AJIYA A DUHU BOOK 1 & 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   191 / 213

570K to 573K   out of 636.6K words

da ake bashi ma da ƙyar yake iya tsakura. Zamu iya cewa ma gaba ɗaya baya a hayyacinsa shi.
     Ba tausayi babu tsoron ALLAH balle rangwantawa yaran Sanata sukama su Gwaggo fyaɗe. Ko kallon tsufar Gwaggo basuyi ba tunda gara Sailu da ƙuruciyarta. Ba kuma mutum ɗaya yayi ba kusan su shida ne kowacce mutum uku-uku. Kai daga baya ma wasu suka ƙarama Sailu wai sunga da sauran ta. Gwaggo kuwa tuni ta suma. Itama Sailu ɗin ta suman daga baya, haka suka saka musu ruwa suka farfaɗo. Sukam ai sun samu nayi, sai suka basu magani wai susha su watsakke kafin gobe. Abin kamar wasa washe gari ma haka suka sake musu fyaɗe, yau kam da Gwaggo ta suma ai ta jima bata farfaɗo ba dan azaba, kuka kam ai ɗan gata ke samun yi basu ba. Sailu kam yau ta banbance tsakanin iskanci da horon azaba. Dan ta gane ALLAH ɗaya ne....

_________★

         Baba Sardauna ma dai sunje Kebbi ɗin tare da AA da Uncle Najeeb. Sun kuma gana da gwamna akan al'amurin. Babu ɓata lokaci a kuma gabansu ya saka kwamitin bincike akan al'amurin. Sannan ya basu haƙuri da tabbatar musu nan da kwanaki biyu in sha ALLAHU zasu ji komai. Basu baro garin ba sai da aka kaisu inda aka ajiye mutanen garin Giro. Babu abinda akai musu na cutarwa, sai dai inda aka ajiyesu baima AA ba dan haka yay magana. Aiko a take mataimakin gwamna dake matsayin ɗan abokin Baba Sardauna yasa aka canja musu wajen zama, tare da basu abinci mai tsafta.
     Sudai basu san su wanene AA ba amma sunata musu godiya da sanya albarka. Haka su AA suka barosu suka wuce Abuja. Suna isowa suka tarar da abin farin ciki Nuwaira matar RK zata haihu. Dangi anata addu'a dan har an shiga da ita ɗakin haihuwa. Sai da suka fara leƙa Abah dake barci dan yanzu sosai barci likitocin ke sakashi dan brain ɗinsa ta huta. Ƴan awoyin da suke barinshi ido biyu ba wasu masu yawa bane sosai.
    Suna fitowa daga inda Abah yake kamar jira Nurse ta fito tana musu albishir da haibuwar Nuwaira. An samu mace. Lokaci ɗaya farin ciki ya zagaye fuskokin wannan ahali. Kowa nata ambaton Alhamdullah. Saura kuma matar Uncle Najeeb, dan itama dai da alama a kusa take gab, duk da dai Nuwaira ta rigata samun cikin. Gaba ɗaya hankalin su Yaya Fawzan ya koma kan RK, suka tasashi gaba da tsokana har sai da ya gudu. Shima haka yake ma kowa dan haka babu mai raga masa suma.
    Bayan an kimtsa maijego da jaririya  aka fiddo da ƴar Babyn. Oh oh yarinya kamar RK yayi kaki ya ajiye. Tun kamin ma ta huce kasan ubanta ce. Yaya Fawzan dake kusa da RK ya matsar da bakinsa kusa da kunensa cikin raɗa ya ce, “Wato Uncle hakan dai na nufin kafi Mamanmu jaraba fa, irin wannan kamanni da ƙanwarmu keyi da kai haka”.
        Dariya Modibbo dake kusa da su ya kwashe da ita. Haka ma AA ya ɗan murmusa yana girgiza kai. Wlhy babu wanda ya kai Fawzan da RK rashin ji a family ɗinsu. Sufa kowa basu bari ba. Shi kansa babban Yaya daya fahimci iya shegen nasu ne ya motsa a fili yace, “ALLAH ya shiryeku kudai kam”.
        Yarinya ƴar dangi sai da kowa ya ɗauketa yay mata addu'a. Daga ƙarshe Baba Sardauna yay mata addu'a sannan aka bama matan. Dan su Maanal duk sun ƙagara su ɗauka. Aiko haka suka zagaye Umma data amsa kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Mah-mah da Gwaggo Khadijah dai sunyi kawaici, amma haka Umma ta miƙa musu duk suka ɗauka suka sanya albarka sannan aka bama su Oum. Daga nan su Maanal daketa zumuɗi suka amsa. AA ya zubama Maanal ido ganin yanda bakinta ya ƙi rufuwa, ta katantane taƙi bama su Najma ma su ɗauka. Idanunsa ya ɗan lumshe yana murmushi. Ashe Yaya Fawzan na kallonsa.
        “Uhm-uhhm! Auta-na-Auta!”.
   “Besty kuma na Besty”.
RK ya karɓema Yaya Fawzan. Aiko a tare suka kwashe da dariya. Uncle Najeeb ya ce, “Kai waɗan nan munafukan yara kun ishemu. Rafeeq da Fawzan ba. Ku kowa baku bari ba. Ajwaad manta da su kaji. ALLAH dai ya kawo wani aikin da za'a shillasu wata ƙasar kona shekara biyu ne mu huta da su”.
       “Ba Amin ba!!”.
   Yaya Fawzan da RK suka haɗa baki wajen faɗa. Aiko babu wanda baiyi dariya ba.. Daga nan suka shishshiga suka duba Nuwaira, Alhamdullah tana cikin ƙoshin lafiya. Dan amma sallameta. Babu wani ɓata lokaci suka tarkata zuwa gida, harda Saheeba da itama aka sallama yau. Sai Nuratu dake jiyyarta. Kasancewar idan Abah na barci ba'a barin kowa tare da shi, kuma akwai securitys har huɗu a ƙofar ɗakin da yake gaba ɗayansu suka wuce gida. Sai Aunty dake jiyyar Mamy itama suna nan.......

