Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
bara na nemi abokina Deen”......
_________★
Sen.. Bukar tare da abokan tafiyarsa na zaune cikin farin cikin nasarar da suka samu ga gasashen rago da drinks zagaye da su cikin katafaren falon da suke zaune. Babu abinda suke sai maimaita videon abinda ya faru da aka tura musu akai musu connecting ɗinsa da television suke suna kwasar dariya. Senator Mai-hula ya danna nama a bakinsa yana faɗin, “Wato Kaugama kai shegen kanka ne, yanzu na yarda da maganar ka da kake cewa faɗan fito-na-fito da yaron nan ba namu bane kodan siyasar mu, jiba cikin abinda bai wuce awa biyar ba ka sake hargitsa zukatan ahalin Darma gaba ɗaya, musamman shegen yaron nan mai taurin kai da izzar banza da wofi. Yanzu sai muga zai dawo da ubansa ne, ko zai ƙwato yan garin surukansa, ko zai ji da kunyar mugun halin uwarsa. Wato matar nan fa da namiji ce itama shegiya za'ai a ƙasar nan”.
Dariya suka sake kecewa da ita. Alhaji Sallau ya amshe zancen da, “Ai ko yanzu sunanta ya shiga tarihin manyan jaruman shegun Nigeria, ni yanzu duk ba wannan ne damuwata ba ma, so nake kawai naji an sanar da mutuwar Aliyu Darma, sai kuma su Mabera suma naji jami'an nan sun kashe mana su shike nan ƙurun ƙus kan ɗan ɓera tatsuniyar ta ƙare”.
“Inafa zata ƙare Alhaji Sallau. Ai in kaga ta ƙare to shima wannan yaron AA Darma mun ƙarar da shi. Idan ba haka ba fa zai kasance mana tamkar mun kashe MACIJI ne bamu sare kansa ba. Shifa wannan shegen yaron tamkar ubansa yake wlhy babu abinda ya bari nashi. Kaga kuwa ai akwai sauran tsalle idan har bamu kwantar da shi ƙasa ba. Kawai ni abinda nake tunani mizai hana wannan wasan garin surukan nashi mu juyashi ya koma kansa kawai kunga mun jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya ko”.
“Tabbas maganarka nakan hanya Hon... Ishaya Badikko. To amma ta yaya zamuyi hakan kenan?”.
“Kowa ya ɗanyi nazari na mintuna muga, idan bamu sami mafita ba sai mu barma gobe ko”.
Duk sun gamsu da hakan, sai dai me a dai-dai lokacin da sukai shirun domin nazari a lokacin wayar Sen... Bukar ta shiga rurin neman agaji. Kamar zai share sai kuma ya ɗaga ganin Oler ne mai kiran sashi. Cikin harshen turanci Oler ya sanar masa akwai matsala fa. Ya duba media yanzun nan an sanar da kama Mabera da ɗansa har ma an iso dasu cikin Abuja suna Genaral hospital. Tsabar tashin hankali ruɗani da bugawar zuciya data samu Sen... Bukar a lokaci guda baima san ya saki wayar ƙasa ba shima ya tafi luuuu yana neman zubewa sai da abokan nashi suka taroshi.
Tambayarsa suke miya faru, shi kuma faɗi yake, “Mun shiga uku, na shiga uku shike nan an yanka ta tashi. Komai ya lalace wlhy”.
“Wai mike faruwa Senator, Dan ALLAH ka gaya mana idan na tayaka kuka ne muyi tare, idan na taimakonka ne mu taimake ka. Amma kana abu kamar ba namiji ba”.
Feettttt!!! Sen... Bukar ya fyace majina yana taba idanu da faɗin, “Bazaka gane ba Alhaji Sallau, wlhy akwai matsala, akwai babbar matsala ne. An kama Mabera da ɗan sa, Mabera da ɗansa na'a hannu yanzu haka kuma babu wanda ya harbesu an dai kaisu asibiti.”
Gaba ɗayansu suma sai da suka razana. Senator Mai-hula yace, “Amma taya haka zata faru? Kenan su Devid amanarmu sukaci? In ba amanarmu ba taya sun ganshi bazasu kiramu su sanar mana ba ko su kashe shi”.
