AJIYA A DUHU BOOK 1 & 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Billyn Abdull Category :  African Stories & Novels

Chapter   155 / 213

462K to 465K   out of 636.6K words

hijjabin ya kwantar da ita a jikinsa ya rungume. Cikin kunnenta ya ce, “Love bafa haka ake gaida miji ba.” murmushi tayi mai sanyi ta ce, “To kayi hakuri zan gyara”. Idanunsa ya lumshe, yana jin daɗin yanda komai yace bata masa musu. Sun daɗe shiru na wani lokaci, kafin ya lalubo lips ɗinta ya haɗe da nashi. A tsorace take matuƙa, amma batai masa musu ba ta barshi yay yanda yake so. Har ya haƙura ya barta dan kansa ya rungumeta kawai, a hankali ya fara sauke numfashi alamar barci ya ɗaukesa. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya ranta fal farin ciki yau gata a jikin Yaya Fawzan. Rayuwa kenan, watanni biyar da suka wuce ko a tunani bata taɓa kawo hakan a ranta ba, tsakaninsu da Yayunsu girmamawace da kyautatawa. Sunama juna ƙauna irin ta yan uwan taka, amma a yanzu jitake Yaya Fawzan shine duniyarta, shine farin cikin ta. Kaunarsa take matuƙa a ƙarƙashin zuciyarta. Fatanta ALLAH ya bata ikon faranta masa, ya kuma bashi ikon sauke hakkin su. Nibras ta faɗo mata a rai, sai kawai ta kauda tunaninta ta gyara kwanciya a jikinsa itama barcin yay gaba da ita.....

________★

       Anan Abuja ana bidiri, acan Kaduna kam al'amari ne babba ya faru. Ammie da Hajiya Basariyya duk suna nan Abuja wajen biki. Yaran Hajiya Basariyya suna Zaria suma basu koma Kaduna ba. Hakama Daddy tun ranar ɗaurin aure daya taho da Hameed da Waleed basu koma Kaduna ba ya zauna yin wani aiki da da Yaya Yazeed ne keyinsa. Shigowar wannan matsalar tashi kuwa duk ya saki abubuwan ya tare a jikin Nazeera. Sai abinda tace yayi yake yi. Shiyyasa Daddyn ya dakata yin aikin Hameed na taimaka masa duk da yaron sai yanzu ne yake js2 a Secondary. Amma da yake yana da kwazo da fahimtar abubuwa sai Daddyn ke sashi yana taimaka masa da ƙananun abubuwa.
     Hajiya Yaya ita kaɗai ce a gidan sai ƴaƴanta. Sai Nazeerah da Yaya Yazeed da sai ma ka jima bakaji motsinsu ba. Tunda Daddy yabar gari mijin Sabuwa biye yake da shi, dan haka shima anan yake nasa shiri. Yau kuma daya kammala komai yay kiran Yazeed a waya. Lokacin yana ɗan barcinsa da Nazeerah ta barsa yi da ƙyar, dan jarababbiya ce ta bugawa a jarida. Shi kuma gashi ALLAH bai yosa mai yawan damuwa ba. Indai ya samu ya biya buƙatarsa dan kwana biyu uku ma sai ayi bai nema ba. Amma ita babu fashi babu ɗaga ƙafa. Kuma dole yay mata yanda take so babu abinda ya shalleta da baya ra'ayi. Wayar ta katse aka sake kira, cikin haushi Nazeerah ta ɗauka da nufin kashewa sai taga sunan Babanta. Aiko wani irin duka ta ɗakama Yazeed ya farka a firgice. Harara ta watsa masa tare da jefa masa wayar tana faɗin, “Kaifa wani lokacin wawa ne, to ihu zaka mana da”.
     A jiyar zuciya ya sauke. A ƙasan ransa yana jin zafin zagin data masa, amma a zahiri sai yace, “Kiyi haƙuri na tsorata ne.”
     Tsaki taja ta maida kanta ta kwanta, cike da wulaƙanci tace, “Tashi kaje can falo ka amsa bazaka daman ba anan barci zanyi. Shima Daddy ya wani kama kiran mutane a cikin dare suna hutawarsu. Mtsowww ”. taja tsaki. Jallabiya Yazeed ya ɗauka ya sanya, sannan ya fita dai-dai kiran baban Nazeera ɗin na sake shigowa. Cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya shiga gaisheshi harda duƙunnawa kamar yana a gabansa. Daga can baban Nazeera ya amsa cike da isa, kafin cikin bada umarni ya ce, “Yazeed kana jina”..........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣1️⃣6️⃣

