Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
haɗa ruwa mai zafi ta sake dawowa. Dole ita da Umma suka kama Maanal ɗin, ai ko ta sakar musu kuka jikinta na rawa alamar bazata iya zama ba. Cikin lallashi Umma ke faɗin, “Daure kinji ƴar albarka, ALLAH yay miki albarka kinji. Sannu komai zai zama labari kowa da haka ta fara”. Ita dai Maanal hawaye kawai take, da suka miƙar da ita kasa tsayawa tai a kan ƙafafunta, dole suka rungumeta har bayin. Basu cire mata rigar jikinta ba, a haka suka sakata cikin ruwan zafin dake fin rabin jacuzzi. Ƙarar data fasa musu na azaba jikinta na sake ɗaukar rawa sai da suka ji kamar su fashe da kuka. Da ƙyar suka iya danneta a ciki su biyun, bama ita ba su kansu sunyi zufa sharkaf. Yanda jini ya ɗan ɓata ruwan Umma ta kasa haƙuri ta ce, “Wannan jini da alama yaji mata ciwo sosai kenan?”.
Doctor ta jinjina kanta, “Eh dama da alamun akwai ciwo gaskiya da taji kodan yanda ta kasa zama ma. Amma kuma fa ina ganin yarinyar nan is a virgin gaskiya”.
“Virgin?”.
Umma ta maimaita da mamaki. Itama Maanal duk da halin da take a ciki sai da kalmar ta daki kanta Sosai. Cike da tabbatarwa Doctor ta ce, “Tabbas Mama”.
Rasama abin cewa Umma tayi, suka sake canjama Maanal ruwa abu na mata kai-kawo a cikin rai. Anan ma tasha kuka. Sai da sukai mata ruwa uku sannan suka barta a cikin ruwan suka fito dan jikinta ma ciwo yake shiyasa duk ta inda aka taɓata take raki. Umma data kasa haƙuri ta ce, “Ƴar nan kin tabbatar da abinda kike faɗa gaskiya ne?”.
“Tabbas kuwa Mama, yarinyar nan budurwa ce cikakkiya. Amma bari ta fito zan sake bincikawa”. Ta yaye duvet ɗin dake saman bedsheet ɗin. Ganin yanda duk ya ɓaci da jini ya saka doctor sakin murmushi da sake faɗin, “Mama kinga wani tabbacin ko. Duk da bakowace mace bace ake ganin jini a daren ta na farko wannan ya wuce jinin jin ciwo kawai. Amma dai kamar yanda na sanar miki bara mu sake tabbatar wa”.
Kai kawai Umma ke jinjina wa, dan ko ita daba likita ba shekarun girma sun saka kai tsaye ta fahimci duk abinda doctor ke son ta fahimta. Gaba ɗaya sai taji ta sake shiga ruɗani, ta zauna shiru tana kallon Doctor dake cire bedsheet ɗin zata canja da wanda ta ɗakko a closet ɗin Maanal. Tashi tai ta koma wajen Maanal dake bayi, wata irin ƙaunar yarinyar ce mai nauyi ke sake mata tasiri a cikin zuciya. Alhamdullahi tayi wankan da sukace tayi, harma ta daddafa ta saka bathroom tana jingine da bango. Kamota Umma tai suka fito tana tafiya da ƙyar, hawaye kam sun gagara tsayawa gaba ɗaya. Sai sauke ajiyar zuciya take a jajjere. Towel ɗin Umma ta naɗe mata a kai dan ya tsane ruwan, ta amshi riga mai kauri da Doctor ta ɗakko ta sanya mata dan rawar sanyi Maanal ɗin keyi, ga zazzaɓi jikinta zafi zau abin tausayi. Kwantar da ita sukai Umma ta fito dan bama doctor damar yin aikinta. Aiko sai da suka sha dagama da Maanal sannan ta yarda ta duba jikinta, sosai doctor ta runtse idonta tana cije bakin tausayin yarinyar dan da gaske ango yayi ɓarna sosai.....
