Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
bataji mi yace ba dan irina ce ba turancin take ji ba. Manaal data fahimci Uwangale bata gane miyace ba a hankali ta riƙe hannun AA ɗin dake yunƙurin sake magana a fusace fiye da farko, sai ta kalla Uwangalen da ɗan murmushi a fuskarta tace, “Kije waje idan mun gama gaisawa sai ki dawo”.
Cike da tsantsar ladabin daya bama Mamy mamaki Uwangale harda duƙawa tace, “To to Hajiya, sannunku da zuwa sannunku, ALLAH dai ya raya mana ƴan biyu ya ƙara miki lafiya hajjaju uwar ɗakina. Hamshaƙiya balarabiya jinin girma da ƙyawun sura. Ai Alhaji ya more ƙwarai da gaske, dan ya samu hurulanin sa ta duniya kam”.
Ita Maanal ma abin na Uwangale dariya yaso bata, mata kamar zararriya ko haɗiyar yawu batayi wajen magana. Sai da ta fita harta rufe ƙofar sannan AA ya dubi Mamy a karo na farko, babu wasa a muryarsa ya ce, “Maanal ƙara gaisheta”.
Ajiyar zuciya Maanal ta ɗan sauke, cike da girmamawa ta sake gaishe da Mamy. Yanzu kam dolenta ai ta amsa, tare da tambayarta ya yaran?. Maanal tai murmushi kawai batace komai ba saboda kunya, ina ita ina amsawa uwar miji lafiyar yara. Ai kodai yayane Mamyn dai mahaifiya ce ko sunƙi ko sun so, baƙin halinta tsakaninta da UBANGIJIN ta ne da ƴaƴanta da mijinta su minene nasu. Sai lokacin AA ya gaishe da Mamyn shima, ta amsa tana share hawayen da shi yasan bana nadama bane ba ko damuwa. Na tsantsar takaici ne da mugun halin daya gama sallamawa da wahala mahaifiyarsu ta canja wlhy, sai dai wani ikon ALLAH kawai dan zuciyar Mamy ta riga ta kangare ta bushe UBANGIJI ne kaɗai ke iyawa da su. Wadda tai yunƙurin kashe musu uba mi kuma ya rage. Bata tambayesa yaran ba, dan haka a dake yace,........✍️200
........“Mamy ga jikokin ki nan, ki saka musu albarka tunda ALLAH ya rubuta zasu zo duniya su sameki a raye damu kammu”.
Harga ALLAH AA baiyi maganarsa da wata manufa ta raini ko izgili ko cin fuska ba. Amma sai Mamy ta fassara ta da wani abu daban har zuciyarta na kumfa a cikin ƙirjinta. Da ƙyar ta iya dannewa a taƙaice tace, “ALLAH ya raya”.
Komai AA baice ba, dan dama iya abinda yay tunanin ji kenan ya miƙe abinsa tare da kama hannun Maanal da mamakin duniya akan Mamy ke neman halakata. Wlhy tayi zato da tsammanin zuwa yanzu zuciyar Mamy tayi matuƙar laushi da rissina. Kai anya matarnar nan mutumce kuwa? Irin waɗan nan matan ne fa ake kira da ainahin rainon shaiɗan fa. Ace duk wannan abubuwan daka aikata suka fito fili ma duniya bama ƴaƴanka da zuri'arka kawai ba amma sam babu alamar sauyi ko nadama. Hu'um wasu dai kam tun a duniya kake shaidasu a cikin ƴan wuta wlhy....
Tunanin Maanal ya katse saboda ɗora mata Hassan da AA yayi a hannu, shi kuma ya ɗauki Hussain da har yanzu ke kuka. Tissue dake a Centre table na falon ya cira guda ɗaya ya goge hawayen Mamy dake a fuskar yaron har yanzu. A mamakinsu kamar wanda aka cirema wani bala'i sai yay shiru ya koma sauke ajiyar zuciya. AA ya rungumesa a jikinsa kamar yana magana da wani babba ya ce, “Oh Oh! Sweetheart, don't cry. We love you so much me and Mah-mah, alright? ALLAH yayi muku albarka, ya tsarkake ku manyan gobe”. Ya sumbaci yaron ya matsa ya sumbaci Hassan shima itama Maanal ɗin ya sumbaceta sannan ya kama hannunta suka fice. Gaba ɗaya sai Maanal taji babu daɗi, amma babu damar yin magana haka suka fice.....
