AJIYA A DUHU BOOK 1 & 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   194 / 213

579K to 582K   out of 636.6K words

bata kife da su ba. Gaba ɗaya sai suka tattara komai a kansa. Koda bayan an tashi har aka zubasu a mota wani mugun kallo suke ma AA, sai dai ta banza tunda iyakarsu kallon ne kawai. Amma na gaba yayi gaba na baya kuma sai labari. A wannan wasan dai AA ne dai yay nasara. Haka aka wuce da su prison da alƙali ya bada damar cigaba da ajiyarsu...

      Su kuma su AA suka wuce asibiti domin duba masu jiki. Sun fara shiga ɗakin Abah, Alhamdullah jikinsa da sauƙi sosai, dan yanzu haka ma Umma na bashi abinci ne ana kuma ɗan hira da shi kaɗan-kaɗan. Harda dariyarsa dan kowa ƙoƙarin bashi farin ciki yake. Koda wasa ba'ayin wata maganar da zata ɗaga masa hankali. Dan haka ko tvn ɗakin da yake ma ba'a kunnawa balle yaga abinda ke faruwa. Abinda ya faru kam koda wasa babu wanda ya taɓa tada zancen a gabansa. Alhamdullahi sai hakan kuwa ke taka rawar gani wajen ingatar lafiyar tasa, har ma ana saka ran bashi sallama a satin nan.
      Sun leƙa Mamy itama kamar yanda Oum ta sharɗanta musu. A ciwo na jiki dai da sauƙi. Dan ƙafarta mai harbi da kumburin fuska duk zamu iya cewa sai ɗan saura, idon ne dai har yanzu a rufe sai in zasuyi treating ɗinsa su kwashe bandage ɗin suyi su maida sabo. Sai kuma ainahin ciwon zuciya da ya gama kassarata tako ina har ya kai ya taɓa mata hanta da huhunta da ƙoda ma. Kuma duk hawan jinin da take fama da shi ne shekara da shekaru taƙi maida hankali akai ne sanadi. Itama dai badan idon ba da sallamar zata samu a yau ma. Amma RK yace su ɗan ƙara jinkirtawa. A duk sanda su AA suka shigo dubata sau ɗaya tak a rana da sukeyi sai tayi kuka, kukan dake sosa musu zukata sai dai suna dannewa su daure suƙi nuna damuwarsu a zahiri.  Ita kuma Aunty duk sanda suka shigo tata tausarsu kenan da musu nasiha. Yanzun ma bata fasa ba sai da ta musu, suka mata godiya suka fita batare da sun sake ma Mamy magana ba bayan addu'ar samun lafiya da sukanyi mata kullum idan sun shigo, gaisuwa ma aunty kawai suke gaisarwa dama.
        Sunje sashen da su Gwaggo suke tasu jiyyar. Acan suka samu su Ammie sai kawunan su Maanal biyu da mata biyu da su AA suka taho dasu a ranar da suka je. Lamarin Babu da Gwaggo dai sai addu'a. Dan kuwa dai Babu ashe duk jiyyar da yake fama da ita tsahon lokaci cuta ce mai karya garkuwar jiki a tare da shi. Wato HIV, zuwa yanzu kuma tana neman kaiwa matakin ƙarshe AIDS ma. An kuma binciki Sailuba itama tana da ita. Kuma suna da tabbacin a jikinta Babu ɗin ya samu.........✍️184



.......Kamar ya da bincike ya nuna Babu ya samu cuta kai karya garkuwar jiki ne a jikin matarsa Sailuba. Sai dai yanayinsu daya kasance ba ɗaya ba yasa shi tashi ta fara bayyana kafin ita, tunda gashi shi har ya kai matakin aids ma. Ita ko Gwaggo ƙaniyarta da taci hannun mazajen yaran su Sen.. ya sata ƙarasa ragargajewa. Itama kuma doctors na ƙyautata zaton zuwa nan gaba za'a iya samun ciwon na HIV a jikinta tunda wanda sukama Sailu fyaɗe sune sukai mata. Tsakanin safiyar yau zuwa yanzu su Maanal basu san iya adadin kukan da sukayi ba. Sai dai mai faruwa ta riga ta faru kuma sai haƙuri. Shi kansa AA da su Babban Yaya al'amari ya daki zukatansu. Wato dai halin da su Gwaggo suka so ganin su Maanal ne a ciki ya koma kansu. Hakan na nufin yanzu tun a duniya azzaluman mutane ke fara karɓar sakamakon ayyukansu kafin aje fagen faman da kowa zaici ubansa dai-dai gwargwado. Su dai sun lallashi su Maanal da musu nasiha akan yarda da ƙaddara da kuma amsarta a yanda tazo ayi haƙuri. Daddy da su Baba Sardauna suka tayasu. Haka dai aka tattaushesu har suka sami nutsuwar zukata....

