Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

AJIYA a DUHU Book 1 & 2 Complete Hausa Novel by Billyn Abdull

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   200 / 213

597K to 600K   out of 636.6K words

bata kula ba wata fa daga nan ake haɗa alaƙa. Watama ba mazan bane da mata ƴan uwanta take lalacewar, innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, mun ɗauki shaiɗanci abu mai sauƙi. Amma kam tabbas a yanzu wayoyinmu sune kawalanmu batare da mun fahimta ba. Amma Alhamdullah hakan ba yana nufin an taru an zama ɗaya bane. Dan wata mace wlhy ka ganta a media kamila, mumina ko ɗar baka ji idan ka ganta da waya koda tsakkiyar dare ne. Saboda abinda zai amfaneta kawai take yi sai nishaɗin yau da kullum. Wannan kam babban ƙalubale ne a gareka Sageer, dolene kuma ka tashi tsaye domin yin yaƙi da shi tun kafin al'amarin ya cigaba da nisa...”
          “Shiyyasa na sameka Toufeeq, dan a wannan gaɓar jinake kamar na haƙura na rabu da Huznah. Bazan iya rayuwa da macen da ba ni ne a zuciyarta ba. Gagangar jikinta kawai kenan na aura komi? Idan hakan ta kasance minene amfanin auren to? Gangar jiki wata rana tsufa zai risinar da ita ya tauyeta, itako zuciya da soyayya ta gaskiya har abada bata tsufa a zuciyar ma'aurata koda ɓacin rai ya danneta lokaci-lokaci sai ka samu tana motsawa.”
          “Hakane maganarka tana kan gaskiya. Amma bazan baka shawarar rabuwa da iyalinka ba. Kaima nasan kishi ne kawai ke cin zuciyarka. Dan haka kada kayi gaggawa. Amma kayi haƙuri ka ɗauki hakan matsayin ƙalubale da jarabawa. Sannan ka shirya fito mata ƙuru-ƙuru kawai tare da nasiha da lallashi da nusar da ita illar abinda take yi bayan ka nuna mata fushinka. Idan ta fahimta shike nan. Idan bata fahimta ba kaga sai muyi tunanin mataki na gaba ko”.
      Kai Sageer ya jinjina masa. Sai kuma zuwa can ya ce, “Shike nan na gode Toufeeq, zan gwada kuma na gani, in sha ALLAHU komi kenan zakaji”.
     “ALLAH ya kawo komai da sauƙi. Amma ka dage da addu'a dan ALLAH, komai yay tsanani maganin sa ALLAH”.
Kai kawai Sageer ya jinjina masa.....

