Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
“To kinga laifina ne Basariyya, ko so kike nazo inda kike mijinki da nawa mijin su ɗauka da saka hannuna a cikin taɓargazarki na zubar da cikin yarinya gata can rai a hannun ALLAH a asibiti. To lalala wlhy ni yanzu nasan ciwon kaina. Ke ni bama wannan ba, nace miki ina buƙatar kuɗina amma najiki shiru babu wani bayani. To gaskiya kiyi ƙoƙarin daga nan zuwa kwana biyu dan zanyi amfani da su ne. Sannan ki ɗan rage min irin wannan kiran a waya bana son mijina ko yaƴana ma wani ga gani, abinda ya daman nima ya daman ji da taki damuwar”. Ƙit ta yanke kiranta. Tun daga wannan yanke kira har yanzu Hajiya Basariyya ta gagara dawowa dai-dai. Mamaki da ruɗani sun saka rayuwarta a gaba..
Washe gari akai addu'ar uku. Dan haka kowa ya fara shirin tattarawa domin wucewa. Har ita Sabuwar duk da bataso haka ba Baba yace ta tattara ta koma gidanta tai jiyya. Suma dangin su kaf kowa ya kama gabansa, sai iya su ƴan gida kawai suka rage. Bayan sallar azhar sai ga ƴan sanda sun doka sallama. A lokacin Daddy da Yazeed sun tafi Abuja domin yoma ahalin Darma jaje. Da yake so suke suje su dawo a ranar shiyyasa ana yin addu'a suka tafi harda Baban su Hajiya Yaya. Su Ammie kuma sai gobe idan ALLAH ya kaimu zasu tafi dan su Shahidah ma suna anan Kadunar da su akayi addu'an uku.
Kowa na sashensa sai ihun kuka da kururuwar Hajiya Basariyya suka dinga jiyowa. Babu shiri suka shiga fitowa, mi zasu gani wai ƴan sanda sunzo kama Hajiya Basariyya. A kammi? Idan sunzo office zata ji. Iya ƙoƙari su Ammie sunyi amma basu sauraresu ba. Haka aka wuce da Hajiya Basariyya tana kuka. Hajiya Yaya ta ɗaga waya tai kiran Daddy, amma sai cayay miye nashi shi kuma. Ta daina ma kiransa akan wata Basariyya shi yana cikin mutane. Suma in zasu kwantar da hankalinsu suyi sabgar gabansu su kwantar. Amma har wanda ya sake kiranshi. Daga haka ya yanke wayarsa bai sake neman kowa ba kuma, suma kuma suna tsoron sake kiransa, sai suka zauna jigun-jigun kamar an sake sabuwar mutuwa a gidan.......✍️
Hummm ALLAH yasa muyi ƙyaƙyƙyawan ƙarshe 😭🙏173
.........Da ga gidan Hajiya Turai asibiti su AA suka wuce. Sun sami su Daddy da Yazeed sai Baban Sageer da Baban Hajiya Yaya. Sun gaisa tare da yima juna gaisuwar waɗan da aka rasa. Suka kuma jajanta musu abinda ya faru. Daddy yace, “Ai daga can gidan naku muke ance kunje gaisuwa, shine mukace bari mu duba su Alhaji sai mu koma sannan kun dawo. ALLAH ya kiyaye gaba. Yay mana maganin wannan azzalumin mutumi. Gashi har yanzu jami'an tsaro basu kamashi ba. ”
Babban Yaya ya ce, “Basu so kamashin ba dai. Tunda sun tabbatar yana cikin jejin bai fita ba har kamashi zai zama abin wahala. Wannan ƙasar tamu kawai sai Alhamdullah, tsatsa tama mutanenmu yawa a zukata ne, ba nasaman ba, ba naƙasan ba, kowa da tashi illar”.
“Wannan haka yake Fadeel, ALLAH dai yay mana maganin waɗan nan abubuwa.”
Suna amsawa da Amin dai-dai Doctor na fitowa daga ɗakin da Oum take. Fuskarsa cike da murmushi yana kallon su AA ya ce, “Alhamdullah Hajiya ta farka”.