_________★
A lokacin da nan Abuja suke cikin farin ciki da murnar samun ƙaruwa a Kaduna sabuwa ce ke cikin kuka da nadamar kufcewar komai. Dan kuwa al'amarin rikicin gida sai da ya kaisu zuwa kotu ita da wanda suka saya a hannun Mabera da kuma su Bakori suma da suka sayar. Bayan kaiwa da komawa na kusan watanni uku kenan a yau aka yanke hukunci bisa hujjoji masu ƙarfi. Gida dai da gaske ya suɓuce tunda mai shi ne ya sayar da hannunsa ya kuma basu takardun sa ga kuma saka hannunsa a jiki. Su Bakori da Hajiya Zahedah da suka amshi kuɗin mutane sukaci suma dole sukai amansu. Dan suna ji suna gani haka aka ɗaga gidansu aka sayar aka biya waɗan can. Wannan abu yay matuƙar fusata Bakori dama ga tsanar Hajiya Zahedah da yayi ya tattara nata kadarar kaf shima ya amshe yace a matsayin gidansa. Ya kuma ɗauki yaransa biyu da aka tabbatar sune nashi yabar garin Kaduna. Suko yara abinka da maza takaicin wulaƙanta rayuwarsu da uwarsu tayi ta haifesu ta hanyar zina da aurenta yasasu sakata a gaba da zagi da rashin mutunci, suma suka tattara yanasu-yanasu suka barta kuma sunce na har abada wlhy. To dama biyu sun riga sun zama ƴan samari, tunda har sun fara University. Ƙaramin ne ke ss2 Secondary. Sun tabbatar mata gara su shiga duniya da zama da ita. Tana kuka da roƙonsu ko kallonta basuyi ba sukai gaba. Bayan taci kuka har bata iya gani da ƙyau ta tattara ta koma Bakori, ƴan uwa sukace ina bazasu zauna da ita ba sai dai tayi gaba wlhy, magiya ban haƙuri babu wanda batayi ba amma suka ƙi saurarenta. Haka ta baro garin tana kuka itama ta shiga duniyar dan kuwa a Kaduna dai duk inda ta shiga hantararta akeyi da ƙyamarta ana nunata matsayin mai karuwanci da abokin mijinta. Dole ta yanki tikitin wucewa Legas a motar ƴan kawo shanu dan ko kuɗin mota bata da, can kuma shine mafakar duk wani shege....
★★★
Sabuwa kam samun takardar sakinta uku daga Mabera ya sata kuka matuƙa har idanunta na komawa dishi-dishi bata gani. Kayansu da aka kwaso kusa ta bincike tsaff babu komai nata mai daraja na kayan kuɗi a ciki Mabera ya tattare. Da kayan gidan kawai ya barta sai sutura. Ga mutuwar Nazeerah har yanzu ta gagara sakin mata zuciya. Ga ƙafarta data goce ɗin nan al'amari kamar wasa yana neman zama gaskiya gareta. Dole sai Baba da Daddy keta cacar kuɗin asibiti anama kafar hoto da gwaje-gwajen amma an gagara ganin komai sai uban kumburi take yi. Sarai Hajiya Yaya tasan komai dake faruwa da ƴar uwar tata amma ko a waya bata taɓa kira taji yaya take ba. Sai ma a wajen Daddy ne take jin komai. Kai tunda suka dawo Abuja ma saboda Sabuwa dake a gidansu taƙi leƙa Kaduna ita da ƴayanta. Tana dai kiran iyayenta ta gaishesu tana kuma waya da sauran ƴan uwanta. Dan a sunan nan ma na Maanal har shirin zuwa suke yimata kara dan dama dai sukam basu da wata matsala da Ammie.
