Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣1️⃣
______________
.........Maanal dai ta isa gida lafiya abinta, ALLAH ya sota a wallet ɗinta akwai kuɗi, haka ta cire ta biya shi tai ciki. A ƙasan maƙoshi AA dake bibiyarta ta hanyar GPS tracker ya sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya kife wayar a saman desk ya kwantar da kansa da bayansa jikin kujerar da yake ya lumshe idanunsa.
Maanal na shiga Nuratu da Hajiya Turai na fitowa a mota, da alama zuwansu kenan. Idon Maanal ne ya sauka akan ƙaton akwatin da Bola ke fitarwa a booth. Tayi niyyar wucewarta, sai zuciyarta ta gargaɗeta da hakan kodan Hajiya Turai dake babbar mace. Dan zata iya sa'a da Ammiensu koma ta girmeta. Duk da ta lura da kallon banzar da Nuratu ke mata saita watsar da ita, kaɗan taɗan matsa kusa da su ta gaida Hajiya Turai dake kallonta itama irin kallon ƙasan idon nan na ƙurulla. Bata kuma jira jin a yanda ta amsa mata ba tai gaba abinta. Daga Nuratun har Hajiya Turai binta sukai da kallo, tsakin da Nurry taja yasa Hajiya Turai faɗin, “Ko itace Maanal ɗin?”.
Baki Nurry ta taɓe, a gadarance ta ce, “Waifa Momy itace, shegiya baƙar banza, tana tafiya tana murguɗama mutane ɗuwawu dan asan tana da su ko”.
Hajiya Turai dake bin Maanal ɗin da kallo har yanzu ta ce, “Yoni Baby yarinyar nan ma nada muhimmanci kuwa a gidan nan? Kamar fa daga wajen aiki take a ƙafa alamar taxi ce ta ajiye ta, ace duk motocin gidan Darma ace surukar gidan na hawa taxi kuma matar AA duk dukiyarsa”.
“To Momy dama ba aikin asiri bane yasa ta shigo gidan, tunda ya riga ya gama da ita tun a titi wace soyayya zata gani kuma. Ba dai na shigo gidan ba, sauran asirin ma dan ubansa zan ƙarasa karyashi ne. Ana gama bikinmu zata ware dan sai ta sha ƙi baƙin cikin shagalin da za'a sha kafin na sa ya saketa.”
Sosai Hajiya Turai ta sanya dariya. Tamkar wasu ƙawaye ta bata hannu suka tafa. Daga hakan suma suka nufi sashen Mamy cike da nishaɗi...
Oho Maanal ma bata san sunai ba, tana shiga sashen Oum sama ta wuce abinta. Ta samu Oum da baƙuwa. Maanal ta gaishe da matar ƙyaƙyƙyawa da ita. Itako cike da kulawa take tambayar Oum, “Hajiya Fateema ko ɗiyar tamu ce?”.
Murmushi Oum tayi, ta ce, “Itace Hajiya Shuwa”.
“Kai Masha ALLAH, yarinya dirarriya ƙyaƙyƙyawa haka ga nutsuwa. A ruwan idon autanki bai tafi a banza ba ashe, ashe yasan miya taka, ɗaya yake son tsamowa a cikin dubu, to ALLAH ya sanya albarka a cikin auren nasu”.
Oum dake ta murmushi ta ce, “Amin ya rabbi”. Sai kuma ta kalla Maanal dake nufar hanyar bedroom. “Baby wai har kun tashi ne? Ina Bestyn naki?”.
Cikin danne komai Maanal taima Oum bayanin su an basu damar zuwa suyi shiri ne saboda tafiyar jibi. Oum ta ce, “Tofa tafiyar ta tashi ke kenan?”.
Manaal ta ce, “Eh Oum.” daga haka ta shige ta barsu. Hajiya Shuwa da gaba ɗaya Maanal ɗin ta ƙara birgeta ta ce, “Kai masha ALLAH, jiba yanda ta saki jiki dake kamar ba surukai ba, haka naso mu rayu da Amisha amma ƙawayen banza sukai mata huɗubar tsiya. Shiyasa yanzu nace masa aure zai ƙara, dan na gaji da ɓacin rai wlhy Hajiya Fateema. Wani lokacin idan aka juya min kan yaron nan ko kallo ban isheshi ba, shiyyasa kikaga nai tafiyar nan marocco ko sallama ban miki ba. Shi ma kansa bai san na tafi ba sai bayan kwana uku”.
