Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
masauki, hakama gidan da su Oum ɗin ke zaune mallakinsa ne. Daga gate su Abah suka juya, su kuma suka ƙarasa shiga ciki. Ai yanda kowa yay tiɓis suna amsar keys ɗin ɗakunan kowa yaja matarsa suka shige. Basu sake jin juna ba sai washe gari, dama Oum ta riga ta cika musu ciki miya rage kuma. Barci kawai. Aiko barcin suka sha sosai, sai washe gari zasu tafi gidan su Oum yin breakfast suka haɗu da juna.
Rayuwar saudia tama su Maanal daɗi, dan wata irin rayuwa ce mai saka farin ciki da shaƙuwar zuminci. Sai suka ji kamar ace inama iya su kaɗai ne kawai. Sun gabatar da umrah, sunyi yawo kuma sosai sunyi farin ciki. Dan ma Maanal bata jin daɗi sosai dauriya ce kawai, har ma su Ameeran kowace laulayi ya sakata a gaba amma suna daurewa dan ji suke kamar kar a koma Nigeria anan kusa, dan tattali da soyayya kawai suke samu daga zaratan Oum. To ashe ma mazan nasu sun shirya musu ma shiri na musamman ne. Dan satinsu uku a Saudia suka ɗauke Aban da Oum suka wuce wata ƙasar. Abah harda musu faɗan ai da sun san yawo suka fito da sun taho da Nibras da Saheeba suma. Su dai suka lallaɓashi kawai aka tafi. Abin kamar wasa sai gashi sun zagaye ƙasashe sosai. Dan kuwa watanninsu biyar ciff Maanal har ta shiga watan haihuwarta. Ameerah da Najma nasu cikin duk sun fito ana gani masha ALLAH. Da yake tuni su Oum sun sake komawa Saudia dan ƙasa uku kawai sukaje sukace sun gaji sukam suka koma saudia suko sukai gaba. Suma saudia ɗin suka sake dawowa. Hankalin Oum ya tashi ganin yanda Maanal tai nauyi sosai. Faɗa ta fara musu akan yanzu haka Maanal ɗin ta koma amma suka zauna. Yanzu ina zasu ɗauketa haka zuwa Nigeria, ai dole su bari ta haihu anan kawai sannan su tafi.
Su duka sun gamsu da hakan, sai suka sake miƙe ƙafafun hutawa a Saudia abinsu.....
_________★
A Nigeria kam tunda su Babban Yaya suka wuce Aunty ma ta tafi Kano Mamy da su Saheeba babu zaman lafiya. Basa taimaka mata da komai koda ɗorata a weelchiar ne dan yanzu dole a kanta take saboda ƙafarta data samu matsala bata iya takata sam. Ba kuma harbin ne yaja matsalar ba ainahin karayar data taɓa yi ce lokacin bikin su Maanal take neman zame mata damuwa a yanzu. Babu kunya idan ta zagi su Saheeba suke ramawa.
A randa Aunty ke cika kwana uku da tafiya sai Saheeba ta saka mai aiki ta dafa mata nama zata ci, ta fita zuwa sashenta ɗakko abu sai ga Mamy ta fito a ɗaki dan yanzu itama a downstairs take saboda babu ƙafafu. Ta gunguro kekenta ta ƙwalama mai aikin kira. Koda ta fito tana kallonta da idonta ɗaya duk da akwai gilashi dan dole take sakawa saboda rufe munin ido ɗayan da Sille ya fasa mata duk da ya warke sun masa dabara an rufe shi amma babu ƙyawun gani kuma bata gani da shi kwata-kwata sai ake sirrintashi da gilashin.
“Mi kikeyi a kitchen tun ɗazun Ina kiranki kizo ki saukeni a gado?”.
Mai aiki na ɗan tuttura baki da yamutse fuska dan ko shakkar Mamy bataji, hasalima har rashin kunya take mata, tana zaune ne kawai dan kuɗi gata dama ba yarinya ba ta ce, “Ayya Hajiya Saheeba ce ta sakani dafa mata nama, kema ya kamata kina ɗaga murya, kuma kina ƙoƙarin kanki bawai komai kice sai an miki ba kina zaune turus”.