________★

         Kamar yanda Daddy ya rantse hakan ce ta kasance. Ya hana Hajiya Basariyya shiga masa gida. Kai daga ƙarshe ma a daren jiya ya gama yankema zuciyarsa shawarar barin garin Kaduna. Dan haka yau shi da Yazeed da sassafe suka iso Abuja. A cikin gidajensa dake na sayarwa a yanzu suka duba wanda ya dace da zaman family gaba ɗaya. Duk da dai da farko yayi tunanin rabasu sai Hajiya Yaya ta shiga roƙonsa akan a'a dan ALLAH kada ai haka. In dai itace wlhy ta kwantar da hankalinta in sha ALLAHU baza'a sake samun wata matsala daga gare ta ba. Dama tasan Ammie bamai matsala bace ba.
     Daddy yace bai yarda ba shi kam yau da gobe yake tsoro. Sai lokacin Ammie ta saka baki. Cike da lallashi tace karya damu yay musu addu'a in sha ALLAHU lafiya zasu zauna. Ita kanta Hajiya Basariyya da yayi haƙuri ya barta ta dawo.
         Daddy yace, “Humm ai na gaya muku saki uku nai mata. Ko zaku sake hallatawa ne?”.
    Haƙuri suka bashi, daga haka kowa yay shiru. Gida dai komai akwai na buƙata, kayan sakawarsu kawai zasu ɗakko da muhimman abubuwansu. Dan haka babu ɓata lokaci a ranar suka juya Kaduna har su Ammie. Tunda fa suka tafi suketa tattare-tattaren abinda ya kamata ana tahowa da su. Yau suka kammala komai cikin amincin ALLAH, Daddy yace kayan da basa so sai su bada su. Ita dai Ammie komai nata Nene ta kaimawa. Duk da ma dai a ranta so take ta ɗauke Nenen ta maida kusa da ita. Itama Hajiya Yaya sai ta bama wasu ƴan uwansu da basu da ƙarfi. Kayan Nazeerah kuma aka kwashe su kaf aka kai gidan Sabuwa. Itama na Hajiya Basariyya haka aka kwashe aka kai gidan Yayanta.
     Ai ko kawo wannan kaya ya matuƙar tada hankalin Hajiya Basariyya da Sabuwa. Dan ita Hajiya Basariyya dama dabi suke da Yayanta yace bazata zauna masa gida ba sai dai ta tafi ƙauye gidan Kawu Manu tai iddarta. Hankalinta duk a tashe yake da wannan batu shiyyasa taketa neman mafita na ganin ta dai-daita da Daddy ko alfarmar zaman ƴaƴanta taje tayi daga nan koma mizai biyo baya ta barma kanta, dan tayi alƙawarin yanda Daddy ya saketa suma su Hajiya Yaya wlhy sai ya sake su sai dai ya sake auro wasu matan kuma. Amma mi kwatsam kuma babu zato babu tsammani yau sai ga motar kayanta. Aiko yayanta yace karma su sauke, zai biya su tare da adireshin inda zasu kaisu. Hajiya Basariyya na kuka da magiya yayanta ya biya masu mota yace su tafi sukai ingawa. Koma muce ƙauyen Ingawar tunda dai Kawu Manu ba'a cikin Ingawa yake ba.
     Ganin babu mafita Hajiya Basariyya ta shirya guduwa, aiko Yaya ta yay ram da ita..........✍️

