Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MATAR Damisa BOOK ONE Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  Drama

Chapter   20 / 44

57K to 60K   out of 131.4K words

Ameen ba.."
jin anyi magana ta bayan ta yasa ta tsayar da addu'ar ta shafe jikinta,
tana zaune akan sallaya
a hankali ta waigo bayan ta tana fuskantar wanda ya shugo cikin room ɗin, samun guri ya yi ya zauna a bakin katafaren gado mai laushin gaske wanda aka ƙera da gwal, ɗakin sai canza haske yake kala-kala ga wasu mahaukatan labulaye masu tsadar bala'i, capet kuwa kana takawa ƙafarka tana lotsewa cikin carpet..
"Shugaba ya kamata ka dakata haka, wai shin mai Junaid ya yi maka ne? yaron da bai san komai ba, hatta mahaifinsa bai san laifin da ya yi maka ba har ka tsane shi balle shi Junaid da bai taɓa sakaka a ido ba,
yanda Ayush take a gurinka a shima Junaid yake jininka ne....."
bata ƙarisa maganar ba ya daka mata wani gigitaccen tsawa yana faɗin "ki kiyayi bakin ki kina shiga gonar da ba taki ba, ki tsaya a iya matsayinki na matata kuma uwar ɗiyata, domin idan ba haka ba zansa Manya-manyan aljiin ɗina su ƙarƙameki a cikin kurkuku na ina ɗaga miki ƙafa ne saboda ke sarauniya ce.."
taso wa tayi daga inda take zaune tana tafa hannayen ta tana dariya ta zauna itama a bakin gado daf da sarki ta kafeshi da ido tana murmushin takaici tace "shugaba dan Allah kada ka fasa sa a ƙarƙame ni nayi zaman daji da yake da sauraye da ƙwaruna da macije da kunamu ga kuma sanyin duniya duk wahalar nan anan nayi rayuwa tare da ɗiyata mun riga mun saba da wahalar ai balle kurkukun ka da yafi ɗakin governor tsaruwa,
shi daman gaskiya ɗaci gareta kuma bazan fasa gaya maka gaskiya ba..."

"Hahahaha! Sarauniya Bara'at shikenam mu zuba tsakani na da ke wazai ci galaba akan yaran nan, ni sarki Raamud bazan taɓa barin Junaid ya Auri ɗiyata ba sai dai mu mutu tare ni da shi, ko kuma shi ya mutu"
ya ƙarisa maganar yana nuna ta da yatsa.
itama murmushi tayi sannan tace "toh mu zuba mana insha Allahu sai Ayusher ta Auri Junaid ko bayan rai na..."
jinjina kai ya yi sannan yace "mai kike taƙama da shi?"
buɗar bakinta tace "Allah shine abun dogaro na,
kai kanada tsafi ni kuma inada Allah....."
tin kafin ta ƙarasa maganar ya ɗauketa da zazzafar mari sai data faɗo daga saman bed ta kama fuskar ta a gigice ta ɗago da kanta tana kallonsa tace "ni ka mara?.."

"na mareki ko kin manta ni wanene? idan kin manta bari na tunatar da ke ni nine *Sarki Raamud* kuma *Sarkin matsafar duniya* ina da magoyan bayan manya-manyar aljanu, ki kiyayi tsayawa a gabana kina faɗa mun maganganu son ranki, kada ki mayar ni ƙaton arne kamar iyayenki da suka mutu a banza da wofi, ni cikakken musulmi ne,
kin koyawa ɗiyata taurin kai itama bata jin magana ta kamar ke,
Junaid kuma zan kashe shi naga iya shegenku, mttsswww!!!"
tashi yayi ya bar mata ɗakin
kifar da kanta tayi ta soma rera kuka......