________★

       Ba'a zuri'ar su Maanal kawai ake rabo raba sida ba. Anan ma Hajiya Turai tashin hankalin da take ciki kenan. Dan kuwa tunda likitoci suka bayyana Sille na ɗauke da ciwon HIV duk wani mai alaƙa da shi hankalinsa ya tashi. Tuni su Hajiya Turai da su Haule aka garzaya asibiti layin gwaji. Mizai faru, mai afkuwa ta riga ta afku, dan kuwa duka su suna da ita. Ita Hajiya Turai ma abu goma da goma dan harda Brain Cancer ke damunta. Dama tanata fama da ciwon kai mai tsanani tunda al'amarin nan ya faru. Ashe-ashe Brain Cancer ɗin ce ke son bayyana kanta. Tana a cikin wannan ruɗanin da tashin hankali sai ga baƙi kamar daga sama. Ba kowa bane face dangin mijinta. A surutan da Sille keyi ya ambaci cewar itace ta kashe mijinta. Nan take aka shiga neman inda suke, dan dama amma Sille allurar dake tare da shi ta maida shi kamar mahaukaci ne dan aji sirrika da yawa. Sai aka samu matsala mahaifinsa Mabera ne keda sirrin ma da suke son ji ɗin. Wanda ke kan Sille ɗin duk surutai ne na abinda ya aikata da inda suke ajiye dukiyarsu dan shine mai adanawa. Da wasu mugayan harƙallarsa da yake yi shi da ubangidansa, da likitan nan daya sayar ma Mamy allurai Gaga shima anyi ram da shi..
     Haka aka kwashe Hajiya Turai akai Lagos da ita. Dan sunce su bazasuyi shari'a da ita a Abuja ba sai acan. Hankalin su Saheeba da Nuratun kanta ya tashi matuƙa. Itama babu shiri ta wuce asibiti gwaji dan Sille ya taɓa tarayya da ita akan zancen AA. Duk da dai ba kai tsaye ta bashi kanta ba bugar da ita yayi ya aikata hakan. Bawai bata iskanci bane ba, tabbas tana yi tun ma a Secondary. Sai dai ba kowa take yarda da shi ba, saboda ma yanda ta ƙwallafa ranta akan AA yasa take kiyayewa sosai sai jefi-jefi. Ta gwamnaci ta aikata ɓarnarta da kanta. Ai ko dai itama ta samo nata sakamakon, dan kuwa dai ta tabbata ta kamu. Gaba ɗaya rikicewa tayi, har sai da likitan ya riƙeta, da ga ƙarshe ma jininta ya haye sai gata a ƙasa. Dole sauri-sauri aka bata gado. Babu wanda yasan halin da take ciki harta farfaɗo, sai Saheeba da rashin dawowar Nuratun ya ɗagama hankali taketa kiranta a waya doctor ya ɗauka ya sanar mata gana asibiti babu lafiya. Bai gaya mata ainahin minene ya faru ba, saboda tsakanin likita da mara lafiya akwai sirri ai. Hankali tashe ta samu babban Yaya da maganar, yace ita da bata da lafiya ina zata ta zauna gida zaije. Amma sai ta dage. Ganin yanda take kuka sosai sai ta bashi tausayi, dan a ganinsa yanzu basu da uwa dole su so kansu sosai. Haka ya ɗauketa sukaje tare. Sun duba Nuratu data farka tanata kuka. Haka Saheeba ta rungumeta tana tayata. Babban Yaya yay musu magana da nasiha sannan suka nutsu. Nuratu dai bata faɗima kowa gaskiya ba aka sallamota suka dawo gida. A lokacin ne kuma batun Hajiya Turai daketa watsuwa a duniya suma ya iso kunnesu. Sai Nuratu ta sake rikicewa, Saheeba kam mamaki ne ya kamata jin wai Sille nada alaƙa da yayar mahaifinsu. Kai jama'a wannan wane irin ruɗaɗɗen al'amari ne haka? Miyasa zasu ga irin wannan ƙarshen. Ta ko'ina su dai ahalinsu nada tabo..
   
