Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
da ke ba. Aliyu ya sanar mana ya sakeki tun bayan rikicin farko daya zaƙulo Dr Tofa ya masa bayani akan abinda ya faru game da zancen fyaɗen da kika saka aima Maanal. Ya tabbatar kece kika ce ace an mata fyaɗe saboda baki san Ajwaad zai amsa shine yayi ba a gabanmu. To wannan ya riga ya faru ya wuce ina sha ALLAHU, amma tun a lokacin ya tabbatar mana bazai iya cigaba da zama dake ba dama zaman haƙuri kukeyi da yima Fateema kawaici. Dan haka ya bamu takardar sakinki har biyu, bayan nan kuma kika sake tafka wannan kuskure na son kashe shi, duk da harga ALLAH munyi shirin gyara komai batare da kin ma sani ba da sauran igiya ɗayan data rage tsakaninku. Amma batun kisa daya shigo ciki yasa muka fahimci babu amfanin yin hakan. Ga shi itama ƴar ƴar uwarki ta sake tafka wata kwamacalar, kuma wlhy ta godema ALLAH abinda ta ƙudira bai faru ba, dan da ace ta samu nasarar cutama Maanal ALLAH sai na shiga kotu da ita. Amma tunda ALLAH ya kiyaye hakan shawara ɗaya zan bama Fadeel ya saketa shima. Daga ƙarshe akwai gida anan Kano na mallaka muku shi ƙyauta ke da su Ku dawo kucigaba da rayuwa a ciki ku barmin zuri'ata ta huta haka nan. Ina son su kasance happy family ya Isa haka ai an wajigu”.
Kuka sosai Mamy take tana kallon Abah, ashe ya daɗe da sarkinta shiyyasa ya daina saurarenta, innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, shike nan abinda tayi fata ga Fateema ya tabbata a kanta. Ta rasa komai, komai da komai ta rasa ita Kamila ta shiga uku ta lalace.
Babu wanda ma yasan tanayi, kowa kuma ya gamsu da hukuncin Baba Sardauna. Oum ce taso yin magana Baba Umar yace mata “Kull babu neman alfarma, abinda Yaya ya yanke ya zartu”.
ALLAH sarki su AA hakan bai musu daɗi ba amma bazasu iya magana ba tunda sun san Mamy ta riga tayi kuskuren da ahalin Darma bazasu sake aminta da ita ko kallonta da daraja ba. Suma da ta haifa suke jin zafin yanda taso kashe musu mahaifi balle su dake mata kara. Damma su Baba Sardauna sun shiga sun fita ne aka kashe maganar kisan Abah a wajen hukuma suka saketa da yanzu ba wannan maganar ake ba ai. A take shima Babban Yaya ya bama Saheeba saki ukun ta. Babu kuma ɓata lokaci aka samo kamfanin masu kwashe kaya aka fara haɗa kayan su Mamy da su Saheeba dan Abah yayi alƙawarin bazasu sake kwanar masa cikin iyali ba. Har kayan Nibras ma ya saka a tattare komai. ALLAH sarki Oum kuka take sosai, dan wlhy har zuciyarta son Mamy take yi, sannan ita har yanzu bata kallon cutarwar Mamy alkairinta na bata ƴaƴan nan uku kawai take kallo da girmamawa. Abinka da kamfani kuma aiki bana mutumin ɗaya ba kafin azhar sun gama komai an lodesu a manyan motoci, masu wucewa Kano suka ɗauki hanya, na Nibras aka wuce gidansu da su.
Su Mamy jirgi zasu bi dan shi Uncle Mahmud ya biya musu, Uwangale kuka take da rokon ita dai a barta nan gidan bazatabi su Mamy ba. Ita bazata iya rabuwa da wannan daula ta koma Kano ba. Amma babu wanda ya kulata. A mamakin kowa Mamy ma kuka take mai ban tausayi, sai dai bataima kowa magana ba. AA, Yaya Fawzan, Babban Yaya da kansu zasu mata rakkiya airport. Yaya Fawzan ya zauna mazaunin driver idanun nuna sun kaɗe sun tara ƙwalla. Babban Yaya na kusa da shi, AA da Mamy a baya da kansa ma ya sakata motar. Idanunsu sunyi jazur, kallo ɗaya zasu baka tausayi amma yaya zasuyi, Mamy itace ta jama kanta, duk da babu shaƙuwa a tsakaninsu da ita ganinta a kusa da su ma ai wani abu ne mai girma. Haka Yaya Fawzan yaja motar Oum na kuka sai da Abah ya rungumeta. Nuratu, Saheeba da Aunty sai Uwangale motarsa daban suma driver ya jasu.....
