Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
alkairai. Dan kuwa da mijin Maanal da zuri'arsa basu tsaya akan al'amurin ba ai da wani batun akeyi ba wannan ba. Lauyan dasu AA suka saka akan case ɗin ne yay musu bayanin komai akan wanda ya sashi taimaka musu. Sai suka ji sun zaƙu da ganin Maanal da Asiya da sauran ƴan uwanta su Shahidah da ma mijin Maanal ɗin kansa. Amma lawyer ɗin yace suyi haƙuri yanzu suna cikin wani halin jiyyar surukin Maanal ɗin ne amma idan komai ya lafa yasan zasu zo har garin Giro. Da wannan ya kwantar musu da hankali...........✍️182
........A can Abuja an kama su Sanata Bukar anan Kaduna Kawu Manu ne da kansa yazo ya wuce da Hajiya Basariyya. Tana kuka tana roƙon Yayanta ya taimaketa yace shi kam miye nashi. Ai tafi ƙarfinsa sai dai Kawu Manu ɗin kam. Dama kayanta tun jiya sun isa ƙauyen. Dan haka yau ziryan ɗinta ta sauka. Suna shigowa taci karo da kayanta kaf a tsakar gida. Iya nata aikinta ko kallonta batai ba sai mijinta da taima sannu ta kuma kawo masa ruwa. A ɗakin data zauna wancan karon wannan karon ma akace ta zauna. Garama wancan karan tasan tana da yaƙinin komawa tunda ba saki bane. Amma yanzu fa, sunan zamanta zawarci ne kotaƙi kota yarda. Gashi babu komai dan account ɗinta Naira ɗari tara ne kacal suma sunƙi fita ne. Kaddarori kaf Mabera ya tattare, har yanzu kuma bataji ance gasu an samu ba. Yanzu ma Daddy ya mata saki ukun nan ta ina zata san an dawo da su. Dan ƴaƴanta ma ya tabbatar mata idan ta sake dawo masa gida duk abinda yay mata ita taja. A jiya taje gidan Daddy maƙwaftansu suka sanar mata ai sun tashi, gidan ma da alama sai dashi za'ayi. Sun koma Abuja da zama. Abuja fa, Abujar data daɗe tana ƙulafuci da nacin komawa tun ludayinta nakan dawo. Dan tama zauna na kusan shekara biyu auro Ammie ya saka Daddy maidota Kaduna. Shiyyasa ta tsani Ammie sosai. Take ganin kuma ta sanadinta ta rasa waccan damar. Sai gashi yanzu an koma kuma zama na dindindin babu ita. Wannan abu ta tayar mata da hankali matuƙa. Ta kuma ci kuka sosai a daren jiya saboda hakan. Ta tashi da shirin kota kwana na binsu Abujan taba Daddyn haƙurin dai kuma sai ga Kawu Manu yazo ya tattarota yau. Tattarowar da take nuna mata ta dawo zama a ƙauyen kenan sai abinda hali yayi.
Miyasa rayuwa zatai mata haka? Miyasa duniya bata tashi yaddata a goyon gatan datai mata ba sai yanzu a gaɓar da tafi buƙatar wannan daɗin fiye da shekarun baya saboda koba komai yanzu girma yazo mata. Ga abinda ta ruguza rayuwarta domin shi yana nan dai tare da ɗiyar tata bai fita ba. A gabanta kuma Sageer ya ɗauki ƴarta da tafi so ya wuce da ita. Kofa kallonta Huznah batayi ba, yanda ta nuna ma san bata son ganin nata. Su Madeena kam tunda tabar gidan ko'a waya basu taɓa kiranta ba balle su taka ma inda take, hakan na nufin suma basu damu da ita ba, ko tace basa son ganinta a yanzu sam, matan uba sun fita a wajensu tunda gashi sun bisu Abuja batare da ko gaya mata sunyi ba. Wasu hawaye masu zafi suka sake wanke mata fuska kamar an buɗe fanfo. Sai da tayi mai isarta har kanta na fara mata ciwo sannan ta haƙura tai shiru.....
