Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
AA tafiya kawai yake, ko gane abinda ke gabansa ma bayayi, Yaya Fawzan kam sarkin karaya jikin Baba kawai ya kife kansa ya fashe da kuka. Babban Yaya dashi aka shiga da Oum ciki.
Nibras da tun ɗazun itama sun iso da Mamanta asibitin da Yayunta tunda ita ALLAH ya ƙaddara bata da rabon wahala, dan daga idi ta wuce gidansu duk hidimar da akai babu ita, sai dai itama tasha tashin hankali matuƙa..
Su Abbu kam suna kan Abah, dan ana kaishi ɗakin daya dace sai almakashi aka saka aka yanka rigar shaddar jikinsa ma. Dan danna aka saka masa oxygen. Kwararrun likitoci da suka san aikinsu da Abbu suka fara abinda ya dace. Dai-dai nan kuma saƙon rasa Anum ya isa ga ahalin Darma. Duk da kasancewarta yarinya ƙarama mutuwar tata ta dakesu ƙwarai da gaske. To itama dai Nana sai abinda ALLAH yayi, ita da Mamy dai har yanzu su akwai doctors a tare da su......
_________★
KADUNA
Gab da kiran magriba ALLAH yay ma Nazeerah rasuwa. A dai-dai lokacin da Sabuwa ke farfaɗowa daga sumar wahala. Tashin hankali ya sakata fasa gigitacciyar ƙarar ihun kuka. To ya za'ayi, ta ALLAH ta riga ta tabbata sai kuma haƙuri. (Irin wannan wa'azin mutuwar ake jiye mana shiyyasa akowane motsi na rayuwarmu ake so mu dinga tunawa da hakan. Babu ruwan mutuwa da shekaru, ba ruwanta da gata, bata jinkirtawa kowa, bata rage maka ko sakanni domin tuba ga UBANGIJI ko ga mutanen daka tauyewa hakkokinsu ko zaluntarsu. Ga dai Nazeefa, iyayenta sun cuta mata matuƙar cutarwa, ALLAH yayi mata gata ya bata mijin aure, maimakon ta nutsu ta nema aljannar sai ta shagala, suma suka saka hannu a wajen shagaltar da ita, da taimaka mata cutar da mijinta da zaluntarsa. Ɗan dazai mata addu'a babu, tabar miji da ɓacin rai da takaicin sakashi a masifar rayuwa. Uwa sai a hankali, uba nacan yana ta tashi rayuwar. Ƴan uwa mu daina tunanin dan munada ƙarancin shekaru rayuwa zata cigaba da bamu damar yin abinda muke so har zuwa gaɓar tuba ko tsufa, shi UBANGIJI ba abokin wasan kowa bane ba. Wlhy mu dawo hankalinmu, ki dinga sakawa a ranki idan gari ya waye da wuya kikai dare, idan dare yayi da wahala kikai safiya, mu yawaita istigafari, mu rage ma kammu ɗaukar nauyin mutane koda na kallon banza ne. ALLAH ya gafarta mana ya gafartama iyayenmu 🙏 😭).
Ba sabuwa kawai ba hatta su Ammie da su Hajiya Yaya wannan mutuwa ta dakesu ƙwarai da gaske. Ƴar samun nutsuwar dawowar su Maanal duk da ance Abah da matarsa ɗaya da ƙanwar matar tasa na cikin wani hali ya ɗan kawo nutsuwa a zukata kaɗan. Ammie da Nene dake shirin wucewa Abuja jirgin bakwai sai suka fasa saboda wannan rasuwar. Haka shima Daddy da Yazeed dole suka haƙura. Gida suka wuce aka bar gawar Nazeefa da Jaririnta mai tsannanin kama da ita anan asibitin sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu za'ai mata sutura a miƙata gidanta na gaskiya. Huznah ma na asibitin aka barta da Salima tunda itace babba..
