AJIYA A DUHU BOOK 1 & 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   181 / 213

540K to 543K   out of 636.6K words

har sati biyu, nan kuma na tada hankalina na samu Malam Yusufa da wasiƙa nace ya bashi. Itama ƙawata na sameta da batun yanda mukai har ina mata kukan cewar zata rabani da shi. Dariya kawai tayi tace ke wlhy Kamila zai dawo, kawai yana latsaki ne, amma ina da dabara ta biyu, dan wlhy in har ba wannan hanyar kikabi ba na tabbatar miki wannan Junaid ɗin ba aurenki zai yi ba, kawai yana lallaɓawa ne ku rabu. Hankalina ya tashi, nanfa na dameta akan ta gaya min ya zanyi. Tace na bata kwana biyu. Kwana biyun na bata, ranar data cika dai-dai da kwanakin takutaha, kun san dai ranar a kano abubuwa akeyi sosai na shagali, da wannan damar muka fita zuwa anguwar su Junaid, kaya rigi-rigi a hannunmu na abinci da kunun zaƙi da kawar tawa ta haɗama saurayinta nima ta ɗiba min wai na kaima Junaid. Na kuma tabbatar yasha kunun zaƙin dan ta saka kwaya a ciki. Nace mata miye amfanin kwayar? Tace itace zata sakashi yin abinda muke so ko baiyi niyya ba. Daga nan an wuce wajen sai yanda kikayi da Junaid wlhy. Zan iya cewa maganarta ta tabbata, dan yau ma mun sami Junaid ne a gida, sai dai maigadinsu mukaima bayanin cewa mu ɗalibansa ne munzo kawo masa abincin takutaha ne. Anan gate ya barmu yaje yay kiranshi, sai ko gashi ya fito. Koda ya gammu sai da ya nuna mamaki ya kuma ɓata rai, amma sai ya dake. Bayan mun gaisheshi ya koma cikin gida yace mu jirashi anan, bai wani jima ba sai gashi ya dawo da mukullin mota. Yace mu shiga, ni na shiga gaba ƙawata a baya. Nayi zaton gida zai kaimu sai naga ya kawomu wata anguwa ne mai sabbin gine-gine. Ya samu waje yay parking sai ga wani da zai iya kaiwa sa'anshi ya fito, yace mana abokinsa ne. Bayan mun gaisa abokin nashi ya shiga damu cikin gidan, gidan sabo ne yace mana na yayansa ne da zai yi aure nan da sati guda.”
        “Abokin nan nasa ne ya min nasiha ya kuma gaya min gaskiya akan gidansu Junaid bazasu barshi yay aure ba yanzu. Amma idan zanyi hakuri nayi karatu kamar yanda ya faɗa min tun farko nan gaba sai aje matakin auren. Yace min na daina damun kaina komai nada lokaci, sannan na daina zuwa gidansu inba hakaba yayunsa ko babansu wani ya ganni za'a bata masa rai ne sosai.. sosai raina yake a dagule, na dinga kuka suna lallashina, da kyar na nuna na amince da abinda suka faɗan. Dan haka ƙawata da abokin nasa suka fita suka bamu waje wai zai sake lallashina. A wannan barin namu ne na bashi abincin dana kawo masa, dan zuciyata ta gama aminta da batun ƙawata dole fa sai nayi hakan ne zan samu Junaid. Idan ba haka ba ina ji ina gani ɗan masu kuɗi zai suɓuce min. Da farko yaƙi cin abincin, sai da na nuna fushina sannan ya yarda mukaci tare. Daga kuma shan wannan kunun zaƙi ne komai ya faru.....” kuka ya sarƙeta. Zuciyoyin su Babban yaya kuwa wani irin rarrabewa suke gida bibbiyu, babu abinda suke sai ambaton addu'a. Yaya Fawzan daya kasa jurewa ya ce, “Abah bama buƙatar wannan labarin a barshi...”........✍️
      