Motar shiru tunda suka ɗauki hanyar airport har suka iso. Yaya Fawzan ya samu waje yay parking. Basu fitoba kowa yayi shiru kusan minti biyu babban Yaya yay gyaran murya. Duk kallonsa sukayi har Mamy data sha kuka harta godema UBANGIJI. Muryarsa da rauni sosai ya ce, “Mamy bazamu ƙiki ba. Dan duk abinda kika zama ke mahaifiya ce, muna kuma sonki muna ƙaunarki duk da kin ɗaukemu tun muna ƙanana a zanen haihuwa kin bama Oum saboda biyan buƙatar kanki. Alhamdullahi Oum ta mana riƙo irin na uwa mahaifiya ba uwar riƙo matar uba ba. Muna alfahari da wannan kamar yanda muke alfahari da haihuwarmu da kikayi. Komai daya faru mun yarda mun karɓesa matsayin jarabawarmu kuma ƙaddararmu. Amma dan ALLAH muna roƙonki a karo na farko kije kiyi nazarin komai da ya faru. Tun daga aurenki da Abanmu har zuwa yau minene suka aikata miki na cutarwa? Wanne kikai musu ke na cutarwa?. Mu wanda kikai mana mun yafe miki shi kuma muna roƙon ki yafe mana wanda muma muka aikata miki ko ƴan uwana?”.
A tare AA da Yaya Fawzan suka jinjina kawuna. Ya cigaba da faɗin, “Idan har kece mai laifi Mamy ki zauna ki nazartu da yanda ƙarshen yazo, ki daure ki shirya canja zuciyarki zuwa kyakkyawa kamar yanda matar can ta faɗa. Ba zamu so rayuwarki ta ƙare da hakkin kowa ba musamman iyayenmu Abah da Oum da suka kyautata rayuwar. Ki koma ga UBANGIJI Mamy shi mai gafara ne, kiyi tuba na gaskiya ALLAH zai yi alfahari dake. In sha ALLAHU zamu cigaba da sauke dukkan hakkinki dake a kammu. Zamu dinga zuwa dubaki a kai a kai, duk abinda kike buƙata ki gaya mana zamuyi miki shi in har baifi ƙarfinmu ba. Idan kun sauka in sha ALLAHU muma zuwa jibi yanda jikin Maanal ya kasance zamu biyo bayanku muga mazaunin naki. Ki riƙe a ranki muna sonki, muna kuma yi miki fatan shiriya, za kuma mu cigaba da roƙon ALLAH ya baki ikon neman gafarar duk wanda kika cutamawa”.
Ya kai hannu ya ɗauke hawayen da suka cika masa idanunsa. Yaya Fawzan kam share-share suke zuba. Shima AA hawayen da suka ciko masa idon yasa yatsa ya ɗauke. Sannan ya kamo hannunta ya matse a cikin nashi, kafin a hankali ya kaishi wajen bakinsa ya sumbata. Daga haka ya buɗe motar ya fita. Suma su Babban Yaya duk suka fita. Haka suka kamata suka saka a wheelchair ɗin. Kamar yanda AA yay mata Babban Yaya da Yaya Fawzan ma haka sukazo suka kama hannunta duk suka sumbata. Sannan Aunty ta kama keken nata suka shige dan jirgin su zai tashi nan da mintuna..........✍️213
.......Nuratu da Saheeba ma haka suka shige suna waigen su AA suna kuka kamar ransu zai fita. Haka ma Aunty kuka take sosai.
Su Babban Yaya basu bar airport ɗin ba sai da jirgin su Mamy ya ɗaga zuwa Kano sannan. Koda suka fito kuma driver ne kawai ya wuce gida su Mawaad Company ma suka tafi, suka kulle kansu a office ɗin AA. Ba wani hira suke ba ba komai ba kowa yana zaune ne shiru kawai. Sai lokacin salla yayi suje massalaci suyi su sake dawowa su zauna. Basu bar Company ɗin ba sai kusan goma na dare. Shima Baba Sardauna ne yay kiransu a waya yay musu nasiha sosai data ratsasu....