A tare suka kalla ƙofar, sai kuma suka zabura zuwa ɗakin gaba ɗaya. Abbu dake ɗan nesa da su basu ma ganshi ba hawaye suka cika masa idanu. Sosai yake jinjina ƙarfin ikon ALLAH da yardarsa akan wannan soyayya dake tsakanin Fatemansa da yaran nan. Soyayya ce ziryan irin ta uwa da ƴayanta. Itama tana farkawa su ta fara ambata tun ɗazun, sai kuma ta sake komawa barci sai yanzu kuma ta ƙara farkawa...
A cikin ɗaki gaba ɗaya su AA sun zagaye Oum. Har rige-rigen tambayarta suke mike mata ciwo yanzu? Ya take jin jikinta? Su kira mata Doctor?.
A hankali Oum ta haɗiye hawayen da suka cika mata idanu, tare da sakin murmushin ƙarfin hali ta kamo hannun Yaya Fawzan dake kusa da ita, ta miƙawa Babban Yaya hannu shima sannan ta riƙo na AA daya zuba mata ido kawai yana kallon ta. Kallonsu take dukkansu fuskarta da murmushin ƙarfin hali, sai kuma ta motsa lips da ƙyar ta furta, “Alhamdullah! Everything is going to be fine, my children” tai maganar tana yunƙurawa zata tashi, kamata sukai a tare suka zaunar da ita, suka daga gadon tare da sanya mata pillow a baya ta jingina. Ƙara binsu tai da kallo sai kuma takai ɗayan hannunta duk ta shafa fuskokinsu, AA ne ƙarshe, ta ƙureshi da ido ganin yanda idanunsa suka canja launi sai taja masa hanci kaɗan tana faɗin, “Waya taɓa min Auta dan anga bana kusa?”.
Kauda kai gefe AA yay yana mai ɗauke hawayen da suka taru masa a gefen ido, sai kuma ya zame a hankali yasa kansa a kafaɗar Oum ɗin ya lumshe idanunsa. Harararsa Yaya Fawzan ya ɗanyi da faɗin, “Kaifa ji kake kamar kai ɗaya keda Oum, yaƴanka suyi shagwaɓa kai kayi an girma ba'asan an girma ba naga dai Lilly ce Autar gidan”.
Idanu AA ya buɗe shima ya rama hararar da faɗin, “Kai kuma kana kishi dani, to nan gani nan bari ɗumamen mayya kai da Lillyn taka babu yanda kuka iya dani”.
“Oh haka kace? Nasan maganinka bari Abah ya tashi shima nasan maganinka, yaji zan saka Lilly tayi sai kazo ka duƙa ka gaisheni kayi biko matsayina na surukinka”.
“Oum kin ganshi ko”.
AA ya faɗa yana kallon Oum kamar zai yi kuka. Dariya Sosai Babban Yaya ya fashe da ita, itama Oum sai ta shiga taya shi tana riƙo hannun AA. Ta ce, “Auta ƙyaleshi kaji, idan yasa ƙanwarsa tayi yaji kaima basai ka saka taka ƙanwar tayo yaji ba har sai yazo ya maka biyayya sannan ka bashi”.
“Yeass! Oum haka ne ma”.
AA ya faɗa yana ma Yaya Fawzan gwalo. Rankwashi ya kai masa a kai, Oum ta kare tana faɗin, “Haba Yaya Fawzan ko mutuwa ai tana kunyar idon mahaifi, a gaban uwarsa”.
“Oum ki daina tausayin yaron nan, jiya da yake baƙya kusa biyayya ya dinga min, amma yanzu kinga rashin kunya ta gashi.”
Kafin Oum ta bama Yaya Fawzan amsa babban Yaya ya zauna yana faɗin, “To ya isa abar min mama ta huta haka, ku ajiye rigimarku idan Abah ya tashi kwa ƙarasa masa. Oum yi brush sai a haɗa tea.”
Abin sha'awa da birgewa a tare suka taimaka mata tai brush ɗin, Yaya Fawzan na tausa mata ƙafafunta Babban Yaya na bata Tea ɗin da AA ya haɗo. A haka Nurse da RK suka shigo. Fuskarsa da murmushi yana danne hawayen da suka cika masa ido yace, “A'a kaga ƴar gatan yaranta. Wato kunzo kun zagayeta irin ko ƙuda ɗin nan karya taɓa muku ita ko? To kuzo nan nima ku nema tabarrakina”.
