Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
duniya idan ba Maanal ba baya jin yana ma wani kira biyu, sai dai Oum ɗin kam da Abah, dan su Babban Yaya ma sun san halinsa sarai shiyyasa ko uziri suke zasu ɗaga suce zasu kirashi back. Amma yarinyar nan hummm. Koda yake tun asali dama ita kaɗai ke masa yanda take so..
Gudu sosai drivern sa yayi, dan cikin ikon ALLAH awa biyu suka iso Abuja, ga wani hadari da ya haɗu sosai. Ta jere suka bi saboda kaucema huldup ɗin zuba, dan tanan ɗin shine ƙalubalensu. Kamar jira kuwa hadarin nan yake motar na shigowa gidan ruwan ya fara sauka. Wayoyinsa kawai ya ɗiba sai ledar tsarabar da yay ma Maanal ta musamman yace driver yakai sauran sashen Oum, shi kuma ya shige nasu sashen dan anan drivern ya tsaya ganin ruwa ya fara sauka. Yanda kuma ya kula ogan nashi ya gaji ya fahimci hutu kawai yake buƙata.
Hakanne kuwa, dan AA tiɓis yake jinsa duk da ba wani aikin ƙarfi yayi ba, amma maganar daya yawaita yau kasancewar ba yawan maganar ke gareshi ba kansa har ciwo yake masa. Bai mayi zaton samun Maanal a sashen ba. Dan yasan da wahala ba tana sashen Oum ba koma tana barci nata. Tsaf falon yake, ga ƙamshi masu daɗi na turaren wuta dana air fresheners na tashi. Komai a kashe sai fitulu marasa yawan haske. Kai tsaye ya wuce upstairs, nan ɗin ma dai fes kuma ƙamshin na tashi mai daɗi. Anan ya ajiye ledar hannunsa sannan ya wuce bedroom, babban burinsa ya cire kayan nan duk sun damesa, shi haka yake manyan kaya na matuƙar takurama rayuwarsa, shiyyasa baya son sakasu sai dole. Yanzu kuma tunda ya auri Maanal ta sashi a gaba da sakasu wai sunfi masa ƙyau. Dama can haka take masa.....
Turus ya ɗan tsaya tunaninsa na yankewa, idanunsa a kanta, tana zaune ne a cikin sofa bathrobe a jikinta alamar wanka ta fito, waya a kunnenta tana magana a hankali. Dan muryarta gaba ɗaya babu walwala a ciki babu sakewa, sai dai jin ta ambaci Didi yasa ya fahimci da ƴan uwanta takeyi. Ƙarasa shigowa yay cikin ɗakin yazo ya zauna a kusa da ita. Karo na farko ta ɗago ta kallesa, sai kuma ta janye a lokaci guda kamar bata ganshin ba. Sai kuma tama miƙe gaba ɗaya zata bar wajen, hannunta ya kamo a hankali, ta tsaya cak, ita bata tafi ba ba kuma ta dawo ta zauna ba. Kuma taƙi juyowa ta kallesa, sai ma wayarta data cigaba dayi. Tsaye ya tashi ya amshe wayar ya yanke kiran, ta kallesa da idanunta da suka kaɗe hawaye cike a cikinsu. Sai kuma ta janye daga cikin nasan ciki-ciki ta ce, “Sannu da dawowa”. Daga haka ta zare hannunta daya riƙe tabar masa wajen. Sai ma ya rasa abinyi ya bita ta da kallo kawai. A zatonsa waje zata canja, amma sai ga ta nufi dispenser ta buɗe ta ɗakko ruwa a ciki da cup ta dawo inda yake, ruwan ta zuba ta miƙa masa. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana amsar ruwan zuciyarsa na sanyi. Ita kuma sake barin mai wajen tai dai-dai zai kai kofin baki nan ma ciki-ciki ta ce, “MANZON ALLAH dai ya hana shan abu daga tsaye”. Daga haka tai wucewarta. Shima ya sani kawai fushinta ya shagaltar da shi ne, dan haka ya ɗan sauke numfashi yana komawa ya zauna sannan yasha ruwan. Yana zaune sai gata ta fito daga closet ɗin cikin doguwar riga mara nauyi sai dai ta mata ƙyau sosai da zaunawa a jikinta dan kamar an mata fenti da ita tsabar yanda tabi ƙyaƙyƙyawar surarta. Cikin nan a kwance kamar babu hanji ma balle ɗam mutum. Sai gashinta dake a warware ta cire ribbon ɗin. Inda yaken ta dawo, bata yarda ta kallesa ba ta durƙusa ta kama ƙafarsa ta zare takalminsa da safan, sannan ta kamo hannunsa ta zare designer agogon companyn mawaad dake a hannun nasa mai shegen ƙyau da baka isa zuwa ko'ina kasamesa ba sai a wajensa, ta haɗa da hularsa daya cire ta ɗauka da takalman ta koma closet ɗin ta ajiye komai inda ya kamata. Shi dai yana zaune yana binta da kallo. Koda ta dawo wucesa tai ta nufi mirror tana faɗin, “Ga ruwan wanka can”. Karo na farko ya ɗan yi guntun murmushi, sai kuma ya lumshe idanunsa yana kwantar da bayansa a jikin kujerar.