________★
Kamar yanda yaron Sanata Bukar ya faɗa an samu nasarar ceto su Babu a hannunsu. Hakan kuma ta farune sanadiyyar cin uban Rabilu da jami'ai sukayi. Tsaff ya kwashe komai yanda yake ya sanar musu. Tun daga kan neman auren Maanal har zuwa aurenta fa AA Darma da abinda ya faru kwanan nan. Shine ya faɗi inda aka kai su Gwaggo dan haka akaima yaran na su Sen.. Bukar dirar bazata. Sun fara samun Babu ne a yashe ƙasan bishiyya kudaje nata binsa kamar wani gawa. Dan jikinsa duk fitsari ne yau ko abinci bai iya yaci ba. Suko su Gwaggo ai halin da suke ciki ma ba'a magana. Ba ƙaramin yagalgalasu yaran Mabera sukayi ba ta hanyar fyaɗe. Sailu kanta dake da sauran ƙwari ta jigata balle Gwaggo da ƙashi da jijiya kawai suka rage. Su suka biyun a sume ma suke sai da aka saka musu ruwa suka farfaɗo. Dole AA da hankalinsa yay mummunan tashi da lamarin yay kiran RK aka turo musu Ambulance har biyu.
Haka aka kwashi su Gwaggo a ɗaya Babu a ɗaya, ALLAH sarki AA sai yaji kamar yayma Babu kuka. Musamman idan ya tuna rayuwar baya, bawan ALLAHn nan ƙyaƙyƙyawan mutum ɗan gayu. Amma jibeshi yanzu duk ya yagule ya ƙone a tsaye kamar bai taɓa shiga ajin makaranta ba. Shi yama rasa wane tunani zai yi, ina aikin ƴan sandan nashi? Ajiyewa yay ko ƙofarsa akayi? Dan ya tabbatar da Babu na'akan aiki yanzu da ya taka babban matsayi, tunda ga kusan mate ɗin aikinsa nan a yanzu duk kusan sune cp na jihohi..
Kai tsaye KK HOSPITAL aka wuce da su. Babu wasa ko ɓata lokaci aka amshesu. Wani sabon aikin ya sake samun su RK. Haka suka suƙufa kansu dan yanda Babu ke buƙatar taimako suma su Gwaggon haka ne. Ta wani fannin ma sun fishi jigata da kasancewa a haɗari. Dan hatta Doctor ɗin dake duba su Gwaggo kuka ta sanya tana tsinema waɗanda sukai musu wannan aika-aikar haka. Musamman ma Gwaggo dake fama da tsufarta....
Wannan fa shine ake kira da ainahin SHARRI ƊAN AIKE NE, DUK INDA KA AIKASHI ZAI JE YA DAWO YA TABBATAR MAKA YA ISAR DA SAƘONKA.🥳🥳
_________★
Anan Hajiya Basariyya na kuka anan Abuja su Maanal ne keta farin ciki. Dan kuwa Najma da Ameerah duk suna tare da ita can gidan taya su Ammie shirin ƴan abubuwan da suka kwaso a Kaduna. Koda yake Manaal ma iya ba aikin take ba, sai ciye-ciye tasa a gaba da surutu dan yanzu kam bakinta dawowa yake ta rage miskilancin nata na tsiya daya hauta a dalilin rashin AA. Ga Aunty Sakeena, ga Shahidah, ga Amaal sai hiran ke tafiya musu yanda ya kamata. Can kuma su Amrah suka shigo harda su Salima da yaran Hajiya Basariyya. Zo kaji yanda falon Ammie ya kacame da cah-cah ɗinsu na surutu. Sai da lokacin salla yayi su Amrah suka koma sashensu, su kuma suna bedroom ɗin kusa dana Ammie wai nasu idan sunzo Maanal da Najma da Amaal da suka fara yin tasu sallar na kan gado, sai Didi da Aunty Sakina da Ameerah nayi.
Amaal ta fiddo wani tsumi a handbag ɗinta tana miƙa ma Najma da Maanal gora ɗai-ɗai. Amasa sukayi, Maanal dake jujjuya goran tace, “Didi zuma ne?”.
“Na mata ba”.
“Ita zumar akwai ta mata akwai ta maza?”.
Harararta Amaal tayi da faɗin, “Ke wai miyasa kullum kanki a tukunya yake ne Auta. Sai anyi magana ji ishi mutane da Besty! Besty! Amma ba ai masa gatan daya dace ”.
Dariya Najma ta sanya, hakama Ameerah da Shahidah dake addu'a. Aunty Sakina ta ce, “Gaskiya Amaal babbar banza ce”.