“Kiyi haƙuri Hajiya Shuwa jarabawa ce, kowa da irin tasa kuma. Amma Amisha ta bama kowa mamaki, dan nidai ina ganinta shiru-shirun nan banyi zaton haka a gareta ba. Ni kaina yanzu saboda tasan yanda muke dake bata shigowa gidan nan, har mukaci bikin nan muka tsare bata leƙo ba, shima Ameer ɗin Fawzan yace baije mana ɗaurin aure ba, shine ma ya haɗasu faɗa shine yake cemasa ai dama Amisha tace ba sonsu muke ba, nice ke zugaki kina wulaƙanta masa mata. Nace ma Fawzan ya barsa baya cikin hayyacinsa ne kawai”.
Kwafa Hajiya Shuwa tayi, ranta na sake mata zafi da halin da ɗan nata yake ɗaya tilo namiji. Su Hajiya Shuwa sune makwaftan su Oum ta hannun damar su, asalinta ƴar marocco ce girman Libya, daga can mijinta Alhaji Mubarak KT ya aurota, yara biyu suka haifa kacal a duniya, Ameer shine babba, bayan haihwarsa ma ta jima bata sake ba harta haƙura ma sai ga ciki. Sunyi farin ciki sosai ita da mijinta, ALLAH ya sauketa lafiya ta haifi mace ƙyaƙyƙyawa itama suka saka mata Ameerah, bayan haihuwar Ameera bata sake ba kuma, yarinyar nada shekara goma a duniya ALLAH yayma Alhaji Mubarak rasuwa sakamakon bugawar zuciya na dare ɗaya daya samu. Shi ɗin babban ɗan gwagwarmaya ne kuma ɗan siyasa ta wani gefen, duk da dai bai saki jiki a siyasar ba gaba ɗaya. Yana kuma kasuwanci sosai. Ya tafi ya barta da yaran su biyu, ita ga cigaba da kulawa da rayuwarsu har girma, duk da dai sanda ma ya rasu Ameer har ya shiga University yana first year ɗinsa. Ameera ce ke primary 4. Tasha wahala da dangin mijinta dan dukiyar ƴaƴanta komawa tai tsole musu ido, acewarsu ai ɗan uwansu ne ya tara, bazai yiwu ya aurota daga wata ƙasa ba daga sama tazo ta mamaye komai, aiko suka ƙulla mata akan ta basu yara su cigaba da riƙewa da dukiyar ita kuma ta koma ƙasar ta. Hankalinta ya tashi, dan babu wanda take tausayi irin Ameera. Nanfa ta shiga faɗi tashin ganin hakan bata kasance ba, tana neman taimakon abokan mijinta, amma mi, kowa sai ya nuna sai in ga amince zata auresa zai yi hakan, wasu ma da iskanci suke zuwa mata. A cikin wannan kai-kawon nata ne suka haɗu da Ambassador Aliyu Darma, ta dalilin nashi abokin shima da ya kasance abokin mijin Hajiya Shuwa. Shima dai yayi mata maganar banza ne, ta fito ranta a ɓace shine sukaci karo da Abah da yaji komai dan yay ƙoƙarin shiga office ɗin ne yaji kalaman abokin nasa sai ya tsaya, amsar da Hajiya Shuwa ta bashi yay matuƙar birgesa, data fito kuma ya ganta mace mai kamala da nutsuwa. Baice mata komai ba a lokacin ta wuce ya shige, bai kuma nunama abokin nashi yasan komai ba shima. Sai da ya dawo gida ya sanarma Oum komai, hankalinta ya tashi baiwar ALLAH harda kukanta. Itace ta ƙarfafa Abah suka shirya taimakon Hajiya Shuwa, washe gari taje har gida ta sameta, zuwa ranar kuma Hajiya Shuwa ta sallama ma dan Oum ta sameta tana haɗa kayanta, tana shirya nasu Ameera domin danƙama dangin uban nasu kamar yanda suka buƙata. “ALLAH sarki na ALLAH baya ƙarewa duk rintsi”____wannan itace kalmar da Hajiya Shuwa ta faɗa bayan Oum ta gama mata bayanin abinda ya kawota, daga haka ta rungume Oum tana kuka...
