Author : Oum Hanan Category : African Stories & Novels
amsa a zafafe
"Idan kaga na fito to mun gama siyayyar da zamuyi ne ai kanada ƙafafu ka shigo ka karɓa mana mara
mutunci". yana faɗar haka yayi hanging calling ɗin yana dariya tareda faɗin
"Autar Ummi quickly please wannan yayan naki bai cika M ba". juyowa tayi tana ɗan ɓata fuska ta
shagwaɓe murya tace
"Kai Yah Mujaheed Yah Habeeb ɗin?".
"Ah ba gaskiya na faɗa ba? ke kanki kinsan halin yayanki ai saidai ki take saboda kinajin tsoronshi".
Baki ta ɗan taɓe tace
"Gaskiya kam Yah Mujaheed kana fama wllhy kaida kuke tare dashi kullum".
"To yana iya? ALLAH ya riga ya haɗa ni kaina watarana shakkar shi nake dan dai kawai ina mazewa ne".
Dariya Seeyamah da Neehlah sukayi shima Mujaheed dariyar ya shiga tayasu yana ƙara cewa Neehlah
tayi sauri ta zaɓi abinda zata zaɓa su tafi kafin Gashua ya fashe.....
*_Zan ƙara yawan pages ɗin ko zuwa 35 ne saimu tsaya kafin mu ɗora book two ALLAH ya bada ikon siya
amin_*
Afwan da yadda yanayin typing ɗin yake zuwa ban cika jin daɗi ba ga hidimar iyali ALLAH yasa mudace.
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu'az 💝
09139964697
*EL HABEEB*💥
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💥
(Home of expert & perfect writer's).
_*Anata tambaya ta book one ya ƙare ne? ƙasan page ɗina na yau na sanar cewar zan ƙara 5 pages
saɓanin baya danace iya 30 page book one zai ƙare yanzu zai ƙare ne a 35 pages fatan kun fahimta
nagode sosai 💖*_
No 31
Kamar yadda Mujaheed ɗin ya faɗa kuwa Habeeb ya cika yai fam ƙiris yake jira ya fashe sai faman girgiza
ƙafa yake yana cije baki shi damuwarshi ma yadda Mujaheed yake kunyata shi a gaban ƙananan yaran su
Neehlah daya sani ma tun farko da Mujaheed ɗin ya haɗasu suka taho shi yayi zamansa dan dai kawai
kuma Ummi zatace baibi umarnin ta ba.
Neehlah dai jin Yah Habeeb nata faman dokawa Mujaheed kira yasa ba shiri sauri sauri ta zaɓi abinda
ya kamata ta zaɓa ɗin daga kan English wear dogayen riguna, huluna takalma da sauran kayayyakin adon
mata, wajen biya sukaje Mujaheed ya biyasu aka zuba musu a ƙatuwar leda sannan suka fito ma'aikacin
wajen ya biyosu da kaya niƙi niƙi booth ya buɗe masa yasa a ciki lokacin har su Seeyamah sun shiga
motar, shima Mujaheed zagayawa yayi ya shiga driver seat ya zauna ya kalli Gashua wanda tun fitowar
su ya ƙara haɗe rai yana faman muzurai.
"Yadai Mr Habeeb Gashua mun barka kanata jira ko?". cikin salon tsokana yayi maganar yana dariya,
idan kujerar da Habeeb yake zaune kai tayi magana to shima ya tankawa Mujaheed, wata dariyar
Mujaheed ya ƙara saki yace
"ALLAH dai ya biya Ogah mun tuba ayi mana afwah kanmu bisa ƙafafunmu". ya ƙarasa maganar yana
kama kunnuwan shi.
"Na rantse zan fasa maka baki Mujaheed". ya faɗa a hasale yana kallonshi, ido Mujaheed ya zaro tareda
buɗe baki yace
"ALLAH ya baka haƙuri Boss".
Tsaki Habeeb ya saki yayi relaxing kan seat ɗinshi ya rufe idanunshi gami da harɗe hannayenshi kan
ƙirjinshi yana faman jijjiga ƙafafu, motar Mujaheed ya tayar ya harbata kan titi suka tafi.