Sagale Mamy tayi tana kallonta, sai kuma cikin ɓacin rai da gadarar data zame mata a jini ta ce, “Iye ni kike gayama haka kina ƙasƙantacciya ƴar aiki na da nake biya. Ko baki san nan gidan mijina da ƴaƴana bane ba...”
“Ake dai biya na, kuma kece ƙasƙantacciya wlhy, dan koba komai ni halak ɗina nazo nema ba son kashe miji da kishiyar da tai min hallacin bani mijinta na aura danna handame dukiya ba. Ƴaƴa kuma na mai su dai Hajiya Fateema matar ƙwarai ba naki ba, dan in za'ai yaƙin duniya na uku zamu tsaya mata ƴaƴa nata ne kekam ga naki can barbaɗaɗɗe Sille yake ko mi. Ke bari kiji nifa badan kuɗin da ake biyana ba babu abinda zan zauna yi a nan, ke har kina tunanin kina da wani sauran capacity ne a yanzu, dibeki fa kamar wata almajira, yo banda ma kishiyar taki data matsa ki dawo gidan harta ɗaukeni matsayin mai aiki na miki hidima da yanzu kina bakin gada kina bara wlhy, dan wannan ƴaƴan da kike tunanin kin haifa ko ƙaunar ganinki basa son yi yanzu banzar mata kawai. Ko ca kike ban san komai a kanki bane yanzu, to na sani wawuya”.
Ta juya zata koma ciki, sai kawai baƙin ciki da zuciya suka kwashi Mamy ta fisgo matar mutane, keda kike zaune kina fama da ƙafa ɗaya ga babu ido ina ke ina faɗa da mace maiji da ƙarfin jiki gata rainon ƙauye jikinta ya ginu da ingantaccen tuwon dawa dana masara ga aiki. Ai ko tana juyowa ta falle fuskar Mamy da lafiyayyen mari, ta kuma shiga jibgarta. Ihun Mamy ya fargar da su Saheeba, suka shigo da gudu, tsabar mugunta Saheeba ta kulle ƙofa da windows tana faɗin, “Wlhy ci ubanta uwangale karki raga mata. Ki mata lilis, kiyi komai ba komai abinki muna bayanki.”
Wannan zuga ta Saheeba ta sake tunzura Uwangale, ta cigaba da jibgar Mamy da ƙyau, Nuratu kam wata dama hakan ya bata, da sauri ta nufi ɗakin da suke ta ɗakko syringe, haka ta ɗiba jinin jikinta tana matse baki ta fito da shi a ɓoye. Har lokacin Uwangale nakan Mamy tana suburbuɗa, sai kawai tai kamar zata taimaki Mamy a hannun Uwangale ta samu ta danna mata allurar wannan jini a jiki. Ta ɓoye syringe a jikinta sannan ta kwaci Mamyn data gama yin lilis sai kuka take yi.
Nunata Uwangale dake hakki tayi, ta ce, “Shegiya munafuka karuwa maima maza fyaɗe. Gobe dan ALLAH ki sake kawo min wargi ki gani. Ke bama ni ba ko wani a ma'aikatan gidan nan kika sake ma koda kallon banza sai na miki abinda yafi haka. Bakince ke muguwa bace mai baƙin hali, to kin sami mai horaki kuwa a gidan nan dan nice zan koya miki tarbiyyar da kika gagara samu tun daga ƙuruciya. Kuma idan ƙaiƙayin bakinki ya jaki kika gayama wani ko Hajiya Shuwa da Maimoon idan sun shigo ko Hajiya Asiya idan tazo zaki sha mamaki wlhy suna fita zan sake zaneki”.
