AJIYA A DUHU BOOK 1 & 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   199 / 213

594K to 597K   out of 636.6K words

“Ni dai na gaji sai dai kayi min”.
      Lips ɗinta ya sumbata ƙasa-ƙasa da yanayin maganar nan tashi kamar an masa dole yace, “An gama my Everbloom”.
       “Thanks you my bestie”.
   Tare sukai wankan, ita tana da kayan barci shiko babu, sai kawai yay canja da wata bathrobe bayan ya cire wadda ya fito wanka da ita gudun mura. Ƙofar suka sakama key, ya ɗauka Naufal dake barcinsa ƙaƙas ya maida kan sofa bayan ya sake buɗe masa ita kamar gado, ya lulkuɓa masa blanket su kuma suka haye gado. Can cikin barci Oum tazo dan ta duba Maanal amma tana taɓa ƙofar yaji a rufe. Mamaki ya kamata, amma sai ta shiga kiranta a hankali. Cikin barci AA ya jita, amma Maanal tayi nisa a barci, sai kawai yay murmushi, a ransa yace Oum dama kin kwantar da hankalinki tana tare da GARKUWA TA. A zahiri kam luf yayi har Oum data fahimci barci Maanal take mai nauyi ta juya ta koma.
       Ana kiran sallar farko AA ya tashi, cike da lallaɓawa ya raba jikinsa dana Maanal. Bayi ya shiga ya watsa ruwa yay alwala ya fito ya maida kayansa, cike da sanɗa ya fita a ɗakin da gidan ma gaba ɗaya. Koda Maanal ta farka da asuba taga bashi nan mamaki ya kamata, amma ganin agogon sa ya sakata sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ga Oum ta shigo tashinta, ganin Naufal a sofa ya bama Oum mamaki, dan tasan Maanal bazata iya maidoshi nan ɗin ba. Sai kuma yanda alamu suka nuna gadon kamar mutum biyu suka kwanta. Can idonta ya sauka akan agogon AA. Sai kawai ta shiga tunanin yaya akai haka? Amma dai batace komai ba ta juya ta fita.
      Koda ta koma nasu ɗakin bayan Abah ya dawo daga sallar asuba sai tai magana. Murmushi yayi da faɗin, “Oh dama kina tunanin Ajwaad zai tafin ne da gaske. Ai ni tunda na hawo saman nan ma naji ƙamshin turarensa nasan bai bar gidan ba”.
      Dariya ma abin ya bama Oum ita kam. Sai kawai ta girgiza kai. Can wajen takwas sai ga AA kamar bashi ba yazo gidan shi a dole lokacin ne yazo. Bayan sun gaisa da Oum da Abah da suma suka basar kamar basu san a gidan ya kwana ba sukace zasu fita ɗan motsa jiki. Suna ficewa ya haura sama. Ya samu Maanal kawai na barci Naufal ya wuce makaranta. Zama yay a kusa da ita yana murmushi, sai kuma ya ranƙwafo a kanta ya sumbaci lips da idannunta. A hankali ta buɗe idanun tana kallon sa, suka sakarma juna murmushi. Cike da raɗa ya ce, “Ƙyaƙyƙyawata yunwa fa?”.
     Baki ta ɗan tura masa ƙasa-ƙasa ta ce, “Bana ji”.
     “Kin tabbatar?”.
  Kanta ta jinjina masa, sai kuma can tace, “Da dai zan samu dafaffen ƙwai naci da yaji ko miyan attarugu”.
        “An gama Bestyn Besty. Bani 30mint kawai in sha ALLAHU yanzu zakiga kwai ke da my unborn”. Yay maganar yana sumbatarta ya miƙe ya fita. Ta bishi da kallo tana lumshe idanunta. Kamar wasa barci mai shegen daɗi ya sake fara figarta, sai kuma kamar wadda aka tsikara ta farka a firgice sakamakon wani irin juyawa da ɗan cikinta yayi, sai kuma bayanta ya riƙe gam, hakama mararta ta ƙulle. Sai kawai jikinta ya hau rawa..........✍️

        😂😂Manyan Mata an shiga halin ni ƴasu🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🤭193