Kasa ma cewa komai sauran sukayi dan tashin hankali. Sai kuma kowa ya ɗauki wayarsa suka shiga bibiyar labarin. Mizai faru sai kuma sukaci karo da maganar data sakasu miƙewa tsaye a lokaci guda. Cikin haɗa baki batare da sun shirya hakan ba suka furta, “What?!!! Aliyu Darma ya farfaɗo shima!!?”.....
Ehem-ehem!! Wannan shine asalin an yanka ta tashin fa, ko nace AJIYA A DUHU 😆🙏.
_______★
A gidan Darma hankalinsu nakan ceto rayuwar ahalin garin Giro anan asibiti cikin hukunci da aminci na UBANGIJI Abah ne ya farfaɗo. Wannan farfaɗowa ce da su kansu su Abbu basu saka rai da samuwarta anan kusa ba ga Abah. Dan gubar ta riga ta fara tasiri mai ƙarfi a jikinsa tsahon kwana biyu fa. Kawai dai sunƙi faɗama su Baba Sardauna gaskiya ne saboda kar hankali ya tashi, sai shi da su RK ne ke cikin tashin hankalin kawai da jiran hukuncin ALLAH. Amma sun gama sallamawa da Abah ba zai sake wata rayuwa mai tsaho a wannan duniyar ba. Dan da nan likitoci suka rufu a kanshi. Su Gwaggo Khadijah dake asibitin sai addu'a suke, sun kira su Baba dake gida suma.
Farkawar Abah ta raba hankalin ahalin Darma biyu, duk da haka basu kuma fasa maida hankali akan alkairin da sukai niyyar yi akan ceto mutanen garin Giro daga halin da aka jefa musu rayuwa ba. Addu'oi kuma basu bar bakinsu ba sam.. Fin awa biyu su Abbu dake fama da tsufansa na kai-kawo akan Abah har ALLAH ya daidaita komai cikin ikonsa. Da gaggawa suka buƙaci jini, dan haka babu ɓata lokaci jinin AA da kowa yasan yana ma Abah ɗin, kai kowa ma yana iya baiwa jini sai Uncle Sulaiman Yayan RK da shima irin jininsu ɗaya da AA ɗin aka ɗiba, sai Lamiɗo shima Autan su Abah ɗin da suke uwa ɗaya uba ɗaya. Haka aka ɗiba jininsu su ukun bayan an tabbatar babu wata matsala a tare da su sannan aka saka masa. Bayan an samu nutsuwar saka masan ne Abbu ya buƙaci yin magama da su baba Sardauna a office ɗinsa. Dan haka shi da Baba suka shiga suka sameshi sai Babban Yaya da Uncle Mahmud..........✍️177
........Bayan Abbu ya gama rubuce-rubuce a nutse ya ɗago yana kallonsu. A nutse cikin kuma lallashi da son kwantar da hankalinsu ya ce, “Rayuwarsa ta samu ceto bisa ƙarfin ikon ALLAH, dan wlhy mu kammu mun fidda rai daga rayuwar Aliyu, munyi muku shiru ne kawai dan kar mu tada muku hankali harta ALLAH ta kasance. Amma gubar ta bar wasu tasiri a jikinsa da muke fatan UBANGIJI daya dawo mana da rayuwarsa a gaɓar da muka sallama zai magance mana su ɗaya bayan ɗaya. A yanzu zai iya fuskantar irin su bugun zuciya da hauhawar jini da matsalar mantuwa. Dan haka akwai buƙatar a kula da lafiyar ƙwaƙwalwasa da tunaninsa. Zamu dinga duba shi akai-akai saboda gudun abinda zai iya biyo baya. A yanzu zamu duba lafiyar zuciyarsa, gwajin jini da fitsari, sai ƙoda da hantarsa. Mu dukanmu kuma zamu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kiyaye wasu abubuwa gudan faɗawarsa a depression. Zamu tabbatar yana shan magungunan sa akan lokaci. Zamu taru mu karfafa masa gwiwa da kulawar farin cikinsa da kowane motsinsa. Zamu guji sa shi cikin tashin hankali, ko maimaita zancen abinda ya faru baya da zai sake tada masa hankali ko tuna masa abubuwan da suka farun. Ina ganin ma nan da kamar sati biyu idan abubuwa sun sake lafawa ya kamata abar ƙasar da shi ta yanda zai samu hutu da sake mantawa da komai in sha ALLAHU”.
