Author : Asmeetah writer Category : Drama
ya yi cilli da ita sai yarabb ta fad'i 'kasi, a tsorace tayi wani irin razanannen ihuu ta mi'ke da gudun bala'i tayi waje! Shima bin bayanta yayi yana fad'in "I will kill you, foolish girl you want to kill my mom."
Ita kuwa compound d'in dazai sadata da harabar gidan ta taka adai den lokacin da tsantsin tiles ya d'ebeta tayi sama zata fad'i 'kasin floor wani irin 'karan gaske tasau harta saddakar kwatsam taji an ri'ke kunkuminta mannata yayi a jikinsa sosai,
Gumi duk ya wanke mata ilahirin jikinta ta d'ago da kanta a hankali tana son ganin wanda ya ceceta lokaci guda ta zaro manya-manyan idanuwanta waje ganin 'kwayar idonta a cikin na tiger eyes! Eyeballs d'insa sun zama blue sosai, gashi yanda yake za'kami kamar kuntaccen zaki, ido cikin ido suke kallon juna ganin kwakwalwarta bazai iya d'auka ba yasa ta sume masa a saman chest d'insa.
'Daukarta yayi kamar wanda ya d'auki jaririya ya nufi harabar gidan kai tsaye ya nufi gurin mai gadi,
Baba mai gadi ganin yanda Junaid ya koma gashi d'auke da yarinya, jikinsa ne yahau 6ari yana fad'in "innahu min sulaimanu wa innahu bismillahi rahmanu rahim, Ku kuke ganin mu bamu ke ganin Ku ba, don Allah don Annabi Junaidu ka rufa mun asiri karkayi mun komai wallahi banida 'karfin ri'keka, wayyoo kakan goggo" Junaid duk yana jin abunda mai gadin yake fad'a saboda bai gama fita hayyacinsa ba,
Katsar da mai gadin yayi tareda fad'in "lafiya klau nake, wannan Yarinya inason kafin na fito tabar gidan nan bana son sake ganin fuskarta a wannan gidan, idan ba haka ba Zan kashe ta har lahira" yana fad'in hakan tare da kwantar da ita asaman daddumar baba tsoho wacce take a sume,
Juyawa yayi ya koma cikin compound ya shige cikin falo daganan upstairs ya haura cikin bedroom, toilet ya shiga shap-shap ya watsa ruwa a jikinsa domin bayaso hankalinsa yabar jikinsa saboda in har hakan ta faru duk wanda yake gidan sai ya raunanasu, amma saka ruwa a jikinsa zai taimaka masa ta wani 6angaren....
Baba mai gadi jin abunda Junaid yace kuma ga a halinda yake ciki yasa ya yi saurin d'auko ruwa yana zuzzubawa Ayush, a razane ta tashi tana fad'in "wallahi ban mata komai ba, Dan Allah kayi hakuri karka kashe ni....." Ganin mai gadi a kanta tsaye yasa tayi shuru ta zuba masa ido tana maida numfashi sama-sama.
Shima mai gadin kallon ta yake cike da mamaki
"Kiyi hakuri Yarinya nasan kina cikin matsala, amma Allah yana tare da ke". A cewar mai gadi..
Ayush bin gidan tayi da kallo gaba d'aya kanta ne yake juyawa da kyer ta iya motsa la66enta tace "aina nake?"..
Mai gadi ya kalle ta yace "ah daman baki san a yanda kike ba? Ni kuwa bar mun ke akayi akace da zaran kin farfad'o kibar gidan kar a kashe ki"
A tsorace ta kalli mai gadi tace "Damusa koh? zai kashe ni wallahii wayyo Allah gashi nam, sai take ganin kamar shine yake nufo gurinta
Kuma gizo yake mata..
Da gudu ta tashi ta bud'e get tabi layi tana gudu tana waiwayen bayan ta, haka ta hau kwalta tana gudun ceton rai ba takalmi a 'kafarta ba kwali a kanta balle mayafi
Haka take gudu kamar mahaukaciya murara!
Shi kuwa Baba mai gadi girgiza kai kawai yayi bashida bakin magana sai abunda yake sa'kawa a ransa
"Oh yanzu Ina ta nufa sai Allah abun tausayi, haka Junaid yake korar duk wata yer Aikin da aka kawo gidan, amma banga laifinsa ba abunda akayiwa mahaifinsa babu dad'i sam,
Gashi shima a sanadiyar cutan nan tashi yasa mahaifiyarsa kwance a gadon asibiti, Allah ya bata lafiya" haka ya zauna akan daddumarsa yana wannan maganar zuci....