______________

Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍

‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

Gyaran gashi da kitson zamani

Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido

Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai

Kayan gyaran fata na gaske

Lalle mai kyau da salo na zamani

Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi

Shirin amare da na musamman

Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391

Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge

__________

.........Murmushi Aunty tayi da girgiza kai, cikin rashin damuwa ta ce, “Wanda dai kika haifa mata ɗinne, kika kuma ɗauka da hannunki kika bata a gaban shaidu halak malak. Kika kumayi alƙawarin wannan ƙyautar bazata taɓa tashi ba har abada. Ni kinga tafiyata, ya kamata dai kima kanki faɗa akan ƴan uwan nan namu kamar yanda na baki shawara, idan ba haka ba bayan ƴaƴan har muma dangin naki sai kin rasamu ɗaya bayan ɗaya dan zuciya nason mai ƙyautata mata”. Daga haka tai ficewarta.
     Idan ana suman zaune to yau shi Mamy tayi kalaman Aunty na jijjiga mata zuciya. Yaushe lalacewar tata takai haka da Aunty ke datsa mata irin wannan maganganun babu ko risinawa. Eh lallai da alama ta fara sakaci da kanta, shiyyasa itama Nana yanzu take kunno mata wasu baƙin ɗabi'u, jiya fa ƙiri da muzu ta tafi ta tare a sashen ƴarta kota kanta batabi ba, yau kuma ga aunty na gaya mata magana akan Fateema da ƴan uwansu.....

       (😆Kamil-mil ta malam Aliyu Darma kenan😜)

_______★

         Matuƙar jin jiki Ameerah tayi a hannun Babban Yaya, kuka kam tasha har sai da muryarta ta dushe. Shi kuma yanata aikin lallashi da kalamai masu taushi da sanya mata albarka. Makarar da suka nema yi ya sashi barinta ya gyara jikinsa ya tafi sallar asuba. Ana idarwa bai tsaya ya haɗu da kowa a yaran nan ba dama su Abah ya baro massallacin. Sai da ya haɗa tea a kitchen ya hau sama ya ɗakko magani sannan ya koma ɗakin Ameerah. Barcin wahala ya ɗauketa yanzu kam, dan haka cikin lallashi ya shiga tada ita. Da shagwaɓar kuka ta farka masa, shi dai yanata ban baki da lallaɓa. Sai da tai shiru yay ƙoƙarin miƙar da ita dan taimaka mata tace ita bata so ya kira mata Maanal.
     Shiru yay yana kallonta a karo na farko, sai kuma yay ɗan murmushi da faɗin, “Bazai yiwu ba My Soha, karfa ki manta Lilly autarmu ce, taya zan yarda tazo taga wannan ɗanyan aiki da yayanta ya tafka. Adai yi haƙuri a tausaya min komai kike so zan miki. Gwara-gwara ma kice in kira miki Aunty Majdiya ko Aunty Siyama”.
      Kafaɗa ta maƙe ta ce, “Uhm-uhm ni ina jin kunyarsu gaskiya”.
   “To nima ina jin kunyar Lilly gaskiya. To kawai ki bari ni da nai aika-aikata nai aiki na ba shike nan ba. Amma kiran Lilly ai akwai ƙura babba”.
         Rigima ta cigaba da masa, ya cigaba da lalaɓata shima, tare da nuna mata agogo lokacin salla na sake nisa. Dole ta yarda yay mata dukkan abinda ya dace, ya gasata yanda ya kamata dama batai zaton zai iya ba sannan ya ɗakkota har kan abin salla. Shi ya saka mata riga da hijjab tai sallar, zata kwanta a wajen ya riƙeta a jikinsa ya bata tea ɗin nan tasha ya bata magani. Sake ɗaukarta yay ya maida a saman gadon daya canjawa bedsheet, ya kwanta shima ya sakata a jikinsa yana raɗa mata, “Oya sleep” a cikin kunne. Ajiyar zuciya kawai ta saki dan tasan dai itama tana buƙatar barcin sosai tunda bai barsu sunyi ba sam, a hankali ta lumshe idanu. Shi ko yana shafa kanta a hankali a haka shima barcin yay awon gaba da su su duka biyun zukatansu cike da nutsuwa da ƙaunar juna mai ban mamaki......