Tunda suka tafi ba wanda yayi magana a cikinsu har suka isa Mudassir & brothers shi Habeeb ma duk
zaton shi gida suka dawo dayaji anyi parking yana buɗe idanunshi ya gansu a wani waje daban Mujaheed
ya kalla kafin yace
"Nan kuma ina ka kawomu MJ?".
"Mudassir & brothers ne". Mujaheed ya bashi amsa.
"Ina ne haka?". yace yana yamutsa fuska.
"Wajen siyar da atamfofi ne da sauran manyan kaya can inda muka baro babu irinsu".
Shiru kawai yayi baice komai ba hakan yasa su Seeyamah suka fita suka tsaya suna jiran Mujaheed ɗin
ya fito su shiga.
"Yanzun ma bazaka shiga ba Gashua?". cewar Mujaheed yana kallonshi.
"Ka fini sani ai". amsar daya bashi kenan yana danna waya.
"Sorry yanzu zamu fito ba daɗewa zamuyi ba". Mujaheed yace yana ƙoƙarin buɗe murfin motar ya fita.
"Ku daɗe ma mana kagani idan banci ubanka ba daga kai har su ɗin". dariya kawai Mujaheed yayi ya
fita daga motar ya maida murfin ya rufe, relaxing ya ƙara yi sosai yana latsa waya yau dai yaga ta kanshi
sai yawo ake dashi cikin gari.
Mujaheed bai daɗe da shiga ba kiran abokin nan nashi da suka haɗu a Dubai lokacin dayaje karatu can
ya shigo wayarsa Auwal Mahmoud Azare wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen koyawa Gashua hausa
ba laifi suna zumunci ta waya bayan ƙare karatunsu kuma shima Auwal ɗin ne ya fara nemansa,
murmushi yayi yai picking tareda kai wayar kunnenshi saidai bai furta komai ba shima Auwal yasan
bazai furta ɗin ba dan haka yace
"ALLAH ya taimaki Ogah".
"Azire ya kake?". Dariya Auwal yasa yana faɗin
"Azare nefa sunan mutumina tun zamanin school nake gyara maka amma har yanzu baka iyaba".
Haɗe rai Habeeb yayi yace
"Kai ka sani dai".
Wata dariyar Auwal yayi yace
"Na shigo garinku fa yau Kano yanzu haka ina cikinta".
"Serious?".
"Yeah munzo ɗaurin aure ne na wani abokin mu daya auri ƴar Kano so su sun wuce ma tun ɗazu nikuma
na wuce Mandawari gidan wani kawuna sai gobe zan wuce da safe nace bari in nemeka mu gaisa".
"Oops gashi bana gida yanzu ya za'ayi inaso mu haɗu".
"Kana ina?".
Kai ya ɗaga ya ƙara kallon ginin dan harya manta sunan da Mujaheed ya faɗa masa ɗazu sunan wajen ya
faɗawa Auwal yace ba matsala gasu nan zasuzo shida ɗan kawun nasa zai rakoshi daga haka suka katse
wayar.
Nan ma siyayya sosai Mujaheed yayiwa Seeyamah harta rasa bakin magana harda Neehlah itama saida
yayi mata tata siyayyar.
Cikin ma'aikatan wajen ne ya rakosu da kayan wajen mota bayan sun biya akasa musu a booth.
Mujaheed na shirin tada motar bayan su Neehlah sun shiga yaji Habeeb yace
"Wait.....akwai wanda nake jira zaizo yanzu".
"Waye?". Mujaheed ya tambaya
"Auwal wanda mukayi school ɗaya a Dubai". yabashi amsa batare daya kalleshi ba.
"Maimakon yaje gida ya jiramu Gashua?".
"Ina ruwanka? ban cika son shisshigi cikin al'amurana ba". yace yana harararshi, baki Mujaheed ya taɓe
bai dai ce komai ba.