Sosai ALLAH ya tasirantar da tsoron Uwangale a zuciyar Mamy, su Saheeba kam suka dinga kwasar dariya. Sai gashi koda Hajiya Shuwa ta shigo Mamyn kasa gaya mata tayi, sai tace wai faɗuwa tayi lokacin su Saheeba basa kusa Uwangale kuma na kitchen haɗa mata abinci. Hajiya Shuwa harda yima su Saheeba faɗa akan su daina nesa da Mamyn, su kuma kamar na ALLAH sukace in sha ALLAHU zasu kiyaye. Hakama da Ammie tazo suka tsarata. Dan Hajiya Shuwa da Ammie suna iya ƙoƙarin su na zuwa duba Mamy, Ammie idan tazo yau sai gobe ta huta jibi tazo, wani lokacin harda Hajiya Yaya da yara suke zuwa. Hajiya Shuwa kuwa safe da yamma ita da Maimoon suke shigowa. Damma ita Maimoon ɗin na fama da kanta ne dan laulayin ta mai wahala ne sosai. Shi kansa Ameer duk bayan kwana biyu yana zuwa yaji mi suke buƙata duk da kuwa komai sai da su AA suka ajiye, ga RK kullum yana cikin musu hidima dan gidan yake kwana ma saboda Nuwaira na Kano. Oum tace kuma bai kamata abar su Mamyn su kaɗai ba duk da akwai masu aiki da securitys da aka ƙara a anguwar dama ƙofar gidan nasu saboda guduwar Sille daga gidan mahaukata, ba'a san ko abin shiri bane watarana yace zai dawo ya cutar da su.
Sai dai duk wannan hidimar da su Ammie, Hajiya Shuwa, RK keyi akan Mamy ba birgeta suke ba, kullum cikin zaginsu take a zuciya da tsine musu, kawai dai ALLAH ya ragema aya zaƙinta ne bata da damar yin wata muguntar gata a tauye babu ƙafa babu idanu bata kuma samu haɗin kan mai aiki da zatai mata abinda take so ba sai ta haƙura. To yanzu ma sai ga Uwangale tazo da sabon salon daya karantar da Mamyn cikin sauƙi..........✍️
🤣🤣Yanzu ne fa Mamy ta shiga ainahin hannun ƴan tuwo-tuwo. Uwangale maganin kukanmu😆😆😆😆🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️
190
.......A ɗan tsakani nan wani irin tsoron Uwangale ALLAH ya dasama Mamy mai girma a zuciya, magana kaɗan Mamy zatayi koda bamai zafi ba Uwangale ta mareta, bata isa sakata komai ba a gidan, sai yazam Mamyn ce ta koma yima kanta komai da kanta. Dan su Saheeba babu abinda ya shallesu sai dai su zauna ma suna dariya da kallon drama ɗin. Karo na farko da Mamy ke addu'ar Aunty ta dawo a gidan kosu AA. Amma shiru kake ji, ko kiran waya Aunty tayi sune suke ɗauka su kanainaye su hanata magana, idan kuma sun bata Uwangale na tsaye a kanta da bulala idan ta faɗi abinda bai musu ba tana ajiye wayar ta zaneta. Haka ma idan Oum ta kira suke mata..
Kai da abu yakai kukan kure tsakanin Mamy da su Uwangale sune suka koma sakata aiki a gidan. Haka zata dinga gungura kekenta tana musu hatta girki. Mopping da shara ana idar da sallar asuba suke tasota, haka takeyi tana kukan zuci dan babu damar yin na fili Uwangale da bulala. Sam RK bai san wainar da ake toyawa ba. Dan barci kawai ke kawoshi gidan. Gari na wayewa yake shiri ya wuce asibiti sai kuma wani daren. Idan ya shiga duba Mamy kuma da safe tsaff yake samunta dan suna dai-daita lokacin shigowarsa ne su killafata waje guda, wani lokacin ma su haɗa kayan daɗi a gabanta Nuratu na mata tausa Uwangale na kai-kawo, Saheeba na bata abinci a baki. Yana fita Saheeba da Nuratu sai sun bata maruka suce ta sauka tai musu abinda sukai mata. Haka zata sakko jiki na rawa tayi dan in ba haka ba taci duka a hannun Uwangale.
Tashin hankali yasa jininta kullum a sama yake, ga zuciya ta kumbura sosai har sai da dole RK yasa aka maidata asibiti. Ya zauna yay mata nasiha dan shi a tunaninsa har yanzu tana nan da mugun ƙudirinta ne a rai bai san ƙaniyarta take ci wajen su Saheeba yan boko haram ba🤣😆. Satinta uku a asibitin dan dole Aunty ta dawo ta zauna da ita. Ji Mamy ta dinga yi kamar kar a sallameta, gashi ta kasa gayama Aunty abinda ke faruwa saboda tsoron Uwangale da su Saheeba. Suna komawa gida kuma kwannan Aunty biyar kawai su Saheeba suka zugeta akan taje abinta zasu cigaba da kula da Mamyn, kuka Mamy ta sanya bata son Aunty ta tafi, sai abin ma ya bama Aunty mamaki sosai. Wai yau Kamila ce da kuka bata son ta tafi, lallai mata sun fara laushi ashe. To ita dai Aunty lallashinta tayi akan tayi haƙuri zatai ƙoƙarin dinga zuwa akai-akai, haka ta tafi tabar Mamy na kuka.