A tare suka hararesa yau har babban Yaya, sai abin kuma ya basu dariya suka shigayi a tare. Nurse ɗin kam sai kallonsu take cike da sha'awa da birgewa. A haka RK ya ɗan yiyyima Oum tambayoyi suna wasa da dariya. Bayan Oum taci abinci an bata magani su Daddy dake shirin wucewa suka shigo suka dubata. Tace ma Daddy ina ƙanwarta. Haƙuri Daddy ya bata akan in sha ALLAHU gobe zata ganta itama. Oum tai murmushi tace ba komai. Sun ɗan jima a ɗakin harda Abbu sai kuma gasu Maanal sun iso da abinci ita da Ameerah da Najma. Yaya Fawzan yace ina Nibras, dan su kaɗai akace su zo anjima su Umma sai suzo.
Ganin yanda ya tsare Najma da ido alamar ita yake jira ta bashi amsa ta ce, “Zata zo tayi baƙi ne ƙawayenta sunzo gaisuwa?”.
“Bakinta sunfi mahaifiyata dake kwance a asibiti kenan?”.
Ganin yanda ya fusata Oum tai gyaran murya, sai ta basar da zancen ta hanyar fara tsokanar su Maanal wai wane abin daɗi suka kawo mata. Da wannan suka saki jikinsu suka zagayeta suma. Gaba ɗaya sai farin ciki ya mamaye Oum taji dukkan damuwarta ma babu ita. Da su Daddy zasu wuce Maanal ta fita sukai sallama, har wajen mota ta rakasu tare da su AA bayan sun sake leƙawa sun duba Abah da har yanzu ba'a barin kowa shiga inda yake. Hakama Mamy, sai dai su AA sun doje a ƙofar ɗaki sunƙi shiga inda Mamyn take. Abun sai ya tsayama Maanal a zuciya amma dai batace komai ba suka shiga itama Saheeba suka dubata suka mata gaisuwa. Sai aikin hawaye take kawai ita da Nuratu dake tare da ita......
_________★
Koda su Daddy suka koma gida ƙiri da muzu yaƙi maida hankali akan batun Hajiya Basariyya. Ammie ce da shi yau ɗin, ta tasashi da naci da magiya amma yay mata shiru. Da yaga zata takura masa sai yace taje sashenta bai buƙatar taya kwanan. Ƙin tafiya tai, ta koma gefe ta ɓata fuska, shima yana gama shan tea ɗin daya saka ta kawo masa yaje bayi yayi brush yazo ya haye gado ya kwanta. Haushi ya sake kama Ammie. Cikin rawar murya zatai masa kuka ta ce, “Amma Daddyn Hamee.....”
“Asia! ALLAH ranki zai ɓaci. Nace ki ƙyakeni! Ki ƙyaleni mana. Ko dolene sai na shiga abinda bai shafeni ba. Matar nan bata da wani haƙƙi a kaina yanzu ko dole sai kin tilasta min ne”.
Sosai gaban Ammie ya faɗi, ta ce, “Wane irin magana ce wannan Daddyn Hameed. Taya zakace matarka bata da hakki a kanka?”.
Harara Daddy ya zuba mata, cike da takaici yace, “Tunda so kike kiji bara na gaya miki na saketa, saki uku kuma. Karki sake min maganarta, idan ba haka ba kuma wlhy zaki bar ɗakin nan shirme kawai!”.
Ba ƙaramin suman zaune Ammie tayi ba, sai kawai hawaye suka shiga rige-rigen zubo mata. Tabbas mutuwar aure kota maƙiyinka ce bata da daɗi wlhy. Tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta miƙe ta fita tabar masa ɗakin. Karan farko da taji kamar ta kama Daddy da duka. Wane irin yanke ɗanyen hukunci ne haka. Koba komai Basariyya ai uwar ƴayansa ce, ƴaƴan ma mata da suke zaune tare da su babu aure. A tunaninsa hakan masalaha ce ko shuka sabuwar cakwakiya a gidansa. Dan duk yanda yake tunanin zasu iya riƙema Basariyya ƴaƴa wlhy bazai yiyu ba tinda yaran dai rainonta ne, komai mugun halin mahaifiyarsu kuma bazasu so su sama da son da suke mata ba...