Wata innarsu ce ta bada shawarar a juya yin na gargajiya ma ƙafar, dan al'amarin dai kam kamar akwai mutanen ɓoye a ciki. Da farko baba ya ƙi dan shi baya son irin waɗan nan abubuwan da ƙyar aka lallashesa. Koda aka gwada zuwa wajen wani malamin magungunan musulunci a kallo ɗaya ya fahimci akwai jinnu a jikin Sabuwa, haka ya shiga mata addu'a da hayaƙin magani sai ko gasu sun bayyana kansu. Basu kuma wani ja al'amarin da nisa ba suka tabbatar da sune suka kadata a waccan ranar, kuma har abada bazasu barta ba sai sun illata mata ƙafafu duka. Dan kuwa abinda tai ne ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya. Tayi ma Hajiya Yaya asiri ne su kuma suka kasa iya komai akan Hajiya Yayan saboda yawan ibada da addu'oi shiyyasa suka dawo kanta, dan su idan aka sakasu aiki basa komawa da shi sai sun tabbatar.
Iya ƙoƙari mutum nan yayi aljanun nan subar sabuwa sun tubure akan babu gudu babu ja da baya. Ran mahaifiyarsu ya ɓaci tace a barta da su, ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan daka. Koda aka gayama Hajiya Yaya mamaki ta dingayi harda hawaye. Wannan wace irin rayuwa muke ciki haka? Wane irin zamani ne wane irin ƙarni ne ace ɗan uwanka ciki ɗaya, uba ɗaya na shirya makirci da muguntar halaka ka akan son duniya da kayan cikinta. A ganinta bata cancanci haka ga Sabuwa ba, dan kuwa kaf ƴan uwanta babu wanda taima gata da yarda da shi hatta gayama sirrinta irin Sabuwa. Amma ta saka mata da irin waɗan nan abubuwan masu ban mamaki. Irin su Sabuwa suke hana zuminci ƙarko, suke hana yarda da juna ko'a cikin ƴan uwa. Suke saka ma zukata jin ko ƴan uwanka ba kowa ke sonka dan ALLAH ba. Kuma duk da haka akwai na kirki na ƙwarai masu ƙyawawan zuciya a cikin zumincin. Kaicon mu da shagala a wannan duniya, kaicon mu da mantawa da rayuwa mai ƙarewa ce, akwai wata can gabammu mai zuwa. Alkairinka ko sharrinka kuma sune kawai zasu zaɓa maka makoma......
________★
Komai yayima Hajiya Basariyya zafi da ɗaci. Dan a yanzu ta tabbatar da micece rayuwa. Wata irin rayuwa akeyi a gidan Alhaji Balala da wanda ya taɓa sanin minene ainahin rayuwar ƙauye ƙarami irin nasu kawai ne zai fahimci abinda take nufi. Komai a birkice yake a wannan rayuwar. Babu maganar bin dokar ALLAH ko wayewar zamani mai inganci dake tafiya da ilimi. A ɓangaren addini daga Alhaji Balala har matansa babu abinda suka sani balle aje ga ƴaƴa. Ita har mamaki take ma da yaje aikin hajji saudia ɗin wane irin aiki yayi na ibada shi kam. To wlhy ko fatiha Alhaji Balala bai iya karantawa dai-dai. Matansa kam alwala wannan cikakkiya basu iya ba. Balle ai maganar wankan tsarki ma to. Bata taɓa sanin akwai kishin jaraba da bala'i ba sai a wannan gida. Ka rasa mi suke ma kishin. Kwana biyu kacal tayi da lafiya a gidan aka sakar mata jini. Ba ƙaramin tashin hankali ta tsinta kanta a ciki ba. Tun tana ɗaukar al'amarin wasa harta fahimci fa ba wasan bane ba. Dan can taji kishiyoyi sun haɗa kai a tsakar gida suna dariya da arerewa sakamakon Alhaji Balala ya zo ya haike mata kamar wata kasƙantacciyar dabba ta ce masa ga halin da take ciki. Sai kawai ya balbaleta da tujara wai miyasa bazata gaya masa al'adarta zata zo ba, ai shi da yasan haka ne da bai yarda ta tare ba sai ta gama. Amma dan mugun hali tayi shiru ga kwanakin angwancinsa biyu zasu wuce a banza tunda bazawara kwana huɗu ne. Itafa dan mamaki ma kasa motsi tayi ta zuba masa ido kawai. Dan wlhy al'amarin fa ya girmi kanta yafi ƙarfinta. Gaba ɗaya ya sillace ta susuce kamar ba Hajiya Basariyya dai da kuka sani ba. Bata da aiki sai zaman kuka da tunanin yanzu haka rayuwa zata ƙare mata. Magana wannan bata iya maidawa ta zafi yanzu.