Washe gari mutanen Kano suka wuce suma da safe saboda jikin Maanal Alhamdullah da sauƙi babu wani damuwa sai fatan ƙarasa murmurewa. Nibras ce dai ƴan uwanta ma sun yanke hukuncin fita da ita waje saboda illar da ƙugunta ya samu.. Sai Oum da itama dai bata jin daɗi saboda damuwar tafiyar Mamy data sakama kanta. Dole aka kwantar da ita asibiti itama.....
__________★
Anan ɓangaren Hajiya Basariyya rayuwa ta mata zafi sosai. Komai babu daɗi. Tun tana tunanin kuɓuta a rayuwar Alhaji Balala harta fahimci al'amarin fa bamai sauƙi bane ba. Ta rame ta lalace tai baƙi kamar ba ita ba. Tun tana hawayen aikin yin tuwon gidan Alhaji Balala a ranar girkinta harta saba. Jini ko tunda Alhaji Balala ya fahimci na asiri ne ya tattara matansa ya musu tas, da yake shima sun san hatsabibin kansa ne babu arziƙi sukaje suka karya asirin ya cigaba da ragargazar amarcinsa. Sai ga Hajiya Basariyya da ciki. Wannan abu ya sake ɗaga mata hankali matuƙa. Tana tsaka da wannan laulayin jaraba suka samu baƙuncin Maman Yaseerah tazo bibiyar bashin kuɗinta. Itama dai Baban su Najma tuni ya tasheta a gidansa ganin iskancinta na ƙara gaba, yanzu haka yaran suna wajen uwargidasa ita kuma ta shiga buga barikinta da hatsabiban yan iskan bariki. Sun kuwa buɗe mata ido dan yanzu haka ma sune suka rakota har nan garin da Hajiya Basariyya ke aure. Babu mutunci suka dinga shekama Hajiya Basariyya dariya wai haka kuma duniya ta maida ita? Ita dai bata tanka musu ba, dan tsoro ma suka bata. Maman Yaseerah tace kuɗinta take buƙata. Hajiya Basariyya bata da su, babu mutunci tai waya da wani akan yazo ya sai kayan ɗakin Hajiya Basariyyar. Haka kuwa mutum yazo da ƙatuwar motar ɗibar kaya daga kankia. Akai cinikin kujerunta dake a waje rufe har yanzu babu wajen sakasu, da yake sayen mugunta ne kuɗin bai kai ba. Suka kuwa haɗa dana ɗakinta, haka suka sauke mata katifa a ƙasa suka zazzage mata kayanta daga wadrob a katifar suka kwashe komai sukai gaba suka barta da kuka da dana sanin sanin Hajiya Jumai a rayuwarta. Kishiyoyi kuma suka samu nayi da dariya da habaici har suna gayyato matan ƙauyen. Aka saka Hajiya Basariyya gaba harda waƙa idan ana luguden daka. Ko'a jikin Alhaji Balala duk da yaji haushin an rage masa jin daɗin hawa katon gado, amma tunda katifar na nan ai ba damuwa a ɗan shana ai rigijib-jib inji (Hadiza Kabara😂).