Hummm su Babban Yaya🤭na daiyi shiru kawai🏃😂
______★

         Yaya Fawzan kam da aka garƙame a cell barcinsa gaba ɗaya mafarkin Najma ne, koda ya farka da asubahi sai yaga wayam babu Nibras a ɗakin. Ƙwafa yayi cike da jin zafi a ƙasan zuciyarsa ya sakko a gadon. Sai kuma gata ta fito daga bayi alamar wanka tayo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Ta wuce tana ƴar dariyar mugunta duk da itama ranta a ƙuntace yake har kuka tayi bayan yayi barci, dan wayar da yayi da Najma jiya da dare a gabanta ta tsaya mata a zuciya. Badan karma yaga gazawarta ba data buɗe masa ƙofar tun daren, amma koba komai gara su kwana a ƙuntacen su duka, ƙofar ta buɗe ta fice gaba ɗaya a dakin tana waƙa. Guntun murmushi ya saki yana mai cije lips, a fili ya furta, “Anjima kaɗan zakiyi kuka yarinya. Kukan jiya da daren ma da kikai ina jinki”. Bathroom ya shiga, dole yay wanka kafin shirin massalaci. Koda ya sakko ɗakin Najma ya nufa, jin ƙofar a rufe sai yay knocking. Cikin mayen barci Najma ta taso ta buɗe masa, ya ɗan zuba mata idanu ganin yanda kayan barcin suka kwanta a jikinta suka mata ƙyau. Kauda kansa yay, cike da kulawa ya shafa fuskarta da faɗin, “Sorry Love na tashe ki ko, lokacin salla yayi ne”.
     Kanta ta jinjina masa, sai kuma a ta furta, “Thanks you Yaya”. Cikin yanayin muryar barci. Aiko sai da tsigar jikin maza ta tashi. Ya dai dake yace, “Nazo na taimaka miki kiyi alwalar? Naga kamar akwai barci a idonki”.
      Kanta ta girgiza masa, sai kuma ta ɗan kallesa ta maida kanta ta duƙar. “A'a Yaya kaje massalacin ka zan iya. Aina tashi”.
     “Kin tabbatar ”.
Nan ma kan ta jinjina masa. Ya ce, “To oya, aimin addu'a fa ALLAH ya bani ƴan uku masu kama da ƴar Zaria”.
     Fuskarta da murmushi tace, “In sha ALLAHU, amma masu kama da ɗan Darma nafi so nikam”.
   Shima sai ya murmusa yana rufe mata ƙofar ya wuce massalaci. Koda ya dawo kai tsaye ɗakin nata ya nufa, ya sameta a kan sallaya tana azkar. Sai ya zauna a bakin gadon shima yana tashi. Koda ya idar ya fahimci itama ta idar cike da kulawa yace, “Taso mu kwanta barci nake ji sosai Love”. Gaban Najma ya faɗi, amma dai ta daure ta miƙe. Batare data cire hijjab ɗin ba taje gabansa ta rissina tana gaisheshi. Maimakon amsawa sai ya kamota ta hawo saman gadon, ya zame mata hijjabin ya kwantar da ita a jikinsa ya rungume. Cikin kunnenta ya ce, “Love bafa haka ake gaida miji ba.” murmushi tayi mai sanyi ta ce, “To kayi hakuri zan gyara”. Idanunsa ya lumshe, yana jin daɗin yanda komai yace bata masa musu. Sun daɗe shiru na wani lokaci, kafin ya lalubo lips ɗinta ya haɗe da nashi. A tsorace take matuƙa, amma batai masa musu ba ta barshi yay yanda yake so. Har ya haƙura ya barta dan kansa ya rungumeta kawai, a hankali ya fara sauke numfashi alamar barci ya ɗaukesa. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya ranta fal farin ciki yau gata a jikin Yaya Fawzan. Rayuwa kenan, watanni biyar da suka wuce ko a tunani bata taɓa kawo hakan a ranta ba, tsakaninsu da Yayunsu girmamawace da kyautatawa. Sunama juna ƙauna irin ta yan uwan taka, amma a yanzu jitake Yaya Fawzan shine duniyarta, shine farin cikin ta. Kaunarsa take matuƙa a ƙarƙashin zuciyarta. Fatanta ALLAH ya bata ikon faranta masa, ya kuma bashi ikon sauke hakkin su. Nibras ta faɗo mata a rai, sai kawai ta kauda tunaninta ta gyara kwanciya a jikinsa itama barcin yay gaba da ita.....