      😂🤣Wayaga ɗaurin goro. ALLAH yasa muyi ƙyaƙyƙyawan ƙarshe 🙏😊.179



.........Sabuwa kam kuka take tana ƙarawa. Dan ganin wannan kaya ya dawo mata ne da mutuwar ƴarta sabuwa fil a zuciya. Da yake tana a gidansu ne bata koma nata gida ba har yanzu. Sai mahaifiyarsu ta bada shawarar akai kayan can tunda itama dai can zata koma da zama. Mizai faru, kawai sunje kai kaya suka samu gida a kulle an tile mata komai na gidan a compound. Mamakin ALLAH ya kama Sabuwa. Babu shiri ta shiga maƙotamsu tana tambaya. Bayan sun sake mata gaisuwa basu ɓoye mata komai ba sukace ai Hajiya Zahedah ce da mijinta da wannan aikin. Hatta motocin gidan gudan huɗu, tata ɗaya, sai ta Nazeerah dana Mabera biyu duk su suka kwashe. Ama taƙaice mata zance gida dai sun saida shi. Sai dai kuma a yau wani sabon rikici ya sake tashi akan ai mijinta ma ya riga ya saida gida kafin ya tafi shima, yanzu haka ita Hajiya Zahedah da mijin nata ma suna police station.
       Sunan station ɗin kawai ta amsa itama, tace motar kayan Nazeerah ta koma da su can gidan babanta. Masu mota haushi ya fara kamasu. Amma da yake ta ƙara musu kuɗi sai suka juya suka koma. Ita kuma ta nufi police station ɗin da akace mata ana rikici tsakanin su Bakori da wanda suka sai gida a hannun Mabera. Tako tadda rikicin, dan har ana fara bama hammata iska sai da jami'an tsaron station ɗin suka shiga ciki. Zuwan Sabuwar kuma rikicin ya sake sama. Gata tana fama da ɗaurarren hannunta mai karaya. Ƙafarma cike da ƙarfin hali take takata.
     Faɗa ya sake tashi tsakanin Hajiya Zahedah da Sabuwa. Bakin Hajiya Zahedah ya suɓuce ta ce, “Wai shin Sabuwa mi kike taƙama da shi? Kin haihu da Mabera kawai? Shiyyasa kike ganin kina da wata isar banza da wofi akan dukiyarsa. To ai kin yi ta banza dama wofi, dan nima nawa ƴaƴan ai jininsa ne sunma fi naki ƴaƴan gadon tunda su maza ne!!”.
      Wani irin shiru station ɗin ya ɗauka na sakanni like shirun nan da yara ke faɗin mutuwa ta ratsa, da ba'ai shiru ba data ɗauka😆😂. Kowa yayi wani irin galala yana kallon Hajiya Zahedah har shi mijin nata Bakori. Sai da Sabuwa ta karya alkadarin shirun da faɗin, “Ƴaƴanki ƴaƴan mijina ne kuma Zahedah?”.
       Shiru Hajiya Zahedah tayi dan ta fahimci kam dai tayi ɓarin baki a wannan gaɓar, sai kuma ta ɗan kalla mijinta kaɗan, ganin ita yake kallo shima da sauri ta kauda kanta. Sai kuma ta maida ga Sabuwa zata fara borin kunya mijin nata ya daka mata tsawa yana wani irin miƙewa. Da sauri ta koma jikin bango ta maƙale, cikin matuƙar tsawa ya ce, “Zahedah! Maimaita abinda kika faɗa! Ƴaƴan nawa ne kike kira da ƴaƴan Mabera?!”.
        Cikin rawar jiki data baki ga hawaye Hajiya Zahedah ta shiga rantsuwa ita ba haka take nufi ba. Ita wlhy kawai dan tana son su amshi gidan ne kamar yanda yace suyi...
     Ganin tana ƙoƙarin tona masa asirin shirin da sukayi akan ƙwace gidan Sabuwar ya sashi sharara mata maruka sai da ƴan sanda suka riƙeshi. Ai ko ya dinga babbotai bazai yarda ba wlhy sai sunje yau ɗin nan an musu gwaji shi da yaran kaf. Da ƙyar ƴan sanda suka tausashi yay shiru. Daga nan aka kwashesu zuwa asibiti. Suma yaran akaje aka ɗibosu da yarinyar Sabuwa ɗaya data rage......