“Naji ba komai Aunty, dama suka samu ina ɗorasu a hanya. Yayyena nake son aima gyara. Su bar ganin su amare ne musamman Ameerah da Najma dake da kishiyoyi idan ban saita su ba ai sai a bar mana su a bakin ƙofa ko”.
“Uhm yayyan ƙarshen zamani kenan, kidai tabbatar da abinda kika basu ko akwai mai ƙaramin ciki, garama Maanal ya fara tasawa”.
“Kai Didi”.
Maanal ta faɗa tana ɓoye fuska. Dariya suka sanya. Shahidah datai maganar tace, “Wane kai Didi daga faɗar gaskiya. Suma su Ameerah ai duk ƴar manuniya ta nuna su”.
A tare Najma da Ameerah suka waro ido waje suna kallon juna. Maanal ta sanya dariyar mugunta da faɗin, “Didi da gaske dan ALLAH?”.
“Hasashene Auta, amma gaskiya kuyi gwaji kam, dan alamunku duk sun nuna hakan”.
Sosai sukai wuƙi-wuƙi da idanu, Aunty Sakeena tace, “Ai tunda kukaji Shahidah ta faɗa to da wuya ku tsallake, kun santa kamar mayya take wajen iya hango ciki tun yana mitsitsi.”
Amaal ta ce, “Wlhy fa, ko wannan cikin itace ta fara gano min shi. Amma zumar nan bata da wata matsala dan nima ina sha, kuma musamman nasa ta haɗa min takun nan dan tace mai kishiya basa sha nace wlhy sai kunsha. Ƴar Sudan ce tasan sirrin kaya. Idan har kuka sha zumar nan sai kun dawo da ƙafafunku yara”.
Fuska suka shiga rufewa, su a dole kunya. Amaal tace, “Munafukai nan za'azo ana tambayarmu miye kaza miye kaza”.
Haka ta tasasu gaba Shahidah da Aunty Sakeena na kare musu. Har la'asar suna ɗakin nan sai da sukai salla, sun sake dasa sabuwar hira Ammie ta korosu su ƙarasa amata abinda ya rage. Haka suka haɗu suka kammala komai daya dace, suka saka turare ko'ina ya ɗauki ƙamshi da ƙyalli.
Suna idar da sallar magrib sukai shirin tafiya, da zasu zo Ameerah ce ta kawosu, yanzu kuma sai Najma ta amsa, dama da motar Babban Yaya suka fito. Har sun kama hanyar gida Maanal tace dan ALLAH suje su sayi ice-cream da fura. Najma ta gangara gefen titi tana faɗin, “Da iznin wa? In har zamun to mu rufawa kammu a siri mu kira mu tambaya. Dan wlhy tsoro name ji, jiya Nibras ta fita bada sanin Yaya ba kamar zai mareta, ke inaga ma ya maretan dan nidai ganin yanda idonsa ya rufe yana masifa ALLAH guduwa nayi ɗaki”.
Dariya suka sanya mata, ta ce, “Oh dariya ma na baku, bazaku gane ba ALLAH kuwa. Kudai kira nima bara na kira”.
Da sauri Maanal ta ce, “Kodai mu kira Oum, kar muzo mu kirasu wani ya amince wani yaƙi amincewa”.
Ameerah tace, “Shawara mai ƙyau, amma idan itama Oum ɗin taƙi amincewa kuma fa”.
Sai sukai shiru kowa na nazari. Ƙarshe dai Najma tace mudai kirasu, idan Oum ta amince sunyi faɗa ta karemu wlhy sai mun bar inda take musha faɗa.” gamsuwa da hakan yasa duk suka kirasu. Sai me kamar haɗin baki kowanne yace bai yarda ba su dawo gida. Idan son ice-cream ɗin suke za'a bada a sayo musu. Dukansu haushi sukaje, Haka Najma taja motar suka wuce gida suna mita. Koda suka shigo gida a compound suka samesu an baza carpets duk sunata hira harda su Uncle RK, su Uncle Najeeb su Modibbo. Sai wasu a kujeru. Sun gaishesu, amma su a dole fishi suke, kowacce ya haɗa ido da miji sai ta zumɓuri baki. Baki suma sukaita taɓe musu, shi AA ma da yafi kowa neman magana harda yima Maanal ƙaramin gwalo. Aiko ta hau tayi fam. Fuuuu ta wuce sashen Oum. Suma su Ameerah sai suka bita.