Manaal dake zaune a stool na mirror tana taje kai wani irin takaici da fushi na sake cika mata zuciyarta, ta wani finciki gashin da cumb. Aiko zafi mai azaba ya ratsata ta saki ƴar ƙara idanunta na cika da hawaye. Idanunsa ya buɗe yana kallonta, ganin yanda ta duƙe kanta a katakon mirror ɗin ya miƙe ya nufi inda take. Hannayensa duka biyu yasa a jikinta yay ƙoƙarin ɗagota, amma sai taƙi yarda, ya ɗanyi jimm dan ya fahimci da gaske fa yayi laifi. Ƙasa ya kai yay irin tsigunnon maza ɗin nan dan ya samu damar leƙa fuskarta. A can cikin maƙoshi ya ce, “Besty!”.
Hannunsa ta ture, ta yunƙura zata tashi gaba ɗaya shima sai ya miƙe ya kamota. Ta ƙoƙarin kwace jikinta, yanzu kam baiyi da wasa ba ya riƙeta da ƙyau, tare da jawota ya rungume. Dai-dai nan ruwa ya sake kecewa fiye da farko da ake yi kamar yayyafi. Tana goggocewa bai barta ba, sai kawai ta kife kanta a ƙirjinsa ta saki kuka......
_________★
“Tashi muje dan ubanki, wlhy bazaki kwana a gidan nan ba”.
Kuka Nibras ta sakarma Yayanta mai maganar, shiko ya haɗe girar sama data ƙasa yana mata kallo mai kaɗa hanjin ciki. Tsawa ya sake daka mata, ta diro a saman gadon da take kwance. Dan tun safen data iso gidan ta samu Momynta bata gida wai sunje jihar Nasarawa gaisuwar wani abokin aikinta daya rasu ta shigo bedroom ɗin ta kwanta taci kukanta, rashin barcin daren da bata samu ba ya ɗauketa a haka, bata tashi farkawa ba sai 2. Shine mai aikinsu ta kawo mata abinci tace bazata ci ba, ta zauna tana lallashin ta da yake babbar mace ce tun ma Nibras ɗin na ƙarama take aiki a gidan. Da ƙyar ta samu Nibras ɗin ta ɗan ci, tana fita ta koma ta kwanta batare da neman salla ba, shine har zuwa yanzu da akai la'asar bata fito ɗin ba Yayanta na biyu yazo gidan mai aikin tasu ke sanar masa halin da Nibras ɗin ke ciki. Shi dama bai cika biyema taɓarar Nibras ɗin koda yaushe ba, shiyyasa take shakkarsa, shine yayanta na biyu. Koda yazo yana tambayarta kukan rashin mutuncin ta sanya masa tana gaya masa abinda Yaya Fawzan ya mata harda abinda itama tayi, daga ƙarshe ta zagi Fawzan ɗin. Aiko ya buge bakinta da ƙarfin gaske har sai da ya fashe. Kafin ya shiga zaginta shima yana faɗin, “Mijin naki kike zagi? Mijin naki ne abin zagi saboda ya ƙara aure. To ke wacece da kika isa haramta masa abinda ALLAH ya hallata masa dan ubanki. Ko an gaya miki duk wani iskancin da kike masa yana ƙyaleki bamu sani bane, ai dama mun zuba muku ido ke da Mom ɗin muga iya gudun ruwanku. Wlhy kaɗan ma yay miki, idan nine sai na lakaɗa miki shegen duka a daren kuma bazaki kwana min a gida ba. Shashasha kawai mara wayo. Kin tashi ko sai na karyaki”.