Gaisuwa da fatan alkairi gareku baki ɗaya 😘😘😘😘

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣1️⃣


______________


........“Baku isa ba, sai an kaishi har ƙarshe. Dan haka oya Kamila muje”.
   Sille ya faɗa yana nuna Mamy da bindiga. Hawaye ta share tare da zufar dake cigaba da jiƙe mata jiki ta cigaba da faɗin, “Junaid yamin fyaɗe.....”
“Kodai kin min fyaɗe dan uwarki! Shegiya mubafuka, idan baki gyara maganarki ba kin faɗi gaskiya wlhy zan harbeki ne nima. Iya ƙoƙarina nayi na son kaucewa ban taɓaki ba amma da yake ke shaiɗaniya ce sai da kika samun abu nasha na aikata hakan”. Mabera ya faɗa a fusace.
        Mamy ta cigaba da faɗin, “Shike nan naji ni na saka maka ka aikata. Maimakon ni nayi kuka akan abinda ya faru duk da wahalar dana sha shine ke kuka sosai da zagina, ya tsareni sai na faɗa masa abinda na zuba a abincin nan. Da farko naƙi, sai da naga yana neman kasheni na sanar masa komai. Nasha maruka a hannunsa, na kuma sha zagi, ya kuma tabbatar min har abada mun rabu kenan. Sai lokacin na fara kuka da roƙonsa. Da ƙyar na samu yace ya haƙura. Koda abokinsa da ƙawata suka dawo sukaga halin da muke ciki bai ɓoyema abokin nashi komai ba. Shima abokin nashi ya girgiza, ya kumayi mamaki sosai musamman da yake kallona ƴar ƙarama babu jikin kirki. Bayan dai ka-ce-na-ce abokin nasa da kanshi ya fita ya samo min magunguna nasha, ƙawata ta taimaka min na gyara jikina a gidan tanata nuna min karna wani damu nasara tamu ce. Wannan abinda ya farun shine tushen komai, kuma shine mafari. Dan bayan jiyyar kwanaki dana sha batare da barin kakata ta fahimci komai ba saboda magani da nake sha da taimakon da ƙawata ke bani cikin dabaru na warke sarai, abinda kuma ya sake bani mamaki Junaid ya koma zuwa gidanmu, tun Baba na ɗaure masa harya saki jiki ya haƙura. Abinda na lura da shi Junaid na kaffa-kaffa da nine kada na faɗama su baba abinda ya faru tsakanina da shi, aiko saina samu na firgitashi, haka yake ɗaukata muje super market ya kaso min kuɗi ni da su Baba. Kawai bayan wata biyu dayin hakan sai yazo min da buƙatar irin wancan al'amarin daya faru, ban masa musu ba na bashi kaina. Nasha wahala a karo na biyun ma amma na daure sosai. Shi ko yayta lallaɓani da min alƙawari kala-kala. Wannan shine ya sake fasan kai na ƙara ji na gama damƙe Junaid a hannu. Sai dai me na daina ganin period ɗina tun daga yi na biyun nan. Na kasa samun koda ƙawata da batun, sai dai na tambayeta mike saka jinin mutum ya daina zuwa duk wata. Sai tace ciki ne. Nice bana gani? Da sauri nace mata a'a wlhy, naji makwafciyarmu ne na hirar jiya ni kuma sai abin ya ban mamaki shiyyasa na tambaya. Da alama ta yarda, dan bata sake min maganar ba nima ban sake mata ba. Sai dai hankalina a tashe yake dan hakan