Kamar jira su Nuratu suke Aunty na wucewa suka kama Mamy suka lakaɗa mata duka wai tana son tona musu asiri wajen Aunty. Haka taita rantsuwa da basu haƙuri. Bayan sun ja mata dogon gargaɗi suka barta da jiyyar ciwon jiki. To wannan irin azabobi fa Mamy ke fuskanta tunda su AA suka tafi, idan kaga ta samu sassauci sai Aunty tazo kwana biyu. Tana tafiya ake ɗorawa daga inda aka tsaya. Da ace wani zai duba jikinta sawun bulalaine kaca-kaca dan sun zame mata tabo.
Yau tunda sukai waya da Oum tace mata sun kusa dawowa ji Mamy tayi kamar tai ihu dan murna. Har yanzu zuciyarta bata ƙaunar Oum, amma tasan dawowarsu gidan zai zame mata rahama ta wani fannin, dan zata samu sauƙi daga cin ubanta da take a hannun su Uwangale da Saheeba da Nuratu.....
😂😂😂🤣🤣🤣😆😆😆Hajiya Kamila tamu, waya gaya miki barno gabas take🥱😜🤏
__________★
Ba Mamy bace kawai ke amsar sakamakon abinda ta shuka, anan ƙauyen su Kawu Manu ma Hajiya Basariyya na amsar nata sakamakon ne. Bana duka ko zagi ko hantara ba, wannan karon ko aiki ma babu mai sakata a gidan su Kawu Manu sun kawo ido sun zuba mata. Azabar canjin abinci dana canjin waje kawai ke ƙona zuciyarta da rayuwarta. Tana gama iddarta kuma kawai wani mutumi dake mutunci da Kawu Manu a can ƙauyen gaba da su yazo wai yana son aurenta.
Mutumin shine mai anguwar ƙauyensu, yana da shanaye da gonakin noma. Dan haka a yankin ƙauyukan yana cikin masu kuɗin da ake lissafi da shi. Suna huɗɗa sosai da Kawu Manu dan abokinsa ne na amana sosai. Matansa uku da yara kusan ashirin da takwas. Yaje makka dan Alhaji Balala ake kiransa ma. Karku ɗauka dukiyar tasa yana da wani haɗaɗɗen gida ne. A'a sam ba haka bane, gida ne dai irin na ƙauye jar laka. Sai dai ƙaton gaske ne dan duk yaransa maza idan sunyi aure anan suke yankar waje suyi ɗaki su kewaye. Hakan yasa ma gidan albarka sosai ya zama family house, dan aƙalla yaransa maza bakwai nada iyalai. Ɗakunan matansa a jere suke reras guda uku falle ɗai-ɗai sai doguwar baranda. Abinda ya ɗan ɗara gidan Alhaji Balala dana sauran ƙauyen filastar da yay ma ɗakunan matansa da wannan doguwar baranda aka kuma shefe gaban ɗakunan nasu suma da simintin. Sai kuma na tsakar gida dake iyakar tsahon barandar da faɗinta. Ba'a abincin safe a gidan Alhaji Balala balle na rana. Tuwo ne ake yi ƙatuwar tukunya duk bayan kwana biyu a raba kowacce ta ɗauki nata dana ƴaƴanta ta adana taita ɗumamensa. Da yake tuwon anayin wadatacce kam sai kwana biyun ma ya cika wata bata gama cinyewa ba, abinda ya rage ɗin saita shanya ya bushe ta adana kayanta, randa suke jin kwaɗari ta dafa da barkono da manja da ɗan magi kamar shinkafa dan sai an dakashi sannan. Shine mutanen ƙauye muke kira da (Dabuwa. Ku wlhy akwai daɗi😂). To wai a hakan mutane ke ganin gidan Alhaji Balala wadace yake da abinci, dan sauran gidaje wasu ma sai suyi sati basu ɗaura tukunyar ba musamman idan damina ta gabato an cinye amfanin gona.