________★

       Anan Abuja ana bidiri, acan Kaduna kam al'amari ne babba ya faru. Ammie da Hajiya Basariyya duk suna nan Abuja wajen biki. Yaran Hajiya Basariyya suna Zaria suma basu koma Kaduna ba. Hakama Daddy tun ranar ɗaurin aure daya taho da Hameed da Waleed basu koma Kaduna ba ya zauna yin wani aiki da da Yaya Yazeed ne keyinsa. Shigowar wannan matsalar tashi kuwa duk ya saki abubuwan ya tare a jikin Nazeera. Sai abinda tace yayi yake yi. Shiyyasa Daddyn ya dakata yin aikin Hameed na taimaka masa duk da yaron sai yanzu ne yake js2 a Secondary. Amma da yake yana da kwazo da fahimtar abubuwa sai Daddyn ke sashi yana taimaka masa da ƙananun abubuwa.
     Hajiya Yaya ita kaɗai ce a gidan sai ƴaƴanta. Sai Nazeerah da Yaya Yazeed da sai ma ka jima bakaji motsinsu ba. Tunda Daddy yabar gari mijin Sabuwa biye yake da shi, dan haka shima anan yake nasa shiri. Yau kuma daya kammala komai yay kiran Yazeed a waya. Lokacin yana ɗan barcinsa da Nazeerah ta barsa yi da ƙyar, dan jarababbiya ce ta bugawa a jarida. Shi kuma gashi ALLAH bai yosa mai yawan damuwa ba. Indai ya samu ya biya buƙatarsa dan kwana biyu uku ma sai ayi bai nema ba. Amma ita babu fashi babu ɗaga ƙafa. Kuma dole yay mata yanda take so babu abinda ya shalleta da baya ra'ayi. Wayar ta katse aka sake kira, cikin haushi Nazeerah ta ɗauka da nufin kashewa sai taga sunan Babanta. Aiko wani irin duka ta ɗakama Yazeed ya farka a firgice. Harara ta watsa masa tare da jefa masa wayar tana faɗin, “Kaifa wani lokacin wawa ne, to ihu zaka mana da”.
     A jiyar zuciya ya sauke. A ƙasan ransa yana jin zafin zagin data masa, amma a zahiri sai yace, “Kiyi haƙuri na tsorata ne.”
     Tsaki taja ta maida kanta ta kwanta, cike da wulaƙanci tace, “Tashi kaje can falo ka amsa bazaka daman ba anan barci zanyi. Shima Daddy ya wani kama kiran mutane a cikin dare suna hutawarsu. Mtsowww ”. taja tsaki. Jallabiya Yazeed ya ɗauka ya sanya, sannan ya fita dai-dai kiran baban Nazeera ɗin na sake shigowa. Cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya shiga gaisheshi harda duƙunnawa kamar yana a gabansa. Daga can baban Nazeera ya amsa cike da isa, kafin cikin bada umarni ya ce, “Yazeed kana jina”..........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣1️⃣7️⃣