Wannan shine sanadin tarayyar su, Abah ya tsaya mata akan komai har sai da aka mata tsakani da dangin Alhaji Mubarak, aiko sai akaita gulma ai sonta Abahn keyi, dan har Mamy ma ba sonta take ba ta kuma tsargu da hakan, musamman data roƙa Abah ya sayi filinsu dake a kusa da su dan lokacin su suna a zone 4 ne. Da farko Aban yaƙi, gudun kar ace ta basu ne shiyyasa suka taimaketa, sai da taita roƙonsa da tabbatar musu zamansu a kusa zai zamar mata garkuwane sannan ya amince. Ƙaton filine amma sai da Abah ya ƙara da wani a bayansu shine ya gina wannan babban gidan suka zama makwaftan juna. Anta jira aga Abah ya aure Hajiya Shuwa amma akaji tsit har ma shekaru suka ja. Ameera ita ta ɗan ragema Oum kewar Maanal a lokacin, har ALLAH yasa ta wuce karatu waje ita, yanzu haka tana can, amma tana gab da dawowa ƙasar haihuwarsa. Amisha ƴar ƙanwar Hajiya Shuwa ce, auren zuminci ne ita da Ameer, duk da kuwa su sukaga juna suka gina soyayyar su ba iyayen suka haɗasu ba. Farkon auren kowa nata yabon Amisha musamman data kasance da suffar mutane masu shiru-shiru da haƙuri, sai da tafiya tai tafiya sai komai ya canja, yanzu Amisha aya take gasama Hajiya Shuwa a hannu, har takai wataran idan ta juye kan Ameer ɗin sai ya manta da Hajiya Shuwa na a gidan ma tare da su gaba ɗaya. Sai ta dage da addu'a sai abin ya sassauta. Watanni kusan bakwai kenan abubuwa suka rikice a tsakaninsu shine kawai ta tattara ta wuce marocco sai jiya ne take dawowa, bata nan akai bikin su AA ɗin, sai bayan wucewarsu aiki ta shigo shine suketa hira da Oum ɗin dan ƙawaye ne sosai...
Baƙi da aka kira Hajiya Shuwa a waya cewar tayi ya sata tafiya gida, sai lokacin Maanal ta fito falon, tayi wanka abinta fes sai ƙamshi take. Takardar da aka basu a wajen aiki ta bama Oum ɗin, tare da zama gefenta ta ɗaura kanta a kafaɗarta. Shafa kan nata Oum tayi tana murmushi, cike da kulawa ta ce, “Ko azumin ya fara duka?”.
Shaf Maanal ta manta da ƙaryar azuminta, ta kalla Oum tana dariya. “Lah Oum ƙarya fa nayi dama babu wani azumi ɗazun ban son karyawa ne kawai”.
Idanu Oum ta zaro waje, sai kuma ta dungure kan Maanal ɗin tana dariya itama. “ALLAH ya shirya kin Baby na to da har yanzu bata canja hali ba”. Dariya itama Maanal tayi, tare da ɓoye fiskarta a jikin Oum ɗin. Itama Oum na cigaba da dariyarta ta ce, “To aiko tare zamu shiga kitchen yanzun nan idan munyi sallar zuhur”.