     (Niko Bilyn ku nace, “Saboda shi kuka SHUKA Saheeba, kunga kuwa dole ku girbe komai daki-daki 😮‍💨)

_________★

         Alhamdullahi an koma kotu, an kuma yanke ma su Sanata Bukar hukunci dai-dai da laifinsu na zama a gidan yari shekaru 25 su da wanda suka sanya sukama su Gwaggo fyaɗe. Tare da horo mai tsananin gaske. Sai dukiyarsu da aka ƙwace dan an gano sun handame ne daga asusun gwamnati. Wannan kam hankalin iyalansu sun tashi. Sai dai kuma babu yanda suka iya. Irin su Rabilu da ba'a da komai kam ai sai dai kukan shiga uku kawai da matarsa ke sha. Haka dole ta tattara yaranta suka koma ƙauyensu, duk da can ɗin ma dai an saka rayuwarsu gaba da tsokana da habaici. To koyaya dai tunda iyayenta nada rai ta samu sassauci.
     Matan Sen.. kam tuni suka ɗiba rabonsu kowacce ta kama gabanta. Sai uwargidan abin ya ƙare a kanta. Ita mai yin soyayyar gaskiya, aiko taga soyayyar gaskiya dan ta tashi a tutar babu sai ɗan abinda take da da wanda yara ke da shi ta tsira. Daga ƙarshe itama dai ƙauyen na su ta koma. Sai dai kuma bata samu karɓuwa ba dan jifanta aka dinga yi ita da yaran, sanda sunada arziƙi basu taimaki kowa ba. Dole a washe gari suka baro garin suka koma cikin Kano suka kama hayar ƙaramin gida dai-dai rufin asiri na talaka suka zauna...

________★

      Al'amarin Mabera kam yayi tsamari sosai, dan ta kai kullum yanzu sai an ƙara masa ledar jini ɗaya, kafin safiya kuma ta tsiyaye tas, sai an sake ƙara masa wani. Al'amarin dai ya cika ya tunbatsa guba ta gama cinye komai na jikinsa. Idan ka ganshi kamar ba Mabera ba. Ba magana sai idanu kwale-kwale sun shige can cikin kwarmin ido saboda azaba. Yayi wata muguwar rama ta tashin hankali. Kaɗan ya rage ya gama komawa kwarangwal dan duk wani nama na jikinsa ya kusa gama cinyewa. Ga dai duniyar ana jinta ana ganinta komai ya rikice. Yana kallon kuma komai da ake nunawa akan Sille da halin da yake ciki na hauka tuburan ga makanta da ciwo a jiki, haukan da yake a ciki ma ya hana ai masa magani. Sai abubuwan suka taru sukai masa yawa, yawa mai tsannanin gaske. A yau da jami'an tsaro suka kammala tattaro dukan dukiyarsa dake ɓoye a Lagos da Abuja kamar yanda Sille ya faɗa sosai mutane suka girgiza. Dan dukiya ce mai yawan gaske da nauyi da shi kansa bai ma san mizaiyi da ita ba. Haka aka shiga warewa da tantance wanda za'a iya gane masu ita. Anan ne nasu Daddy ya fito. Haka aka nemesu shi da Yazeed sukaje suka amsa. Hakama sauran mutane duk wanda aka gane tashi an bashi, wanda kuma suka kashe an nema iyalansu an basu. Sauran kuma jami'an suka danne wasu, wasu aka fitar aka raba gidan marayu da gidajen yari. Wannan baƙin cikin rabon gadon dukiyarsu da akayi ya shaƙar da Mabera bai kwanan duniya ba a wannan dare. Haka ya mutu yana garzaza ihu da faɗin dukiyarsa-dukiyarsa a matsayin kalmar shahada.
      Oh-oh waɗan nan fa sune ɓurɓushin jinin ƙaruna da alama. An rayu da son tara dukiya an kuma samu, izza gadara taƙama da jin ƙarfin iko akan hakkokin wasu duk ya rufe musu idanu suna jin babu yasu. Yau kuma gashi cikin sauƙi komai ya tsaya cak, irin cak ɗin da bata da madadin sauyi, sai kuma anje can babbar kotu a girba daga abinda aka shuka. Dan UBANGIJI baya yafe laifin wani akan wani komai ƙanƙantarsa komai kuma yawan ibadarka. Yanda ka shuka haka zaka girba abinka.
       Mutuwar Mabera tama mutane da yawa daɗi, ta kuma jijjiga mutane da yawa, wasu ko suna a tsaka tsaki. Dan ita kanta Mamy tana cikin ƴan tsakkiya, ƴan bama farin ciki, ba kuma ma baƙin ciki. Dan itama dai tata ya isheta ma.
      Sille kuwa sai abun nashi ya ƙara tirewa gaba ɗaya hauka tuburan. A daren ya ma gudu daga asibiti. Babu neman da ba'ai ba aka kasa ganosa. Sai da safe aka samosa tsirara cikin kasuwa yara na binshi yana jifansu da tiƙar rawa. Sai surutai yake yana faɗin matan da yay iskanci da su. Gangami akayo daga asibiti domin ɗaukarsa amma ya gagara kamuwa, daya damƙi wani ma'aikacinsu ma sai da ya suma. Suko sukaga bazasu saka kansu a wahala ba suka barshi. Kafin gari ya waye yayi gaba ma....