........Tsaf AA ya haɗama Maanal dafaffen ƙwan daya cire bayan da miyan attaruhun yasa mata albasa sosai suka haɗe jikinsu sannan ya juye plate. Daga shi har su Yaya Fawzan sun iya girki, yanzu ne dai kawai basu damu dayi ba sai sun so. Coffee ya ɗan haɗama kansa shima sannan yasa a tray yay sama. Dai-dai lokacin da ciwon ke ɗan lafa mata, sai dai kallo ɗaya yay mata ya fahimci bata cikin ƙoshin lafiya. Tray ɗin ya ajiye idanunsa a kanta ya ce, “Babie what happened?”.
          Maanal ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya tana danne ɗan sauran abinda take ji idanunta da suka kaɗe akan tray ɗin daya ajiye ta ce, “Ba komai. Ka bani naci”.
        Zama yay kusa da ita, dan gaba ɗaya bai yarda da abinda ta gaya masa ba, sai kallonta yake yi da lallaleƙa jikinta. Ta tura baki gaba da katseshi ta hanyar faɗin, “Besty yunwa fa nake ji”.
      Ajiyar zuciya yayi kaɗan, “Okay tashi muje kiyi brush”.
   Batai musu ba ya taimaka mata suka muƙe tare, haka ya rakata tai brush ɗin sai kuma tace kawai ya mata wanka da ruwa masu ɗumi. A tunaninta in akai wankan zataji sauƙin abinda take ji a jikinta. Haka yay mata wankan suka fito, ya duba mata simple doguwar riga irin na Egypt ɗin nan masu babban mayafi dan su take sakawa yanzun. A maimakon mayafin ya saka mata hula sannan ta zauna cin kwan. Shi kuma yana shan coffee ɗinsa amma idanunsa ƙyam a kanta. Ko yaya ta yamutsa fuska sai yace minene?. Sai ta girgiza masa kai ta cigaba da cin kwan cikin dauriya. Taci ya kai shida tafa kasa daurewa saboda exactly irin ciwon ɗazu dake taso mata. Plate ɗin ta miƙa masa jikinta na rawa, zata kai kwance sai kuma ta kasa dan bayan ta ya riƙe. Ai baima san ya wancakalar da plate ɗin ƙwan da kofin coffee ɗin hannunsa yayo kanta ba da kiran sunanta. Dai-dai nan Oum data iso ƙofar har ta kai hannu zatai knocking taji yanda AA ɗin ke kiran sunan Maanal ita kuma ta saka masa kuka tana kiran “Besty bayana, ƙafata, marana ya riƙe”.
     Ai kawai shigowa Oum tayi, cikin tashin hankali ta iso inda suke, kallo ɗaya ta fahimci haihuwa ce. “Auta ɗagata muje maza-maza haihuwa ce wannan”.
         Ko musu baiyi ba ya ɗaga Maanal gaba ɗaya suka fito, Abah na falo ya miƙe da sauri yana tambayar lafiya? AA bai iya ya amsa masa ba sai Oum dake biye da su da kayan haihuwa tace, “Gadanga haihuwa ce”.
      “Suhanallahi”. Abah ya faɗa yana binsu a baya shima. Sai waya a hannunsa yana ƙoƙarin kiran asibiti. Dole a falon ƙasa AA ya ajiye Maanal, sai dai tana jikinsa tana kuka. 20min kawai sai ga Ambulance tazo ɗaukarsu.......

________★

      Kamar yanda Kawu Manu ya faɗa hakan ce ta faru, washe gari maƙota da abokan arziƙin iya suka nufi ƙauyen su Alhaji Balala yin jere. Dan tunda sassafe ya aiko akori kurarsa ta ɗiba kayan. Sun wuce babu jimawa Yayan Hajiya Basariyya ya iso garin, tare yake da wani kawunsu shima ta ɓangaren mahaifiyarsu. Shima dai ba mutum bane mai wasa, amma a zuciyarsa yaji tausayin Basariyya. Dan rayuwa a ƙauye bayan ba'anan aka haifeta ba, sannan ta auri mai kuɗi irin Chalawa har ta haifi yara duk sun zama manya zuwa yanzu da shekarunta ace tazo wannan ƙauyen tai aure da gidaje basufi goma sha ba abune bamai sauƙi ba gaskiya. To amma hakan shine kawai punishment ɗin da zasuma Basariyya ta dawo cikin hankalinta ta kuma fahimci micece ainahin rayuwar kanta. Tunda da yarinyarta datai yunƙurin zubarma ciki ta rasa ranta ai daba wannan maganar akeyi ba kuma yanzu ko. Gwara ta ɗanɗana idan da rabo gaba sai ta koma gidan ƴaƴanta tunda saki uku ne dama.
       Bayan sun gaisa dasu iya ansha hirar bayan rabuwa tsakanin Kawu Manu da Uncle Faruk akai kiran Hajiya Basariyya. Kallo ɗaya yayanta yaji zuciyarsa tayi rauni, sai dai dole ya dake abinsa dan Basariyya bata buƙatar a nuna mata tausayawa. Tana da busashiyar zuciya kamar ba mace ba. A yanzun ma da tazo da farko ƙin gaishesu tayi, sai da Uncle Faruk yay mata tsawa sannan. Yayanta kuma ya shiga zaginta, dan yanda take musu raini sosai a ciki. Tuni suka ajiye batun tausayinta a gefe suka mata tatas, tare da sharruɗa masu ƙaifi akan wannan auren. Ta inda suke shiga bata nan suke fita ba. Sai da suka tabbatar sun razanata sannan suka sallameta, sun kuma sanar mata anan zasu kwana su da kansu zasu kaita ɗakin mijin ma kawai, dan sun fahimci bazata taɓa tanƙwaruwa ba..