_______★
A ɓangaren dangin su Mamy basu san wainar da ake toyawa a sashen AA ba, dan suma a nasu sashen sun kwana sun tashi ne da tashin hankalin halin da Mamy da Nuratu suke. Sai yanzu da safen nan ne Hajiya Turai tazo tare da Doctor ɗin dake duba Mamy dan tun daren Maman Saheeba ta kirata. Lokacin shigowar tasu ne taga Oum ta nufi sashen AA da kaya a hannu, shine take tambaya taga matar can na nufa sashen Ajwaad da sassafen nan.
Kai tsaye Maman Saheeba da Saheeba suka fahimci abinda ke faruwa, aunty Babba kuwa naji bata tanka musu ba. Su kuma sauran da basu san abinda ke faruwar ba suka shiga tambaya. Bayanin kuwa Hajiya Turai tai musu. Mariya ce ta miƙe tana faɗin, “Bara naje naji mike faruwa, dan inba wani abu ba itako mizai kaita sashen yara da safen nan dan masifa”.
Bata jira cewar kowa ba ta fice. Koda ta shigo falon ƙasa babu kowa sai tai tsaye, zuwa can kuma ta ɗan zauna tana jiran taga ko Oum zata sakko amma shiru kake ji. Fin mintuna biyar ta fara ɗan jiyo magana sama-sama daga upstairs. Miƙewa tai kawai ta shiga haurowa saman itama. A dai-dai nan Doctor ke fitowa daga ɗakin Maanal. Dan da Umma ce da Oum ke magana bayan Oum ta shiga duba Manaal amma ta ɓoye fuska a barko taƙi yarda ta kalla Oum, shine ta fito ta barsu ta dawo wajen Umma. Sai kuma ga RK shima ya fito daga ɗakin AA. Duk kallon Mariya dake gaishe da Umma sukai. Batare da damuwa ba RK daya gaisheta fisha shima ya kalla Doctor ya ce, “Ya ake ciki Aunty?”.
Kai Doctor ta jinjina, sai kuma ta kalla Mariya. RK ya fahimta, dan haka ya ce, “Karki damu kiyi bayani nan duk ƴan gida ne kuma iyaye”.
Kanta ta jinjina masa. Ta cigaba da faɗin, “Dole za'ai mata ɗinki gaskiya dan taji ciwo sosai. Gashi har yanzu a firgice take.”
Caraf Mariya ta ce,.........✍️
Na kula Mariyar nan ƴar ɓare-ɓare ce fa😂
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣8️⃣
______________
........“Ciwo kuma, yarinyar daba budurwa ba miyya haɗata da ciwo? Ko ɗinkin nan na zamani taje akai mata?”.
Babu wanda maganarta bata zafeshi ba a cikin su Oum, amma sai babu wanda ya tanka sai doctor da tai murmushi da faɗin, “Wlhy ko ɗaya Hajiya babu wani ɗinki. Hasalima yarinyar nan cikakkiyar budurwa ce yau aka fara taɓata.”
“Budurwa? Kai likita sake dubawa dai da ƙyau. Ko ana rasa budurci ne ya kuma sake dawowa a karo na biyu? Yarinyar nan fa shekara takwas data wuce an mata fyaɗe”.
Kallonta Oum tai zatai magana rai a ɓace yanzu kam Umma ta riƙe mata hannu ta girgiza mata kai alamar kar tace komai.
Doctor ta ce, “Tabbas Hajiya budurci sau ɗaya yake ga kowacce mace, kuma baya maimaita kansa, duk ma wadda tace zata iya dawo da shi da wani magani ko ɗinki ƙarya take, sai dai tayi abinda za'a mace amma ba dawo da budurci ba. Dan sau ɗaya tak ake yaye wannan tantanin. Dan haka zan sake jaddadawa yarinyar nan cikakkiyar budurwa ce yau ne karo na farko data fara sanin namiji. Idan kuna kokwanto kuma za'a iya sake kaita asibiti ma ko a kira wasu doctors ɗin su dubata banda haufi akan hakan. Fyaɗen da kuke tunanin kuma an mata gaskiya ku ƙara bincike akwai abinda ya kamata Ku sani”. Daga haka ta juya tana kallon RK. “Doctor zanje na dawo yanzun nan. Amma zaka iya samo ma su Hajiya wasu likitocin su duba yarinyar nan kafin na dawo dan su sami nutsuwa.”