Duk wannan tujara ta Alhaji Balala matansa na laɓe suna jinsu. To shine fa yana fita suka samu na sanyata a gaba kamar wasu ƙananun yara. Tun bata fahimci da ita ake ba harta gane. Sai kawai ta ɗaukesu mahaukata, amma kuka ya gagara tsaya mata da dana sani da nadama. Ta dinga tuno rayuwar kishi ta gidansu tsakanin ita da Hajiya Yaya da Asiya. “Kai jama'a na cuci kaina wlhy na cuci kaina. ALLAH na tuba ka yafe min ya ALLAH, ALLAH ka sake bani damar gyara kurakuraina. Ya ALLAH ka cireni a cikin wannan gafalalliyar rayuwar na tuba”. Kuka yaci ƙarfinta sosai har tana shiɗewa..........✍️
Hummmmm Hajiya Basariyya kowa ya tuba dan wuya.....🤕201
...........Ƴan Giro dai sai ƙus-ƙus ake da ganin waɗan nan abubun ƴan gayu. Koda su Maanal suka fito daga sashen Mamy zuwa lokacin kowa ya shige ciki, sai su Shahidah dake jiran fitowar tasu. Tunda suka fito kuma suka dinga musu video har suka iso bakin sashen nasu, ɗan harararsu AA yayi yana miƙa musu Hussain, Shahidah tace, “ALLAH dai yasa banda ni a wannan hararar? In ba haka ba ko wankan jego ya tabbata a gidana”.
Hararar ya sake zuba mata kuwa, kai tsaye ya furta, “Idan kin tashi sai ki nema ɗaki babba dan mu huɗu ne”. Yanda ya wani fuske sai ka rantse ba shine yayi maganar ba. Mi Amaal da su Ameerah zasuyi in ba dariya ba. Maanal ta ɗan kallesa cikin waro idanu, ido ɗaya ya kashe mata tare da duƙowa ya sumbaci fuskarta ko kunyar su Shahidah babu. Da ga haka ya shige sashen nasu dan babu abinda yake buƙata irin wanka. Mugun tasa Maanal su Amaal sukai da iskancin tsokana wai da alama kafin arba'in an sake samo wasu twin's ɗin kam. Nibras zuciyarta kamar zata fashe, hawayen da suka cika mata ido ya sakata barin wajen da sauri. Karo na farko Najma ta bita da kallon mamaki ita da Ameerah. Sai kuma suka kalli juna. Sai dai zukatansu ayyana musu kawai suke haihuwar take ma kuka. Bakuna suka taɓe, daga haka akama Maanal rakkiya ciki su ma suka wuce sashensu dan hutawa suka barta da ƴan uwanta. Saheeba da Nuratu ko leƙe basuyi ba, Nuratu ta fake da bata da lafiya, Saheeba kuma haɗama Babban Yaya abinci. Yanzu haka tunda ya shiga sashen tana can ta kasa ta tsare yau harda taimaka masa a wajen wanka. Shi kam Yaya Fawzan ai baima ga idon Nibras ba sai data shiga tana sharar hawaye. Lokacin ya fito duba Najma tunda wadda take gidan bata da niyyar bashi kulawar data dace, ka dawo daga tafiya kusan watanni biyar amma matarka ta aure mai amsa sunan uwargida ko'a jikinta, wace irin mace ce Nibras? Wlhy lokaci kawai yake jira yayi maganin ta.
Wanka Maanal ta wuce yi, yaran suma aka hau gyara su dan bayin ALLAH sun gaji, dan ma Hajiya Shuwa ta kawo dabarar nan ta hana ɗaukarsu kowa sai dai ya gani a jikin iyayensu. Ai da sun gane ALLAH ɗaya ne yau wannan uban taron mutane. Tsaff Hajiya Shuwa ta gyara yaran aka basu abinci sannan aka shirya su aka kwantar da su. Daga nan ta nufi ɗakin Maanal. Umarnin zuwa ta bama mijinta abinci ta bata, ta kuma yimasa sallama dan ba ganin ta zai sake yi ba sai kuma safiya gyaran suna za'ayi mata. Batai musu ba dan Hajiya Shuwa uwa ce, Amaal ta haɗo mata komai ta amsa ta nufi ɗakin AA, yana zaune alamar wanka yayo dan jikinsa da bathrobe, waya yake yi, bayan ta ajiye basket ɗin abincin ta ɗan duƙo ta sumbaci kwantacen gashin fuskarsa. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, sai kuma ya kamo hannunta yasa a jikinsa a hankali saboda cs ɗinta. Suna a haka har ya kammala wayar ya ajiye.