    A can kuwa ƴan jere basu sami tarbar mutuntawa ba a wajen matan Alhaji Balala. Tun jiya ya sanar musu ya ƙara aure, ya kuma tabbatar musu duk wadda ta kawo masa hauka zai saita mata layi ta tafi gidansu ya cike gurbinta da wata matar. Shi dama haka yake, indai zai ƙara aure babu batun tausasawa a tsatinsa. Saboda yanda yake jin alfaharin yana da kuɗi matan bazasu iya barinsa ba.
     Hakan ne kuwa, dan suma bazasu iya tafiya ko'ina ba. Dan kaf ƙauyen sune matan mai kuɗi masu ci su ƙoshi kullum duk da kuwa ɗumamen tuwo ne abincin. Sutura kuwa sai shekara-shakara kuma roba-roba atamfa ce da takalmin roba na danƙo shima. Da salla kuma za'a yanka musu akuya ko tunkiya matsayin naman salla. Suyi tuwo miyar taushe. Idan kuma ALLAH ya jarabci dabbobinsa da ciwo baya sayarwa zai yanka a ci a gida. Shiyyasa wani lokacin da biyu yaran ke buge dabbarsa dan a yanka musu. Sai dai kuma idan ya ganoka ka shiga ukunka.
      Tunda sassafe ya saka yaransa gaba suka gyara ɗakin da Hajiya Basariyya zata zauna suka hau shafen farar ƙasa, harta ƙofar ɗaki ma aka yayyarfa mata kamar dai yanda akema ɗakin amarya a ƙauye. Lokacin da ƴan jere ke isowa har sun kammala. Dan haka babu ɓata lokaci suka fara aikinsu. Sai dai gadonta na gidan Daddy ne kawai ya shiga da wadrobe sai mirror. Amma ko bedside drawers basu samu waje ba ɗakin yayi kaɗan. Dole haka aka tattara sauran kayan aka jibge mata a ƙofar ɗakin, sai kuma ga kishiyoyin nata na leƙen ɗaki daga nesa. Dan basu gaɓa ganin irin wannan kayan ɗaki ba haka. Su dai ƴan jere bayan sun gama suka zauna sukaci taliya da mai da yajin da kanwar Alhaji Balala ta dafa musu Karime. Harda kazarsu guda sukutum. Sai da sukaci sukai nak sannan suka kullo ɗaki suka taho sai kuma gobe tarewa......

_________★
SAUDIA

      Karɓar gaggawa akama su Maanal a asibiti, abinka da babu wasa komai ana bashi haƙƙinsa yanda ya dace babu ɓata lokaci aka hau yi mata abinda ya dace. Sai dai ga haihuwa gadan-gadan amma ta kasa yi da kanta. Dole likitar ta shiga binciken minene matsalar. Babu wani jimawa ta fahimci yarinyar bazata iya haihuwa da kanta bane ba dalilin yanayin jikinta ƙugu yayi jaɗan, bayan kuma ga komai matsa ALLAH a zahiri. Dole suyi mata aiki da gaggawa. Babu wani ɓata lokaci ta fito tanama su Abah bayani. Dan zuwa lokacin suma su Babban Yaya sun iso asibitin duka dasu Najma. 
       Sun gamsu da bayanin duk da akai musun, dan haka babu ɓata lokacin AA ya saka hannu ga dukkan abinda ake buƙata. Su kuma suka shiga da ita cs na gaggawa, dan tana a matakin buƙatar taimakon gaggawar.