Nan suka cigaba da zama kowa ya kama waya yanata danne danne har zuwa lokacin dasu Auwal suka
ƙaraso wajen, Habeeb da Mujaheed suka fita suka taresu.
Jikin motar Auwal suka tsaya suna gaisawa da tambayar bayan rabuwa sosai Habeeb yayi murna da
ganin Auwal Mujaheed dayake yanada saurin sabo nan da nan suka saba da Auwal da ɗaya saurayin
daya rakoshi Abbas.
Wayarshi dake hannunshi ya nemo number Neehlah ya kirata cikin faɗuwar gaba ta ɗaga kiran, tana kai
kunnenta taji shi cikeda faɗa yana faɗin
"Idan kika sake nazo wajen nan saina karya ki dan ubanki kina ganina da baƙo kinfi ƙarfin kizo ki
gaisheshi ko?". bai jira abinda zatace ba ya kashe wayar.
"Yaa ALLAH". Neehlah tace tana dafe goshinta shidai mutumin nan idan bai ƙaƙalo laifi ya ɗorawa
mutum ba bayajin daɗi yanzu meye laifinta anan? hannun Seeyamah taja tana faɗin
"Please Sisi zo ki rakani in gaishe da baƙon Yah Habeeb kafin a karyani a kanshi".
Fuska Seeyamah ta yatsina tace
"Nidai kam Neehlah da kinje kin dawo kawai nifa tsoron yayan can naki nake wllhy".
"Dan ALLAH kizo muje please banason zuwa ni kaɗai wllhy". Ganin yadda duk ta damu yasa Seeyamah
ta buɗe murfin motar ta fita itama Neehlah ta fita suka nufi inda su Habeeb suke tsaye.
Tunda suka doso inda suke Auwal ya kafe Neehlah da kallo yanajin wani irin al'amari na shigar shi
wanda bai taɓa tsintar kanshi cikin yanayin ba, har suka ƙaraso bai ɗauke idanunshi daga kanta ba
wanda har Mujaheed da Abbas dake tsaye a wajen suka gane hakan Habeeb dai baisan me akeba dan
kanshi na ƙasa da waya a hannunshi, tsaki Neehlah taja cikin ranta ganin irin kallon ƙurillar da wannan
abokin na Yah Habeeb yake binta dashi kamar wani maye, rissinawa sukayi suna gaisheshi lokacin da
suka ƙarasa Auwal ya amsa yana wani washe baki, tunda Mujaheed yaga haka wani irin ɓacin rai ya
kamashi zuciyar shi ta dinga tafarfasa kawai sai yayi musu sallama ya koma cikin mota ya zauna.
Su Neehlah ma suna gaisheshi suka dawo wajen motar su, ta cikin glass ɗin motar Mujaheed yake
kallon yadda Auwal yabi bayan Neehlah da kallo kamar zai biyota sai wani murmushi yake yana shafa
sumar kanshi tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka yaji a lokacin ko ba'a faɗa masa ba yasan da wani
abu a cikin zuciyar Auwal ɗin lallai lokaci yayi daya kamata ya fallasa sirrin zuciyar shi bai taɓa zama yayi
maganar data danganci soyayya da Neehlah ba ada bai taɓa tunanin ma sonta yake ba ya ɗauka duk
soyayya da shaƙuwa da sukayi na ƴan uwantaka ne sai baya bayan nan ya gane cewar sonta yake.
Suna zuwa suka shiga motar Neehlah na ƙara jan wani tsakin ta tsani kallo a rayuwarta kuma tanajin
idanun mutumin a kanta lokacin da suka juya baya, shima Abbas wanda suke tare da Auwal mota ya
shiga yana jiran Auwal ɗin.
"Mutumina wai wace wannan yarinyar da kuke kama da ita ne? badai ƙanwarka bace?".
"Yes she is my sister". habeeb ya bashi amsa.
"Wow masha ALLAH amma baka taɓa faɗa min kanada ƙanwa haka ba Gashua". Auwal yace yana
murmushi.
"Kasan komai kamawa take". cewar Habeeb.
"Gaskiya ne amma fa she's very beautiful tayi ba ƙarya yaushe zakuyi mata aure ne?".