___________★

          Anan Abuja kam Nibras da aka gama treating da magunguna iri-iri da aka amsa a wajen likitoci daban-daban a Nigeria da ƙetare ce ke shirin komawa gidan Darma. Duk da kuwa tunda Fawzan ya wuce basu taɓa waya ba. Maimakon ma ta damu ita hankalinta nakan AA, dan kuwa uwarta na nan na damuwa da tsalle-tsallen ganin ta samu lafiyar mahaifa ita tana nan tana shirya matakan takawa zuwa ga cimma AA. Dan a watan jiya ta cire tsoro ta fara tura masa saƙwannin soyayya ta WhatsApp da sabuwar number ɗinta. Sai dai tafi sati uku tana turawa kullum babu gajiyawa amma bai taɓa ko buɗe saƙon ba ma balle yasan tanayi. Sai ranar tana tura saƙon barka da juma'a taga an buɗe ko second biyu ba'ai ba. Kai tsaye ta fahimci a mistake ya taɓa irin saƙo ya shigo makan nan ka taɓa kawai. Tata jiran wani motsi ko zai duba amma bata sake jinsa ba, data cigaba da turawa kuma ba'a sake buɗewa ba. Ta tabbatar idan ta kira shi sai ya gane itace, dan haka ta koma turawa ta text message nan ma cike da roƙo da magiyar dan ALLAH ya saurareta. Amma har zuwa yau shiru kake ji. Ga wasu irin mahaukatan magungunan mata Mom ɗinta nata ɗura mata. Tun basa damunta har sun fara cizonta. Dan haka a karo na farko tace ita kawai a ƙarasa shirya mata komai ta koma tunda Yayanta yayi waya da Fawzan yace a satin nan suke saka ran dawowa matar Autansu kawai suke jira ta haihu. Wannan yasa shirye-shiryen komawar tata ya kammala tsaff dan so suke ana gobe zai dawo ta koma in sha ALLAHU.
      Kwance take yanzu ma a ɗaki ita kaɗai tunanin AA da sha'awar kasancewa da shi ta gama zagaye gurɓatacciyar zuciyarta, wayarta dake saman cikinta ta ɗauke ta shiga lalubo layin sa. Kawai sai zagayen cycle ɗin nan na dp ya nuna mata green alamar AA ya saka status. Mamaki ya kamata dan abinda bata taɓa gani yayi ba. Ko dp ɗinsa hoton agogone kawai a jiki, kuma tunda ta sanshi bataga ya taɓa canjawa ba. Da gudu ta danna, sai ko kai tsaye ya kaita status ɗin nashi, hoton jarirai guda biyu a cikin white showal da sky blue. Masha ALLAH yaran ƙyawawa masu matuƙar kamanni da juna, sai dai ƴan ƙananu da su dan basu da wani gurma. Gabanta ya faɗi wani ras. A take wata irin zufa ta shiga karyo mata, rawa jininta ya fara. Da gudu ta fito ta koma account ɗin Yaya Fawzan. Nan ma sai ga hoton jinjiraye ya rubuta Alhamdullah my boys sun iso. Tashin hankali, ai cike da rawar jiki ta dinga bin status na duk numbers ɗin ahalin Darma da take da number ɗin shi. Al'amarin kamar wani wutar jeji ko'ina ta shiga hotunan yaran ne ana musu addu'oi da su da mamansu. Ai bama tasan ta cillar da wayarta gefe ta fashe da kuka ba. Kuka sosai take yi jikinta har yana girgiza wa. Yanzu shike nan dai Maanal da gaske ta mata nisa tunda gashi har ta haihu da Ajwaad ɗinta. Haihuwar ma yara har biyu a lokaci ɗaya, ai ko wlhy bazata ƙyaleta ba, bazata barta ba, yanda tai mata wannan babban raunin a zuciya itama sai ta bar mata tabo a tata zuciyar. Dan duk abinda zatayi dan rabata da Ajwaad sai tayi.........✍️
     195


........Sai da ta gama haukarta da duƙe-duƙen alƙawarinta sannan ta tashi ta shiga bayi tai wanka, fitowa tai ta gyara jikinta tare da ƙarasa haɗa kayayyakinta sannan ta ɗauki wayarta, sai yanzu kuma wani tunani yake zuwa mata a rai, shin miyasa taga status ɗin AA? Hakan na nufin yayi saving number ɗinta kenan?. Sai kawai taji wani irin sanyi mai daɗi ya ratsa mata zuciya, murmushi ya kufce mata. Kaso ashirin cikin ɗari na nauyin da zuciyarta yay mata ya sauka. Haka ta shiga gunguro akwatina ta fito. Mom ɗinta na falo zaune sai Yayanta ɗaya da yazo gidan duk suka ɗago suna kallonta ita da akwatinan.
      “Ke lafiyarki kuwa? Ina zuwa da akwatina haka da yammar nan?”.
     “Mom gidana zan koma. Gara na koma yau Maanal ta haihu, Kinga kuwa daga yau zuwa koyaushe zasu iya dawowa ƙasar nan ko”.
         “To kuma shine dan rashin hankali babu bayani babu komai sai ki kama kinkimo akwatina zaki yafi? Ke wai yaushe zakiyi hankali ne dan ALLAH Nibras? Ke dai kullum kina girma amma gaki nan shashasha, sakara-sakara, gaula-gaula.”
    Baki ta cika da iska jin baƙaƙen maganar da Yayan nata ke jera mata. Idanunta cike da ƙwalla tace, “To amma Yaya Ma'aruff ya kake so nayi, kufa kuka matsa saina koma ɗin nan, naƙi kanata min faɗa kai da Yaya Asad, yanzu kuma na yarda zanyi abinda ya dace kana zagina. Suma can nazo ban koma ba ace ina baƙin cikin ta haihu har ƴan biyu”.
       “What! Yan biyu fa Nibras?”.
   Cewar Mom kafin Yayan nata yace wani abu. Idanun Nibras cike da hawaye ta ce, “Wlhy Mom ƴan biyu duk maza”.
     “Tab ɗi! Aiki ga mai ƙare ka. Lallai ita wannan da shirinta tazo...”
   “Shiri kuma kamar ya Mom, dan kawai ta haihu ƴan biyu shine kuma shiri? Ba ALLAH ne ya bata ba.”
         “Uhmm! Ku maza shashashai ne ba gane komai kuke ba. Ke ajiye akwatinan nan ki jirani zuwa anjima zan rakaki da kaina amma not now”.
      Sosai al'amarin ya girmi kan Ma'aruff. Sai yaji ma ya kasa yin magana ya miƙe kawai yay ma Mom ɗin tasu sallama dan ya fahimci yanzu hankalinta bama a kansa yake ba..
      Yana wucewa Nibras ta dasa sabon kuka, ita manufar kukanta daban, abinda Mom ɗinta ke fassarawa daban. Haka ta zauna ta lalace a lallashinta da tsara mata abubuwa babu kunya yanda zata dage wai itama ta samo cikin, idan kuma ya gagara nanda watanni uku dashen da Doctor ya basu shawarar yi shi zasu koma ai mata. Haka ta ƙara ɗiɗɗirka mata maganin mata da abubuwa iri-iri ta tattara mata sauran kayanta anayin sallar magrib suka tafi gidan Darma....