Tun kafin magriba Hajiya Basariyya ta dawo gidan, sai dai tunda ta shige sashenta ta zauna a falo tai tagumi bata iya ta motsa ba har ƴan asibitin suka shigo kusan takwas na dare. Motsin dawowar mutanen gidan ya saka zuciyarta dukan ɗari-ɗari, sai dai tun tana tsumayen shigowar wani a cikin yaƴanta ko Daddy harta sallama. Dan ko autarta bata gani ba. Kasa haƙuri tayi ta tashi tana leƙawa ta window. ALLAH sai da taji zuciyarta kamar zata zubo dan tashin tashin hankalin hango Sageer, Yazeed, Daddy, Baban Sageer, Yayanta, da Baban su Hajiya Yaya da tayi a tsakar gidan. Da sauri ta nufi bedroom ɗinta kamar zata faɗi.
“Na shiga uku ni Basariyya badai na rasa Huznah ba?”.
Babu mai bata amsa, ta kai zaune bakin gado, sai kuma ta sake mikewa zaram tayo waje. Sai tayi kamar zata buɗe ƙofar falo ta fita sai kuma ta koma da baya tana girgiza kai. Hawaye kam da tarawa ake da yanzu an cika wani abu ai. Waya ta ɗauka tai kiran Madeena ƴarta ta biyu, amma bata ɗaga ba. Sai ta ƙara ruɗewa tai kiran Maman Yaseerah. Itama dai bata ɗauka ba. Tun tana leƙa window tan hango su Daddy harta leƙa taga su Ƴaƴanta sun shiga mota, sai karaf taji makwafcinsa na faɗin, “Alhaji Usman ALLAH ya ƙara haƙuri, ALLAH ya jiƙanta ya gafarta mata. Bari muje sai da safen an haɗu wajen jana'iza”.
Yaraf kake jin Hajiya Basariyya a ƙasa. Ta daddage ta fashe da ihun kuka da faɗin, “Na shiga uku ni Basariyya na bani, shike nan na kashe ƴata da kaina. Wayyo Huznah wayyo ALLAH na. Ba ƙaramin tayar da hankalin kowa wannan kuka yayi ba. Kowane sashe suka shiga fitowa a guje. Amma duk sai Daddy yace su koma. Haka duk suka koma suna jiyo ihun Hajiya Basariyya da kururuwa tana ƙwala kiran sunan Huznah. Tun tanayi da buɗaɗɗiyar murya har muryar tata ta dishe. Daddy kuma ya hana kowa zuwa inda take har ƴayanta. Kuka taci na innalillahi. Daga ƙarshe ta zube anan falon tana nishi ƙarfinta ya ƙare sai hawaye, tayi wujiga-wujiga da irin kukan mutuwar da ba'ason ma musulmi yayi ma mamaci koda ace mutuwar ce.
Washe gari ana idar da sallar asuba dangin su Hajiya Yaya suka fara isowa gidan, musamman mahaifiyarta da ƴan uwanta. Dan da farko ance tunda babu aure tsakanin Nazeefar da Yazeed aje can gidan su Sabuwar ai jana'izar tata sai shi Baban su Hajiya Yaya ya roƙi alfarmar yi anan ɗin, tunda koba komai a wajen haihuwar jinin gidan ALLAH yay mata rasuwar. Ba kuma kowa ma yasan da batun sakin ba sai isu isu. Babu wanda ya nema Hajiya Basariyya balle tuna halin da take ciki har aka iso da gawar Nazeefa cikin gidan dana yaron misalin takwas da rabi. Kukan tashin hankalin da Sabuwa keyi ne ya farkar da Hajiya Basariyya daga barcin wahalar daya figeta da asuba. Ko salla batayi ba. Zane kawai ta yayuba ta ɗaura, ko ɗankwali babu a kanta ta fito daga sashenta tana tangaɗi. Hakan yayi dai-dai da fito da gawar Nazeefa a mota za'a kaita sashenta. Hajiya Basariyya taje da gudu tana kuka ta riƙe gawa ko lura da Sabuwa batayi ba da itama ta riƙe ɗin. Kuka take iya iyawa da kiran ta shiga uku Huznah ta yafe mata. Nan dai ta shiga tonama kanta da kanta asiri akan abinda babu wanda yasan ya akayi daga Daddy sai Yazeed, sai Sageer da Huznah ta turama massege..