Sai daya dalla masa harara kafin yace
"Ina ruwanka?". dariya Auwal yayi yace
"Kaifa ba'a maganar arziƙi dakai abokina naga dai ƙanwarmu ce kuma kasan hausawa sunce idan kaga
kare yana shinshinar takalmi to ɗauka zaiyi".
Wani banzan kallo Habeeb ya jefawa Auwal yace
"Kunada matsala wllhy shiyasa dole ƙananan yara su rainaku bakuda girma saina jikinku".
"Eh munji ɗin kaidai har yanzu bazaka canza ba wannan shegen son girman naka yana nan muna nan
mun zuba ido muga wadda zaka aura".
"ALLAH ya tsareni da auren ƙaramar yarinya kowa ma mara aikin yine irinku".
"Lokaci ne zai nuna mana hakan dude kaidai kayi addu'ar ALLAH yasa karka folawa ƙaramar yarinya
wllhy duk wani girma da jiji da kai bakasan lokacin da zaka saukeshi ba kazo kana ƴar murya".
Tsaki Habeeb yayi kawai duk ya ɗauki maganganun Auwal ɗin shirme auren ƙaramar yarinya ko ɗorawa
kai wahala.
Sallama sukayi da Auwal wanda yake ta ƙara yimasa maganar Neehlah yaƙi kulashi Auwal ya shiga
motar shi shima Habeeb ya nufi tasu motar.
Tunda suka tafi Mujaheed baiyi magana ba jin ranshi yake duk ba daɗi shi kanshi habeeb ya lura da
canjin yanayin da Mujaheed ɗin ya shiga ya buɗe baki ya tambaye shi dalilin hakan ne yake jin wahala.
Neehlah da Seeyamah ma sun kula da Mujaheed ɗin ya daina walwala duk da basu san meya canza shi
ba.
Hanyar unguwar su ya nufa yana faɗin
"Su fara zuwa can ɗin basai ya koma ta gidansu ba, Habeeb dai bai tankashi ba har zuwa gidan su
Mujaheed ɗin daga nan yayi musu sallama ya sauka Habeeb ya koma driver seat ɗin dan cigaba da tuƙin,
amma maimakon ya fara driving ɗin saiya ɗauki waya kawai ya fara dannen dannen waya, kallon juna
Seeyamah da Neehlah sukayi cikin mamaki.....
Afwan kamar kullum😁
_A ƙara haƙuri dai yanayin labarin ne yanada tsayi sosai so banaso muyi gaggawa mubi komai hankali
har zuwa lokacin da ALLAH zaisa muje inda mukeson zuwa_
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu'az 💝
09139964697
*EL HABEEB*💥
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's).
No 32.
Sunfi ƙarfin 20min a wajen batare da sun tafi ba kokuma ya buɗe baki yace musu wani abu gaba ɗaya
sun gaji da zaman cikin motar, hankalinshi kwance yake latse latsen wayarshi.
Sai zuwa yanzu ne Neehlah ta fara tunanin dalilin dayasa yaƙi tafiya idan suka tafi a haka ya zama
kamar wani direbansu kenan ya buɗe baki yace wata ta dawo front seat a cikinsu shine ba zaiyi ba kai
jama'a ALLAH ya shiryi mutumin nan.
Bakinta takai saitin kunnen Seeyamah ƙasa ƙasa kamar munafuka tace
"Sisi ki taimaka ki koma gaba nasan abinda yasa yaƙi tafiya kenan wllhy ba kuma zai buɗe baki yace wata
a cikinmu ta koma ba". Ido Seeyamah ta ɗan zaro itama cikin ƙasa ƙasa da murya tace
"Nifa tsoronshi nakeji Neehlah please ke ki koma gaban". Kai Neehlah ta girgiza tana shagwaɓe fuska
tareda zungurin Seeyamah cikin raɗa tace
"Please and please Sisi kar muyi haka dake mana". Kan dole Seeyamah ta buɗe murfin motar ta fita
jikinta har rawa yake ta buɗe front seat ta zauna, bai juyo ya kalli wadda ta zauna ɗin ba haka kuma bai
bar danna wayar dayake ba, Seeyamah gaba ɗaya a tsorace take gani take kamar zaiyi mata wani abun.