Ƙasa-ƙasa tace masa “Ga abinci nan zan koma Ummu na jirana ne”.
“Ummu kuma? Bata wuce gida ba?”.
“Anan zata kwana ai, zatai min gyaran suna tace na maka sallama ma tun yanzu”.
“Yanzu dai ana nufin ni kaɗai za'a bari a ƙaton ɗakin nan Besty sai wani abu yazo ya bani tsoro?”.
Murmushi tai masa mai sanyi da ƙayatarwa, tare da ja masa hanci kaɗan tace, “Yau dai wayonka bazaiyi aiki ba Besty. Da kake kwana kai ɗaya harna kwana goma a Saudia fa. To kama shirya arba'in uku zamuyi 120days kenan kuma”.
“Karki wani damu kanki, ai tare zamuyi abummu arba'in ukun. Iyakaci dai mu ƙarasashi kina aman laulayi”.
Da sauri ta waro idanu tana tashi a jikinsa ta ce, “Laulayin me kuma?”.
Wani shegen murmushi ya sakar mata, idanunsa na shanyewa tamkar mai jin barci ko yake a cikin maye ya matso fuskarsa gab da ita ya fara shinshinar wuyanta. Muryarsa na fita a ƙasa sosai ya furta, “Cikin wasu twins ɗon nawa mana Besty ” sai kuma ya fara sakar mata kiss a wuyan. Jin jikinta na neman fara amsar saƙonsa a hankali ta turashi baya kaɗan, da yake nashi jikin ya fara saki sai ta samu ta miƙe. Idanunsa ya lumshe ya buɗe yana sakin murmushi da kaiwa kwance yana kallonta. Ita ko kamar wadda ma ke jin kunyarsa yau sai ta ƙi kallon nasa. Abincin ta nufa kawai tana faɗin “A zuba?”.
Da ƙyar ya iya amsa mata da, “Karki damu jeki kar Ummu taga na riƙeki da yawa. Kima su twin's kiss inji Abiee”.
Kai kawai ta iya jinjina masa, ya bita da kallo yana wani cije lips tare da lumshe idanunsa. Sai kuma ya kai hannu ya ɗan dafe cikinsa dake masa ciwo. Kwana goma kacal a takure yake wlhy, shiyasa ma yace taje ɗin, in ba haka ba komai zai iya faruwa, ga doctor ta gaya masa ainahin hutun dazai bata kodan cs ɗin jikinta damma Maanal ɗin nada jiki mai ƙyau ne fa, dan yanzu haka idan ba gaya maka akai ba bazakace cs akai mata ba. Ya daɗe kwance yana ƙullawa da kwancewa, kafin ya tashi yaci abincin ya shirya ya fita dan RK na jiranshi, ga telansu zai zo kawo kayan da zasuyi amfani da shi gobe idan ALLAH ya kaimu shi da su Yaya Fawzan. Dan suna fa sosai aka shirya da yafi wani bikin auren ma. Ba shirin kowa bane kuma hakan sai na RK duk dan ya sake baƙanta ran Mamy. Aiko ran nata yay baƙi, dan tunda su AA suka baro sashenta take shan kuka. Aunty watsar da ita tayi kamar bata gani ba, dama wannan karon kaf dangin su babu wanda yazo, ita kaɗaice a sashen sai Uwangale da Nuratu. Daga ƙarshe dai allurar da akai mata ce ta sata barcin dole. Ko sanda su Yaya Fawzan suka shigo gaisheta ma tayi barci abinta...
_______★
Yau dai Saheeba an samu yanda ake so, an kuma kwantar da kai ma babban Yaya. Shima kuma bai nuna mata komai ba yana mata fatan shiriya. Abinda kawai ya taɓa masa zuciya yanda ɗazun tana bashi abinci take bin cikin Ameerah da mummunan kallo. Ya fahimci itama kuma Ameerah ta lura dan yaga sanda ta shafe cikinta da addu'a har sai da abin ya saka shi murmushi