Mutane anyi cirko-cirko ana kallonta, sai Ammie ce tai ƙarfin halin zuwa ta kamasu ita da sabuwar, amma babu wanda ya saurareta. Abin ya bama yayan Hajiya Basariyya haushi kawai yazo ya ɗauketa da maruka har biyu. Anan ne fa dole ta saki gawar, taruwa akai ana bashi haƙuri, ita kuma aka kamata aka maidata sashenta. Sai lokacin ake sanar mata bafa Huznah bace ta rasu Nazeefa ce. Huznah na asibiti ita. Wannan shine ya kawo ma zuciyar Basariyya salama. Asiri dai kuma ta riga ta tonama kanta shi ai, dan yanzu dai kowa yasan mike faruwa sai ALLAH wadai ake da halinta........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣7️⃣0️⃣
______________
........Anan Abuja har dare babu wani bayani akan Abah da Oum. Dole su Umma suka tattara kowa aka wuce gida musamman ma su Maanal dake buƙatar wanka da abinci tunda an dubasu babu wata matsala. Itace ma dai abinka da mai ciki sai da suka ɗan saka mata drip. Anan aka bar su AA. Gawar Anum ma sai zuwa safiya zasu amsa. Haka suka kwana su da suke gidan, da su da suke a asibitin babu wani kwanciyar hankali..
Washe gari anayin sallar asuba suka koma asibitin. Isarsu babu jimawa kuma ta ALLAH ta kasance akan Nana itama ALLAH ya ɗauke kayarsa. Gigicewa su Nuratu sukayi matuƙar gigita ma kuwa. Musamman Saheeba da sai lokacin ta farko daga nata barcin wahalar. Dan itama dai ta maku matuƙar makuwa. Ga ciki ya fita gaba ɗaya mahaifarta kuma ta samu babbar matsalar da har abada bazata sake haihuwa ba. ALLAH sarki Aunty kuka take tana ƙari ƴan uwa duk suna neman kuɓuce mata. Dan itama dai Mamy ɗin sai a hankali. Ga abin kunyar data tafka na ciyar da Abah guba, wai uban ƴayanka kai jama'a, wannan wane irin rashin imani ne da bushewar zuciya. A yanzu haka tana kwancen amma hannunta ɗaya da handcuffs. Dan ita ƙarƙashin ma jami'an tsaro take. Mahaifin su Nuratu ma da ƴan uwansu duk sun iso Abujar. Haka suka ɗauki gawar Nana suma aka nufi gidan Hajiya Turai da ita. Ita kuma Anum gidan Darma. Saheeba kam ma babu damar barin asibiti, haka ta dinga kuka sai da akai mata allurar barci mai ƙarfi.
Umma ce tama Anum wanka, aka sallaci yarinyar aka binneta anan cikin gidan ta garden tunda yarinya ce sosai. Amma rasuwarta ta daki yan gidan, dam itace suka fara rasawa a gidan yarinya mai wayo. Sauran na baya da suka rasu duk ƙannanu ne basa wuce 2years. Itako har ta kusa 5 ma. Da yake su AA duk da su aka sallaceta suna gida. Suna ƙoƙarin komawa asibiti Baba Sardauna ya hanasu yace suje suyi wanka su kwanta su huta, zuwa anjima sai suje suyi gaisuwar Nana itama dan su su Baban sunje dasu akayi jana'iza ma. Sune dai basu je ba. Badan sun so ba suka zauna ɗin. Maanal na falo tare da su Shahidah sun gama yima su Ammie gaisuwar Nazeefa da itama har an kaita makwancinta AA ya shigo. Har zai wuce sama ganin su Shahidah yasa ya dawo ya zauna suka gaisa. Sun masa ta'azziyar Anum da Nana, da yima su Abah addu'ar samun lafiya. Sannan suka sanar masa saƙon Ammie. Sai yanzu yake jin rasuwar Nazeefa shima. Sosai abin ya dakesa matuƙa, ya dinga ambaton innalillahi wa-inna ilaihiraji'un dan gaskiya yaji mutuwar yarinyar itama. Kai jama'a duniya-duniya, duniya budurwar wawa kenan. Ashe duk abinda yarinyar nan ke aikatawa rayuwa tazo mata gangara, kai kai kai iyayenta sun cuceta wlhy. Da wannan sambatun a zuciya ya tashi ya haura sama. Sai lokacin Maanal tai ƙarfin halin miƙewa zata bishi. Harta fara tafiya Shahidah tai kiranta. Dawowa tayi ta zauna. Shahidah tace, “Ki samu wani abu mai ɗan ruwa-ruwa ki haɗa masa Maanal ya samu ya ɗan ci, sannan ki daina wannan kukan kodan ki ƙarfafashi, amma a haka ai karyar masa da zuciya zaki sake yi, bayan yanzu mai ƙarfafashi yake buƙata”.