__________★
SAUDIA

         Ba'a basu damar ganin Maanal ba a lokacin, dan sunce sai an gama ƙara mata jinin da aka ɗiba jikin AA. Shima kansa AA ɗin basu barshi ya tashi ba sai bayan awa ɗaya ya samu natsuwa, haka suka dawo inda su Oum suke suka samesu cikin matsanancin farin ciki. Kafin ma su tambayi mike faruwa Oum ta fara basu labari, Ameerah ta nuna musu hotunan babys data ɗauka. A karo na farko kawai AA yaji jikinsa na tsuma koda wasan wasa basu taɓa kawoma ransu twin's ne a cikin Maanal ba. Dan basu ma taɓa yarda an duba musu mace ne ko namiji ba. Saboda duk abinda ALLAH ya basu suna farin ciki, hasalima sunfi ƙulafucin samun macen kodan basu da ita a gidan, dama Anum ce dan haka suka so yarinyar kamar ransu, yanzu kuma ta kufce ta barsu. A hankali AA ya zame yay sujidar shukur, kafin ya miƙe ya fita massallaci. Ai babu ɓata lokaci su Babban Yaya suka bishi, dan Abah ma yana can. Dukansu sai da sukai sallar godiya ga UBANGIJI tare da addu'oi, kasancewar azhar tayi suka gabatar sannan suka dawo. Zuwa lokacin an sake fito da yaran zuwa ɗakin da za'a maida mamansu dan dama sunje da su ne ana sake duba lafiyarsu da duk abinda ya dace. Babban Yaya ya fara amsarsu duka, ya rungumesu a ƙirjinsa yana mai jin ƙaunarsu tamkar Naufal. Yay musu addu'a sosai sannan Yaya Fawzan ya ɗauka. Shi kam ai sai da yaji hawaye na cika masa ido, yana masifar son yara a rayuwarsa kodan bai samu nashi da sauri bane. Amma haka yake ma su Naufal gata dama kamar kamar mi. Shima bayan ya gama rurrugumesu da musu addu'a mai gayya da aiki ya amsa. Shi kam da farko idanu ya zuba musu, zuciyarsa na wani irin rawa a cikin ƙirjinsa, shi Ajwaad Aliyu Abubakar Darma ne da ƴaƴa har biyu mallakinsa, ƴaƴan ma daga jikin Maanal Habib Giro Bestynsa. Yarinyar nan dai daya rayu da ita tun ƙuruciya, yay mata wanka yay mata wanki da abubuwa daban-daban, yarinyar da yake jinta tamkar jini da tsokar jikinsa, dan bai taɓa jin ƙaunar wata halitta bayan MANZON ALLAH da iyayyensa da ƴan uwansa irin Maanal ba. Da ace ana buɗe zuciya aga yanda asalin soyayya take da idan aka buɗe tashi sai masoya da kansu sun girgiza. A hankali hawayen da suka cika masa idanun suka ɗigo akan yaran, sai kawai ya rungumesu a cikin ƙirjinsa ya ɗauke hawayen batare daya bari kowa ya lura ba. Addu'oi sosai yay ma yaransa. Bai iya ya sake bama kowa ba sai da akazo aka amshesu dan ba'a son ana yawan daƙunasu. Daga nan ne fa suka fara kiran ƴan uwa nan Nigeria ana sanar musu tare da tura musu hotunan babys. Kafin wani dogon lokaci ahalin Darma ya ɗauki farin cikin ƙaruwa da suka samu. A kusa-kusa an haifa musu yara huɗu kenan. Ga ta RK, ga na Uncle Najeeb dan shima matarsa ta haihu namiji kusan wata uku kenan, tsakaninta da Nuwaira babu nisa. Ga kuma na AA har biyu. Saura Najma da Ameerah kuma da Maimoon, duk da dai na Maimoon basu da ƙarfi a kansa suna son kayansu..