dai na fahimci ana nufin cikine da ni. Ga kakata ta fara ƙannanun magana akan tunda na kusa gama makaranta ya kamata na fitar da miji haka nan. Babana ma ya hau ya zauna akan batun. Tsoron sake yima Junaid magana nake yi akan aure tunda ya gaya min gaskiyarsa, amma yanda suka matsa min dole nai yunƙurin yin hakan. A mamakina wannan karon baiko musa min ba yace ya yarda zamuyi aure, amma akwai wani aiki da zai sakani na watannin da basu wuce biyar ba kacal. Dan haka zai samu Baba da batun cewa zai aureni amma mahaifinsa baya nan a bashi lokaci har ya dawo. Ko damuwar jin wane aikine zan masa banyi ba na amince. Haka kuwa ya samu Baba ya tsarashi, mukai sa'a kuwa ya amince. Wannan ne ya bani damar yin jarabawar ssce ɗina batare da matsawarsu akan batun aure ba. Ga ciki maƙale a jikina na rasa wazan tunkara da batunsa tsakanin ƙawata da Junaid, balle zuwa wajen likita nama tabbatar shi ɗin ne ko kuwa. Kwatsam a ranar da mukai final exam ɗinmu na dawo gida da murnar kammala Secondary na tarar da anguwarmu a cike taf da mutane anata hayaniya. Da ƙyar na kukkutsa na shiga ainahin inda hayaniyar take sai na samu ƙawata shimfiɗe a ƙasa ga ƴan sanda da babanta da mamanta zaune gabanta sunata kuka. Hankalina yayi masifar tashi na tambayi wani ɗan anguwarmu dake kusa da ni sai yace min iyayentane suka gane tana da cikin shege shine suka kamata da duka akan sai ta faɗi wanene yay mata, da ƙyar aka ƙwaceta a hannunsu sai ma akaga ta rasu. Tashin hankali kenan wanda ba'a saka maka rana. Ban san sanda na nufi gida ba saboda gudawa dake neman zubomin. Wannan al'amari yayi matuƙar tayar min da hankali, dan har aka tafi da iyayen ƙawata ita kuma aka binneta da fin sati biyu ban dawo dai-dai ba. Sai dai faruwar hakan ta sakani sake yin gum da bakina akan abinda nake tunani a kaina nima game da ciki, sai dai na tasa rayuwar Junaid gaba akan batun aure. Dan a shirmena lokacin cikin zai cigaba da ɓuya har muyi aure kafin na haifeshi. Saboda wani magani dana amsa a hannun masu tallar magani, masu faɗin sunci dubu sai ceto ɗin nan. Haka na saka maganin nan gaba naita sha a ɓoye wai ciki zai kwanta har nayi aure, dan a lokacin ni sam ban kawo wani batun zubar da shi ba, dan zubar da ciki ba abu ne mai sauƙi ba sai da kuɗi sosai kuma bamma san ina zamuje nayi hakan ba tunda bayan ƙawata data rasu ba wani ya taɓa sanin halin da nake ciki ba, dama itace ke nuna min hanya yanzu kuma babu ita. Iyayenta ma ance an kaisu prison. Matsawar da naima Junaid yasa jarabawarmu na fitowa ban san yaya akai ba ya shiga ya fita wajen babansa aka nema min jami'a, bayan iyayensa sun kawo kuɗin aure na. (Ashe ba iyayensa bane hayarsu yayi) Sai dai a lokacin mu duk bamu sani ba, shi kuma baba ganin har iyayensa sunzo gida babu gardama ya yarda zan fara makaranta.”