Kanta ta jinjina mata, tasa bakin hijjab ɗin jikinta ta share fuskarta. Da kanta taje kitchen ta haɗa masa tea tana son soya masa ƙwai bazata iya ba dan bata son ƙamshinsa yanzu. Sai kawai ta haɗa masa sandwich tai toasting ɗinsa tunda tasan yana so, ta ɗaura a ƙaramin tray da ruwa ta nufi saman. Kai tsaye bedroom ta nufa ganin babu shi a falon, dama tasan da wahala ya zauna. Maybe ma wanka yake dan yau kwana kusan uku rabonsa da wanka daga shi har su Yaya Fawzan.
Sosai gabanta ya faɗi ganin duhu a ɗakin ya kashe fitila, cikin ƙarfin hali ta kunna mara haske saita hangoshi can a zaune a ƙasa kan carpet ɗin gaban gadon kansa a duƙe ya riƙeshi da hannayensa duk biyu. Cike da sassarfa ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a table ɗin gaban sofa ta nufi inda yake. Duƙe ta kai a gaban nasa, tare da kama hannayen ta janye. Karo na farko ya ɗago idanunsa da gaba ɗaya sunƙi ko sassauta jan da suke ciki tun a randa su Mabera suka tafi da su sai ma ƙara rinewa da sukeyi ya zuba mata. Ita sai tama ji kamar jikinta na kaɗuwar tsoro. Amma sai ta daure ta dake itama tana kallon cikin idanun nasa. Hawayen dake neman zubo mata yasata matsawa ta shige jikinsa kawai ta ƙanƙamesa. Shiru yayi tsahon lokaci bai motsa ba, bai kuma rungumeta kamar yanda ya saba ba shi. Tsahon mintuna biyu suna a haka shiru kafin a hankali yay mata zobe da duka hannayen nasa ya ɗaura haɓarsa a saman kanta ya lumshe idanunsa a karo na farko sai ga hawaye a fuskar maza yau ma. Maanal bata san kuka yake yi ba sai da suka ɗiga mata a saman goshi ta ɗago da sauri tana kallon fuskarsa. A firgice tai yunƙurin tashi amma sai ya hanata, sai ma kife fuskarsa da yayi a saman cikinta hawayen suka cigaba da sauka. Itama an kai gaɓar da bazata iya riƙe nata ba, sai kawai ta ƙanƙame kansa dake a cikinta ta fara nata. Dole su baka tausayi, sun tsara abubuwa masu yawan gaske a wannan bikin sallar da yawace-yawace daban-daban amma komai ya juye, juyewa mai ban mamaki da tashin hankali. Sunsha kukansu har suka gode ALLAH, batare da kowa yacema ɗan uwansa komai ba akan hakan Maanal ta tashi ta cire hijjab ɗin jikinta ta ɗakko tray ɗin data shigo da shi ta dawo gabansa. A yanzu ya kwantar da bayansa ne jikin gadon kansa na a saman gadon yana kallon sama, fuskar Mamy kawai take masa kai-kawo a cikin idanunsa sanda take zayyane musu ainahinta. Hannunsa ta kamo, hakan ya sashi ɗagowa yana kallonta. Murmushi tai masa, muryarta a dasashe tace, “Tashi kaci abinci sai kayi wanka”.