  A Nigeria babu wanda yasan halin da ake ciki, dan basu kira kowa ba sai suketa faman kai-kawo da addu'oi, dole Babban Yaya yaja AA a jikinsa ya rungume. Dan kallo ɗaya zakai masa ka fahimci yana cikin wani matsannacin yanayi. Jarumtarsa da iya kame damuwa ce kawai ta ɓoye komai. Kasancewar safiya ce babu wani uziri daya saka ɗayansu barin ƙofar ɗakin. Haka suka kasance zaune idanunsu a ƙofa tsahon awanni. Zuwa can sai ga wata baƙar fata Nurse daga ganinta kaga ƴar Nigeria kodan fetalin dake fuskarta ta fito daga ɗakin. A tare duk suka miƙe suna tambayarta yaya ake ciki. Murmushin kwantar musu da hankali tayi cikin yaren hausarta daya fara canja salo ta ce, “Alhamdullahi, komai lafiya, everything is fine, an ciro baby lafiya, yanzu muna buƙatar jini ne, idan kun amince a ɗauka na asibiti....”
     Da sauri AA yace, “No! Ba buƙata. Muje a ɗiba nawa”.
    Murmushi Nurse ɗin tayi tana kallon AA ɗin ƙasa-ƙasa. Gaskiya zaratan mazajen uku sun tafi da imaninta. Musamman wannan mai duhun fatar da kallo ɗaya zai tabbatar maka da ingarman namiji ne a tsayensa. Duk da dai suma sauran masha ALLAH babu rago. Itace ta jagorancesu zuwa wajen ɗibar jinin. Dan Babban Yaya da Yaya Fawzan basu bar AA ya tafi shi kaɗai ba. Kusan mintuna talatin da wucewar tasu wata macen baturiya ta fito da jariri a hannu cikin kyakkyawan fari ƙar ɗin showal da kallo guda idan kai masa kasan zai yi bala'in laushi. A tare su Oum suka miƙe har Abah, sai kuma ga wata ta fito itama, sai dai ita ɗin balarabiya ce. Itama ɗauke da jariri nannaɗe a sky blue na exactly irin wancan farin. Gaba ɗaya sai aka koma kallon kallo tsakanin su Abah da su Ameerah. Su kalla juna su kalla matan da suka jeru suna kallonsu da murmushi. Oum ce tai ƙarfin halin ƙarasowa gabansu, ta leƙa na farko sannan ta leƙa na biyu. Jarirai ne kuwa guda biyu masu tsannanin kammani da juna, kama kuma irin tata da yaranta da Abah, a taƙaice dai suma gida suka kwaso, wato kamanni Darma Family. Ai da sauri Oum ta juya tana kallon Abah, ta ce, “Wlhy Gadanga da gaske ƴan biyu”.
       Da wani irin sauri su Najma suka ƙaraso, hakama Abah. Ma'aikatan asibitin dake ɗauke da yaran suna dariya sukace, “Congratulations an ciro twin's duk maza. Suna cikin ƙoshin lafiya kuma, hakama mamansu Alhmdllh babu wata damuwa a tare da ita sai cs da akai mata, in sha ALLAHU nan da kwanaki kaɗan kuma zata koma normal”.
        Farin ciki ya saka Abah da Oum summa kasa magana, sai Oum dake hawaye, Abah kuma ya koma gefe yay sujidar shukur kamar yanda yayi a lokacin da akai masa albishir da samuwar cikin. Yau dai alƙawarin ALLAH ya cika ga jinin Ajwaad ɗinsa gauraye dana Maanal ɗinsa waje guda kamar yanda ya daɗe yana fata da addu'a a rayuwarsa........✍️194