      A ɓangaren Ammie ma da yaran gidansu tunda Oum ta kirata ta sanar suka kaure da farin ciki. Ammie harda hawayenta. Itama batayi ƙasa a gwiwa ba tai kiran Nene a waya ta sanar mata. Suma su Shahidah Aunty Sakeena ta kirasu ta gumtsa musu. Sai kuma ga hotuna AA ya turama Ammie da kansa. Suma nan suka fara yawo a tsakaninsu. ALLAH sarki Yaya Yazeed sai da yaji hawaye na neman cika masa ido, lallai ya yarda wani baya haihuwar ɗan wani. Yau ga ƴaƴan Ajwaad da Maanal dai a duniya. Hajiya Yaya kam kunya taji ta mamayeta, sai hawaye kuma suka shiga biyo baya. Ta zuba ma Yazeed idanu cike da tausayi da rauni ta ce, “Ka yafe min Yazeed, nasan na cutar da kai, na rabaka da Maanal bayan nasan kana sonta. Duk da dai wani baya haihuwar ɗan wani, haka wani baya auran matar wani. Amma nima nayi abinda bai kamata uwa tayi ba kodan ƙyawawan hakayyarka na ɗa nagari. Duk cikin ƴaƴana babu mai min irin biyayyar da kake min da hidima. Amma son zuciyata da zugar sabuwa ya kaini ya baroni na ƙuntata yarinya saliha irin Maanal....”
       “Dan ALLAH Mamma ki daina cewa haka, duk abinda ya faru yana cikin ƙaddara tane ai, tun farko kuma dama Maanal ba matata bace ba. Harga ALLAH kuma na haƙura dan ta dace da Ajwaad, shine ya cancanci dama aurenta kodan soyayyar dake tsakaninsu mai ƙarfi tun ƙuruciya. Nima in sha ALLAHU ALLAH zai bani tawa”.
      Ammie da zuciyarta ta ƙara raunana da tausayinsu tace, “In sha ALLAHU Yazeed ALLAH bazai taɓa taɓar da kai ba. Kuma ALLAH da zaka yarda mizai hana ayi ƴar gida kai da Khadijahn Kano, yarinyar nan nada nutsuwa da hankali. Gata da iliminta na addini dan Kawunku Sani baya wasa da ilimin addinin yaransa. Amma fa idan har kaji ta maka dan babu mai sake tirsasaka auren wanda baka so kaji”.
      Murmushi Yazeed yayi yana wani sinnar da kai, ƙasa-ƙasa yace, “Ammie in dai tana sona mizai hana na amince”.
    Yanda yay ɗin sai ya bama Daddy da Ammie da Hajiya Yaya dariya dan duk suna a falon Daddy ɗinne. A karo na farko Daddy ya ce, “Wannan kuma aikinka ne Son, kai zaka sameta ka koya mata soyayyar ka. Mu namu addu'a ne da farin ciki, dan suma ƙannan nan naka na gaji da zamansu haka, zan basu gargaɗi na ƙarshe idan son samu ne zuwa ƙarshen shekarar nan kaga sai a haɗa duka na aurar daku nima na huta, sai nasan hidimar ƙannenku ne kawai ya rage min”.
         “Karka damu Daddy in sha ALLAHU zamuyi ƙoƙari, yaran nan kuma ka barni dasu kawai yanzu lokacin da zaka fara hutawa ne”.
      Sosai Daddy yaji daɗin bayanin Yazeed, hakama su Ammie da Hajiya Yaya....