Kai ya girgiza mata alamar a'a. Shiru tayi tana kallonsa, idanunta na cika da sabuwar ƙwalla. A hankali ya sake girgiza mata kai alamar kada tai kuka. Sai kuma ga hawayen, muryarta na rawa ta ce, “In dai baka son nayi ka tashi kaci abinci dan ALLAH. Besty rayuwa bazata yiwu da yinwa ba. Abinda ya faru ya riga ya faru, ƙaddararmu ce kuma tun ran gini tun ran zane. Yanda bamu hanata faruwa ba, bamu isa gogeta a jikinmu ko zukatanmu ko kundin tarihinmu ba a yanzu. Amma zamu iya tawakkali da haƙuri da juriya sai komai yazo ya wuce tamkar ba'ayi ba koma bai faru ba. An jarabci ANNABAWAN ALLAH, an jarabci Sahabbai, dammu UBANGIJI ya jarabcemu sai kuma mu kasa haƙuri da godiya a gareshi bisa sauran ni'imomin da yay mana a rayuwa kashi-kashi. Bayan kuma ta hanyar haƙurin da juriyar ne kawai zamu nuna godiyar tamu a gareshi. Dan ALLAH kaci abinci, kayi wanka ko yaya zakaji nauyin zuciyarka ya ragu, zaka samu ƙarfi kaima da sasautawar abubuwa. Kalla kaga Babynka shima kuka yake yi fa tun jiya”
Cikin nata data dafa ya zubama idanu, sai kuma a hankali ya saki ɗan guntun murmushi da kai hannunsa kan cikin shima yana shafawa. Yanda take masa magana cikin lallashi da karaya ya sake saka zuciyarsa raunana. Maanal da Oum kaɗai ke saka zuciyarsa irin wannan laushin da karayar a lokaci ɗaya.
“Zakaci ko?”.
Ta faɗa a hankali.
Kansa ya jinjina mata shima a hankalin, sai ta lumshe idanu tana sakin murmushi, tare da matsawa ta sumbaci lips ɗinsa da suka ɗan bushe suka tattare waje ɗaya. Sannan ta matsar da bakinta cikin kunensa ta raɗa masa, “I love you my Root-Soul”.
Siririyar ajiyar zuciya ya sauke, ya shafa kanta kaɗan. Itama sai ta gyara zamanta kawai ta fara bashi abincin. Fuska a yatsine yake amsa, kai daga gani kasan baya masa wani daɗi. Amma duk yanda yaso dojewa Maanal bata yarda ba, sai da ta tabbatar yaci sosai sannan ta barshi. Ta maida tray ɗin gafe ta tashi. Bayi taje ta haɗa ruwa masu ɗan ɗumi tasa kayan ƙamshi a jacuzzi sannan ta fito, yana zaune inda ta barsa idanunsa a lumshe batace komai ba ta durƙusa gabansa ta fara cire botiran gaban rigar, sannan ta zare agogon hannunsa ta taimaka masa suka cire rigar. Duk fa yafi ƙarfinta ta shiga kiciniyar kamashi wai ya tashi, shi sai ma taso bashi dariya. Amma sai ya biye mata, ganin ta fara ƴar zufa ya ɗanyi murmushin gefen baki ya miƙa da kansa. Kayan ta taimaka masa suka ƙarasa cirewa sannan suka nufi bayin, ta juyo zata fita ya riƙota, zatai magana yay mata alamar zipping a baki, tare da ɗaukarta cak suka shige cikin ruwan a tare. Lokaci guda suka saki ajiyar zuciya, ɗumin ruwan da ƙamshinsa na ratsa musu jiki. Da taimakonta wankan ya gudana, daga baya kuma salon ya canja saboda yanda ta dinga jan ra'ayinsa. Al'amarin kamar zai tsaya a wasan sai aka ɗauki wata hanyar daban, dole dai bayan anyi wanka an fito sai da aka sake komawa yin wani.
ALLAH sarki AA sai sauke ajiyar zuciya yake, ko yaya kulawar da Maanal ta bashi ta rage masa nauyin ƙirjinsa sosai. Dan cikin ikon ALLAH suna kwantawa barci yay gaba da shi, itama tun tana kallon sa har barcin ya kwashe ta. Basu tashi farkawa ba sai 2 da wasu mintina. Hakan na nufin sun makara salla. Wanka suka sake yi sannan sukai sallar azhar, suna idarwa Maanal ta fita nema musu abinci.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
171
.........Su Shahidah sun gudu, sai abinci data samu jere a dining. Murmushi tayi cikin jin daɗi da ƙaunar ƴan uwanta, ta haɗa komai ta koma sama. Yanzun ma haka taita hillatarsa da lallashi da magana mai daɗi ya ɗanci, itama