikinshi gabanshi ya fad'i, ido suka had'a da Mujaheed ya wurga masa wani kallo duk da baisan ainihin
abinda yake faruwa ba.

Gefen Mujaheed ya zauna kusa da k'afafun Ummi yana saurarar abinda Ummin zatace, hannu ta
mik'awa Mujaheed sanin abinda take nufi yasa ya d'ora mata wayar akan hannunta bayan ya cire
pattern, play ta danna sannan ta mik'awa Habeeb wayar kallonta yayi cikin rashin fahimta tsawar data
daka masa ne da kuma muryar yarinya dayaji tana magana tana kuka yasa yayi hanzarin karb'a. Ido ya
d'an zaro jin abinda yarinyar take fad'a gabanshi yayi wata irin bugawa ba shiri ya mik'e tsaye yana bin
Mujaheed da wani irin mugun kallo shima Mujaheed d'in k'yar yake kallon Habeeb d'in ba tareda shayin
komai ba.
Tsaye Ummi ta mik'e ta tsaya a gaban Habeeb tana binshi da wani tuhumammen kallo cikin rawar
murya Ummi tace

"Abbuna meka aikata haka? me kakeso ka zama ne? me kake nema a rayuwar ka da har saikayi
garkuwa da mutane? nace me kake nema?". ta k'arasa maganar cikin tsawa tareda sakar masa wani
mahaukacin mari a kuncinsa na dama kafin ya dawo daga tsananin rud'ani da mamakin daya shiga na
marin da Ummin tayi masa ta k'ara bashi wani marin a kumatunshi na hagu, da sauri Mujaheed ya taso
ya rik'e hannun Ummi lokacin datake niyyar k'ara kai masa wani marin.

"Dan ALLAH Ummi kiyi hak'uri ki zauna dashi kuyi magana ta fahimta kiji dalilin shi na d'aukar yarinyar
please Ummi I'm sorry".

"Har wani dalili yake dashi dan ubanshi dazai d'auke yarinyar jama'a? ka sani idan har wani abu yasamu
yarinyar mutane ALLAH bazai tab'a barinka ba shashasha sakarai saikuma ta canza harshe cikin yaren
larabci ta shiga zazzagawa Habeeb fad'a ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, Habeeb dai yana tsaye
tamkar wanda aka dasa kanshi a k'asa idanunshi har wasu ruwa suka tara tsabar bala'in dake cinshi duk
wannan fad'an da Ummi take sama sama yake jinta kawai yana kissima yadda zaici uban Aleeyu dashi
kanshi Mujaheed d'in tunda munafuki ne shi ta yaya har ya gano Seeyamah tana wajenshi? koda yake ba
laifinshi bane duk laifin Aleeyu ne da baiyi sakaci ba da duk haka bata faru ba zai nuna masa waye
HABEEB GASHUA.

Mayafin doguwar rigar dake jikinta Ummi ta gyara ta cewa Mujaheed suje ya kaita wajen yarinyar, tun
kafin taga yarinyar tausayin ta ya kamata kuma take taci burin insha ALLAH tabar gidan marayun kenan
ita zata d'auke ta tadawo hannunta da zama zata zame mata uwa uba zatayi mata gatan da zatayiwa
d'an data haifa a cikinta.

Fita sukayi suka barshi nan tsaye har lokacin bai d'ago kanshi ba ajiyar zuciya kawai yake saukewa ta
b'acin rai idanunshi sun kad'a sunyi jawur jijiyoyin kanshi duk sun fito rad'a rad'a dasu, suna fita
Mujaheed ya dawo falon kusa da Habeeb yaje ya tsaya yace

"Kayi hak'uri abokina banyi haka dan in b'ata maka raiba kokuma dan in had'aka da Ummi ba hakan
danayi shine daidai I'm so sorry Ummi tace kazo mutafi tare". bai jira amsawar shiba yayi hanyar fita dan
yasan idan zai kwana yana masa magana a lokacin dai bazai tankashi ba gari banza ma anyi magana ya
share mutum bare yanzu da ranshi yake a b'ace? ai sai abinda mutum yagani kawai.

Sai a lokacin Habeeb ya d'ago kai yabi bayan Mujaheed da wani irin kallo na tsabar takaici jiyake tamkar
yayi masa d'iban karan mahaukaciya wllhy sai yaci ubanshi badai shi yayiwa haka ba? k'wafa ya saki da
k'arfi yana jijjiga kai gamida cije baki, da k'arfi yake takawa kamar zai tashi sama ya fita daga falon....




Alhmdulillah nasamu sauk'i ku tayani addu'ar ALLAH yasa kar ya dawo tunda akayi cikon dai har yanzu
bai k'ara tashi ba ALLAH yasa ya tafi kenan nagode sosai da addu'oen ku a gareni sakallahu khayran💔.
Yaudai Gashua ansha maruka😝 fuskar zata k'ara nuna yanzun😂.



Wasu zasuce Mujaheed bai kyauta ba nidai yamin daidai aradu ko nice haka zanyi masa😄



Maryam Ibraheem Aleeyu

Mrs Salees Mu'az 💝

09139964697.