Saida aka kwashi kusan mintuna biyar sannan ya ajiye wayar ya tada motar suka tafi a tare Neehlah da
Seeyamah suka saki ƙaramar ajiyar zuciya, tafiyar kurame dai aka ƙara yi har zuwa lokacin da suka ƙarasa
gida. Idi mai bawa fulawa ruwa shine ya shigar musu da kayan sukabi bayanshi, Habeeb ma kuwa cikin
motar suka barshi sukayi gaba Neehlah na faɗin tunda dai sun fito lafiya alhmdulillah yau dai Mr ɗacin
rai ya zama direba.
Bedroom ɗin Ummi suka fara shiga suka sanar da ita dawowarsu tayi musu sannu da zuwa daga nan
suka wuce nasu bedroom ɗin lokacin anata kiran sallahr magreebah, suna shiga sukayi alwalah suka
gabatar da farali sannan suka koma bedroom ɗin Ummi suna nuna mata kayan anan Neehlah take
faɗawa Ummi ai duk Yah Mujaheed shine ya biya kuɗin siyayyar Ummi taji daɗi sosai ta shiga sa masa
albarka.
Bayan sallahr Esha'e Ummi ta shiga gidan su Hajiya Inna zuwa lokacin tasan Alhaji Sulaiman yadawo
gida dan tanaso tayi magana dasu, part ɗin Alhaji Sulaiman ɗin ta fara shiga suka gaisa dashi da matarshi
ta sanar dashi akwai maganar datake so suyi dashi da Hajiya nan yace mata taje sashin Hajiyan ta jirashi
zaizo.
Cikin tsantsar kulawa da mutunta juna Ummi da Hajiya suka gaisa daga nan suka fara taɓa hira har
lokacin da Alhaji Sulaiman ya shigo sashen.
A tsanake daki daki Ummi ta shiga yiwa su Hajiya bayani daga lokacin da Mujaheed yazo mata da
bayanin komai da gidan dataje ta ɗauko yarinyar ta maida ita gidan marayun ta gangaro kan ɗauko
yarinyar datayi zuwa gidanta dan cigaba da riƙonta a taƙaice dai tana neman afwarsu na yadda ta yanke
hukuncin ɗaukar yarinyar ba tareda neman shawarar su ba.
Sunyi mamaki ƙwarai kuma daga Hajiya har Alhaji Sulaiman sunga sanarwar da akayi ta sace yarinyar
ashe habeeb ne ya ɗauke ta, sai yanzu Hajiya ta fara tunano lokacin daya shigo yaga Heedayah a wajenta
irin yanayin daya shiga da kuma neman ƙarin bayani dayazo ji a wajen ta ikon ALLAH kenan Heedayah
ƴan biyu ne? to amma kuma Ramlah bata taɓa faɗa mata ba tace mata Heedayah ita kaɗai ce ƙanwarta,
idan hakane kuwa itama zataso ace Habibu ya binciko musu gaskiyar lamarin abin akwai ɗaure kai sosai.
Duk cikinsu ba wanda ya kushe abinda Ummin tayi saima yaba mata da sukayi taimakon maraya ai ba
ƙaramin lada gareshi ba ubangiji yanason masu taimakawa marayu kuma ɗa na kowa ne, sun ƙara
tattauna maganar sannan Ummi tayi musu sallama zata tafi Alhaji Sulaiman na ƙara jaddada mata duk
hidimar yarinyar idan ta tashi ayi masa magana Ummi tayi godiya, daf da zata fita daga falon ta tsinkayi
muryar Hajiya na faɗin gobe ta turo mata Neehlah da yarinyar cikin girmamawa Ummi ta amsa mata da
insha ALLAH zata turosu. Har ta fito ta tuna da maganar Aleeyu ta sake komawa ta roƙi alfarmar ya
taimaka ya samar masa wani aikin cikin harkokin kasuwancinsa, ba tare da wata gardama ba ya amince
yace insha ALLAHU zai duba yagani mutumin yanada sauƙin kai godiya Ummi tayi ta fita.