Duk sun gamsu da bayanin Abbu, atare suka tabbatar da zasu bada haɗin kan da duk ake buƙata....
________★
An samu nasarar cafke Rabilu a gidan da yake haya a die-die. Dan kuwa bayan sun dawo daga Giro maƙudan kuɗaɗe abokan Sen... Bukar suka bashi da shi kansa Sen.. Bukar ɗin ma. Dan Rabilun bai taɓa faranta masa rai mai girman gaske irin wannan karon ba. Har alƙawarin ya koma ƙauyensu ya nema takarar kansila zasu tsaya masa sukayi. Tsabar farin ciki Rabilu jinsa yake kamar sabuwar haihuwa yau ɗin nan. Tun kafin ya iso gida ya saka aka fara duba masa gida zai saya. Ya kuma tsaya ya sayi kaji da kayan kwalam da maƙulashe ya cika bayan motar da aka bashi ya nufi gida. Babu wanda ya damu da motar da yazo da ita dan yana shan zuwa da wanda suka fita motocin ogansa kenan. Shiyyasa yanzun ma mutane basu maida hankali ba. Sai dai abokan zaman hayarsa yanda yake shigowa da kayayyaki sai da suka tsaya suna kallonsa. Shi ko sai faman washe musu baki yake yi. Daɗi sukaci na haƙiƙa shi da iyalinsa a daren ranar, washe gari da abubuwa suka fara yawo a media yau kenan bai san mike faruwa ba dan yana ɗaki kwance gashi bashi da babbar waya har azhar. Mutanen gida kuwa da maƙwafta duk sunga video sunata mamaki, sun kuma shiga ruɗanin shine ko wani ɗan uwansa ne haka a kayan sojoji dan kamar dai ta ɓaci gaskiya. Makwafcin ɗakinsa daya kasa haƙuri har knocking ƙofa yay musu amma sai yace ma matarsa tace barci yake yi. Itako ta faɗi haka tana wani ciccika da batsewa su a dole sun samu duniya dare ɗaya.
Anyi hakan baifi da mintuna talatin ba jami'an tsaro suka iso gidan. Mutanen gida duk sun firgice, ana tambayarsu Rabilu suka nuna ɗakinsu. Da ƙarfi ɗaya a cikin jami'an ya shiga buga ƙofar, Rabilu da barci ya ɗauka matarsa na masa tausa ga yaransu a gefe na danƙarar naman kaji tun jiya ja'iran sun kasa haƙura (yo babu a house, an daɗe kuma ba'a haɗu ba🤣🤌). Matar zata miƙe a fusace Rabilu ya ce, “Koma ki zauna, dole ne na fita naci mutuncin Lado ni bana son harkar maula. Ka buga ance maka barci nake dan mayata bazaka kama kanka kayi haƙuri har na tashi ba”. Ƙey yaja riga ya saka batare daya lura rigar matarsa bace. Tana ƙoƙarin fahimtar dashi rigarta yake shirin sakawa fa bai ma saurareta ba. Itako sai ta barshi kawai, acewarta ai garama matan gidan su gani su sake tabbatar da tafi ƙarfinsu mijinta na sonta. (🤣🤣🤣🤣🤣Sai dake matar soyayya)
Mizai faru Alhaji Rabilu masu kuɗin dare ɗaya na banko labule ya fito aka ɗaura masa bindiga a saman kai, wani jami'in ga matso da handcuffs a hannu ya ce, “You are under arrest!”.
A matuƙar firgice Rabilu ya ce, “Arrest! Akan mi? Mina aikata to?”.
“Idan kaje can kaji”.
“A to ku barni na kira maigidana a waya. Na kuma shirya”.
“Baka da wannan lokacin.” jami'in ya faɗa a tsawace tare da kwashe ƙafafunsa sai gashi a ƙasa, baya aka maida hannayensa aka saka masa handcuffs. Haka aka fita da shi matarsa na kuka da kururuwa hakama yaransa. Anguwa cike mutane nata ƙus-ƙus. Ga wasu jami'an sun shiga ɗakinsu sunyi bincike. Maƙudan kuɗaɗen da su Sen... Suka bashi a tsirararsu aka fito da su, sai wayarsa Nokia rakani kashi da key ɗin motar da takardunta......