Lokacin da Iya ke sanarma Hajiya Basariyya batun Alhaji Balala hankalinta tashi yayi, ta shiga wassafo Alhaji Balala data san yana zuwa wajen Kawu Manu duk bayan kwana biyu a cikin idanunta. Kawu Manu ya fishi shekaru, amma shi ƙato ne da ƙibarsa ga tsayi masha ALLAH. Kullum zaka ganshi cikin manyan kaya na yadi mara fasali shi adole ga Alhaji. Amma wuyan rigar kawai ka kalla da hularsa dauɗar dake jikinsu sai ta sakaka amai. Bakinnan ba'a magana dan yana cin goro. Ga uban gashi ya tara a fuska babu gyara duk ya ƙududune yay ƙuda-ƙuda sai kace dole sai ya ajiye sajen a fuska. Ƙafarsa ko faso ba'a magana sai kai ajiyar ƙwandala a wani ramin ta zauna abinta tana hutawa. Yana da arziƙin kudin ƙauye sai dai fa ba'a ci sai iya cikinsa, dan kuwa kullum yana ƙauyen su Kawu Manu wajen mai shayi da tsire dan su babu a nasu ƙauyen. Shiyyasa ƙaton cikinsa ba'a magana, idan yana tafiya har nishi yake kamar mai shirin haihuwa. Ji Hajiya Basariyya tai amai na shirin taho mata, ta fashe da kuka tana faɗin, “Haba Iya, nice wannan kucakin mutumin zai ce yana so har azo ana gaya min, wlhy ALLAH ya kiyaye, ai ko a ɗan aikin gidana ba zan iya ɗaukarsa ba”.
Dariya ma abin yaba iya, ta ce, “Lallai samun wuri, ina ma laifi da kika samu Alhaji Balala ɗin? Mutumin kirki abinci baya yankewa a gidansa. Ke har mafarkin samun wata daular rayuwa da tafi wannan kike yi? To ai saiki matsa kiyita jira”.
Da harara Hajiya Basariyya ta raka bayan iya tana ƙunƙuni. Kamar magana ta wuce kawai bayan kwana biyu Kawu Manu yace mara taje soro su gaisa da baƙo. A tunaninta Daddy ne ko wani dai daga birni, kawai taci karo da Alhaji Balala shirim a zaune cikin wata daddauɗar shaddarsa datai uban squeezing, ga wata shegiyar hularsa a karkace shi a dole yazo zawarci. Jitai amai na neman taso mata, ta kauda kai tana zubar da yawu. Shi ko sai faman washe mata baki yake haƙora jazur da goro.
Ganin taƙi yin magana ya ce, “Hajiyata an fito? Ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya?”.
Maimakon amsa masa gaisuwar sai cewa tai “Miya kawoka wajena?”.
“Haba Hajiya Basari, (Basari🤣 Alhaji Balala ya iya saka suna fa) duk namijin da kika gani yazo gun mace kamarki ai alkairi ne ya kawoshi, alkairin ma na aure. Mu ba yara bane dan haka babu wani batun kwana-kwana aure ya kawoni, kawunki ya sanni, ya kuma san wanene ni. Kai duk kewayen ƙauyukan nan kikace Alhaji Balala ko yaron goye in dai yana magana zai ce miki ya sanni. Dan haka babu wasa a lamarina, zan riƙeki amana kuma zan hidimta miki gwargwadon iko......”
“Mtsowww!! Kai nifa ka isheni da magana. Karma ka wahalar da kanka ni bana sonka, jibeka, kai banda ƙaddara ko a hanya ka ganni ka isa min magana ma. Dan maigadin gidana ma ya fika komai wallahi wawa baƙauyen banz......”
Bata ƙarasa ba taji saukar lafiyayyen mari a kumatunta. Juyowar da zatayi taci karo da Kawu Manu. Fuskarsa na nuna matsanancin ɓacin rai da fushi ya ce, “Yanzu Alhaji Balala ɗin kike zagi Basariyya? Saboda ki nunama duniya ke mara tarbiyya ce. Da shekarunki da komai amma sam baki da isashen hankali. To bara kiji auren