Murmushi RK yay da faɗin, “Karki damu Aunty ni dai na gamsu, iyayena ma nasan sun gamsu in sha ALLAHU. Wanda bai yarda ba sai ya kawo nashi likitan. Amma ko shi ma Ajwaad ɗin a yanayin da yake ciki yau ne karonsa na farko da hakan ta kasance. Sannan da bakinsa ya sanar min Maanal budurwa ce babu abinda ya faru a waccan ranar”.
Wasu irin hawayen farin ciki ne suka silalo a idanun Oum. Ta shiga tuno kalaman AA a randa ta turkeshi akan batun fyaɗen. (Oum dan ALLAH ki bar zancen kawai. Amma ki yafe min. Ki kumayi haƙuri komai daren daɗewa UBANGIJI zai warware komai cikin sauƙi da rahamarsa. Amma a yanzu babu wani bayani da zan yi a fahimta ko a yarda. Abinda kawai na sani shi ALLAH baya barci. Ki tayani da addu'a kawai ALLAH yasa na gano inda su Maanal suke. Wannan shi nafi buƙata a yanzu) Hawaye suka sake ziraro mata. Ita kanta Umma tuna ranar da suka tirke Ajwaad ɗin take. Marukan daya sha wajen Abah da Uncle Mahmoud har sai da fuskar yaron nan ta kumbura da shatin yatsunsu. Amma akai juyin duniya yaƙi cewa komai. Daga ƙarshe ma ya yanke jiki ya faɗi, faɗuwar data zame masa sanadin ciwo na shekara kusan biyu da rabi. To mike faruwa? Ko tace ma miya faru a waccan ranar? Ranar da ranar farin ciki ce da suka taru domin yin shagalin bikin yaran su shida reras. Amma komai ya hargitse ya lalace a sanadin wannan maganar fyaɗe. Mi hakan ke nufi? Miya kamata su sani? Miyasa Ajwaad ya zaɓa yin shiru akan faɗin gaskiya?...
Mariya kam tuni ta fice a sashen jikinta na rawar mazari na gulma. Tamkar wadda aka jeho haka ta faɗo ma su Mamy dan ɗakinta duk suke a yanzu ana dubata. Fuskarta ta kumbura suntum idanun sun shige ciki, hakama ƙafarta ta dama da hannun haggu sun kumbura da alama dai taji ciwo koma karaya kamar yanda doctor ta faɗa, har ma tama wani abokin aikinta daya san harkar ƙashi magana zai zo ya duba Mamyn yanzu. Shayin da likita tace a kawo Mamyn ta sha Haule ta haɗo mata da zafinsa. An bata kenan zata fara sha da hannunta mai lafiya Mariya ta afko, duk kallonta suka juya sunayi harda Haule dake duƙe tana haɗama Mamy ƙwai a cikin bread wai ko zata iya ci dan bakin ma a kumbure yake saboda raunin haɓarta. Hakama goshinta yay wani irin tulluwa. Kai fuskar dai babu ƙyan gani kamar wadda tai haɗarin mota.
Cikin matuƙar fargaba da ƙaulani da su Maman Saheeba ke ciki na jiran sakamako dama ta ce, “Mariya lafiya kuwa?”.
“Uhhhmm!! Lafiya Lau, wani abin mamaki ne ko al'ajabi zan kira shi oho. Wai yarinyar nan matar Ajwaad budurwa ce, babu wani fyaɗe da aka taɓa mata yanzu likita ke faɗa, wannan yaron kuma ƙanin Hajiya Fateema shima yace Ajwaad yace masa babu abinda ya faru a waccan ranar wai.”
“What!!”.