Ayush tafe take a tsakiyar kwalta bata san Ina zata ba, duk fuskarta ya tuje yayi jawurrr tanata sharar kwallah sai ji tayi 'katuwar mota trailer ya yi wani irin hornnnn a bayanta a tsorace ta juya bayan ta da wani irin ihuu ta toshe kunnuwanta da hannaye biyu ta 'kame 'kamm a waran, idonta kuwa ta 'kan'kamesu a rufe!
Ganin anyi wani irin hajijiya da ita an rungumota ne yasa tayi saurin bud'e idonta
Ana kawar da ita daga tsakiyar kwaltan kuwa 'katuwar motan nan ta wuce ko seconni ba'ayi da kawar da itaba!!!!
Zuciyarta kuwa wani irin bugawa take tsabar ta gama tsorita
Sai ji tayi ance "ke ashe bakida hankali, waya gaya miki ana wasa da rayuwa?" Ya kalleta da kyau a hankali ya furta "ke ce Ayusha wacce kike tare da Doctor Fatima?" Ya karisa maganar tare da 'kura mata eyeballs d'insa.
Itama kallonsa take baki na kakkarwa ta kasa cewa komai sai idanunta wad'anda suka canza launi zuwa light red tsabar azaba da firgici.....
"It's okay, nasan duk wannan firgicin a saboda Doctor Fatima tana kwance gadon asibiti ko? Kar ki damu ta samu sau'ki muje ki ganta" ya ri'ke hannunta yasata a gaban motarsa shima ya shige suka nufi hospital.
Doctor Hasheem kenam wanda shima ya baro asibitin ne zai sai kayan fruits a Mommy,
Shine ya tarar da Ayush a wannan halin har yayi 'ko'karin ceton raanta!
Abokin Junaid ne tin suna primary suke tare har Allah yasa kowa ya samu aikin yi Junaid ya samu aikin Soja saboda d'aukar fansar mahaifinsa, shi kuma Hasheem ya karanci fannin lafiya har mahaifiyar Junaid ta bashi aiki a hospital d'inta,
Kuma duk ba Wanda yayi Aure a cikin su........
Ta 6angaran Boka Zalimun Baban Ayush kuwa ganin mota ta nufi kan Ayush
Kad'a hannayensa ya soma yi yana fad'in "aa aahh, aahh Ayush ban shirya mutuwa ba karki mutu kuje Ku ceci yarinyataaaa...." Lokaci guda kuwa ya sume akan kujerar mulkinsa, a tunaninsa motar ta take Ayush, ga kuma madubin tsafi a gabansa Wanda yake ganin komai a ciki,
Yaga mutuwa gaba d'aya ya manta da tsafinsa, (toh kuma Ina Aljanun nashin? Ashe akwai abunda tsafi bazaiyi aiki akansa ba, tinda Gashi ya kasa ceton d'iyarsa kuma rayuwarsa π) sai kuma tarin ba'kin cikin Junaid dake cikin zuciyarsa, already ya ajiye Junaid a gefe zaiyi maganinsa tinda har ya wulakanta masa d'iya a cewar Sarkin tsafi Baban Ayushh!.........
*****
Isar su Ayush hospital
Dr. Hasheem ne ya zagayo ya bud'e mata murfin motar ta fito daman sunbi ta shago ya siya mata takalmi da kuma mayafin data rufa a kanta,
Ri'ke hannun ta yayi yace "muje mu ko"
Ita dai binsa take kawai da eyes bata cewa komai, amma already ta sanshi tin zuwanta asibitin kuma shi ya kaita gidan Dr. Fatima....
Bud'e kofar d'akin yayi da sallama a bakin sa yana ri'ke da ledoji d'ayan hannun kuma yana ri'ke da hannun Ayush.
Juyowa Dr. Fatima tayi ta amsa sallamar ciki-ciki har an cire mata oxygen tana kwance
Murmushi tasau a saman fuskarta ganin Ayush, ta mi'ka mata hannu tana mata alamar tazo da hannunta, Ayush da sauri ta nufi yanda Mommy take kwance,
Itama Dr. Fatima tashi tayi ta zauna ta rungumi Ayush a kirjinta tana shafa kanta alamar rarrashi
Ayush kuka ne yaci ranta sosai
Dakyer aka samu tayi shuru har da had'in bakin Dr. Hasheem waran rarrashin ta.
Mommy taji sau'ki sosai,
Doctor Hasheem ne ya baje mata kayan fruits a glass plate
Tana ci tana bawa Ayush a baki, ita kuwa ta langwa6e kanta a jikin Mommy, da haka suke cin fruits d'in,
Dr. Hasheem ne yayi musu sallama ya fice a d'akin!
Yana fita kuwa saiga Junaid shima ya shugo da sallama a bakinsa,
Idonsa ne suka sauka akan Ayush wacce take kwance jikin Mommy sai faman cin fruits suke yi hankali kwance,
Tashin hankalin da ba'a saka masa Date!!!