.......Sageer na fitowa a wanka shiri yayi ya barma Huznah gidan batare da ko kallonta yayi ba. Dan wlhy gaba ɗaya ransa a jagule yake, zuciyarsa a ƙuntace take. Yana buƙatar bama gidan iska ya samu ya huce idan ba haka ba komai zai iya faruwa, ji yake kamar ya mammari Huznah koma ya daketa, sai dai zuciyarsa na hanashi. Ace matarka ta aure da har rabo ya ratsa na haihuwa tana rayuwa da kai amma zuciyarta na akan wani can da baima san tana yi ba. Duk wani ƙoƙari yayi domin ganin ya karkato da hankalin Huznah a kansa sun taru sun rufawa juna asiri ashe a banza ne. To abanza mana tunda ta kasa ajiye abinda ya zama kabari a rayuwarta. Idan yace ma ya zargi AA Darma ko yaji zafinsa shi minene laifinsa tunda ko'a baya baice yana sonta ba, zuwa yanzu ma yana da tabbacin ya manta da wata Huznah a duniyarsa. Hakafa lokacin da akai kidnapping su AA ɗin nan tunda ya ɗakkota daga Kaduna suka dawo Kano ta saka kanta a wani hali, shi duk zatonsa abinda mahaifiyarta ta aikata mata ne akan yunƙurin zubar da ciki ya sakata shiga yanayin, ashe-ashe damuwarta akan AA ne. Abinda yasa ma har ya tuna haka a yanzu yanda ta dinga maimaita masa zancen da tambayarsa yaya ake ciki? An saki su Maanal? Suna cikin ƙoshin lafiya kuwa?. Duk da ya ɗan yi mamakin yanda ta damu da al'amarin Maanal ɗin tunda yasan ba sonta take ba sai yay tunanin ai yanzu Huznahr ta canja ne, ga yanda Ammie ta dinga kai-kawo akan nata al'amarin maybe shiyyasa itama yanzu ta damu da halin da Maanal ta shiga. Ashe-ashe nata tunanin ita daban ne. Kofa motar daya saya bata nuna farin ciki ba kamar yanda ta nuna damuwa akan kidnapping ɗin nan.....
        “Sageer wai kana lafiya kuwa?”.
    Abokinsa da tun ɗazun yake magana amma babu alamar ya jisa saboda yanda yay zurfi a tunani ya faɗa yana zungurarsa. Firgigit Sageer ya dawo hayyacinsa, sai kuma ya sauke kakkauran numfashi tare da furzar da shi ya juya yana kallon abokin nashi. Shi da shi amanar juna ne, basa ɓoyema junansu komai na rayuwarsu sai abinda shari'a ta hanesu da bayyanarwa wato sirrin aurensu. In ma zasu bama juna shawara ta wannan ɓangaren sai dai cikin hikima da iya lafazi bawai kai tsaye ba. Dan ko akan zamantakewar sa da Huznah ɗin ya taka rawar gani sosai a kai da shawarwari. Sageer ya sake furzar da huci sannan ya ce, “Toufeeq akwai matsala ne wlhy?”.
        “Matsala tami kuma?”.
     “A gidana”.
“Gidanka kuma? Ai na zata mun wuce wannan matsayin komai ya wuce kuma itama Huznah ta kwantar da hankalinta yanzu tunda kayi wining game ɗin har ga Usman Fodio”.
       “Humm Toufeeq kenan, a zahiri ne nai wannan nasarar. Amma a zuciyar Huznah har yanzu bana ciki. Dan kuwa jiya da rana sanda nake cemaka zanje gida nakai mata naman nan karya lalace kawai na sameta cikin zurfin tunani.......” tsaff ya kwashe komai ya sanar masa. Mamaki sosai ya kama Toufeeq.
     “Kai amma Huznah bata ƙyauta ba, wannan ai rashin wayo ne kamar batai islamiyya ba dai. Koda yake wannan itace irin masifar dake yawo a gidajen aurenmu tsakanin mata a wannan zamanin. Ƙiri-ƙiri yarinya da igiyar auren wani a kanta harma da ƴaƴa tsakani sai kaga ta mutu a son wani dake waje. Imma tsohon saurayinta, in ma haɗuwar media bayan aure. Idan sun samu sakarkarun samarin mazan nasu sai kaga anata yaɗa fasadi ta hanyar waya da charting kai miji kana nan wasarere da baki kana ciyar da ƙatuwar banza kullum kana rana. Tun abun na tsayawa a wayar sai kaga sheɗan ya tunzurasu haɗuwa zina kuma ta shiga da aure. Shiyyasa wani lokacin wlhy bana ganin laifin mazan dake hana matansu yin harkar social media ɗin nan musamman masu rawar kai da son ƙarya. Dan wata acan take haɗuwa da lalatattun ƙawaye su sakata a group dake da maza sai mazan suna biyosu, idan wata

199 / 213

Chapters