_________★
Anan Kaduna an sallami Huznah daga asibiti. Daddy kuma ya bama Sageer umarnin wucewa da ita Kano kawai dai baiga amfanin zamanta a Kaduna ɗin ba. Dama ga Ammie da Hajiya Yaya ma sun wuce Abuja. Shi kansa Daddyn Abujar zai wuce saboda sanarwar farfaɗowar Abah data cika gari. Ga wannan batu na Giro shima Ammie ta sanar masa ƙoƙarin da su Baba Sardauna ke kanyi akan al'amarin. Sai kawai ya yanke bari yaje shima ya bada tashi gudunmawar kodan su Shahidah.
Yazeed shine yayta roƙon Daddy da masa magiya shi da Sageer akan a saki Hajiya Basariyya. Taci darajar haihuwa da tayi. Da farko dai Daddy ya turje, sai shi Sageer ne daya kalla Huznah sai ta bashi tausayi. Yasan bazataji daɗi ba idan taji shi ya saka an rufe mata mahaifiyarta a police station harna tsahon kwanaki. Sannan ai koba komai ALLAH ya tsallakar masa da cikin datai niyyar salwantar wa duk da kuwa basu da tabbacin yana cikin ƙoshin lafiya. Cikin lallashi da kwantar da kai shima sai kawai ya shiga bama Daddy haƙuri da tabbatar masa ya haƙura ya yafe. Daddy zai hau yimasa faɗa Yaya Yazeed shima ya cigaba da ban haƙurin.
Sai kawai Daddyn ya hararesu da faɗin, “Oh kai zaku haɗe min kenan? To babu ruwana, sai dai ku sani idan kun fiddota karta sake taje min gida”..
Daga haka yay gaba ya barsu a wajen. Koba komai tunda ya yarda dai su fiddota ai da sauƙi. Sauran batun kuma sayi daga baya..
Sun fiddo Hajiya Basariyya da tai wuƙi-wuƙi. Kaida ka ganta kasan ruwa ya ƙarema ɗiyan kada. Ba duka babu zagi amma ba ƙaramar muzanta bace ace ka kwana police station tsahon kwanaki cikin datti, ƙazanta da wari. Ga wata tantiriya data samu a wajen ta dinga sakata tana mata tausa. Idan taƙi yi ta shara mata matuka dole tayi. Da daddare kuma ta dinga lalubarta, sai hakan yasa bata barcin kirki saboda tsoron kar matar nan ta lalubeta. Rashin barci da waɗan can abubuwan suka maidata wuƙi-wuƙi kuma wujiga-wujiga. Ko kallon inda take Sageer baiyi ba sai Yazeed ne ke mata magana. Suna fitowa kuma a gabanta ya saka Huznah da ko kallonta itama batayi ba a motar da batasan ya saya ba bayan tahowar Huznah Kaduna yaja ya bulesu da ƙura har Yazeed ɗin yay wucewarsa.
Shi Yazeed ma abin sai ya bashi dariya. A fili yace, “Ɗan iska zaka dawo ka saman ai”.
Sarai yasan wanene Daddy, Dan haka ya nema ma kansa mafita ya tari napep ya saka Hajiya Basariyya yace a kaita anguwar da yayanta yake. Shi kuma yace mata zaije wani wajene kuma gidan babu kowa suna Abuja. Hajiya Basariyya dai batace masa komai ba, suna barin wajen da ƙyar tace ma mai napep ya kaita gidan Chalawa.....
_________★
Alhamdullahi zuwa dare an samu fiye da abinda ake buƙata a jikin Abah. Sai gwaje-gwajen da akai masa kawai ake jiran result zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu. Dan haka a wannan daren kusan dukan ahalin Darma sun raba dare ne akan sallaya suna kaima UBANGIJI kukansu. Washe gari suka wayi gari da son jin yaya results zasu kasance sai kuma batun zuwa Giro.
Cikin amincewar UBANGIJI da yardarsa suna isowa asibitin da sakamakon gwaje-gwajen Abah suka fara cin karo. Alhamdullahi nasara ta samu, dukkan abinda ake tunanin za'a samu na matsala ba'a sameshin ba sam. Sai ɗai-ɗai da za'a iya magancesu da magunguna. An kuma basu damar shiga duba shi sai dai da mutane kaɗan-kaɗan.