Hajiya Basariyya bata gane ALLAH ɗaya bane sai da aka fara aikin gona. Ashe Alhaji Balala tattara matansa yake kaf da ƴaƴa da jikoki aje gona aiki. Tana kuka tana komai ga laulayi babu tausayi haka ya sakata a gaba kuwa itama aka tafi. Tun bata iya ba harta zage tana aiki. A wannan halin yayanta da su Madeena daya kwasa suje dubata suka sameta. Kuka su Madeena suka dingayi dan da farko wlhy basu gane Ummy ɗinsu bace ba ganin yanda ta ƙomaje ta tsofe ta fita a hayyacinta. Shi kansa Yayanta ya girgiza. Ga ciki, wlhy da babu ciki sai ya raba auren nan, amma yaya za'ayi da ikon ALLAH. Asibiti kawai suka kaita tai kwana uku, Alhaji Balala nata fushi amma yaya zaiyi. Ta ɗan murmure, Ƴaƴanta ya sake siya mata kayan ɗaki dai-dai zaman ƙauyen ba irin wanda ta rasa ba, ya bata jarin yin sana'a. Data kalla yaranta sai hawaye. Ko maƙiyi ya kallesu yasan suna jin daɗi suna kuma cikin kwanciyar hankali. Da zasu tafi ta basu kayan kuka kuɓewa daddawa sunkaima su Ammie. Haka suka tafi tana kuka sunayi. Bayan tafiyarsu da kusan wata guda Sageer ya tilasta Huznah suka zo suma. Suma hankalinsu ya tashi da ganin makomar Hajiya Basariyyar amma yaya zasuyi. Huznah na kuka Hajiya Basariyya nayi da neman gafararsu ita da Sageer. Da zasu tafi ya kawo alkairin mai yawa yayi mata. Ranta fal mamakin yaushe Sageer ya jiƙe haka, ga mota mai ƙyau ga kuɗi, kallo ɗaya tai musu shi da Huznah ga ɗan yaronsu kamar ta cinye dan kyau tasan hankalinsu kwance suke. Ga Huznah ɗin ma kamar da ciki a tare da ita. Suma haka suka wuce suka barta cike da jimami dan basu kwana ba.
Labarin da su Madeena sukaje suka bama su Ammie akan halin da Umminsu ke ciki ya ɗagama su Ammien hankali sosai. Haka Yazeed ya shiryo shima yazo ya mata alkairi sosai, a ransa kuma ya kudira sai ta ɗauketa a garin nan ko bajika koba daɗe. Koda ya koma shima ya labartama Daddy komai ko tari baiyi ba balle ya nuna ya jishi, dole ya tsuke bakinsa dan wargi ma waje yake samu......
★ Bisa tirsasawar Daddy su Basira duk sun fidda mijin aure suma. A yanzu haka an tsaida rana harda Yaya Yazeed da Khadijah da suka daidaita kansu. Ƴan uwa nata farin ciki da wannan al'amari. A tsakanin ne kuma Amaal ta haihu. Kasancewar Maanal na asibiti bataje ba, hakama Oum na fama da kanta. Sai Ameerah da Najma. Su Umma ma sun zo daga Kano. Ta haifi namiji abinta.
_________★
Su Mamy an isa Kano lafiya, gidan babu laifi da ɗan ƙyansa gwargwado amma dai ƙarami ne dai-dai zaman mutum ɗaya. Su Saheeba da sunce bazasu zauna ba. Dan haka suka wuce gidan Babansu wai can zasu zauna. Haka suka wuce can kayansu ma can aka sauke.
Kamar gaske matar babbansu ta tarbesu da farin ciki da murna. Suko suna sha mata ƙamshi saboda ganinta ƙarama. Basu san kwantar musu da kai tayi ba kawai. Tun suna nuna isa har suka fara sakkowa ganin ita babu ruwanta, shima Babban yana sake ji da su saboda tausayin halin da suke ciki, duk da ya yarda su masu laifi ne dan har kiran Abah yayi ya sake bashi hakuri da su AA. Amma yayi imanin duk laifin uwarsu da yar uwarsa Turai ne da Mamy da suka ɗorasu a kan hanyar banza.
Da wayo da wayo sai da sabbin ƙawayensu suka sakasu salwantar da komai da suka zo da shi, na kayan ɗaki da sutura da duk wani kayan adonsu. Sai da komai ya ƙare aka fahimci harkar shaye-shaye suka shiga, aiki matar babansu tace bazata zauna da su ba dan sun fara mata ƴan sace-sace. Rikicin yau da ban na gobe daban babu arziƙi suka bar gidan dan baban nasu ma ya daina raga musu. Komai matarsa ta gaya masa sunyi yarda yake dan ta fisu gaskiya, duk kuma rantsuwar da zasuyi baya saurarensu sai yace dama haka suke da baƙin hali kamar uwarsu. Ganin fa abin bana wasa bane babansu na neman tsine musu suka tattara suka koma wajen Mamy da tuni Uwangale ta gudu ta barta. Sai wata mai aikin da su Babban Yaya suka ɗauka mata dan sun zo har sau biyu sun dubata. Sai dai ranar suke suwa su koma dan har yanzu Maanal da Oum na asibiti. Amma suna saka ran a satin nan za'a sallamesu. Idan kuma an sallamesun ƙasar zasu bari dan samu su huta zuwa nan gaba sa dawo ko hakan zai sa su sami sauƙin zuciya dana al'amura.