*EL HABEEB*💥



©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF.



*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).



No 26.



Yana fita yaga Ummi da Mujaheed har sun shiga motar da ake kai Ummi unguwa ƙatuwar Jeef ce black
color sai walƙiya take, bai nufi inda suke ba saiya nufi inda yayi parking ɗin tashi motar a fusace ya buɗe
ya shiga yana shirin tada ita yaga Mujaheed ya fito daga ya nufo inda yake, so yayi ya figi motar tashi
yabar gidan sai kuma ya fasa ya cigaba da kallon Mujaheed ɗin ya fito ya lakaɗa masa dukan tsiya.

Glass ɗin motar Mujaheed ya ƙwanƙwasa bayan isowar shi sai daya mula sannan ya zuge glass ɗin
tareda watsawa Mujaheed wani banzan kallo, cikin matse dariya Mujaheed yace

“Ummi tace ka fito mu tafi gaba ɗaya”. Banza Habeeb yayi masa ya ƙara cewa
“Wai bakaji abinda nace bane Gashua?”. A fusace ya ɗago ya kalleshi cikin kufula yace

"Na rantse idan baka ƙyaleni ba zan take ka da mota a wajen nan".

Ido Mujaheed ya zaro sosai yayi baya da sauri yana ɗage hannaye sama cikin son bada haushi yace

"Innalillahi! bayan kidnapping ɗin kisan kai zaka fara Gashua?". Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare
maƙwogwaron Habeeb saidai bai tankawa Mujaheed ɗin ba dan yana tarashi ne wllhy saiyaci uwarshi
tunda munafuki ne shi, fitowa yayi daga motar bammm ya maida murfin ƙofar da uban ƙarfi ya nufi inda
Ummi take Mujaheed ya rufa masa baya yana masa dariya.

Front seat ya buɗe ya shiga Mujaheed kuma ya shiga driver seat bayan ƙarasowar shi ya tada motar
suka fita daga gidan.

Tunda suka tafi ba wanda yayi magana kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarshi jefi jefi Mujaheed
ke juyowa ya kalli Habeeb so yake yayi tsokana amma ganin Ummi a wajen kuma bata cikin yanayi mai
daɗi yasa yaja bakinshi ya tsuke, shima Habeeb ɗin dayaga hakan kawai saiya kwantar da kanshi bayan
kujera ya rufe idanunsa dan zai iya kaiwa Mujaheed ɗin naushi batare daya sani ba.

Parking sukayi a ƙofar gidan Mujaheed da Ummi suka fito daga motar shikam gogan naku yasani sarai
anzo amma ko motsi yaƙi yi yayi bakam dashi, Ummi ce ta buɗe side ɗin dayake da larabci ta shiga
yimasa cikin faɗa kamar zata dakeshi ba shiri ya fito yana wani kumbura fuska kamar zaiyi kuka, gaba
Ummi ta tasa shi tabi bayanshi shi dama Mujaheed tuni yana bakin ƙofar yana knocking da alamu
Aleeyun yana ciki.

Ba'a daɗe ba sukaji muryar Aleeyu yana tambayar waye? shiru akayi ba wanda yayi magana sai Ummi
ce data kalli Habeeb wanda ya gane ma'anar kallon datayi masa dan haka murya ƙasa ƙasa irin wanda
aka takurawa ɗin nan ya amsawa Aleeyu daya buɗe ƙofar shine.

Mamaki ne ya cika Aleeyu yasan ko lokacin dayake ɗan yawan zuwa gidan farko farkon kawo Seeyamah
kenan baya masa knocking saidai ya kirashi a waya yazo ya buɗe masa, bai damu ba kuma bai kawo
komai cikin ranshi ba dan yasan halin ubangidan nashi bauɗaɗɗen mutum ne da ba'a gane gabanshi bare
bayanshi yau kuma ra'ayin knocking ɗin yayi dan haka kai tsaye ya buɗe ƙofar yayi tozali da Habeeb ɗin
tsaye bakin ƙofar ya soke hannayenshi cikin aljihun wandonshi yana binshi da wani matsiyacin kallo mai
hautsina zuciyar duk wanda akayiwa, wata faɗuwar gaba ce ta sameshi lokaci ɗaya musamman mutanen
daya hanga a bayan Habeeb ɗin da sauri ya kauce yabasu hanya suka shiga yana gaida Ummi amma sam
bata kulashi ba ta shige ciki suka rufa mata baya banda faɗuwa ba abinda gaban Aleeyu yake shikenan
yasan yau yarasa aikinsa tun daga irin kallon da oga Habeeb ke jifanshi dashi daga ni ba sauƙi, Mujaheed
ne ya yiwa Ummi jagora zuwa ɗakin da Seeyamah take Habeeb kam daga falo ya coge yayi tsaye tamkar
wani dogari har lokacin bai cire hannayenshi daga cikin aljihun wandonshi ba, Aleeyu dayake duk a
tsorace ya buɗe baki zaiyi magana kenan Habeeb ya jefeshi da wani irin kallo cikin tsawa yace

"Stop it! idan ka sake ka furta kalma ɗaya a nan zan

14 / 21