Maman Saheeba, Hajiya Turai, da Saheeba suka faɗa a lokaci guda suna miƙewa tsaye zambar. Yayinda kofin shayin hannun Mamy ya suɓuce shayin ya ƙyalaye mata a jiki gaba ɗaya kuma akwai azabar zafi. Aiko babu shiri ta fasa ƙarar da ta sakaku juyawa kanta gaba ɗaya. Cikin sauri Doctor ta ɗauka gorar ruwan sanyi data gani kusa da Mamy ɗin ta juye mata a jiki. Sai dai ina azabar ta riga ta gama ratsata har wajen fitsarinta saboda a yanda take zaune ƙafa a bubbuɗe...
Haule ma jikinta har rawa yake ta fice. Gaba ɗaya tabar sashen ta nufi can wajen garden ta kira sille a waya.
Harta tsinke bai ɗaga ba, ta sake kira. Tana gab da tsinkewa ya ɗaga yanzu. A fusace ya ce, “Bana faɗa miki zan dawo yau ba. K nifa bana son jaraba dan nasan abinda ya dame ki kenan kiketa son damuna”.
Cikin raunin murya ta ce, “Wlhy ba haka bane Dear, Update ne da ɗumi-ɗuminsa. Wai matar Ajwaad budurwa ce ba'a taɓa mata fyaɗe ba. Yanzu wata ƴar uwarsu ta shigo tana faɗa da'alama daga sashen Ajwaad ɗin take”.
Wata irin mahaukaciyar dariya Sille ya kwashe da ita daga can irin ta ƙeta. Kafin ya ce, “Ajwaad! Ajwaad!! Shegen yaro. Tabbas na yarda ya cini wannan wasan, amma kuma ya jira sabon wasa dan yanzu ne za'a fara tsakanin ni da su. Ƙarfe biyar na yamma kizo gida ki saman zan bada saƙo a isar min da shi cikin gidan..” daga haka ya yanke wayarsa. Kasare Haule tai tana kallon wayar dan babu abinda ta fahimta a zancen nasa. Hasali ma ita har yanzu bata san ainahin abinda ya haɗa AA ɗin da Sillen ba. Kawai dai ya sata ta dinga ɗauka masa rahoton kowa na gidan da motsinsa. Amma har ga ALLAH tana son sanin minene tushe sanadin wannan BASHIN GABAR.....
________★
A ɓanagaren su RK ma tuni Oum ta fito ta nufi sashen Abah duk da tasan akwai su Uncle Mahmud dan anan suke kwana kasancewar akwai ɗakuna wadatattu. A falo ta samesu zaune zasu sha coffee. A yanda Oum ɗin ta shigo duk suka bita da kallo, ita ko babu wani damuwar ganin ƙannen nata a tare da Abah ɗin taje ta rungume Abah ta sakar masa kuka. Sosai hankalin Abah ya tashi, suma su Uncle Mahmud duk suka miƙe nasu hankalin a tashe. Cikin ƙarfin hali Abah daya rungumeta shima ya ce, “Lafiya kuwa Fateema? Ko wani ne ya rasu?”.
Kai ta girgiza masa.
Ya ce, “Rashin lafiya ne?”. Dan yayi zaton zuwa yanzu tasan halin da Mamy ke a ciki. Amma a nan ma sai ta girgiza kanta.
“Gobara ce?”.
Cikin kuka Oum ta ce, “Ajwaad bai yi ma Maanal fyaɗe ba Gadanga, babu abinda ya faru a waccan ranar ashe. Shiyyasa ya ƙi magana akan dukkan tuhumar da kukai masa”.
Shi kansa Abah sai da yaji abu ya tsarga masa. Su Uncle Hussain ma suka shiga kallon kallo. Cikin ƴar rawar Murya Abah yace, “Ban gane komai ba Fateema. Yimin bayani, Please yimin bayani yanda zan fahimta. Taya akai kika gane Ajwaad bai aikata ba?”.