Cikin kuka sosai ta ce, “Amma Yaya ko kishina baka ji, na gama gaya maka abinda yay min kace na tashi na koma dan kaga Mom bata gid....”
Bata ƙarasa ba ya sake kaima bakinta duka. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake hayewa da kumburi, itako ta ƙara ƙarfin kukanta. Belt yay ƙoƙarin fara zarewa daga jikinsa, da gudu ta dirgo a gadon ta kama akwatinta taja ta fice ko ɗan kwali babu a kanta, sai shine ya ɗiba mata ya bita da su. Motarsa ta shiga, ya kuma hanata kuka yaja suka bar gidan. Kai tsaye gidan Darma ya nufa, suna gab da isowa aka fara yayyafi, lokacin da AA ke shigewa sashensu lokacin motar yayan Nibras ke shigowa gidan. Da ga shi har Nibras ɗin kuma duk sunga AA ɗin, shine dai bai gansu ba dan hankalinsa ba'a kansu yake ba sam.
Yayan Nibras bai fita a mota ba yay kiran Yaya Fawzan, lokacin yana rungume da Najma yana mata wayo, kamar bazai ɗaga ba ya dai amsa wayar dan Najma ce ta miƙo masa, cikin ɓata fuska ya ɗaga yana kaiwa kunnensa batare daya nutsu yaga ma waye ba. Sai da Yayan Nibras ɗin yay masa sallama sannan ya amsa yana ciro wayar a kunne yaga sunansa. Maidawa yay suka gaisa. Yayan Nibras yace gasu a gidan cikin mota shi da Nibras, idan ba damuwa zasu shigo ciki. Fawzan da sai ɗazun nan bayan la'asar yake farga da babu Nibras a gidan cikin ɗan furzar da iska yace, “Bismilla ku shigo”. Daga haka ya yanke kiran. Ganin yanda yay wani ciɗin da fuska yana kwanciya rigingine yasa Najma zuba masa ido, sai kuma cikin sanyin murya tare da kai hannunta saman jikinsa a kunyace ta ce, “Yaya miya faru ne?”.
Shiru yay na ɗan sakanni, kafin ya jiyo yana kallonta da idanunsa dake cike da soyayyarta, ganin damuwa a fuskarta itama sai ya gyara tashi ya murmusa yana mai jan hancinta kaɗan. “Soyayyar love ce ta ƙara ƙaruwa a zuciyar Yayanta mana”.
Murmushi ta saki yanda yake da zolaya na sake birgeta.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣3️⃣2️⃣
______________
........Murmushi kawai AA yay yana shafa bayan Maanal dake rusa masa kuka bil haƙƙi, sai da tafi mintuna biyu tana yi sannan ya ɗago fuskarta ya riƙe cikin tafukan hannunsa duka biyu. Kallonta yake sosai kamar yau ya fara ganinta, itako idanu a rufe tana kukanta kai kace saƙon mutuwar Babu aka kawo mata. Cikin wata irin murya mai fita da sanyi da kauri kaɗan, ainahin silent voice na masu aji da ƙarfin tasirin soyayya ya motsa lips a hankali ya furta, “I'm sorry”. Sai kuma ya sauke numfashi kaɗan tare da sake maida voice ɗin nashi can cikin maƙoshi, oily eyes ɗinsa na sake narkewa a kallonta ya sake furta, “Please for give me. Kin san in har ba kukan shagwaɓa kike min ba duk duniya babu abinda ke ɗaga min hankali irin hawayenki Besty, kece idanun Ajwaad kuma kece zuciyarsa. Sannan tattausar muryarki ce kawai kesa na jini a cikakken namiji. Why zaki dinga karya min zuciya da kukan ki. Ki gaya min laifina zan hukunta miki kaina duk da ina ji a raina na san laifin”.