★★

      Kamar yanda doctors suka faɗa basu sami ganin Maanal ba sai dare, kusan 8 ta farka daga barcin da suka sakata sannan aka barsu shiga ɗakin da take ita da babys ɗin. Tunda suka shigo ta zuba musu idanunta da suka shanye suka ɗan kumburo. Suma kallonta suke kowanne fuska da murmushi, Oum ta zauna kusa da ita tana mai kamo hannunta cikin nata, Abah kuma ya zauna a kujerar kusa da gadon, sai AA ya zagaya can ɗayan gefen shi da su babban Yaya. Ameerah da Najma na zaune suma a bakin gadon ta gefen da mazansu suke.........✍️
     

196


........A hankali ta motsa lips ɗinta ta ce, “Oumna? Abanah!”.
      Cike da so da ƙauna suka amsa mata a tare, sai kuma ta kalla Ameerah da Najma suma ta kira sunansu. Amsa mata sukai suma cike da farin ciki. Ta sake juya kanta a hankali ta kalla Babban Yaya da Fawzan suma tace, “Yayana, Yaya F.” Suma da kulawa suka amsa mata fuskokinsu da murmushi har babban Yaya da kakan daɗe baka yana yi ba. AA ta tsare da kallo na sakanni, shima kallon nata yake ƙasa-ƙasa, yana jira a kira sunansa yaji tsitt. Sai kawai catai “Yaya F. Wanene wannan?”.
     Mi zasuyi inba dariya ba, musamman Yaya Fawzan. Ya ce, “Lilly baki ganesa ba ko?”.
     Kai ta jinjina alamar e. Aiko aka sake sanya dariya. Babban Yaya shima dai yau ya ɗana. Ya ce, “Lilly wani ɗan riƙo ne da aka kawo mana kin manta da shi, miskili, rigimamme ga dukan yaran mutane saboda Bestynsa. Ga kishi da duk wanda ya kula masa ita. Idan kaga yana dariya sai da besty, idan kaga yana surutu sai da Besty”.
     A hankali tana murmushi ta ce, “Lah Yaya na tunashi. Yaushe yazo?”.
AA dake kallonta yana murmushi ya duƙo yana dungure mata kai kaɗan, cike da raɗa yanda ita kaɗai ta jisa duk da suna a kusa da su ya ce, “Randa na baki cikin my twins baby's nazo.”
         Sosai maganar ta bata kunya, tasa hannu ta ture masa fuska. Su dai su Abah murmushi suke cike da jin daɗi da farin ciki. Irin wannan yanayin yake fatan dinga ganin iyalansa a ciki akoda yaushe, yana son farin cikin iyalansa matuƙa. Dan haka yake jin daɗin ɗan zaman nan nasu na saudia kamar su kasance a haka dindindin. Amma ba komai, ko Nigeria suka koma ya shirya tsaff da sabon shirin gyara zamantakewar gidansa fiye da ta baya in sha ALLAHU...


_________★


Amarya Hajiya Basariyya dai ta tare gidan Alhaji Balala. Bayan yayanta da Uncle Faruk da Kawu Manu sun mata faɗa sosai da nasiha. Maƙwafta da abokan arziƙin iya sukai mata rakkiya a motar Yayanta driver ya kaisu. Dan duk da Alhaji Balala ya turo mashina dan ya burge Yayanta ya hanasu hawa. Hajiya Basariyya zata iya rantsewa bata taɓa shiga baƙin cikin rayuwa irin na yau ba. Ji take kamar zata mutu, babu abinda ke dawo mata a zuciya da ruhi sai fuskar Daddy. Ƙyaƙyƙyawan mutum ɗan gaye ga son ƙamshi da tsafta. Iya magana ga ilimin addini dana zamani. Kuɗin idan ka ƙwanƙwasa kuma akwaisu masha ALLAH. Iya ƙoƙari yanayi akansu su iyalanshi. Ga jarumta dan duk da shekaru sunja su duka ukun Daddy yana iyawa da su har ke da kika kwana da shi sai kinji a jikinki. Hakan kuma baya hana washe garin kwananki ya sake jigataki, girkin wata ya shiga washe gari itama ta samu makamancin farin cikin da kika samu. Duk da wannan ƙyaƙyƙyawar rayuwar data rayu a cikin kusan shekaru ashirin da tara yanzu ta ƙare a auren ƙauye, ƙazamin mutum irin Alhaji

200 / 213

Chapters