      “Ana gobe zan fara zuwa makaranta Junaid yazo gidanmu ya ɗaukeni wai zai min siyayya, a wannan fita ce ya sanar min ainahin aikin dazan masa. Ya nuna min hoton Fateema. Yace Kamila wannan sunanta Fateema Abubakar Ishaq Darma. Kamar yanda zaki shiga makaranta gobe itama gobe zata fara zuwa. Ƙanwar abokina ce. Ina son ki shiga jikinta ku zama ƙawaye aminai na gaske. Cike da mamaki nace masa duk akan mi zan yi hakan, daga ganinta ƴar masu kuɗice irinka Junaid, kodai budurwarka ce?. Tsaki yayi da faɗin kefa shashashace wani lokacin, yanzu nake gaya miki kanwar abokina ce. Ainahin aikin kuma ba'a kanta bane akan abokin nawa ne, sannan banda wata alaƙar soyayya da ita wlhy. Kin dai ji na rantse miki. Kawai ina son mu takata ne a matsayin tsani samun kuɗaɗen aurenmu, dan babana ya rantse tunda aure nake so bazai min komai ba na auren sai dai nayi da kaina, yasan bani da inda zan samu kudin nayi shiyyasa yace hakan. Kinga dole na haƙura, ni kuma a wannan gaɓar wlhy bazan iya haƙura ba sai na aureki, dan kin ɗanɗana min zumar da ban san haka take ba. Sannan ina son aurenmu ya zama aure na musamman da kowa zai san kin auri wanda ya isa. Ki nunama ƙawayenki kin wuce da su na har abada. Tabbas maganganun Junaid sunyi tasiri matuƙa a zuciyata, saboda bani da burin daya wuce ace muma gidanmu munyi kuɗi, mamana da ƴan uwana da suka gudu suka barni saboda talauci suzo su samu na wucesu fintinkau, dan haka ko musu banyi ba na amince masa. Matuƙar farin ciki ya nuna min da amincewata da kalamai masu daɗi na soyayya da suka sake zurmani a ramin. Washe gari na fara shiga makaranta, kuma Junaid ya kaini, sai dai bamu haɗu da Fateema ba. Da aka tashi na koma gida, da daddare da Junaid yazo hira na faɗa masa sai yace kada na damu wai batajin daɗi ne shiyyasa amma gobe zatazo. Washe gari ma nata jiran shigowarta amma shiru har malami ya shigar mana aji, harna fidda rai da zuwanta kawai sai gata. Cikin sauri na ɗan fiddo hoton da Junaid ya bani dake cikin jakata na kalla. Ita ce kuwa, dan har ma tafi ƙyau a zahiri fiye da hoton. Kawai sai zuciyata ta shiga raya min anya ba yaudarata Junaid keyi ba sonta yake yi. Taya za'ace wannan ƙyaƙyawar budurwar da wani manufa ta kuɗi kawai zai ce na raɓe ta. To amma ya rantse min ai, da kuma son nata yake tunda yace yayanta abokinsa ne danmi zai zo ta wajena. Ina wannan tunanin har ta ƙaraso inda nake ban sani ba, sai da ta taɓani na dawo firgigit, tai min murmushi na mayar mata, ta buƙaci zama kusa da ni da gudu na matsa mata kuwa ta zauna zuciyata fes komai yazo min da sauƙi. Wannan shine mafarin alaƙata da Fateema. Junaid na cigaba da tsara min mataki-matakin zama da ita har naci galaba a kanta..........✍️