_________★

        Daddy ya kira Kawu Manu yay masa bayanin dawowar kayansu. Ga kuma na Hajiya Basariyya a hannunsa. Amma sai kawu Manu yace su zauna da yayanta a rabawa ƴaƴanta kowanne a bashi dan Hajiya Basariyya bata dace da abata dukiya ba a yanzu. Ana bata zata sake samun damar komawa ga bokaye koma ta gudu a gida. Sosai Daddy ya gamsu, haka kuma aka zauna aka rabawa yaranta komai yanda ya dace batare data sani ba. Na Huznah aka bama Sageer, dan a yanzu ko sunan Hajiya Basariyya Huznah bata ƙaunar ji, takanta ma take yi haihuwa ko yau ko gobe. Alhamdullahi Sageer da iyayensa kuma na tsaye a kanta. Dan ko darajar Daddy bazasu taɓa barin Huznah ta wulaƙanta ba a rayuwa. A tsakanin ma ALLAH ya sauketa lafiya ɗa namiji, Alhamdullah kuma babu wani matsalar da ake jima tsoro data sameshi. Haka su Ammie da ƙannenta suka shirya sukaje Kano ana kwana biyu suna. Yaro yaci sunan Daddy, Maanal taso zuwa AA yaƙi yarda da yake a tsakanin bata da isashen lafiya gasu Babu a asibiti, ita kanta Ammie dauriya ce kawai.........✍️