________★

          Tunda su Saheeba suka shigo gidan ta saka maigadi ya rakasu inda kabarin Anum yake. Durƙushewa tai tana kuka mai ban tausayi. Shike nan ta rasa ƴar Anum ɗinta. Ƙyaƙyƙyawar yarinya mai tsannanin kama da mahaifinta. Anum na sonta fiye da Naufal. Duk da dai shima har yanzu yaro ne. Amma yanda Anum ke ƙulafucinta shi sam bayayi, gaba ɗaya rayuwarsa ma yafi sonta a sashen Oum.
    Nuratu data riƙota tace, “Aunty ya zamuyi, shike nan mun rasa Mama mun rasa Anum a lokaci guda. Na rasa Yaya AA kema kin rasa cikin da akasha wahala kafin samunsa kin rasa mahaifarki har abada. Shike nan Aunty mun rasa komai”. Suka sake fashewa da kuka. Sun jima sunayin abinsu babu mai lallashi dan babu wanda ma yasan suna a wajen kowa hankalinsa nacan akan Nuwaira maijego. Daga ƙarshe dai da ƙyar Nuratu ta saka Saheeba suka taso suka dawo sashensu. Babu kowa a sashen dan Ameerah ma tana can sashen Oum. Su Babban Yaya kuwa suna sashen baƙi tare da su Uncle Najeeb. To haka dama ita rayuwa take, ana bikin duniya wasu ke na kiyama. Lokacin da kai kake kuwa wani a lokacin yake samun farin ciki, sanda kake farin ciki wani a lokacin yake kuka. Shiyyasa kuma masu iya magana sukace IDAN ZAKA GINA RAMIN MUGUNTA, KA GINA SHI GAJERE DAN MAYBE FA KAI NE ZAKA AFKA BATARE DAKA SANI BA.
     Ga dai Saheeba komai ya suɓuce ya ƙare a gaɓar da ba'a shirya ba ko hasasowa balle tsarawa. Kullum cikin shiryama rayuwar wasu MUGUNTA ake da son taɗe su. Ba'a shiryama zuciya da rayuwa alkairi sam tamkar suke da yau da gobensu. (Ƴan uwa sai mu hankalta. Mu kuma sani duk yanda ka kai da muguntarka baka isa canja ƙaddarar kowa ba. Haka taka a karan kanka. Kana can kana shirya ma wani bala'i kai bala'in na tunkaro rayuwarka baka sani ba. A maimakon damuwa da damuwar wani ko burin tarwatsa shi yafi ƙyautuwa mu maida hankali wajen addu'ar neman kariya da wadatuwa da ƙyaƙyƙyawar zuciya. Mu saka gaskiya a dukkan al'amuran mu wlhy sai kuga anata bugawa haggu da dama amma an kasa cimmaka. ALLAH zai tsare ka ya kuma baka kariya tako wane ɓangare)
       A wannan gaɓar ma Nuratu ta fi Saheeba ƙarfin hali, dan ita ta taimaka mata tai wanka ta fita samo mata abinci. Sai ta samu Ameerah a kitchen, bata kulata ba itama Ameerah sai tai kamar bata gantan ba ta cigaba da aikinta. Dama cikin haushin Babban Yaya ya tasota tana hirarta wai ta masa kunun gyaɗa. Indomie Nuratun ta shiga store ta ɗakko, ta buɗe fridge ta ɗauki ƙwai. Ameerah dai nata faman motsa kununta kamar bata san da ita ba. Sai kawai Nuratun ta dinga jin kamar ta ɗaga tukunyar kunun ta kife a fuskar Ameerah ɗin..
       Da sauri wani sashi na zuciyarta ya gargaɗeta. (K Nuratu ki dawo hankalinki, yanzu abinda duk ya faru da ku bai zame miki iznah ba kenan. In dai ba so kike babban Yaya ya saki ƴar uwarki ku tattara ku koma Kanon da baƙya so ba toki kama kanki) Ajiyar zuciya ta saki a ɓoye. Sai kuma ta ajiye kayan ta fita akan sai Ameeran ta gama ta dawo. Ameerah da duk take sane da ita tai murmushi da faɗin, “Ashe gyaɗa dai taji matsa. Ai na zata zaki kawo min wani wargi ne na baki mamaki.” haka ya kammala aikinta harta kwashe tabar kitchen ɗin Nuratu bata dawo ba. Sai da tai wanka ta fito falo Babban Yaya ma ya shigo dan tare sukai wankan sannan taji motsin Nuratun a kitchen. Batai magana ba sai shi Babban Yayan, batare data kalli ko hanyar kitchen ɗin ba ta bashi amsa da, “Nuratu ce”.
     Kawai tai shiru. Bata sake magana ba ta cigaba da bashi kunun. Mizai faru Nuratu na fitowa zata gitta da indomie ɗin nan ƙamshinta ta daki hancin Ameerah. Da sauri ta miƙe tana toshe hanci. Gudu-gudu sauri-sauri tabar falon. Shi babban Yaya ma sai abin ya girmeshi. Ya bita da kallon mamaki kawai yana kallon kununsa da bata ƙarasa zubawa ba. Itama Nuratu sai tai kasade tana bin hanyar da Ameerah tabi da kallo. Tsohon lokaci zuciyarta na bugun ɗari-ɗari kafin taja ƙafafu da ƙyar zuwa sama.
      A yanda ta shigo ɗin ya saka Saheeba kallonta da jajayen idannunta da har yanzu hawaye sun gagara tsayawa a cikinsu. “Lafiya kuwa?”.
        “Da dai sauƙi kam Aunty, anya yarinyar nan ba cikine da ita ba?”.
     Mugun faɗuwa gaban Saheeba yayi, ta ce, “Wace yarinya?”.
     “Ameerah mana!”.
Ai tsabar yanda maganar ta daki Saheeba bata san ta zubo ƙasa ba daga gadon. Lips ɗinta na rawa ta ce, “Mimm mi mikika gani?”.
       Tsaff Nuratu ta kwashe labari ta bata. Gaba ɗaya Saheeba sai taji kamar kanta zai fashe dan tashin hankali. Dole ta zube a kwance jin ɗakin kansa na juya mata.....