*****

"Bros wai dan Allah wacece wannan Ayushert daka damu akan ta ko abinci ka kasa ci kullum sai ambatar sunanta kake, kai ka daina damuwa akan dukan da Oga Junaid ya yi maka ma.."
turɓune fuska tayi tana kallon Dr Hasheem wanda yasa abinci a gaba ya kasa ci sai labarin sufar Ayush yake ta badawa.
Alhamdulillahi Dr ya fara samun lafiya, ya dawo gida ƙanwarsa ce take temaka masa da wasu abubuwa sai ƙannensa biyu maza,
ƙanwarsa wacce ake kira da Lailah ƴer shekara 18 tana zaune a gaban Yayanta Dr Hasheem tana son jin ƙarin bayani akan Ayushert, domin ta fahimci ba ƙaramin so yayanta yake yi mata ba, hatta fuskar wayarsa photon Ayush ce a jiki.
murmushi ya yi sannan ya kalli ƙanwarsa Lailah yace "ita ɗin rayuwata ce, kuma mutuwa ta domin idan babu ita zuciyata bugawa zata yi"
zaro ido waje Lailah tayi ta jinjina kai sannan tace "tab al'amarin babba ne, amma dan Allah Bros kar ka mutu ka barmu kaga bamu da kowa, iyayen mu basa raye, kaine mai kula da mu karka mutu akan wata mace..."

murmusawa ya yi sannan yace "Hummm ƙanwata kenam! muga wayarki"
miƙa masa wayar hannunta tayi mai ƙirar iphone ya kunna fuskar wayar yace "wannan photon waye akan screen ɗin wayar ki" ya juyar mata da wayar yana nuna mata,
sunkuyar da kanta ƙasi tayi a hankali tace motsi da leɓɓen ta tace "Oga Junaid ne.."
yace "meye matsayinsa a gurinki?"
still kanta a ƙasa tace "Bros kaima fa ka sani ina masifar son Oga Junaid"

short laught ya yi sannan yace "ke masifar son Junaid kike ni kuma bala'in son Ayush nake,
ni bazance kada ki so Junaid ba sai dai kisa a ranki cewa Junaid bazai Aure ki ba domin shi babu maganar Aure a story book ɗinsa, shine abunda zan gaya miki, ki maida hankali wajen karatunki duk da nasan Junaid ba wani kiranki yake a waya ba...."
turɓune fuska tayi
sannan ta fisgi wayarta ta tashi da gudu tana kuka ta nufi ɗakinta, ita a rayuwa ta tsani taji ance Junaid ba Aurenta zaiyi ba..

itama Lailah ba'a barta a baya ba wajen kyau, chaculat colour ce ita ba baƙa ba ita ba fara ba kyakykyawa ce ga gashi sai dai ita tanada ƙiba dirin jikine da ita ko ina a cike yake ɓul-ɓul.

iyayensu su huɗu suka haifa Allah ya yi musu rasuwa a tafiyarsu ƙasar saudi jirginsu ya faɗo,
Dr Hasheem shine babba sai second born wato Muzaffar shi yana karatu a ƙasar egyph, sai Haydar shi kuma yana karatu anan nigeria day yake yi a gida, sai Autar su Lailah...

*MASHA ALLAH*

Follow me on my whatsApp
09065443871

More comments more more read more😘
*SHARING*

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of tinger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ -------> 63 & 64 <-------

🫶🫶🫶🫶🫶🫶 "Yaya Junaid" murya ciki-ciki ta furta sunan sa, jiki a mace ya ɗago da shanyayyun idanuwan sa ya kafe ta dasu yana son jin abunda zata faɗa, silently ta taso tazo gabansa ta tsaya "shin kana sona har cikin zuciyar ka?"
ƙura mata eyes ya yi sosai lokaci guda kuwa ta fara masa ƙwarjini cike da fargaba ya girgiza kai "a'a bana sonki, bani da ra'ayin yin Aure just kije ki zaɓi Dr Hasheem zaifi dace wa da ke, ina miki fatan alkhairi".

Kuka ne ya kuɓuce mata ta riƙe gaban rigar sa tana faɗin "Yaya Junaid kar ka mun haka dan Allah wallahi ina bala'in sonka, ka tausaya mun..." zamar mata da hannu ya yi daga cakumar data yi masa fuska ba annuri yace "kinga Yushert stop this robbish, i said i'll not marry you, please stay away from me Yushert"

tsayar da kukan tayi cike da mamaki take kallonsa leɓɓen ta na kakkarwa tace "Yaya Junaid... ji tayi ya riƙo hannunta yaja ta bakin ƙofa ya fitar da ita daga cikin room ɗinsa sannan ya rufe ɗakin ya yi komawar sa ciki..