Da farko Mamy taƙi amsar su Saheeba. Sai da Aunty Babba ta saka baki tare da mata nasiha sannan. Dan Mamyn kam yanzu ba tada bace. Tayi laushi sosai kawai dai har yanzu ALLAH bai bata ikon kwantar da kanta ta nema gafarar kowa bane. Amma har kiran Oum take taji yaya jikinta. Ta kuma kira AA a haɗasu da Maanal itama tai mata yaya jiki. Hakan na ɗan saka musu jin farin ciki a ransu. Suna kuma mata addu'ar shiriya da ƙara gane gaskiya koda anan gaba ne kafin dai lokaci ya ƙure mata..
Dawowar su Saheeba gidan kuma sai rashin jituwa ya shiga tsakaninsu, kullum faɗa ita da su. Wani lokacin tana zaginsu suna zaginta. Basa raga mata sam. Bata isa sakasu aiki ba. Dan kai tsaye zasuce bazasuyi ba. Ga yawon darensu na tsiya. Ga kudi data ajiye su sace. Tun tana iya daurewa harta fito fili ta sanarma su babban Yaya saboda wani duka da Saheeba da Nuratu suka haɗu suka laƙaɗa mata saboda Saheeba tayi shaye-shaye tazo ta musu amai a falo Mamyn tayi magana.
Babu ma wanda ya sani babban Yaya ya zo Kano. Shi kansa yanda yaga su Saheeban sun koma sai da mamaki ya kamashi. Kallo ɗaya zaka fahimci shaye-shaye suke yi. Basu da wata maraba da karuwai wlhy. Ga uban ƙarin gashi, ga ƙarin farce dana girar ido. Idanu duk sun juye saboda shaye-shayen ma na hauka sukeyi komai aka samu ɗorawa ake yi. Aiko ya lakaɗa musu shegen duka ya korasu, ya kuma saka yan bijilanti duk randa suka gansu a jikin gidan ma su musu dukan tsiya. Sai ya samu mijin Aunty Babba ya roƙesa akan ta dawo nan ta zauna tunda dama can gidan ya musu kaɗan ita da kishiyarta, yaranta kuma sun kaisu karatu waje shi da su yaya Fawzan ita kaɗai take zaune. Sai kawai ya amince Aunty ta dawo nan kusa da Mamy ɗin. Aka samo musu mai tayasu aiki. Duk wata zasu dinga aiko mata da maganinta na HIV, ƙafa da ido dai an riga da an rasa su sai haƙuri. Koda ya koma Abuja bai bama kowa labarin nan ba. Dan yanzu har kunyar kawo zancen Mamy suke gaban Abah da Oum dama matansu. Abin farin ciki kuma ya samu ma an sallami Oum da Maanal daga asibiti, bayan jiyyar kusan sati uku. Dan Maanal gaskiya ta wajigu matuƙar wajiguwa. ALLAH dai ya ƙaddara tana da sauran kwana ne a gaba da yanzu wata maganar akeyi.........✍️214
.......A washe garin da aka sallami Oum da Maanal suka bar Nigeria gaba ɗayan su. Kuma da alama wannan tafiyar mai daɗewa ce. Dan ƙasar Chaina suka dira. A block ɗaya suka kama wajen zama. Sai dai kowa da apartment ɗinsa, amma floor ɗaya suke kuma a jere guda huɗu reras. Kowanne a nashi akwai bedroom ɗaya, kitchen, falo, sai wajen karatu. Komai dai tsaff, babu takura babu gajiyawa. Tsarin kuma duk iri ɗaya ne. Duk a gajiye suke, dan haka kowa yaja matarsa suka shige nasu. Oum ta amshi ƴan biyu ita da Abah, idan akai musu wanka a maido su. Hakan ya bama AA damar jan hannun Maanal suka shige nasu suma. Dan shekaran jiya ƙiri-ƙiri da aka sallamosu asibiti taƙi zuwa sashensu ta wuce wajen Oum. Haka ta barshi ya kwana shi kaɗai, sai a jirgi ne suka zauna waje ɗaya. Suna shiga ya maida ƙofar ya rufe ya mannata a