     ★★ Anan falo kam jin shiru Ameerah bata dawo ba Babban Yaya ya tashi ya bita. Yana buɗe ɗakinta ya shiga dai-dai ita kuma ta fito daga bathroom tana goge fuska da ƙaramin towel. Kallonta ya tsaya yanayi, sai kuma a hankali ya ce, “Miya faru?”.
     Fuska ta yamutsa, kamar zatai kuka tace, “Ba komai fa. Kawai warin indomie ɗin can da Nuratu ta gitta da ita ne ta nema ɗaga min hankali”.
      Kallonta kawai yake yi, shi dai indomie ɗin can baiji tana wani wari ba. Hasali ma ƙamshi yaji. To lafiya kuwa Ameeransa take. Tunaninsa ya katse saboda matsowar da tai ta kama hannunsa tana faɗin, “Muje kasha kunun kada ya huce”. Riƙota yay ya saka a jikin shi. Cike da kulawa ya ce, “Amai kikayi?”.
       Kanta ta jinjina tana sake narke masa. Ya ɗan furzar da ajiyar zuciya da faɗin, “Bar batun kunu muje na kaiki asibiti”.
     “No! Yaya nifa babu abinda ke damuna. Ƙamshin indomie ɗin ce kawai bana so.”
       Ganin yay shiru yana kallonta ta marairaice masa fuska da faɗin, “ALLAH da gaske nake ni lafiyata ƙalau”.
        “Shike nan naji, basai kin min kuka ba muje”.
    Yay maganar yana kama hannunta suka fita. Wajen dining ɗin suka koma ta zuba masa kunun ta miƙa masa.
     “ALLAH yay miki albarka”.
Ya faɗa a hankali yana kallonta. Zama tayi itama a kujerar kusa da shi ta saka kanta a kafaɗarsa ta amsa da “Amin mijina”.........✍️

    Ehem-ehem 🤣. Nace nayi shiru ko nayi magana🤯😂.180



........Ta tabbata dai Sille ya makance, dan kuwa likitoci sun tabbatar da jinkirin kwanakin da aka samu batare da kawoshi asibitin ba ƙasa cike da idanun sun lalace. Kuka sosai Mabera ya dinga yi, dan shi an masa maganin nasa ciwon

191 / 213

Chapters