Junaid sakin ledar hannunsa yayi Wanda ya d'anyo siyayyarsa na abin kwad'ayi har na hango banqararrun kaji πππa ciki πππππππππππ
*MAFII* *MISHKILA*
sai mun sake had'uwa kuma duu a wani Karon π«‘π«‘
*ASMEETAH* *CE* βοΈβοΈβοΈ
π
*MATAR* *DAMUSA* π
(the wife of tiger)
*MALLAKIN*
*ASMEETAH* βοΈβοΈ
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alΖalaminmu Ζ΄ancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
π«π« *{{N W A}}* π«π«
Ψ¨ΩΨ³ΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩΩ
Ω Ψ§ΩΩΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΩΩΨΩΩ
ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΩΩΨΩΩΩΩ
*BOOK* *ONE*
*PAGE*β‘οΈ 33 & 34
___________________________
Mom ganin Junaid yasa ta ware fararen idanuwanta baki ya gagara rufuwa tace "Junaid my son, taho mana ya ka tsaya daga nesa, am really miss you my son" jiki a mace yake takowa gurin Mom, idonsa kuwa a kan Ayush wacce tin shugowar Junaid jikinta ke 6ari ko ido ta gagara had'awa da shi saboda gudun ganin rikitattun idanuwansa nan, ga wani irin mungun tsoronsa da take ji!
Junaid ne ya zauna kusa da Mommy gwiwowinsa suna gogan na Ayush da sauri ta mi'ke tsaye ta koma kan kujeran dake nesa dasu, shi kuwa ko kallonta baiyi ba sai cewa yayi "Mom what happened to you?"
Mommy kuwa kallon 'kurilla take yiwa Junaid tana tariyo abunda ta gani game dashi aranta take fad'in "Anya ba mafarki nayi ba, ga fa Junaid lafiya klau yake, toh meya faru da ni?" Idon ta nakan Junaid wanda ya katseta da cewa "am asking you Mom meya faru dake??"
Mom tayi mamakin tambayar da Junaid yake mata sai cewa tayi "what happen to me or what happened to you?"
Junaid kansa ne ya d'aure shifa bai fahimci maganar Mom d'insa ba,
Mommy ce take 'ko'karin yaye rigar Junaid tana fad'in "jikinka duk ya faffashe, har naman jikinka ake gani, kana saman jikin bango ga kuma jini duk ya wanke maka jiki, Junaid yanzu banga ciwon komai a jikinka ba, wai meyake faruwa ne" idonta duk ya cicciko da kwalla tana abu kamar wata zararriya.
Shifa Junaid abun tsoro ya bashi "karfa ace Mom ta samu ta6in hankali, innalillahi" yana maganar ne a zuciyarsa, ri'ke hannun Mom yayi yana fad'in "nifa lafiya ta klau ba abunda ya sameni, ki kwantar da hankalinki"
Cikin kuka Mom tace "toh meya kawoni hospital"
Kallon yanda Ayush take zaune yayi wani irin harara ya wurga mata sannan yace "Mom ki tambayi wancan yarinyar ita ta Sani" ya 'kare maganar idonsa akanta.
Ita kuwa Ayush duk abunda suke tattaunawa akai tana jinsu "duk abunda mom ke fad'a gaskiya ne, nasan dalilin daya kawota asibiti sai dai ba nice silar hakan ba, amma yazo yana d'ora mun laifin da banida masaniya akanta" ta 'kare maganar tana zubda kwalla amma sai dai duk maganganun da tayi acikin ranta tayisu.
Mom ce ta kalli yanda Ayush take tace "Allah sarki yarinyar kirki itace ta taimaka mun a lokacin da na ganka cikin wani hali, tabbas abunda na gani ba mafarki bane amma kuma al'amarin babbane sai dai Kai bazaka fahimci hakan ba"
Ta kalli yanda Ayush take ta kuma cewa "ke alkhairi ce a garemu Ina kuma alfahari dake, nasan ke kika ceto Junaid daga halin da ya shiga, nayi mamakin ganin faruwar hakan, ciwonsa sai gaba yake ba bayaba....." Adai den lokacin ta face da matsanancin kuka mai ratsa zuciya....
Shi kuwa Junaid kamar ya shige 'kasi haka yake ji tsabar takaici da ba'kin ciki rufe ido yayi sosai yace "please Mom enough, ya za'ayi kina fad'an sirrina a wannan 'karamar yarinyar wacce bata mallaki hankalin kanta ba" ya 'karisa maganar yana watsa mata wani irin kallo na 'kas'kanci.
A rayuwar shi ya tsani raini especially idan akace macece, ya gama rainawa mata wayo Gashi yana kallon kansa jarumi gashi kuma sojaa.....
Itama Mommy ta fahimci Junaid bayason ta yawaita fad'an matsalolin da suke tattare da shi....