______________

........“Eh Daddy ina ji”.
   “Yauwa aiki zan saka ka yanzun nan. Kaje sashen Babanka ka buɗe wardrobe ɗinsa ka bincika min ko ina na cikinta ka tattaro min takardun duk wata kaddara da dukiyarsa. Ka ɗaga har ƙasan gado. Na baka daga nan zuwa asuba zan kiraka ka fito waje ka kawo min”.
      Ɗan jimm Yazeed ɗin yayi, baban Nazeera ya daka masa tsawa. A firgice ya ce, “To Daddy an gama an gama kayi haƙuri idan ranka ya ɓaci, nama san duk inda yake ajiyewa ai”. Har tuntuɓe yake ya fice zuwa sashen Daddy. Ya taɓa ƙofar a kulle sai ya shiga laluba jikinsa. Jin babu key ya juya ya koma sashensu. Ɗakinsa ya wuce ya ɗakko key ɗin sashen Daddy da yake da shi kamar wanda ake controlling da remote jikinsa har rawa yake yi. Haka ya buɗe ya shiga. Duk da ba shiga ɗakin barcin Daddy yake ba sai inta kama kai tsaye yasan inda duk Daddy ke ajiye abubuwansa mai muhimmaci. Aiko ko cikin minti talatin ma ya tattara komai a cikin akwati ya fito, Baban Nazeera ya kira, ya sanar masa gasu. Abun sai ya bashi mamaki, jin an samu wannan da sauki sai yace, “Kaima jeka tattaro min naka. Ka kuma shiga sashen matan Babanka dana uwarka duk gwalagwalansu da nasu takardun ka tattaro min”.
     “To Daddy an gama” Yazeed ya faɗa yana nufar sashensu. Kaf abubuwansa hatta atm bai bari ba sai da ya tattaro. Harda su system ɗinsa ta aiki duk ya tattara ya haɗe dana Daddy sannan ya fito. Sashen Hajiya Basariyya yaje, ya taɓa ƙofa a rufe nan ma, sai ya zagaya ta kitchen, bawan ALLAH sai zufa yake, cikin sa'a nan a buɗe yake. Aiko ya shiga, kai tsaye bedroom ɗinta ya shiga. Ita kam bai san inda take ajiye abubuwanta ba sai da yasha wahala sosai kafin ya gano, aiko kaf ya tattaro harda sarƙoƙin ƙanensa na gwal da nata, da takardun kaddaririnta da take tunƙaho da su. Dana yaranta dan Daddy duka yayansa babu wanda bai mallakawa takardar fili ba da anan gaba zai amfana da shi. Sai da yay mata kat sannan ya shiga ɗakin ƙanensa nan ma yay kaca-kaca da shi sai dai bai samo komai ba sai takardunsu na makaranta, dan Hajiya Basariyya bata barin komai a hannunsu. Daga nan sashen Ammie ya nufa, can dai tako ina a kulle dan Sakina sai da ta rufe ko ina saboda tsoron halin Nazeerah sannan ta wuce. Harta window ya gwada shiga amma bai samu dama ba dole ya haƙura ya siɗaɗa sashen Hajiya Yaya. Kai tsaye ɗakinta ya nufa, tana barci motsinsa ya sakata farkawa. Da farko firgita tayi, sai da ta kunna fitila taga shine sai mamaki ya kamata. Ta shiga yimasa magana cikin faɗa, kawai yazo yasa abu ya

155 / 213

Chapters