Haka ɗin kuwa akai, bayan Oum ta kammala duba takardun ta riƙe a hannunta akan zata nunama Abah, duk da dama ta masa bayani akan tafiyar amma bai ce mata komai ba. Salla suka je sukayi, koda suka fito kai tsaye kitchen suka nufa, sun fara aikin kenan Mamy da Hajiya Turai da Nurry suka shigo sashen. Oum ce kawai ta fita suka gaisa, basu wani jima ba Hajiya Turai tace bara ta wuce tunda taga Oum ɗin aiki suke itama zataje wani waje ne. Godiya Oum tai mata, sunzo zasu fita Maanal ta fito ta gaishesu. Tana kallon hararrata da Nurry take bata kula ba ta koma kitchen ɗin abunta. Sai da zasu fita Mamy ke faɗin, “Lafiya ƴarki ta dawo aiki da wuri haka yau?”.
“Lafiya Lau, daga office ɗin ne aka basu damar zuwa suyi shirin tafiya ne”.
Sai Mamy ta rasa ina zata kamo zancen tafiya kuma. Amma bata nema ba'asi ba dan tana son su fita su ƙarasa zancensu da suke da Hajiya Turai. Ba kuma tason ma Hajiya Turai ta fahimci bata san da zancen da Oum ɗin keyi ba dan yanzu ta gama cika mata baki akan batun dawowar Maanal a taxi. Ta nuna itace ta kafa sharaɗin sai dai Maanal ta hau taxi amma ba motocin gidan ba, shiyyasa sukaga hakan. (Mamy an iya ƙayya🤣🙏)
Tsulum Nuratu taja ta tsaya tana faɗin, “Momy bye nima zan zauna taya Oum girki, bara naje wajen sis.. Manaal ɗin”. Daga haka ta juya ciki ta nufi kitchen tabar su Oum na murmushi. Duk da dai abinda Nuratun tayi ya bama Mamy takaici, amma sai ta danne... Maanal na cikin aikinta ita da su Inte dake musu ƴan yanke-yanke a work table Nurry ɗin ta shigo. Ko kallon inda take Maanal batai ba, sai su Inte ne ke gaisheta a girmamame, itako tana amsa musu a yamutse. Sun riga sun san halinta shiyyasa basu wani damu ba. Dai-dai nan Oum ta dawo, dan haka Nuratu ta nufi wajen Maanal cike da makirci tana faɗin, “Sis.. Maanal mizan tayaki da shi?”.
Wani shegen murmushi kawai Maanal ta saki tana kallon Nurry ɗin a tsakkiyar ido, a zuciyarta faɗi take, (Yarinya ai indai makirci ne baki yar a ƙasa ba, idan kuma kikace ni dake ta haka zamu buga wasan ƙasa zaki sha kuwa a hannuna). A fili kam maimakon bata amsa fruits da za'a gyara ta nuna mata da hannu fiskarta da murmushin har yanzu. Oum data ƙaraso inda Maanal ɗin take ta ce, “Yauwa gyara su kam Nuratu, sai a gama da wuri dan yau nasan Auta a jigace zai dawo gidan nan ba'a aika abincin rana ba hira da Hajiya Shuwa ta ɗauke min hankali”.........✍️
_Hhhhh gaskiya Maanal baki ƙyauta ba, ya zaki bama Nurry ɗinmu gyaran fruits 🤣🤣_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖2️⃣2️⃣
______________
........Matuƙar tiƙe Nuratu takaici yayi, amma bata da damar cewa bazatai ba tunda itace ta kawo kanta. Sannan duk iskancin nan nata mugun shakkar Oum take ji, sosai matar na mata bala'in kwarjini, ga son da kowa yasan AA na mata tana son tai kamun ƙafa da ita. Kai bama ita ba, ko iyayen nata kan faɗi irin cika musu idon da Oum ɗin keyi, dan duk yanda suka shirya tunkararta da rashin mutunci suna yin arba da ita komai ke ƙwace musu. Cike da son ƙular da Nurry Maanal ta shiga yima Oum hira suna dariya. Aiki sosai Nuratu ta shaƙa, dan ji ta dingayi kamar ta juya ta caka ma Maanal wuƙar hannun nata.