Kawai sai Yaya Fawzan ya sanya dariya. Waɗanda suka lura da abinda ke faruwa suma suka shiga tayashi............✍️183
..........A Lagos Ra'iz bai tsira ba, sai dai rashin tsirar tashi ba'a kamashi bane ba. Da farko dai Jami'an tsaro sun isa anguwar da yake domin kama shin, an kuma zagaye gidan da yake zaune da sauran yaran su Mabera dake masa hidima suke kuma kai-kawo akan miyagun kwayoyin da yake sayarwa. Gidan hawa uku ne, su Ra'iz ɗinne kuma a hawan ƙarshe. Sanin sun riga sunzo hannu Ra'iz yayi ƙoƙarin bi ta wata hanyarsu ta sirri da take a sauran gidajen dake ƙasan nasu guda biyu. Sai aka samu matsala cikin mutanen anguwa wani yay masa shune. Jami'an tsaron sun buƙaci ya miƙa wuya kawai amma yaƙi, daga ƙarshe ma kawai suka fara jin ruwan harbi a kansu. A take jami'in su ɗaya ya rasa ranshi, biyu suka ji rauni. Hakan ya fusata su masuƙa, kawai suka buɗema Ra'iz ɗin wuta. Sai gangar jikinsa data gama huhhujewa da bullet ce ta zubo ƙasa, jininsa ya shiga fallatsa a jikin mutane.
Wannan al'amari ya tayarma mutanen anguwar hankali matuƙa, duk da dama zaman su Ra'iz ɗin ya gallabesu dama. Suna lalata musu yara ƙanana ta hanyar fyaɗe da koya musu shaye-shaye. Tun anayi iya yara mata har yakai mazan ma lalata musu ake ta hanyar fyaɗe. Tsoro kuma ya hana su tunkaresu, sai dai kawai mutum idan yana da hali ya tarkata yabar anguwar yafi masa kwanciyar hankali. Dan in tsageranci da taurin kai yasa kai magana sai sun kasheka kuwa.
Abinda ya faru ya fara yawo a media da kafafen yaɗa labarai. Ya kuma isa har kunnen Mabera da Sille. Inda Sille dake fama da makantaccen ido ya birkice musu, dan a duniya bayan Baa babu wanda Sille ke so da ƙauna kamar Ra'iz. Ƙauna yake masa irin ta fansar da rayuwa akansa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya hargitsa ɗakin da aka ajiyesu. Yana wani irin ihu da gunjin kuka da tabbatar da wlhy bazai yarda ba, sai ya ɗauki fansar ƙaninsa. Kuma sai ya wulaƙanta rayuwar Bakori.
Al'amarin kamar wasa yana neman zama babba. Dan kuwa securitys ɗin da aka bari suna gadinsa abin yafi ƙarfinsu. Dole aka turo wasu Jami'an, ga Mabera tunda idonsa ya sauka akan gawar Ra'iz ya yanke jiki ya faɗi wani irin tari ya sarƙeshi. Sai ga aman jini ta baki ta hanci. Ana son a taimaki rayuwarsa haukan Sille ya hana kowa iya shiga ɗakin. Daga ƙarshe dai sai da takai an harbi Sille a ƙafa ya faɗi sannan aka samu nasarar shiga aka ɗaga Mabera da yay kaca-kaca a cikin jini. Shima Sillen sai a lokacin ya fahimci wane hali Baa ɗin nasa ke ciki. Aiko ya ƙara kware murya yana kwarara musu ihu na haƙiƙa. Ga azabar harbi gata mutuwar Ra'iz gana halin da Baa ke ciki.
Fin awanni biyar ana kai-kawo akan Mabera. Kafin likitoci su tabbatar da akwai guba a jikinsa, ta riga kuma ta masa babbar illa da karya dukkan wata garkuwa ta jikinsa. Da yake abu ne na haɗin baki da sanin likitocin komai dake faruwa sai sukace gubar ta jima wai a jikinsa kusan tsahon sati biyu ma.
Zancen dai yasa anata cece kuce. Ga Sille ya koma kamar mai ciwon hauka. Dan sai surutai yake da zabure-zabure. A daren dole aka raba musu ɗaki da Baa ɗin nashi. Tun kowa na kallon al'amarin a matsayin tashin hankali ne da raɗaɗin mutuwar ɗan uwansa har dai zuwa washe gari tabbacin akwai ciwon hauka a tare da shi ya bayyana. Dole aka canja masa asibiti zuwa na mahaukata.