Washe gari itama Hajiya Yaya ta sameshi da zancen Hajiya Basariyya saboda ganin yanda damuwa ta fara bayyana a fuskokin ƴaƴanta. Ta saka Yazeed yaje ya bincika station har ya gano inda Hajiya Basariyya take. Koda yay ƙoƙarin yin belin ta sukace bazasu bada ita ba. Dan ana zargin ta ne da yunƙurin kashe rai. Hankalin Yazeed a tashe yazo ya sanar ma Hajiya Yaya, itama ta kira Ammie. Sosai al'amarin ya girgizasu. Yazeed yace shifa yana zargin Sageer ne yasa aka kama Hajiya Basariyya kuma da haɗin kan Daddy. Nan ma zancen sai ya ƙara basu mamaki, Hajiya Yaya tace bara ta samu Daddy ɗin to taji ta bakinsa. Shine tazo itama ta samu kalar tujarar da yayma Ammie a daren jiya. Haka ta fita ta barshi.
Jin abinda yace shima Yazeed yace bari to ya sameshi shi. Yana shigowa Daddy ya dakatar da shi. Dan a harzuƙe ya ce masa, “Dakata anan, idan kaima iyayen naka ne suka turoka akan batun Basariyya ALLAH tak kace da ni sai ranka yafi nasu ɓaci. Dan haka ka rufama kanka asiri ka koma inda ka fito tun muna mutunta juna”.
Jiki a sanyaye Yazeed ya fita, koda ya koma inda su Hajiya Yaya suke duk abinda ya faru ya sanar musu. Hajiya Yaya ta dafe kai da faɗin, “Matsalata da Alhaji kenan Ammien yara, shi idan yay fushi babu mai iya tankwarashi. Ya kamata ya duba kodan yaran nan ai”.
Kafin Ammie tace wani abu Yazeed ya ce,.........✍️174
.......“Mammah abunne fa da ciwo, itama tayi ganganci wlhy, kuma taso zuciyarta, yanzu da yarinyar nan ta rasa ranta fa. Ko taje ta haɗu da wata matsalar. Doctor ɗin fa yace allurar da sukai mata muguwar allura ce wlhy, kuma da ba'ai saurin kawota asibiti ba komai zai iya faruwa da ita. A yanzu haka suna tunanin ta ɗan taɓa mata brain ma, shi kansa cikin duk da bai zube ba sunce da wahala ya zaman ba'a taɓa lafiyarsa ba. Shiyyasa ma sai a yau zasu sallami Huznahr. Wanne irin son zuciya ne wannan ace har ɗanka daka haifa a cikinka baka bari ba. Idan tace bata son haɗa zuri'a da Sageer sai ta tuna shi jinin Sageer ɗin a jikin ƴarta yake, kuma cikin nan ya fara girma, ai gara ta bari idan yazo duniya sai ta kashe shi kinga tasan dai jinin Sageer ɗin ta cutar”.
Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un su Ammie suke maimaitawa kawai, amma sun kasa ma iya cewa komai dan su kansu al'amarin Hajiya Basariyya ya gama kaisu maƙurar mamaki a wannan gaɓar.....
_______★
Alhamdullahi anan Abuja an sallami Oum itama yau da safe, dan ta matsa ma RK bata son zaman gadon asibitin. Gefe farin cikin da kowa ke son gani a fuskar ta musamman su Yaya Fawzan da komai suke mata inba abinda ya shafi shiga bayi ba ya sake bata nutsuwa. Baiwar ALLAH ana sallamarta Mamy ta fara cewa a kaita ta gani bayan Abah da ta leƙa ta glass dan shi kam ba'a barin shiga inda yake har yau ɗin nan. Shiru su AA sukayi cirko-cirko kowa yaƙi magana kuma yaƙi motsawa. Oum ta zuba musu ido kawai, sai kuma ta koma tana kallon RK cike da tuhuma. Shima dai fuskarsa ta canja amma bai ce komai ba saboda su Babban Yaya.
“Magana fa nake da ku, nace a rakani inda ƴar uwata take kunyi shiru kamar gunkinaye.”
Wayancewa Babban Yaya yayi ya zaro waya zai kai kunne wai ana kiranshi. Yana ɗaga ƙafa zai bar wajen a dake Oum ta ce, “Fadeel!”.