Sunata aikinsu da hira, dan Maanal ma dai ke girkin Oum hira kawai take tayata, Nurry kuma anata aikin gyara fruits da take yi cikin takaici shiyyasa bata wani sauri, koda yake ba aikin ta iya ba dan bayi take ba sam. A gida komai masu aiki ne ke mata shi, idan iskancinta na ka ma hatta underwears ɗinta basu take su wanke sai tace matching baya wankewa da ƙyau. Su Inte dai sun gama sun gyara wajen sun fita suna gyaran falo da saka ƙamshi. Dai-dai nan AA ya shigo da sallama. Da sauri Nurry ta juya har tana neman yankewa da wuƙa, sai Oum da itama ta juya tana masa murmushi. Maanal kam tamkar batana san mike faruwa ba aikinta kawai take yi.
“Lallai yau Auta ne da tashi a office ko five baiyi ba ma?”. Oum ta faɗa tana miƙa masa ruwan data tsiyaya masa a cup. Amsar ruwan yayi, tare da jan kujerar work table ɗaya ya zauna. A kasalance ya janye idanunsa dake akan ƙullin da Maanal tai ta bayanta na rigar girki dake jikinta. Kamar wanda baya so ya ce, “Oum na gaji ne ALLAH shiyyasa na gudo”.
Murmushi kawai Oum ɗin tayi, dan tasan ba hakan bane ba, ta tabbata dan Maanal ta dawo ne. Cike da ɗan rawar murya Nuratu data tsaresa da kallo ta shiga gaisheshi. Ikon ALLAH, to shifa sai yanzu ma yasan akwai wani a kitchen ɗin bayan Oum ɗinsa da Maanal. Waiwayowa yay ya kalleta, sai kuma ya ɗauke idanun a taƙaice ya amsa, cikin kuma halin ko'in kular nan nasa kai kace baima gane Nuratun ba. Oum da bataji daɗin yanda yayma Nuratun ba tace, “Nuratu ce fa baka ganeta ba ne Auta?”.
“Na ganeta mana Oum! Nifa yunwa nake ji”.
Sarai Oum ta fahimci zancen Nuratun yake so a kawar, dan haka ta girgiza kai kawai da juyawa ta kalla Maanal dake ta aikinta. Juyowa tai ta kalla AA kuma, sai taga ya zubama Maanal ɗin ido ne a kaikaice. A take Oum ta fahimci akwai abinda ke faruwa a tsakaninsu, dan da wuri take gane idan sunyi faɗan nasu. Nan ma kanta ta ɗan girgiza, batare da tace komai ba ta buɗe ƙaton freight ɗin kitchen ɗin ta fiddo kwalin fresh milk, a gabansa ta ajiye tana faɗin, “Fara da wannan ga Baby nan na mana girki an kusa kamallawa”.
Idanu ya waro waje, “Kai Oum ana dai mana jagwalgwalo, miyasa baki mana da kanki ba?”.
Dariya Oum tayi, ta nufi hanyar fita tana ƙoƙarin ɗaga wayarta dake ring, ta ce, “Oh jagwalgwalo ko? Babyn ce ke jagwalgwalo! ALLAH yasa ta hanaka abincin nan mu gani”. Ta fice batare data jira mizai ce ba. Shima bai ce komai ba, sai ma ajiye kofin fresh milk ɗin daya ɗauka zai fara sha yay ya miƙe. Nuratu da gaba ɗaya jikinta ke wani irin tsuma, tana jin kamar ta daka tsalle ta rungumesa take ji ta bisa da kallo, duk da tun kwalliyar safe ce a jikinsa yama cire jacket ɗin samna suit ɗin sai fara tas ɗin long sleeve shirt dinsa dake clean harda karin gugarta kamar yanzu ya sakata wani irin ƙyau yay mata, ga ƙamshinsa mai saka kasala na tashi kamar a yanzu ne ya saka turaren.
AA kam ko kallon inda take baiyi ba, hankalinsa kwance, kansa kuma tsaye ya ƙarasa inda Maanal take ya tsaya dab da ita. Ita ko da yake ta juya masa baya bama tasan da zuwansa wajen ba, tadai ji yawaitar ƙamshin turarensa sosai. Hannayensa duka biyu ya zagaya a saman cikinta ya rungumota, tare da ɗora kansa a wuyanta duk a lokaci guda. Harga ALLAH tsorata tayi, dan haka tai wata ƴar zabura tana