Ɗagowa Oum tai tana share hawayen da ke cigaba da ziraro mata. Babu wani ɓoye-ɓoye ta shiga yi musu bayanin komai daya faru a sashen AA. Aiko Abah sai da yaji shima hawaye sun cika masa nasa idon. Ya tuna yanda ya ringa zubama fuskar AA maruka a waccan ranar masu gigitarwa. Da yanda ya fara jifansa da munanan kalamai sai da Baba Sardauna ya kwaɓesa, ya tuna yanda AA yaƙi magana, ya ƙi musu bayanin komai. Ya tuna wahalar ciwo daya sha na tsawon shekaru har biyu. Ya tuna yanda ya daina shiga sabgar yaron gaba ɗaya duk da yana cikin halin rashin lafiya. Har depression ɗin daya shiga a lokacin da akace a dinga zama da shi shi yace babu mai zaunawa yama haukace sun sallama shi. Haka zaije asibiti ya duba Oum amma ko kallon gadon AA bayayi duk da matsanancin halin da yaron ke a ciki.
Jagwab ya kai zaune abubuwa masu yawa na dawo masa ta yanda ya hora Ajwaad babu tausayawa babu rangwame dan harga ALLAH yaji zafin abin nan ne matuƙa. Ya ji zafin yanda Ajwaad ya lallata Maanal ƴar su ta amana. Su kansu su Uncle Mahmud komai ji sukai ya tsaya musu cak, dan suma dai gwargwadon iko sun taka rawar gani a hora Ajwaad.....
________★
A lokacin da ɓangaririn biyu ke a wancan yanayin anan sashen su AA doctor ce ta dawo tare da wata Nurse. Sun sami Umma nata lallaɓa Maanal tasha tea da RK ya haɗo ya kawo. Sai dai yanda bakinta babu daɗi ta kasa sha. Ga zazzaɓi sai uban rawar sanyi take yi. Ga azaba dan ko zama ta kasa yi sai da aka saka mata fillo ta karkace a kishingiɗe tunda ba damar tasha tea ɗin a kwance. Da ƙyar tasha rabin kofi Umma ta fita doctor ta fara aikinta. Bayan tama Maanal allurar kashe zafi. Ji Maanal take a ranta yau mai rabata da AA sai ALLAH a gidan nan, dole ma ayi walle-walle kowa ya kama tsaginsa dan sashen Oum zata koma. Ita zai ma wannan baƙin muguntar ya gudu ya barta ko sannu baizo ya mata ba...
Tuni ta saki wannan saƙe-saƙen nata saboda azabar zafin ɗinkin duk da anyi allurar kashe zafi. Tako sha kuka sosai da jerama AA ALLAH ya isa a zuciya tafi cikin kwando. Doctor data bama tausayi tana gamawa ta rungumeta tana lallashi da share mata hawaye. Ta ɗora da mata nasiha mai ratsa jiki, da yanda zata kula da kanta dan wajen ya warke da wuri. Kafin ta sake mata allura ta shiga ɗaura mata drip kuma. A haka Oum ta shigo ta samesu. Kan Maanal data fara lullumshe ido ta shafa cike da so da ƙauna da tausayawa. Fuskarta ko murmushi ya kasa ɓacewa. Yanzu ta shiga ta dake shiga sukaga Ajwaad ita da Umma shima dake barci mai nauyi saboda alluran da RK ya masa ga ruwa da ya sanya masa. Shima yasha albarka da tarin addu'oi a wajen Umma dan yau ji take kamar ta ɗaukesa shi da Manaal ɗin ta goye tai ta zagaya Abuja da su.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖7️⃣9️⃣
______________
.........Har sashen su Abah suka shiga suka duba AA da Maanal, duk da dai basu shiga ɗakin da Maanal ɗin take ba. Sai dai na AA kuma yanata barcinsa. Hakama matan sun cika sashen anata taya juna murna. Suma sun shiga sun duba Maanal. Su Baba Sardauna kansu da ke Kano tuni labari yake kunnuwansu, haka ma sauran ƴaƴa da suka wuce dan dama a maza Uncle mahmud, Hussain, Hassan ne kawai suka rage sai yau suma zasu wuce da matan dan su gaba ɗayansu suna nan Abuja ƴaƴa da