Yanayin da Sille ya shiga ya sake tabbatarwa al'umma dole ne fa akwai dai wani abu a ƙasa. Sai dai idan wani abin akai musu. Lallai wannan hasashe ya kawo cece kuce da kace nace tako ina. A cikin talakawan dama manyan ƴan siyasar ƙasar da masu damar faɗa aji. Tako ina fashin baƙi ke tashi, da wanda suka fahimci al'amarin da wanda basu fahimta ba ma. Da masu ikon faɗa ajin, da mu talakawa ƴan bani na iya. Wai akance duk baƙin hali da mugun halin mutum zaka samu yanada masoya. Kodai masu irin halayyar tasa ko kuma ma'abota tauye gaskiya saboda son zuciya. Sai ko ga Mabera da ƴaƴansa sun samu masoya yan faɗin ai musu adalci. Suna kuma tada jijiyiyin wuya da maida yanda akayi dama wanda ya dace ayi. Acewarsu bai kamata aima su Maberan hakan ba. Sai dai idan bayan su Sanata Bukar akwai wasu manyan dake tare da Mabera ɗin suke gudun asirinsu ya toni shiyyasa sukai hakan.
To a taƙaice dai kam hakanne, dan nasu Sanata Bukar ya fito ne kawai a bayyane. Amma akwai wanda suka fisu zama ƙuraye a bayan fage kuma manya-manyan shegun ƙasar da suka gina Maberan suke kuma amfani da shi matsayin makami. Shi kuma jiƙashi da suke da kuɗaɗe da tsatsar data zagaye zuciyarsa yasa shi basu haɗin kai da rayuwarsa gashi sun kaishi ƙasa cikin sauƙi.
To shi dama al'amarin rayuwa haka ya gada. Shiyyasa masu iya magana kance ba farkon ba ƙarshen. Yanzu dai su Mabera mi kuma ya rage musu? Ta duniya dai ta ƙare, kuma ita ba komai bace ba. Dan babban tashin hankalin na gaba, zasu fara kuma fuskantarsa ne tun daga tsayawar mala'ikan mutuwa a kansu. Ranar farko ta kabari, (Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Bayin ALLAH akwai fa aiki a gabammu wlhy tallahi. Kunga zare rai da ranar farko ɗin nan kawai ta kabari ta ishemu tabbatar da mun shiga ukunmu. Balle abubuwan da zasu biyo hakan. Ya rabbi ka gafarta mana badan halinmu ba😭🙏. ALLAH yasa muyi ƙyaƙyƙyawan ƙarshe 😭🙏).
________★
A dalilin abinda ya faru na su Mabera akai gaggawar kai su Sanata Bukar kotu. Dan kuwa gaba ɗaya zargi na zahiri ya koma ya ta'allaƙa akansu ne. Duk da mafi rinjayen mutane basu yarda su kaɗai bane. To da yake wanda basu bayyanar ba sun fisu ƙarfin iko sai suma suka bi ta ƙarƙashin ƙasa dan ganin an shafe babin su Bukar ɗin da wuri-wuri. Balle kuma ga al'amarin case ɗin ƴan Giro da ya zama gaba-gaba shima. Tun a zaman farko hankalin su Sanata Bukar yay matuƙar tashi, dan kai tsaye rashin nasara ya bayyana a garesu. Duk da kuwa iyalansu sun narka kuɗaɗe wajen ɗaukar gawurtattun lauyoyi akan case ɗin.
Su AA sun halarci zaman suma. Tun shigowarsa kuma ido cikin ido AA sukayi da Sanata Bukar. AA ya wani lumshe idanu yana sakar masa murmushi. Wani abu mai nauyi ya tokare zukatan Bukar da abokansa. Ji suke kamar su kama AA ɗin su shaƙure har sai ya daina numfashi, dan a ganinsu komai fa da ya faru da su kamar shine sanadi. Tunda da Mabera bai je ya aikata abinda ya aikata a gidansu ba ta tashi da shi da ba'a kai haka ba. Da AA bai je ya bama jama'ar Giro taimako shi da ƴan uwansa ba nan ma da