da gudun gaske ta sauƙa down stairs tana kuka ta nufi ɗakin Mommy kai tsaye saman gado ta haura tana kuka mai cin rai,
Mommy fitowar ta kenam daga cikin toilet ta watsa ruwa ganin Ayush a wannan halin yasa ta nufo gurin ta tana faɗin "lafiya kuwa Ayusher keda waye kike kuka?"
shuru Ayush bata bada amsa ba, sai ma ƙara ƙarfin kukan data yi.
"Humm kar dai kice mun Junaid ne, domin kunfi kusa ke da shi anjuma zaki koma masa ne..."
dai dain lokacin anata ƙiraye-ƙirayen sallar mangrib,
tashi mommy tayi ta sanya kayanta sannan ta tsayar da sallah already tayi alwala kafin ta fito.

Ogah Junaid kuwa zama ya yi a bakin bed yayi tagumi wani irin ƙunci ne ya ziyarci zuciyar sa, idonsa ne sukayi jawur shi a rayuwarsa ya tsani ayi masa maganar Aure ji yake kamar ya sheƙe kansa, shi har cikin zuciyar sa yana son Ayush amma maganar Aure ne baya so.
ji yake zuciyarsa tana haurowa, kwakwalwar sa tana tafasa, idanuwan sa ne suka fara canzawa like tiger eyes! hankalinsa ne ya fara fita daga jikinsa yana huci cikin ƙanƙanin lokaci ya faɗi ƙasi yana juye-juye ya riƙe kansa sosai yana wani irin gurnani da ƙarfin gaske,
ji yake kamar ana hura masa wuta a jikinsa, jijiyoyin jikinsa sun fito sunyi burtsi-burtsi launin fatarsa ta koma yellow, sumar kansa sun mimmiƙe daga kwance da suke!
miƙewa ya yi da ƙarfin gaske ga rikitattun eyes ɗinsa na tsoro, tarwatsa ɗakin ya fara yi ya fiffige labulayen ɗakin, duka ɗaya yayi wa mirrow ya dagargaje, wadrobe ɗinsa ya faɗo dashi ƙasi, ya ɗago da makeken katifarsa da hannu ɗaya yayi wurgi dashi,
ya zamar da ɗakin kamar kasuwa,
jawo ƙofar ɗakinsa yayi ya ɓalla door sannan ya fice yana taku irin na ƙarfafan zakuna, ya sauƙo falo da ƙarfin gaske ya finciki ƙatoton plasman dake manne a jikin bango yayi wurgi da shi (wayyo my plasman🥺)
ya harhargutsa kujerun ɗakin, duk ya finfincike flawowin ɗakin, labulayen falon masu tsadar gaske na UK duk ya yayyaga su! gurnani yake na gasken gaske haɗe da ihu-ihu sai ta'adi yake ta yi musu...

Mommy kuwa tana sallah jin yanda Junaid yake ta gurnani yasa hankalin ta yabar jikinta,
Jikin ta ne yake kakkarwa sallar bazai yuba a halin yanzu hakan yasa ta sallame, da gudu ta nufi falo tana faɗin "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Junaid na shiga uku ciwonka ya tashi kuma babu maza a gidan...."

Itama Ayush tsabar tsoro jikin ta ne yahau ɓari yana kakkarwa ta kasa sauƙa daga kan gadon, lokaci guda kamar wanda aka zaƙuleta ta tashi ta gudu itama ta nufi falon,
Mommy murya na kakkarwa tace wa Ayush "ki koma ciki kar yaji miki rauni Ayush, ki shiga cikin ɗakin ki rufe, ki barni zanji da shi.."