Hakan kuwa akayi, su Baba Sardauna suka fara shiga, bayan sun fito su Oum suka shiga suma da su Umma. Sai su Babban Yaya, su Uncle Mahmud har dai akazo kan ƙananu su Maanal. Duk wanda ya shiga zai fito da farin ciki. Dan duk da Aban baya magana yana gane kowa, harda ɗan murmushin ƙarfin hali yake musu kaɗan-kaɗan. Sai hakan ya sake saka zukatansu a cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Suka cigaba da masa addu'ar samun lafiya mai ɗorewa.
An saka Oum komawa ciki domin goge masa jiki ya ɗan samu ƙarfi suna son a fara bashi abu masu sauƙi kamar ruwa mai gina jiki (ORS, fresh juice, electrolyte-rich drinks). Abinci mai sauƙi da gina jiki kamar farar shinkafa, farfesun wake ko kaza, fresh kayan lambu. Banda abinci mai miya, mai, yaji, ko abubuwan da za su iya wahala wajen narkewa. Dan haka babu ɓata lokaci Najma, Ameerah, Maanal suka koma gida domin yo masa girki. Sosai su AA sukaji daɗi a ransu. Yaya Fawzan ya zubama Nibras dako motsi batayi ba duk da su Maanal sun mata magana. Sosai take bashi mamaki a wannan gaɓar. Shi kanshi AA sai da ya kalletan. Suna haɗa ido sai ta miƙe zambar tana faɗin, “Au bara naje kar su tafi su barni”.
“Koma ki zauna”.
Yaya Fawzan ya faɗa a dake. Har tsakiyar kai sai da taji kaushin harshen nasa. Ta kalla inda AA yake, sai taga ko kallon inda take bai sake yi ba. Abinda tayi ɗin kuma ya bama kowa dake wajen mamaki, amma babu wanda yace komai dai..........✍️178
........Kwanaki biyu kenan da kama Rabilu, kwanaki kuma biyu da farfaɗowar Abah. Har zuwa yanzu su Sanata Bukar basu san an kama Rabilu ba, dan haka gaba ɗayan ƙulle-ƙullensu ya ta'allaƙa ne akan taya zasu kashe Mabera, su kuma juya al'amarin daya faru a Giro kan AA. Ga su Gwaggo dake hannunsu sun saka yaransu sai wahalar da su suke. Babu ne kawai dake kwance sharaf babu yanda suka iya sai ido. Amma Gwaggo da Sailuba sunci wahala ta haƙiƙa, dan suma sunyita har sun gaji. Koda Sen... Bukar ɗin ya je yau a karo na farko ya gansu haka suka rinƙa kuka suna roƙonsa ya yafe musu sun tuba. Sailu harda faɗin wlhy ita bata da alaƙa da su sai matar uba. Kuma tsakani da ALLAH sanda aka amsar masa kuɗi ya ganta?.
“Amma dake akaci ai”.
Cewar Gwaggo tana gyagygyaɓin kuka da rawar jiki. Sailu zata sake magana Oler ya daka musu tsawa. Hannu suka saka suka riƙe baki jikkunansu na rawa sosai. Sen.. Bukar da tunda ya shigo bai ce komai ba ya wani taɓe baki, cikin kaushin murya ya ce, “Yanzu dai kuna nufin kun yaudareni kun cinye kuɗina? Kun aurama ɗan gidan Darma ƴarku”.
Sosai mamaki ya kama Gwaggo, ta shiga girgiza kai da rantse-rantsen wlhy babu ruwansu, su basu san ma Maanal tayi aure ba sam.
“Ya za'ayi ku sani kidahuman banza ƙauyawa. Ni yanzu banda lokacin wani cece kuce da ku. Na farko zan tura yarana su saida min duka gonakinku, sannan dole ne ku biya fansar ƴarku dana ƙwallafawa ran morewa. Dan haka Oler a cikin yaran nan a samu masu buƙata suzo su musu fyaɗe”. Yana gama faɗa ya miƙe. Wani irin ihun kuka Gwaggo da Sailuba suka sanya suna roƙon Sen.. amma ko waiwayensu baiyi ba. Haka shima Oler yay ficewarsa ya rufe ɗakin. Shi Babu yana can an yasar a ƙasan wata bishiya na harabar kamfanin anan yake kwana bai san abinda ma akema su Gwaggo ba, azabar ciwo da wahala ma sun isheshi. Abincin