Cak ya tsaya yana matse idanu, sai kuma ya juyo a hankali ya kalla Oum ɗin. Ganin yanda tai kicin-kicin da fuska ya duƙar da kai ƙasa yay shiru. Sam babu wasa a tattare da ita ta ce, “Mi kuke nufi? Bakuma san ɗakin da aka kwantar da ita ba kenan ko mi?”.
Rai a ɓace Yaya Fawzan ya buɗe baki zai yi magana. Bubb Oum ta buge bakin nasa kaɗan, sannan ta shiga nunasu da faɗin, “Duk wanda ya sake magana a cikin ku sai na fallama fuskarsa mari. Yau she har zukatanku sukai irin wannan bushewar akan bijirema abinda yake hakki a kanku ya kuma dace kuyi. Ni zakuma haka ƴar uwata na kwance cikin matsannacin hali ku kasa zuwa ku dubata? Shike nan nagode, nagode sosai Fadeel tunda ka zama babban banza. Rafeeq wuce ka raka ni”.
Ba ƙaramin tashi hankalinsu AA yay da ganin ɓacin ran Oum ba. Cikin sauri duk suka bita suna bata haƙuri. Amma ko kallon su batayi ba. Su Baba Sardauna sai murmushi suke zukatansu na ƙara jin ƙaunar gudan jinin nasu. Ai duk ahalin Darma basa maida sharri da sharri sai alkairi. Wannan mutuntawarsu ce. Har ɗakin da Mamy take kwance su Babban Yaya suka shiga a karo na farko, Aunty ce tare da ita, dan tun jiya da akai addu'ar uku ta dawo asibitin. Suma su Baban Nuratu sun wuce Kano dan ba wani karɓar gaisuwan ake anan Abujar ba. Amma Nuratu na tare da Saheeba ita ke jiyyarta.
Farin ciki da kunya suka kama Aunty duk a lokaci ɗaya. Sai faman duƙar fa kai take tana ma Oum ya jiki. Sai da Oum ta ce, “Haba Aunty miye amfanin hakan, karfa ki manta kefa yayace a garemu”.
Sosai Aunty ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta shiga share hawayen dake kwarar mata. Itama Oum a karo na farko hawayen take yi data kalla Mamy. Tana kwance idonta biyu sai dai babu ido ɗaya sai ɗaya. Wanda Sille ya ya daka ya tsiyaye tas ya kuma zazzago waje sai da aka mata aiki aka maida shi, shine aka rufe shi da uban bandage. Hakan kuma sai ya saka fuskar kumbura gaba ɗaya ɗayan idon shama ya shige ciki sai kaɗan-kaɗan take iya ganin mutane da shi. Hakama hancinta ya kusa shanyewa a kumburin fuskar, lips ɗinta sun zama ƙatin-ƙatin babu ƙyawun gani. Ga ƙafa a naɗe itama da uban bandage. A kwanaki biyar kacal ta sake wani irin mugun rama a jiki ta tashin hankali da baƙi, sai ƙaton kai da ƙatuwar fuska da ƙafa itama data kumbura. Da rabin idon nata take kallon su Oum da su Babban Yaya. Ga ƴar sanda mace dake gadinta har yanzu da handcuffs a hannunta.
Sharrr hawaye suke rige-rigen sakkowa ta idon ɗaya suna zirara mata a cikin kunne. Tunda aka baro jejin nan da ita sai yau ne take ganin ƴaƴan data ɓata tsahon shekarunta na ƙuruciya akan fafutukar mallakarsu da mahaifinsu. Gasu dai zagaye da Fateema maƙiyayyarta suna take mata baya like sarauniya da fadawanta. Yanda ko kallonta babu wanda yayi a cikinsu ya sake tabbatar mata tursasa musu akai zuwa dubata yanzun ma....
Gaishetan da Oum keyi yay mata wani irin duka a zuciya da ƙoƙarin riƙe mata numfashi. Ita kanta bata san irin tsanar da taima matar nan ba. Musamman a yanzu da suke wata gaɓa mai tabbatar mata da taci wannan wasan. Fateema taci wannan game ɗin kota yarda koma karta yarda. Duk gwagwarmaya da faɗi tashinta sun tashi a banza. A banzan da bata da sauran ƙarfi ko damar canjawa ko aiwatar da koda ƙaramin abune daga tarin plans ɗinta. Babban tashin hankalinta jin Abah