Junaid kuma tsayawa yayi yana fuskantar Ayush ya zuba mata raunannun idanuwansa sai gurnanin daya ƙaru, itama Ayush tsayawa tayi tana kallon sa ta kasa motsawa.
Mommy ce tayo kansa da igiya a hannun ta zata ɗaure shi, ta lallaɓo ta bayansa ta wurga masa igiyar ai kuwa ita da igiyar haka ya yi wurgi da su wani irin ƙara mommy tasau Allah yaso ta akan doguwar sofa ta faɗo abun yazo mata da sauƙi,
a razane Ayush tace "Mommyyy" tayo kanta da gudu ta ɗagota, cikin ƙirar ƙarfi Junaid ya yo kansu gadan-gadan zai kai musu hannu da gudu Ayush ta shige tsakiyar sa ta rungume shi sosai jikinta na kakkarwa, ta ƙanƙame idonta rub tana jiran ta yanda za'ayi wurgi da ita sai kuma abun mamaki wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sau yana numfashi sama-sama ya rufe idanuwan sa rubb, wani irin hajijiya ne ya ɗebe shi zai faɗi ƙasi Ayush ta rirriƙe shi sosai a hankali ta kaishi ƙasi ta kwantar da shi,
kanta ta kwantar saman ƙirjin sa, tana jin yanda zuciyar sa take harbawa da ƙarfi-ƙarfi da haka har zuciyar sa ta dawo normal, sai dai jikin sa ba ƙwari ya kasa motsa ɗan yatsar sa ma still idonsa a rufe...

Mommy sake baki tayi tana kallon ikon Allah, a ranta tana furta "wacece wannan yarinyar? daga ina take? anya kuwa mutum ce, a karo na uku kenam ina ganin yanda take ceton Junaid, Alhamdulillah Allah na gode maka daka kawo mana ɗauki ka kawo mana wacce zata magance mana matsala..."
Murmushi ne akan fuskarta ga haƙorin makkan ta kuwa ya yi matuƙar yi mata kyau,
a hankali take tafe tayo kan Ayush tace "Ayushert ki taso..."
"a'ah Mommy jikinsa da sauran zafi idan na raba jikin mu ciwon zai iya dawowa"

a hankali yake motsi da hannayen sa da ƙer ya iya ɗago hannun ya ɗora su akan gadon bayan Ayush, idonsa ya fara buɗewa a hankali yana kallon dishi-dishi har idon ya washe,
Idonsa ya washe sosai ya koma fari sol kamar ba shi bane idonsa ya koma green colour ba,
Lips ɗinsa yake motsawa a hankali ya furta "Yushert..."
itama ɗagowa tayi suna fuskantar juna ido cikin ido,
"are you okay?" ya furta hakan yana kallon ta! kaɗa masa kai kawai tayi tana ƙoƙarin miƙe wa, Mommy tayo kan Junaid tana tana cewa "my son kana lafiya, tashi maza sannu ko" ta kai hannun ta kansa ta tallafa masa ya tashi idonsa kuwa na kan Ayush wacce ta kawar da kanta gefe ga ido ya yi jawur daga ƙarshe kuwa ta juya da gudu ta koma cikin bedroom ɗin su,
soyayyar Junaid zai mata illah sai dai yaƙi amince wa da soyayyar ta, zuwa tayi ta kwanta a saman gado wani sabon kuka ne ya sake zuwa mata, a cikin ranta kuwa tana faɗin "dole na koya wa zuciya ta hakurin rashin Yaya Junaid, meye amfanin soyayyar da ba Aure? meye mafita? wani shawara zan ba wa zuciya ta?"
tana kwance tana raya abubuwa da dama a cikin ranta, can kamar wanda aka zabureta ta tashi tana faɗin "na samo mafita, yes! yes!! yes!!!, zan ƙaurace masa na wasu kwanaki shi da kansa zai nemeni, ni kuwa nace masa indai bai aure ni ba bazai ƙara gani na ba tinda naga yanzu inbai ganni ba baya jin daɗi"
tana cikin wannan tunanin saiga Mommy ta shugo idon ta akan Ayush tazo ta zauna kusa da ita, tace "Ayush nagode sosai da ceton Junaid daga halin da yake ciki, haƙiƙa ke ƴer baiwa ce, kuma ke kece maganin Junaid! zan so ki Aure shi Ayush kuma naga kin shaƙu da shi sosai, soyayyar ku ya yi zurfi" tayi ajiyar zuciya sannan ta dafa kafaɗar ta tace "kun dace da juna"
juyowa Ayush tayi tana kallon Mommy tana motsi da leɓen ta a hankali tace "Mommy Yayana Junaid baya sona, yace kada na sake masa maganar Aure.." ta ƙarasa maganar tana zubda

20 / 44