“Ni ka daina yaudarata da daɗin bakinka, dan kasan bana taɓa iya samun nutsuwa da sukuni na awa guda batare da jin muryarka ba shiyyasa kake yarfani da hakan. Na kiraka 10 miss call plus amma kaƙi ɗaga min, idan kace baka gani ba da farko saboda uziri tsakanin kiran da yanzu awa nawa? Ni zaka yarfa Besty, ni Maanal ni zaka ma wannan abun saboda na gundirek.....”
“Noooo! Please Babie, ki daina faɗar haka, har abada bana jin ke dai zanji gundira dake koda na awa guda ne. Sai dai bazan miki gardamar samun saɓani na yau da kullum a tsakaninmu ba, wannan kuma normal ne ga ma'aurata Besty. Ire-iren abinda ya faru yau kuma shike kawo shi, dole ne ɗaya ya aikata wani abu ma ɗaya a bisa kuskure ko saɓani ko wani dalili, idan yayi uziri sai a samu maslaha. So Please kimin uzirin kema, duk da nasan a wannan gaɓar ni ne da laifi, amma ina da dalili, naje Kaduna ne, dan kar kisan ina can shiyyasa ban ɗaga ba nasan zaki iya saka min rigimar sai kinje shiyyasa kuma na ɓoye miki”.
Tunda ya ambaci Kaduna hawayenta suka tsaya cak. Ta wani sake zuba masa idanunta kamar zata cinyeshi da su. Da yasan maganar kadunar nan zata hasalata ma fiye da laifin farkon da yayi shiru. Haba tayi mamakin ganin ya saka manyan kaya batare da takurawarta ba, wai mi ake ɓoye mata ne? Ta fa tambayesa Ammie tunda suka tashi amma yace mata ai tana wajen Daddy, sai tai zaton can gidan Daddy tunda tasan sukan sauka idan sun shigo Abujan. Shiyyasa ko tambayar Oum batai ba dan tana jin nauyin hakan, da kuma taga kayan Ammie a ɗakin Oum sai ta sake yarda da maganarsa. Ashe ba haka bane, amma sai ta danne idanun nata na kallonsa ta ce, “Wajen wa?”.
AA bai iya ƙarya ba, idan ma ya kwatanta yi da wuri ake gano shi. Kuma Maanal da Oum sunfi kowa saurin harbo shi. Idanu ya lumshe a hankali ya sake buɗewa, sai ya ɗan cije lips kaɗan ya ce, “Wajen Ammie”.
“Ammie! Dama ba gaskiya bane da kace min tana wajen Daddy? Mi kake ɓoye min? Miyasa Ammie batace min ta koma Kaduna ba ɗazun da mukai waya? Kuma ina ƙyautata zaton kana tare da ita a lokacin ma?”.
“Karki damu zaki sani. Fara taimaka min nayi wanka dai Please”.
Baki ta tura masa zata bar kusa da shi ya riƙeta da ƙyau, sai kawai ya sake rungumeta sosai suna sauke ajiyar zuciya a tare.” daga haka dai ya lallaɓata ya ƙarasa taje mata gashin ya ɗaure mata shi, yana dariya a zuciyarsa da mamakin irin wannan saurin fushi da kuka, kodan ba damuwa yay da harkar mutane ba shiyyasa yake mamakin dama haka matan keyi idan suna da ciki. Abu kaɗan a tujareka aita zuba maka rigima, idan kace kaima hawa zakai kamar su tuni rayuka zasu ɓaci, dole kake dake zuciyarka ka sassauta koda kaji taka zuciyar ta hasala dan a wannan gaɓar ƙwarai da gaske su ɗin abin tausayi ne, kulawa da soyayyar miji kawai sukafi buƙata. ALLAH ya sakama iyaye da alkairi, sai yaji yana sake yima Mamy addu'ar samun sanyin zuciya akan tata damuwar, tare da yima Oum ta gamawa da rayuwa lafiya. Dan Mamy tasha wahalar rainon cikinsu da haihuwa, Oum kuma ta ƙarasa sauran wahalhalun raino zuwa tarbiyya har girma... Daga wanka aka tsaya wanke juna, balle yanda ake zabga ruwan sama dole ne ma'aurata su ji matuƙar jin kwanciyar hankalin yanayin tare da soyayya mai nagarta.....