Man Sageer ALLAH shi raya Usman fodio🥰🤏185


.......Anan gidan Darma ma kuwa gagarumin shirin shagalin sunan yarinyar RK aka shirya tare da bikin shekarar musulunci dana samun lafiyar Abah. Dan kuwa a ranar aka sallamesa. Yarinya taci suna Maryam. An yima Mah-mah takwara. Matuƙar raƙashewa akai da ƙwallewa dan su Aunty Rufaidah basu rage komai ba. Kuma Alhamdullah mutane sun halarta sosai dan ahalin Kura basuji ƙyashin zuwa Abuja an haɗu anyi komai da su ba. Cikin ƙanƙanin lokaci farin cikin taron sunan nan ya danne kaso mafi yawa na ɓacin ran abubuwan da suka faru. Su Mamy dai ana asibiti sai a tv aka gani da ido ɗaya🤭.
       Ana kammala taron suna dana sabuwar shekara washe gari ƴan Kano suka tattara suka koma gidan kodan masu aiki su koma kan ayyukansu maijego da ita aka tafi. Suma anan dai su Maanal shirin komawa aikin sukayi. Yayinda Oum da Abah ke shirin wucewa ƙasar Saudia a birnin Madeena domin hutawa. Dan Abah yace can yafi buƙatar zuwa. Yana son zuwa kusa da MANZON ALLAH yay hutun. Haka kuwa akayi. Kwanaki uku bayan wucewar kowa su AA sukai musu rakkiya cike da kewarsu. Sai dai suma sunce nan da kwanaki kaɗan zasu iskosu. Ko yanzun ma basu bisu bane saboda abinda suka shirya kar Oum ta ɓata musu shiri..
     Bayan wucewar su Oum gida ya koma daga su sai su. Sai kuma duk suka ji babu daɗi. Musamman Ameerah da Najma, dan ita Maanal tana fita aiki. Nibras da Saheeba da Nuratu ko ba shiga harkar su suke ba. Musamman ma Nuratu da kullum tan ɗaki tana kuka yanzu ta kasa gayama Saheeba ma matsalarta. Itama dai Saheeban ba'a dai-dai take ba. Dan har yanzu tana cikin matsanancin damuwa da tashin hankali. Ga Naufal ma ya wuce tare da su Oum, za'a saka shi makaranta a can Saudia ɗin kamar yanda su Babban Yaya da su Yaya Fawzan suka yanke shawara.
       A wannan tsakanin Saheeba da Nuratun sukaje Kano bisa umarnin babban Yaya, dan baban nasu na shirin ƙara aure shine aka son raba musu gadon abinda Nana ta bari. Abin ya musu ciwo, a ganinsu babban nasu bai ƙyauta ba da zai yi aure ko arba'in uwarsu batai ba. Koda suka iso Kanon sukai ƙorafi sai dangi sukai musu caa, dole sukai shiru. Haka suna ji suna gani akai musu rabon abubuwan da basu taka kara sun karya ba su da mahaifinsu. Aka kuma shiga gyaran gida, sukace zasu dawo akace basu isa ba dole su zauna a gama bikin babansu. Tsoron dangin mahaifinsu suke yanzu dan sun san basu da wani gata kuma ko mai basu kariya a yanzu, balle Babban Yaya ya tabbatar ma Saheeba idan yaji wani abu da bai masa ba wlhy ita zai hukunta. Wannan ya ƙara tsoratata dan a yanzu bata fatan abinda zai rabata da gidan Darma, ta tabbata hakan na faruwa rayuwarsu ta shiga garari ita da ƴar uwarta. Gidan Turai kansa ƴan uwan mijinta sun zo sun saida shi. Har an tattaroma Nuratu kayanta ma an aiko mata. Hatta motar Nuratun ma sun ɗauke sunce kuɗin dan uwansu ne, kai duk ma wani abu mai muhimmanci da Hajiya Turai ta sai mata sai da suka rabata da shi. Suturunta zuwa tarkacen takalma da bags kawai suka aiko mata. Ga batun Hajiya Turai kowa ya kasa bibiya a ƴan uwan nasu ana jin tsoro dan dangin mijin nata dai basu zo da wasa ba.
     Haka dai akasha bikin Babansu da aka bashi budurwa sabuwa a leda, yarinya shiru-shiru mai nutsuwa ga ilimin addini. (Dama fa haka duniya take, wani sai yasha wuya a farko ƙarshe ya baje kolin more romon dimokuraɗiyyar sa hankali kwance kamar dai baban su Nuratu. Miyafi ransa budurwa a ledarta jama'ata😂🤌). Ai ko shi dai sai yace wannan mutuwa gwara da akai. Dan ta sama masa filin shaƙatawa da na sabuwar duniya. Ƙullin goron da Nana ta masa na asiri duk ya sake shi, ita kuma ta tafi da nauyin a kanta tana can tana amsar walmakalifatu a kabari.
     Da dare bawan ALLAHn nan babu kunya ko nauyin su Saheeba dake gidan ya shige ɗakin amaryarsa. Aiko washe gari amarya bata ma fito ba suka baro Kano a motar haya sai ganinsu su Maanal sukai tsulum a gidan da sassafe da yake weekend ne kowa yana gida. Babu wanda yace dasu ƙala, dan basu aikesu ba, kai ko sallama ma basuyi musu ba da zasu tafi.

      Su Oum nada sati biyu a Saudia Ameerah da Najma suka kwanta ciwo a tare, al'amarin kamar wasa dai Maanal zata awo su babban Yaya sukace su bita a tunanin kowa zazzaɓi ne na yau da kullum. Sai me gwajin farko ya nuna su dukansu akwai ciki a tare da su. Ruɗewa Maanal tayi saboda farin ciki. Sai tama rasa wazata fara kira tsakanin Babban Yaya da Yaya Fawzan. Yaya Fawzan dai wannan shine abinda dama

194 / 213

Chapters