*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_💞AJIYA A DUHU....💞_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣2️⃣


______________


........Hankalina rabe yake biyu, akan batun Fateema da cikin jikina da har yake motsi, duk da kullum cikin tamkesa nake a cikin zani dan kar kowa ya sani, Alhamdullah kuma babu wanda ya gane ɗin har kakata da babana da muke kwana muna tashi a gida ɗaya, dan bana laulayi sam, sai zazzaɓin dare, da gari ya waye kuma shike nan. Sai dai a wani weekend ina tsakar gida ina wankin kayanmu dana Iyalle mukai wata baƙuwa daga kauyen mu. Duk motsina idon matar nan a kaina, harna fara tsarguwa itama ta kasa daurewa sai da ta furta Amma yarinyar nan cikar budurci ya miki ƙyau kamar mai ciki. ALLAH sai da naji zuciyata ta kusa faɗowa ƙasa saboda tsorata, sai ALLAH ya taimakeni Kakata ta amshe zancen, karaf tace Haba Safare wane irin magana ne wannan da mugun baki, cikin lafiya yarinyar da ake shirin aurarwa. Ki dai tsaya a kyawun cikar budurcin kin san yaran yanzu abincin da suke ci mai ƙyau ke sakasu ƙyawun jiki, balle ita yaron nan Junaidu na ƙoƙari matuƙa akanta damu kammu. Safare da taga ran kakata ya ɓaci sai ta shiga bata haƙuri, ta kuma ja bakinta tai shiru. Washe gari ma tabar garin dan na tasata gaba da harara da jan tsaki da mata ALLAH ya isa akan tamin fatan cikin shege, rashin samun sake tace washe gari zata wuce. Aiko sai na sake ɗaura ɗamarar cigaba da tamke cikina da zani duk da ina shan wahala, kullum ina cikin hijjabi, dan ma ALLAH ya soni cikin bamai girma bane kodan na fari ne oho. Safare tana wucewa baifi da kwana uku ba ciwo ya kwantar da kakata, a kuma tsakanin muka kammala jarabawar zango na farko a makaranta muka samu hutu. Shine ban koma ba har aka koma da kusan wata biyu Fateema tazo bikona. Bikon daya canja komai daga ƙaddarata da Junaid a dalilin ganin Aliyu Darma. Ganin Aliyu ya sani yima labarina kwaskwarima na nunama Fateema iyayena ke biya min kuɗin makaranta da ƙyar, dan haka tace karna damu na saurareta. Bayan wucewar su Fateema da daddare ina cikin damuwar zuciya akan Aliyu sai ga Junaid da abokinsa, mun gaisa munyi hira Junaid yace ya kamata nazo na koma makaranta tunda Fateema tazo har gidanmu, abin farin cikin ma harda Aliyu, dan haka nasarar aikinmu ta fara zuwa kenan. To kawai nace masa dan harga ALLAH a ranar ko ganin fuskarsa bana son yi ma...”
     A zafafe Mabera ya katseta da faɗin, “Muguwa saboda kinga mai kuɗi ba. Cigaba sai akai yaya?”.
       Mamy da azaba ta gama isarta har kanta ya fara mata nauyi saboda jinin da take zubarwa a inda Sille ya harbeta ta cigaba da faɗin. “Baifi kwana huɗu da zuwan su Fateema ba suka dawo da tarin aikairi a garemu, sun biya min kuɗin makaranta, sun kuma bama Baba jarin sana'a. Aka kuma kai iyalle asibiti. Saboda zan koma makaranta wata ƴar uwarmu tazo daga ƙauye ta zauna da Iyalle a asibitin. Kwana biyu da kwantar da su na fara wani irin ciwo dana gagara gane kansa, ashe wai hakane naƙuda. Na rasa yanda zan yi abu ya isheni ban san wazan tunkara da batun ba, kawai cikin ikon ALLAH naje na kaima su iyalle abinci asibiti na dare sai na samu mai jiyyarta da suke kira Inne na bata labarin abinda surukarta tai musu. Wai tana naƙuda taƙi gayama kowa sai da ta haihu a ɗaki ta yanke cibi sannan ta kirasu. Caraf nace kuma Inne dama haka na faruwa?. Daƙuwa Iyalle tai min, wai mizaisa na saka baki a zancen manya. Sai Inne tace A'a barta iyalle, ita da za'ayima aure ai dan ta san waɗan nan ba komai bane. Ballantana kunce mijin nata ɗan gidan masu kuɗi ne, kinga bamu san yanayin iyayensa ba da halinsu. Ita wannan ba tattalinta muke ba amma tai shiru da bakinta dan karta haihu a gabammu kinsan yaran yanzu abinda basa so kenan wai haihuwa a gaban surukai. Dole Iyalle tai shiru Inne ta fara bani labari dalla-dalla, niko inda ban gane ba nai mata tambaya musamman yanke cibiya. Tsaff ta bani labarin komai. A dalilin wannan hira ne na fahimci kenan naƙura nake yi. Tab lallai banga ta zama ba, dole ne na nemi mafitar data dace kodan samun damar mallar Aliyu Darma. Haka na dawo gida a daddafe

181 / 213

Chapters