______★
A wannan gaɓar Mamy ce can a sashenta ita kaɗai kamar mayya, sai su Haule dake ƙasa da bata ganinsu sai in waya ta kira tace su kawo mata wani abun. Yau gaba ɗaya ta cinye yinin ne cikin tunane-tunane da ƙulle-ƙullen abubuwa daban-daban. Musamman akan al'amarin Sille dana Oum. Sai kuma ga kira ta samu daga wanda ta sanya aiki dai-dai ruwan nan na sauka tana daga jikin bedroom ɗinta tana kallon compound ɗin gidan da motar AA data shigo. Sai da ya gama shigewa sashensu sannan ta saki labulen ta maida hankalinta ga wayar yanda ya kamata. Daga can ya ce, “Hajiya kina saurarena kuwa?”.
A dake ta ce, “Eh”.
Yaja fasali da fara mata bayani dalla-dalla. “Tabbas bincike ya tabbatar min sunan shi wannan mai zuwa wajen naki Junaid ne, kuma sunan mahaifinsa kenan shima Junaid. Kuma tabbas yana raye bai mutu ba.....”
Wani irin sakin wayar Mamy tayi a ƙasa jikinta na rawa. Batare data farga tama yadda wayar a ƙasa ba ta ce, “Junaid na raye?”.
Kasancewar a hans-free wayar take raɗam wancan yaji, bai kumayi ƙasa a gwiwa ba ya ce, “Kwarai da gaske yana raye. Dan shine ma ya raini yaron a Lagos na tsawon shekaru, kafin ya sake dawowa gida bayan an fidda rai yana a raye, tunda tsahon shekarun nan duk an fidda rai ya rasu ne sakamakon ɓacewarsa ɓat ta lokaci guda. Wanda duk ya gaya min ya kuma tabbatar min da babu wani abinda ba haka yake ba, saboda shine da idonsa yaga Junaid ɗin a Lagos har yazo gida ya sanarma iyayensa, bama su gaskatashi ba da farko sai da suka haɗa shi da wani yaje ya ganshi ya tabbatar da shine ɗin sannan. Bayan hakkane shi Junaid ɗin ma ya dawo gidan......”
Iya wannan bayanin kawai Mamy ta iya ji a cikin kunnenta, daga haka ta sulale ƙasa jagwab, ba suma tayi ba idanunta biyu amma komai ya tsaya cakk a jikinta hatta da jinta, sai wani shuuuiii duniyar ke mata kamar irin an kunna redio ɗin nan anƙi dacewa da tashar ƙwarai......
________★
Tunda Fawzan ya fito shi kansa Yayan Nibras ya fahimci ya samu natsuwa da kwanciyar hankali, dan sai wani irin glowing yake ƙyawunsa ya sake fitowa matuƙa alamar angwanci. Ko kallon Nibras Fawzan baiyi ba, ya zauna yana bama Yayanta hannu suka gaisa cikin mutunta juna dan shi kaf yayunta yana darajasu, hasalima ta wani ɓangaren yana haƙuri da halinta ne saboda su. Basu da yawan damuwa, duk da soyayyar da suke mata matuƙa suna mutuntashi da girmamashi da kiyaye haƙƙoƙinsa na miji a gareta. Suna cikin gaisawar ne Najma ta fito sanye cikin dogon hijjab har ƙasa. Dan Yaya Fawzan ɗin ya sanar mata baƙone harma da alaƙar, shiyyasa ta daure ta taso ta fito. Cikin girmamawa tama Yayan Nibras ɗin sannu da zuwa, shiko ya amsa mata da kulawa, bata zauna ba ta wuce kitchen, babu jimawa sai gata da ruwa da shayi data dafa ma Yaya Fawzan ɗin ɗazun bayan la'asar sakamakon ganin hadari, to bata kai ga bashi ba saboda yaje ya kanainayeta a ɗakin. Sai kayan gara