Bayan fitar Ummi ma su Hajiya sun ɗan jima suna tattauna maganar da Alhaji Sulaiman har lokacin
Hajiya bata daina jinjina al'amarin ba tana ƙara faɗa masa irin tsananin kamannin da yarinyar suke
Heedayah mai zuwa wajenta ta yadda ba yadda za'a ga ɗaya ace ba ɗayar bace shi kanshi Alhaji
Sulaiman yayi mamaki sosai.
Sai bayan ta koma sannan sukayi dinner, yau basuyi zaman kallo bama suna gama dinner suka haye
upstairs suka shige bedroom Neehlah ta taya Seeyamah jera kayan da aka siyo a wardrobe su kuma
manyan aka ware su za'a yiwa mai yiwa su Ummi magana yazo ya karɓa a ɗinka mata.
Ummi ma bata daɗe ba ta tashi ta bar falon, lokacin daya shigo ba kowa a falon sai a lokacin ne yazo yin
tashi dinner bai wani ci abincin kirki ba ya tashi ya haura sama yaje ya yiwa Ummi saida safe ya sauko ya
fita ya koma nashi side ɗin.
★★★______★★★
Washegari bayan sun gama breakfast Ummi ta cewa Neehlah suje da Seeyamah su gaida su Hajiya.
Hajiya sakin baki tayi tana ƙarewa Seeyamah kallo har Seeyamahn ta fara tsarguwa da irin kallon da
Hajiya take mata tunanin Hajiya anya ba raina mata hankali akayi ba kuwa ya za'ayi ace wannan ba
Heedayah bace? kai al'amarin nan akwai ban mamaki da ɗaurewar kai duk yadda taso ta gasgata eh da
gasken ba Heedayah bace ta kasa dan haka ta kira number Aunt Ramlah tace ta haɗata da Heedayah a
take Aunt Ramlahn ta miƙawa Heedayah wayar dama suna zaune a falone dukansu lokacin, gaisawa
kawai sukayi Hajiya ta kashe wayar
'Qadeeran Alaa man yasha'u'. Hajiya ta furta cikin zuciyar ta, lallai al'amarin ubangiji da girma yake
wannan yafi ace kama kawai suke da juna komai ɗin ne iri ɗaya.
Sun ɗan jima a gidan sannan sukayi mata sallama suka biya ta sashin Alhaji Sulaiman suka gaishe da
Hajiya Rahma matarshi shi a lokacin ma ya riga ya fita, har suka fito daga part ɗin Hajiya Rahma batasan
ba Heedayah bace duk zatonta itace yau ma tazo gidan.
Tun daga ranar da sukaje siyayya Seeyamah bata ƙara saka habeeb a ido ba ita hakan ma saiyafi mata
daɗi, tana matuƙar jin daɗin zama a gidan koyaushe Ummi cikin janta a jikinta take haka Neehlah sunyi
shaƙuwar ban mamaki cikin ƙanƙanin lokaci suna waya da ƙasashen ta na gidan marayu da kuma wasu
daga cikin shugabannin gidan marayun ana jin lafiyar juna a wayar Neehlah.
Yammacin Lahadi.
Habeeb ne ya fito cikin shirin shi na ƙananun kaya kamar yadda ya saba, baƙin wando da brown ɗin riga
mai dogayen hannu ƙafarshi sanye cikin rufaffen takalmi na zallar fata baƙi hannunshi kuma ɗaure da
agogon fata kalar brown, sai ƙamshi yake bazawa motarshi ya shiga ya fita daga gidan kai tsaye rijiyar
zaki ya nufa gidansu Heedayah bai manta gidan ba duk da cewar wancan zuwan da yayi da dare ne
lokacin da Hajiya ta haɗashi da mara kunyar yarinyar nan ya kawota dayake a farkon layin ne gidan.
Sai